Showing 66001 words to 69000 words out of 122554 words

Chapter 23 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt

26 Jan 2025

23779

Wayar Anty Rahila nan taji lbri mara Dadi ita ta Kira S.jibiya take gayamata Dukkansu sun jajaantama Aneesa Tare da yin alkawarin saka Mr bello Cikin Addu"o'insu.


Uncle Aminu Ko Dake Kasar Spain bai da Lbrin Abunda ke Faruwa Domin Tunda yayi ta kiran Nombar Bello bai samu ya Hakura tunda bashi da Nombar ya Muktar ammh kullum sukayi mgana da Ammi sai ya Tambayeta ko Bello yazo.? Nan take gayamai Tun Zuwanshi lokacin Daya sanar da ita zai Fara Lecturing a Buk kano bai kara Dawowa ba,Aminu ya Shiga damuwa sosai ammh yana kokarin ya kamallah abun ke gabanshi ya Dawo domin Sauranshi Wata Biyar yagama komai ya Dawo gida.


Sani bai samu lbri ba Sai Daga baya Har Abuja yazo yama Ya Muktar Jajen Abunda ya Faru ya kuma ce in zasu koma India zai bisu yaga Halin da Bello ke Cikin,achan india kuwa Daada ta bama Muktar Shawaran yaje Adamawa ya Taho da Modibbo,Mtsayin Jika yake gareta Saurayi ne irin bai yi karatun Boko mai Zurfi ba iyakarsa Sakandiri sai na Addini,aikin Gyaran Motici yake agarin Adamawa tace ya Daukosa Su Taho tare koda An Fito da Bello Aneesa Tayi kankantan Iya kula da Bello itakuma ta Tsufa ga jikin Girma Nan da nan ya karbi Shawaranta yaje har Adamawa ya Taho da Modibbo iyaye da yan"uwa nata Faman addu'an samun Sauki ga Bello.


Ana saura kwana Uku Afito Da Bello Suka Dira Akaasar india Shida Sani da Modibbo,Daga modibbo har Sani Suna Tsaye Cikin Kofar Dakin da Bello yake suna Hangensa Kwance sambal cikin Na"ura mai amfani da Na"urorin Computer,Sani na Hawaye modibbo nayi suna Tunanin bawa mai Rai ne Cikin Wannan Abun Lalle Allah kadai ne Mai Nuna aya alokacin dayaso Shi kanshi Ya Muktar yanzu bashi da wani karfin gwiwa kamar mace zaki ga yana Share Hawaye Shar Shar kamar ba Soja ba wanda yasha gwagwamaryan Rayuwa...


Awannan Dawowar ne ya Razana da Ganin yadda Aneesa ta koma Dama ba Auki ba,ta kara ramewa duk tayi baki,nan Daada ke Fadamai bata cin abinci sai kuka zama yayi yana ta lallashinta Tare da Sanar da ita bayan anfito da Bello sun ji sakamako in zai koma Nageria zai Tafi da ita nan Aneesa Taka Rushewa da kuka Tana babu inda Zata ita zata Zauna anan kukan Datakeyi sai da ta saka Ya Muktar share kwallah Saboda Tsausayinta.


Ranar da za"a fito da Bello Daga Cikin Wannan Injinan Dukkansu ba Wanda ya Runtsa kwana Sukayi Addu",an Allah ya sa ansamu Nasara matakin Farko Da Sassafe suka yi ma Asibitin Tsinke Likitoci Sunfi Goma Suka Shiga Dakin sun Dauki Tsawon Awanni Aciki kafin Su Fito basu ma kowa bayani ba Illah Dr khabir khan dayace musu Suyi ta Addu"a yanzu za"a kara Tafiya dashi Dakin gwaji abunda sakamako ya Fitar Shine zasu yi Aiki Dashi.


Aneesa Sulalewa Tayi Jikin Daada Tana Kuma duk Addu"an da tazo bakinta Daga gida Nageria ma Duka ya muktar Duk ya Kira su yana Rokon atayasu da Addu"a Anty Rahila ma Tuni ta Kira borno ta sanar dasu Kowa dai Yana ta Addu"an Allah ya sa Anyi a Sa"a.


