Showing 69001 words to 72000 words out of 122554 words
Chapter 24 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt
Daada ita kuma taki gayamata sai cemata datayi wai Ya muktar din bai kira Waya ba,duk ta damu Ciikin Zuciyarta Zullumi ya isheta.
Ranar da zasu dawo Haka tatashi Bata jin Dadi Ciwon kai take Fama Dashi Dakyar ta iya yin Wanka ta saka wata Doguwar Riga kirar Armani,tunda Tu bayan dawowarsu ta Dauko sauran kayanta Daga Shashen Bello Tunda Sauran na kano mgani tasha ta koma ta kwanta nan da nan kuwa barci ya kwasheta mai cike da mafarkin Bello.
Karfe 3:30Pm na Narana Jirgin daya kwasosu Daga Birnin Delhi Zuwa Babban Filin Jirgin Nmandi Azikiwe Internatinal Airport, ya sauke su Tawagar ya Muktar suka zo Daukansa Daga Filin Jirgin Shi ya Gunguro Bello Daga Cikin Jirgi wanda ke kan Wheel Chair,akallon Farko bazaka taba Zaton yana da wata mtsala ba,saboda yadda yake sanye Cikim Riga da wando na Kamfanin DKNY,wandon Sky blue ne Rigar kuma mai Dogon Hannu ce Navy Blue ce,Fuskarsa ta kara Fayau ,ya kara Fari da kyau,hancinsa ya kara Fitowa Sumar kansa tafara yawa Haka ma Sajen Fuskarsa ya kara yawa Baki Silub,fatar Jikinsa ta kara kyai da Murjewa Duka Jikinsa lullube da kananun gashi kafarsa sanye da wani bakin Takalmi mai igiya Hatta Tsitsiyan hannunsa yana Sanye da bakin Agogon Fata na kamafamin Rado
Kowa yamai kallon Farko zai ji yana Son kara kallon Fuskarshi ammh Daya Kara Nazarinsa ya Fahimci yadda Wuyansa ke Zuwa gefe Lokaci Daya kuma miyan bakinsa na Zuba sai ka mai kwallah Namiji har Namiji sai dai kuma ya Nakasa,Modibbo ne ke Fama da Tissue tun acikin Jirgi yake Faman gogemai da Zarar ya Fito dashi saboda kar ya batamai gaban Riga.
***
Bata Farka ba Sai 4 da wani Abu Shima wai mafarkin Bello tayi ya Shigo Cikin Dakin Datake da kakafunsa,shi ya Farkar da ita tatashi afirgice Duk Jikinta yayi sanyi sai kuma taji Hayani a Falon Daada,Mamaki ya kamata kodai baki akayi sai ta kuma Tuna Dazu taga ana ta gyara bangaren baki,bata kawo komai acikin Ranta ba sai tayi Tunanin Dangin su na Adamawa ne domin Taji Daada na Tadinsu kwana nan..
Cikin kasala ta mike ta Fada Toilet ta Dauro alwala tazo tayi sallar azahar ta hada da la"asar ta dade tana addu"an Allah yabama Uncle Bello lafiya kafin ta mike Lokaci Daya tana kwabe Hijabin Data gama sallah Dashi,gaban madubi ta isa tana kallon kanta,tana Daura bakin Dankwalin Doguwar Rigarta Kai Tsaye ta Bude kofa ta Fito Falon na Daada saboda cikinta ba komai yunwa takeji.
Turus tayi ganin Mutane Cike da Afalon idanuwanta suna ta Wulgawa,Ya muktar,Ya Ali,Anty Rahila Dasu Hibba sai Modibbo da Daada gefenta kuma Bello ne kan Wheelchair dinsa,idanuwansu suka sarke cikin na Juna Lokaci Daya ya Saki Boyayyiyar Ajjiyar Zuciya dama Ita yakeson gani Tun bayan Dawowarsu ammh kuma baisan ya zai yi yayi mgana ba,ganinta Dayayi yasa yaji Dadi ya kafeta da ido yana Budewa yana Rufewa alamun Murna,gefen bakinsa kuma na Zubar da miyau.
