Showing 1 words to 3000 words out of 80273 words
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Da sunan Allah me rahama mai jinqai, salati da daukaka su tabbata ga manzon tsira annabi
Muhammad(s.a.w)_ _Tsarki ya tabbata ga ubangijin da mulkinsa bashi da iyaka, Wanda
jinqansa da rahamar sa suka cika ko ina_
_Ya Allah yanda na fara wannan rubutun da ikon ka, ya Allah ka bani ikon saukeshi lfy_
_Page: 1_
_________Kwance take a kan madaidaicin gadon dake d'akin, duk tabi ta barbaza takardunta
na makaranta kan gadon, sanye take cikin wasu riga da wando blue and white, wanda sukai
matik'ar karb'an jikinta kasancewarta fara, gashin kanta a d'aure yake cikin wani blue ribom
wanda ya k'ara fito da ainihin kalar bak'in gashin dake kanta, wani lumsashshen gashi ne ya
sakko daga gaban goshinta ya kwanta wanda hakan ya k'arawa halittar fuskarta kyau, kallo
d'aya zakayi mata ka fahimci tayi nisa sosai a cikin karatun nata sbda jarrabar dazasuyi ta
Waec,
Qofar dakin aka shiga kwanjwasawa cikin nutsuwa, A hankali ta dago fararen idanunta masu
matik'ar haske gamida wani irin maik'o a cikinsa, zubawa k'ofar idanu tayi cike da zak'uwar sin
ganin wanda ke knocking din,
Rumana ce ta shigo dakin da sallama fiskarta dauke da murmushi, A nitse ta k'araso bakin
gadon ta zauna tareda binta da wani irin kallon wanda yafi kamada na mamaki tace, "Umaisa
kardai kice min har yanzu karatunnan kikeyi?" Tayi maganar cike da mamaki,
Yarinyar da aka kira da Umaisa ta dago fararen idanunta, tareda yi mata wani irin kallo tace,
"gashi kuwa kin gani,"
Maida kanta k'asa ta sakeyi sannan tayi murmushi tace, "I don't won't fall my exam that's why
nake karatun sosai," kin sani sanin kanki cewar a rayuwa ta na tsani fad'uwa, nasara kawai na
sani kuma itace fatana, ta k'are maganar tana yatsina fuska tareda cuno d'an k'aramin cute pink
lips dinta,
Dariya sosai Rumana tayi sannan tace, " to naji sarkin son karatu" , "idan kin ga dama Dan
Allah ki zama jikar manga pak.
dariya sukayi gaba daya
Sannan Rumana ta kalli k'anwar nata tace, "yauwa kinga ma ni wllh har na manta ma da
abinda ya kawoni gurinki wllh,"
Da kulawa Umaisa take kallonta sbda jin abinda Rumanan tace,
Murmushi Rumanan tayi sabida ganin ynda Umaisan take kallonta sekace bata tab'a ganinta ba
sannan tace, " yauwa dama yaya khabeer ne yace in kira masa ke"
Gaban ta ne yay wani irin fad'uwa a lokaci guda sbda jin sunan Wanda Rumana ta Ambata!!!
cike da karayar zuciya kamar zatayi kuka ta kalli Rumanan tace, " Dan Allah da gaske kike
Ruman?"
