Showing 84001 words to 87000 words out of 122554 words

Chapter 29 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt

Advertisement

26 Jan 2025

23950

Falon Farko na Modibbo ina jiyo Hiransu Daganan Don na Lura suna yar gyada,Haka takemin koda yaushe In taga Aikin gida sai Ammi ta Turo ta taimakamin Babu Abunda Zamu ce ga Uncle Aminu sai godiya Domin Sun mana komai agarin kano Raihana ina jinta tamkar yar"uwata ta jini,Duk da Anty Aisha ma ta yawan Zuwa Dubamu ita da mijinta.


Muna Zaune suka Shigo Modibbo an sha wanka wai zasu Fita Cikin gari,ko zamu Fita..? Nace adawo lafiya ba inda zamu nida mijina muna gida Dariya suka samun Suna Tsokana na wai ina kishi Bello ne shiyssa na daina yarda muna Fita tare na Tura baki ina Fadin eh din haka suka Fice Ina Fadin suyomana Tsaraba.


Ko Minti goma Sha biyar basu yi da Fita ba na mike ina Fadin"B.love na kawo maka Fruit? Ido ya kada min,Na ijiye littafin Hannuna saman kujera na Nufi kichen yabini da kallo,ina cikin yayyankamai kankanan naji Shigowar Mota nayi Dariya ina Fadin"Tsegumanmu ko sunyi mantuwa ne..? Duk azatona na Su modibbo ne.


Hankalina kwance na gama Shirya komai na Zuba bisa wani Filet mai Fadi na Dauko mana karamin knife guda Daya,wanda zan bashi dashi nima naci Tunda ya koyamin Nima cin Fruit ina Kokarin Fitowa naji motsin Shigowar Mutum Falon da muke ban kawo komai ba na Fito ina Fadin"Meya dawo da ku..?ko kunyi mantuw...."


Sauran mganarne ta makale ne ganin wanda ke tsaye cikin Tsakiyar Falon,yana sanye cikin Riga da wando Na Kamfanin Armani,Rigar jikinsa mai Dogon Hannu ce,fara mai Ratsin baki haka wandonsa kafarsa baki me sai Rufaffen takalmin dake kafarsa,ya kara girma da haske,Fuskarsa na cike da wani munafukin mirmishi Lokaci Daya yana Kada key din hannunsa cikin wani izgilanci.


Filet din hannuna na saki lokaci Daya naja da baya ina Nuna shi da Yatsa bakina na motsi..."K...






Ki biya ki karanta cikin Salama...




*Anitha...*
8/19/20, 11:23 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_




*Wattpad:Janafnancy13*


*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*


    *🅿�29*


"KASIM....." Tafada muryanta na rawa Cikin kaduwa.


Mirmishin mugunta ya saki kafin yace"Yes princess...." Yafada yana Kura mata ido cikin kallon Kurillah Cikin kwarewa a bariki Har wani Shafa sajensa na Fuska yake Lokaci Daya yana Sakin Mirmishi.


Aneesa Da jikinta ke rawa ta juya tana kallon Bello wanda Gabadaya Hankalinsa da idanuwansa na kan Kasim ne yana kallonshi cike da mamaki Lokaci Daya Kuma Tsoro ya bayyyana akan Fuskarsa.


Kasa karisowa cikin Falon nayi illah kaina Dana Sunkuyar ina Raba Ido Duk da Nasan kasim da Bello yan"uwan Juna ne ammh Jikina bai bani da Zuwansa awannan Lokacin ba.


Cikin Takun sa na yan Duniya yafara Taku Zuwa gaban Aneesa bata sani ba sai dai kawai Taji Hucin Numfashinsa Bisa Fuskarta tayi kokarin Taja da baya yayi Saurin Riko Habarta Lokaci Daya yana kallon kwayan Idanuwanta,Cikin Aneesa ya sake Daukan Rawa Cikin Rawar murya tace"Don...Allah...Ka....Ka sakeni.."Tafada tana kokarin kwace kanta,sai ma ya Hada da hannunta duka ya rike da Dayan Hannunsa,Yana Dariya cike da mugunta ya waiwaiya yana kallon Bello Wanda Saboda Bacin Rai idanuwansa sun Chanza Launi..


