Showing 57001 words to 60000 words out of 122554 words
Chapter 20 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt
saka Tsoffin ta na gida Tun da baya barinta Shiga Dakin Dalilin Mganar da Daada Tayimai ne ya Daina Rufe Bedroom din nasa,Da Asuba in ya Fita Sallah Ta lallaba ta Shiga tayi Wanka ta Chanza kaya,ta Fito ta koma Falo kamar Wata Munafuka,Ranar Data Fara Shiga Saboda Shegen Gulman Aneesan Har ya Dawo Masallaci batagama Abunda Zatayi ba inda bata leka ba Saboda Gulma,yana Shigowa ya ganta gaban Dressing Mirror dinshi tana Fadi Cikin Ranta Ji kayan kwalliya kamar Wata macen,batama san ya Shigo ba,shi kuma yana ganin ta Daure da Towel ya koma Da baya yana Tsaki Falo ya koma ya Zauna yana latsa waya sai da Aneesa Tagama Kallen kallenta kana Ta Shirya ta Fito sai taci karo Dashi Dauke kai Tayi tana Tura baki cikin Ranta tana Fadin"Andai Cuceni Wlh...Saboda mugun Hali Tiolet ma in mutun zai Shiga sai yana Sata.."Yana kallonta ta gefen Ido bai tankamata ba Saboda sanin Bata ma kansa Rai kawai zaiyi,Kwata kwata Yanayin Rayuwarsu bai zo Daya ba gashi An Riga An Daureshi da Jijiyoyin Jikinsa,Ya muktar,Daada,uwa uba kuma Anty Rahila yana ganin Girmanta ga su Ya Ali Wanda bazai iya Cin Zarafin Aneesa ba ya gama duk iya hangensa bai gano ma kansa mafita ba
Haka Ranar Cikin Dare Cikin Aneesa ya baci taji Zawo Ta rasa ya Zatayi ganin Wankin Hula Zai kaita ga Dare yasa Ta isa bakin Kofar Bedroom din Bello tana Bugamai Cikin Barci yaji Muryanta Harda kuka Take Hadawa Wajen Rokansa ya Bude Domin Har tafara Zawon Awando,Saurin Saukowa Yayi Daga kan gado ya Bude Duk atunaninshi Wani abu ne ya sameta ko gama Bude kofar bedroom din baiyi ba ta Tureshi da Karfi ta Shige Ciki Cike da mamaki ya juya yana kallonta ta Fada Tiolet Aguje Saboda Sauri ko Rufe Kofar tiolet din batayi ba yana Tsaye yake Jin karan Zawon nata irin mai Fata Fata din nan ne,Yamutsa Fuska yayi Lokaci Daya yana Toshe hanci Saboda Warin Dayake Fitowa Daga Tiolet din Zuwa Cikin Dakin,ganin zai halaka da Wari ne yasa ya Fice Daga Dakin haryana ja mata kofa Bakinciki kamar ya kasheshi karshenta dai Ranar kan kujeran da Aneesa ke kwana ya karishe Daren Farkawa kawai yayi da Asuba ya ganshi kwance ya Dunkule Cikin Hijabin Sallarta Cikin Takaichi ya mike saboda kyamkyamiv ko Bedroom din Bai Leka ba ya Fice a masallaci yayi alwala Abunda bai tabayi ba Sallar Asuba batare Da yayi Wanka ba.
Ita ko Aneesa bata Dawo Hayyacinta ba sai da tagama barin Wuta,tayi floshing kana ta Tube kaya tayi Wanka Tana ajiyar Zuciya afili ko Fadi take kai kashi Rahma ne babu Abunda yafi kahi Daraja Wlh..,bata Fito ba sai da Ta Fesa Airfresher jin Bayin ya Chanza ganin bata ganshi adakin ba yasa ta kyakyale da Dariya tana Tuna Sanda ta Tureshi ta Shige Bayi,Kaya ta Sauya kafin ta Leko Falon ta ganshi Zaune kan kujera yana Hamma,Baya ta koma Harda sakama Kofar key Tana Dariyan Mugunta,cikin Ranta tana Fadin"Mugu yau kaima ka Dandana kwanan Falo,Ta ko Haye gado Harda Shigewa Cikin Bargonsa Tana Shakam kashim Turaransa Tana lumshe ido Cikin Lokaci kankani barci ya kwasheta bata Farka ba sai da Taji Yana Dukan Kofar tashi Tayi Tana mika Lokaci Daya take Fadin"Waye ne...?
