Showing 36001 words to 39000 words out of 80273 words
batareda ya fito ba, tun yana sa ran ganinta harya
fitar da Rai, dan hka ya juya kan motar ya fara tafiya, kamar ance masa ya juya ya ganta ta
tsaya a gurin wani dattijo tana siyan a gwaluma, tsaida motar yayi tareda zuba mata manyan
idanunsa yana kallonta, a nitse ya bud'e murfin motar tareda nufar gurin cikin takunsa na
k'asaita, harya k'arasa gurin bata lura dashi ba, sabida yanda duk tabi ta maida hankalinta akan
agwalumar, ledar agwalumar da mutumin ya mik'a mata ta karba tareda mik'a masa kudin sa,
ledar Maheer ya rik'e da sauri, hakanne ya bata damar d'ago manyan idanunta don ganin
waye, ja da baya tayi tareda sakin ledar agwalumar a k'asa, nan da nan idanunta suka ciko da
k'walla, juyawa tayi zatabar wajen, dan haka da sauri ya tareta tareda zuba mata tsimammun
idanunsa,
Tsayawa tayi chak tana kallonsa lokaci guda hawayen suka samu nasarar zubo mota, da k'yar
ta iya bud'e baki tace "meyasa kake bibiyata ne?
"Abinda kayi min kwanakin baya isheka ba shine yanzuma ka sake biyo ni har nan? Wai
meyasa kake bibiyar Rayuwata ne don Allah? da sauri ya matso kusada ita yace" ni kaina
bansan dalilin dayasa nake bibiyarki ba a Rayuwata, illa kawai abinda nakeji a tareda ke wanda
har yanzu ni kaina na kasa fahimtar ma'anarsa, wllh tun ranar dana fara ganinki kika kasance a
tunanina , ada nayi tunanin cewar abinda kikayimin a had'uwata dake na farko ne yasa bakejin
haushinki, sedaga baya na fahimci cewar ina matik'ar Sonki Umaisa, nikaina ban tab'a zaton
zan tsinci kaina a soyayyar wata 'ya mace ba, amma se gashi Qaddarah ta Riga fata!!!.
Tunda ya fara magana take kalonsa sabida tsabar firgitar datayi da kalamansa, lokaci guda
zuciyarta da jikiyoyin jinin dake gudana a sassan jikinta suka tsaya cak da aiki, sabida tunda
take a Rayuwarta namiji betab'a zaiyana mata kalamai masu tasiri irin haka ba, hawayen
idanunta ne suka tsananta zubowa sabida bazata iya jure hakan ba, dak'yar ta iya bud'e bakinta
wanda yayi mata nauyi tace "wllh duk abinda ka fad'a ba gaskiya bane, sabida duk duniyar nan
banida mak'iyin da baya k'aunata sama dakai, har yanzu k'iyayya nake gani a k'wayar idanunka
ba soyayyah ba!! Inda ace kana sona bazaka tab'a zama silar zubar hawayena ba, don girman
Allah na rok'eka ka fita a Rayuwata ka dena bibiyata.!!! Tana kaiwa nan ta juya da sauri tabar
gurin
Kasa motsawa yayi daga gurin tamkar gunkin da aka dasashi a gurin, kallo d'aya zakayi masa
ka fahimci tsantsar tashin hankalin dayake ciki sanadin kalamanta, ganin da yayi cewar wankin
hula ze kaishi ga dare ne yasa ya fad'a motarsa yabar unguwar zuciyarsa nayi masa wani irin
zafi.
*_ADAMAWA (YOLA STATE)_*
Cikin ikon Allah Abdul ya sauka Yolah lfy, yana sauka be b'ata lokaci ba ya nufi Family hause
dinsu dake cikin yola, sosai sukai farin ciki da ganin Abdul d'in har hakan ya gagara b'oyuwa a
fuskokinsu, seda suka sha hira da matan baffaninsa sannan ya nufi d'akin Baba Ma'u wadda ta
kasance yayar mahaifinsa wadda suke kiranta da (DADAJI).