Cikin Wata Murya ya Shiga fadin"Kalli yadda na koma Saboda ke princess na rame na lalace Tunda na rasa ki ban kara samun Farinciki ba,Ammh ke kalleki kina Zaune Babu Abunda ya Dameki meyasa kikeda Taurin kaine..Kice ya sakeki Kizo mu Rayu Tare domin Dani kika fi Dace bada shi ba..."Yafada cikin Muryan Rauni Lokaci Daya kuma yana Sakarmata Makirarrun Idanuwwnsa wanda yake amfani Wajen yaudaran yaran Jama"a.


Itama kallonsa take Cike da Tsana da Takaichi kafin ta Daddage ta Fizge kanta Lokaci Daya da Hannunta Tana Hararansa,Nishi take saki cikin Fada tace"Mallam ka Fice mana Daga gida bama Bukatarka...Kuma ka Rubuta ka ijiye ni Aneesa Bukar Bulama ko Yau aka wayi gari B.luv ya bar gidan Duniya Wlh Tallahi sai dai ka Mutu na Mutu ammh bazan Taba Auran ba..Na Shafe Babinka Acikin Rayuwata sai Bayan Haka ta Faru ne ma na Fahimci ko Abaya ban soka ba kasim kawai Wani Kadadaren al"amari ne Daga Ubangiji yasa na amince Dakai..."Tafada idanuwanta Sun kawo kwallah..


Ran kasim yafara baci cikin Budewar ido yace"Kina Nufin Kindaina sona saboda wannan Musakin Nakashashe mara amfani balle Mamora..?yafada yana Nuna Bello wanda ke Zaune yanaji da zai iya tashi da yanzu kasim yazama sai Tarihi.


Wani mirmishi Aneesa ta saki kafin ta koma bayan Bello Tana Fadin"Eh...kaga wannan,bata bashi Zarafin Mgana ba tacigaba da Fadin"Yafi ye min kai Sau Dubu Miliyan Goma..Kai ne mara amfani kuma wanda baida Mamora ammh ni mijina Yana da matukar amfani awajena da Kuma Rayuwata..."Tafada Tana Dawowa ta gaban Bello Ta Tsaya Lokaci Daya tana Harde Hannuwanta Bisa Kirjinta.


Dariya ya saki harda Rike ciki kafin ya dago yana Fadin"Karya Kike princess Bazaki Fada bane kawai Ammh kina Cutuwa Wata Mamaora awajen wanda ko kansa bai iya ma wani Abun...princess ki bar wannan Maganar kizo mu tsara rayuwarmu Kibar wannan na Zaune bazai iya yi miki komai ba,Ni ne Cikakken Namiji mai cikakken Mazantaka.."Yafada yana kashe mata ido Daya.


Cike da Haushi Aneesa tace"Sai kayi kuma..Dama Ai mai Hali baya fasa Halinshi kayi kuskure Tunanin Haryanzu kana Raina...Tuni na Shafe babinka Acikin Rayuwata,Kazo ka Fice mana Daga gida tun kafin na Tara maka jama"a.."


Dariya kasim yayi kafin kuma ya koma Daure Fuska yana Fadin"Taurin kanki Zai ja na aikata Abunda ba Haka naso ba princess..."Cikin mamaki da Tsoro take kallonsa Cikin Kaasa kasa da ido yace"Yes...Na lallasheki kin ki jina,toh yanzu ai zakiji ni dakyau...Naso sai acikin gidan Auren mu akuma kan gadonmu,zan Dandani Zumarki princess,ammh kin kasa Fahimta ta Saboda Haka yanzu zan Karbi Abunda yake dama nawane a gaban idon Wanda kike kira Mijin naki .."Yafada yana Sakin Siririyar Dariya...


Aneeea data Tsorata Taja Baya Lokaci Daya tana kallon Bello Wanda Shima Fuskarsa ta bayyana Tashin Hankali,ganin Kasim na Nufota yasa tafara ja da Baya Hawaye sun Fara gudu Bisa Kuncinta Cikin Magiya ta shiga Fadin"A"a kasim kar kamun Haka Karka manta Nifa matar Aure ce Don Allah karka ketamin Mutumcina..."Tafada Tana Hada hannuwanta,cikin kuka.


