Showing 114001 words to 117000 words out of 122554 words

Chapter 39 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt

26 Jan 2025

23746

Wani Salo,Da Sauri na Kara kamkameshi Cikin Farinciki Shi kuma yana ta Shinshinar Wuyana Cikin Fitan Hayyaci na Dago kaina na Hade bakinmu Waje Daya Cikin Shauki da muradi mai girma Shikenan Fushi ya Tafi sai kuma muka Hau Siradin Neman Ladan Allah.




Kibiya ki karanta cikin Salama.






*Anitha...*
8/22/20, 10:26 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_


Â
*Wattpad:Janafnancy13*


*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*


    *🅿�39*


..."kalaman da Mijina ya Fadamin su suka saka na watsar da Duk Wani Tunani acikin Raina na Rumgumi Mijina muna cigaba da gudanar da Rayuwarmu cikin Farinciki da Muradin Juna..


Na toshe kunnuwa na kamar yadda yace ko B.kaita tazo zata fara gayamin zan Dakatar da ita da cewa nafi kowa sanin Waye Mijina bazai taba yin Abunda zai yi Failing dina,ba mganar wasu yan matan Jami"a nasan basa gabansa da wannan na samar ma kaina lafiya bana jin Labarin komai sai na samu lafiya,wani lokacin yana Dawowa gida zai Kashe Duka wayoyinsa saboda Bani Dukkan Lokacinsa kuma Hakan na matukar min Dadi.


Sai lokacin na Fara zuwa awo anan Wani Private Hospital mai Suna International Hospital Dake Cikin Birnin kano,shi yake kaini Duk bayan sati hudu nayi Awo kuma ya Jirani ya Dawo dani Wahala da kuma Dawainiyar mijina akaina Shiyake karamin Kaunarsa acikin Raina.


Wata Daya Hibba tamana kafin Hutunsu ya kare Nida shi muka je Abuja muka Maidata,chan mukayi Weeked din mu sai Saturday muka dawo da yammah,ba inda nake zuwa koda yaushe ina gida ina Fama da kewa in nagaji da kallo na koma latsa waya domin ni haryanzu ban saba da Chart ba,wani lokacin nayi karatun Littafi Tuni kewar gida ta Fara zuwarmin Raihana kuwa nafikowa matukar kewarta Ita da Modibbo Saboda Sanda Suna nan ban Shiga wannan kewar ba,ganin zaman kadaicin yamin yawa yasa na sakashi in zai Fita zuwa wajen aiki sai ya kaini gidan Ammi ko Wajen Anty Aisha na Wuni sai in ya tashi Daga cikin Makaranta ya biyo ya Daukeni bama komawa gida sai mun Biya Munyi Takeway watarana kuma muci awaje kafin mu karisa gida,Rayuwarmu dai muke gudanarwa gwanin Ban sha"awa.


Ranar kawai tun 7 zai shiga cikin Makarnta ina kwance ina kallonsa yana gyara zaman Hulan kansa sanye yake cikin Wani Farin Boyel,mai Sharara domin Har ana iya hango Farar Vest din Dake Jikinsa babu aiki jikin kayan Domin Dinkin Zamani ne,sai links din da akama Gege da Gefen Hannun Kwalliya kanshi bakar hula ce yake murzawa kamar yadda kafarsa ke sanye da bakin Sawu ciki na Fatar Damisa Haka Agogon Hannunsa ma baki ne na Fata na kamfanin Rado.


