Showing 51001 words to 54000 words out of 122554 words
Chapter 18 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt
Tana kallonta Lokaci Daya tana Zubar kwallah.
Gyada mata kai tayi kafin tace"Eh ban yafemiki ba..Saboda Sune ginshikinki..Kuma Bangonki kuma garkuwanki ko Bayan Raina Ban yafe miki ba Matukar kika Bijirema Umarninsu Dukkansu ba.."Kuka Aneesa Ta Fashe dashi mai karfi Falmata Dake Danne Hawayenta ta cigaba da Fadin"Ina miki Fatan Samun Gidan zama har Abada..Ya albarkaci Aurenki kuma ya Raya Zuru"ar Da zaki Haifa,Tashi kuje Aneesa In kika Rike Abunda na baki Har Abada zaki Rabauta Tashi kuje..Allah yayi miki albarka.."Tafada lokaci daya Hawaye Suna wanke mata Fuska.
Da Gudu Aneesa Ta mike ta Isa jikinta ta Fada mata Tana Shesshekan Kuka,Lokaci Daya Falmata ta Rumgumeta tana Bubbuga bayanta,na Tsawon Minti Biyar kafin ta Saketa ta Juya ta Shiga Cikin uwar Dakinta da Sauri Tana Share Kwallah,Dukewa Aneesa Tayi Tana Gunjin kuka Lokaci Daya Ta Dauki Qur'anin da Hisnul muslim din Data ijiye Agefe Ta Rumgume Tana kuka Lokaci Daya Wani Son Mahaifiyarta ya kara Lullubeta Domin Ta bata Abunda ba Wanda ya taba batashi.
Koda 3:50pm tayi Suna Filin Jirgin Maiduguri,4pm Daidai na Yammah Jirginsu ya Tashi Zuwa Abuja Acikin Masu Rakiyan akwai Anty Yagana,Anty Nafee,Anty Aisha,khadija Matar ya Ali,sai Cikin Dangin Babanta Guda biyu,sai Aneesa da Sanah,B.kaita,S.jibiya,Da Anty Rahila da Hibba da Junoir,sai Ya Muktar sai Daada, kadai Suka Tafi Mama yana Ita sai bayan kwana Biyu Zata zo da Sauran kaya,Har Jirginsu Ya Daga Aneesa Na Dunkule kanta Cikin Cinyoyinta Tana Kuka,mai Cin Rai ba wanda yabi ta kanta Tunda batajin Lallashi.,gefe Daya kuma Tana Rike da Abunda Falmata ta bata bata yarda ta bama wani Ajiya ba.
*******
Tawagar su Kasim Duk Agidan Abba kabiru suka yada Zango,Lokacin Gida ya cika ya Tumbatsa da yan"uwa da Abokan Arzuka anata Hada Hadar Arziki,Hatta gidan Abba garba Duk suna gidan Abba kabirun,Inna Rukayyah ma Tazo Ita da gayyarta.
Sai ga shi Sun Dawo da Mugun lbri Wanda ya girgiza mutane Dadama,Gabadaya a Falon gidan Suka yada Zango Abba kabiru na maida Bayanin Abun ya Faru Kasim na gefe Kan Cafet Shida Abokinshi Haruna,Sauran Abokansu kuma Wasu Daga Filin jirgi suka Dauki Tasha Mota Suka Koma Kaduna,Haruna ne kadai Tare Dashi Domin Shine Babban Abokin Ango.
Lokacin da Abba kabiru ya Furta da Bello Aka Daura aure Zulfa da Zubaida Atare Suka Mike Dafe da Kirji,lokaci Daya Suka Kwalolo ido Zubaida ce Tace"Wani Bellon Abba..? Dakuwa Abba Kabiru ya sakarmata kafin yace"Bellon Ubanki Shegiya,bama zaki Jajantama Dan"uwanki ba bisa Tozartanshin da Bellon yayi ba,A'ah ke Naki Tunanin Dabam Sakarya Kawai.."
Â
Yafada Cike da Takaichi kamar ya Fashe da Kuka,zubaida da Zuciyarta ke Bugawa ta saki kuka kafin ta Fice Daga Falon ita kuwa Zulfa Dabas ta koma ta Zauna Kusa da Mama Sahura tana Jin kamar Hajijiya zai kwasheta ganin Haka yasa Mama Sahura ta Rikota Lokaci Daya tana Girgiza mata kai Inna Rukayyah ce ta Mike Tana Fadin"innalilahi...Ammh Wannan yaron Bello anyi Tijararre ya Kabiru,toh ku Wani mataki kuka Dauka Akanshi..?