Dariya ya saki yana Fadin"Ki adana Rokonki Nima bazanji kiba kamar yadda ke ma kika jin nawa..."Ganin Ya kusa cimmata yasa tabi ta bayan Bello ta kwashi Guda Zuwa Daki Zaraf ya Bita Cikin kwarewa ya saka kafa ya Tarota tatafi luu sai gata Bisa Kirjinsa tana ganin Haka tafara kokarin kwaceta kanta tana Fadin"Ka sakeni mugu kawai...Zan maka ihu zan tara maka jama"a.."Yana Daga mata gira yake fadin"Dagaske...? Toh yi ihun mugani ko za"a iya kwatanki Ga Mijin naki nan Zaune agaban idanuwansa zanji Dadi Dake In ya isa ya tashi ya kwaceki.."Yafada yana kai kanshi Bisa Wuyanta kuka ta saki da kara Lokaci Daya Tana Fadin"Na shiga uku...Wani ya taimakeni.. "


Take fada tana kallon Bello Wanda ke kallonta Idanuwanta Sunfara Zubar da kwallah,Kokarin Tashi yake kakafunsa Suna rawa ammh ya kasa,Shiko kasim bakinsa yakai wajen Wuyan Aneeesa yana Shinshina Lokaci Daya kuma yashafa Kanta gashin kanta wanda ya Sabule mata Dankwali,zuwa bayanta da Tudun Kugunta yana wani lumshe ido kamar Tsohon maye,Aneesa ta kurama Bello ido Hawaye na Zubomata Hannunta ta Mika mai cikin Kuka tace"Ka taimake ni...Kada ka bari ya ketamin Haddina don Allah..."


Dariya kasim ya saki yana yana Tura kanshi Cikin Kirjinta Lokaci Daya ya saki Numfashi yana Fadin'Bazai taba iya kwatanki ba...Har Abada bai da amfani..."yafada yana Tura Aneesa Bisa Kujera cikin Dariya yake kokarin Balle Blet dinsa cikin Farinciki,bai ankara ba sai yaji Anbugamai wani Abu Asaman keyarsa wanda ya kusa shashi Faduwa yana ganin Jiri


Taga Taga yayi zai Fadi ya Sunkuya yana Rike kujera Da Hannu Daya,Dayan hannun kuma yana Dafe keyarsa data Fara Zubda Da Jini,Da Sauri ya waiga yana kallon Bello Wanda Ya saka dayan Hannunsa ya Dauki Wayar Aneesa Dake kan Kujera ya saita keyar Kasim ya Bugamai,wayar tafadi gefe ta rabe,Aneesa cike da mamaki take kallon Bello Kasim kuwa Dariyar Rainin Hankali ya saki yana Kallon Jinin Daya Tabo Daga kansa yace"Au...Ashe kana da Mamora.."


Yafada yana wata Dariya kafin ya Juya yana kallon Aneesa Cikin Mirmishi yace"Bazai taba iya hanani Kudirina ba.."Yafada yana Nufarta Cikin,Sauri tafara matsawa Jikin Kujera ammh ya saka hannu ya jawota ya karisa Cire Belt dinsa ya Danneta yana kokarin Hada bakinsu Waje Daya kara Aneesa ta saki taneman kwatan kanta Mari ya kifa mata yana Fadin"wlh in baki tsaya ba Zan miki dukan Tsiya kuma na aiwatar da kudurina..."Yafada yana lasan Wuyanta.


Kuka take tana Tureshi Bata Saki Wata kara ba sai Dataji yana Taba kasanta da Hannunsa yana kokarin Cire mata Sikat din Jikinta karar Daya karade gidan gabadaya Hatta Salihu maigadi Dake Zaune sai da ya mike Afirgice,cikin tashin Hankali yana Kallon Cikin gidan.


Bello kuwa karar Da Aneesa Tayi Ita ta dinga mai amsa kuwwa acikin kunnansa Idanuwansa suna ganin Dishi Dishi ganin kasim ya fara Kokarin Raba Aneesa da Rigar Jikinta Cikin Mika Hannu yana Kokarin mikewa ammh ya kasa Sai kawai ji yayi ya Furta..."Aneesa...!


