Showing 51001 words to 54000 words out of 80273 words
Chapter 18 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf
mik'e yabar office d'in
Ransa a b'ace.
Wani irin Kallo Usman kebin khabeer dashi wanda yafi kamada na tuhuma yace " amma ya
Golden senake ganin kamar be kamata ka....... "Kaga malam banason yawan surutu ka gane
ko?
Shiru yayi yana kallonsa sannan ya kamashi sukabar office d'in suka fita daga cikin Asbitin, a
ran Usman yana mamakin Hali irin na yayan nasa, abu d'aya ya qudurtawa zuciyarsa shine
seya binkito abinda ya Golden d'in ke boyewa wanda bayaso ya sani.
B'angaren Maheer kuwa sosai ya rasa kwanciyar hankali sabida tsoron Abinda zeje ya dawo a
tsakaninsa da yarinyar dayake da tabbacin cewar tariga ta zama jini da tsokar dake yawo a
cikin gangar jikinsa, tabbas ita kad'aice mahad'in kwanciyar hankalinsa da salamar Ruhinsa,
bayajin ze iya jurar Rashin ta koda na k'ank'anin lokaci ne a rayuwarsa, babban abinda ke tayar
masa da hankali a yanzu guda d'aya ne shine Dr.khabeer! Tun ranar daya kalli Qwayar
idanunsa yaga daskararriyar soyayyar dayakeyiwa Queen d'insa ya kasa kwanciyar hankali,
dukda cewar shine *ZAB'IN RANTA* ba khabeer din ba!
Wayarsa ya lalubo ya danna number d'inta, kwance take bisa kafet din dake d'akin tayi shiru,
gaba d'aya kewarsa duk tab'i ta takura mata, dik wani bugu na zuciyarta yana bugawane da
soyayyar maheer dinta!!. Qarar tellphone dince ta katseta wanda ko ba'a fad'a mata ba tasan
Maheer ne, da sauri ta mik'e ta nufi gurin zuciyarta fal farin ciki ta d'auka ta kara a kunnenta
tareda yin sallama, lokaci guda suka saki ajiyar zuciya ita dashi, wadda take baiyana tsantsar
kewar junan da sukayi!!!.
Wani irin lumshe idanu maher yayi sabida jin muryarta da yayi, hka kawai yakejin wani irin
baqon al'amari a tattareda yarinyar, musamman ma idan yana kallonta kokuma yanajin
muryarta, Allah ne kad'ai yasan irin yanayin da zuciyarsa take shiga a kanta, wani irin so yake
mata wanda baze iya misaltawa irinsa ba. Da wata irin kasalalliyar murya yace "i miss you
Queen, dariya tayi har yana iya jiyo sautin dariyar yace " dariya ma kikemin ko? To tunda ke
bakya missing d'ina barina kashe wayana kawai....... Da sauri tace "i miss you too Jan!
Dariyar shima yayi sannan suka afka Duniyar hira, sun jima suna waya sannan sukayi sallama
da juna, wasa-wasa kullum Qara shaquwa suke da juna tamkar ana Qara izamusu wutar
Qaunar dake tsakaninsu. Ita kanta har mamakin kanta takeyi idan tana wani abun akan Maheer,
sam bata iya b'oye irin son da takeyi masa, Ameerah ce ta shigo d'akin da sallama tareda kallon
kallon yayar tata tace " ya Umaisa Mamie is calling you, she say data kuma kiyi shauli kizo.
Tana kaiwa nan ta juya harda d'an gudunta tabar d'akin
A nitse ta mik'e cikin nutsuwa, sannan ta nufi d'akin Mamie, a hankali take taka step din tamkar
wata k'asaitacciyar sarauniya harta kai k'ofar d'akin ta murd'a tareda kunna kai ciki had'e da
sallama, a zaune ta samu Mamie bisa d'aya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun dake
perlourn nata,
Zama tayi daga gefan Mamien tareda fad'in "Mamie gani.
Kallonta Mamie tayi kimanin daqiqu biyar sannan tace " Umaisa a matsayina na mahaifiyarki ina
so ki sanar dani meye a tsakaninki da wannan matashin yaron wanda yazo gurinki shekaran
jiya?
Qirjinta ne ya buga da Qarfi lokaci guda kuma wata irin zufa ta fara keto mata dukda uban
sanyin Ac dake perlourn, inda-inda ta farayi tana sosa gefan kanta sabida yanda duk tabi ta
rude da tambayar da Mamie tayi mata.
Kallon tsaf Mamie tayi mata sannan tace " haryanzu ke yarinya ce Umaisa, ni uwace bazan
tab'a tauyeki ba, tunda kema kinada haqqi akaina, nayi mamaki k'warai da baquwar d'abi'ar da
kika shigo da ita cikin Rayuwarki Umaisa, ada komai naki bakya iya boye min shi amma se
gashi dayake al'amari ne na soyayyah bakiyi shawara da kowaba kika jefa kanki cikinsa, kinsan
al'amarin d'a namiji kuwa Umaisa?
Kuka ta fashewa Mamie dashi har da shashsheqa, cikeda karayar zuciya tace " iya dnt know
why i love him Mamie, ni kaina bansan meyasa harna amince dashi irin haka ba Mamie, wllh
koke kika ganshi zaki yaba da halayansa da kuma d'abi'unsa, komai nasa a tsari yakeyinsa, he
is very friendly and social Mamie, bayan kasancewarsa genues bravo...... Keep Quite idiont, i'm
i your mate, don ubanki zaki tsaya kina expresing how you fill akan wani wani banza can?
