Showing 42001 words to 45000 words out of 122554 words
Chapter 15 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt
Bello yayi kafin yace"Innalillahi garin yaya..? Shaye Shaye yake da Neman mata fa..ko ya Daina ne..? Wani kallo ya muktar ya sakarmai kafin yace"Meka ke fada ne Bello? Bangane ko ya Daina Shaye Shaye Da Neman mata ba..?
Mikewa Bello yayi yana Fadin"Ya Muktar Kasim fa Dakake gani Ba Namijin Aure bane,Shaye Shaye yake fa Da Neman mata ko Bunsuru ya Shafamai lafiya,ya kamata ku Fara Bincike kafin ku yanke Hukunci koda Kuwa Ni nan kaina ne,ya kamata ka Bincika Personal life dina balle wani.."
Hannu Muktar Ya Dagamai yana Hararansa yake Fadin"Ka bani Mamaki Bello,Ban taba Zaton Dom Baka Shiri Da Su kasim zai Saka kamai Wannan Kazafin ba Shedar Zina fa karfi gareta.."Cikin Rantsuwa Bello yace"Wlh Yaya Am Telling u d Truth Naji Abakin Wanda bazai Tabamin Karya ba.."Tsaki Yaya Muktar yaja kafin yace"Au Ashema Ji kayi ba gani ba..plz mubar wannan mganar bana son Talking Rubbish kuma Daga bakinka u better keep ur mouth Shout Domin babu Abunda Mganarka zai Chanza On Firday akwai booking Flight Zuwa Maiduguri Duka tare dasu Abba kabiru zamu Wuce,Mu Dawo Aranar tare da Amaryar Asabar Suyi bikinsu Anan on Sunday kuma Akaita gidan Mijinta a kaduna so in zaka je u are Welcome in kuma U are not Coming No problem u can Stay..."
" Ya kareshe Fada yana Zakuda mai kafada,Daga Haka ya barshi nan Tsaye ya haura sama Cikin Sassarfa ransa bace da kalaman Bello Wanda Suka bata ma rai Bai Dauka Bello yana da Wannan Halin ba sam.
Shiko Bello Jikinsa ne yayi Sanyi Har Ya Muktar ya kulema ganinsa,Ajiyar Zuciya ya Sauke Cikin bacin Rai da Jin Haushin Yadda Ya muktar yaki Sauraranshi Saboda Wani Uzuri Nashi mara Tushe Ammh Tsakani ga Allah In Har Suka Auramata kasim Sun cutar da Ita Abun nashi Yayi yawa bayan Neman mata harda Shan giya Haba Zasu kashemata Kuruciya wlh,Cikin Bacin Rai Shima ya bar part din ya Muktar din Zuwa part Dinshi Ranshi na Kona Tiolet ya Fada ya sakarma kanshi Shower Haka Kurum yaji Ransa na Kara baci na ganin yadda Ya Muktar ya nuna yafi yarda Da Bangaren da Suka Cutar da Rayuwarsu Fiye Dashi Abun in ya Tuna yana Kara batamai Rai Sosai.
Baisan lokacin Daya kwashe yana Cikin Shower ba sai da ya gaji da Kanshi yayi wanka ya Fito bayan ya Dauro Alwala,wata jallabiyan ya sake sakawa Wanchan ya Barota Cikin Bucket din Dake Tiolet,Shafa"i da Wuturi yayi kafin yayi Addu'o'insa Daya Saba, Gadonsa ya Haye bayan ya Cire Jallabiyan ya Rage Dagashi sai Boxers,jakarsa ya Bude ya Fito da karamar laptop dinsa Daya Chanza a Malesia,kunna ta yayi bayan ya Kara Haura wa saman Tsakiyar gadon Sosai,ya sakata Atsakiya yafara Shige Shigensa.
Duk yadda yaso yayi aikin Abun ya gagareshi,Duk da Ko ya ci karo da Sakon Farinciki Daga Jami"ar Bayero University Dake Kano BUK tun Yana Malesia ya Tura musu Takardunshi ta Email Shine yanzu Suka Turomai Sakon Sun Daukeshi lecturing a Mathematics Department,Yanzu Suna Jiransa yazo ya karbi Appointment latter dinsa,bayan yazo yayi Reporting,Domin Dama Tunkafin Tafiyarshi yasaka ma Ranshi in ya Dawo zai bar Koyarwa a Makaranta Secondry ta kwatar kwashi Zai koma Wata Jami"ar Agida Nageria Suma Su Amfana da Basirarsa.