Abba Kabiru yace"Hmm Rukayyah kenan Wani Mataki Zamu Dauka Tunda bamu da Gaskiya inda Shi kasim din ya Rike Mutuncin kanshi da Duk Sonshi daya Tozartamu Ai bazai samu Dama ba,Ammh Dayake ka Haifi Da baka Haifi Halinshi ba Abunda Yakeso Shi yaje yana Aikatawa.."Yafada yana Hararan kasim din Wanda kansa ke Duke yana Tsiyayan Kwallah
Abba garba yace"Toh kai Yaya Kana Wata mgana Allah ma ya Taimake mu ba wani Jami"in Tsaro Ai da Tuni muna an Tsarenmu yaron Daya Dinga mganganu yana nuna mu mukayi Sanadiyar Mutuwar iyayensa kuma muka Cinye musu Dukiya ku godema Allah da Abun ya Tsaya iya Haka Yayi Hakuri ba ita kadai bace Autan mata zai samu Wacce Ta Fita,kuma ka Kyaleshi karmuji kace zaka Dauki mataki domin Wannan yaron yafika Tantiranci..."Umma tace"Wlh kuwa Allah nagode maka ma da Abun Bai Tabbata ba,Domin Wannan yarinyar ba matar kwarai bace..."Tafada Ranta ya mata Dadi Sai Abu Dayane ya bata mata rai yadda Aka Tozarta Hallayan Danta a idon Duniya.
Hashim dai na Zaune kanzil bai ce ba Sai da Kasim ya Mike yana Rangaji zai Fice ya kallesa yana Fadin"Saura kuma ka koma Shashenka kasha giya har ka kasa Tashi,Domin ba Hankali gareka naga Abunda ya Faru dakai bai zama izina gareka ba,In zaka bar Hallayarka ka bari in bazaka bari ba Wlh ko gaba ka Nemi Aure Abunda zai sake Faruwa dakai kenan.." kasim Dake kokarin Fita ya Waigo yana Kallon Kowa Dake Falon kafin yace"Kada ku aika akarbo duk Abunda nakai...Na barma Aneesa Har Abada.."
Yafada yana Juyawa Da Hanzari Umma tace"Ka ce me..? Wlh bata isa ba sai an karbo komai.."Abba Kabiru yace"Ina Ruwanki ba Kudinshi bane,Kuma Tunda yace ya barmata ki kama bakinki kawai malama.."Yafada Yana Hararanta Mama Sahura da Sai yanzu ta saka baki tace"Gaskiyan kam.."Wani Banzan Kallo Umma ta Watsamata itako Mirmishi Ta Saki alamun ke keda Haushi kuma.
Ko jiyowa Kasim baiyi ba ya Fice yana Rangaji Haruna yabi bayanshi Dauke Da Babban Rigarsa da Hula Har part Dinshi,Kan gadonsa ya Fada Lokaci Daya ya Fashe da Kuka Kan Stool Haruna ya Zauna bayan ya Watsa kayan Dake hannunsa kan Wata Kujera Dake Bedroom Din Cikin Bacin Rai yace"Na gaji dajin kukan ka Kasim ka mike ka Share Hawayenka,kamar yadda kace ya samu Nasaran Auren Aneesa ammh kuma Shima yakamata ya kare Rayuwarshi Cikin Kila wakala.."Kasim ya mike yana Share Hawayensa yace"Raina na Kuna Haruna...Aneesa Wacce na gama Tsara Duka Rayuwata da Ita..Kai ina Bazan kyaleshi ba sai na saka an kashemin Shi Har Lahira.."Dariya Haruna ya saki kafin ya Mike ya Dawo Kusa Dashi yana Fadin"Ka kashe shi fa kace..? Haka kurum ka dora ma kanka Diyyah...? Manta kawai Abokina So nake amai Kisan Rayuwa Wanda yana Raye ammh Shida Mattace Duk Daya.."Da mamaki Kasim ke kallonsa kafin tace"Bangane ba..? ..