"Tafada tana Kunshe Dariyanta Ransa bace yace"U better open d door Bf4 i loss my Temper..",Yafada Cikin Sanyi ammh Cike da Fada,Dariyarta ta saki yana jinta Tadaka tsalle akan gadon tana Dariya Sai da ta saka hijabi kana Ta Bude Kofar,ta Rabe a bayan Kofa,Shiga dakin yayi yana Hararanta Lokaci Daya yana Kara Toshe bakinshi Cikin Tsawa yace"Ke wata irin kazama ce zaki gama Amfani da Tiolet baki Wanke ba..? Yafada yana kara Rufe Hanci Abun ma Dariya ya bata ta kama baki tana Fadin"Ikon Allah kashin nan fa kowa nayi.."Hannu ya saka ya make mata baki yana Fadin"Sa'an wasanki ne ni...? Yafada yana Nuna ta da Tsaya baki ta Tura tana Sosa lebenta har ya Tashi,Hanyar Tiolet ya Nuna mata yana Fadin"Wuce maza ki Shiga ki wanke min Tiolet Tas,Zan Shiga nayi wanka kuma In kin isa karki Wanke Dakyau kiga yadda zan Dake.."Yafada yana Direct dinta da Hannu Wucewa Tayi Tana Kunkuni Tsawa ya Dakamata yana Fadin"Wai ina wasa Dake ne...?kinsan Allah zan Zaneki fa.."Yafada Lokaci yana yunkurowa ai da gudu ta Fada Tiolet din tana Hawaye Cikin Ranta tana Fadin mugu kawai,Haka ta Cire Hijabi ta Zage Ta wanke bayinan tas,ya koma yana kamshi kana ta Fito tana Haki Duk ta Jika kayanta Da Harara yabita kafin yace"Now get Out..Next time in kinji kazanta go to Anoder room don"t came back Here again...".
Tabe baki tayi ta Dauki Kayanta Dake saman Akwati Wanda ta Fito Dashi ta Fice Zuwa Shashen Daada Cikin Ranta kuma Dariyan Bello Take in ta Tuna yadda yake Toshe hanci afili tace"Ji yadda yakeyi sai kace shima baya kashin Waya sani ma ko Shima Zawon yake kamar nawa.."Tafada Tana Dariya Haka Dataje Shashen Daada tana mata Fada ammh Tana Dariya ta bata lbrin Abunda ya Faru Hartana kwatanta Yadda Bello ke rufe Hanci Ita kanda Daadan Sai da ta Dara Tana Girgiza kai Cikin Ranta tana Addu"ar Allah ya Shiryi Aneesa.
wai kuma duk wadanan Abubuwa kuma ace Dole sai ya Tafi da ita yana nan Zaune sai gashi Ta Fito Sanye da Hijabi Tana Dauke da junoir Hannunta kuma na Rike da Hibba Suka sauko Zuwa Shashen su ya muktar yana kallonsu har Suka Shige baisani ba ko ta ganshi itako batama lura dashi ba tana Shiga ta Hadu da alheri sai ta mika mata su ta juya ta koma Ta Fara Taka steps kenan taji taku mutum Abayanta ko Waigowa batayi ba Tadaga Hijabi da kafa ta Rumtuma da Gudu ta Shige Dakin Tana Dafe Kirji Tsaki yaja a Cikin Ranshi yana jin Takaichi kamar me,ko zama bata samu yi ba ya Shigo Falon bai kalleta ba illah Wucewa Dayayi gaban Tibi ya Dauki Remot ya Rage karan Cartoon din da ta kunna ma su Hibba,Takowa yayi Zuwa Tsakiyr Falon Lokaci Daya kuma ya juya Zuwa Bedroom dinshi.