Kasa gaba tayi ta kuma ta kasa Baya Ya Ali ne yace"yau ga iskancin banza irin na Aneesa mijinki ya Dawo ba lafiya ba sannu ba komai sai kallon Mutane ."Daada tace"Mamaki take Ali Bata san da Lbrin da Dawowarku ba.."Tafada Tana kallon Aneesa wacce ke kallon Bello Lokaci Daya tana Toshe bakinta kar kuka ya kwace mata Juyawa Tayi ta koma Dakinta ta Fada Bisa gado tana Fadin"Bai Warke ba..mafarkina ba gaskiya bane.."Take fada tana kara saka kuka.
Har ta Shige idanuwansa na kanta Kuri yayi gwanin ban Tsausayi ya Ali yabi Aneesa da kallo har ta shige yana Fadin"Tsiyana da Aneesa fa wani Lokacin Sakara ce,toh miye Abun kuka keda kullum ke kukan kina so ki koma ki ganshi yau kuma ya Dawo kuma kina wani Sakarci.."Anty Rahila ta Murmusa tana kallon Bello yadda ya wani bata rai Lokaci Daya take Fadin"Har ka manta Auta ne fa.."Tafada Cike da Tsausauyin Bellon,Daada ta lura da yadda ya tsurama wajen ido sai ta kama hannayensa duka biyun tana Fadin"Karka damu zata Fito haka take kuka kullum saboda Tsausayin halin da ta barka koni da Dan"uwanka Aneesa bata kaimu Damuwa ba...Ka Riketa ko bayan Raina Bello in ka Warke ka sota kuma ka Hidinta mata Ita din mace tagari ne awajenka"Tafada tana kallonsa Hawaye na taruwa acikin idanuwanta Shima kallonta yake Lokaci daya kuma ya Lumshe idanuwansa.
Ko abinci da ya Muktar ke bashi abaki Bai wani da ci da yawa ba,Duk da dama Rabi ya Shiga ne rabi ya Fito Daga bakin,Duka Rabin Hankalinshi naga kofar Bedroom din Aneesa Data Shiga Tundazu Bata Fito ba,Modibbo ne ya gogemai jiki,inda ya babbata da Abinci,lokacin mangariba ta kawo Jiki da zasu Tafi maallaci dashi suka Tafi saboda ko achan bayan an Faramai gashin kashi Da Lokacin sallah yayi modibbi zai mai alwala ya saitashi agabas ya barshi bayan ya gamai yayi sallah yanzu ma Haka suka mai Ya Ali yamai alwala suka Turashi Zuwa Cikin masallacin cikin Sahu aka yi jamm"i Dashi Sukansu ma"aikatan gidan sun zubar ma da Bello kwallah hatta Sojijin dake Tsaran lafiyan gida na Lt.gen Muktar muhammed Jikamshi.
Haka kuma suka Turoshi Zuwa Cikin gida har Shashen Daada,inda Suka bar Ya Muktar da Ya Ali Shashen Anty Rahila suna mgana,Modibbo ne ya kariso Dashi Daada kuma na ciki na Sallah,yana ijiyesa Cikin Falon yadinga kallon Kofar Bedroom din Aneesa Kansa na lamgwabewa ammh bai gaji ba,Modibbo bai kula dashi ba sai da Daada ta Fito daga daki Hannunta rike da Chasbaha ta kariso Falon ta Zauna kujeran dake Fuskantan Bellon tana Fadin"har kun dawo sallar..?
Modibbo dake latsa waya yace"Eh Daada.."Bello ta Kurama ido ammh sam shi baya kallonta Juyawa tayi ganin inda yake kallo yasa tace"Gunta zaka..? Da Sauri ya lumshe ido yana Kallonta Mirmishi tayi kafin tace"Allah Sarkin Baiwa...Modibbo kaisa Dakin Aneesa Wajen matarsa yakeson zama.."Tafada Cikin Tsausayin Bellon Dariya Modibbo yayi yana Fadin"Kinga laifinsa Hajiya Daada lallashi zaka ko Baffa Bello.."(Haka suke kiranshi saboda Bello baban Hassatu Baffansu ne..)