Mirmishi ya saki kafin yace"Kawo kunnanka kaji.." Nan da nan Kasim ya mikamai kunnansa ya Fadamai Wata mgana Wanda nikaina banji kome Suka ce ba sai dai naga Kasim ya Zaro Ido yana Fadin"Kai don Allah..."Gira Haruna ya Dagamai yana Fadin"Zakace na gaya maka.."Hannu ya bashi Suka Tafa kafin kasim yace",Nagode Abokina....Har kasa naji Farincikina ya kamani Wlh...",Dariya Haruna ya Saki yana fadin"Tashi ka shiga Wanka ka Fito mu karisa mgana.."Jiki na Rawa Kasim ya Mike ya Shiga Tiolet yana Dariya kamar bashi ne yagama Kuka yanzu ba.
*****
Sai Bayan Mangariba kana tawagar Motocin ya Muktar,Suka je Filin Jirgi Suka Taho Dasu Bello Dake Kwance Cikin Bedroom Dinsa Cikin Bargo yaji Dawowarsu Kansa ne ke bala"in Ciwo Tunda Suka Daawo Ganin Halin Dayake Ciki ne ya saka Sani bai Wuce kaduna ba Aranar ya bari sai Washegari,ya Zauna Tare Da Bello,Daga nan ya saka Sani yayi Waya Zuwa Cikin Shashen ya Mukrar akwai Telephone direct Zuwa Kichen,Alheri ce tazo ta kawo musu Abinci da Abunsha Sanin ne kadai yaci Shi Bello Fruit kadai yaci Yayi Taking pracetamol ya koma ya kwanta Zuciyarsa na Kuna Gabadaya Ya Muktar ya batamai bajet,Aneesa fa Bata Daga Cikin matan Dake burgesa ammh Kuma bakin alkalami ya Rigaya daya Bushe.
Shashen Daada aka Sauke Aneesa ita da Kawayenta da yan"uwan babansu,Sauran kuma Su ka koma Shashen baki,agajiya Suke Shiyasa Abinci kadai Suka ci Kowa yabi Lafiyan gado yana Warware gajiya,Aneesa ko yunwa ce Taji Zata kasheta Tatashi Taci Abinci kadan Ta koma ta kwanta Kusa da B.kaita Barci Ranar barawo ne ya Sace Aneesa ammh kwana Tayi kuka,ga Zazzabin Jikinta Saura kuma Suna Dakin Daada chan Suka Kwana.....
Sai da Safe kana ya muktar ya Shiga part din, Bello inda ya Tarar Dashi kwance Cikin Blanket,sai Sani Dake Shirin Tafiya,Gaisawa Sukayi da Sanin kafin ya karisa Gefen Gadon ya Zauna yana yaye bargon da Bello ya Lulluba Dashi Lokaci Daya Yana Taba goshinsa.
Bello Dayaji Motsi sai ya Bude Idanuwansa Da Suka kumbura ya Sauke kan ya Muktar Kokarin Mikewa yake da Sauri ya Rikesa ya Taimaka mishi ya mike Zaune yana Dafe kanshi Cikin Tsausayi Ya Muktar yace"Sannu kan ne..? Gyada kai Bello yayi yana Yamutsa Fuska,Ajiyar Zuciya Ya Muktar ya Sauke kafin ya Mike yana Fadin"Ka Shirya muje Asibiti Anjuma.."Bello ya Dago kansa yana kallonsa bai yi Mgana ba,Saboda Bakinsa yamai Nauyi Lokaci Daya Ya Muktar ya Nemi Hanyar Fita Daga Bedroom din yana cema sani.."Badai Tafiya Zakayi ba.? Kai tsaye sani yace"Eh Ranka ya Dade."
Ya rike Handle din Kofar ya Waigo yana Fadin"Ayyah badamuwa Mungode..In zaka Wuce ina Haraban gida..mungode.."Daga Haka yafice Daga Bedroom din yana Fitowa da wayarsa Wacce ke Aljihun Wandon jallabiyansa.
Sani ya karisa kusa da Bellon yana Fadin"Malamin mkranta Ni zan kama Hanya.."Gyada kai Bello yayi Kafin ya Furta.."Nagode Sani.."Mirmishi yayi kafin yace"Bakomai..Ango plz ka cire Damuwa Aranka Dama chan itace matarka,Mganar kasim kuma karka damu bai isa yamaka Abunda Allah bai maka ba.."