Ture Computer yayi yana Dafe kanshi Lokaci Daya Aneesa Ta Fadomai Arai,ya Runtse Ido yayi yana Tunata tun Farkon Zuwanta gidan Har Zuwa Lokacin Daya bar Kasar Tsiwarta Rashin kunya da Tsoronta yake Tunawa Tare da karamin Bakinta,Aranshi yanaji kamar in ya bari Aka Aura mata Kasim ba"a ma Maraicinta Adalci ba,Mikewa yayi ya Fara Zagayen Bedroom Dinshi Lokaci Daya Yana goya Hannayenshi Abaya Kansa ya Dau Zafi bashi da Wani Hop in ba Ya Muktar ba Aneesa bashi da kyakyawan Alaqa da Ita koma yana Dashi yanzu Lokaci yakure,Kansa ya Dafe yana Tunanin mafita kafin Lokaci Daya Wani Abu ya Fadamai Arai da Karfi ya Furta
""Sani....Yes bari na Kira sani Zai Taimakeni Insha Allahu Tunda yasan Komai da Hanzari ya Nufi Wayarsa ya Dauko Contact Dinshi ya Shiga ya Lalubo Lambar Sani,wanda yama Saving da Sani kaduna,har sai da Wayar Ta katse Sani bai Dauka ba,Tsaki Bello yaja kafin ya kara Kira Yana Fadin"Kai pick d Call plz.."Yake Fadi Lokaci Daya yaji Sani ya Daga Kiran yana Fadin"Ah Malamin makranta Yau Agari.."?
Ajiyar Zuciya Bello ya Saki kafin yace"Sani How are u..? Sani yace"am Fine ka Dawo kasar ne..? Don kwanaki in ban manta ba kace zaka Haura malesia ko..? Gyada kai bello yayi kafin yace"Eh naje Yau ma na Dawo kasar."Washe baki sani yayi yana Fadin"masha Allah Sannu da Zuwa An Dawo lafiya.."Bello Cikin kaguwa yace"Lafiya lau,Don Allah sani Ranar Friday kana Available..? Yafada yaji ko Sanin zaije Daurin Auren Ko A'ah..'
Sani yayi jim kafin yace"Gaskiya bana garima gabadaya Borno zamu tafi Wajen Daurin Auren Wannan Abokin aikin nawa kasim Wanda na Taba Nuna maka Hotonshi nace ko ka sanshi Shima Iyayenshi y'an Jikamshi ne..?"Cikin Farincikin Bello yace"Oh Allah Sarki na ganeshi ba Wanda kuke Zencensa kai da Wani Abokinsa kan ya Cika Shigen Neman mata da Shaye Shaye ba.."?Dariya sani yayi kafin yace"Extaly Malamin makaranta Baka da Mantuwa Shi kuwa Kasim Kabir Jikamshi ba, Aiko Zaiyi Aure Kanuri zai Auroma .."Yafada yana Dariya,
Gyara Tsayuwa Bello yayi kafin yace"Ahf toh ya Daina Neman Matan ne Dazai yi Aure? Sani yace"Umh ya Daina mene..? Sai ma Abunda yayi gaba yanzu Haka ina bakin Titi ne Muke Wayar nan naga Wucewarsa Amota Shida Wata kasan Abunda kebani Haushi da kasim..? Bai bashi Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Kazantarshi Tayi yawa bama zai Tsaya ga ya"yan Hausawan mu ba Harda kabila da Arna marasa Addini,kuma Duk yadda yake Fadin yana Son yarinyar dazai Auro Wlh bai daina kwana Cikin maye ba,kuma bai iya Hakura sai ya Kwana Tare da mace,Fisabillahi me Ake da Hali Irin na Kasim kwata kwata ba Tsari Aini Wlh ina Tsausayama Yarinyar dazai Aura Kawota kawai Zaiyi Bakincikinshi ya Kasheta.."Bello yayi Ajiyar Zuciya Takaichi na Cikashi yace"Gaskiya fa..Toh Ba"ayi bincike bane Dagachan barayin Ita yarinyar..'?