Cikin Wani Amon Tashin Hankali Daga ita har kasim sai da Suka waiwaya suna kallonshi Cike da mamaki,ganin Hannun sa na Dama yadagashi yana miko mata Duka hannuwansa,Ganin Yadda kasim ya shagala da kallonsa ne yasa ta sakarmai cizo mai Zafi adamtsen Hannunsa ya saki kara tayi Saurin ingijeshi Ta mike tana Sakin Numfashi Tana kokarin gyara Rigarta Daya fara Sabule mata Cikin kuka ta Nufi bello Daidai Lokacin kuma da Modibbo da Raihana da Salihu mai gadi suka Shigo.


Cikin mamaki Suke bina da kallo lokaci Daya kuma suna kallon Kasim Daya mike yana Gyara wandonsa Cikin Dan Rudewa,Modibbo ya ware ido yana Fadin"Matar baffale wai meya ke faruwa ne..? Mun shigo Salihu ke fadamana yaji ihu acikin gida wani Abun ne ya Faru..? Wannan fa..? Yafada yana Nuna kasim.


Na kasa mgana sai kuka nake Ina kallon Bello Kukan Farinciki nakeyi bana Komai ba,ban gama mamaki ba naga ya saka Duka hannuwansa ya Dago kafadata na mike ina kallonsa Bisa Cinyarsa ya Zaunar dani Yana kallona Cikin wani yanayi Hannunsa Ya sanya yana Sharemin Hawaye,yana kuma kallon Kwayan idanuwanta,Bani kadai ba Hatta su Modibbo sun Daskare da mamaki Bamu kara Sakin baki ba sai da muryansa ta Daki Dodon kunnuwan mu..


"Ku Fita dashi...Har Abada kar a kara bari ya sake shigowa gidan nan Salihu.."Yafada cikin kasaitattaciyar muryan nan nasa mai Cike da amo da Zati,ai sai modibbo yayi kasa kawai bayan ya kalli gabas,yana kwarara kirari ga Allah,Raihanaa ma baki yaki Rufuwa,Haka Salihu maigadi dayayi kasa yana Fadin"Allah Abun Godiya yallabai..bakinsa ya Bude.."


Kasim kuwa Jikinsa ne ya Fara rawa mai Hakan ke Nufi Bayan ance har Abada Bello bazai kara mgana ba Balle Motsi da wata gaba na Jikinsa,Gabadaya Zufa ke ketomai,ganin modibbo ya Nufi Bello ne yasa ya zare jiki ya Fice Ba wanda ya Lura dashi ammh Bello na kallonsa Suka kuma Hada Ido Lokaci Daya Bello ya sakarmai Wani Boyayyen Mirmishi.


Kasim har yana Tuntube ya Fice Zuciyarsa na Buguwa taya ya kuma Haka Zata Faru...?Alhalin Kuma An Tabbatar mai da Cewa haka zai kare rayuwarsa Cikin Mutuwa ko Rayuwa..? Cikin rawan Jiki ya Fada Motarsa ya Bata Wuta Allah ya taimakeshi Tun Sadda Salihu maigadi ya Budema Modibbo get yana Cikin Rudani bai Rufe ba Shiya bashi Damar Ficewa Da Gudu ko Da Salihu ya Fito ya fice maida get din yayi ya Rufeshi yana Tunanin Duk yadda akayi Kasim ba Mutumin Arziki bane..."




Modibbo kuwa Bakinsa yaki Rufuwa Fadi yake"Baffale wai yau kai kake mgana..Allah Abun godiya.."Yafada yana kwallan Farinciki Nima kwallar nake ina kallonsa shiko kawai Mirmishi kadai yake sakarmana bai kara mgana ba Modibbo ya Mike Jiki na rawa yana Fadin"Bari nayi ma Ya Muktar albishir..."Yafada yana Dariya nan take kuwa ya kirashi yana gayamai Ya Muktar Dake Shashen Daada ya mike da karfi yake Fadin"Midobbo bama irin wannan Waasan dakai are u Telling me d Truth...."?