Karamin Tsaki Aneesa ta Sauke kafin Ta kwanta Harda Juyamai baya bai damu ba Tunda ya Sake Juyowa ya kalleta ya Dauke kai yana Fadin"Ke ki shirya gobe da Safe zamu tafi kano.."Yi tayi kamar bataji ba Ackin Ranta tace"Kaga ke mallam."Ganin Yadda Tamai ne yasa ya Hadiyeshi Fushinsa yana Fadin"Ke wai badake nake mgana ba..ke Aneesa.."Sai Lokaci ta juyo tana Wani Tura Kirji Sauri kauda kai yayi yana Kara girman idanuwanshi yana Fadin"Kina jin Abunda nace..?..
Baki ta Motsa kafin tace"Hum..Me kace..? Wani Haushi ne ya kamashi Cikin Fushi ya Nufota yana Fadin"Ok bakiji ba ko..?bari nazo na Kara gayamiki ."jin Haka kuma ganinshi ya Nufota yasa ta Zabura ta Mike tana Fadin"A"ah Wlh naji naji..Ba cewa kayi gobe na Shirya zamu kano ba..? Tafada Tana Takurewa Jikin Kujera Fuska ya hade kafin yace"Gud...karki batamin Lokaci in ba Haka sai dai ki sameni achan..."yafada yana Shigewa Cikin Bedroom Dinsa da harara Ta bishi kafin tace"Baza"a je din ba.."Sai kuma tayi Sauri Ta Damke bakinta tana kallon Bedroom Dinsa da kallo Sanin yadda Kunnansa yake kamar na Maciji saboda ji.
****
Washegari Tun karfe 7:30am Bello ya gama Duka Shirya Shiryansa Abun da yabama Aneesa mamaki ganin Uban kayan da zai Tafi Dashi Jakunkuna Uku,mallam.Inuwa yazo Har Falon ya Dauka ya Saukan mai Dashi Zuwa Cikin Motarsa,kirar 4matic baka,kuma komai na amfaninshi ya Diba,ita azaton zasu gidan Anty Aisha ne,sai da ya barmata bedroom din tayi Wanka Ta Shirya Cikin Riga da Zani na Wani leshi mai kyau kalan milk da ja,ta sanya Jan mayafi da jan Takalmi kuma Duk Cikin kayan Auren da Kasim ya bata ne,Sai da ta Shiga Sashen Su Daada gaishesu ne Taji Daada na Zolayanta zasu barsu da kewa,Sai lokacin ta gane Tafiyan ba na Dawowa bane,Nan da nan Hankalinta ya Tashi Cikin Son tayi kuka tace"Daada chan zamu koma da Zama..?kai Daada ta Dagamata kafin tace"Chan mijinki ya samu aiki.."Bata rai Aneesa tayi Daganan kuma sai kuka Daada na lallashinta Anty Rahila dai bata mata mgana ba ganin iskancin na Aneesa nada yawa sai da Suka zo Tafiya ta gane kukan sabo ne itama sai da ta Share kwallah hibba ko da Junoir Haka Suke kuka Aneesa nayi Shikanshi ya Muktar ya sani Yasani zasu ji kewan Aneesa Hatta su Mallam Inuwa Sunji ba Dadi da Tafiyar Aneesa,Alheri da Jummai suma Harda kwallansu Aneesa dai Haka Suka Fice Daga Haraban Gidan Tana gaban Mota Tana Kukan Rabuwa dasu Daada,gashi Bello ya hanata Daukan kayanta Duka Akwatuna uku Ta Dauka yace takoma ta mayar dasu ta Dauko Daya Hala chan zata tare,waye zai Dinga mata Jigilan Zuwa da kaya yana maidamata,tana kuka tana komai haka ta maida akwati biyu Acikin yar Babban ta saka Duk Abun Amfaninta,bawai don zasu Isheta ba,sai don muguntar Bello Cikin Ranta ko Allah ya isa takemai domin ai Shi ya Diba kayansa Duka sai itane zai Hanata batasan ko Kwatan kayansa bai Diba ba,Wardrope dinsa maa baisan an Dibi kaya ba Saboda Tsabar yawansu.