Yafada yana Dariya,Daada ma Murmusawan Tayi tana cigaba da Jan carbi shikuma ya Turasa Zuwa Dakin Aneesa Tura Kofar Modibbo yayi da sallama yana Fadin"Toh kefa matar baffa mijinki yagaji da jiran Fitowarki ya biyo ki.."Yafada yana Shigowa dashi Dakin.
Tana Zaune kan sallaya tana Addu"a suka Shigo Da Sauri ta waigo Jin Abunda Modibbo yace Saurin mikewa tayi tana kallonsu Shiko Bello ido ya kafeta Dashi yana so ya Tambayeta meyasa take kuka..?ammh kuma ya kasa Mgana balle ya tambayeta Yana kallon Cikin idanuwanta wani Abu na Shiga Zuciyarsa Tun Ranar da Abun nan ya Sameshi Kukan Aneesa ya tsayamai arai Bai taba Tunanin zata iya damuwa dashi bayan shi kuma bai damu da Ita,bashi da bakin mgana sai dai yayi ta mgana da Zuciyarsa.
Mirmishin yake tayi kafin tace"La...dama yanzu nake shirin Fitowa.."Dariya yayi yana Fadin"Kedai kyaji dashi jan aji ne kawai a sassautama Baffalenmu kinganshi dai ba lafiya ne dashi ba"Yafada yana Ficewa.
Ki biya ki karanta cikin salama.
*Shakira..*
8/19/20, 11:17 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_
 Â
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*
    *🅿�24*
Fitar Modibbo yasa tayi Saurin Sadda kanta kasa Tana wasa da gefen Dankwalin kanta Shiko Kura mata ido yayi bai ko Kiftawa Domin yanzu idanuwansa Sune gabadaya Jin kanshi.
Jin kamar yana kallonta yasa Ta Dago kanta karaf suka Hada ido kansa ya karkace gafe ammh kuma bai daina kallonta bq Tsausayi ya bata ta Zauna gefen gado tana fadin."Kun Dawo lafiya...?
Tafada kai tsaye tana kallonsa bai mata wani alamu ba illah Taga ya maida idanuwansa kasa,Shuru kawai tayi tana binsa da kallon Tsausayi kwallah na Taruwa acikin idanuwanta,Lokaci bayan lokaci sai ya dago ya kalleta kuma ya maida idanuwansa kasa,kusa dashi ta kariso tana Fadin"Kana son wani abune..?ko yunwa kake ji..?
Lumshe mata ido yayi ya Bude alamar A"a,ajiyar Zuciya ta sauke tana kallonsa Araunane tana Durkushe agabansa,Miyan Dake Zubane Duk ya bata gaban Rigansa bata san sadda ta saka gefen Dankwalin abayarta ba ta Shiga goge mai ammh bata yarda ta kalli Fuskarsa ba,Kuramata ido yayi Cikin Zuciyarsa yana jin Wani game da ita wanda ya kasa ganewa sai da ta gama ta koma ta Zauna agabanshi bata bari sun Hada ido ba Shiko ya kafe ta da ido kamar ita kadai yake iya gani yaji Dadi.
Sun Jima Zaune Shuru batacemai komai,Cikinta ne keta Faman Kugi Saboda yunwa yasa ta mike Zata Fita saboda kallonta yana so ya juya kansa ya kasa kadan ya Rage bai Fado bisa Wheelchair dinsa ba,Da hanzari ta dawo garesa Batasan sadda ta Riko Duka hannuwansa ba Tana Fadin"Ina zaka..? Zaka koma wajen Daada ne..?bai lumshe mata ido ba illah Kada idanuwansa kadai da yayi alamun A"a,Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin ta sakeshi ta kama hanyar Fita Harta bude kofar ta Sake Juyowa tana kallonsa ganin yana so ya waigo ne ya Kalleta ammh kuma ya kasa.