Agaban idonsu aka Fito da Bello Zuwa Dakin Gwaji kamar gawa ya yi Fari kasumba ta cikamai Fuska da jiki,Numfashi ne kadai zai sa kagane Bello yana Da Rai,Tsawon awa Hudu Suka kwashe Cikin Dakin gwaji kafin Likitocin Su Fito,Yadda ya muktar yaga Fuskar Dr Khan ne yasa Yaji gwiwansa Tayi sanyi Hawaye Sun Taru Acikin kwarmin idanuwansa Daga yadda Indiyanwan Likitocin ke mgana zaka san Abun ya basu mamaki basu samu ganin Dr khan ba sai da Suka Fito Daga Meeting din Da Suka Shiga Akan Cutar Bello.


Gabadayansu Suka D'uru Cikin Office din Dr khan Lokacin yana Tare da Dr Sunhat,suna kara Duba Duka Record din Bello Suna kara mamaki Dr Khan ya Zare gilashin Idanuwanshi yana kallon Ya Muktar kafin yace"Am Srry to say...Ammh wannan Gwajin matakin Farko bamu Samu Nasara ba,Munyi matukar mamaki ganin yadda ya Fito Daga cikin Wannan Na"uran ammh kuma Duka Sakamakon Farko gwajin ke Nuna mana Gabadaya kanmu ya Daure babu Wanda aka taba sakashi cikin Wannan matakin ba batare da Kaga An samu Naasara ba.."


Gabadayansu suka Dau Salati Ya Muktar ya Dafe kai yana Fadin"Ya Allah gareka muke...Kuma gareka zamu koma...Mun yarda mu musulmai ne Mun karbi Jarabawanka Hannun bibbiyu ina Fatan Dukkanmu Allah ka bamu ikon Cinye wannan Jarabawan.."Yake fada yana Kifa kanshi bisa Tuberun Gabanshi yana kuka,Sani ma Hawayen yake Shida Modibbo Daada ko kanta na kasa Tana Share kwallah Aneesa Fita Tayi Daga Office din Tana kuka.


Dr khan da Dr.sunhat ne keta basu baki Cikin Harshen Turanci Lokaci daya suna mai Sanar dasu Akwai wani Baturan Likita Daga Kasar babban Birnin America U.S Wato Dr Philphil,kwararan Likitane kan Harkan Gaashin kashi,Duk bayan wata Shida yake Zuwa Asibitin nan yana musu aiki na Wata Uku,Toh insha Allahu zai zo nan da Kwana goma Saboda Bello Domin Sun Turamai Duka Record din Gwajen gwajensa Suna Fatan Wannan karon ayi Nasara.


Koda suka koma masauki bamai lallashin Wani,Shi kanshi Bello bayan anfito Dashi Daga Dakin gwaji wani Daki na Musamman aka kaishi,Ya muktar bayajin Wahalan Fitar da kudi indai Akan Tilon kaninsa ne,ya kashe Miliyoyin kudi wanda baisan iyakarsu ba,Duk dai domin Yaga Bello ya Tashi kafafunsa kuma Bakinsa ya Bude,Haka suka Shiga Dakin Suka taru kanshi Suna kuka sani yana Rike da Hannayensa yana kallon Bello bello fa,Bello shinre yanzu Cikin Wannan Halin Lalle kuduran Allah,Aneesa kuwa Tana Daga gefe Sau Daya ta kalleshi bata kuma Saboda Yadda Bello yayi Tsufan karfi da yaji kasumba da gemu sun cikamai Fuska.


Anan Asibitin Suka bar Ya Muktar da Modibbo Shima Dakyar Hukumar Asibitin ta yarda Akidarta bata barin Majinyaci saboda Su Atsarinsu komai akwai masu kula Dashi Tunda ga Yima Patient wanka,Bashi abinci kula da bashi magani chanzamai kaya Goge goge inda yayi ba haya ko Fitsari,Ammh Ya muktar ya Dage Dole Suka kyaleshi da gargadi Dagashi ba kari,ahaka ya yarda tunda ko yaya naka Awaje yake yafi da"ace wasu Turawa ne ke kula maka da Naka.