Kallonsa yayi Ido Cikin Ido kafin yace"Nagode Sani..Ammh ni kasim baya gabana karamin alhakine,kai ne zan ce ma ka kula Kada yace zai bataka Wajen aikinka.."Yafada Cikin Sanyin Murna Sani ya Rausayar dakai yana Fadin"Haba bai isa ba ai bashi ya Dauke ni ba,Allah ya baka lafiya.."Yafada Lokaci Daya Suna musabaha kafin Sani ya Dauki Wayarsa ya Fice Daga Bedroom Din Bello yabishi da kallo.
A haraban gidan ya Iske Ya Muktar na mgana awaya sai da ya Jira yagama,kana Suka sake Sallama 50k cash Ya bashi da Farko kamar bazai karba ba sai da Ya Muktar din ya mtsamai,musabaha Sukayi Ya Muktar na karamai godiya Mallam Inuwa Direba ya Daukesa Zuwa Filin Jirgi inda Zai Shiga Wani Jirgin Zuwa Kaduna garin Gwamna
Sun wayi gari Cikin Hidima Abunsu Kamar Babu Abunda ya Faru,Kafin karfe goma baki Sun Fara Zuwa kawayen Anty Rahila na nan Abuja,can sai ga Maman B.kaita ta iso,maman S.jibiya ne Bata samu Zuwa ba bata nan Taje Jibiya,Tuni Dama su Alheri Sun kamallah Girke girke,dama Tun Safe Ya Muktar ya Fice Daga Gidan,Aneesa ko kwanciyarta Tayi Taki Tashi tayi Wanka Tana gani su B.kaita Sukayi Wanka Suka Dau kwalliya bata yi Wanka ba sai da Taga yan Sch dinsu na Kwatar kwashi Sun Fara Zuwa Wata Rabi daga Suleja sai Mariya Daga kaduna Shiya Tilastama Aneesa Wanka ta Shirya Cikin Wani material Riga da Sikat,ta yane Mayafin Material din kamar Lifaya,bata wani yi kwalliya Ba Fuskarta Kodai kodai ba Wanda ya Bi ta kanta gwarama Daada ta Shigo ta mata Nasiha Shine Har ta saki Ranta ta Shige Cikin Kawayenta anata Hira,Su B.kaita Su suka Fara kyankayasama Su Rabi Wanda Aneesa Ta Aura nan suka saka guda Abunda ya kara saka Aneesa Ta Fashe da kuka Suko Suna mata Dariyan Shakiyanci.
Ba laifi Yan makrantarsu Aneesa Sunzo musu,zasu kai goma Kowa Tazo Taji Aneesa ce ta Auri Mr Bello sai Taji Aneesa Tayi Sa"a,Domin Samun Namiji kamar Mr bello abu ne mai Wahala,sai Tambayanshi Suke sai ace musu baya nan Alhalin yana part dinshi yana Fama da Ciwon kai Da Tunanin yaya Makomar Rayuwarsa,Anyi Biki lafiya Sha"ani Yayi Dadi Kowa kagani Cikin Farinciki banda Aneesa da Bello,Wanda Anty Rahila Ya Muktar ya Kira yace Ta Shiga Ta Dubashi da yammah Mallam Inuwa zai kaishi Asibiti.
Duka bakin Washegari Ranar Lahadi Kowa yayi Haraman Tafiya Kawayen su Aneesa Wasu basu kwana ba,Wadanda suka kwana kuma da Safe suka Tafi,Haka B.kaita Tabi mamanta Tun Jiya S.jibiya ne Direban gidansu yazo Ya Dauketa Suka Rabu da Aneesa da Kuka,Anty Yagana da Anty Nafee,da Sanah da Yan"uwan Babansu kuma da La"asar Aka kwashesu Zuwa Filin Jirgi inda Suka Shiga Jirgin Maiduguri,Anty Aisha kuma mijinta ya aiko aka Dauketa ta Wuce kano nan Suka bar Aneesan Falon Anty Rahila bayan Sun mata Nasihohi da kuma Lallashi Data Rumgumi Auranta,Haka Suka barta Tana ta kuka kamar Ranta Zai Fita Daada ma kasa lallashinta Tayi Saboda Tsausayinta.
Sai bayan Sallar Mangariba Bello ya Fito daga Shashensa Cikin Riga da Wando,Duk ya Rame kamar bashi ba,Mallam Inuwa ya kaishi Specialist hop,ya karbo manguguna Dama anan Suke da Fayel,daya Dawo Dakyar ya iya Shiga Masallaci yayi sallar Isha"i yana Komawa Shashen nashi ya Shiga Bedroom dinsa kenan yaji Mganar ya Muktar Da Daada bai kai ga Fitowa ba ya Muktar ya Bude Kofar Bedroom dinsa yana Shigo yana kallonsa.