Cike da jin haushi Rumana take kalonta sannan tace, "ai kinsan na saba yi miki qarya, 'yar renin
hankali kawai," tana kaiwa nan ta fice daga dakin gaba daya, tana k'unshe dariyata,
Jikin Umaisa ne yay bala'in sanyi sbda tasan halin yayan nasu Sam baya wasa dasu
musamman ma ita,
A hankaki ta fara k'ok'arin Mik'ewa tareda sakko da santala santalan fararen k'afafunta k'asa,
Zarazara hannunta tasa ta dauki wani Dan k'aramin mayafi ta rufe kanta dashi sannan ta
sinkuya ta jawo wani tattausan takalmi me yalwar gashi a jijinsa, a nitse ta zira kyakkyawar
k'afarta ma'abociyar dogayen yatsu a ciki,
Masha Allah kawai na iya firtawa sabida ganin cikar zatin da Umaisa take dashi,
Fita tayi tareda Jan k'ofar dakin nata ta rufe, sannan ta fara takawa a sannu a hankali sekace
wata me tausayin k'asa,
Wani siririn corridor naga ta biyo, sannan ta fito wani katafaren makeken parlor me azabar kyau
gamida tsari, sbda yanda aka k'awata shi da mata'ulhayat na duniya,
A hankali take tafiya kamar wata wahainiya sabida tsari, har ta samu nasarar k'arasawa bakin
k'ofar da zata sadata da side din yayan nasu, Da sallama ta tura k'ofar dakin tareda kutsa kai
ciki,
Parlor ne me girma wanda aka k'awatashi da wasu rantsatsun Royal chiars yan gaske masu
launin ruwan madara ganida yarfen ruwan zinare, komai na perlourn ya dace da inda aka
ajiyeshi,
K'ofar bedroom din ta zubawa idanu tana jiran taji fitowar sa amma shiru babu alamarsa, Shirun
da taji yayi yawa ne, yasa ta mik'e ta nufi bedroom din zuciyarta na dukan uku uku, Da sallama
ta shiga had'e da tura k'ofar bedroom din,
A hankali ya amsa sallamar ta yanda ba lallai mutum yaji ba indai ba bakinsa kake kallo ba,
Zaune yake akan makeken gadon sa k'irar Italian,
Sanye yake da wata farar Riga armless, se wani black jeans dake jikinsa, Ya Khabeer irin
black beauty dinnan ne, fiskarsa a d'auke take da dogo hanci da kuma madaidaicin baki Wanda
yayi daidai da tsarin halittar fiskarsa,
idanunsa Fararene sosai Wanda launin k'wayar idanunsa ta kasance golden colour, dogo ne
sosai ma'abocin kwarjini da kuma haiba, kallo d'aya zakayi masa ka fahimci Shi ba ma'abocin
yawan magana bane,
A zaune yake ya mik'e dogayen k'afafunsa a kan wani Dan k'aramin table na glass, gefansa
kuma laptop ce wadda ya maida dukkan hankalin sa akan laptop din, da 'alama wani Abu me
mahimmanci yakeyi a ciki,
Shigowa tayi tareda dan, rissinawa tace, "ya khabeer, sanu da aiki
Dagowa yayi tareda zuba mata manyan idanunsa,
jikinta ne ya fara rawa a lokaci guda,
"Tsawa ya daka mata, nan da nan ta ida firgicewa, sbda a rayuwar Umaisa ta tsani tsawa,
fashewa tayi da kuka tareda toshe bakinta da d'aya hannun nata,
Cikin daga murya ya fara magana yace , "Umaisa Ashe baki da hankali Dan k'aniyan ki,? yau
kwannan ki nawa rabonki da islamiya?
cikin sark'ewar murya tace "wllh..da...dama"
A fusace yace, " rufe min baki kafin na tashi na ballaki a nan gurin, nonsense kawai"
"Wllh kinji na rantse, dik ranar da na kumaji ance bakije islamiya ba, wllh sena karyaki"
Cikin kuka tace, " I'm so sorry ya khabeer insha Allah baran k'ara ba wllh!!