Sani yace"Waya saninmu su Kasan yanzu ba Duka Aure Ake ma Bincike ba Indai kana da Naira Alhaji ka gama mgana,balle Shi naji yana Fadin ko Matar Wani yayanshi to kanwarta ne.."Bello yayi Saurin Cewa"Ok Nama Tuna Ranar nima zani Maidugurin Wani Daurin Aure ko zaka Shigo gobe don Allah Sani mu Tafi Tare.."Shuru sani yayi kafin yace"Kash.Gashi Tare da yan Office,dinmu mukayi Booking din Jirgi zamu Tafi."Da Sauri Bello yace"No karka damu Sani Nima anan zan mana Booking Din Flight plz Dont Say No.."Ajiyar Zuciya Sani ya Sauke kafin yace"Shikenan ammh ni bansan Wajen Daurin Auren bafa..? Bello yace"Karka damu ba ga Waya ba.."
Jin Haka yasa Sani yace"Ok goben Zan Shigo Jirgi Zuwa Abuja in na Shigo zan Kira ka,long Time Daman bamu Hadu ba.."Cikin Jin Dadi Bello yace"Yauwa..Sai na Jika.."Daga Haka Suka yanke Kiran Gefen Gado bello ya koma ya Zauna yana Mirmishin Nasara Kafin lokaci Daya ya mike laptop dinsa ya Dauke ya Kashe ya Ijiyeta kan Side Drower,Kan gadon yahaye Lokaci daya yana Lullubewa da Blanket,bayan ya Zuro Hannu ya Rage Hasken Dakin bai Dau Lokaci ba barci ya kwasheshi Cike da Jin Dadi.
******
Washegari Around 4pm Sani ya Kirashi yana Filin Jirgi Shida Mallam Inuwa Suka je Suka Daukoshi koda suka Dawo Sun Iske Ya Muktar ya Dawo Gidan Dama Meeting ya Fita Wanda Suka gudanar Afadar Shugaban kasa,koda Asuba Sun Hadu Amsallaci Bellon na gaisheshi Dakyar ya amsa kamar Wani mai Ciwon baki Shidai Bello bai Bi Tankanshi Domin yana Ji Aranshi bazai Taba bari Kasim ya Auri Aneesa Ba ko bakomai In Hallayarsa ta Fito Filo sai anfi ganin laifi Ya Muktar Fiye dana Kowa.
Koda Sani yazo har Falon Ya muktar ya kaisa Suka gaisa Ganinsa da bako yasa ya saki Fuska Suka gaisa Daganan Mension Din Bello Suka koma Sukayi Wanka Suka Ci Abincin Da Ya saka Alheri ta Hauro musu Dashi,Sai da Suka kamallah Suka Shiga Hiran Duniya kana Bello ya gyara zama yana kallon Sani Lokaci Daya ya Warware mai komai kuma ya sanar dashi Irin Taimakon Daya ke Bukatar ya bashi Gobe in Sun Isa garin Borno.
Zaro Ido Sani yayi Cikin Kaduwa da jin Bayanan Bello yace"Kai Bello gaskiya bazan iya yima kasim Haka ba kamar nafa Tozartashi ne a Idon Duniya karka manta an Taru ne za"a Daura mai Aure..kai gaskiya Bello bazan iya ba Wlh ."Yafada yana Kallon Bello Cike da Wani Tunani.
Mirmishin Yake Bello yamai kafin yace"U hv to do dis Sani kar ka manta Aneesa zamu Taimaka fa,ni kuma na Cire yayana Daga Zargi yazakaji in mai irin Halin kasim yazo Neman Auren kanwarka Alhalin bashi da kyawun Hali kuma,in ka Fahimci Haka Koda Lokaci ya Kure zaka yarda ka Aura mata Shi.?."Tsuru Sani yayi kafin ya girgiza kai yana Fadin"A"ah gaskiya bazan Bata Shi ba kam..Ammh bello baka..'Hannu Bello ya Dagamai yana Fadin"Ba ruwanka kadai kawai Shaida zaka bada ni zan karisa Sauran Aikin ammh Tabbas Ni muhammed Bello Jikamshi bazan Bari Adaura Auren Aneesa da Lallatattacen yaron nan ba Insha Allahu kawai kamin Abunda na Rokeka plz.."