Sosai Dadaji taji dad'in zuwan Abdul, nan ta shiga tambayarsa Maheer, Abdul be boye mata
komaiba akan abinda ya faru tsakanin Maheer din da Dady, sosai hankalinta ya tashi akan
al'amarin don haka tace "Amma Nasiru ya tabka babban kuskure a rayuwarsa daya biyewa
son zuciyarsa, dukda cewar idan akai duba da irin labarin daka bani za'a fahimci cewar ba laifin
Nasiru bane harda sa hannu a cikin lamarin, don haka karka damu insha Allahu zamu dage
wajen gayawa Allah.
Wayarta ta d'akko sannan ta shiga kiran wayar Baffah iyah, yana d'auka ta sanar dashi cewar
duk abinda yake faruwa da d'an uwan nasu, sannan tace dashi " ka kira Baffa Umaru shima ka
sanar dashi halin da ake ciki a gameda Rashin lafiyar Nasirun.
Kan kace me tuni zancen ya karad'e kunnuwan mazan dake familyn, suna idar da sallar
Azarahar aka shiga meeting akan matsalar Dadyn, a nan Baffa gidad'o yake sanar dasu cewar
"yaje kaduna kwanaki amma Dady yasa mai gadi ya hanashi shiga gidan, tun daga lokacin ya
fahimci a kwai abinda ke damun d'an uwan nasu, sabida kaf cikinsu Dady yafisu son zumuci.
A nan suka yanke shawarar zasuje su taho dashi nan yola domin a nema masa lfy, haka kuwa
akayi a Ranar sukayi boking flight da Abdul da kuma Baffa gid'ad'o da Baffa Umaru suka nufi
garin na Kaduna.
Cikin ikon Allah da yardarsa suka sauka lfy, nan Abdul ya kwashesu zuwa gidansu dake
unguwar Rimi, cikin mintuna kad'an suka iso k'ofar makeken gidan nasu me cikeda tarin
mata'ul Hayat na duniya, horne yayi sannan mai gadi ya wangale musu k'ofa suka kunna kai
zuwa ciki, a nitse yayi perking motar sannan suka fito cikin shigarsu ta alfarma, kallo d'aya
zakayi musu ka fahimci daga tsatson fulanin asali suka fito,
Direct part din Dady suka nufa, a hankali ya zaro mukullin dake aljihunsa kasancewar yanada
wani extra bayan wanda yabawa Sulaiman ya fara k'ok'arin bud'e kofar, tunkafin ya murd'a keyn
k'ofar ta bud'e dan hka gabansa yay wata irin fad'uwa!!!!! A rude ya tura k'ofar ya shiga da
sauri, Direct bedroom din Dadyn ya nufa, nan ma k'ofar a bud'e take, a tsorace ya maida
kallonsa kan makeken gadon dake d'akin, babu kowa akai sema yamutsa gadon da akayi,
wanda ya bashi tabbacin cewar seda akayi kokawa da Dady kafin a d'aukeshi, zubewa yayi a
k'asan kafet din dake shimfid'e a tsakiyar d'akin, a nan yaga drip din da aka sakawa Dadyn kafin
ya tafi yolah an jefar dashi a Qasa da alama ma fisge masa shi a kai da k'arfin tsiya duba da rin
jinin dake jikin allurar da kuma kafet d'in, wata Razananniyar k'ara ya saki tareda kiran suna
Allah..! Se'a lokacin su Baffa Gid'ad'o suka iso cikin d'aki.
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
*_This page is 4 you my sweetheart Shahidah Isah Abduí ¾íµ°, Qanwata ta kainah, Allah yayiwa
rayuwarki albarka_*
_Page:25_
___________í ½í³– cikeda tashin hankali Abdul yake nuna musu gadon yana fad'in "shikenan
suna tafi da Dadyn mu baffah gid'ad'o! Gaba d'ayansu kallo d'aya zakayi musu ka fahimci irin
zallar tashin hankalin da suke ciki, babu abinda suke fad'a se innanillahi'wa'inna'ilaihirraji'un!!!
Baffa ummaru ne yayi k'arfin halin cewa " gaskiya be kamata muzana muna b'ata lokaci ba, ya
kamata mu sanar da jami'an tsaro halinda ake ciki sabida a tari abin da wuri.
