Showing 78001 words to 81000 words out of 122554 words

Chapter 27 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt

26 Jan 2025

23759

Addu"a kafin su tashi matan suka Shiga ciki sukayi sallar azahar,mazan kuma suka Fita har da Bello Zuwa masallaci wanda ya muktar ya turasa,Suna Dawowa suka su Fito,bayan Mama falmata ta kara bama Aneesa wasu addu"o'in tace ta yawaita karantamai Amanar Rasuli kafin ya kwanta Tafiyar Jirgi sukayi daman kuma da Zasu koma ma Jirgin suka bi Zuwa Maidiguri Dagachan zasu Shiga mota Zuwa Borno.


****
Wannan Dalilin shi ya karama Aneesa da iyayenta kima acikin Zuciyar Daada da Ya Muktar sukaji Duk Duniya basu da kamarsu su Abba kabiru ne dama ya muktar ke jawosu inta Bello ne ko Daada ko Ajikinsu suma sai suyi wata ko kira basu yi ta waya ba Yanzu Hankalinsu ya kwanta suna ganin mai basu mtsalan yana kwance ba lafiya babu Abunda zai iya yi Shiyasa lokaci daya Shifa da Abba garba Suka cire fargaban watarana Bello zai iya maka su ga Hukuma Tunda bashi ma da lafiya ta kanshi yake.


Hashim ne ke zuwa dubashi in yasamu lokaci shima ba sosai ba,matarshi ko Sau biyu ta taba Zuwa Zubaida kuwa sai D'ayan datazo bata dawo ba dama son bana Allah da Annabi bane na tsabar kyanshi ne,kuma yanzu Babu amfani Tunda ba ma mora,sai dai bare ne ke tafe Zuwa dubashi kowa na kawo nashi Taimakon,Sani da Aminu sune aminin kwarai ga Bello cikin kowani sati suna Hanyar Abuja Duk da Aminun zai Fara Koyarwa da University of lagos kwanan nan ammh hakanan yake Fizgan lokaci yana Zuwa,kasim kuwa ko Sau daya bai taba Zuwa ba,Duk da yana da lbrin duk halin da Bello da Aneesa ke ciki,abakin Abba kabiru ko Hashim sai ya kirasu yana Dukan Ruwan cikinsu Har Ya Muktar din yana ma haka ya kirashi yana Tambayanshi ya Bello..? Aneesa na nan tare dashi,Abun yana matukar bashi Haushi ganin Shuru Target din shi bai yi aiiki ba,shiyasa yayi lambo yana kara Tunanin ya kamata kota karfin tsiya ne Aneeea ta Zama tashi,wacce ta ma manta da wani Hallita wai kasim.


Tun washegarin Tafiyar su Ya Ali Modibbo da mallam inuwa suka Dawo,da sakon Baffa Hardo Aneesa Aka damkamawa bayan an mata karin bayani,gefe guda kuma tana ta Shirin komawarsu kano haka kurum takejin gwara su koma chan suyi zamansu kamar zasu fi jin dadi,Kayansu ta riga tagama Shiryamusu Sauran kayanta ma Ashashen Bello taje ta kwaso,duk da bata Diba da yawa ba,Tunda suna da Wasu achan ana gobe zasu koma chan ta yima Bello aski ta gyaramai kai da Sajensa ta askemai gashin jiki tas,itama tayi Tsifa Alheri ta mata kalaba,bayan angama tazo tana Nuna ma Bello ya Dinga kallo acikin ranshi yana ta yabawa Sabawar datayi Dashi yasa take Fahimtar wani Abu Game dashi in yana son Abu ta Fuskarshi take ganewa toh Ranar ma ta gane yana son ta bar kanta abude karta maida dankwalinta,haka kota Zauna sai in zata Fita ne sai ta saka Vail ta Rufe kanta.


Washegari suka koma kano Ita da Modibbo da Anty Rahila da Daada ,hibba da junoir suka rakasu,Tuni Modibbo yazoma Ya Muktar Da takardunsa shikuma yayi mai alkawarin zai cikamai burinsa,Ya muktar bai bimu kano ba,Ranar ma yana Zaria yazo Jaji passing out,Tun kafin suje Aminu ya kai kanwarsa Raihana taje gidan ta gyara ko"ina hatta kichen duk angyara an zuba sabon cafane an zubar da wanda na bari Duk sun Rube,abinci kuma Ammi ta Dafo suka zomana Dashi bayan mun Sauka Salihu Maigadi kuwa baki har kunne yana ta kwarara ma Bello Addu"ar samun lafiya.


