Showing 45001 words to 48000 words out of 122554 words
Chapter 16 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt
Dake cikin aljihu ya Kira Sani Wanda ke Wajen su kasim Suna Shakiyansu na Abokai,yana ganin kiran Bello yayi Saurin matsawa gefe ya Daga Kiran cikin Muryan Bello mai Cike da karfin Gwiwa yace"Sani Juyo bayanka. ? Da Sauri Sani ya Juya Suka Hada Ido Da Bello bai mai mgana ba Illah alamar ya Taho Dayayi mai Da Hannu yanke Kiran Sani yayi ya Nufi Bello Ashe Duk Kasim na Kula Dasu Haka Kurum yaji jikinsa bai basa ba,yana ganin Sanda Sani ya karisa kusa da Ya Ali Suka gaisa kafin Su Juya Su Nufi Cikin Falon dasu Abba kabiru Suke kuma gashi Sauran Mintina a Dauran Yagane ya Ali yayan Aneesa ne Domin Bayan Isowarsu ya muktar ya kaisa Wajen Ya Ali Daya Sunusin ya gaishesu.
Ganin Zuciyarsa bata basa bane yasa yace ma Abokinshi Haruna yana Zuwa Cikin Sassarfa yabi bayansu Lokaci Daya yana Jin Faduwar gaba,Suna Shiga Falon Shima ya biyo bayansu Bello Dake bayan ya Ali ya bayyana Atsakiyar Falon Daidai Lokacin Daya Muktar ya Dago Suka Hada 4 eyes Dashi Ware ido yayi yana kallonsa Lokaci Daya gabansa na Fadi ganin Bello Hakama Su Abba Kabiru Suka wani Razana Da ganinsa Haka Kurum Sukaji Zuwan Bello Waje ba alheri bane Abunda ya basu mamaki yaron Da"a kace baya kasar kuma ya Suka ganshi anan wajen.
ya Muktar bai samu Zarafin Mgana ba Ya Ali yace"Ga Bello nan yazo ammh ya Rokeni da Kafin Adaura Aure Akwai Mganar da zai gabatar.."Ya Fada yana kallon ya Sunusu Wanda ke Zaune kusa da Limamin Masallacin Dake kusa dasu Wanda Shine zai Amshi Auren Aneesa,Ya Sunusi yayi jim yana kallon Bello ya Dauke kai Fuskarsa ba Annuri kafin yace"Ok Bismillah muna Sauraransa.."
Jin Haka yasa,ya Muktar Saurin Mikewa kamar Iska sai gashi gaban Bello ya saka Hannu cikin Zafin Nama da Bacin Rai ya Kama Jansa yana Turashi Waje lokaci Daya yana fadin"Get out....."Bello Shima ya Cije Cike da Taurin Zuciya yana Kallon Shi kafin yace"Cos of wht..? U don"t Want us to say d Truth baka Tunanin Hakan Zalunci ne..?
Yafada Shima Cike da Fushi kasim Dake tsaye Tuni yaji Yafara Zufa Hakama yan Falon da Hanzari kowa ya Mike ya Sunusi ne Daya ya Ali suka Taho Da Sauri Suna Fadin"Ash Subhanallah Muktar Lafiya..? Ammh ko Sauransu bayayi kara Damkan Wuyan Bello yayi yana Fadin"I Said get Out..Wlh in ka sake ka Fada Wata banzar mgana Wacce Ta lalata Auren nan zan Harbi kwakwalwarka da Bindiga.."Yafada yana Huci Idanuwansa Sun Juye Daga gani baya Cikin Hayyacinsa Alluran Sojojin Tatashi.
Su Abba Kabiru Suka Zaro Ido Suna kallon Ikon Allah Sani Ma Dake Gefe Jikinsa ne ya Fara Rawa,kalli Yadda Muktar ya Shake Bello kaninsa Toh ina gashi da basu Hada komai bs kila sai ya kusa Kasheshi Zufa ce ke Karyamomai yana Kallon Kasim Dake Jifansa da Wani Mugun kallo.