Achan gida Nageria kuwa Haka suka samun Lbrin Rashin Nasaran Matakin Farko aikin Bello sai dai kowa ya koma Addu"an Allah yasa Mataki na Biyu ayi Nasara,Tunkafin Dr.philphil Ya kariso Ya Muktar ya Riga yagaama Biyan Duka Kudin Gashin gashin da Za"a ma Bello Kawai Jiran Likitan Suke da kuma Lokaci.


Kwana goma na Cika kuwa Sai ga Dr philphil ya Diro kuma yana Zuwa da File din Bello yaFara Cin karo dama already ya Fara Duba bayanan da Dr.khan ya Turamai ta Email dinshi sai bayan ya gama Duba komai ya sanar dasu Ya Muktar cewa za"a ma Bello gashin kashi na Tsawon Wata Biyu kwana Sitti kenan In Har kwanaki suka cika bawani Chanji He is Srry to say su koma gida kawai Domin Zasu cigaba da Bata kudinsu ne a Banza Bello haka zai kare Rayuwarsa Cikin Mutuwa da Rayuwa.




Ki biya ki karanta cikin salama.


*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_




*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_


*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*


      *🅿�23*


Cikin Nasara da Fatan Dacewa Aka farama Bello gashin kashi,kwana uku Tsakani Sani ya juyo ya dawo gida Nageria,su ya muktar kuwa sai da aka kwana goma da Farawa kana suka dawo gida shida Daada da Aneesa wacce Dakyar da sidin goshi,ta yarda ta biyosu sai da yamata alkawarin in an kwana biyu zasu dawo tare.


Anan suka bar modibbo ba domin ko Zai Dingama Bello wani abu ba sai domin ba"a bar Bellon Shikadai ba ammh komai na Bukata Ma"aikatan Asibitin kemai kama Daga Wanka,cin abinci,Wankemai Najasa da Sauransu,Arana sau uku ake mai gashin Kashin da safe,da rana,da yammah.


Tun da Aneesa ta dawo gida sai damuwarta ta karu Gabadaya ta Fige ta rame kamar ba ita ba dama gata ba kiba sai ta kara zama wata iri sai ido da suka Fito,in kaga Aneesa taci abinci sosai Daada ce ta matsamata Zakaga taci abinci da yawa,in ko ba Haka ba,bazata ci ba,Ko Anty Rahila tamata mgana bataji sai ta fashe mata da kuka Ya muktar kuwa shima yayi Rauni Sosai Kallon Aneesa ma saka masa Rauni yake shikanshi Raman yake atsaye Bello ke chan India ammh Gabadaya Rabin Hankalin Muktar yana kanshi baya iya samun barci gabadaya kwana yake addu"an Allah ya sa asamu Nasara Bello ya mike kan Kafafunsa


Dawowarta yasa ta saka wani Layi ta kira Su B.kaita ta sanar dasu ta dawo,Kwana biyu Tsakani sai ga B.kaita Direban gidansu ya kawota koda tazo Aneesa na Dakinta tana kwance sai da Ta gaisa da Daada da Anty Rahila kana ta Shiga wajen Aneesa Tana ganinta ta tashi da Gudu ta Rumgumeta Lokaci Daya ta saki kuka Bubbuga bayanta B.kaita keyi Cike da Tsausayi kafin Ta Dagota Lokaci Daya tana Share mata kwallah.


Cikin Tsausayawa B.kaita ke Fadin"Kibar kuka Aneesa..Insha Allahu Uncle Bello zai Warke.."Kada kai Aneesa Tayi kafin ta Riko Hannun B.kaita su Zauna gefen gado,Lokaci Daya tana Fadin"Yaushe...? Wata rana Billy,Likitoci fa sunce matukar Akagama wannan matakin bai mike ba toh Haka zai kare Rayuwarshi cikin Mutuwa ko Rayuwa.."


