Showing 54001 words to 57000 words out of 80273 words

Chapter 19 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2751

ɗaurin goro da alewa, a nan yake
sanar dani cewar ya bada Aurena ga wani almajirinsa, a ranar nayi kuka kamar Raina ze fita,
Adda Dije kuwa ranar kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha sabida murna, a ranar babana ya kaini
ɗakin mijina, sannan yayi min nasiha sosai tareda gargaɗina kan cewar muddin na kashe
aurena karna kuskura na dawo masa gida, a haka muka rabu da babana ya koma gida nikuma
ya barni a gidana,
A lokacin danayi arba da mijin da Babana ya Auramin na girgiza sosai, sabida ganin tsarin
halittar da Allah yayi masa, bugu da ƙari gashi ɗan gata a sosai, ko kaɗan ɓe ƙyamaceni ba ya
nuna min soyayya da kulawa ta yanda ma bakina baze taɓa iya misaltashi ba. A haka muka
cigaba da Rayuwa dashi cikin Aminci da kuma ƙaunar juna, se'a lokacin na fahimci cewar gata
mahaifina yayi min daya Aura min Bawuro.

Kwatsam Ranar
28/12/1997 a wata Alhamis wadda bazan taɓa mantawa da ita ba a rayuwata, Bawuro yayi
tafiya zuwa wani gari wanda be sanar dani ba, seda ya ƙwashe sati biyu sannan ya dawo, ni
kuma ina ɗauke da tsohon ciki, a wannan ranar Bawuro ya sakeni saki 1 sannan ya Umarceni
dana bar masa gidansa a daren baya son ganina. A ranar kasa kuka nayi sabida tashin
hankali, musamman ma dana tunada maganar mahaifina ta ƙarshe.

wannan dalilin ne yasa na yanke shawarar nayi nisa da garin Adamawa kozan samu kwanciyar
hankalin da bansan ɗanɗanonsa ba. Wannan tafiyar danayi itace ta tazama silar canzawar
akalar Rayuwata harna samu damar shigowa cikin Ahalin na Alhaji Mahmoud muhammad.

Ina cikin tafiya a daren naƙuda ta kamani a kan hanyata ta zuwa jumeta, a nan ne muka haɗu
da mahmoud, ganin dayayi zan iya rasa rayuwata ne yasa ya ɗaukeni yasa a motarsa, be dire
ko ina dani ba se a wani babban asibiti dake cikin jumeta, ban wani sha wahalaba Allah ya
saukeni lfy na haifi ɗiya mace, seda na kwashe kwana 7a Asbiti sannan aka sallameni, dukda
hakan mahmoud betaɓa gazawa dani ba hakama abinda na haifa, bayan ya kaini gidansa ne ya
raɗawa yarinyar suna Fatimah yakeyi mata laƙabi da Umaisa.

Duk wata ɗawainiya da gata wanda ɗa ya kamata ya samu daga gurin ubansa to umaisa ta
samu a gurin Alhaji mahmoud, bayan nayi arba'in ne ya nuna yana son Aurena, batareda
tunanin komai ba na amince na Aureshi,

Bayan ya kamala aikin daya kaishi yola ya ɗaukoni ɓe dire a ko ina dani ba se garin gano, a
nan ya gabatar dani ga mahaifiyarsa wato Baba, a matsayin matar daya aura batareda sanita
ba, Mamie ta faɗa yayin da take kallon baba da jajayen idanunta waƴanda suka rine sabida
kukan data gurza, shiru baba tayi tana kallonta sannan mamie ta cigaba da cewa "bamusha
wahala wajen shawo kan Baba ba musamman ma dataji anyi mata takwara, kwanan mu biyu a
Gano muka dawo abuja, kuma baku nuna ƙyama a gareni ba kasancewar Alhaji yafi ƙarfin
gidansa, wannan shine ainihin gaskiyar labarin da muka daɗe muna ɓoyewa nidashi, amma
magana ta gaskiya itace akwai Aurataiya a tsakanin khabeer da kuma Umaisa.! Ta ƙare
maganar tana wani irin kuka me ban tausayi.