Bello da Jijiyoyin kansa Suka Mike Radau Idanuwansa Suka Chanza Launi Cikin Harzuka da Fushi Ya Daddage ya Hankade ya Muktar yayi Baya Ya Tsaya da Kakafunsa Domin Shima Akwai karfi Gyara Wuyan Rigansa yayi kafin yace"Sai dai ka kasheni ya Muktar ammh Wlh sai na Fadi gaskiya Bazan yarda Ayi Wannan Auren Cikin Duhu ba,ya kamata ka Dawo Cikin Hayyacinka kana Kunfar baki kan Wadanda basu Dauke ka da Kima ba har ka Manta Wadannan Daka ke Tsaye kansu Sun So Da yanzu bama Numfashi a doron kasa Sukayi Sanadiyar Sakamu Cikin maraici Suka Cinyemana Dukkan Dukiyarmu Suka maidamu bayinsu Suka Tona mana Asiri ammh Daga Karshe Sune kake Wani Hakilon Kokarin Son kaga Asirinsu ya Rufi bayan mu sun Taru Sun Tona mana Namu Asirin Shame of u ya Muktar Whh baka Kishin Abbi da Ummi baka Kishinsu baka Jin Dacin Mutuwarasu Kamar yadda nake ji Acikin Kirjina baka kwana da Bakincikin kashe maka iyaye da Sukayi Wlh ko yau Su Abbi Suka Dawo Gidan Duniya bazasu yi alfahari dakai ba..."Yafada Cikin Wani yanayi Lokaci Daya Kirjinsa na Tasawa kamar ya saki kuka.
Gabadaya Wajen Kowa Jikinsa yayi Sanyi da Kalaman Bello Hatta ko Ya Muktar din Idanuwansa Sun kawo Ruwa Cike da Rauni Su Abba kabiru kuwa saboda Tsoro kamar su Saki Fitsari ya Hashim kuwa Zare ido kadai yakeyi ya Ali da ya Sunusi Suka kalli Juna Cikin mamaki Kasim kuwa Zufa ce ke karyomai kamar An Watsamai Ruwa.
Liman ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Abar wannan kace nace din lokacin Daura Aure yayi fa,kai Saurayi matso kusa ka Sanar damu muke Tafe dakai in Bayaninka Abun a tsaya Aduba ne sai Aduba Insha Allah.,kowa ya koma ya Zauna Afahimci Juna.."Jin Haka yasa Kowa ya koma ya Zauna Jiki ba laka Kasim kuwa Durkushewa yayi Zuciyarsa kamar ta Fito Waje Saboda Fargaba Gaban Liman Bello ya Zauna bayan ya Jawo Hannun Sani Sun zauna Tare Cikin Jarumta yace"Allah gafartama Mallam ya Hallata ka Aurama Mashayi kuma Mazinaci Aure,bayan kuma iyayen yarinyar basu da Masaniya kan Hallayar Shi yaron da Zai Auri yarsu..?
Shuru Liman yayi kafin yace"A"a gaskiya baya Hallata Hakan Domin Muna Bin Tafarkin Annabin Rahma ne Sallahu Alaihi Wasallam,Domin Shi yagayama na cewa In Wani yazo Neman Auren Yarku Toh kafin ku bashi ya kamata ku Fara bincikan Addinsa da Hallayarsa da Sana'arsa da kuma Mu"amalansa da Mutane,kagane Baya Hallata a Dauki Mata Abama Wanda Ke Shaye Shaye da Neman mata,Sai dai in Cikin Rashin Sani ne.."
Bello ya Gyada kai yana Fadin"Gud...Mallam Toh Wannan Auren da zaka Daura kamar Shine misalin dana baka ne.."Da mamaki kowa ke kallonsa Barima kasim Dayaji ya Kusa kuka bai basu Zarafin mgana ba ya Nuna kasim yana Fadin"Mu"amalanshi da Mutane Bata Cika,ba Uwa uba kuma Dabi"arsa ba Nagartattaciya bace..Mashayi ne kuma Mazina ci ne ya Ali Auramasa Aneesa Wlh Cutarwa ne,yakamata ku Duba Wannan mganar.."Gabadaya Wajen ya Dau Salati Abba Kabiru ya Mike yana Fadin"Karya kake..Don tsani Kasim bai Chanchanci ka mai Kazafi ba, D'ana ba mashayi bane kuma ba Mazinaci bane Karya kakeyi.."