B.kaita tayi Tagumi Tana Fadin"Kai in bawa na raye bai gama ganin Rayuwa ba..Kibar yawan Kukan nan Kinga yarda kika Rame duk kin chanza,Addu"a zakitayi mai Allah ya bashi lafiya muma masoyanki zamu Tayaki Addu"a Insha Allahu zai mike.."


Mirmishin Dayafi kuka Ciwo Aneesa ta saki kafin ta mike tana cemata bari tazo Fita tayi ta samo mata Abun motsa baki,kafin Alheri ta gama Shirya mata abinci,Bayan ta Dawo ne Suka kara gaisawa da B.kaita Suna Zaune bisa cafet din Tsakar Dakin B.kaita ta kalli Aneesa bayan tasha Ruwa tace"Kin samu lbrin Resuilt dinmu ya Fito..?jiya Rabi Suleja ta kirani ta ke gayamin."


Girgiza kai Aneesa tayi kafin tace"Wazai gayamin B.kaita..? Duka duka yaushe na Dawo garin,Ni yanzu ba wanna ne agabana ba Gabadaya bana cikin Natsuwata.."Dan mirmishi B.kaita Tayi tana Fadin"Nifa ina mamakin Wani Abu Aneesa Bukar Bulama..."?


Kallonta Aneesa ta kalleta tana Fadin"Kamar na me kenan..?B.kaita ta gyara zama tana Fadin"Mamakin ganin yadda kika damu da Halin da Uncle Bello ke Ciki,in naga Haka sai Na Tuna kece fa kike Tsanar duk wanda ya Nuna yana Son Uncle bello ko kuma yana Burgeshi sai gashi yanzu wai kina kuka Saboda Halin Da Mr Bello ke ciki Abun ne ke Matukar bani mamaki.."


Tafada kai tsaye tana kallonta Mikewa Aneesa tayi ta isa gaban Madubin Dakin ta Harde Duka Hannuwanta kan Kirjinta Lokaci Daya Aneesa tafara fadin"Karki manta Lokacin Akwai yarinta da Kuruciya Tare dani,lokaci na Tafiya girma na kara kamamu B.kaita ko alokacin bawai ina kin Uncle Bello bane A"a ina ganin bani da makiyi kamarshi sakamakon Shine ya karyamin kwarin Rashin son Mkranta ta Sai Daga baya na gane Bayan iyayena Shine Mutum na biyu Daya Inganta Rayuwa Tunda ya Tursasamin na Zama mai Ilimi kuma nayi karatu,kuma ko ba Haka Ko makiyinshi ya ganshi Cikin Wannan Halin sai ya kokamai balle Ni da nake da Igiya uku Rataye Awuyana amatsayinshi na Mijina..."Tafada Hawaye suna cika mata karmin Idanuwanta...


B.kaita ta gyada kai kafin tace"Kuma fa Hakane kinyi Mgana kema.."Aneesa ta saki Numfashi tana Fadin"Ni ba ina Sonshi bane ko yana Burgeni ba kawai Tsausayin Halin Dayake cike ke sakani kuka,Ki Tuna Abaya yana Tafiyansa,yana cin abinci,yana iya Fadin Abunda yakeso da wanda bayaso yanzu fa yana kwance komai na Bukatar rayuwa sai anyi mai Baya iya mgana sai dai ya bika da ido koda yana da Bukatar wani Abu bakinshi bazai iya Furtawa,Shikadai ne in na Tuna sai naji kuka yazomin bana iya Sarrafa kaina Billy kaita.."Tafada tana Rushewa da kuka.


