Showing 99001 words to 102000 words out of 122554 words

Chapter 34 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt

26 Jan 2025

23744

ya Budemana kofar Baya shi yafara Fitowa sai ni wanda muke Rike da Hannun Juna Mallam Inuwa da Sauran Securitys din gidan gabadaya suka zubamana ido Barin ma Bello da suke kallonsa cikin mamaki ganinsa tsaye bisa kafafunsa.


Da hanzari mallam inuwa ya karisa bakinsa har kunne yake Fadin"Yallabai kai ne nake gani tsaye agabana..? Kai ya gyada mai kafin yace"Nine mallam Inuwa..Allah ya bani lafiya.."Yafada yana sakarmai Mirmishi.


Zubewa yayi agabanshi yana Mai Nuna Farinncikinsa Cike da murna,haka ma Securitys din gabadaya suka Saramai alamun Barka da Arziki Gajiya nayi da tsayuwa yaji na Fara zamewa zuwa Jikinsa yasa ya kalleni yana Fadin"Kin gaji ko..? Sannu mu shiga ciki ki kwanta.."Rausayar Dakai nayi ina Fadin"Zazzabi nake ji.."Rumgomini yayi yana Fadin"Ayyyh..Am srry Duk nine ko.? Bazan kara baki wuya ba kinji My Anee..."Batayi mgana ba Illah kara lafewa bisa jikinsa datayi tana Shakan Kamshin Turaranshi.


Modibbo Tuni ya Shige ya barmu Afalon Farko muka Ciro da Alheri Itama cikin mamaki ta zube Tana gaishemu shine kadai ya amsa ni ban iya mgana ba sai dai binta da ido har muka wuce zuwa Falon Anty Rahila tana binmu da kallon Mamaki,nan muka tarar da Jummai tana gyara Falon Tana ganinmu ta zube itama tana gaishemu Lokaci Daya tana mamakin ganin Bello yana Tsaye da kafafunsa kamar bashi bane aka Fita dashi Cikin keken Marasa lafiya.


Modibbo Shashen Daada ya Iskesu ya muktar da Anty Rahila Sakamakon Jiya ya Dawo Daga India Checkup yana gida bai Fita ba Ganinsa kawai sukayi kwatsam ya muktar ya kallesa sanda yake zama Bisa Daya Daga cikin Kujerun Falon Cikin mamaki yake Fadin"Ikon Allah Modibbo Allah yasa dai lafiya..? Yafada yana kallonsa Mirmishi ya saki kafin yace"La lafiya lau...Ji idanuwan Daada toh sha kuruminki taremuke da Baffalen da kanshi.."Hararansa Daada Tayi kafin tace"Kaji dashi dai..Nidai nace banayi Dakai Bello dai shine megidana ayi gaba.."Dariya ya saka yana Fadin"Allah ya raka taki gona..Daada Ai ni ko akafa aka Dauran ke na kwance.."


Dakuwa Ya muktar ya sakarmai yana Fadin"Kaniyarka Daadar ce zaka ce ma haka..? Dariya ya karasakawa kafin yayi mgana Bello da Aneeesa sun sawo kansu Falon Bakinsu Dauke da sallama Gabadaya Daada da Anty Rahila da ya Muktar suka zubama kofa ido Kusan Daskarewa sukayi ganin Bello Yashigo Shida Aneesa Dukawa yayi ya Sabule Sawun cikin Dake kafarsa itama Aneesa ya taimakamata ta cireta nata suka Dago Atare suna kallon Juna kafin su Damke hannun juna suna bin Fuskokin su Ya muktar da kallo wadanda gabadaya suka mike sun kame waje Daya kowa na Salati da hailala acikin Zuciyarsa.