Sani ya Dade yana kallonsa kafin ya Sauke Numfashi yana Fadin"Shikenan Allah ya kaimu.."Mirmishin Jin Dadi Bello ya saki Har fararan Hakoransa na Bayyana Waje yace"Nagode Sani.."Daga Haka Suka Cigaba da Tattauna Batun,Sani na kara bashi Lbrin Wasu Gurbattatun Halin Akuyancin Kasim Abun ba Dadin Ji,.
Sai bayan Sallar La"asar Bello ya karbi Key din Mota Ya jasu Suka Fita yawo Cikin gari Shiko ya Muktar Tuni yayi Waya Zuwa Filin Jirgi An Riga an yi musu Buking Din Flight Dukkansu Harda su Abba kabiru da Kasim da Hisham da Sauran Abokan Tafiya Wannan Nauyin Muktar ya Daukeshi na Zuwansu Borno da Dawowarsu Batare Daya kara Bi Takan Bello ba Bai san Shi kuma anashi barayin yagama Shiryama goben ba.
Ki biya ki karanta cikin salama.
*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*
*🅿�15*
*BORNO*
_maiduguri_
"""Washegari Ta kama Jumma"a ne Ranar Daurin Aure,Tun jiya Gidansu Aneesa Suka Sha Bikinsu Sosai In kaga Aneesa Lokaci Daya bazaka iya ganeta ba Saboda yadda Takara kyau da Haske Duk inda ta Shiga Tana Haskawa Ga wasu Sirrinka kamshi Dake Tashi Ajikinta Fatarta Ta koma kamar na Tarwada Saboda Santsi,Tasha kyau kamar ba ita ba.
Ita dasu B.kaita akama Kunshi ja da baki Suka kuma je gyaran Kai,Aneesa Ta sanya kayan alfarma sosai Na Cikin kayan Da kasim yayi mata ne Wanda Suka zo da Wasu nan Maiduguri Anyi Shagali Sosai Kowa kagani Cikin Farinciki musamman Anty Rahila da Anty Yagana kamar Sune Suka Haifi Aneesa Saboda Sune kan gaba Bisa Komai.
Yau din An Tashi da Shiryen Shiryen masu Zuwa Daurin Aure ne Daga Cikin Gida kuma Mata nata Shirin Wadanda Zasu Raka Aneesa Abuja Dagachan kuma Su Mikata kaduna,Daga Haraban Gidan Kuwa An Share ko"ina Motocin ya Ali dana ya Sunusi Waje Suka maida su,filin Wajen Aka Kawata Shi Da Fararan Kujeru Daga Cikin Falon su na Baki Dake Wajen Cikin gida Shima an gyarashi Tsab Saboda nan ne Waliyan duka bangarorin zasu Shiga Domin Gudanar da Daurin Aure gefe Daya kuma An Baza Tabarmu Abun Sai Wanda yagani.
Tun karfe 8am na Safe Tawagar ha Muktar Suka Rakashi Zuwa Filin Jirgi na Nmandi Azikiwe International Aiport Abuja Inda ya samu Abba garba,Abba kabiru,Hashim,Kasim Ango da Amininshi Haruna Sai Wasu mutane Biyu Daga cikin Abokan su Abba kabiru,Wanda Tun Jiya suka Iso Gidan Hashim Suka Sauka Wanda Tuni Matarshi da Zubaida Suna Katsina Ana Shan biki Suma yau ne Taron Bikin nasu.,Kasim kuwa Tun Ranar Alhamis ya Baro Kaduna Zuwa Katsina Shima sai da Hashim yamai Dirar makiya Acikin gidanshi inda yakara Tarar Dashi da Wata mace Agida,Abun ya batamai rai ya Dinga mai Fada Kuma ya matsamai Suka zo katsina Tare bayan yayi mai Rantsuwan ya bari.