Kibiya ki karanta cikin Salama.
*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_
 Â
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*
    *🅿�18*
"Kallonsa Bello yayi Lokaci Daya yana Lumshe idanuwansa,bai kariso Tsakiyar Bedroom din ba yace"Ya Jikin naka...? Cikin Sanyin Murya yace"Am better Now..."
Kada kai ya Muktar yayi kafin yace""Daz gud...Ka samemu Afalo zamu yi mgana dakai.."Kai Shima ya gyada mai baiyi mgana ba Har ya Muktar ya Fice Daga Falon da Kallo ya Bisa Lokaci Daya yana Tura Hannunsa Bisa Sumar kanshi Lokaci Daya kuma yana Sakin Ajiyar Zuciya,bai Fito ba Sai da yadan Bata Lokaci kana ya Fito Falon,nan ya Tarar da Daada Da ya Muktar suna kan Kujera mai zaman mutum Biyu Sai Anty Rahila dake kan Mai zaman Mutun Daya Aneesa ke Zaune akasa kanta Duke Cikin Farar Lifaya,Hibba na gefen Abbanta Junior ne ke kusa da Aneesa yana wasa da Gefen Mayafinta.
Cikin Sanyin Jiki ya kariso Gaban Daada ya Zauna Kusa da Kafafunta,kanshi ta Dafa Tana Fadin"Babban Megidana,Duk ka Rame.."Tafada tana kallonshi Mirmishi ya Sakarmata Kafin ya Rike Hannunta yana Fadin"Nayi kewarki Daada.."Yafada yana Sauke Kwayan idanuwansa kasa Lokaci Daya yana gaida Anty Rahila,ta amsa cikin Sakin Fuska,Da Gudu Hibba ta Dane Jikinshi Tana Fadin"Oyoyo Uncle.."Riketa yayi yana Shafa Kumatunta lokaci Daya yake Fadin"Hibbatullahi Ta zama yan mata ko.."Baki ta Washe Ita adole ance Ta zama yan mata Dukkansu Sai da Suka saka Dariya Banda Aneesa dake Hararan Bello ta Cikin mayafinta Shiko Tunda ya Shigo Falon ko kallon Barayin Datake baiyi ba Ballatana ma Har ta samu Wani kyakyawan kallo ..
Ya Muktar ne ya gyara zama yana Fadin"Bello...."Yafada Cikin Muryan ba Wasa,Dago da kansa Bello Yayi daga Wasa da Hibba yana Fadin"Na"am yaya..."Bai Tsaya Sauraransa ba yacigaba da Fadin"Nasan kasan Dalilin Zaman mu anan ko?kowa yasan yadda lamura Suka Chanza yanzu dai ka Tabbata miji ga Aneesa itama ta Tabbata matarka toh gatanan An kawo Maka ita ina Fatan Zaka Riketa bisa amana da adalci.."Yafada yana kallonsa kansa Bello ya Maida kasa yana kananan Sauke Numfashi Cikin Muryan Sanyi yace"Insha Allahu Yaya..."Mirmishi Daada Ta Saki kafin tace"naji dadi Hakan Sosai Megidana naasan bazaka bamu Kunya ba Don Allah ku Zauna Lafiya da Junanku Tasanka kaima ka santa Tunda Duk Gida Daya Kuka tashi...Allah ya baku Zaman lafiya,Ayita Hakuri Aneesa kamar kanwa Take gareka Itama tamkar wa kake gareta In kun saka Hakuri Acikin Zamanku kubama kowa mamaki in kuma kowa yaki Saukar da Halinshi kuma Kusha Wuyan Juna..."Bello kansa na kasa bai yi Mgana ba Illah Wasa da yakeyi da Hibba,nan da Daada Da Ya Muktar suka kara yi musu nasiha Sosai Aneesan ma Suka ja mata kunni Sosai Anty Rahila ma ta mata nata Nasihan Sosai kafin Su Rufe Wajen da Addu"a Sun mike zasu Tafi kenan ya Muktar yace"Ku cigaba da Maneji anan Kafin Kagama Shegen Ra"ayinka ka Fara Aiki mai kyau domin Nasan Ko Cewa nayi ka Shiga Daya Daga Cikin Gidajena na nan Abuja bazaka yarda ba.."