Basu samu komawa Aranar ba sai Washegari ammh kafin su wace sai da suka biya gidansu Aminu suka gaida Ammi kana suka Wuce su kabar ni Daga ni sai Modibbi wanda muka sauke cikin Bedroom din Falon Farko koda Suka tafi ma Bello na Haraban gidan Uncle Aminu da Modibbo sun Fita dashi Suma sun saka Fararren kujeru suna hira Lokaci Daya suna Shan iska ko Bello baya mgana ammh kallo Daya zakamai ka Fahimci yana cikin Farinciki.


Niko ina cikin gida ina Jeramana kaya Cikin Wardrope tare da wasu kayayyakinmu,Duka Ruwan Addu"an munzo dashi harda su na Fito dasu Kusa Tunda Amfanin kullum ne,bayan na gama kuma na Fada kichen nema mana Abunda zamu ci daddareg gefe daya kuma Hankalina kwance Tunda Bello na tare dasu Modibbo..




Ki biya ki karanta cikin Salama...






*Anitha..*
8/19/20, 11:22 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_


Â
*Wattpad:Janafnancy13*


*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*


    *🅿�27*


Farar Shinkafa Na dafamana da Miyar ganye,sai na Dafamana Zobo na saka cikin Fridge,kafin na karisa girkin ya riga yayi sanyi Fruit na yankama Bello Domin yafi sonshi sosai.


Bello saboda ganin Uncle Aminu ne yasa ya bari Modibbo ya bashi abinci har ya karba,shikanshi Moddibon yana ta mai Tsiya,Sai dai kawai ya sakamai ido,Nan suka Wuni tare Ko sallah zasu tare suke Tafiya da Bello daya ke akwai wani masallaci nan kusa damu nan suka turasa suka je,sai yammh kana Uncle Aminu yamana Sallama ya tafi kan gobe zai dawo suyi sallama da Bello jibi Zai wuce lagos.


Washegari dayazo mai sallama bai Tafi ba sai da ya Daukesa suka Fita cikin gari shi da modibbo Sun dan jima kana suka Dawo gidan,Bayan Uncle Aminu yayi muna sallama kan sai bayan Wata Daya zai dawo ammh kanwarsa Raihana zata dinga Zuwa tana taimakamin Tunda tana gida bata Zuwa ko"ina Tun bayan candy dinta,Ba wata babbace kamar sa"a tace ko zan girmeta bai wuce da Wattani ba,kullum zata zo mu wuni tare muyi girki tare tatayani na gyara gidan muna yi muna Hira Dayake babu Ruwanta tana da Kirki sosai,ta gayamin cewa School of Hygen take son Shiga da Zarar Result dinsu ya Fito,Ni kuma nace mata namu ya Fito ban Duba bane dayake na abayanmu suka Rubuta nasu jarabawan kenan ina gabanta da Shekara Daya kenan.


Rayuwarmu muke gudanarwa cikin Farinciki Sosai Nida Bello,Raihana da Modibbo na Debemana kewa,Mu zauna muyi ta Hira Bello sai dai ya Dinga bin mu da ido,Sai yammah tayi kana Modibbo zai maida Raihana gida amotar Bello Dayake Tun Muna Abuja Mallam Inuwa ya koya masa Tuki,Bama cikin matsala Nafara maida jiki na,duk ba Ban koma kamar da ba,shikanshi Bello ya kara kyau sai dai Ramar Jiki kawai na ciwo,Koda yaushe y muktar cikin kiran mu yake awaya yana tambayanmu ko muna cikin mtsala,hakama Daada itama kullum cikin kira suke suna tambayanmu lafiyanmu Hankalinsu ya kwanta jin muna cikin Farinciki ba wata mtsala.
Â
Haka zan tsala wanka nayi kwaliya Shima namai gayu Modibbo da Raihana suyi ta kashemana Hotuna suna mana Dariya,Niko a jikina domin na gama Sabawa da mijina Fiye da kowa na Duniya Sirrinsa nawa ne Hakama Sirrina nashi ammh haryanzu bana iya kallonsa Tsaf sai dai na dinga Runtse Runtsen ido Ranar bayan na gama mai wanka zan ciremai gajerun wando na Runtse idanuwana cikin Mistake hannuna ya taba mahood dinshi jin na taba abu kamar icce ya sani bude ido Abunda na gani ne ya Tsorata ni na Kusa sakin ihu jikina na kyarma sakinsa nayi Na Fita Daga Tiolet din Da Sauri kirjina na Bugawa Ranar wankan daban karisa mai ba kenan modibbo ya karisa mai ya shiryashi,kuma Haka na Wuni ban bari mu hada ido ba duk ko na cin kallona dayake yi,Kullum Dare kuma bana kwanciya sai munyi karatun alqur"ani bayan mungama sai na Shafemai cikin da Ruwan zamzam din da Baffa Hardo ya aiko mai dashi,,in zamu kwanta gefe nake kwanciya,ammh saboda ina da mugun barci kafin gari ya waye na gama hayowa cikinsa na kamkamesa ko Tunanin bai da lafiya bana yi toh ina na sani Tunda Cikin barci ne sai gari ya waye na Dinga Dariya ni kadai,kuma bai hana gobe na Sauya wajen kwanciya ba ammh Duk da Haka sai na isa gareshi,na saba kwanciya ina Juye juye Kamar wata yarinya.


