Showing 33001 words to 36000 words out of 122554 words
Chapter 12 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt
da Aneesa Barin ma hannayenta da Suka Fara Jan Hankalinsa sai da kofar Tagama Tatanceshi kana ta Wangalemai kofa ya Sawo kanshi Falon Cikin Siririyar Sallamarshi.
 Aneesa Tayi Nisa Cikin Game dinta batama Jisa ba Kara gyara zama Tayi tana Sarrafa Game din Cike da Salo har Dan kwalinta ya zame gabadaya Kitson kanta ya bayyana Cikin Daskarewar Numfashi da Sarkewar Murya Kasim ya Bude baki yana karema Aneesa kallo Domin Lokaci Daya yaji jikinsa ya Saki Duk yawon Duniyanshi bai Taba Haduwa da Yarinyar da ko gama kallon Fuskarta baiyi ba yaji tatafi da Imaninshi ba Kamar Aneesa ba.
Cikin Sanyin Murya mai Cike da Yaudara ya Furta"Tsarki ya Tabbata ga Allah Shugaban Hallitun Duniya Wanda yayi Wannan kyakyawan Halitar..."
Yafada yana Kafe ta da Ido kamar daga Sama Aneesa Taji Wata Murya na mgana Cikin Sauri Ta Dago kanta Karaf ko Idanuwansu Duka Hudun Suka Hade Waje Daya,cikin Numfashi Sama sama Kasim ke kallon Aneesa yana jin Wani Abu na yawo Acikin Jikinsa Sosai Karon Farko Atarihin Rayuwarsa Daya Hada Ido da mace yaji baya Bukatar ya lashi Zumarta So Daya ya dauwama yana lasarta kuma yana kallon kyakyawan Fuskarta cikin zuciyarsa gayamai take Dakai Wannan Cute Face din Ta Dace.
Aneesa ko Kallon ne ya Sanyayamata Jiki ta Sauke idanuwanta Lokaci Daya Tana Mikewa Dankwalinta taja ta Aza bisa kanta Cikin Sanyin Murya tace"Am Srry Sannu da Zuwa,Zauna.."Tafada Tana kara kallonshi Tana so Ta Tuna Inda ta sanshi Shiko Mirmishi yayi kafin yace"La..No problem karki damu Nafiki jin Dadin Hakan Domin Idanuwana Su samu Damar kallanki Dakyau..",Yafada Cike da Bariki lokaci daya kuma yana Sakarmata ido,yam Aneesa Taji bata yi mgana ba Ta fara Taku Zata bar Falon Rigar Jikinta na Rawa Kowani Sako na Jikinta na Rawa Gabadaya Kasim sai Yaji yakasa Control din kanshi da mayun idanuwanta ya Bita da kallo har Ta fice Daga Falon Wanda Tana Ajikinta Cewa Idonsa na yawo Akanta Duk sai Ta Tsargu.
Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Karisa Kusa da Junior ya saka Hannu ya Daukeshi yana Cillashi Sama Shiko yana bangala Dariya Domin Tunda ya Shigo yake Miko mai Hannu yana Zillo Domin Haka Junior yake yafison Maza Su Daukeshi Fiye da Mata,yana Tsaye yana ma Junior Wasa Aneesa Ta Dawo Wannan karon ta sanya Wani karamin Hijabinta Fari Cikin kallon Ido Cikin Ido Tace"Ka kariso Ciki mana ka Tsaya Anan..."
Lumshe mata ido yayi kafin yace"Toh ai ba"amin Jagora bane...Shiyasa na Tsaya Anan.."Mirmishi Tayi kafin tace"La..ba Haka bane,.."Yana kallonta yace"Toh yane...?
Yafada yana kallonta Kur Cikin Idanuwasa Sauke idanuwanta Tayi kasa Kafin ta Juya Tana Fadin"Afuwan Yanzu mu Shiga Ciki.."Bayanta yabi Da kallo yana Fadin"Angama princess."Wani Iri Aneesa Taji sai Nanata Sunan Take Acikin Ranta Duk da ba yau ne karo na Farko da Maza ke Nuna Sha"awarsu Akanta ba Ammh Dis is d First time da Wani Namiji yake mata mgana Taji ya Burgeta......
.
