Showing 30001 words to 33000 words out of 122554 words

Chapter 11 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt

Advertisement

26 Jan 2025

24067

Nuna Jin Haushinta Sosai,ko Mahaifiyarsu Hajiya Yana bata Nuna Jin Haushinta Domin Duka Dayane.


Aneesa kwana Tayi kuka Kamar Ranta zai Fita Babu Abunda ke Tadamata da Hankali sai Dutsen nan da Kuma Debo Ruwa,Kai Gabadaya Mkrantan ma Bata Kaunarta ammh ya zatayi Bello yasaka ma Rayuwarta Ido kya ce Shine Bukar Bulama,Ko ya Ali yadda yake mata wani Abu,gani Take yafi kowa iya Shisshigi ,Toh in ba Haka ba,me Suka Hada Daga Yayarta na Auran Wanshi Itafa ta gaji da Wannan Ikon Nashi Allah sa Tagama Mkrantar Borno zata koma in ba Haka sai ya kara Sakamata Wani Tsaman.


Bata da yarda Zatayi Tana Kuka da Hawayenta Da Safe Aka saka Duka kayanta amota,Bayan Tayi sallama Dasu Daada,Bayan Motan ta Shiga Ita da Uncle Amunu Shi kuma Mallam Inuwa da Bello Suna gidan gaba Wanda ke Kallon Aneesa yana Kunshe Dariya Ranar ko Ya Muktar batama Sallama ba gani Take Hardashi Aka Hada baki Aka Maida ta Makranta Har Motarsu Ta Fice Daga Haraban Gidan Aneesa na Kuka Wiwi batayi Shuru ba sai da Bello ya Waigo yana Kallonta Cikin Dakewa yace"In baki kama bakinki ba...Zaki Sha Wuya ne yanzu nan.."..


Uncle Aminu kuma Kunnenta ya Murde yana Fadin"Bush gal,Banda Kauyanci Wata Mace kiga tana Gudun karatu,Zaki zama mara amfani Ko Aure kika yi In dai baki da Ilimi.."Tura baki Tayi Tana Kwallah Cikin Ranta ko Tana Fadin"eh din naji ina Ruwanka Mugaye Allah ya sakamin.."Take Fada Tana Share Kwallah Tundaganan Tayi Shuru sai dai lokaci bayan Lokaci Tana Share Kwallah..


Su S.jibiya sai dai Suka ga Aneesa Kwatsam Bayan Sun Dawo Daga Karatu Wajen karfe 2pm,wannan karon ma Hostel dinsu Daya Dr Karima part 1,Kuma Wannan karon ma Ajinsu Daya SS1a,Lokacin da Suka ga Aneesa basu gasgata ba sai ta Ta dago Tana kallonsu Tana Hararansu ga Hawaye na Zubomata ganin Haka yasa Suka Tabbatar da Aneesansu ne Suka Ruga Suka Fada Jikinta suna Ihun Murna,Da Farko Taki kulasu kuka kawai Take Sauran yan Ajinsu na Baya Duk Wanda yazo yama Aneesa mgana ko Kallonshi batayi Daga Baya Taga ba Sarki sai Allah ta saki Jiki,saboda ganin su B.kaita Tare Suka Tayata Shirya provision Dinta Cikin Lokarta Ranar ko pref basu Fita ba,masallaci ma basu Fita ba Cikin Hostel Suka yi Shi Sai Washegari Aneesa Tafara Zuwa Aji Domin Suna Zuwa Mr.Bello ya Damkamata Uniform dinta da Check dinta da Takalmin Mkranta da Jaka da Littafanta Sabbi,Hakanan Ta karba ammh Cikin Ranta bata gode ba.