Muna yawan Fita Yawan Shakatawa Nida Modibbo da Raihana Watarana ma har gidan Ammi muke zuwa mu Wuni sai yammh mu dawo duk domin muyi keeping Bello company kuma Abunda na lura yana jin Dadin Haka,wani lokacin ma Restaurant muke zuwa muci abinci ayita kallonmu ana Mamaki ga Mutum har mutum aamh babu Lafiya,masu tsausayi kuma suna tayamu addu"a acikin Ransu,Cikin Haka ne Watarana muka Fita Shooping bayan mun je wajen Siyan ice cream,tunda ina bala"in son kayan sanyi,harda gashshiyar kaza,da Kifi ina sonshi sosai domin modibbo na Fita ya siyomana watarana


Shopprite muka je bayan mun gama Siyan ice cream sai muka Shiga Al-pen store,Raihana da Modibbo na baya ni kuma ina gaba Ina Tura Wheel chair din bello,jikina sanye nake da Doguwar Riga kirar bahrain,Baka nayi Rolin da Vail din Rigar karamar jakace Rataye agefen kafadata,sai kafata tana sanye da Ruffafen takalmi mai kyau da Tsari Fuskata babu kwalliya ammh nayi kyau sosai,hannu na sanye da agogon Fata na gucci,Bello ma na Shiryashi ciki wata Shadda saky blue sakamakon Ranar Jumma ce,Riga da wando dinkin zamani kansa kuma na aza mai Hula zanna bukar kafarsa kuma Takalmi ne baki budadde na Fatar damisa,Hannunsa sanye da agogon Fata na kamfanin Rado,Kallo daya zakamai sai ka kara saboda yadda yayi kyau sosai Fuskarsa Na fitar da Annuru kyau da koshin lafiya.


Muna tafe ina Duba Wasu jerin turaren miski,na Sunkuyar da kaina ina Fadin"Na siya mana miski..? Na fada ina kallonsa Kallona yayi kafin ya Lumshe idanuwansa,dariya nayi kawai na Daga hannu zan Dauko ni ban ma Lura da mutanen dake wajen ba sai ji nayi ance"Wanake gani kamar Mr bello..."Aka Fada Daga gabanmu cikin Sauri na Daga kaina ina kallon mai mganar Ido na Zaro ina kallonta Lokaci Daya nace"Anty Jidda madaki.."


Nafada cikin Bayyana mamakina,Hankalinta na wajen Bello sai kuma taji muryata cikin Sarkewa Numfashi tace"Anee...Aneesa Bukar Bulama u again..",Tafada tana nunani cikin Farinciki muka isa ga Juna muka Rumgume,Cikin Fara"a Ta Dagoni tana Fadin"Anee kin girma fa sosai yanzu anyi hankali ko..? dariya nayi mata ina gaida wanda suke tare har su Modibbo suka kariso hannu na ta Rike tana Fadin"Meye haka Anee..? Yana ga Mr bello kuma bisa Wheelchair..?


Tafada muna kariswa gabansa niko sai binta da kallo nake ganin ta kara kyau ta zama babban yarinya,kafin na bata amsa Modibbo yace mata"Ayyah...Baya da lafiya ne Tun bayan wata Takwasa Da suka Suka wuce yake Rayuwa Ahaka.."Ido jidda ta Zaro tana kallon Bello lokaci Daya tayi kasa Agabanshi idanuwanta na Taruwa da kallo cikin Sarkewar murya tace"Innalillahi meya sameshi Hatsari yayi..?