Mikewa B.kaita tayi ta isa gareta ta Dafa ta tana Fadin"Bar kuka Anee don Allah,kukan ki na Dagamin Hankali kuma kuka ba Mgani bane,Addu"a itace mafita bake kadai ba Kaf Daliban Kwatar kwashi Zasu koka da Halin da Mr Bello ke Ciki bama ke da kike Mtsayin matarsa ba.."Kan Kafadarta ta yada kanta tana Cigaba da kuka B.kaita na lallashinta sai da tayi Shuru kafin su koma su zauna,Tana janta da Hira har ta saki jikinta nan B.kaita ta kira S.jibiya tana gayamata gata gidansu Aneesa,nan ta bata wayar suka gaisa ta mata yamai jiki,Kafin su rabu sai da S.jibiya ta bama Aneesa Hakuri kan cewa Suna Jibiya an musu Rasuwa sai Sati na sama zata Dawo in Allah yarda da Zaran ta dawo zata zo Har Abuja Sunsha Hira kafin su yanke Kiran,Sai La"asar B.kaita tayi Shirin Tafiya bayan sunyi salla Sunci abinci Direban gidansu wanda ya kawota ya juya da Ita Har Haraban gidan Aneesa ta Rakata bayan tayi musu Daada sallama tana Dagamata Hannu Har suka Fice Daga Haraban gidan...


Ba laifi Zuwan B.kaita ya saka Aneesa ta saki jiki kadan,Tadaina yawan kuka da Damuwa ta maida kanta Daga kwanciya sai Karatun Qur"ani domin koda yaushe Sukayi Waya da Mama Falmata Abunda take kara Jaddamata kenan Aneesa ki rike Allah,shi zai zama gatanki,in ta gayamata Haka sai Hawaye sun Fitoma Aneesa,Tagama tabbatarma kanta Bayan Allah iyaye sune kan gaba kan komai Musamman ma Uwa,wacce tafi kowa sanin Damuwa Dan data Haifa,Gabadaya Aneesa ta koma bama yayyinta Tsausayi Ba wanda baya Kiranta yana Bata baki Anty Nafee ce kadai bata taba kiranta tace ya mai jiki ba bata sani ba ko tana kiran Anty Rahila ammh Anty Yagana da Anty Aisha Kusan koda yaushe sai sun Kirata,Haka mama Yana itama tana iya bakin kokarinta ganin Aneesa ta saki Ranta ta dawo da Jikinta kamar baya.


Achan india kuwa ana ta ma Bello gashin gashi ammh kam Babu Wani Chanji,Modibbo Kullum Cikin kula Dashi yake,Shi ke kiran ya muktar Vedio call ya Rinka Haskomai,Bello yana ganinshi,Muktar yana kallonsa yana Share kwallah Shiko Bellon sai dai ya kafama wayar ido yana kallon Ya Muktar kansa na Lamgwabewa gefe miyau na Zubomai kamar Wani gaula gwanin ban tsausayi Muktar ya riga yagama Sarewa Domin Abu harzuwa Tsawon Wannan Lokaci ba Chanji game da Bello yana nan yadda Suka kaisa sai dai Abunda Allah yayi kuma.


Daga Jami"ar Bayaro kuwa Malamai Shida ta Wakilta Suka je Har india suka Dubo Mr Bello,suma Haka suka dawo gabadaya Jikinsu yayi sanyi Lokaci Daya Suna kara Tsorata da Duniya,Kuma sun kara yarda bawa awajen Allah ba"a bakin komai yake zai iya yin ikonshi Akanka Koda bai Rabaka da Numfashinka ba.


*****


Sannu Sannu bata Hana Zuwa sai dai Adade ba"a je ba,Gashi har Bello ya cike kwana Sittin Da Faramai Gashin gashi har an kammallah ana gobe za"a maidashi Dakin gwaji ya Muktar suka sauka akasar Shida Ya Ali,Washegari aka Shiga daBello dakin gwaji Wanda Suka Kwashe Tsawon awa uku kafin Afito Dashi Tundaga yanayin Fuskar Dr Philphil da Dr.khan suka Fahimci babu Nasara kan Kafadan ya Ali ya muktar ya Sulale yana Kiran Sunan Allah Cikin Karfin Hali Ya Ali ya rikesa Suka karisa Cikin Office din Dr khan.