Falon Anty Rahila Suka Shiga,Waje Ta Nuna mai ya Zauna kafin ta Shiga kwalama Alheri kira da Hanzari ta Fito nan ta Umarceta Data kawo ma Kasim Abun Sha Da Ruwa,kallonsa Tayi Tana Fadin"Anty Rahila na Ciki bari na Kirata.."Da Sauri yace"No...Kyaleta Dawo Mu gama Mgana Princess,In zan Wuce sai ki kirata mu gaisa.."
Da baya Aneesa Ta Dawo Ta Zauna kan kujeran Dake Facing Dinshi Bai samu Zarafin mgana ba Alheri Ta Shigo Cikin Uniform dinsu Domin kaf masu Aikin gidan Suna da Uniform,Katon Faranti ne Cike da Abun Sha Bisa Dan Madaidacin Tebur din Dake gabanshi ta ijiye kafin ta Dauki Kofi ta Tsiyayamai Ta Mikamai Karba yayi da Hannu Daya Yana Fadin"Thanks..."Yafada yana kafa baki Lokaci Daya kuma yana Kallon Idanuwan Aneesa Ita ko Kai ta Sunkuyar Tana Wasa Da Adom Doguwar Rigar Dake Jikinta.
Sai da yagama Sha ya maida Kofin Kan Farantin kana yayi gyaran Murya,Da Sauri Aneesa Ta Dago Cikin Dage mata gira yace"Ya.... ? Kinsanni..? Girgiza kai Aneesa Tayi kafin tace"Naso na ganeka Ammh kuma na Kasa Tuna Inda na Sanka.."Mirmishi yayi kafin yace"Ayyah...Niko kinga ina ganinki na ganeki ba.."Ido ta Waro kafin tace"Da gaske...? To Wacece ni din...?
  Dariya ya Saki yana kara Gyara ma Junior zama Wanda ke Ta Wasanshi Cikin Muryan Takama yace"Ah..Kaji wayau ko..? Bazan Fadi Sunan ba,Sai dai na baki Satar amsa bake bace kanwar Anty Rahila Dake Zaune Awajenta ba.."Yafada yana kallonta Domin baisani ba Cinka kadai yayi Saboda bai Taba katarin Zuwa gidan Sun Hadu da Aneesa ba Domin yafi Zuwa Lokacin Tana Zamfara Abakin Zubaida ne me yake Jin lbrin wata kanwar Anty Rahila na zaune awajenta kuma yana ganin Aneesa jikinsa ya bashi itace ko domin kamar da suke da Anty Rahila.
Dariya Tayi kafin tace"La..Da gaske kuwa kasanni,Niko na Rasa Inda na Sanka.."Dariya yayi mata kafin yace"Sunanki ma Wace...? Cikin Sauri Tace"Aneesa nake..."Dariyan Nasara yayi mata Ckin Sauke idanuwansa Akanta yace"Wow....Nice Name Aneesa..."Yafada yana Yar Dariya sai Lokacin ta gano Wayau yayi mata Hararan Waasa Tamai kafin Tace"Zan Ra ma ne..'"
Bai ce mata komai ba Illah Ido Daya Zuramata kawai yana Kallonta Abun sai ya Dameta Ta sadda Idonta kasa Tana Jin gabanta na Faduwa Cikin Sarkewar Murya Taji yace"Kinsan Zubaida..?
Kanta ta Dago Tana kallonsa Lokaci Daya Tace"Zubaida gidan Abba Kabiru..? Kai ya Gyada mata Cikin Dariya tace"Eh Sosai Ita da Zulfan gidan Abba garba Suna Zuwa Hutu nan Sosai.."cikin Sanyin Murya yace"Toh ni wanta ne.."Baki Aneesa Ta Rike kafin tace"Koda naji... Fuskarta nake gani,Shiyasa Na Rasa Inda na Sanka.."Bai ba mganarta Muhimmaci ba Ya Tsare ta Ido Cikin Dakewa yace"Aneesa...:!Idonta ta saka Anashi,suna kallon Juna na Wani Lokaci kafin Yace"Kina Sona...?Zaki Aure ni...?