Cikin Mirmishi Bello yace"Daada,ya mukatar,Anty Rahila...Nine dai...Jiya Allah yayi ikonsa Na tashi Bisa kafafuna ni na Hana akiraku saboda ina so na baku mamaki ne."Yafada kamar zaiyi kwallah ai sai Ya Muktar ya Zube kasa ya Daga Hammu sama yana Fadin"Alhamdulillah...Alhamdulillah...Allah mungode maka..Allah mungode maka kai ne Shugaban Halittun Duniya...Baka Haifa ba kuma Ba"a haifeka ba...Godiya ta tabbata ga Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam.."Yafada Lokaci Daya Hawaye suna kwaranyowa Daga kwarmin idanuwansa,Daada da Anty Rahila suma godiyar sukema Allah suna Share kwallah Cikin Farimciki Bello ya Saki Hannun Aneesa ya karisa ga Dan"uwansa ya Duka suka Kamkame juna Lokaci Daya Cikin Tsantsan Farincikin ahaka suke mike tsaye Daada tazo ta Hadasu ta Rumgumesu cikin kuka take Fadin"Allah mungode maka...Allah Abun godiya.."Ita kanta Aneesa sai da taji Tahowar kwallah Cikin Sanyin Jiki ta karisa ta Fada Jikin Anty Rahila suka Rumgume Juna,anan ne taji jikinta da Zafi da sauri ta Dagota tana Fadin"Aneesa baki da lafiya ne..? Jikinki ya Dau zafi.."?


Da Sauri Bello ya saki ya muktar da Daada yana Fadin"Eh bata jin Dadi...Taho my Anee kije ki kwanta ko zamu tafi kiga Dr ne.."?Yafada yana Rikota kai ta girgiza tana kwanciya Bisa kafadansa cikin Sanyin murya tace"Zan kwanta.."kura mata ido yayi yaga har ta Dan Fada Rikota yayi sosai Bisa Jikinsa yana Fadin"Oya muje ki kwanta ki Huta...In kin tashi in zazzabin bai sauka zai mu tafi kiga likita ko..?kai ta gyada mai suka Fara Tafiya su Daada suka bisu da kallo Cike da Sha"awa tafiyar Aneesa ne ta Fallasata Mirmishi Anty Rahila tayi cikin Ranta tana Fadin"Aneesa ta girma..."cikin jin Dadin mara misaltuwa Ya muktar ko baki yaki Rufuwa Shi ya Dauki waya ya kira y Ali yana Labatarmai wannan Daddalan Labari kowayaji sai ya saaki kabbara cike da Farinciki Ita kuma Daada ta kira Adamawa ta sanar ma Baffa hardo Shima haka yayi ta kabbara yana Zubama Allah kirari yaji Dadi sosai kuma ya tabbatar da Babu Abunda ya karfin Allah Tabbas Kudaran Allah ne yasa wani Abu ya Giffta aka hako wannan Jakin da aka binne da Rai wanda akayi Ma Bello Shihiri dashi.


Haka Abun yafaru dama an binne Abun atsakanin Dajin Abuja da Minna ne, Cikin Ikon Allah sai Titi yabi ta wajen nan da nan Turawa suka saka inji suka markade kasar wajen suka hako abun batare da sun sani ba,dama kuma makarin karyewar Asirin Shine ahako wannan Jakin Dake cikkin Rami wanda aka Daure Wuyanshi da layan Sihirin,toh wajen hako Abun Inji ya Darkake jakin Shi kuma layar ya bar Wuyan Jaki bayan injin din yayi Fata Fata dashi ,wannan Shine Dalilin Daya sanya Bello ya Taka da Kafafunsa kamar bai taba wani Abu mai kama da Jinya ba.


Dakinta na da ya shiga da ita ya kwantar da ita bisa gado ya lulluba mata blanket yana kallon Fuskarta yace"I love...U my Anee...Banajin Dadin ganinki ahaka..Ki gafarce ni banyi da niy..."Bai karisa ba ta rufemai baki tana girgizamai kai tace"Kadai na bani Hakuri kada Allah yayi Fushi dani Abunda yake mallakin ka ne fa ka karba B.love...Ko yanzu kace kana Bukatata ni mai mika Wuya ce...Kasani ni matarkace kuma Rufin Asirinka...Ina sonka Gwarzona ina Kuma alfahari da samunka amatsayin mijin Aurena..."Tafada tana Sakarma Hannunsa Kiss Dadi ya kamashi ya Duka ya bata sumba mai tsawo kafin ya mike ya zauna kusa da ita yana matsa Tafin Hannunta yake Fadin"Kece Abun Alfaharina Aneesa...Naso na Tafka asara da na bari kasim ya Aureki da yanzu bana cikin Farincikin Danake ciki yanzu..I realy Love u my wife.."Yafada yana Kara matsemin Hannu Lumshe ido nayi cikin so da Kauna nace.."Love u...Forever and Ever...B.love.."Nafada ina jin kamar na Bude Zuciyata na sakashi Saboda yadda Zuciyata ke Bugawa da kowani Harafi na Soyayyarsa.