Ki biya ki karanta cikin salama
*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_
Â
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*
     *🅿�20*
Sun Fara nisa kukan Aneesa,yafara isar sa Dole ya gangara gefen titi ya faka motar Cikin Tsawa yafara mgana"ke kukan me kike ma Mutane...? Ko dai salon iskanci kine ya tashi..?ko kuma salon mutane suganki kina kuka Suyi Tunanin Sato ki Nayi..?
Ko kallonsa Aneesa batayi ba,illah Cusa kanta Datayi Cikin Cinyoyinta tana Cigaba da Shesshekan kuka Tsaki yaja kafin yatada Motar yana Fadin"U better keep u mouth Shout in ba Haka ba wlh kinfi kowa sanina Sai na Watsaki Cikin Dajin nan na barki na kama gabana.."Jin Haka yasa Aneesa Tayi Dif sai dai na Zuciya sanin Halin Bello Tsaf zai Iya aikata Abunda yace don ba Mutumci ya cika ba...
Wajen 10am na Safe suka isa Gidan nasu dake Buk road,Megadin gidan Wani Bafullatani ne,mai kirki sai faman musu barka da Zuwa yake yi,Fitowa Aneesa Tayi Daga motar Tana karema Haraban gidan kallo Bello ko takanta bai bi ba ya Bude Booth ya kwashi jakunkunarsa ya bude Kofar Falon gidan ya Shige ya barta,don mugunta yasan fa bazata iya Daukan Akwatinta ba Ganin Tana jansa ne yasa Salihu maigadi wanda ya Fadamata Sunanshi bayan sun gaisa ya Dauka ya kai mata Falon Farko.
Aneesa Tsayawa tayi afalon Tana ta uban kalle kalle,Falon Farko Shi keda 1 bedroom da Kichen Guda Daya Shima duka ko"ina yaji kayan alfarma na Morewan Rayuwa,Wani korido tabi tana jan Akwatinsa sai gata ta bayyana awani katon Falo mai kyau da Tsari Wanda yaji Ubansu Rolay Chairs,Daga ganin Falon Zaka san Ankashe kudi,Kuma yafi na Farkon Girma,shi yana da wajen Dinning da Kichen mai girma sai Kofofin 2 bedroom Kusa da Juna,Tana Tsaye tana Faman Wurga ido Bello ya Fito Daga Daya Bedroom din yana Waya ya Fice ko kallonta baiyi ba,ganin haka yasa taja kafa Zuwa Dayan Bedroom din Shima ya Hadu karshe makeken Royal bed da Madubinsa,sai Wardrope babba da Tiolet,bata zauna ba ganin kura Adakin sai Ta Hau gyara wajen itace Har Falon da Kichen sai da ta Share tayi mooping Dayake ta samu Abun Shara agidan,Sake komawa Tayi Falon Farko ta gyarashi Shima Da Bedroom din Acikin Ranta tana Tunanin kila anyi Wajen don Baki ne.
Sai Wajen Azahar ta gama Tagaji Tubus Wanka ta Fada Tare da Dauro Alwala,cikinta Kugin Yunwa yake yi Domin bata karyaba rabonta da Abinci Tun Jiya Da Daddre,gashi kuma Tunda Bello ya fice bata karajin Motsinshi ba ta fito Falo ta leka ta taga ba taga Motarsa ba, kenan yayi Nisa ya manta da ita,gabas ta Saisaita ta Tada sallah ko kayanta Data so ta jera cikin Wardrope kasawa Tayi Saboda ta gaji Tana sanye da Wata Bakar Doguwar Riga tabi lafiyan gado Duk da yunwa dake damunta haka barci ya Kwasheta..