Dam! Aneesa Taji gabanta na Faduwa Sosai,cikin Rawan Baki tace"So kuma...? Ba..bangane ba.."Mikewa yayi Dauke da Junior ya iso gabanta bai Tsaya ba kawai sai ya Durkusa kan Kafafunshi Har Gwiwansa na Gogan na Aneesa baya taja da kafarta Tana kallonshi Cikin Wani yanayi Kallonta Shima yake kafin yace"Eh So nace Aneesa..?Tun Shigowata idona ya Hadu da Idanuwanki naji kin Sace zuciyata,naji na samu matar Aurena..plz Aneesa Don"t say no..Ki Amsamin zaki Aure ne...? Kuramai ido Tayi tana gasgata Gaskiyarsa Cikin Ajiyar Zuciya tace"E....."Bata karisa ba Kasim ya Riko Hannunta Guda Daya yana Fadin"Thanks So much peincess zan Tababbatar da Kinfi kowacce, mace Dacen Samun Gwarzo Namiji kamar kamata.."Yafada Cike da Farinciki Da Sauri Aneesa Ta janye Hannunta Lokacin Dataji Wani yam Ajikinta Domin wannan shine karon Farko kenan da Wani Namiji,ya Taba Tabata kuma taji wani bakon yanayi ya Shigeta.,Saurin mikewa Tayi Tana Fadin"Nifa...nifa ban.."Mganarta Ta makale ne Sanda ya Sakarmata Idanuwansa Da Suka Chanza Launi Suna kallonta Shuru Tayi ta kasa Mgana sai ma Sun kuyar dakai Datayi ta koma ta Zauna Tana Wasa Da gefen Hijabinta.
Gefenta Kasim ya Zauna yana Cigaba da Marairaice ma Aneesa yana Cigaba da gayamata kalamai,masu Sanyaya jiki Wanda Daga Dukkan Alamun mganganun nasa Suna Tasiri Acikin Zuciyar Aneesa Suna Cikin Wannan Halin ne,Anty Rahila ta Sauko ganin Kasim Kusa da Aneesa Yayi kasa kasa da Murya sai Abun ya bata mamaki ita ta katsesu Cikin Mamaki take Fadin"A"ah Wa nake gani kamar Kasim..?
 Da Sauri Suka Dago Suna kallonta Tashi Yayi kusa da Aneesa Dauke da Junior yana Fadin"Nine Anty Rahila munzo Workshop ne Anan Abuja na Kwana Hudu so gobe zamu koma kaduna Shine nabiyo mu gaisa,ina Zuwa kuma Allah ya Hadani da Matar Aurena..."Dariya Anty Rahila Tayi Tana Fadin"Ikon Allah Ina Matar Auren naka..? Tafada tana son Tababbartar da Zarginta Cikin Fara"a ya Nuna Aneesa yana Fadin"Gata Anty Rahila..Princess dina kenan.."Baki Anty Rahila Ta Rike tana kallon Aneesa Dake Kyafta ma Kasim Ido Dundu Takai mata abaya Cikin Dariya take fadin"Ja'ira sai ya gayamin.."Bayanta Aneesa Ta Dinga Shafawa Cikin Shagwaba tace"Kai Anty Rahila kin kusa Ciremin Kashin baya.."Da Sauri Kasim ya Juyo gareta jiki na Rawa yake Fadin"Wayyo Da gaske..?mugani princess..."Yafada Yana Kallonta Cike da Tsumewa,Da Sauri tace"Bafa komai.."Tafada tana kauda kai gefe,Dariya kawai Anty Rahila ke musu Cikin Ranta tana Jin Dadi Domin dama Babban Burinta kenan Aneesa na Gama Mkranta ta samu Miji Itama Tayi Aurenta,kuma harga Allah zata fi kowa Murna Tunda ita bataga makusan Kasim din ba
Nan dai Ta Zauna Suka kara gaisawa Dashi,junior ne yafara kuka sai ya mika mata Shi,cikin marairaice Murya kasim ke kara Sanar da Anty Rahila Shifa Dagaske yake Domin in ya koma kaduna in zai je katsina Weekend da Mganar zai jema Abba kabiru Don Allah za"a bashi Aneesa..? Jin Haka yasa Aneesa Tatashi da Gudu Ta bar Falon Suka bita Dadariya,Anty Rahila tace"Kada ya damu su basu da mtsala yafara Tuntuban iyayen nashi yaji.."Da Haka suka bar mganar nan yake Tambayanta Lambar Wayar Aneesa Tace mai bata da Waya Saboda Mkranta sai Tayi Candy,jikinsa na Rawa yace Anty Rahila bazai yuyu ba Na Dinga Nesa da ganin princess kuma Muryanta ta Dinga min Shamaki da Zarar su Abba sun zo zan Siyamata Waya Daddy yayi Hakuri kawai.."Kallonsa kawai Take Tana Dariya Saboda ganin yadda yake Rawan kafa.