Bai yi mgana ba Illah Saka Wayar Cikin Speaker Dayayi ya kanga ma Bello yana Fadin"Gashi zai maka mgana..."Shima ya Muktar din wayar ya saka cikin Speaker Daidai Lokacin da Bello yace"Ya Muktar....."Cikin Sanyin Muryansa.




Allahu Akbar.....Ai Dagashi Har Daada sai gasu sun Zube kasa Suna kwaroroma Allah Kirari na Godiya da Yabo Cikin Hawayen Farinciki Daada ke Fadin"Zaka Tashi da izinin lahi..Zaka taka da kafarka da yardan Ubangiji Megidana..."Cikin Mirmishi yace"Ameen Daadata..."Ya Muktar yace"Gamu nan tafe yanzu...Gani nake kamar ba gaske ba..",Daga Haka ya yanke Kiran Anty Rahila na Bedroom dinta Ya Muktar ya Shigo da wannan Lbrin bayan ya Dagata sama yana Juyi da ita Cikin Farincikin Data Dade bata gani ba.


Raihanaa kuma Yayanta ta kira Uncle Aminu ta sanar dashi Shima bai gasgata ba sai da aka bama Bello yaji Muryansa,Nikuwa Farinciki ma ya Hanani mgana,Dakyar ya yarda na Sauka Daga kan Jikinsa na Dauki wayata na Hadata sai gata ta dawo da aiki Mama falmata na Fara kira na gayamawa Ita ma tayi Murna sosai Daga ita sai Ya Ali Shima wai kin yarda yayi sai dai aka bama Bello sukayi Mgana Duk wanda yaji lbri sai ya Jinjinama Kudaran Ubangiji mai Hikima da kari ga Mgana Lokaci Daya kuma Hannunsa na Hagu ma ya Mike yanzu Abunda ya Rage kawai Shine kakafunsa da kugunsa Suma Insha Allahu Komai Zai Daidaita.


Kasim kuwa Tun yana Mota ya Kira Haruna yana bashi lbrin Abunda ya gani Cikin mamaki Haruna yace"Kai toh garin yaya Haka ta faru...? Kasim yace"Ban sani ba ammh tabbas hannayensa Duka suna motsi kuma naji da kunuwana yayi mgana..."Cikin mamaki Haruna yace"Ikon Allah...Gaskiya akwai mtsala Toh yakamata mu koma Muji Yadda Abun ya koma Haka.."Kasim yace"Ya kamata Har Abada bana Bukatar ganinshi yana Taku adoron kasa,yadda na rasa Aneesa Shima ya rasata har Abada.."Haruna yace"Ba mtsala zan shigo katsinan sai mu tsara tafiyan.."Daga hakan kowa ya yanke Kiran cike da mamaki.


Ya Muktar,Daada,da Anty Rahila Hibba da Junior wajen La"asar sai gasu Jirgi suka Biyo Modibbo yaje Filin jirgi ya Taho Dasu,koda suka zo na sake ma Bello wanka na gyarashi tsab yau wankan yasha Bambam Domin munyishi ne Cikin Farinciki,yana so mu hada ido ni kuma Kunya nakeji,wajen samai kaya ma Jawoni yayi jikinsa Cikin Muryansa mai cike da Izza yace"Bai miki komai ba ko..? Kallonsa nayi kafin na Rausayar dakai na girgizamai kai,Ajiyar Zuciya ya Sauke Lokaci Daya yana maida Numfashi,Miskili kenan Koda bakinsa ya Bude baiyi Mganar Data kai goma ba sai dai kawai ya Dinga Bina da Ido......


Raihana ta taimakamin muka Shiga Kichen muka Dafa Musu Farar Shinkafa da Miya sai slat,Sai muka hada musu da kunun Aya,Sanda suka iso ina wanka,murna kamar bakinsu bazai Rufe ba Ya Muktar Rumgume Bello yayi yana Murna da jin Dadi Haka Daada,Hibba ko da Junoir Duka kan Jikinsa ya Dorasu cikin Sanyin Murya yake Tambayan Hibba ya makaranta itako Fadi take Uncle ka warke ne .? Kai ya gyada mata yayi yana Mirmishi.