Kallona yayi yana Mirmishi kafin yace"Mai ciki yadai..? Fuska na tabe kafin nace"Ni wai Fita zakayi ka barni ni kadai acikin gidanan...? Yana Fesama jikinsa Turare ya juyo yana Fadin"Naga yau kina jin Lalaci ne,zan Fita baki Shirya ba Balle na ijiyeki Gidan Ammi ko Wajen Anty Aisha..."Baki na Tura na Yunkura na mike da Cikina wanda ya Fito sosai kamar ba Wata bakwai ba domin ya Turo sosai Shiyasa Duk wasu aiyuka ma Ya Daukemin in bai yi da Safe ba in ya dawo da yammah zai Share Mana Falo da Bedroom dinmu ni kuma kafin ya Dawo na gyara kichen na goge abunda na bata,bancika yin girki ba Tunda ya Hanani sai dai mu fita muci ko kuma in zai Shigo ya Shigomin Dashi.


Sai da na mike kana nace"Nifa na gaji da zuwa gidan mutane Hakanan B.love,Zaman kadaici ya Dameni ko zaka maidani Abuja ne wajen Su Daada zan fi Jin Dadin zamana achan.."Harara ya sakarmin kafin yace"Ni kuma ki barni kadaicin ya kasheni ko..?comon jare shirya mu tafi Sch tare yau 12 zan bar cikin School din.."Kallonsa nayi kafin nace"Da gaske...? Lum yayi da ido kafin yace"Zan sauya Ra"ayi ."Ai da gudu na Fada Tiolet ina Murna da kallo yabini baki Bude yana Dariya.


Agurguje nayi wanka na Fito Shiya taimakamin na Shirya Cikin Riga da zani na wani Leshi Domin yanzu bana saka Riga da Sikt Tunda Cikina ya girma Matseni Suke Duk sun man kadan,dogon Hijabi yace na saka Dama Tuni ya hanani saka karamin mayafi sai babba yau kuma Ra"ayin Hijabi yake ji Hakanan na saka Muka Fito yana Rike da karamar Jakata da wayata da key din mota muka Fice ko karyawa bamu yi ba yace Karna damu zamu karya in muka isa office dinsa.


Salihu megadi ya wangalemana get yana Fatan Dawowa lafiya,Muna Tafe muna Hira har muka Shiga cikin Makarantan,Tun Shigarmu naji Dama banzo ba saboda yadda gabadaya Hankalin Dalibai dake wajen parking space Daga Nesa suka sakarma ido,shi ya fito Cikin Kasaita bayan ya kashe motar ya zagayo ya Budemin Ya Taimakamin na Fito Tunda yanzu nayi Nauyi Kuma Duk da Dogon Hijabin Dana Sanya bai Hana cikin jikina Fitowa ba.


Shi ya Daukomin Jakata, kuma muka Sarke Hannayen Juna muka Fara Tafiya zuwa cikin makarantan ta ko"ina ido ne ke kanmu,saboda yanayin yadda Jikina ya bani na gane kallonmu kawai ake da Gayyar na Sadda kaina Bisa kafadansa ina Marairaicewa Da Hannu Daya ya Rike Jakar Dayan Hannun kuma ya Zagayo kuguna Dashi ahaka muka Ratsa Filin Haraban na Mathematisc Dep,har zuwa Cikin Kayatattacen office din Mijina


Ya zaunar dani bisa Kujeran Dake Office din ya Dauko min Madaran Hollandia da cake ya bani yace na Jirashi zai shiga karatu yanzu ammh bazai Dade ba zai fito kai na gyada mai na Kishingide ina Jan iskar A.C Dake Kadawa Lokaci Daya tana bada wani Sautin kamshin mai Dadi.


Ranar Gabadaya Jami"ar BUK ta Dauki labarin MR Bello Jikamshi yazo da matarshi,Kai wasu da basu ganni ba suna Fadin zasu so ga wata mai sa"a ce ta samu Nasaran Zama matar The young Teacher,harda labarin ma ina da ciki cikin Hakane B.kaita ta Tsinci labarin a Department dinsu tana jin Haka ta Daga waya ta Kirani Lokacin ina ta Danne danne Bisa System din mijina ina kara Jinjina ma baiwar da Allah yayimai,na daga muka gaisa nan take Tambayata na shigo cikin Sch ne nace mata eh ina Office dinshi shi kuma yashiga karatu jin Haka yasa tace bari su zo ita Aliya.