Yana ta matsa min Hannuna yana min kalamai kauna mai Tsayawa azuciyar Masoyi Har barci ya kwasheni sai da nayi barci kana ya lallaba ya Fito Falon Daada nan fa aka hadu ana ta Hira kafim kace kwabo labari ya kai kunnen yan"uwa da abokan Arzuka sai kiran waya ake ana Tayasu murna,Uncle Aminu ma sai gashi ya kira kila Ammi ta gayamai Su Abba kabiru ne kadai ya muktar ya manta dasu bai kirasu ba,kuma ba wanda ya Tunamai yan'uwana sai kiran wayata suke domin Tayani murna ammh basu samuna Domin ina kwance ina barci Anty Rahila ya baiwa wayar take dauka tace nazo bana jin Dadi ya muktar kuwa yana Cikin Farinciki wanda saboda murna yace gabadayansu zasu tafi su sauke Farali wannan Shekarar Harda Baffa Hardo Tunda Daada ta sanar da Bello komai na taimakon shi Dayayi kan wannan Ciwon nashi Bello yaji Dadi kuma yace insha Allahu zai taka har Adamawa ya kaima Baffa hardo gaisuwa tare godiya Modibbo kuwa Tundazu ya koma shashen Bello ya Shige ya kwanta yana ta waya da Raihana,yana sanar da ita Wannam Shekaran Allah ya kirasa zai sauke Farali nan tayashi Murna kafin su shiga Hiran Soyayyahrsu.


Aneesa bata tashi ba Sai Bayan la"asar kana ta tashi Shima Anty Rahila ce ta tada ita ta mike tana Mika Lokaci Daya tana Fadin"Anty Rahila anyi Azahar ne..? Hararan wasa ta kai mata tana Fadin"Eh lalle toh har la"asar anyi Azahar kuma sai dai na gobe..ki tashi kiyi sallah mijinki ya hana atasheki yanzu ma yatafi shashenshi ne,yasa na shigo na Tadake."Saukowa Tayi Daga kan gadon Tana Fadin"Allah Sarki B.love.."Tafada tana gimtse baki jin kasanta na mata Zafi Da kallo Anty Rahila ta bita kafin tace"Kin shiga ruwan zafi kuwa..? Cikin jin kunya Ta Daga kai batare Data waigo ba Anty Rahila bata mata mgana ba ta nufi Tiolet din ta Hada mata ruwa mai Zafi ta Fito Tana Fadin"Ki gasa jikinki sosai...In kina so kidaina Dingishi kuma wajen yayi Saurin warkewa..Ba"a taurin kai awannan harkan in baki kula da kanki ba ke kika sani.."Tafada tana rabata ta Fice Daga Dakin Kunya ta kara kama Aneesa tayi mirmishi ta Fada Tiolet din.


Taji Dadin Ruwan Dumin sosai Ruwa biyu ta chanza kafin tayi wanka ta Dauro alwala ta Fito,cikin kayan ta Tun na gida ta saka wata Doguwar Rigar Atamfa Tunda kayansu na Mota ba laifi taji Dadin Jikinta ta Daina ma Dingisa kafar sai da nayi sallar Azahar nayi la"asar na sallame kenan Bello ya Turo kofa ya Shigo yana Fadin"Anee wannan barcin yayi yawa.."Yafada kenan sai kuma ya ganni tsaye ina Kokarin kwabe Hijabin jikina


Mirmishi ya sakarmin yana Fadin"Ashe kin tashi..? Kaina Gyada mai ina Fadin"Anty Rahila ce ta tasheni nayi sallolin dake kaina.."Na fada ina hamma Riko ni yayi yana karba Hijabin hannuna ya ijiye yana Fadin"Sai da fa nace karta ta tasheki..ya zazzabin..? Ya sauka..?kai na Damgwabe ina Fadin"Daidai nake jina sai dai yunwa dana ke ji.."Mirmishi yayi yana lakacemin Hanci yace"Oya muje na baki abinci ki ci ki koshi har ki kasa tashi.."ware ido nayi shi kuma sai ya Riko hannuna yana Dariya kan Kafadarsa na yada kaina Muka Fita Daga Dakin Zuwa Falo.