Bello ya Mike yana Rike da Hibba yana Fadin"Allah ba Haka bane Yaya..Na Riga Na Turama BUK C.v Dina Ta Email dinsu Har Sun Turomin da Sakon naje na karbi Appiontment letter.."Kallonsa Ya Muktar yayi kafin yace"Ok..Chan din Dai yayi maka,ga University of Lagos Tun yaushe Suke Nemanka.."Bata Fuska Bello yayi yana Fadin"Nifa Yaya bana son Zama a kudu Allah..."Jinjina kai yayi kafin yace"Ba mtsala Duk Dayane Allah yabada Sa"a.."Da Ameen Dukkansu Suka amsa kafin Su yi musu sallama su fice Daga Falon Bello na Biye Dasu Dauke da Hibba Junoir ko Da Kuka ya yarda Anty Rahila ta Daukeshi ya makalema Aneesa Wacce Ke Hawaye.
Suna Fitowa ya Muktar ya juya ya karbi Hibba yana Fadin"Ka koma Ciki...Gud Nite.."Mikamai ita Yayi Tana Dagamai Hannu Shima Dagamata yayi Har Suka Sauka Daga kan Steps din Suka Nufi Shashen ya Muktar din Suna Tafe Suna Hira ya Dade yana kallonsu Har Suka bacema ganinsa Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya koma Cikin Falon Lokaci Daya yana Kulle Kofar Dakin da Makulli kallo Daya yayima Aneesa Dake Durkushe Inda Su Anty Rahila Suka barta ya sake Hade Rai,Wucewa yayi Zuwa bedroom dinsa cikin takun Sa na isa yana Shiga ya Turo Kofar lokaci Daya kuma ya saka ma Kofar key da Harara Aneesa Ta bishi kafin Ta Dago da kanta Lokaci Daya Tana yaye,Lifayan Jikinta,Doguwar Rigar Atamfa Dake Jikinta ta Bayyana,Kan kujera ta Hau Tana Karema Falon kallo lokaci Daya Tana Tabe baki Aranta tace"Falo kamar na wata mace.."Domin Ita Tunda Take bata Taba Shigowa Shashensa sai Sau Daya Shima Anty Rahila ce ta matsa mata ta kai mishi Coffea Wai bayason su Alheri na Shiga mai Part lokacin kuma Data Shigo bata lura Da Falon ba Sosai
Saboda leke leken Aneesa Har Kichen Ta leka Tana Dube Dube Tana Tabe baki,ammh Sanda Take kar yaji motsi ya Fito Kichen Din Shima kamar na wata macen Aure,komai na Bukatar Girki akwai aciki Cikin Frigde din Kuwa Shake da Madaran Hollandian da Kayan Marmari Tabe baki tayi Tana Fadi afili.."Oh wato Shiyasa bai damu ba Cin Abinci ba,ashe ga Abunda yake sakama Cikinsa nan..."Fitowa Tayi Daga Kichen Din Cikin Takaichi,Gashi Wayarta Batasan Wanda ya karba ba Tun a borno bata kara ganinta ba,Tana so tasan Halin da Kasim yake Ciki,ammh ba Hali kan Doguwar kujera ta Haye,Tana Tura baki ita kadai Cikin Ranta Tana Fadin Andai Cuceta an Hadata da Mugun Mutum kuma wai Kowa Ahaka gani yake ta dace,Kodai Bata Dace ba.
Tun Tana Tunani da Zencen Zucci Ta gama Tunanin kasim da Halin Dayake Ciki,Har sai da Tayi kuka Daganan Batasan Sadda barci ya Kwasheta ba,Dama already Tun Adakin Daada Tayi sallar Isha"i Dinta Hade da Shafa"i da Wuturi Shiyasa Taasaki Jiki bisa Kujera tana ta Sharar barcinta hankali kwance Kamar tana Dakinta Saboda Gajiyar Baki dama gashi kwana 2 bata samun Barci ba Sosai.
Bangaren Bello Kuwa Da Gayyah ya Rufe Kofar Bedroom Dinshi Saboda Kar Aneesa Tayi karambanin Shigowamai Daki,Bedroom ya Fada yayi Wanka tare da Dauro alwala yana Fitowa ya Zura kayan Barcinsa Pjs,Riga da Wando masu Ruwan Kasa bai kwanta