Sun Dade suna Hira kafin tamai Jagora Zuwa Shashen Daada,Suka gaisa ya Zube mata Kudi masu yawa Tana saka albarka Hibba ma Haka ta Daneshi Tana Murnan ga Uncle kasim,Anty Rahila ce Take cema Daada Toshiyar baki ne kasim ya bata Saboda yaga yar gidan ta yana so,Cike da mamaki da Fara"a Daada ke Fadin"Toh Hakane,Shiyssa naga ta Shigo da Gudu ina mgana Akayi banza Dani Aka Shige daki..? Toh maza karo kudi domin Wadanan Sunman kadan,kuma na janye Godiyata Domin Diyata ta Musamman ce"Aka Saka Dariya Gabadaya Duk da Wasa take mai masa cikin Shaukin Soyayyar Aneeesa baisan sadda ya sake Damko Wasu kudadan ya Mika ma Daada ba Tako Amsheta tana Fadin"Karka damu Aneesa Ta zama naka ka kwantar da Hankali kamar Kana saman Jirgi mai ya Kare.."Anty Rahila ta saka Dariya ita da Kasim,bai wani Jima ba yace zai Tafi Faufau Aneesa Taki Fitowa Daga Daki Cikin Bada Umarni Daada tace"Kaga Kasimu Shiga ka sameta Sabon Shiga ce.."Da Hanzari ko ya Shiga Bedroom din Aneesa na Kwance Ruf da Ciki Tana Mirmushi Ita kadai Taji mganarshi Asaman kanta da Sauri Ta mike zaune tana Zaro Ido,gaban gadon ya Durkusa yana kallonta Cikin Sanyin murya yace"Zan Tafi princess,Ammh inaji kamar Zuciyata tana Zafi,gaskiya bazan iya komawa kaduna ba sai nazo na ganki da Safe kinji ko.."?gyada mai kai tayi kafin ta Sauko Daga Kan Gadon Tana Fadin"Nima mun kusa komawa Mkranta Zamfara zan Tai.."
Yamutsa Fuska yayi kafin yace"Haka Anty Tagayamin Allah Da"ace baki kusa kamallah wa ba,sai dai ki Karashe Karatunki Akaduna bazan yarda da Wata Bording Sch ba,Ammb bakomai yanzu ma Duk Visiting muna Tare princess.."Da Kallo Ta bishi Tana mamakin yadda Lokaci Daya Ya Rude Akanta Tare Suka Fito Daga Dakin Nan ko Daada Ta Shiga mata Tsiya da Sauri Ta bar Falon Tana Rufe Fuska nan yabama Anty Rahila kudi Itada Hibba da Junor kafin yayi musu Sallama ya Fito Aharaban gidan ya iske Aneesa Tsaye Tana Jiransa Ranar kasim bai bar gidan ba Sai da yagama Dasa Kaunarsa Azuciyar Aneesa Taji ko bata Fara Sonshi ba yana Burgeta gashi Tana Jin Wani Abu game Dashi Sun Rabu da Cewa In ya samu lokaci zai Biyo gobe da Safe In kuma Taji Shuru ya Wuce zasu yi mgana ta Wayar Anty Rahila da ta bashi Nombar kafin su rabu,Kudi da yawa ya Debe Daga aljihunsa yabama Aneesa Ta ki karba Daya mtsamata sai Tafara Kwalkwal da Ido Zatayi kuka,dole ya kyaleta ammh kuma ta kara samun Wani Matsayi mai girma Acikin Ranshi,Sallama sukayi ya Shiga Mota ya Fice Daga Haraban Gidan Suna Dagama Juna Hannu.
Tadade Tsaye Awajen Tana Jin kanta kamar ba Ita ba Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin Ta Juya Zuwa Cikin Gidan Wani Shashe na Zuciyarta na Murna Samun Namiji kamar kasim wanda bata taba mafarkin samu ba.