Babu kowa cikin Falon na Daada,Zaunar dani yayi kan kujera yaje ya Karbomin Abinci a kichen yazo ya Zauna kan Cinyarsa ya Zaunar dani yana Bani abinci har sai da na koshi,Yana cikin bani ruwa sai ga Daada ta Fito Daga Daki baki ta rike tana kallonmu Lokaci Daya take Fadin"Lalata..Kai Bello miye haka nan fa ba gidan ku bane.."


Kallonta yayi yana Fadin"Daada ki koma ciki kawai in dai bazaki iya gani ki kyale ba...Nifa bana iya zama ban rabi my Anee ba itama Haka.."Dariya Aneesa tayi ganin yadda Daada tayi,bata samu Zarafin mgana ba Modibbo ya Shigo ganin mu Ahaka yasa ya shafa keya yana Fadin"Au Daada kema kin gani ko..? Haka nake fama muna kano Baffale na kan keke ya iya barna.."Yafada yana Dariya Hararansa mukayi Duka Tare Kada kai Daada tayi kafin tace"Umh...Naga alama Marasa kunya.."Tafada tana juyawa zuwa Cikin Bedroom dinta muka Bita da Dariya,Modibbo ko Waje yayi yana Fadin"muma mun kusa shiga wannan Stage din..".


Mudai bamu bi ta kansu ba..Bayan ya gama bani Abinci Muka koma muka lafe Bisa kujera ina kan Jikinsa ina waasa da Sajensa muna Hira sama sama sai da aka kira sallar mangariba kana muka rabu yatafi masallaci ni kuma na shiga daki nayi tawa ina idarwa sai ga Hibba ta shigo Dakina da gudu tana Fadin oyoyo Anty Anee..Rumgumeta nayi na Dagata sama ina Murnan ganinta Daganan muka Fita Falon Anty Rahila inda na isketa tana waya da Ya Sunusi har tabani muka gaisa yana min Barka da Arziki naji kunya sosai,nan ya bama su Mama Yana da Falmata mukayi Mgana suna kara nuna Jin Dadinsu Ashe hardasu a wadanda Ya Muktar ya zana zamu hajji bana naji Dadi sosai.


Dakyar Daada ta kori Bello ya koma Shashensa Da yace anan zai kwana ga matarshi bazai kwana da kato ba Modibbo na Dariya yana Fadin Allah ya sakamun Baffale nine kato,hararansa Bello yayi yana Fadin"Toh in ba kato bane mace ne kai.."Daada ko ta iza keyarsa tace ya Fice mata Daga Shashe bata son Rashin Kunya bai da yarda zai yi Haka ya Tafi Ni kaina banji Dadi ba Domin na saba kwana Bisa Kirjin Mijina Nima ina Tura baki da kunkuni na Nufi Dakina ina Fadin"Daada wai ina ruwanki da Shiga tsakanin miji da matarsa.."Tace an shiga din ba anan zaku man rashin kunyarku na Diyan zamani ba..Su ya muktar naji suna Dariya Dole dai kanwar naki Hibba nace tazo Tatayani kwana,ammh Kusan Raba Dare mukayi muna waya na Tambayeshi ina Modibbo yace yana cikin Daki shi kuma Falo ya Fito bayaso yaji Sirrin ma"aurata Dariya kawai nayi muka cigaba da Soyewarmu.