Yake Fada yana Nuna Bello Cike da Fusata Lokaci Daya Abba Garba ya Mike yana Rikosa ammh yana Zillewa Mirmishi Bello yayi kafin yace"Kaga Dattijo Rufe bakinka Tun yanzu kafin kaji kunya ban Fadi Abunda na Fada ba sai don Ina da Hujja...Sani Da muke Tare Dashi Abokin kasim ne Wajen Aikinsu Daya Akaduna gashinan zai muku bayanin komai.."
Yafada yana Nuna Sani wanda Ya Dukkar dakai ganin Ido ya Dawo kanshi Cikin Rawan Murya ya Ali yace"Muna jinka Bawan Allah..."Sani yafara mgana yana Fadin"Hakika Duk Abunda Bello ya Fada gaskiya ne Banso Ace na zama Silar bata Auren kasim ba..Ammh kuma Allah zai kamani matukar na sani kuma na Boye sani mganar gaskiya Kasim mashayin giya ne kuma Manemin mata ne Shi yasan nasan Komai Domin wajen Aikinmu Daya Dashi a kaduna, gani gashi ya Bude baki ya karyata Abunda nace.."Sai Aka Fara kallon kallon Kafin Kallon ya koma kan kasim Wanda ke Tsiyayan Zufa Cikin Bacin Rai Abba kabiru yace"Bude baki kayi mgana ka karyatamin Wadanan makiyan naka Dake gabana.."
Kasim kanshi na Duke bakinciki kamar zai Mutu baizai iya Rayuwa ba Aneesa ba,Bazai iya Juran Rasata ba Cikin karfin Hali yace",Ni bansan Mganar Da Suke ba Karya Sukemin Wlh Allah Abba...Kumin Rai karku ce bazaku bani Aneesa ba.."
Yafada Hawaye na gangaromai baki Sani ya saki yana Kallon Kasim Ido Cikin Ido Bello ko Kallonshi Shima yake Cike da Takaichi Mikewa Abba Kabiru yayi yana Fadin"Kunji ko..? Don Allah karku yarda Dasu..Dama wannan Akwai Takun Saka Tsakaninmu ku manta da Komai Lokaci ya Kure mu Gabatar da Abunda ya Taramu.."Yafada yana gyara zaman Babban Rigansa.
ya Ali da ya Sunusi Sukayi Shuru Suna Nazari,Yayinda ya Muktar ke Gefe kanshi Sunkuye Tunda Aka Fara mganar bai Dago ba...Ya Ali yaace"Shikenan bazamu Yanke Hukunci ba Domin Shaidar baki ba Shaida bace...Liman Agabatar da Daurin Aure.."Da Sauri Hashim ya Mike yana Fadin"A"a...Adakata..."
Gabadaya Aka Juya Ana kallonsa Cikin Mamaki Abba garba yace"Adakata kuma Hashim...? Gyada kai yayi kafin ya kalli kasim kai Tsaye yace"Kasim ya kamata ka Fito Fili ka Fadi gaskiya Domin karyan bata da amfani...Mganar gaskiya,Abunda Bello da Abokinsa Suka Fada Akan Kasim gaskiya ne...",
Ai sai Su Abba Kabiru Suka saki baki Suna kallon Hashim,ya muktar ma ya Dago kanshi Cikin mamaki yana kallon Hashim Shiko kasim Kuka ya Fashe Dashi Yana Fadin"Na yarda gaskiya Suka Fada...Ammh Allah na bari Tun Haduwata Da Aneesa na Tuba..na daina komai.."Yafada yana Hada Duka Hannayensu.
Kai Tsaye Hisham yace"Karya kake Baka Daina ba..." Gabadaya sai kallo ya koma sama Cikin Dattako Hisham yace"Saboda kana Kanina Uwa Daya Uba Daya bazan Ki bin bayan gaskiya ba...ya juya wajensu ya Ali yana Fadin"Mganar gaskiya Kasim Duka yana aikata Wadannan Zunuban,Kuma bai bari ba Kuma ko yayi alkwarin zai bari bazai iya bari ba...Abun ya zamarmai Jiki..Na Fadi gaskiyan Dana sani Bakuma zan Rokeku da ku Aurama Kasim yarku ba,Saboda ko Ni ne bazan iya bashi Auren yata ba Saboda in nayi Haka na Zalunceta..."Daga Haka yayi Shuru ya Sadda kai kasa,Abba Kabiru da Abba garba kuwa Jiki yayi Sanyi Ga Kunya Duk ta kamasu.