Koda Bello da ya Muktar Suka Hadu Bayan sallar Asuba bai saki Fuska ba Shima bellon Dauke kai yayi ya Hade Fuska da Sani kadai Suka gaisa Agaban Idonshi Ya Muktar din ya Fita Zuwa Filin Jirgi Ansha Uban babban Riga Suma karfe 9am na Safe Suka isa Filin Jirgi Shida Sani Dukkansu Suna Sanye da Manyan kaya,Sani yana Sanye da Wata Farar Shadda Riga da Wando Dinkin Tazarce Da Hulla zannah Bukar Sai Bello Dake Sanye da Wata Gezner Mai Ruwan kasa Aikin Jikin Riga Brown Clour ne Haka Rufaffen Takalmin kafarsa ma Brown clour sai Hulan kansa Zanna Bukar mai sakan Brown Agogon Hannunsa na Fata ne,Shima Brown Clour ne,Fuskarsa Tana Fitar da Annuru na musamman kallo Daya zakamai ka Fahimci Lalle Bafullatani ne,Wani Lokacin kuma Sajensa sai ya Rikidar Dashi ya koma maka Sak Balarabe.
Suna Filin Jirgin kafin Su Tashi Yan Office din su Kasim Suka ma sani Waya kan gashi Sun Tashi Ta kaduna Shi kuma yace su Hadu Achan gashi Afilin jirgin Abuja Tanan zai Tashi basu Dauki Lokaci ba around 9 da wani Abu Jirginsu ya lulula Sarararin Samaniya Domin Daurin Auren Safe Ne 11am bayan An Sauko daga Masallacin Jumma"a Ayi Walima bayan Daurin Aure, Karfe 4pm na yammah Jirgin da ya Muktar yayi booking na Amarya da Tawaganta Zai Tashi Zuwa Abuja...
Su ya Muktar Sun Isa Borno ba Dadewa,Domin Waya kadai yayi Daga Babban Headquaters dinsu na nan Maiduguri Aka zo da Motocin Alfarma Aka Daukesu Zuwa Cikin garin Borno,Sun iso ba Jimawa Tawagar yan kaduna Suka Iso Wato Abokan Kasim da Sauran yan"uwa,Suna Zazzaune Aharaban Gidan Bayan Angama gaisuwa Suma barayin Su Yaya Ali Baki ne Ta ko"ina ke Bullowa kama Daga Abokansu da Abokan Aikinsu Da kuma Toffin Abokan Marigayi Bukar Bulama,
Ango kasim Kuwa Ya matsu Yaji Ance an Shafa Fatiha Yadda bakinshi yaki Rufuwa Lokaci Daya,Yana Sanye Cikin Wata Ubansu Farar Shadda Riga da wando Da Babban Riga,Shima aikin Jikin Kayan nashi Baki ne duka Abunda ke Jikinsa Bakake ne kama daga Hula agogo,Takalmi Kallon Farko zakamai ka Fahimci Shine Ango Duba da yadda Duka Fararan Hakoransa Ke Waje Zumudi yake Tayi zai Shiga Cikin gida yaga Aneesa Abokansa na Rikesa Suna mai Shakiyanci Tun Daran Jiya bai Bar Aneesa Ta wani Runtsa ba Suna ta waya yau da Safe ma Tun da Suka iso yake damunta da Kira Har Tagaji ta Daina amsa Kiransa Domin Ita gabadaya Yau Din da Faduwar Gaba tatashi Zuciyarta Tsinke Jikinta Duk baya mata Dadi Tana chan Bedroom din ya Ali Tana kwance kamar Zazzabi ne ya Rufeta Su kuma Su B.kaita Suna Tsakar gida Ana Ta Hada Hada Abincin yan Daurin Auren da Su Anty Rahila Su suka Tsaya Akan komai ya kammallah.
Sun Sauka a Filin Jirgin Maiduguri,Karfe 10am da wani Abu Daganan Tashan Mota Suka Dauka Zuwa cikin garin Borno Bello yana Ta Uban Duba Agogo kada su Makara Adaura Auren basu isa ba Sani kuwa Daya daga Cikin Abokan Aikinsu ya kira ya Tura musu Address din gidan su Aneesa sun Iso Kofar gidan 11am saura Minti goma Sha Biyar Ajiyar Zuciya Bello ya Sauke Bayan Sun Sauka Daga Motar da Suka Hawo Daga Aiport sani ya sallameshi Bello Kofar gidan Yake bi da kallo Lokaci Daya da Haraban Gidan,Domin get din Gidan yana Wangale ne ga Mutane nan Zazzaune Lokaci kawai Ake Jira Bello bai Taba Zuwa Borno ba Wannan shine karon Shi na Farko Watakila kuma Zuwan Nashi bazai ma Mutane dadama Dadi ba.