Na girgiza mata kai kafin tace"Ba daya...Daga dare zuwa safe ya tsinci kansa cikin wannan Hali watansa uku akasar india an Dora misa Gwaje gwaje da kuma Ayuka har guda biyu ammh kuma babu wani cigaba shiyasa aka dawo dashi gida ana gwada na Islamic har Allah yasa a Adace..."Hawaye suka zuboma jidda ta dago tana kallon Saurayin da Suke tare Hannunshi ta Riko tana Fadin"Habibi Da"iman kalleshi shine Mr bello dana ke baka lbrin He si my Fisrt luv shina fara so Tun bansan kaina ba..Ka tuna ina baka lbrin He is handsome,brilliant,..Ammh kalli yadda yau Allah ya maidashi.."Tafada tana kara gudan Hawayenta,kusa da ita ya Durkusa yana Fadin"Allah sarki...Sannu Allah baka lafiya a head alot abount u Awajen Jidda my Wife to be...nice to meet u.."Yafada yana mikamai hannu Shuru yayi yana binsu da kallo Aneesa ta kama hannun Bello ta mikamai tana Fadin"Bazai iya baka hannu ba sai dai...Kai ka kama nashi.."Tafada cikin wani yanayi Cike da Tsausayi ya kama hannun nashi yana Mai sannu da Jiki,kafin su mike yana Rike da Hanmun Jidda Jakarta ta Bude ta ciro katin bikinta tana Fadin"Here is my Weeding programme Anee,ina fatan zaki zo ko..? Kai ta girgiza kafin tace"Ban miki alkawari ba...In na tafi baizai ji dadi ba.."Da mamaki ta kalleta kafin tace"Meyasa...?


Cikin Wani kallo Aneesa tace"Saboda Mijina ne..."Ido jidda ta waro tana Fadin"Are u sure..? Modibbo yace"An daura musu aure ba dadewa Lalurar ta sameshi.."Cikin Wani yanayi jidda tace"Allah Sarki...Anee dama na taba fadamiki watarana Kiyayyarki ga Mr bello zata Rikide ta koma soyayyah Allah ya bashi lafiya.."Suka amsa da Ameen kafin su rabu sai da suka karbi Nombar juna,suka rabu jidda na jadaddamata zata zo har gida suka wuce suma suka cigaba da Tafiya,miskin da bata dauka ba kenan sai dai suka karisa wajen Ruwan Zamzam tana kokarin Daukowa taji muryan wata Abayanta tana Fadin"Feedy kalli Namiji har Namiji ga kyau da Zati ammh ya nakasa.."Tafada tana ya fito wacce suke tare Lokaci Daya tana Nuna mata Bello.


Fasa Daukan Goran Ruwan Zam-zam din tayi ta waigo afusace kamar wata zakanya tana bin yanmatan da wani matsiyancin kallo cikin Masifa tace"Ina ruwanki da mijina da zaki dinga Gulmarsa har kina nunashi a kalle shi..? Uban wa yace miki mijina Nakashashe ne,Shegu kawai yan iska masu kallon mazan mutune.."Na fada ina jijjiga jiki tsayawa sukayi suna kallona Modibbo da Raihana suka kariso suna Bani Hakuri shiko yana Zaune bisa kekensa yana kallo yana so yace na bari ammh bashi da baki.


Wacce aka nuna mawan ne ta kalleni ta saki wani Shewa tana Fadin"Au Ashema mijinki ne..? Su masu miji an ji jiki wlh.."Wlh kin ci Sa"a mijin naki dakike hakilo akanshi bai da mamora kemabai miki ba balle ni,da wlh sai nanuna miki ke karamar yar isk..."Bata karisa ba na saka Hannu na Tsinketa da mari Lokaci Daya naci kwalan Riganta ina Fadin"In kika kara Fadin mijina bai da Mamora wlh sai na Datse miki harshe...Kin ci sa"a kura tayi lafiya da lokacin da nake amsa suna Aneesa bukar bulama ne wlh da yau kin gane kuranki banza sakaara kawai.."Nafada ina Huci lokaci Daya ina Ingizata baya ta Fada jikin yar"uwanta,


Dafe kunci tayi tana kallona cikin Mamaki Raihana ne da Modibbo ke basu hakuri niko ko ta kansu banbi ba na isa ga Mijina na Shiga Turasa ina masifa ni kadai kamar Wata Zararriya bansa ya suka kare ba,nidai abakin mota suka sameni ina ta bala"i ni kadai shiko yana Zaune yana ta bina da kallo,Su modibbo na karisowa Rike da ledojin shooping din da mukayi ina ganinsu na Fara masifa ina Fadin"Meye na basu hakuri..? Bakuji me suke fadi ba shegu yan iska kawai wlh sunci babbar Sa"a da ace ada ne wlh sai na koyamata Hankali.."Ta inda nake shiga bata nan take Fita,kawai sai naga sun kalli juna sun kwashemin da Dariya Raina ya baci harda Hawaye na Bude bayan mota ina Tura baki na Shiga kici kicin Sauke shi na sakashi cikin mota,Da Sauri modibbo yazo ya taimakamin muka sakashi cikin mota,shi kuma ya Nade Wheelchair din ya saka Cikin Booth,Raihana ta shiga gaba Shi kuma Modibbo ya Shiga bangaren Direba muka bar Mall ina ta Tura baki da bata rai kansa na kam cinyana ya dameni da kallo ammh naki bari na Mu hada ido.