ya Ali da ya Sunusi Suka ji Wani Iri Acikin Ransu Lokaci Guda Suna godema Alla da basu Shiga gaba ba Wajen Ruguza Rayuwar Tilon kanwarsu ba,ya Muktar kuma Kansa yake Jinjinawa Shima kunya ta kamashi Bello kuwa Mirmishi ya saki yana kallon kasim Wanda ke kallonsa Yana Zubar Kwallah Lokaci Daya Zuciyarsa na kara Tsanan Bellon
Mikewa Bello yayi batare Daya cema Kowa komai ba ya Fice Daga Falon Waje ya Fita inda yaga Mutane suna Mganan Lokaci ya Tafi ammh ba"a Daura Aure ba ga masu Shed'a nan Sunja Tunga,suna jiran afara gudanar da Daurin Aure su fara Sheda, Bisa Wata Farar Kujera ya samu ya Zauna yana Cigaba da Latsa Wayarsa ransa Fes,ko Alama babu Damuwa Tare Dashi..
Acikin Falon kuwa Kasim ne ya Tuma Gaban ya Ali yana Fadin"Don Allah kumin Rai karku Hanani Aneesa..Wlh ina Sonta bazan iya Rayuwa babu ita ba...Na muku alkawarin na Bari Daga yau.."Yafada yana kuka kamar karamin yaro....
Ya Sunusi ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Karka damu koma ka Zauna.."Yafada yana Rike kasim Din Komawa yayi ya Zauna ya Share Hawayensa da Babban Rigan Dake Jikinsa,ya Sunusi ne ya kalli ya Ali kafin yace"In ganka Mana Ali.."Jin Haka yasa ya Ali ya Mike Lokaci Daya yana ce musu.."Kud'an mana Hakuri yanzu zamu Dawo.."Ba wanda ya samu Zarafin mgana Illah Gyada kai da Abba garba yayi suka Fice Daga Falon Suka bi ta Kofar da Sadasu da Cikin Gida,kafin Su Fita Yaya Ali yace"Muktar..."
Ya Dago kansa.."Kaima taso.."inji ya Sunusi..Jiki ba kwari yamike yabi Bayansu Suka Bace Daga Falon,sai Wajen ya koma kamar gidan makoki bamai mgana Abba Kabiru Tagumi yayi yana Jinjina kai Hakama Abba garba Shima kasim Kansa na Duke yana Salati Cikin Ranshi Lokaci Daya yana Jin In Har Bello yayi Sanadiyar Aka Hanashi Aneesa..Wlh sai ya Dauki mataki akansa.
Shiko Ya Hashim shima kansa na Duke Zuciyarsa kuma Tayi Sanyi Sosai yana Fatan kar su bashi Aneesa..Hakan kila zai saka Kasim ya Shiryu Liman kuwa Shuru yayi yana Jadadda Lamarin Acikin Ranshi Sani Kuwa Tun Bayan Fitan Bello Shima ya bi bayanshi.
Ki biya ki karanta cikin salama.
*ANITHA..*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_
 Â
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_
 Â
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*
 Â
*🅿�16*
"Sai da Sukayi Nisa da Falon kamar zasu Shiga Cikin Gidan,kana Suka Tsaya Cirko Cirko Suna kallon Juna,ya Ali ya kalli Yaya Sunusi yana Fadin"Sunusi ya kake ganin zamu Bullo ma wannan lamarin ne .? Nifa kaina yakulle...?
ya Sunusi yace",Umh...mganar Gaskiya Ali Indai Mganar mu bashi Auren Aneesa ne bai Taso ba,karka manta koda Take kanwa garemu Amanace akan mu Lokacin Abba na gabda Da Rasuwa bai da Wata mgana sai na Mu kula da Aneesa Kada mu barta Bayan bashi tayi maraici kuma yace matukar muka Bari Rayuwar Aneesa Ta Shiga wani hali bai yafemana ba, baka ganin in har muka yadda aka Daura Auran nan alhalin kuma mun sani Allah bazai Tambaye mu ba..?ka fa Duba hakkin yarinyar nan in mukayi Haka Hakika mun Cutar da Ita.."Yafada lokaci daya yana Saba babban Rigansa Cikin Firgici.