Bata Farka ba sai bayan La"asar ta Tatashi ta Dauro alwala tayi sallar la"asar,Yunwa yafara illatata Domin Jiri take gani in ta mike,kichen ta Shiga tana Bude bude ammh babu komai na girki sai kayan Tukwane dasu gas,har Fridge ta bude bakomai,fridge din ma Daga gani Babu Abunda Aka Taba sakamai Falo ta Dawo Tana Rangaji ta Zube bisa kujera tana maida Numfashi harda kwallanta,Shuru Shuru ba Bello sai Bayan sallar mangariba kana ya Shigo gidan Hannunsa da Lodoji guda Hudu manya,Lokacin Tana kwance nan kan kujera Saboda yunwa ma ta kasa Tashi tayi sallar Mangariba.
Yana Shigowa kallo Daya yayi mata ya kauda kai Cikin kichen din ya Shiga ya ijiyemata Duka Ledojin kana ya Fito Hannunsa Rike da goran Ruwa yana Fadin"Ga Abinci chan a kichen da Wasu kayan Cefenan,ban samu Lokacin Shiga kasuwa ba gobe in na Fita za"a saka komai Cikin Store.."Jin yace ga abinci can yasa wani karfi yazoma Aneesa ta mike da Hanzari Tana ganin Jiri kamar zata Fadi sai da Ta Rike bango da kallo ya Bita kafin yace"zaki dinga dafa Duk Kalan Abinci da kike so buh ke kadai Karki sake kice zaki yi girki dani don ni ba sa"anki bane,Su Daada ne suka matsa na Nataho dake amnh ni zuwanki da Rashinsa Duk Daya ne, so zaki iya Dafa abinci ki ke kadai sai ko megadi in zaki samai and kuma ki Duba komai kiyi list dim Abunda Babu ki bani gobe in na Fita zan Shiga kasuwa na Siya miki komai ga bedroom dinki nan Nima i hv my Own so karki Shiga Harkata nima bazan Shiga Taki ba Kowa yayi Rayuwarsa Am i Clear.."Yafada yana Kurban Ruwan Daga Tsaye ko jinsa batayi Sosai ta gyada kai Tsawa ya Dakamata kafin yace"Bakin ki na Ciwo ne.? Da zaki amsamin da kai.."Jikinta na Rawa saboda yunwa tace"Naji insha Allahu Zan kiyaye..."Juyawa yayi yana Fadin"Gud.."Daga Haka ya Shige Bedroom dinsa ya Rufo.
Dakyar ta iya karisawa Kichen din Tana laluben Hanya Saboda Yunwa ledar Farko ta Raruma nan Taga Take away din Shinkafa da Miya da Salat,sai Kaza Gashasshiya da Yoghourt,sai ruwan Faro mai Sanyi ai Aneesa bata tsaya wasa ba ta Zauna Dirshan Atsakiyar kichen din ta Tura Abinci gabanta ta Faraci ko Takan Cokalin Dake Ciki batayi ba Tana ci tana Hadawa da yoghourt,Sai da ta Shareshi Duka ta kuma Shanye duka yoghourt din ta jawo Ledan kazan itama taci Rabi ta Hada da Ruwa kana Tayi gatsa tana Shafa Cikinta kafin tace"Kai yau naji ta Babuwa..",Gaskiyan almajiri ne Dayace Yunwa bata da Hankali.."Take Fada Tana Dariya,sai da ta gama Hutawa kana Ta iya mikewa Dakyar Fridge ta bude ta saka Sauran kazan Tana Fadin'Na gobe don ba lalle bane ya Tuna Dani da Wuri.."Sauran Ledojin ta bude,kifi,Nama,kayan miya,green beans,Karas,Cabeji da Cray Fish,sai kwalin indomie guda Biyu,sai katan din Ruwa guda Daya Tana ga dai ya Siyo ne kafin gobe,Duka kayan Ta saka Cikin Fridge din shi kuma indomie ta barshi nan domin Store din yana Kulle ne sai Lokacin Ta iya Fitowa Falo tana Tura Ciki Hakikanin gaskiya Tayu Mugun Ci Daki ta koma ta Fada Tiolet wanka Tayi kana Ta Dauro alwala ta Fito tayi sallar Mangariba ta Hada da Isha"i Shafa"i da Wuturi tayi kana Ta Bude Akwainta ta Zaro Doguwar Rigar barcinta ta saka,sai dai ta Hau gado zata kwanta kana ta Tuna da,Abunda Bello yace ta Rubuta mikewa Tayi ta Bude Zip din Jakarta Inda ta Sako Littafanta Da Biro sai Qur"anin da Falmata ta Bata da azkar ta Yago Fallon Takarda Tayi Zaman Dirshan Akan gado ta Fara Rattaba Rubutu Wani Abun ma Harda mugunta su Semovita ne,wai harda aya da Dabino ta saka,wai na yin Kunun aya,hartagama Sai ta tuna da Abun Zobe Haka ta sake Rubutawa sai da ta Cika Takarda kamar Hauka,wani Abun ma Saboda Mugunta ta saka ba domin Tana ci ba,bata kwanta ba sai Wajen goma kana ta Nannade Cikin bargo sai barci.