_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:36_

___________ gabaɗaya ahalin babu wanda be girgiza ba dajin wannan batu, Usman da
Frouq kuwa daskarewa sukai a zaune saɓanin khabeer dayasan komai, shiru perlourn ya ɗauka
na ɗan wani lokaci sannan Baban Gano ta fara magana kamar haka "haƙiƙa Allah mai hikima
ne akan dukkan lamarinsa, duba da irin abubuwan da suka faru a tsakanin Mahmuda da kuma
Badi'atou, dukkan wani me hankali da tunani dolene ya fahimci cewar akwai abinda Allah ya
ɓoye a cikin wannan babban al'amari wanda na tabbata badan soyayya ta bijiro a tsakanin

kabiru da Fatsima ba da wannan sirrin be baiyana ba.

Don haka babu abinda zamuce sedai muyi godiya ga Allah dayasa hakan ta kasance da wuri,
duk wannan abinda sukeyi Umaisa bama ta iya jin abinda Baban take faɗa tunda taji cewar ba
Abba bane mahaifinta, gaba ɗaya tama kasan kukan sabida tsabar tashin hankalin datake ciki,
babu abinda bakinta yake faɗa se "innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!! Yanzu ina zata saka
rayuwarta taji daɗi?

Taya kuma zata rayu da wani uban saɓanin Abbanta kuma abin sonta?

Tabbas ya khabeer ya cuci rayuwarta daya zama silar baiyanar wannan mummunan labarin
wanda bata taɓa zatonsa ba bale tsammani a cikin rayuwarta! Kamar daga sama taji saukar
hannun Abba akan kafaɗunta, ɗago idanunta tayi waƴanda suka soye sabida tashin hankali
tana kallonsa, murmushin ƙarfin hali Abba ya sakar mata sannan yasa hannu ya share mata
ƙwallar dake shirin zubo mata yace " Mamana! Ki kwantar da hankalinki har yanzu nine
Abbanki, haka kuma babu wanda ze rabani dake har duniya ta tashi, sabida son da nake miki
ban taɓa nunawa kowa irin soyayyar danake miki ba, sabida banaso ki nemi wani abu ki rasa a
cikin rawarki, wllh kaf ƴaƴan dana haifa a cikina bantaɓa fifita soyayyar danake musu akan taki
ba, hasalima kenake fifitawa akan tasu soyayyar! Don haka ki sanyawa zuciyarki cewar duk
wanda kikeso ki Aura wallahil'azeem shi zan Aura miki, don haka ki sanya a ranki cewar
Abbanki har yanzu yana tareda ke Umaisa, haka kuma muddiɓ yana raye bazaki taɓa neman
wani abu ki rasashi ba!

Faɗawa tayi a jikinsa ta ƙanƙameshi, lokaci guda kuma kukan datake dannewa ya samu
nasarar ƙwace mata, kasa magana tayi illa ƙara ƙanƙame Abban datakeyi a jikinta, a ranta
kuma wani irin zafi takeji a zuciyarta wanda bata taɓa ɗanɗanar makamacinsa ba a tarihin
rayuwarta, babban abinda yake ƙara ɗaga mata hankalima shine, shin ta ya zata rayuda wani
uban wanda ba Abbanta ba??

Ji take dama ta mutu kota huta da wannan gagarumin bala'in dayake shirin kutsowa cikin
Rayuwarta!!!

Ba umaisa kaɗaiba hatta Rumana seda zuciyarta ta karye, Ummie kuwa babu abibinda takeyi
se kuka, shiko khabeer ji yake kamar ya janyota ya rugumeta a ƙirjinsa ya rarrasheta, amma
sedai babu damar hakan.

A fusace Abba ya maida kallonsa ga khabeer yace "tunda ka lalata komai ai hankalinka ya
kwanta yanzu ko?
Be jira cewarsa ba ya kama hannunta sukabar perlourn zuciyarsa a dagule, be dire a ko ina da
itaba se'a ɓangarensa, a babban perlourn dake part ɗin Abba suka zauna, kallonta Abba yayi
tareda miƙa mata wayar dake hanunsa yace "Mamana sakamin number ɗin yaron da kikeso
ɗin, karkiji komai har yanzu Abbanki yana taredake, haka kuma duk wanda kikeso wllh shi zan
Aura miki Uwata.