Cikin Haraban gidan Suka Shiga Sani ne ya nufi Wajen Abokan Aikinsu Dake Tare da Kasim Ango Suna gaisawa Kallon Kallon Akayi Tsakanin Kasim da Bello Lokaci Daya Kasim yaji gabansa ya Fadi Dayaga Bellon Wanda baisan Dalili ba,shiko Bello kallonsa yake kai Tsaye Cike da Tsana ammh Fuskarsa bata Nuna ba Takowa yake Cikin Izzarsa Zuwa garesu su kansu Tsayawa Sukayi Suna kallon Tsabar kyau da Zati Lokaci Daya Har ya kariso Garesu yana basu Hannu da Ido Suke Binsa Sai da yazo kan Kasim kana ya Dauke Hannunshi yayi kamar bai Ganshi ba,Kallonsa Sani yayi yana Dan Zungurinsa Ammh Bello yayi Fuska sai ma Komawa Dayayi gefe ya Fito da Wayarsa Hankalinsa kwance yana latsawa Lokaci Daya kuma yana Bin Mutanen Dake Haraban Wajen da kallo..
Cikin Mamaki kasim ya kalli Sani yana Fadin"Sani Dama kasan Bello ne..? Batare da Sani yabama Mganar Kasim Muhimmamci ba yace"Eh Tare mukayi universiy of Ibadan Mun zauna Daki Daya He is My Friend Ashe ma Dan"uwanka ne na Biya ta Wajensa Jiya yake cemin Shima yau din zai zo nan Daurin aure.."
ajiyar Zuciya kasim ya Sauke kafin yace"Umh."Daga Haka shima ya Dauke kai ammh Azahirin gaskiya Jikinsa Yayi Sanyi Wanda baisan Dalili ba.
Su Abba kabiru da su Ya muktar Suna Daga Cikin Falon cikin gida wanda keda kofa ta Waje So basu san Bello yazo ba Yaya Ali ne ya Fito Daga Cikin Gida yana Saba Babbar Rigansa Bello Dake latsa Waya ya Hangonsa da hanzari ya Nufeshi Domin Sun Taba Haduwa sau biyu Lokacin Dayazo Har Abuja yadaki Aneesa yana gidan Lokacin,kuma ko ba Haka ba Kana kallonsa kaga Aneesa Agareshi Domin Suna Diban kama yana Isa Kusa Dashi ya Bashi Hannu lokaci Daya yana mai sallama.
Mikamai hannu ya Ali yayi yana Kallonsa Cikin Mirmishi da mamaki yake Fadin"Ah...Wanake gani Kamar Muhammed Bello..? Cikin Dariya Bello yace"Nine ya Ali ya gida..? Yace"Lafiya lau kamar kwanaki naji Rahila na Fadin baka kasar ko? Bello ya gyada kai yana Fadin"Eh Ya Ali Shekaran Jiya na Dawo kasar.."Ya Ali na Rike da Hannunsa yake Fadin"Masha Allah..Allah sama Abunda Aka je nema albarka.."Bello ya Rankwafa yana Fadin"Ameen Ameen Nagode.."
Ya Ali yaja Hannunsa yana Fadin"Shigo Ciki iyayan naka na nan Ciki ."Saurin Tsayawa yayi yana Fadin"a"ah ya Ali kafin mu Shiga Ciki Akwai Wata mgana Da na Danikeso kabani Dama mu Shiga Ciki Ayita kafin Adaura Auran.."Jim ya Ali yayi yana kallonsa kafin yace"Wata mgana kenan Bello? Ina Fatan Lafiya ko..?kada kai Bello yayi yana Fadin"Lafiya ba lafiya ba..In kabani Izini yanzu zan Kira Wanda muka zo Tare sai Mu Shiga Ciki.."ya Ali da mganar ta mai Wani iri Yayi Jim kafin ya kada kai yace"To Shikenan ba Damuwa.."Yafada Lokaci Daya yana Boye Tsoron Daya Shiga Ranshi
Cikin Hanzari Bello ya ciro Wayarsa