*******
*Kaduna...*
Â
Kasim da Aisha kuwa suna Cigaba da soyewarsu bata Tunanin wani Abu zai iya Faruwa anan gaba cikin wannan Halin ne ta fara ciwo,zazzabi komai taci baya zama acikinta Tunda kasim yaga Haka Hankalinsa yatashi yafara zargin Ciki ne nan ya dauketa suka tafi Asibitin Barau dikko dake Kaduna agwajin Farko Ciki dan Wata uku ya bayyana ajikin Aisha


Ta firgita sosai nan ta Shiga Rusa kuka,Ammh sai Kukanta ya tsaya Jin Kasim na rokar likitan ya taimakamai ya Zubar da Cikin Jikin Sadiya cikin mamaki ta waro ido tana kallonsa kafin tace"A zubar fa kace..? Toh saboda mene..?.


Kasim ya wurgamata wani bazan kallo kafin yace"Eh haka nace..Saboda mene kike Tambaya? in kika Haifi D'an Shegen wa zai zama Ubanshi balle har yamai Dawainiya.."Cikin mamaki da Nadama Aisha ke kallonsa kafin tace"Akwai wanda ya kamata ya Zama Uban abunda ke cikina Bayan kai,Saboda kaine Ubansa kafi kowa sanin banta sanin wani Namiji ba bayan kai.."Wani Banzan Kallo ya Cigaba da Jifanta dashi bai mata mgana ba illah yafice ya barta Domin Tuni Likitan yace su barmai Office su wannan Asibitin ba asibitin Zubar da ciki bane..


Da Hanzari Aisha ta mara mai Baya Cikin kuka yana Shirin Tada motar ta Fada Motar tana Haki Bata samu zarafin mgana ba ya Figi motar suka bar Haraban Asibitin sai da suka Dauki Hanya kana ya kalleta cikin Kakkausan Murya yana Fadin"Ki tabbatar da in baki bari an zubar da Cikin nan ba...Toh sai dai ki zama uwarshi da Ubanshi ke kadai Domin ni ban Shirya fara Haihuwan Shege ba.."Aisha ta Kuramai ido tana Hawaye tace"Kasim kasan kuwa me kake Fada..? Hararanta yayi kafin yace"Bansani ba..."Yafada Cikin bacin Rai kara Rushewa Tayi da kuka tana Fadin"Wlh bazan Zubar da cikin jikina ba...Da Farko munyi kuskuren aikata Zina bazamu Tuba ba bayan Abunda muka Dade muna aikatawa yafito Fili ba..Ba zan yadda na kara aikata wani Zunubin ba Kila ma wajen yunkurin zubar da Cikin Jikina na Mutu me zan ce ma Allah in na mutu cikin wannan Halin..?


Ko kallonta bai yi ba Daidai Lokacin da suka kariso gida ya kashe motar yana Fadin"Alrigt...Tunda Haka kika Zaba ki sani Lokacin Rabuwarmu Tazo kada ma ki kuskura ki Nuna kin Taba sanina.."Ya fice yana Daukan wayarsa da Sauri Aisha ta Bude Murfin Mota ta Fice Da Gudu ta tari gaban kasim tana Fadin"Bangane Nufinka ba..Ina alkawarin da kamin na zaka Aureni komai Runtsi..? Ka Rifamin Asiri kasim ka Aure ni mu Rufama juna Asiri.." tafada tana Kara sakin kuka Kamar Ranta zai Fita


Dariya ya saki kafin yace"Na Aureki..? Kinyi kuskure Babban Aisha Da kike Tunanin zan iya Auranki kinganni nan Bazan iya Auran kowacce mace ba sai Aneesata,in kuma ba ita ba sai dai na samu wata yar mutumci na Aura bake ba gantalalliya wacce taci amanar Tarbiyar iyayenta ba.."Yafada yana Kallonta Cike da Raini.


Aisha ta Dago tana kallon Kasim Cikin mamaki tace"Ka cuceni kasim...Tsakani na dakai Allah ya isa..Kuma Aneesa Dakake mgana har Abada bazaka taba samunta ba Mugu Azzalumi insha Allahu sai kagani.."Tas..! Ya sharara mata Tafi sai da ta kife Cikin Fushi yake Fadin"Ke kika Cuci kanki Aisha Domin bani nakira ki ba ke kika kawo kanki da Kafarki..Kuma bari kiji na gayamiki albarkacin Aneesa kikaci har na Kulaki ammh ke baki kai matsayin Da zan Hada Jiki da ke ba..Na dai mori jikin ki ne kawai Malama ki tashi ki kwashe kayanki ki Ficemin Daga Gida Asarrrariya mara Tarbiya.."Yafada yana Nuna ta da yatsa Lokaci Daya ya Shure ta da kafa ya Shige cikin Falonsa.