Sai da na Shirya kana na Fito Cikin Riga da Sikat,na atamfa Rumgume Juna Mukayi Nida Anty Rahila da Daada Ya Muktar kuwa Fadi yake sannu da kokari Anee ta Bello.."Mirmishi kadai nake ina Satan kallonshi wanda ke Sauraran Hirar Hibba.



Sai da akayi sallah kana aka baje Afalo aka ci Abinci Shidai ne bai ci ba Domin dama baya wani Cin Abinci Sosai yana Zaune Bisa Wheelchair dinsa Yana bin mu da kallo Kuma wani Ikon Allah Dagani har shi ba wanda ya sanar ma da kowa Abunda ya Faru na Zuwa kasim muka ja bakinmu mukayi Shuru.


Kwana biyu su Daada Suka mana,Kafin su koma Bayan sun Biya gidan su Uncle Aminu Sun kara musu godiya Harda Ya Muktar,Komawarsu Abuja dama Tun kafin su tafi Ya muktar ya sa akawo masa Tirela guda na Shinkafa yace Duk arabama Mabukata tare da Addu"ar Allah ya Kara bama Bello lafiya.


Daada kuwa Baffa Hardo ta kira tana gayamai Mirmishi yayi mata yana Fadin"Karki damu...Tafiyarma Lokaci kadan ne zai zama Tarihi..."Daada taji Dadi sosai kuwa nan da nan ta saka Suma Ya Muktar ya aika musu da Tirela guda na Shinkafa da masara da Kudi arabama Dangi mabukata,tare da addu"ar Allah ya kara bama Bello lafiya.




Kibiya ki karanta cikin salama




*Anitha...*
8/19/20, 11:23 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_




*Wattpad:Janafnancy13*


*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*


     *🅿�30*


*AFTER 1 WEEK...*


Duk wanda ya kamata yaji Abun Farincikin Daya samemu yaji Barin ma ni,Gani nake duk wanda bai zo ya tayamu murna ba,ba masoyin mu bane,Hatta Uncle Aminu Dake lagos yazo Yaga Bello ya kara Tabbatar da Idanuwansa Haka suka Sarke hannayen Juna Suna Mgana Cike da Shaukin Abota da kuma Farinciki mai girma.....


Abba kabiru kuwa Abakin Ya Hashim yaji labarin Budewar Bakin Bello bai zo ba sai da ya kira ya muktar din ta waya sukayi mgana hakama Abba garba,Shidai ya Hashim din ne yazo har kano shima bai Dade ba ya koma,Zubaida ce kadai ta damu da Halin da Bello ke ciki ammh banda Zulfa wacce Ta Dinga Godema ma Allah,Inna Rukayyah ma Tunda muka zo kano bata leko ba Tun Muna Abujan ma Sau Daya tazo,ba wanda ya damu Hatta ko Shi Uban gayyar Ya muktar Tunda Abun nan ya faru Hankalinsa ya koma kan Bello toh balle Shi Gwarzon da basa gabanshi da Zuwansu da rashin Zuwansu Duk Dayane shi awajensa,Kokarin da Shakikansa Sukeyi akanshi yafi komai yin Tasiri acikin Ransa.


Bangaren kasim kuwa Haka ya koma katsina yana cizon yatsan Rashin Cimma Buransa kan Aneesa,Da kuma Fargaban Samuwar Bakin Bello tare da Motsuwar wasu sassan Jikinsa,gefe Daya kuma ga Aisha ta dameni shi da kira,Akan wai yazo gida ta riga tagama gayama iyayenta komai akanshi Haushi ta bashi ya Rufeta ta daina samunshi Sam,Yariga yasakama Ranshi bayan Aneesa babu wata macen da zai iya zaman Aure na har Abada da ita sai dai ya Yaudareta yaji dadi da Jikinta kawai.


Kwana Biyu Tsakani Haruna yazo Suka Tafi chan kauyen Niger Delta suka samu Bokan Suna mai Complain Abunda ke Tafe dasu ya dade yana Dube Dube kafin ya kora musu Bayanin Halin da"a ake ciki ya sanar dasu Aljanu sunyi kyau Sosai akan Bello Domin Jaki ne Da Ranshi aka Binne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login