*****
Karfe 7:3am na Safe ya Fito Daga Dakinsa Cikin Shirin Fita,Sanye Yake Cikin Wasu Ubansu American Suit,Ash And black,Ya matse Wuyansa da Tie baki kafarsa Sanye Cikin bakin Takalmi Rufaffe Na Fatar Damisa Haka Tsitsiyan Hannunsa Sanye da Agogo Baki na Fatar na kamafanin Rado,kallo Farko zakamai ka Fahimci Kwarjinsa Tare Dashi Wata karamar Jakar Briefcase ne Ahanunsa sai Wayarsa Dayake latsawa da Hannu Daya babban yatsansa na Sagale da key din motarsa.
 Â
karfe 8:00am yake da lecture din Yan level 1,Baya so yayi African Time Domin baya Cikin Tsarinsa,tun jiya bayan isowarsu Fitan dayayi Cikin makaranta ya Shiga ya karisa Abunda bai gama ba,bai Fito har sai da komai ya kamallah Har Office dinsa an basa mai girma da Tsari Saboda Samun Sa Very Young Teacher ga Talend da Brilliant,Kasashen Wajema Nemansa Suke ammh yaki yafison Aiki a Kasar Haihuwarsa.
Lokacin Aneesa na Kwance bata tashi ba Tun bayan Sallar Asuba,gashi bayason ya makara ita kuma ta bata masa Lokaci Kofar Besdroom din nata ya isa yana kwankwasa bayan ya lallashi Zuciyarsa Aneesa Cikin barci Taji Ana Kwankwasa Kofar Bedroom din data ke ciki ta tashi da Sauri sanin kowaye Hamma ta saki Lokaci Daya tana mika ta Bude Kofar Suka ci karo da Fuskokin Juna,Harara ya Zabgama Lokaci Daya yana Dauke kai saboda Rigar barcin Dake Jikinta mai kwashashiyar Wuya ne,gabadaya saman Nonuwanta abude Suke ita ko Lura batayi ba bai mata mgana illah hannu Daya mika mata,tana Hamma tajuya ta koma cikin Dakin Saman Side drower din gadon inda ta jera harda Qur"anin Datazo Dashi,ta Dauko ta kawomai bai Tsaya kallonta ba ko Duba Takardan ba ya juya yana Wani Fitar da kamshi ya Fice Daga Falon,Da kallo ta bishi tana Tabe baki kafin tace"Mutum Har mutum...Ammh ba kyan Hali.."Tafada kafin ta maida kofa ta Rufe ta koma ta kwanta tana Fadin Shegiyar katifan nan Dadin Kwanciya gareta kara Shigewa blanket Tayi tana lumshe ido Ita Adole Wata Hegiya.
Da salihu maigadi Suka gaisa kafin ya Shiga motarsa ya Fice Daga gidan,sai da ya Fara Tafiya kan Titi kana ya Duba Takardan,Zaro ido yayi yana mamakin