Ranar Mkrantan Kwatar-kwashi Ta Dauki lbrin Aneesa Bukar Bulama ta Dawo makarantar Ranar ko Sai ga Jidda Tazo Wajenta Har Hostel tana mata Mitan Tana ta Sauraran Kiranta Karya Aneesa Tamata da Cewa Nombar ta bace mata ne Shiyasa Marairaicemata Jidda tayi Tana Nuna mata Irin Son Datakema Mr.Bello gashi Saura Sati Daya su bar Mkranta Ta mata Kokari,Gyadamata kai Aneesa Tayi da Cewa ta bata da Zuwa Gobe Insha Allahu zata san yadda Zatayi Da Haka Suka Rabu da Jidda Tatafi Tana Jin Dadi Itako Anesa Mirmishin Mugunta Take mata na zakici Ubanki ne,Bayan Jidda ma Iri iritan Sun Ta Zuwa Wajen Aneesa Suna mata magiya ita kuma tana Sakasu akwana Aranta tana musu kallon Wawaye.


Wannan karon Seniors Suna Saman Bene ne,Shiyasa Sai Wahalan bata kai na Baya ba,kuma ba laifi Sun san kan Mkranta sai dai Su kalli Sabbi Dauka in sunga suna iyayi,barima New Comers Jss1 Dariya ma Suke basu kafin Sati Sunci Kwal Ubansu Ko Debo ruwa ma Aka barsu ya Ishesu balle Muguntar Seniors Abun da Zai sake Baka Mamaki Har Ss1 Dinsu Mr.Bello Shine Formaster Dinsu yana Lura da Aneesa Shiyasa Ko Taso Tayi Wasa Batayi Duk da yanzu ya Rage Wata Muguntar Akanta ganin Ta Dan Fara Hankali ba kamar baya ba.


Ranar da yan SS3 Zasu yi Candy,Ranar ne Dukkansu Suka Hau Saman Dutsen na Kwatar-kwashi Suka Debo Gayyayyanki da Sauran Abubuwa wasu da Aljanu Suka Sauko Aneesa Tace kamar Dole mezai aiketa ko Candy zasuyi Wlh bata iya Hawa Wannan Dutsen Domin yana bata Tsoro Haka Lokacin Zafi in ya Dauki Zafi Wuta yakeyi Da Kanshi Lokacin Sanyi kuma yana Fitar da Huturin Sanyi Wani Lokacin ma Bacewa yakeyi Kwata kwata ba Aganinshi.


Da Jidda Ta Mtsama Aneesa da Magiya sai ta Mata karya da Cewa Uncle Bello yace Taje ta Sameshi Haka ta Dingama Saura Acikin Ranta Tana Dariyan Mugunta,aiko kuwa Sunyi Nadama Domin Koran kare Bello yayi musu bayan yayi musu kaca kaca,Kowacce tasha Kuka kafin ta bar Makranta barin ma Jidda da Takejin Soyayyar Bellon Har Cikin Ranta Itakuwa Aneesa Boye kanta Tayi Har Suka bar Mkrantan.


*****


Tafiya tayi Tafiya Cikin Jin Dadi Da Akasinsa Domin gashi Har su Aneesa Sun Shiga Ss2 Abun da zai baku mamaki yadda Aneesa Bukar Bulama ta zama zakaran Gwajin Dafi Wajen Kokari Acikin Mkrantan Duk Dalilin Bello yanzu Aneesa Ta Daina Kukan Zuwa Mkranta Tunda ta Fahimci bello bazai Taba kyaleta ba,Tana Da Kokari Afannin Darasinshi dana Uncle Aminu Domin ita dasu S.jibiya Turanci Abakinsu sai ka Rike baki,Ahutun da suka samu ne na First Time Anty Rahila ta Haihu Ta Haifi Da Namiji Wanda Yaci Sunan Muhammed Suna Kiranshi Junior,Lokacin Haihuwan Duka yan Borno sun Taho Harda mama Falmata mahaifiyar Aneesa da Anty Nafee da Anty Yagana,da Anty Aisha Daga kano sai Matan Ya Ali dana ya Sunusi da Ya"yansu Harda Sanah Tazo wannan karon,Hakama bangaren Su Abba kabiru Hajiya karima tazo ita da Zubaida duk da Zubaidan Tana nan Abujan ne Wajen Ya Hashim tana Shekarar Farko A base University Zulfa ce Take Katsina Umaru musa yar"aduwa.