A taqaice yace, "is better for you,
And This is the last warning da zan sake yi miki, a kan makaranta," yana kaiwa nan ya Nuna
mata hanya yace get out !,
Da gudu ta fita tana kuka, D'akinta ta koma tareda fad'awa kan mdaidaicin gadon ta, sannan ta
saki wani irin kuka me cin rai, Seda tayi kukan me isarta sannan tayi shiru sbda ciwon da taji
kanta ya fara, mik'ewa tayi taje ta kulle k'ofar d'akin da key sannan ta shige toilet danyin wanka,
Bata dauki lokaci me tsawo ba ta fito sbda wani irin ciwon da kanta yake mata , a daddafe ta
daura alwalar sallar la'asar sannan ta fito,
Wata doguwar riga maroon me k'aramin hannu ta dakko ta sanya a jikinta, sannan tasa
hijjabinta ta fara gabatar da sallar la'sar din,
Ta jima kafin ta idar , bayan ta idar ne ta shiga gabatar da tasbihinta data sabayi ko wace rana,
Tana kammalawa ta mik'e ta hau kan gadon ta, lamo tayi sannan wasu sababbin hawaye suka
shiga bin kumatun ta,
Har akayi magrib bata fito ba, kasancewar Ummien su yaya Khabeer ce da girki, shiyasa babu
Wanda ya nemi inda take,
Har Abba ya dawo babu Wanda yabi takan Umaisa hakan ne yasa ta k'ara fashewa da wani
sabon kukan takaicin, abinda ya Khabeer din yayi mata, har akayi sallar ishsha bata fitoba,
Seda kowa ya hallara a kan dining, tin daga kan yaya khabeer da yay Usman har zuwa kan
yaya Farouq kowa yana nan amma banda Umaisa,
Mamin Umaisa ce ta sakko sanye cikin wani dakakken lace maroon colour, wanda aka yalwata
dinkin da fararen christel stons masu matk'ar kyau gamida daukar idanu, hannunta sanye cikin
wani murd'add'en zobe na zinare, inada hannunta na dama yake Rik'e dana Ameeyra wadda
takasance k'anwa ga Umaisa,
A nitse take sakkowa daga kan step din tamkar wata wahainiya sabida k'asaita harta iso daining
aria din,
Da fara'arta suka gaisa da Ummie da kuma mamah, sannan su Khabeer suka gaisheta suma
cike da girmamawa,
Ba'a dad'e da zuwan Aunty amarya ba Abba ya k'ara so falon shima,
Cikeda kulawa ya dubi kowa sannan suka Dan taba wasa da dariya kamar yanda ya sabayi da
iyalan nasa kullum, sannan Ummie ta fara saving kowa dake dining din,
Kujerar da Umaisa take zama Abba ya kallah sannan ya ajiye spoon din dayake k'ok'arin kaiwa
bakinsa yace, "ina Mamaba ta shiga ne haka ban ganta ba?
Rumana ce tayi sauri tace, " Abba tana dakinta, tin dazu bata fito ba har yanzu ina zaton ko
bacci takeyi ne shiyasa, ta k'are maganar tana kallonsa,
Harararta Abbah yayi sannan ya kalli Khabeer dake shirin fara cin abinci yace" son jeka
dubamin lfyr Mamana na, sabida banaso ta dinga zama ita kadai a daki haka,
Wani malolon takaici ne ya tsayawa Khabeer a wuya, dan haka dak'yar ya iya hadiye abincin
dake bakinsa sabida takaici, amma babu yanda ya iya dolansa yaje yazo da ita kamar yanda
Abba yace masa,
Yana mik'ewa Aunty Amarya tace, "Haba Alhaji don Allah, senake ganin Umaisa fa ba yarinya
bace balle ace se'an kirata sannan zata fito taci abinci , "idan taji yunwa ai dole ne ta fito ta nemi
abinda zata saka a cikinta,"
Wani kallo Abba ya dinga bin Mamie dashi hakan ne yasa tayi shiru taci gaba da cin abincin ta
ba tareda ta k'arasa abinda tayi niyar fad'ar ba,
Ganin hakan ne yasa Khabeer ya nufi nakin Umaisa zuciyarsa na masa wani irin tafarfasa,
Knocking din k'ofar ya shigayi,
tanaji amma tak'i budewa , hakanne ya k'ara fisatashi, cikin d'aga murya yace, "zaki bude k'ofar
ko sena shigo na karya ki sannan zaki bude"?
Da wani irin gudu ta diro daga kan gadon har tana tin tibe sabda tsoro, tabbas koda ace bata
nunfashi taji muryar nan seta shaida mamallakinta balle kuma yanzu da take tareda
numfashinta, Budewa tayi jikinta banda rawa babu abinda yakeyi, buguda k'ari kuma ga wani
irin recing da heart dinta keyi,
Da gudu ta juya zatayi baya sabida ganin irin yanayin dake fuskar yayan nata, Cikin wani irin
mugun zafin nama yasa dogon hannunsa ya wani irin fuzgota sabida haushinta dayakeji,
tsayawa yayi cak sbda wani irin zafin dayaji jikinta yayi a lokaci guda,
Da wata irin kakkausar murya ya kalleta yace, " are you sick?"