Mirmishi Tayi kafin ta girgiza kai Tana Fadin"Yanzu zan dawo abinci zan sako ina jin yunwa.."Sai Lokacin ya Sauke Numfashi Ficewa tayi ta barshi Zuwa Shashen Anty Rahila babu kowa Kamar sun Tafi sallah ne,Kichen ta Shiga Alheri kadai ta Iske ta gaisheta ta amsa,da kanta ta Dauki Filet ta Zuba Sakwaran da Akayi Miyar Agushi,Kadan ta zuba domin Aneesa bata wani cin Abinci Fridge ta bude ta Dauki Ruwa mai Sanyi,Har ta Fita ta Dawo ta ce Alheri ta yanka mata Fruit nan da nan ko ta Dauko Wani Babban Faranti ta yayyanka mata aciki ta ce ta biyota dashi har Zuwa Cikin Dakinta,cikin ladabi Alheri ta ijiye tana gaida Bello da kacokan Hankalinsa ke kan Aneesa.
Gabanshi ta Zauna ta Fara cin Abincin Dagowa goma sai sun hada ido mirmishi tayi ta Nuna mai Cokali take Fadin"Zaka ci..?Ido ya Lumshe mata ya Bude Gyada kai tayi batace komai ba sai da Taci kusan Rabi tasha Ruwa,ta jawo Filet din Fruit din ta Fara ci nan ma ya saka mata ido Karamar Wukar ta soka cikin yankakkiyar kankanar ta mikamai sai kawai Taga ya Bude baki Cike da mamaki ta mike ta isa gabanshi ta saka mai abaki ya karba Dariya ta saki kafin tace"Oh hakane fa na manta kai dama abinci bai dameka ba Masoyin kayan lambu ne.."Tafada tana Dauko Farantin kayan marmarin Gefen gado ta Zauna yarda zatayi Tsawo dai dai da kansa ta Dinga basa abaki yana karba,lokaci Daya yana kallon kwayan idanuwanta,Ita kuma kallon Dayake mata yana kashe mata Jiki sai ta dinga kauda kai,kusan shi ya cinye ita ko Tunda ya Nuna yana so ta hakura ta barmai Yana so yace itama taci ammh babu baki,sai da ya koshi zata karamai kawai ya Langwabe kai Sauran na bakin nashi na Fitowa Waje,Mirmishi tayi kafin tace"Ka koshi ne..?ido ya kada mata mikewa tayi ta Dauki Filet din Data ci abinci da na Fruit din ta Fita chan sai gata ta Dawo da Tissue ahannunta ta gogemai baki tas,dagaban Rigansa kallonsa tayi tana Fadin"Zanyi sallar Isha'i kaima bakayi ba ko..?bai kauda idanuwansa ba Yadai Rage musu Girma yana kallonta bata kara mgana ba takoma ta bayansa ta Shiga Turasa Zuwa Cikin Tiolet dinta,Tattare Hannayen Riganta Tayi Tafaramai alwala ko kafin ta gama Tajika kanta Shima Duk ta Jikamai kayan Jiki,Kallonsa Tayi tana marairaicewa tace"Kayi Hakuri Na jika maka kayan Jiki Ban iya ba ko .?
Yana so yayi mirmishi ammh kuma ya kasa sake lamgwabe kai yayi
Yana kallonta Mirmishi tayi tana Fadin"Yauwa baka ji haushi bako..? Karka damu da haka zan koya Na dinga maka Tunda Modibbo Watarana Tafiya zaiyi,In mun koma gidanmu na kano Har wanka zan dinga maka kana so..? Tafada tana kallonsa kara girman idanuwansa yayi alamar mamaki ganin Haka yasa ta Rufe Fuska Tana Dariya Lokaci Daya take Fadin"Bazan kalle ka ba,Rufe idona zan dinga yi.."Lumshe idanuwansa yayi ya Bude yana kallonta bata kara mgana ba itama alwala ta Dauro ta Turoshi Suka Fito Daga Tiolet din,Gabas ta karkatasa Itama ta Zura Hijabinta Suna Sahu Daya Takallesa tace"Muyi sallah kaji..? Ido ya kada mata Kafin ta Tada sallah shima sallar ya Fara har ta Idar tagama Addu"o'inta,ta juyo tana kallonsa tace"Ka idar kaima...?