Zuwanan da Sukayi kowa yayi mamakin Yadda Aneesa ta kara zama sai dai Fa mai Hali baya barin Halinsa,Rashin kunyanta da Tsiwanta na nan bai barta ba Sai dai yanzu ilimi ya Ratsata ta Rage Wasu abubuwa kamar su Faduwa akasa tana Kuka da Wasu Abubuwan,ko da Sunan sai da Takai Zuciya nesa Ammh Haka Anty Nafi ta Dinga kyaranta da Anyi Abu sai tace samun Waje ne,Har Sanah ma Ta iya kallon Banza Saboda Tana Da Girman Jiki tana ganin ta kamo Aneesan Aiko taci Ubanta Don Aneesa bata Daukan Raini gayamata tayi Ita kanwar Uwarta ce ba abokiyar Wasanta ba,Saboda Haka ta Shiga Taitayinta,Dole Ta Shiga Natsuwarta Sanin Halin Aneesan Ko Lokacin Data zauna agidansu bata da Sauki balle yanzu da Girma ya kara kamata ta kara zama yan"mata sosai.


Falmata har Acikin Ranta Taji Dadin ganin Aneesa ta kara Chanzawa ko bata Nuna ba Kowa ya kalli Fuskarta zai gano Tana Cikin Farinciki Awannann Zuwan ne Har suka zauna da Aneesan Suka danyi Hira saboda kwata kwata babu Shakuwa Irinta Uwa Atsakaninsu Domin kaf Ragamar Kuruciyar Aneesa Alhaji Bukar Bulama ne keda Hakki Akanshi Shine yasan Komai na Aneesa Saboda gatan Datasamu Awajensa,Wananan Hutun taso Zuwa gidansu B.kaita da S.jibiya sai bata samu Hali ba Saboda haihuwan Anty Rahila din,Sai ta bari sai da suka kara samun Hutun Second Term kana ta Roki Anty Rahila da Daddy Suka barta,Salamatu Jibiya suna Dutse ne da Zama Mallam Inuwa Shi ya kai Aneesa Ta Kwana Daya agidansu S.jibiya Kana ita da Aneesa Suka Tafi katsina gidansu B.kaita Hakika kawaancen Kawayen Junan Abun kallo ne Duk da Kullum Cikin Yin Fada Suke barinma B.kaita da Aneesa basa Iya zama Waje Daya batare da Sunyi Tsiya ba,Kwansu Biyu Akatsina Direban gidansu B.kaita na Yawo Dasu Cikin gari Dayake bayan Mallam Inuwa ya kawota sai ya koma,Iyayensu duk sunajin Dadin kawancensu Sosai Tunda Dukkansu yara ne masu Tarbiya da Hankali Ko Tsiya Tatashi Tsakanin B.kaita da A.bukar bulama in tana so Ta Harzuka ta tace mata yar Baka,ko kuma tace mata Tana son Uncle Bello yanzu Aneesa zata Birkice Tafara Tsiyarta B.kaita ta Biyemata Suyi ta kasa Hali ba Ruwansu bai Hana Kuma anjuma ka gansu Tare ba,Sai da suka Dawo Ta Dutse kana Baban S.jibiya ya sanya Direba ya Maidota Har Abuja Booth Dinta Cike da Kayan Arzikin da Iyayen kawayenta Suka Hada mata bayan Ta Dawo ta kwana Biyu Suka Tafi Borno Ita da Anty Rahila da Hibba wacce ke Mkranta yanzu a British International School Abuja Suma sun Samu Hutu ne sai Muhammed Junor Ajirgi Suka Tafi Borno Wanda Suka Shafe Sati Daya,Anty Rahila ta Koma Ammh sai ta bar Aneesa Da Hibba Anan Suka karisa Hutunsu kafin su Dawo Abuja.


Zuwan da Aneesa tayi ne Wannan Karon ta Sauka Dakin Innarta Falmata badomin komai sai Domin Tafara Hankali ta Fahimci Uwa ta Wuce Wasa,Kuma Ita Din wani Jinshiki ne Ashe Falmata na Sonta kawai Hallayarta ne ta Tsana da Kuma kawaici Haka ta Dinga ina zata saka Da Aneesa,wannan Hutun kam su Ya Ali basu yi Ciwon baki ba Kullum kuma godiya sukema Bello Domin Yayi Abunda Su baza iya ba Ya Dawo da Aneesa mai Hankali Ilimi ya Ratsata ba kamar Baya ba,sai dai yaransu suna cin ubansu bata Raga musu Duk wanda yashi ga Gonarta Dafashi Take ba Ruwanta Balle Hibba da Tsokana in Ta Tsokanesu Suka Daketa Har Dakin Uwar yaro zata Bika ta Daka Uwarshi bata isa Tayi mgana ba in ma Tayi Toh yanzu Aneesa Zatace Suma haka babanninsu uka nadeta kamar Jaka Dole ta rama kan ya"yansu Tunda bazata iya Ramawa kan Su ba.