D'aga masa kai tayi a hankali tace , "yeah"
Cikeda kulawa yace, " Kinsha magani ne?"
Girgiza masa kai tayi, idanunta a cike tab da k'walla alamar 'a'a
A hankali ya rage sautun muryarsa alamar rarrashi yace,, "meyasa bakijin magana ne ke a
Raywarki?"Kinga dazu ma kece kika sa nayi miki fada sbda bakisan zuwa makaran ta," kinsani
kema bazamu taba shiryawa dake ba muddin bazaki canza wannan dabi'ar taki ba", ya fada
yana dungure mata kai,
Janta yayi har suka k'arasa parlon batareda k'ara cewa komai ba, yana zuwa yace, "Abba
gatanan,"
Hannu Abba ya mik'a mata alamar tazo gareshi, da gudu ta k'arasa inda yake sannan ta fada
jikinsa tareda sakin wani irin kuka,
Cikin sigar tsokana Rumana tace, "babbar magana yaufa shagwabar ta motsa", ta fad'a tana
k'unshe dariyar datakeyi sabida Abbah,
"hararar ta Mamah tayi sannan ta dauke kanta tareda Jan tsaki, Sabida yanda lamarin Umaisa
yake matiqar bata haushi, amma babu dama tayi magana yanzu Abba seya rufeta da fada,
Sam Abba baya son lefin Umaisa kokad'an shiyasa take zuba iskancin shagwabarta San ranta ,
Ya Usman ne yayi k'arfin halin daka mata tsawa,
shiyasa ta hadiye kukan da takeyi babu shiri,
*WAI WAYE ABBAH NE*
Alhaji Mahmoud Muhammad shine cikakken sunan sa ,Shi haifaffen garin Gano ne, wadda take
daya daga cikin k'auyikan kano, shikad'ai iyayensa suka haifa, dan haka suka d'auki son
duniya suka d'ora masa, duk inda mahaifinsa malam muhammadu zashi to da Abba yake
tafiya, tun mutane k'auyen suna gulmarsa har suka gaji suka dena, lokacin da wayewar ilimin
boko ta shiga garin na Gano dayawa iyaye sun nuna rashin amincewarsu dashi, dan haka suka
hana yaransu yi,
Lokacin da Malam Muhammadu ya samu wannan labrin murmushi kawai yayi, sannan ya kalli
me d'akinsa *BINTA* wacce Abba yake kiranta da suna *Gwaggo* yace, " Binta nifa jikina yana
bani cewar nan bada jimawaba wannan al'amarin da turawannan sukazo dashi nan gaba ze iya
zama me amfani a rayuwar mu, "dan haka zan sanya *mamuda* (Abba) ya dinga zuwa,
Shiru gwaggo tayi kamar me tinanin wani abu sannan ta kalli mai gidan nata tace, " nidai malam
bank'i ta naka ba, ammafa magana ta gaskiya idan naga d'abi'ar mamuda ta sauya tofa ze dena
zuwa, sabida ni baza'a koyawa yarona yahudanci ba.!