Kuka Aisha take na Nadama da Danasani,kafin ta rarrafa ta mike tana Tangadi ta shiga cikin Falon yana Zaune kan kujera yana Daga kwalba ko kallonshi batayi ba Ta Shiga Cikin Bedroom din ta Shiga Hada kayanta tana kuka Tana Cikin Tura kayanta Cikin Akwatunta ne taci karo da wani karamin Littafi mai Dauke Adireshin wani gida akatsina tana gani jikinta ya bata Adireshin Gidansu Kasim ne bata tsaya wani Tunani ba ta Dauka ta Tura cikin akwatinta ta Fito Tana kuka jaye da Trolley dinta ta Tsaya gaban Kasim tana Fadin


"Zan tafi...Ammh ina so kasan wani Abu Daya Zan dawo...Zan dawo na kawo maka Abunda kayi Sanadiyar samuwarshi...Da izinin Lahi yadda kayi Sanadiyar Lalatamin Rayuwa sai rayuwarka Ta D'aidai'ce...Allah ya isa Tsakanina dakai...Na barka da Allah shi zai min sakayyah mafi girma.."Tafada tana Sakin Gunji kuka kafin taja Jikinta ta Fice Daga Falon tana kuka ko kallomta Baiyi ba banda ma Mirmishin Mugunta da Kasim ke saki Wayarsa ya jawo ya Kira Haruna yana gayamai Abunda ya Faru.


Cikin Rashin Jin Dadi Haruna yace"Kash...Meyasa kayi mata Haka kasim ina tsoron fa watarana..? Cikin maye Kasim yace"Dillah manta da ita babu abunda ta isa tayi karamar yar iska ce.."Yafada yana Dariya Shidai Haruna Jinsa kadai yakeyi ammh kuma wata Zuciyar nashi na Tsoron Faruwar wani Abu.


Sadiya tana kuka Ta Shiga Adaidaita zuwa Tashar mando nan ta samu motar maiduguri,Ta Shiga ta Rufe Fuskarta da Hijabi tana Rusar kuka Lokaci Daya tana ma kaduna kallon karshe,Domin ta yarda bayan Rasa mutumcinta datayi harda karatun da iyayenta suka ci Buri akanshi shima ta Rasashi Kasim ya Cuceta da izinin lahi sai yaga Sakayyah.


*****


*ADAMAWA..*


Tafiyar jirgi mukayi Zuwa Adamawa bayan mun kwana Biyu agarin Abuja Dukkanmu muka Tafi Ya muktar,Daada,anty Rahila da Hibba junior sai modiboo da ni ba Bello,muka tafi kai naga Tarin Dangin su Daada kyawawa Farare Ashe anan Mijina ya Debo kyau da Tsari irin na Fulani,




Baffa Hardo kuwa Rumgume Bello yayi yana Murna Haka Yan"uwa aka zagayemu ana Nuna ni amatsayin matar Baffale,suna mamakin yadda nayi Namijin Kokarin Kula Da Bello kai gaskiya naji Dadin Zuwan mu Adamawa Sosai Sai da muka Shafe kwana Hudu kana muka Dawo Abuja nan muka bar Modibbo sai ya kwana Biyu zai Dawo bayan mu rabu kan in zai dawo zai zo da passpost din Baffa hardo saboda Shirin tafiya aikin Hajji nan da wata Biyu,Tunda shikadai ya rage musu duk sun rasu sai dai ya"ya da suke tasowa sukayi Aure suka Hayyafa.


Mun Dawo Abuja da kwana Daya Bello yakoma kano Saboda zai Shiga Cikin Jami"a ya saka Hannu dawowrshi aiki ammh bazai Fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login