Bataje gidan Anty Nafee ba Ita Datake Aure aMaiduguri Anty Yagana tabi Ibadan Ita da Hibba bayan Tazo,wajen Sati Tayi musu achan Mijin Anty Yagana yana ta Tsokanarta suna Tuna mata Abunda Tayi sai dai Tayi Dariya kawai batacewa komai,Toh me zatace Ita kanta Tasan Aneesa Tayi Lokaci,Tasani lokacin Akwai yarinyata yanzu kuwa ba laifi Budurci ne yagama gauraye Jikinta Shiyasa Tabar yayin Wani Abun Ammh Fa Tura baki da Kunkuni Aneesa Bata Daina ba sai dai Wanda yafi karfinta bai Shiga Harta ba yanzu bakin nan zai yi Tsini kamar zai Fado kasa


Sunsha Hutu Sosai Kafin Mallam Inuwa yazo ya Daukosu bayan Sun Dawo Borno,Kafin su Tafi Haka Anty Nafee tazo Tana ta yada mata da Mgana wai saboda Ita bata dashi Shiyasa taki zama awajenta,ammh sai gashi ta Zauna Wajen Rahila Tunda Mijinta wani ne Akasar Gabadaya kuma yana da tarin Dukiya Shiyasa Koda tazo batayi Tunanin Zuwa Wajenta ba,Aneesa na Jinta ta mata Kunnin Uwar Shegu Domin ba Tun yanzu ba tasan Babin da Anty Nafee ta ijyeta taso ta zauna Wajenta tadinga mata Bauta Tunda Jakarta ne,mama Yana ce Ta kama ma Nafeen Fada kana Tayi Shuru Falmata kuwa tayi Tayi da Aneesa Taje gidan Nafeen Tace bafa zata je ba,Wannan karon sai dai Wani Hutu Wanda Cikin Ranta ta saka Kano zata Gidan Anty Aisha bazata Dawo Bornon ba.


*******


Kwantashi babu Wuya Awajen Ubangiji Domin gashi Har Aneesa Sun Shiga Matakin Karshe Asecodry,Sun zama Manya yanzu bamai Takura musu Abunda Suka ga Dama Sukeyi,Gashi Abun Murnan Aneesa Uncle Bello baya Makrantar yanzu Tun Suna Third Time a Aji biyu,ya Tafi Malesia yin PHD ,dinsa Hakama Uncle Aminu Shikuma ya Haura Kasar Spain,Shima yaje Hado Master Dinsa Duka Tare Suka Tsara Tafiyan Kusan Lokaci Daya Suka Tafi Leave Without pay batare da Sun Ijiye aikin koyarwasu ba Hakika Mkrantan Kwatar-kwashi Tayi Rashi Sosai Wasu Dalibai da yawa basuji dadi ba irinsu Aneesa ko sai bude Shafin Iskanci Juniors kuwa suna Cin Ubansu Wajen Aneesa ba wanda baisan Set din 3stars ba Gwara kowa da Aneesa domin Wlh Karonta da Mutum ba Dadi gashi Lokacin Ita ta Rike Headgal,Uncle bellon Da kanshi ya bata Lokacin da Yan Ss3 suka Tafi kafin Shima ya bar Kasar kenan,ita kuma S.jibiya House Captain ce,sai B.kaita Dake Mtsayin labour,sun zuba Lokaci kuma suna gan Zubashi domin ba"a Taba mugayen Set kamar su ba Na kasa dasu suna Dandanawa Sosai.