Murmushi kawai malm Muhammadu yayi batareda ya sake cewa komai ba,
washe gari kuwa da sanyin safiya mlm ya kama hannun Mahmoud ya kaishi makarantar Boko,
wannan shine mafarin karatunsa, kullum idan ya dawo yana bitar karatunsa a gida, se Gwaggo
tayita fad'a kamar ta ari baki, wai ya cika mata kunne da sunan yahudawa mak'iya Allah, shidai
malam sedai kawai yayi murmushi yana kallonsu
A haka Mahmoud ya samu nasarar kammala karatunsa tun daga kan primarynsa har zuwa
scondry,
daga nan kuma yanwuce K.S.U.T dake Wudil, inda ya yayi dgree dinsa na farko akan abinda ya
shafi kasuwanci, haka ya dinga lallab'a rayuwarsa har ya samu nasarar fara aiki a *FEDIRAL
WORKS OF HOUSING* dake garin abuja,
Dukda cewar Alhaji Mahmoud muhammad girman K'auye ne sam hakan besa mahaifinsa ya
matsa masa kan seyayi auren wuri ba, har seda ya himmata dan ra'ayin kansa sannan sukayi
aure da matarsa ta farko *Hadiza,* wacce itace ta kasance mahaifiya ga *Khabeer* da kuma
*Usman,* suna kiranta da Suna *Ummie*
bayan aurensa da Hadiza Abba be d'au wani lokaci me tsaho a tare da ita ba ya sake auren
matarsa ta biyu wato *Marym,* wadda itace ta kasance mahaifiya ga *Umar Farooq* da kuma
*Rumana,* suna kiranta da *Mamah,* tundaga lokacin Abba be sake k'ara aure ba seda ya
d'auki lokaci me d'an tsaho kafin ya sake Auren matarsa ta uku wato *Badi'atou,* wadda itace
mahaifiya ga *Umaisa* da kuma *Ameerah,* inda su Khabeer suke kiranta da *Aunty Amarya*
Sabanin su Umaisa da suke kiranta da suna Mamie,
Bayan haihuwar Ameerah Allah yayiwa mahaifin Abba malam muhammadu rasuwa, sosai Abba
yaji mutuwar mahaifin nasa, dan haka yayi kuka harya gode Allah, gwaggo ma tayi kuka
tamkar ranta ze fita, daga k'arshe dai suka hak'ura suka dinga binsa da addu'ah.
Bayan wani lokci Abba ya nuna yana son tafiya da Gwaggo Abuja amma fir tak'i yarda wai
bazata tafi tabar garinta na haihuwa ba, badan Abba yaso ba haka dan dole ya barta a nan
d'in, sedai duk abinda takeso yanayi mata Shi, haka kuma idan anyi hutu yakan sa a kai mata
yaransa gurin mahaifiyar tasa.
Kaf cikin yaran Alhaji Mahmoud Muhammad yafi son Umaisa fiyeda kowa, sabida sunan
gwaggonsa ne da ita Fatimah, shiyasa suke kiranta da Umaisa
Dan haka baya son bacin ranta ko kad'an, kuma baya sassautawa dik Wanda ya tab'a masa ita
koda kuwa waye shi, Shiyasa shagwabarta tayi yawa sosai, ta yanda kowa ma yi masa takeyi ,
Dukda yawan shagwabarta amma Sam hakan besa ta kasance me raina mutane ba, tana da
respect sosai fiyeda duk zaton me karatu, bugu da k'ari kuma gata da son mutane, Itadai kawai
ka barta da yawan shagwabar ta,
D'abi'ar Shagwabar ce ma tasa yayyen ta maza suke yawan jin haushinta, gata da shegen
nacin kuka,
Abindai bekai ayi masa kuka ba a gurinta abin kuka ne, shiyasa suke yawan fad'a da yayyen
nata idan aka cire yaya Usman, shikam yana son 'yar k'anwar tasa sosai, haka kuma yana ji da
ita,
Wani irin mugun kallo Abba ya jefa masa Dan haka ya hadiye bacin ransa cikin sauri, sabida
gudun bacin ran Abban nasu,
Sbda takaici Khabeer mik'ewa yayi yabar falon gaba daya sbda idan yaci gaba da zama a gurin
to tabbas fa ransa ne zeta baci a banza,
Comment
Nd
Share
*Zm muhmd (ChuBaDo)*
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:2_
________Daki ya koma a ransa yana mamakin hali irin na Umaisa, wani siririn tsaki yaja tareda
firzar da wata iska me zafi, a hankali ya firta cewar dole ne inyi maganin yarinyar nan tin kafin
lamarin ta ya ida lalacewa, Laptop dinsa ya jawo ya cigaba da aiyukan dake gaban sa,
Washe gari da sassafe Umaisa ta tashi kasancewar mamien tace da girki kuma gashi zataje
makaranta, A nitse ta mik'e ta nufi kitchen Dan ta temakawa Mamien da wani aikin kamar
yanda ta saba, da sallama ta shiga kitchen D'in, A tsaye