_Masha Allah awannan page din na yau na kawo karshen Free page da zan baku na Mr Bello,Kuna Bukatar sanin yaya Soyayyar kasim da Aneesa zai gudana...? Ko kuwa kuna bukatar sanin shin su Abba kabiru zasu yarda da mganar kasim na Son Auren Aneesa..? Ina labarin Mr Bello...?kar ku manta Yana da labarin Duka hallayar kasim din na Neman mata da Shan giya Shin zai bari Aneesa ta aureshi? Ko kuwa zai sani kuma ya take sani saboda basu da Shiri da Aneesa..? Yaya Zulfa da Zubaida zasu kare da soyayyar Mr Bello..? Shin zai auri daya Daga cikinsu ko kuwa kowa zai rasa ne..? Ya ya rayuwar su Abba kabiru zai kare shin Bello zai yi karansu kotu ne domin Fansar ran Iyayensu da kuma Dukiyarsu da suka Hau kanta,..? Wani irin Soyayyah ce Zata faru acikin wannan littafin..? Kina bukatar ganin wani gwarzon ne zai ja Ragamar Jagoran Rayuwar Aneesa..? Toh zaki samu amsar tambayoyinki ta Hanyar Nuna min kauna wajen Siyan Novel dina Kun gwada kun gani kun tabbata bazan baku kunya ba siyan na gari mai da kudi gida_
*How to pay....â‚?200 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..â‚?400...or MTN card aturo ta wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*
_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👠Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �350 ne,VIP �600, Single one �200 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_
Happy sallah in Advance zaku iya cigaba da payment dinku bayan sallah in sha ALLAHU zamu dora Daga inda muka tsaya Fatan zamu sallah lafiya Ameen.
*Shakira...*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�
*🅿�12*
Washegari Kasim bai samu Dawowa ba yadai kirata Awayar Anty Rahila ya Sanar Da Ita Sun Wuce Kaduna,basu Wani jima suna waya ba ya yanke Kiran Da cewa Zasu yi mgana in ya Isa Kaduna.
Tunda Kasim ya koma Kaduna Koda Aiki yayi mai yawa bai Hanashi bama Soyayyar Aneesa Kulawa ba Wuni Suke Waya da Ita ta Wayar Anty Rahila Kafin Arufe Sati Zuciyar kasim Ta Rufe Ta Kulle ba Wacce Yakeji Da gani sai Aneesa Itama Duk da Bata Taba Soyayyah ba, ammh Tana Jin Dadin Soyayah da Kasim ko banza yana Burgeta kuma gashi, ba Laifi ya iya Soyayyah ga iya Tsara kalamai,lokaci kadan ya samu Matsugguni Acikin Zuciyarta.
Hatta da Ya Muktar ya samu lbrin Komai yayi murna Sosai, Shima Hardashi Ake Taruwa Ana Tsokanar Aneesa,bai nemi Kasim ba Tunda Anty Rahila Tace ya bari Shi kasim di ya Nemishi din kamar yadda yace.
Sati biyu da Haduwarsu Aneesa Ta koma Makranta,yayinda kuma Asatin Suka Rabu da Kasim kan zaije Weekend Katsina Tatayashi Addu"a zai gabatar da mganarsu Wajen Abba,da Fatan Alheri Tabishi Suka Rabu Cike da Kewa Harda kukanshi Wai zai yi kewarta Yanzu ba zai ganta ba..? Kuma bazai ji Muryanta ba Sai nan da Sati Hudu..? Dakyar ta lallasheshi ya Hakura Dafarko ma Tubure mata yayi akan Shi zai zo ya kaita Makranta Dakyar ta lallasheshi ya Hakura,Haka suka yi sallama kowanne Zuciyarsa ba Dadi,Saboda Zuciyoyinsu Sun Saba da Juna.
*******
Karfe 11am na Safiyar Ranar Asabar kasim ya Isa makeken gidansu Dake kofar laura Katsina,sai da ya Fara isa Shashensa yayi wanka ya Sauya kaya Tukunnah,ya iso cikin Falon gidan Inda ya Ci karo da,hamdiya Tana Zaune Tana kallo ganinshi ya sanya Ta Mike Tanamai Sannu da Zuwa Fuskarsa ba Annuri ya Zauna kan Daya Daga Cikin kujerun Falon yana Fadin"Yaushe kika zo ke kuma...?