Wata zabgegiyar Toyoya benza bak'a wuluk na hanga bisa babban titin garin na kaduna, gaba
d'aya ilahirin glasan motar a lullub'e suke da tintake, gudu kawai suke zubawa na fitar hankali
har suka samu nasarar d'auke hanyar birnin taraiya, seda sukai tafiya me nisan gaske sannan
suka yi perking a wani k'aramin k'auye wanda yake dab da garin TAFA, cikin mintunan da
bazasu gaza 15 ba sega hajiya murjah ta fito daga cikin wata hatsabibiyar 4matic C350, wadda
ta kasance fara tass da ita, sanye take cikin wani dakakken leshi milk colour, se wani uban
glass data kafa a fuskarta wanda ya cinye ilahirin rabin fuskarta sabida girmansa, a hankali take
takawa cikin takun isa da kuma tak'ama, inda aminiyarta Binta 'yar kwabo ke take mata baya.
A gaggauce Mutanan dake cikin bak'ar motar suka firfito gaba d'ayansu sanye da wasu
manyan riguna bak'ak'e wa'yanda suka k'arawa jikinsu cika da kuma girma, fuskarsu a lullub'e
suke ciki bak'ak'en macks, baka ganin komai face idanunsu wanda ya kasance abin tsoro ga
duk wanda ya kallesu, suna isowa inda take suka sanarda ita sun gama aikin data basu.
Wata uwar dariya Murja ta saki sannan ta basu umarni da su saka matashi a cikin motar ta,
haka kuwa akayi, nanda nan suka kinkimi Dady wanda ya sume tun bayan satonshin da sukayi
suka jefa matashi a mota, seda tayi musu gargad'i sosai kan cewar karsu yarda su koma
Kaduna, sabida tanada tabbacin cewar muddin suka koma tofa jami'an tsaro zasuyi ram dasu,
murmushi Ogansu yayi sannan yace "kinga Hajiya kawai ki sallamemu da kud'ad'en da mukai
alk'awari dake, ba wai ki tsaya kina b'ata mana lokaci ba.
Dariya tayi sannan ta tura Binta 'yar kwabo ta d'akko mata wata jaka wadda ke shak'e da kud'i
ta mik'a musu, suna karb'a suka fad'a cikin motarsu sannan suka figeta da wani mahaukacin
gudu, nan suma su Murja suka fad'a tasu motar suka d'auki hanyar birnin taraiya Abuja, cikeda
kwanciyar hankali gamida nutsuwar zuciya Hajiya Murja take tuk'a motar, inda wani b'angare
na zuciyarta yake a cike taf da farin ciki, wayarta tasa Binta ta d'akko sannan tace " maza ki
kira min lambar Abdul. Zaro ido Binta tayi sannan tace "meyasa zamu kirashi kuma Murja?
Shin waike bakya tsoron abinda ze biyo baya ne?
Tab'e baki Murja tayi sannan tace " kedai anyi sakarya wllh Binta, nima ai ba bisa Radin kaina
nasa aka satomin Alhaji ba, kawai nayi hakan ne bisa shawarar da sabon Manajan companyn
B.N.M.A ya bani, sabida na sanardashi cewar mijina babban mutum ne wanda ya mallaki
millions of Naira's, amma sedai ban haihu dashi ba, duk wasu tarin kadarorin daya mallaka
gab'a d'yara yaransa ya d'ora akan komai, shiyasa duk wasu mahimman abubuwansa baya
sanar dani se 'ya'yansa, to shine ya bani shawarar cewa in tura a sato min Alhaji inyaso daga
baya senayiwa iyalansa barazana aka indai sunaso mahaifinsu yaci gaba da rayuwa to ya zama
dole su kawo min takardun compaynsa na takalma dake garin Abuja, tareda takardun hannun
jarin dasuke dashi a k'asar Tokey.
Yanzu haka zancen danake miki na zuba kud'ad'ena kimanin million 60 a wannan companyn
na B.N.M.A kuma an juyasu harna samu ribar million Ashirin tareda uwar kud'ina, ajiyar zuciya
Binta ta saki sannan tace "yanzu kam na gane kuma nima insha Allah da zarar min k'arasa
inda xamu zan saka nawa hannun jarin a wannan companyn na B.N.M.A. sannan ta fara kiran
wayar Abdul wanda ke zub'e a kan kafet d'in d'akin Dady, se faman rarrashinsa Baffa gidad'o
keyi tareda kwantar masa da hankali. K'arar wayarsa ce tasa perlourn yayi tsit, Baffa gidad'o ne
yayi masa inkiya da hannunsa Alamar ya amsa wayar, dan haka hnnunsa na rawa ya d'aga
wayar tareda sanyata a ansakuwa,
Wata uwar dariya Murja ta saki sannan tace" d'ana ya kake ya mutanan yola? Angaya maka
Murja shashasha ce kamar yanda tunaninka ya baka?