Dr.philphil Shine yayi musu Bayanin komai Wanda ya kara Raunana musu Zuciya ya basu Tabbacin Bello bazai taba warkewa ba domin Wannan ne karo na Farko da suka taba ma wani wannan Aikin kuma basu samu Nasara ba,ammh basu sani ko kila nan gaba ya Tashi ammh Azhirin batu Duka gwajin Sakamakon Suna Nuna Normal ne Abu ma daya kara Dauremusu kai Duka Joint dinshi lafiya kalau basu da Mtsalan komai Komai na Jikinshi yana lafiya ammh kuma gashi kwance ko yatsan Hannunshi baya iya Dagawa Daga karshe ya basu shawaran Su koma gida kawai Domin Ko wani Asibitin Suka je sai dai su sake Wani Asaran kudin kawai."


Kasa ya Muktar ya Sulale ya Rufe Fuskarsa da Tafukan Hannayensa yana Shesshekan kuka Ya Ali ne da Modibbo suka Rikosa suna bashi baki,Su kansu Jikinsu yayi sanyi Waje ya Fita yana Share kwallah Daada ya kira awaya tana Dauka yasaka mata kuka tana jin Kukansa tace"Ba"a samu Nasara ba ko Muntari..?


Yana Sharban Majina da Hawaye yace"Daada sunce Bello bazai Taba Tashi ba...Kuma Duka sakamakon gwajinsa ya nuna bashi da Mtsalan komai ammh Daada bello yana nan kwance yadda kika barshi ba"a samu wani Cigaba ba..."Daada ta Sulale Bisa Kujera tana Kiran Sunan Allah Lokaci Daya tana Dauke Hawayen idanuwanta da Haban Zaninta cikin Dashewar Murya Daada tace


"Ya zamuyi Muntari bamu da yarda zamuyi In Har Haka Allah ya Tsarama Bello bamu da yarda Zamuyi sai dai mu Tayashi Rumgumar kaddaranshi..."Ya muktar ya Share kwallar idanuwanshi wanda ke Zuba ba Control ya rasa Dalili yana da Jarumta kan komai ammh banda Kan Abunda ya Shafi Bello sam Baya da wani Jarumta Cikin Muryan Amo yace"A"a Daada Insha Allahu ba Haka Allah ya Kaddaroma Bello ba...Da Izinin Lahi matukar ina da lafiya da kudi da Mukami Sai na yawata da Bello Duka kasashen Duniya wajen Nema mai mgani yanzu ma na yanke Hukunci gobe zan Wuce Dashi spain suma su Gwada nasu Mugani Daada.."


Cikin Sauri Daada tace"A"a karma kafara Muntari Maza ka Dauko kaninka ku dawo gida ina ji ajikina Cutar Bello bata yawon kasashen Duniya bace,ku dawo gida mu Jarabamai na Hausa ko Allah zai sa Adace.."Ya bude baki zai yi mgana ta Dakatar Dashi da Cewa"Kayi Abunda Nace Muntari ka Dauko Kaninka Bello ku Dawo Gida.."Daga Haka ta yanke Kiran tana Sharan Kwallah shima Daga barayinshi kwallarsa ya Share kafin ya koma office din wajen su Dr.khan


Bayan godiya daya yi musu,nan take yace Su Rubuta musu Takardan Sallama zasu koma gida,Gobe in Sha Allahu,Duk da Abun ba Dadi ammh iya gaskiya kenan gwara su koma gida ajaraba achan kila adace,kafin Zuwa Waye wan garin sun gama Duka Shiryan Shiryansu na Tafiya,koda Aka Fito da Bello kan WheelChair,likitocin indiyawa da Turawan sai kama Hannunshi Suke suna mai bye bye,Haka Dr khan da Dr.philphil suka Rikemai Hannu Cike da Tsausaya Shikuma sai dai ido kadai ya ke saka musu,Fatan samun lafiya suke mai Har Suka Sakashi amota suka Fice Daga Asibitin da suka kwashe tsawon Wata Uku Aciknsa Shikan Modibbo ya saba da Wasu Da yawansu saboda Zama,duka Rocord din Gwaje gwajen Na bello suka basu bayan sun ijiye ainihin Original din.


****


Babu wanda ya sanar da Aneesa Da dawowar Su Ya Muktar da Bello,Ta damu bayan tafiyarsu bataji wata mgana ba tayi ta Tambayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login