Ajiyar Zuciya ya Ali ya Sauke kafin yace"Wannan ma mganar bata Taso ba Sunusi,Mganar Bashi Aneesa bata,Saboda kada muyi Abunda zamu zo muna masu Nadama nan gaba ko ba Haka ba Muktar...?..
ya muktar ya saki Numfashi yana Fadin"Hakane...Toh ammh in Kuka yi Haka ya zakuyi da Dimibin Jama"ar Dake Waje Suna Jiran Tsammani .? Kai ya Ali ya Dafe yana Sakin Numfashi Shiko ya Sunusi Dafe goshi yayi Lokaci Daya yana Tura Hularsa baya Cike da Fargaba da Tashin Hankali,kafin ya juya yana Dora hannayensa Duka biyu Akungunsa yana Fadin"Ya illahi...Bakomai Haka Allah ya kadarra.."
Cike da Tsausayinsu Ya Muktar yace"Insha Allahu bazan bari ku Tozarta ba..Kuzo muje,Babu Abunda zai Chanza yanzu Za"a Daura Auren Aneesa da yardan Allah..."
Yafada lokaci Daya yana Juyawa yafara Tafiya Zuwa Cikin Falon Baki Bude ya Ali da ya Sunusi ke binshi da kallo kafin Sukalli Juna Lokaci Daya kuma Suka Rufamai baya Har Zuwa Cikin Falon Da su Abba kabiru ke Zaune Suna Jiran Tsammani Tunda kasim yaga Sun Shigo Fuska ba Annuri Jikinsa ya kama Rawa Hawayensa Suka Cigaba da Zuba Lokaci Daya Zuciyarsa na Harbawa...
Basu zauna ba Daga Tsayen ya Ali ya kalli Abba kabiru yana Fadin"Kuyi Hakuri da Abunda zan Fadamuku,mganar gaskiya mun Janye Mganar baku Auran kanwarmu Aneesa awannan Lokaci bisa la"akari da Abubuwan da Suka bayyana,kuma koda Aneesa Take kanwa garemu Tana da Hakki mai girma Akanmu matukar muka Rufemata muka Aurar da Ita ga D'anku Hakika mun Ci Zarafinta kuma Allah bazai barmu ba...Shiyasa muka yanke Shawaran Mu baku Hakuri Don Allah kuyi hakuri mu bar mganar wannan Daurin Auran Fata zaku Fahimce mu,bisa yadda muka sa kuka baro garuruwanku muka bata muku Lokaci.."Daga Abba kabiru Har Abba garba ba baki sai Zufa Suke Sharewa suna kallon Juna Cike da Kunya da Takaichi.
ya Hashim ne da Liman ke Gyada kai Alamar gamsuwa Liman yace"Mganarka gaskiya ne Aliyu...Hakan Shine Daidai..."Shiko Kasim kasa ya sake Durkushewa Yana Fadin"karkumin Haka Don Allah karku ce zaku Rabani da Aneesa Ina Sonta Itace Rayuwata Na muku alkawarin zan bar Duka Abunda nakeyi Daga yau Don Allah karku Hanani Aneesa.."Yafada Hawayensa na kara Gudu Lokaci Daya yayi baya Dafe da Kirji Abba kabiru Dake kallonsa yaji kamar ya Fashe da Kuka Saboda Tsausayin D'anshi.
Baya Yy Ali ya juya bayan ya saka Haban Babban Rigansa,yana Share Kwallar Data Zuraromai ya Sunusi ne ya Rikesa yana Fadin"Kabi Ahankali kasim,kayi Hakuri Haka Allah ya kaddara ina maka Fatan Allah yasa Sanadin Shiryuwanka kenan..."ya Hisham ne kadai ya amsa da Ameen Su Abba kabiru ko kansu na Duke suna Tunanin Wannan Wani Irin Tozarci ne..
ya Muktar ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Allah gafarta mallam don Allah Ajirani kadan in Dawo yanzu za"a Daurama Aneesa Aure babu Abunda Zai Chanza..."Yafada yana Juyawa da Sauri ya Fita Zuwa Waje,Kowa da Ido ya Rakashi Cikin Mamaki Hatta ko da Kasim Sai da ya Dakata da Kukan Dayake Yaji Zuciyarsa ta Tsaya cak Lokaci.