Murmushi ta saki sannan taci gaba da cewa "ina ai salon ya dade da canzawa, da alama kuka
kakeyi sabida b'atan mahaifinka ko? Dariya ta kumayi sannan tace " kiranka nayi in sanar
dakai cewar na rantse da Allah idan kukai yunk'urin sanar da jami'an tsaro kokuma kace zakabi
diddigina wllh kaji na rantse to abakin ran mahaifinka.
Jikinsa ne ya d'au rawa tamkar mazari, dukda irin tafasar da zuciyarsa takeyi hakan be hanashi
bata haquri ba, yana kuka yake fadin "don girman Allah karki cutar da mahaifina, wllh bashida
lfy, a halin yanzu babu abinda yake buk'ata face kulawar likita! Kinga kome kike so ki fad'a
wllh xan baki amma don Allah karki cutar mana da Dadyn mu na rok'e ki plsssss, ya wani ja
pls din kamar ze shid'e.
Kashe wayar tayi tareda sakin wani shaid'anin murmushi,
Kuka Abdul yakeyi bilhaqqi da gaskiya sekace wani k'aramin yaro, dan haka baffan nin nasa
suka shiga aikin rarrashinsa, sosai suma lamarin hajiya Murja ya girgizasu, musamman ma
kashedin datayi kan cewar muddin suka sanar da jami'an tsaro to a bakin Ran Dadyn, shiru
sukayi aka rasa wanda zece k'ala, dukkansu mamakin Rashin imaninta kawai sukeyi, Baffa
Ummaru ne yayi azancin cewa " tunda kunji abinda tace sam be kamata mu shigo da hukuma
cikin wannan babban al'amarin ba, tunda dukanmu muji abinda ta fad'a da kunnuwan mu ba
gaya mana akayi ba, a Rashin imaninta wllh zata iya aikata abinda tace d'in, don haka babu
abinda ya kamata muyi a yanzu face addu'a, sabida babu abinda yafi k'arfin ubangiji.
Haka kuwa akayi dole suka karb'i shawarar da Baffa Ummarun ya kawo sabida itakadai ce
mafita a garesu,
A nitse take tuk'inta zuciyarta fess, dan haka Binta 'yar kwabo ta kalleta tace, Murja, wai a gidan
wa ma zamu sauka ne da wannan mutumin wanda bashida maraba da gawa? Tab'e baki Murja
tayi sannan tace "ni wllh dad'ina dake gaggawa Binta, idan kinyi haquri ai zan sanar dake a inda
zamu sauka, dan haka ki dena damun kanki a gidan manager zamu sauka.
Se wajen bayan sallar ishsha sannan suka isa masaukin su, babu lefi gidan yanada kyau sosai
dukda cewar bashida girma sosai amma hakan baze hanaka ganin kyansa na, nanda nan aka
cika musu daining da abinci kala-kala masu rai da lafiya, seda sukaci suka k'oshi sannan hajiya
Murja ta fara neman layin manager, nan yake sanar mata da cewar baya nan amma da safe ze
dawo, wani kasuwanci companyn su ze gunar na kimanin naira Billion d'aya, kuma za'a samu
riba sosai, nan da nan hajiya Murja tace don Allah itama tanaso ta zuba nata hannun jarin, da
farko da manager yaso yaqi Amincewa, sabida bayason harka da k'ananan kud'i amma ta nace,
don haka yace to shikenan setayi masa transifar din iya dadadin kud'in dazata zuba a cikin
account din companyn, sannan ya shaida mata cewar ze turo motar Asibiti don akai Dady
Hospital sabida idan wani abu ya sameshi tofa duk wani shirinsu ya lalace.
Murmushi tayi sannan tace " karfa ka manta shifa sannan mutum ne, be kamata mukaishi
Asibitin gwamnati ba, shiru manaja yayi tareda nazari akan maganar ta, don haka yace
"shikenan zan kira *SUSHMER INTERNATIONAL HOSPITAL* dake centeral Aria Inyaso semu
kaishi can tunda babban Asibitin kud'i ne ba lallai hankalin mutane yakai kansa ba, sedai ina me
gargad'inki kan cewar da zarar sun tambayeki me yake damunsa ki gaya musu cewar firgita
yayi shine ya suma, daga haka karki k'ara komai, a haka sukayi sallama dashi kan cewar gobe
zata tura masa da kud'in.