Wasu Dadama jin Billy kaita ta sanni yasa sukayi gayya suka Biyota har cikin Office din Mijina Domin Su ganni su karemin kallo,ban nuna wani Abu ba duka na basu hannu muka gaisa wasu har suna Min murna samun gwarzo Miji kamar Mr Bello nace ina godiya,muna nan tare aka kirasu zasu shiga lacra sai gani nida abaya bana bama karatu muhimmanci naji nima ina Sha"awar Kasancewata Daya Daga cikinsu nan suka barni suka min sallama suka tafi,Aji daya yama karatu Ranar ko 12 din bamu kai ba muka bar cikin Makaratan muka koma gida Ranar Wuni mukayi Cin Soyayyarmu kamar Babu Abunda ya Damemu,Tun kuma Daga Ranar in zai shiga makaranta tare muke Shiga Ya barni office dinshi,watarana ma in na saka tsiya Dani yake tafiya Class din na samu waje na zauna ina kallon Bakin Mijina Yana Turanci kamar bai taba Jin Hausa ba,shi kuma Duk da ina cikin Ajin baya nuna ina wajen har sai yagama Abunda yake in zai Fita ya Yafito ni da Hannu,na taso ya kama Hannuna mu Fita,Dalibai dadama Soyayyarmu na Burgesu Wasu yanmatan da suka mutu kan sonshi sun ma cire rai Dashi ganin baya ji baya gani sai akaina.


*****


Cikina na Shiga Wata Na Tara Daada Ta ma ya muktar mganar ya kamata Bello ya maidani gida chan Borno na Haihu cikin Yan"uwana da Dangina Tunda Haihuwan Fari ce,ya muktar shi ya kira Bello yamai mganar kai Tsaye yace shi bai yarda ba ba inda zani haihuwa a kano zan Haihu,sanin halin Taurin kan Bello yasa Daada bata bi ta kanshi ba Ta tacema Anty Rahila ta Shirya su Tafi kano su Taho dani bata mata musu ba,suka Taho kano ni ban ma san da maganar ba Jiya Dai Daddare naga baiyi wani barcin kirki ba Lokaci bayan Lokaci sai yayi ta sakin Tsaki Shi kadai.


Basu min wani bayani ba suka Shiga Hadamin kayana wai tafiya dani zasu yi Abuja gobe Mallam Inuwa yakaini Borno Achan zan Haihu Duk da naji Dadi ammh kuma sai naji na Damu Saboda nafikowa sanin Halin Mijina Belle ma Naga kamar baisan da Tafiyar ba kuma ko ya sani bada Yardanshi bane,Dana ce zan Kirashi ma Daada ta Hana ni kiransa ina ji ina gani suka gama Hadamin kusan Rabin kayana su ka kuma kwashi na Haihuwan da muka Taho dasu Daga Eygpt,Suka Tisa keyata sai cikin Mota ina kuka ina komai Sai da muka Dauki Hanya kana Daada ta Kirashi tana sanar dashi tazo ta tafi dani gobe zan Wuce Borno achan zan Haihu banji mai yace mata ba,ammh Daga yanayin Nagane Fada yake ta ma Daada ta kashe Wayarta bata Biyemai ba,Shiko yana cikin Office dinsa Daada ta kirashi tana gayamai Abunda ya kusa sakashi ya Rasa Control dinshi kawai saboda an maidashi Sakarai sai azo atafi Dani batare da saninshi ba kuma Hardani aka taru aka Raina masa Wayau meyasa ban kirashi na gayamai ba Ransa yayi mummunar Baci Ranar Sukansu Dalibai Sun gane an Tabo Mr Bello domin Motsi kadan kikayi sai kiji yace out.