Har muka koma gida ban saki Fuskata ba,Raihana ko da modibbo da sun kalleni sai su saka Dariya Sai na kara kufuluwa,Har ta tafi gida ban Shiga Harkansu ba,Da na tuna sanda naji suna yabamin miji sai naji wani bakiciki ya cika ni haka in na tuna sanda tace wai namiji har Namiji ba mamora sai naji kamar Zuciyata zata Buga saboda Takaichi har na gama mai Abubuwan da nike mai kafin mu kwanta,ban yarda mun hada ido ba Ranar ma wajen kafafunsa na saka kaina ina tura baki kamar wata yarinya,kamar shi yayimin laifi ko ina ruwan mara lafiya.


Har Washegari ban saki ,Fuskata ba Fara"a ko kadan,Modibbo kuwa bai takaleni ba,sai da Raihana tazo ne na dan saki kadan,har na warware,Shiko Bello cikin Ranshi ma Dariya nake bashi ganin irin salon kishina,Ransa na masa Dadi in ya kalleni Zuciyarsa ta gama Tababbartamai ba iya tsausayinshi nake ba har da soyayyarsa kamar yadda Nawa Son yayi mishi kamun kazan kuku.


*****


Haka muka cigaba da Rayuwarmu cikin jin Dadi da kwanciyar Hankali,Duk bayan sati biyu Ya muktar kan zo ya Dubamu ya barmana kudi duk da bamu da bukatar komai na bangaren Rayuwa sai dan Abunda ba"a rasa ba,iya kula muna samu ba laifi Modibbo da Raihana sun taimaka wajen Debemana kewa sosai,Bello kuma nine Farincikinsa Komai nakeyi yana Nanike dani ko kichen nake ina girki muna tare yana kallona Modibbo da Raihana kullum cikin mana Tsiya suke wai wannan irin Luv haka Sai dai na Zabga musu harara bana bi ta kansu ba.


B.kaita ta kirani awaya take Fadamin sun Dubo Resuilt dinsu ita da Salamatu jibiya,kuma Alhamdulillah sunci duka,har ma zasu Rubuta jamb,in suka ci zasu shiga jami"a nayatasu murna sosai,ammh ni na gayamusu ban Dubo nawa ba domin baya gabana Tunda ko na Dubo ba wani amfani,kula da Mijina Shine Aikina da kuma jami"ata,


Achan borno,kuwa Anty Nafee sai da tayi magana dataji wai har mun koma kano har ni ta kira naki Dagawa Domin kiran Anty Nafee bana alheri bane,ina gani naki Daga kiranta bana son ta Dagamin Hankali ina Zaune lafiya Nida Mijina,aiko tayi ta zagina tana fadin ta cire bakinta,akaina naje na karata babu Ruwanta Ba wanda ya gayamin ni kuma ban damu domin Anty Nafee bata gabana ko Cikin yan"uwana dama bama da wani Shiri sosai.


*****


Yau tun safe dana tashi naji ina kwadayin koko da kosai,Tun bayan da nayi sallar Asuba ban koma ba,Bayan na ma Bello wanka na Shiryashi cikin riga da wando black and white na kamfanin Armani,Da zan tafi kichen ya chanza fuska sai na Turasa muka tafi tare.


Ina sanye cikin Riga da wando na pakistan kaina yana Daure cikin Gyalen kayan,yana ta baya ni kuma ina gaban gas din ina ta faman Juya kosai gefe daya kuma na saka ruwan zafi,na dauko Wata karamar roba inda na Dauko garin kuni na wanda na saka Raihana tazo min dashi Daga Gidansu,Bayan na kwashe Kaskan farko na zuba wani,sai na koma wajen Dama kokon na Dauko karamar tukunyar da ke cike da Ruwan zafi kawai tsautsayi sai Hannu Daya ya Subuce Ruwan ya kware,da Sauri na saki Tukunyar nayi tsalle gefe ina Sakin kara,lokaci daya ina yarfe kafata inda Ruwan ya Tabeni ina Hawaye cikin Son ya mike ya kasa Cikin ikon Allah kawai naga ya Daga Hannnunsa na Dama yana miko cikin Razana da Tashin Hankali.


Ai mancewa nayi da Kunan danayi na isa gabanshi da Sauri ina kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login