Karɓar wayar tayi jikinta har wani rawa yakeyi ta sanyawa Abba number maheer ɗin, komawa
Abba yayi kan ɗaya daga cikin kujerun dake perlourn ya zauna, sannan ya shiga kiran wayar,

Maheer dake kwance bisa ƙaya taccen perlourn sa, gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa sabida
yanda tunanin duniya da kuma damuwa suka tisashi a gaba, komai na duniyar ma yanzu sam
baya yi masa daɗi, yanzu babbar damuwarsa shine Rashin lafiyar mahaifinsa da kuma khabeer
wanda ke shirin rabashi da abar ƙaunarsa, a haka wayar Abba ta shigo cikin wayarsa, ɗagowa
dara-daran idanunsa yayi lokaci guda ya saukesu bisa kan wayarsa dake ihun neman agaji,
shiru yayi yana kallon wayar tamkar baze ɗauka ba, haka kawai yaji gabansa yana faɗuwa don
haka da sauri ya amsa wayar tareda yin sallama.

Amsawa Abba yayi tareda cewa "Sunana Alhaji Mahmoud Muhammad mahaifin Umaisa.

da sauri mahir ya miƙe zaune tareda rissinawa tamkar Abban yana kallonsa ya shiga gaisheshi
cikeda girmamawa, basu wani jima suna wayarba Abba ya sanar dashi cewar ya turo
magabatansa gobe idan Allah ya kaimu, sannan ya shaida masa cewar ya bashi Auren umaisa.

Waiyo Allah zando me karatu yaga irin farin cikin da maheer yake ciki, tamkar wanda akayiwa
bushara da gidan Aljanna, haka itama Umaisan dukda irin tashin hankalin datake ciki hakan be
hanata jin daɗin hakan ba.

nasiha sosai Abba ya dingayi mata kan cewar ta daure ta saki ranta, haka kuma ta danne
zuciyarta ta yarda da ƙaddarar da Allah ya aiko mata, babu yadda ta iya tunda haka Allah ya
ƙaddaro mata, amma kuma meyasa Mamie bata sanar da ba tun farko cewar ba Abbane ya
haifeta ba?
Wannan dalilin ne yasa taji a ranta cewar Mamie bata kyautawa rayuwarta ba, haka kuma
batayi mata adalci ba, Tabbas mamie ta cutar da zuciyarta amma babu komai haka Allah ya
ƙaddaro mata, haka kuma ta karɓu ƙaddarar hannu bibbiyu.

Washe garida safe maheer ya shirya tsaf cikin wani dakakken boyal fari tass, wanda ya baiyana
ainihin cikar halittarsa gamida haibarsa, haka kawai yakejin kansa cikin wani iriɓ farin ciki mara
misaltuwa, a da ya ƙudurawa zuciyarsa cewar bazetaɓa zuwa Asibitin ba, amma haka kawai
yau seya samu kansa da son ganin mahaifin nasa da kuma ƙaninsa Abdul da kuma baffaninsa,
dukda cewar suma suna matiƙar son du haɗu dashi ɗin amma kuma yaƙi yarda su haɗun.

motarsa ya faɗa tareda murza mata key yabar harabar gidan, cikin mintunan da bazasu gaza
30 ba ya iso harabar Asibitin, tun kafin ya ida perker motar ya hangi motar gidansu hakanne ya
tabbatar masa da cewar su baffa Giɗaɗo suna cikin Asibitin, wani irin farin cikine ya sake sarƙe
zuciyarsa, a nitse ya fito daga motar cikin takunsa na isa da ƙasaita, a haka harya isa word ɗin
da Dadyn yake, ya jima a tsaye a bakin ƙofar glass ɗin dake ɗakin, seda ya ɗauki lokaci me
tsaho yana kallon Ahalin nasa sannan ya tura ƙofar tareda sallama.

_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:37_

___________Ƙuri Dady yayi masa yana kallonsa, hakama su baffa Giɗaɗo dake zaune a
ɗakin, shiko Abdul kasa motsin kirki yayi sabida ganin yayan nasa, babban abida yafi komai
ɗaure masa kai shine yanda yaga maheer ɗin yayi masa duhu kuma ya rame, buɗe masa
hannayensa maheer yayi alamar Abdul ɗin yazo gareshi, Da sauri Abdul yazo yay hugging
nashi harda hawayensa, a haka suka ƙarasa ɗakin hannunsu a sarƙe dana juna.