Har muka isa Abuja Ban saki Raina ba,Tun muna mota naketa kiranshi yaki Daga kirana,Sai na Hakura na kyaleshi sai da Daddare na Turamai sako


_Salam B.love....My Love am srry da Abunda ya faru ba laifina bane naso kiranka na gayamaka Daada ta hanani...Kasani nima ina cike da kewarka kamar yadda kake cikin kewata...Zuciyata ta cika da Kuncin Rashin Ganinka akusa dani...Ina cikin Kukan Kewarka Mijina..._


Na turamai sai da ya tafi na kwashe wayar na kwanta ina Hawayen kewar mijina da Tsausayinshi.,Shima anashi Barayin Hakane koda yayi Fushi Dani Haka ya Dinga Juye Juye saboda kewata sakona kuwa ya karanta yafi sau goma shi ya Debemai kewa Har ya iya yin Barci Washegari Haka ya tashi Duk bayajin Dadi ko Sch kasa Shiga yayi Gabadaya bai saba Rayuwa Bani ba ya saba dani,yasaba da komai nawa Sai yanzu kuma Lokaci Daya azo aragemai jin Dadi.


Kamar Yadda Daada tace ko Washegari Aka Duramin kayana cikin Booth din mota,Mallam Inuwa ya kaini Har Borno kafin mu isa kafafuna sun kumbura saboda Zama,mutanen Gidanmu sunsan da zuwana Tunda Anty Rahila takira Mama yana ta Fadamata kafin mu iso ta gyaramin Cikin Uwar Dakinta inda zan Sauka,mallam inuwa yaso ya koma sai Ya Ali ya hanashi Sai da ya kwana Washegari ya koma Duk da ina cikin Damuwar Rashin Mijina Domin yayi Fushi Dani ko na kirashi baya Dauka sai dai na Turamai sako ya Karanta bazai bani amsa ba Duk na Damu ammh ganina cikin Dangina yasa na Saki Jikina Mama yana dasu Ya Ali bansan wanda yafi wani kula dani ba,Haka matansu Ya Ali komai nace suna Rawan Jiki su bani Mama Falmata kuwa Sai kawaichi ammh cikin Ranta tana min Addu"ar Allah yasa na Bude ido lafiya.


Sati na Daya Da zuwa Borno ammh haryanzu Bello bai sakko ba Abun yafara Damuna Sosai Duk da Cikin Jikinna sai na Fara rama,gashi ba"a san masu Juna Biyu su Shiga Tunani,nan da nan kuwa sai ciwon kai mai zafi sai da aka Dangana ni da Asibiti nan akace Jinina ya Hau na kiyaye Da Tunani Saboda zan iya sanun Mtsala Nida Da Abunda ke Cikina nan suka Rikeni sai da na kwana na Wuni kana muka koma gida Ranar ina zaune Kan gadon Mama Yana ina Shan Mangwaro sai ga Kiran Wayata ina Dubawa naga B.love ne.


Duk da Abun yabani mamaki ban yi Saurin Dauka ba na Zubamai ido yana ta Kira ban Daga ba,har Sau uku kafin ya Dakata da Kira ni kuma ban Daga ba Domin Azahirin gaskiya yagama batamin rai kuma yabani mamaki ban taba zaton koma mai nayi ma B.love zai iya yayimin Irin wannan Hukunci ba balle kuma yafi kowa sanin Bani da laifi.


Nagama Shan Mangwarona kenan Sai ga Khadijan ya Ali ta kawo min Wayar ya Ali wai mijina na Mgana Karba nayi ina basarwa bata Tsaya ba ta Fice ta barni,Ba a dauki Lokaci Ba sai ga Kiransa ya sake Shigowa Tana gabda Tsinkewa kana Na Daga Tunda na Dauka banyi mgana ba cikin Sanyin Muryansa ya Furta"Wani Tunani kika saka Aranki Har yana neman ya Tabamin lafiyanki da Abunda ke cikin ki..?..