*How to pay....â‚?200 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..â‚?400...or MTN card aturo ta wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*


_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �350 ne,VIP �600, Single one �200 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_




*Shakira..*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_




*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_
    Â
*🅿�11*
   Â
Sun Dawo Hutun First Time a Lokacin kuma Duk Wasu gabobin Burdurci Sungama Bayyana Ajikin Aneesa Bata kara Kiba ba sai dai takara Murjewa Zama Cikin Hutu da kuma Rayuwa Cikin A.C Don ma In ta Koma Makranta Takanyi baki da Rama Duk da duk Jin Dadin da Aneesa ke ciki bata yadda ta Chanzama Fatar ta launin sa ba,ammh takan shafa mayuka masu kyau da taada su suka sa Tayi kyau Fatar ta Murje.


Kirjinta kuma ya Cika da Dukiyar Fulani masha Allah,hakama Kugunta Shima yana Tsuke,masha Allah ta Ko"ina Aneesa Ta Cika Budurwa domin Lokacin Tana da Shekara goma sha Tara Aduniya Tana Jinta kamar Babbar Mace,haka zalika yanzu Tafi jin Dadin Rayuwarta na ganin Uncle Bello baya nan Sai Cin karanta Take ba Babbaka,Uwa uba Daada da Daddy basu son Laifinta har Gwara Anty Rahila na mata Fada Wani Lokacin,komai na Bukatar Rayuwa Babu Abunda Aneesa Tanema Tarasa Babu Abunda Zatace da Anty Rahila da Ya Muktar sai godiya Domin Sun Taimaka Wajen Inganta Rayuwarta Uwa uba kuma Muhammed Bello,Wanda ko Ayanzu Takan godemai Wani Lokacin badomin Shi ba da yanzu bata zama mai Ilimi ba balle Ta Rike Shugaban Dalibai na Mkrantan kwatar kwashi Baki Daya ba,Takan Godemai Acikin Ranta Duk da ko bata daina jin Haushin sa ba.


Zulfa ko da Zubaida sun Janye kafa da Zuwa Hutu gidan Daddy sai Lokaci bayan Lokaci Tunda Suka Fahimci Shi Gwarzon nasu basa gabanshi Daga karshe yazo ya bar kasar Duk da Zubaida na Abujan bata Cika Zuwa ba Balle Zulfa Dake Katsina karatu ya Tasa ta Gaba,Shiyasa yanzu basu cika Zuwa gidan Akai akai kamar Baya ba.


*****


Tana Zaune A kan Three Sittet na Cikin Babban Falon Gidan,wayar Anty Rahila ce Ahannunta Tana Game din Tample Run,domin Ita Anty Rahila ta Hana Ya Muktar ya Siyamata Waya tace ya bari Tayi Candy,itama Aneesa bata damu ba Tabari sai Tagama Candy Lokacin Ta koma Borno Domin bata da Burin Cigaba da Zama Abuja kuma..


Sanye Take da Doguwar Rigar Jallabiya Baka,wacce Ta Dace da Surar Jikinta,kanta Kitson kalaba da Alheri mai Aiki ta kama mata Tunda Dama bata son Kitso D'an Kwallin Jallabiya ne ke Kanta bata Daura ba yama Kusa Zamewa kafarta na kan Cafet din Dake Shimfide Afalon Wanda Ta dura kafa daya kan Daya Tana kadawa,Daga Kumbunan ta kuwa Suna Sanye da Jan Lalli daga Saman Kumbunan kuma Ta Cike Da baki Har Zuwa Hannayenta Dake Rike da Waya,Fuskarta Tayi kyau Sosai Duk da batayi makeup ba ammh Ta sanya Hoda,da liptck sai Fuskartata tayi kyau Sosai.


Daga Tsakiyar Falon kuma Junior ne kan Wata keke mai Azaban kyau da Tsari Bata da Tsawo sai dai Fadi,gefe da gefe kamar wajen ijiyema yaro ko madara ko ruwa Daga baya kuma Wajen zaman Babban ne Daga Alamu dai nKekan koyon zama ne Domin yana Zaune sai Wasa yake da Fiddar Dake Hannunshi Haka yake Bashi da Rigima Batasan Hayaniyar Hibba ne yasa ta baro Shashen Daada Ta Dawo nan Anty Rahila kuma tana sama ta Kwanta bata jin Dadin Jikinta.