Tun kafin su ƙaraso Dady yaketa faman miƙawa maheer hannu cike da tsantsar soyayya,
kansa a duƙe ya ƙarasa inda Dadyn yake tareda kama hannunsa da duka hannayensa biyu,
wani irin sanyi ne yake ratsa zuciyar maheer tareda tsantsar ƙaunar mahaifin nasu, haƙiƙa yayi
kewarsa ba ƴar kaɗan ɓa, tayanda bakinsa da laɓɓansa sunyi kaɗan wajen misaltawa me
karatu yanda yakeji a wannan halin.

Ada yayi tunanin cewar ze iya Rayuwa batareda dady ba, Ashe abinda be sani ba shine yayiwa
kansa ƙarya, jawoshi dady yayi zuwa jikinsa, lokaci guda kuma ya Rumgumrshi ƙam a ƙirjinsa,
wasu irin zafafan hawayene suka shigayiwa ɗan da kuma uban zarya, a wannan lokacin duk
wanda ya kallesu ze fahimci hawayen dake zuba a idanunsu ba hawaye bane kawai, isharace
wadda ke sauka a bisa ɗanba ta soyayyar ɗa da mahaifi.

Sun jima a haka sannan Dady ya zare jikinsa daga na maheer, lokaci guda kuma ya ƙanƙame
hannayensa yace "haƙiƙa na cutar dakai ɗana, hakakuma na zalunceka, banyi tunani ba ko
kaɗan akan hukuncin dana zartar a gareka ba ko kaɗan, yau gani a gabanka ina me roƙonka
slfarma a karona biyu don girman Allah ka yafewa mahaifinka kaji yarona !! Don Allah ka
yafemin !!! Ya faɗa yana wani irin kuka kamar wani ƙaramin yaro.

Da sauri maheer ya rungumeshi yace "a'a Dady, har kullum kaine sama dani, haka kuma
dukkan abinda zakayimin a matsayina ɗanka ɗolene nayi haƙuri dashi kuma nayi maka biyayya,
amma kash se gashi na gazayin hakan, kabani Umarni amma na bijire maka sabida zafin raina
na banza da wofi, a ƙarshe nazama nine silar rushewar ahalinmu, don haka nine ya dace na

baka haƙuri Dadyna don girman Allah ka yafemin kozan samu nutsuwar zuciya Dadyna!

Shafa kansa kawai Dady keyi yana hawaye, lokaci guda kuma ya saki murmushin farin ciki yace
"kaƙika tayi gaskiya datace a kwai ranar dazata zo maheer zeyi magana me cikeda tarin
farsafa gamida ilimi a cikinta, Allah sarki! Da ace tana raye da idanunta sun gane mata wannan
rana da mafaɗacin ɗana yayi magana cikin tattausan lafazi gamida soyayyah.
Kunyace ta kama maheer lokaci guda kuma ya sinkuyar da kansa ƙasa yana murmushi, se'a
lokacin ya ɗago ya gaida su baffa Umaru, dariya sukayi gaba ɗayansu sannan sukace seyanzu
ka ganmu kenan.

A nan baffa Giɗaɗo yayita musu nasiha akan sakaci da addu'ah, a haka Dr. Abdullah ya shigo
ya samesu, bayan sun gaisa ne ya fara duba jikin Dadyn, bayan ƴan rubuce-rubucen dayayi ne
ya rubuta musu takardan sallamah, a nan ne Dady yake tambayarsa ina Dr. Khabeer?

Murmushi Abdullah yayi sannan ya sanar dashi cewar khabeer bashida lfy, amma yace ya
sanar dashi cewar dazarar ya ji sauƙin jikinsa zezo har gida ya sake duba jikin nasa, sosai
Dady yaji dadin hakan tareda yi masa addu'ar samun sauƙi. A haka suka tattara suka bar
asibitin suka ɗauki hanyar Garki inda gidan Maheer yake,
Tun kan su shiga farfajiyar gidan Abdul yake yaba yanayin tsarin gidan, cikeda tsokana ya kalli
maheer yace "yaya gaskiya gidannan yamin kyau sosai wllh, da ace na isa Aure wllh da a nan
zan zauna da matana inyaso kai ka nemi wani, wata uwar harara maheer ya sakin mai dole
tasa Abdul ya tsuke bakinsa, horn suka zuba me lafiya, da sauri lawan mai gadi ya wangale
musu get ɗin suka kunna kai zuwa cikin gidan, a nitse suka nufi perking lot ɗin da aka tanada
don ajiye motoci suka perker motocin, dannan suka fito cikin Aminci gaba ɗayansu, cikin
takunsa na isa yayi musu jagora zuwa cikin gidan, a daidai ƙofar shiga maine perlour ɗin gidan
yay kaciɓus da victoria, cikeda gimamawa ta kalleshi tace "barka da dawowa sir, dama wancan
matan da muke horarwa ne ciwon dake ƙafarta yayi tasanani, a halin yanzuma banda wari da
tsutsa babu abinda yakeyi, shima ɗayar matan bashida lfy amma sedai ciwon nasu ba iri ɗaya
bane.