Ya Dade yana Waige Waige Cikin Haraban Gidan kafin idonshi ya Hangomishi Bello,Zaune bisa Kujera yana latsa wayarsa,kafin ya karisa Wajensa sai da ya biya ya bama mutanensa Hakuri kan Yanzu za"a Daura Auren,Bello na Zaune kawai sai jiyayi an finciki hannunsa Lokaci Daya kuma anfara Jansa,Da Sauri ya Dago Lokaci Daya yana kallon ya Muktar Dake Jansa Cikin Fushi kuma yaki Bari yaga Fuskarshi bai Direshi ko"ina ba sai da Suka bar Haraban gidan Suka Fita Daga get Din Gabadaya kana ya Sakeshi Lokaci Daya yana Fuskantanshi.
Bello ya tsaya da Kakafunsa yana kallon Fuskar ya muktar bai damu ba Illah saka wayarsa Dayayi Cikin Aljihun Gaban Rigansa,Lokaci Daya kuma yana Saka Duka Hannuwansa ya Harde kirjinsa ganin kallon Da ya Muktar ke mai ne yasa Ya Dauke kai gefe ya Raba gefensa zai Wuce,Da Sauri ya saka Hannu Cikin Fushi ya sake janyosa Zuwa gabanshi Lokaci Daya yana Hararansa,kafin yace"Kayi Nasaran B'ata Auran yanzu Dawa kakeso Adaura...?
Tamke Fuska Bello yayi kafin yace"Bangane ba ya Muktar...? Look nifa Awannan al'amarin Taimakon Aneesan nayi,kuma Kaima na Taimake ka Domin da an Daura Auren Lbrin ya Fito kome ya Faru dakai za"ai kuka."ya fada yana Zakuda kafada Irin ko ajikinsa din nan.
Ajiyar Zuciya Ya Muktar ya Sauke kafin yace"naji...Toh yanzu ya zasuyi da jama"ar da Suka gayyata..? Kai tsaye yace"Su basu Hakuri mana Yaya..."Hararansa ya Sakeyi kafin yace"Ita Aneesan fa...? Baka Tunanin Wani Hali Zata Shiga in ta samu lbri..? Fuska ya bata na gajiya da Irin Tambayoyin Ya Muktar Cikin kosawa yace"Sai ta koma mkranta Is dat so..."Kirjinsa Ya Muktar ya kaima Duka kafin yace"U are Animal Bello...Baka da Zuciyan mutane...Baka da Tsausayi ko kadan,toh baka isa ba Tunda har Ka lalata wanchan maganar toh kai zaka maye gurbin kasim Wuce muje yanzu Dakai zaka Daura Auren..."Yafada cikin Tsawa Lokaci Daya yana Fuzgar Hannun Bellon Da karfi
Shiko Bello Kamar Aradu Haka yaji Mganar,Cikin Zaro ido yace"Ya Illahi ya..muktar Wht of all dis kuma..? Plz dont do dis for me am begging u ban taba kallon Aneesa Amtsayin Wacce zan iya Rayuwar Aure da ita ba...infact ma Ban Shirya yin Aure yanzu ba...plz leave my Hand.."Yake Fada kamar yayi kuka ammh ya Muktar ko Sauraransa Baiyi ba Haka yake Jan Hannunsa Har Zuwa Cikin Falon Mutanen Dake Waje Suka bisu da kallon mamaki Sani Dake Cikin Abokansa ganin Haka yasa Shima da Sauri ya Rufa musu baya.
Ya Muktar bai Dire Bello Ko"ina ba Sai agaban Liman kafin Shima ya Zauna Kusa Dashi Lokaci Daya yana Dafe Hannunshi,domin yaga Bellon kokarin Tashi yake, Hannu Daya ya Zura Cikin Aljihun wandonsa ya Fito da Kudi Bandir Biyu Daya ya ijiye gaban Liman Daya kuma gaban Hashim kafin yace"Wannan Sadakin kasim ne na maido muku da kayanku..."Yafada yana Nuna da Kudin Dake gaban Hashim kafin ya Dora da Fadin"Wannan kuma Sadakin Aneesa ne...Zan ma Kanina Bello Walicci..."..
Gabadaya Falon sai ya Dau Shock ya Ali ko Da ya Sunusi ko Junansu Suka kallah Lokaci Daya kuma Suka Saki Mirmishin Farinciki Abba garba ko