Yafada cikin Kaushin Muryansa Ina jin Abunda yace na sakamai kuka,Wiwi Shuru yayi bai cemin komai ba Har nagaji nayi Shuru na koma ina Sharbe Hanci Cikin Muryan Kuka nace"Har ma tambayata kake meke damuna..? Ina da wata damuwan Data wuce ka ne..? ka manta da ni Kwata kwata Baka Daukan Kirana kuma baka Kirana.."nafada ina Tura baki,Mirmishi ya saki kafin ya Koma ya Kwanta yana Dafe Kirjinsa Cikin Wata Irin Murya ya Furta.."Laifi kikaman Anee Shiyasa.."Cikin Tura baki nace"Laifin me nayi maka kuma...?


Yace"Laifin kin tafi kin barni mana my Anee kinfi kowa sanin Ba wanda na saba dashi sama dake....ammh baki damu ba kika Biyema Daada ta Rabani Dake...Ya kike Tsamanin bazan Damu ba...Bana iya barci Saboda kewarki Akullum Sakon ki ne ke Debemin kewa ammh Jiya najiki Shuru kuma nayi ta kiran wayarki Tana kashe na Damu sosai sai na kira Ya Ali shine yace min kina Asibiti baki da lafiya Jininki ya Hau...Na Shiga Damuwa Sosai My Anee Duk da kin Batamin rai buh na Riga na yafemiki fata nima zaki yafemin Kuskurena.."Yafada cikin Alamun Shagwaba..


Ido na lumshe Lokaci Daya ina Jawo Filon Dake kan gadon na Matse Bisa Kirjina ina Fadin"Naki wayon bayan kasa Babynka ma yayi kewarka..."Cikin Mirmishi yace"Zan zo anjuma na lallashi kayana ba Ruwanki.."Dariya na saki ina Fadin"Anee tayi kewar Mijinta sosai..."Cikin Wani Shauki ya gyara kwanciya yana Fadin"Mr bello ma yayi kewar Matarsa Sosai Fiye da yarda Tayi kewarsa..."yafada lokaci Daya yana Sakarmin Kiss Cikin Kunnena Kasa nayi da ido kawai ina Sauraran Labarin Irin kewata Dayayi,Nima nan na shiga bashi labarin Kewarsa Danayi Tuni muka manta da wani Fushin Juna muka Shiga hirar Soyayya sai da muka ji Kiran Mangariba kana muka Hakura wayar Ya Ali kuwa Sai kira mutane suke muna sakasu cikin Call Waiting,muna gama wayar na lallaba na tashi Zuwa Shashen Ya Ali tunkan na Shiga na cikaro da Yarsa Samiha na mika mata na juyo ina Dariyan Sanin Halin masifan ya Ali.


Bayan sallar Isha"i muka Dasa Daga inda muka tsaya Muna waya Yana kichen yana Dafa Indomie haryagama yaci muna mgana sai da zai shiga wanka muka Hakura bayan ya Fito kuma koda ya Kirani barci ya kwasheni sai da safe naga sakonsa.


*Sleeping Beauty...My Wife...*


Mirmishi nayi Lokaci Daya ina Sumbatar waya kamar Shi nake gani,Tunda muka Shirya sai muka koma bamu da aiki sai waya,in yana gida ko yana makaranta sai dai kuwa in ya Shiga Clasa ne zamu Hakura yace min zai zo ammh sai Weekend.




****
Ranar Jumma"a Tun Safe Dana tashi naji bana jin Dadi Ciwon baya,sai ban Nuna ma kowa ganin Dama ya sabamin irin haka,Ashe Naguda nake bansani ba Sai wani Lokacin naji marata ta Daure Duk ban kawo komai ba sanin naji labarin Haihuwa ba Haka take ba,Su Ya Ali duk basu nan sun tafi masallacin Jumma"a na Shiga Tiolet zanyi alwala na Durkusa zanyi Fitsari naji Wani Ruwa na Biyo nayi kokarin Tashi na Duba ban iya ba Saboda wani Azaba danaji ya kamani Bansan sadda na Fasa Ihu ba Saboda ji nayi kamar zan mutu ne.