Harararta maheer yayi sannan yace "toni ina ruwana me zan musu? Kedai kawai kuci gaba da
horar dasu shine kawai aikinku, ya juya da sauri ze shige Dady ya jawoshi, cikin tattausan
lafazi yace "boy suwaye waƴannan yaran? nd kuma wasu matane kake cewa a horar dasu?

murmushi yayi sannan ya waske yace " Dad muje don Allah banaso kai stresing kanka akan
waƴanda basuda wani amfani, all you want yanzu is to rest muje kawai,

wani irin kallo Dady yayi masa dole tasa ya fara shafa kai, baffa Umaru ne ya kalli Victoria yace
"ke muje ki kaimu muga wasu matane wannan haka. Kallon Maheer Abdul yayi sabida tabbas
yasan a kwai Lauje cikin naɗi, dole a kwai abinda maheer ɗin yake ɓoye musu wanda bayaso a
sani, aiko suna haɗa ido da maheer ya kashe masa ido ɗaya, da sauri sukabi bayansu baffa

Umaru zuwa ɗakin da Hajiya murja suke, tun kafin su ƙarasa ɗakin wani irin wari da ƙarni ya
gauraye musu hanci, dole hakan yasa suka tsaya daga ɗan nesa da ɗakin, wani irin kallo
dukansu sukebin maheer ɗin dashi wanda yafi kamada na zallar tuhuma. Turo baki yayi sekace
wani ƙaramin yaro, cikin wani irin salon irin na sangartattun yaran masu kuɗin nan yace "uhmn
Dady nifa banyi komai ba kawai nayi abinda ya dace ne" ya ƙare maganar yana wani male
baki.

murmushi dady yayi sannan yace " nasani bakayi komaiba yarona, amma zo nan kaji wani
magana, maƙe kafaɗa yayi sannan yace "naƙi wayon wllh idan nazo murɗemin kunne zakayi.
Dariya suka kwashe habaɗayansu dashi , sannan Baffa Umaru yace "Maheer kenan dama me
hali ai baya fasa halinsa. Victoria yayiwa inkiya data fito dasu Hajiya murja da kuma Aminiyar
tata.

cikin mintuna kaɗan victoria da Yukeria suka fito dasu waje tamkar wasu kayan wanki suka
wurgosu gabansu Dady, nan da nan warin ƙafar ya gauraye gurin, da sauri suka toshe bakinsu
da hancindu da hannayensu, gaba ɗaya duk sun jeme sun koɗe tamkar basu ba , sabida
yanda rayuwa ta juya musu baya.
Lokacin da Hajiya murja ta ɗago idanunta ta kalli Dady wani irin mugun sanyi jikinta yayi, lokaci
guda kuma ta fashe da wani irin kuka tareda ƙoƙarin kamo gefan rigar Dadyn, da sauri Abdul
bige mata hannu tareda jifanta da wani ɗan iskan kallo wanda yasa gabaɗaya taji ta muzanta a
gabansu, kasa magana Dady yayi illa kallonta kawai dayakeyi, daƙar ya iya buɗe baki yace
"tabbas bahaushe yayi gaskiya daya kirayi duniya da sunan makaranta! Zuwa yanzu na tabbata
ta koya muku karatun da baku taɓa jin kamarsa ba balle kuyi hadda, dama ita duniya haka take,
a yayin data shimfiɗawa mutum tabarmar isa da iko ya hau kai yayi kane-kane sekiga gaba
ɗaya ya manta da mutuwarsa ko makomarsa, na tabbata baki taɓa zaton duniya zata juya muku
baya irin haka ba, amma se gashi tun ba'ayi nisan kiwoba kin fara girbar abinda kika shuka
wanda na tabbata da cewar wannan ciwon dake ƙafarki shikaɗai ma ya isa yayi ajalinki, don
haka ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login