Lumshe ido yayi ya Bude Gabansa ta koma ta tankwashe kafa tayi Tagumi kawai tana kallonsa Shima ita yake kallo,idanuwanta Suka kawo kwallah Tayi Saurin maidasu Tana Fadin"Kowa na gaisheka yan gidanmu na Borno gabadaya,Mama yana,mama Falmata mamata kenan.."Tafada tana kallonsa kafin ta ci gaba da cewa"Su B.kaita ma sunce na gaida ka zasu kara zuwa Su dubaka ka ganesu kuwa..? Kawayena Bilkisu kaita da Salamatu s Jibiya.."Tafada tana kallonsa Rage girman idanuwan yayi Tayi mirmishi tace"Allah Sarki Sai da kayi mgana da ido.."Tafada hawaye na gangaro mata,Bata rai yayi yana kallonta Wuyansa na karyewa gefe Tana Share kwallah ta Tura mai baki tana Fadin"Miye kuma kake bata Rai..?
Idanuwansa ya Kara ma girma yana kallonta Hawayenta ta Dankwalo tana Fadin"Wannan..?ido ya lumshe mata mirmishi tayi tana Fadin"Na goge ka gani..? Sai lokacin ya saki Ransa Haka ta tasashi gaba tana mai lbrai kan kukan Datasha bayan ta Dawo Gida ta barshi achan,wani Lokacin sai ta gaji da mgana ta Tura baki tana Fadin"Sai mgana nake ni kadai ko kanuna ma kana jin dadin lbrin.."Sai ya lamgwabe mata kai sai tayi Dariya tana fadin"Karka min kuka mu cigaba.."Sun Dauki Tsawon Lokaci tana mai Hira har Su ya muktar suka Shigo dakin bamu sani ba Sun Dade suna kallonmu cike da Tsausayi Modibbo ne yayi gyaran Murya nayi Saurin Dago kai ina kallonsu Daada tamin mirmishi tana Fadin"Matarsa ta Rike sa da Hira.."Dariya nayi ina Sadda kai ganin ya Ali Awajan
Ya muktar yayi mirmirshi yana Fadin"Dare yayi gobe da safe sa karisa modibbi kama sa ku Tafi ku kwanta.."Daada tace"ammh badai ba Shashensa ba ko..? Yace nan mana Daada na saka Mallam inuwa ya Bude barayin Tun dazu ya gyara.
Girgiza kai Daada tayi tana Fadin"A"a zaka wahalar da mai Wahala dashi shi kanshi Bello zai Wahala bene ne fa hawa da Sauka ka barsu su zauna Shashen baki.."Ya Ali yace"Hakane Saboda kada ajikkata Shi Bellon mara lafiya.."Jinjina kai ya Muktar yayi yana Fadin"Shikenan Modibbo kama sa kuje ku kwanta."Cike da ladabi ya isa Bayan Bello ya Fara Karkato Dashi shiko Rai yabata yayi Kicin kicin da Fuska kamar zaiyi kuka yana kallon Aneesa ya muktar ne ya lura dashi Cikin mamaki yace"Bello kwanciya zai kai ka kayi ka Huta sai gobe ko..? Kallonsa yayi sai kuma ya karkata kai yana kallon Aneesa Wacce ta Ware mai ido tana Fadin"awajena zaka kwana.? Da Sauri ya lumshe ido yana kallonta Gabadayansu suka Tsaya Suna kallonsa,Daada tace"Ikon Allah toh kaji wajen matarsa zai kwana"
Ya muktar yace"A"a Daada Modibbo ya Tafi dashi yaushe Aneesa zata iya da Dawainiyarsa."Da Sauri Aneesa tace"Allah zan iya ya muktar.."Tafada kamar zatayi kuka ya muktar zai yi mgana Ya Ali yace"Ka kyaleshi mana Muktar,ko bata iya ba ya kamata takoya,ai modibbon zai koma Shima bakin Sana'arsa ko..? Dole dai itace zata Dinga kula Dashi.".