Bayan sun kammala wayar da manager, nan ta sanar da Binta duk yanda sukayi dashi. A nan
itama ta tubure kan cewar sedai su tura masa da kudin tare, don wllh bazataci ribar mak'udan
kudi itakad'ai ba, dariya hajiya Murja tayi, sannan tace " kai Binta kedai Allah yayi miki shege
son kud'in tsiya wllh, dariya tayi sannan tace "wazek'i kud'i k'awata?
A haka har motar Asbitin *SHUSMER INTERNATIONAL HOSPITAL* ta iso, cikin mintunan da
bazasu gaza shabiyarba suka kinkimi Dady suka sakashi a motar, kafin su tafi dashi seda suka
tabbatar sun Auna Bp dinsa, a nan suka tabbatar da jininsa ne ya hau nan suka shiga bashi
taimakon gaggawa, cikin mintuna kad'an suka sak'ala masa Drip a hannunsa.
Kukan munafinci Hajiya Murja suka dingayi, hartana kama hannun wata nurse tana cewa " don
Allah sister ki taimaka min, wllh bana so in rasa mijina don Allah!!
Murmushi nurse din tayi mata sannan tace "ki kwnatar da hankalinki Hajiya insha Allahu komai
zeyi daidai, yanzu dai ki koma cikin gida kuyita masa addu'a ze samu sauk'i da yardan Allah,
dak'ar nurse din ta lallab'a Hajiya Murja suka koma cikin gida sannan suka tafi dashi,
kasancewar ba'a buk'atar wani mejinya a asbitin shiyasa basu tafi da kowa ba.
Duk wani taimako da Dady yake buk'ata seda suka bashi shi, a k'ark'ashin kulawar Dr.
Abdullah, sosai ya tsananta binkice akan rashin lafiyar Dadyn, a nan ya tabbatar da cewr a kwai
wata k'waya wadda mara lfiyan yake yawan amfani da ita, hakanne yasa jijiyar dake kai sak'o
zuwa ga k'wak'walwarsa ta samu matsala, wanda hakan yay sanadiyar taruwar jini a cikin
k'ok'on kansa, hakanne yasa Dr. Abdullah ya kira Dr. Khabeer Mahmoud ya sanar dashi halin
da ake ciki, a wannan lokacin khabeer yana zaune a Daining sunayin Deener, gefe guda kuma
Farouq ne se tsokanar Baba yake suna kwasar dariya dashi da Usman, seda Abba yaci ubansu
sannan suka shiga taitayinsu, mik'ewa khabeer yayi da sauri, sannan ya kalli Abba yace " Abba
zan wuce Asitlbitin mu yanzu aikin gaggawa ne ya taso mana, wani mara lfy aka kawo wanda
yake buk'atar surgery cikin gaggawa.
Fatan alkhairi iyayen nasa sukayi masa sannan ya karbi mukullin motar Farouq ya nufi k'ofar
fita daga perlourn, harya kai k'ofar fita Umaisa tace "all d best yaya Golden.
Dak'uwa yayi mata yana murmushi sannan ya fice, a daren ranar aka shiga da Dady tiater,
k'ark'ashin jagorancin Dr. Khabeer Mahmoud Muhammad, cikin ikon Allah da hikimarsa suka
samu nasarar kammala tiatern ba tareda wata matsala ba. Sannan aka turoshi zuwa wani d'aki
na musamman.
Washe gari tun safe su hajiya Murja suka nufi Banki don turawa manager kud'in da sukayi
alk'awari dashi, nan ma batasha wahalaba tatura masa kaf kud'in dake cikin Account d'inta
Million 100, inda Binta kuma ta tura masa million 60, a haka sukabar Bankin zuciyarsu fess,
bayan sun koma gida ne hajiya Murja ta shiga kiran wayar manager, amma kuma bata shiga,
seda ta kirashi sau 6 amma bata sameshi ba, a nan hankalinta ya fara tashi!! k'irjinta ya fara
dukan tara-tara.........
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_