Kanta na Duke Tace"Mun kwana Biyu ya Kasim,gobe ma zamu koma Munzo Hutu ne nida ya Ummu.."gyada kai yayi kafin yace"Ok kuna Wani Aji ne yanzu..?cike da girmamwa Tace"Ni ina Jss3 ne Ya Ummu kuma Tana Ss2.."
Kai ya Jinjina kafin yace"Oryt..Ku maida Hankali banda Wasa Kunji ko..? Abba na gida..? Yafada Lokaci Daya yana Fiddo da Wayarsa Cikin Aljihun Bakin Wandon Dake Jikinsa,kai ta gyada kafin tace"Insha Allahu Yaya..Eh Abba na nan Umma ma Tana Shashensa.."
Bai ce komai ba Illah Mikewan Dayayi ya Nufi Barayin da Zai Sadashi da Shashen Abba Kabiru Nan ya sake cin karo da Ummu salma Ta Fito Daga Falon Umma,Rankwafa Tayi Tana gaisheshi kallo Daya yayi mata ya kauda kai ya amsa a cike ya Wuceta da kallo Ta Bishi Tana Tura mata Baki Acikin ranta Tana Fadin Ya Hashim ya fishi Kirki Sosai Shi ko kullum Fuska Ba Annuri,bai Jita ba Ammh yaga Sanda TaTuramai baki bai bi Ta kanta ba Domin Shi yanzu Aneesa ce Agabanshi.
A kofar Falon ya Tsaya yana Doka Sallama Hajiya karima da Suke Kira da Umma ta amsa mai Lokaci Daya kuma Tana mikama Abba Kabiru Tea din Data Hadamai Awani kofin Tangaran Ya karba kenan Kasim ya Sawo kanshi Falon lokaci Daya yana Zame Takalmin kafarsa Kusa da ,Umma Ya zauna Wacce ke Zaune kusa da Abba kabiru Akan Cafet yana karyawa Domin ga kayan karyawan nan nashi Bisa Wani Katon Tire Dake gabansu.
Cikin Sanyin Murya yace"Abba barkanmu Da Safiya,Umma ina kwana..? Dukkansu suka amsa Cikin Sakin Fuska Kafin Abba Kabiru yace"Kasim yanzu kake Tafe..? Ya wajen Aikin naka.? Yafada yana Kurban Tea din Dake Hannunsa,Cikin girmamawa Kasim yace"Eh Abba,lafiya lau ba Wata mtsala.."Abba kabiru yace"Masha Allah.."Daga Haka Falon ya Dau Shuru Abba kabiru na Cigaba da Kurban Shayinsa kafin ya Dire yana Fadin"Ke ko Karima Wani Lokacin kina da Wauta kinga yaro ya Dawo da Safe,baki Hadamai Abun kari ba,kila bai karya ba ammh kin zauna kin Zuramai ido Mtseee..."Ya saki Tsaki Cike da Jin Haushi.
Fuska Umma Ta bata kan Tace"Ikon Allah Alhaji Shi kasim din yaro ne,balle ace sai an mai Nuniya ko Dole,ko kuwa gidan bakonsa ne? Naga in yana Bukata da kanshi zai Shiga Kichen ya Nema.."Tafada Tana Kauda kai Dariya Abba kabiru yayi kafin yace"Wannan ba Hujja bane,Koda yake Dan Gida amatsayin Bako yake Zuwa Tunda Ba Anan yake Zaune ba.."Baki Ta Tabe kafin Tayi mgana Kasim yayi Saurin Cewa"Ah"a Umma bakomai Na Riga na Tsaya Kan Hanya na karya sai dai Zuwa anjuma.."dariya Umma Tayi kafin Tace"Toh kaji ma kai da Kadamu kanka.."Harara ya Jefamata kafin ya Cigaba da Shan Tea dinshi Umma na Dariya kasa kasa,kasim ma sai da ya Murmusa sanin Halin Abba Kabiru yana da Fada Sosai Umma ce kuma Daidai Dashi.
Cikin girmawa Kasim yace"Abba Dama ina son mgana Dakai ne.."Abba kabiru na Sauke Kofin Hannunshi yace"Topha..Wata mgana kenan kasim..? Kan Kasim na Kasa yace"Kan mganar yarinyar Danake Nema ne.."
Gabadaya Suka Zubamai Ido Cikin Fara"a Umma