Ya muktar yayi jim kafin yace"Hakane..Ammh bazata iya Dawainiyar Dagashi Daga kan keken nan ba.."Da sauri Aneesa tace"In ba zan iya ba Zan kira Daada ta kamamin ko Daadata..? Kai Daada ta gyda mata kwalla na Taruwa acikin idanuwanta ganin Ya Muktar yayi Shuru ne yasa Aneesa Tace"Don Allah Ya Muktar kabar shi ya kwana anan kaga fa yadda yayi zai yi kuka.."Tafada Lokaci Daya hawaye na Wankemata Fuska kallonta yayi yana Tunanin Wani Abu Cikin Ransa Ajiyar Zuciya yayi kafin yace"Shikenan...'Daga haka ya juya zai Fita yana Dauke kwallar idanuwansa,.
Sai da ya Rike handle din kofar kana ya waigo yana Fadin"Modibo ku Tafi Da Ya Ali Chan Shashen ku kwanta sai da Safenku.."Daada tace Allah tashe mu lafiya,Ransa ya saki ganin baza"a tafi dashi ba Karamar Jakar kayansa Modibbo ya Dauko ya kawo ma Aneesa Shi da ya Ali Suka kama shi Suka Sauko Dashi Daga kan keken Nashi Zuwa kan gado,Modibbo ya ciremai Riga da Wandon Jikinsa ya sakamai Wata Doguwar Jallabiya saboda yaji Dadin barci bayan ya gama ya kalli Aneesa yana Fadin"Da Asuba zan zo na masa wanka..."
Kai ta girgiza tana Fadin"Basai kazo ba zan masa Da kaina.."Kai tsaye yace"Kin iya ne..?baffale na Nada Nauyi fa bazaki iya Daga sa ba.."Yafada yana mata Wasa ganin Ya Ali ya Fita ne yasa Tace"Toh shikenan na yarda gobe da Safe kazo ka gwadamin yadda Ake mai wanka Daga gobe Ni zan Dinga karban ladan wanda ka samu ya isa Hakanan ko Daada.."Tafada tana Tura baki Dariya Modibbo yayi yana Fadin"Ah maida Wukar zan koya miki komai Matar Baffale kema ki samu ladan Jinyar Mijinki.."Yafada Yana Dariya Daada na Tayashi Haka Suka Fita suna Musu Sai da Safe binsu Tayi ta kulle Kofar ta Dawo ta kwabe Hijabinta Duk yana Binta da kallo,wardrope dinta Ta Bude ta Dauko Doguwar Rigar barcinta tana Juyowa suka Hada ido kunya Taji yasa ta Dauki Hijabinta ta Shige Tiolet ta saka Rigan barci da Hijabin ta Fito,
Keken da Matsar gefe tana Fadin"Kana jin barci..? Ya kada mata ido Tashi tayi tana Fadin"Toh muyi karatu kafin mu kwanta gobe da Safe kuma ma cigaba da lbrinmu ko..?Ido ya Lumshe mata Mirmishi tayi tana kallonsa Har ta Dauko karamin Qur"aninta Gadon Ta Hawo gefensa ta Zauna ta Bude Tana Fadin"Bismillah mufara ka dinga yin naka acikin Zuciyarka kaji ko.? Ido ya kada mata taciga ba da Fadin"Kullum mukayi Waya da Mamata tana Fadamin cewa na Laminzi karanta Qur'ni koda yaushe,Shi alQur"ani mganin kowani Waraka ne"
Kallonta kadai yakeyi kansa yayi gefe Bisa Filon Ta Bude Suratul Maryam Tana Fadin"Suratul Maryam zamu karanta.."Daga Haka tayi Bismillah ta Fara karatun cikin Siririyar Muryanta mai cike da gardi Cikin Zuciyarta tana kara godema Bello Domin Shi ya Jajirce Har ta samu wannan Ilimin,Kullum Suna karatun islamiya lokacin Suna Mkranta sai da tayi Haddan Talatin,kafin su gama Tana ta karatu Shima cikin Zuciyarsa yake binta Cike da Farinciki Saboda gajiyarvtafiya yasa Lokaci kadan barci ya kwasheshi bata sani ba sai Zuwa chan ta Juyo ta ganshi ya Bingire kai yana Sauke Numfashi Miyau ya bata Gefen bakinsa Mirmishi ta saki kafin ta Saka Gefen Hijabinta ta Share mai Miyan daya Zuba Saukowa Tayi Daga kan gadon Ta maida Qur"anin bisa Side Drower din gadon,Sake