Mama yana nake kira Kamar Muryata zata Fashe ita da Falmata suka Rugo zuwa cikin Bayin na Dakin Mama yana suna Saka kansu Cikin Tiolet din na saki Nishi jin Wani Abu na Shirin Fitowa Daga kasata,dafa kasan Bayin nayi ina kuka lokaci Daya da Hawaye Zanin Jikina Tuni ya yaye kanshi Saboda azaba,ko kafin su kariso kusa dani na Saki gatso Lokaci daya ina Fadin"Innalillahi...Hasbunallahi...Mama...mama ki Dubamin kashi ne yaki Fito ko menene.."Na bani Zan mutu..."Haka na ke Fada kafin na saki Nishin da karfi sai ga D'an Da ya Fito Lokaci Daya mama yana ta saka hannu ta jawoshi tana Fadin"Alhamdulilah...Lalle kin gado Falmata Haka tayi Nakudar ki Daga zuwa Fitsari sannu Kinji Aneesa.."Tsakar bayin na koma na kwanta ina maida Numfashi Mama Yana ta mikama Falmata Yaron Daya cika wajem da kukansa Ita kuma tayo kaina Ta shiga matsamin Ciki sai ga Uwa ta Biyo Baya,Mama yana ta Shiga gyarani ita kuma mama falmata ta yanke Cibiyar ta Nade Yaron Cikin zani ta Fita dashi nan da nan Mama yana ta hadamin Ruwan zafi mai zafi ta min wanka ta kamo ni muka Fito,ita kuma Tuni Mama Falmata ta gaya su Khadija Haihuwan sun saka Ruwan zafi sun Wanke Jaririn Tas,sun sakamai wasu kayan sanyi masu kyau,Kafin kace kwabo sun gama gyaramu Nida Jaririna kato mai kama da Ubansa sak,sai dai su Ya Ali suka Dawo suka ganni kwance kan gadon Mama yana nida Jaririna bayan Sun Hadamin Faten wake mai cike da Kayan ciki,da kunun Tsamiya na Daddaka kana na koma na kwanata,kowa sai mamakin Naguda ta yake Cikin Lokaci wai na Haihu kuma agida.


Ni na Turama Bello Text da cewa..." _Alhamdulillah...MR BELLO MUHAMMED JIKAMSHI is Now a father..._ na Turamai ko minti goma ba"ayi ba sai ga Kiranshi cikin Rawan Jiki yana Fadin"Anee wai da gaske kike..?ina Dariya na karamai kukan yaron wanda Tunda ga Fitowarshi Duniya na gane yana da da Rigima Hawayen Farinciki suka Kawo cikin Idanuwansa cikin Murna yake Fadin"Masha Allah Alhamdulillah..Allah Nagode maka Wlcm to the World...Muhammed Amin.."Yafada yana Dariya cikin Farinciki Nima Murnan nake kafin kace kwabo Haihuwata ta Zaga Dangi da Abokan Arzuka,waya kuwa har nagaji da amsawa,sai washegari kana Muka tafi asibiti aka dubamu Nida Jaririna aka tabbatar da komai lafiya kana muka Dawo


Tuni Ruwan Nonona yazo Saboda Mama yana batamin da Wasa abinci nake ci kamar gara,Dama gashi yaron akwai Rigima ga Tsotso,Kwana biyu da Haihuwarmu ango karni ya Diro Shida Takwaranshi wato Uncle Aminu,Haka suka tasa yaron nan gaba suna kallo,ni kuwa agabansu Anty Nafee da Matan su Ya Ali Bello ya Rumgumeni tsam yana Juyi Dani nine ma naji kunya ammh Shi ko ajikinsa sai wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login