*******


Security Suna ganinshi Batare da Wani Tambaya ba Suka Wangalemai get ya Sulala bakar Motarsa cmry Cikin katon Farfajiyan gidan Da Sojoji suka kawatashi da Zagaye,cikin Takama yagama Daidaita Motar Bisa parking Space ya Dade kafin ya Bude Murfin mota ya Fito Wani Cute and Handsome guy nagani Dogo ne,Shi ba Fari ba Kuma bazaka Sakashi Cikin layin bakaken Maza ba,Irin kalarsa Tafi kama da Labaranawan Egpt,yana da Zati daidai gwargwado da Kyakyawan Fuska sanye yake da Riga da Wando na Kamfanin Armani Rigar Blue ce Mai Dogom Hannu sai Wandon kuma Navy Blue ne,ammh ya matsemai jiki Ba sosai Kafarsa sanye da Wani Bakin Takalmi booth mai kyau da Tsari,Fuskarsa kuma Toshe da Wani Bakin glass Wanda ke karamai kyau da Zati.


*KASIM KABIR JIKAMSHI* kenan,Matashin Saurayi mai ji da Kudi da Naira,Kasim Irin Matasan nan ne Masu Budewan Ido Tun Zuwanshi kasar Waje karatu Turawa Suka lalatashi ba Sharholiyar Da baya yi Har giya yana Sha Neman mata kuwa kamar Bunsuru,Daya kyal ido yaga mace Toh babban Burinshi ki bada Hadin kai ya kwalfi Ruwan Dadi Ko da ya dawo Babu Abunda yafasa yana samun Aiki a kaduna wanda ya Muktar ya samarmai yaje ya Dasa Daga Inda ya Tsaya Duka iyayensa ba Wanda ya Taba sanin Halin Dayake Ciki sai Hashim Wanda Ya Taba Riskanshi Cikin Halin Buguwar giya Lokacin Daya kaimai Ziyara agidanshi Dake Kaduna Duk dq ya mai Fada Harda Barazanar zai Sanar da Abba Kabiru bai sa Kasim ya bari ba,Ko yana so ya bari sai yaji bazai iya ba Yadai Furtama Hashim Din Daya bari ammh bawai Don Ya bar Abunda yake aikatawa ba,akallon Farko in kayi mai zaka Gane Cikakken Dan Duniya ne Dayasan Harkan bariki.


Yau kwanansa Hudu Agarin Abuja Sunzo Wani Worshop ne Daga Wajen Aikinsu Gobe zasu koma kaduna Shine bayan ya biya gidan Hashim sun gaisa da Matarshi Shi baya gida,sai kuma yace bara ya biyo ta gidan Ya Muktar su gaisa Da Anty Rahila Duk da yana da Tabbacin Baya gida yanzu,dama ko chan yakanzo Lokaci bayan Lokaci Duk Dashi da Bello kowa najin kanshi ya Isa,ammh bai sani ba Bello ya Fishi Iskanci da Taurin Zuciya,kuma Abunda Kasim bai sani ba Duk Iskancin da Kasim ke aikatawa Bello nada lbri Saboda Akwai Wani Abokin Aikinshi da Suke Aiki Tare a Kaduna,Tare Sukayi Universty of ibadan da Bello,Toh ya Taba ganin Hotonshi Awayarshi,inda yake Nuna ma Wani yana bashi lbrin Irin Iskancin da Kasim ke Zubawa babu babu Abun da yafi Batama Bello Rai Irin Neman Mata da Shan Giya da akace kasim nayi ko bakomai suna da alaqar jini,lokacin Har Abokin na Kasim sani na Fadin garinku ma Daya Muhammed Bello Shima iyayenshi mutanen Jikamshi ne yake kawai yayi koda Wasa Bai Nuna ma yataba ganinshi ba.


Cikin Isa da Takama ya kama Hanyar Kofar da zata sada ka Da Babban Falon gidan,yana Tafe yana Cilla key din Motarshi Kofar Falon ta glass ne na Waje in zai Shigo yana ganin na Ciki Tun Alokaci idanuwansa suka Fara Masa Tozali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login