Tashi ki fice min daga d'aki tun kafin kija abinda zan nakaita ki akansa, in banda lalacewar
zamani har ke zaki iya kallon Qwayar idona kina gayamin irin wa'yannan banzayen
maganganun?
Ina kunyarki da tarbiyar da muka baki Umaisa?
Wani tuquqin baqin ciki ne ya tasowa Mamie, sabida baqin ciki jitake kamar zuciyarta zata fasa
qirjinta ta fito, miqewa Umaisa tayi da mugun sauri tabar d'akin tana kuka,
Dafe kanta Mamie tayi a ranta ta qudurtawa kanta cewar koda Umaisa zata mutu seta Auri
khabeer sabida shine zabinta ba wani sakarai can ba.!
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:34_
*_Al'umar musulmi muji tsoron Allah mu muƙa dukkan lamuran mu ga Allah, wannan jarrabawar
da muke fama da ita na curona-virus Allah ubangiji ka kawo mana sauƙinka da agajinka, ya
ubangiji Allah ka yafe mana laifukanmu badan halayenmu ba!í ½í¸í ¾í´²_*
___________í ½í³– Fita tayi daga É—akin tana wani irin kuka wanda yake baiyanar tsantsar
damuwar datake ciki, a perlourn ƙasa sukai kaciɓus da Ruman tana ƙoƙarin hawa steps ɗin,
kallonta kawai Ruman takeyi a ranta tana jinjina dalilin kukan ƙanwar tata, wuceta Umaisa tayi
da sauri tareda toshe bakinta da hannayenta.
yanda take kuka kad'ai zaka kalla kasan tana cikin tashin hankali kamar wadda ake zare ma rai,
a haka ta koma d'aki tana gurzan kuka, Abinne ya d'aurewa Rumana kai, sabida ganin irin
kukan da Umaisa keyi yasa tabi bayanta da sauri, tana shiga d'akin ta zube a K'asan Capet din
d'akin ta sake fashewa da kuka.
A haka Rumana ta shigo ta sameta, a nitse ta dafa kafad'unta zuciyarta aatik'ar dagule sannan
tace " meyake damunki ne haka? Zuwa yanzufa ya kamata ace kin dena irin wayan nan
banzayen koke-koken naki, ya kamata fa ki fahimci cewar kefa ba yarinya bace Umaisa.
Dagowa tayi da jajayen idanunta wayanda suka canza launi sabida kuka tace "Rumana shin
laifine dan naso mutumin daya nunamin k'auna da dukkan kulawarsa gareni? Maheer ya soni a
lokacin da shi kansa besan menene so ba, haka kuma ya soni a lokacin da betab'a mafarkin
hakan ba, wllh Ruman bazan tab'a iya son wani d'a namiji a rayuwata kamarsa ba, wani irin so
nake masa wanda ban tab'a jin kwatankwacin irinsa a tareda kowa ba!
Amma se gashi Mamie ta kasa fahimtar hakan, batareda tunanin irin halinda zan shigaba amma
Mamie take ƙoƙarin Rabani dashi, nikuma wllh indai akan rabuwa da Maheer ne sedai in rasa
rayuwa........ "Anya kinada hankali kuwa Umaisa? Rumana ta katse ta cikin wani irin yanayi.
Kafeta Ruman tayi da manyan idanunta sannan taci gaba da cewa " Umaisa karki bari giyar
soyayyah gamida mayentasu rufe miki idanu ki bijirewa umarnin Mahaifiyarki!!, shi namiji da
kike ganinsa ba abin yarda bane balle har a saki jiki dashi, a matsayina na 'yar uwarki ina me
baki shawara kan cewar ki mik'a dukkan lamarinki ga Allah sannan kuma kiyiwa Mamie biyayya
akan dukkan abinda ta umarceki, sabida su iyaye da kike ganinsu wllh basuda mahadi balle aja
dasu, bijire musu daidai yake da janyo fishin Allah (S.W.T).
Rungume ta Umaisa tayi tareda fashewa da wani sabon kukan, dak'yar Rumana ta samu
nasarar Rarrashinta, tareda gaya mata tausasan kalaman da zasu rissinar da zuciyarta, sannan
ta samu Umaisan tayi shiru,
sedai dukda hakan ita kadai tasan irin Rad'ad'in da zuciyarta take ciki, haka kuma batajin zata
iya Rabuwa da Maheer É—inta, jira kawai takeyi Abbanta ya dawo ta sanar dashi damuwarta,
shikadaine wanda tasan ze goya mata baya kuma ya barta ta Auri *ZAB'IN RANTA.!*
Yau sab'anin kullum Abba be samu nasarar dawowa gida ba har wajen 9:00pm, wannan dalilin
ne yasa Umaisa ta yanke shawarar taje ta sanar da ya khabeer abinda Mamie take shirin aikata
mata, tun daga d'akinta take ta sharar k'walla harta kai part din Khabeer d'in, a hankali ta tura
k'ofar ko sallama batayi ba sabida tashin hankalin datake ciki.
Kwance yake bisa makeken Royal bed d'insa, inda Dr. Abdullah yake k'ok'arin gyara masa
zaman igiyar drip din dake É—aure a tsintsiyar hannanunsa, seda ya gama tsaf sannan ya koma
gefe ya zauna yana kallon Khabeer din ransa a matiqar b'ace yace" wllh kaji kunya kaidai, akan
yarinya Qarama kake qoqarin halaka kanka a banza, har zuwa wani lokaci zaka d'auka kana
boye mata abinda yake Ranka?
Kaga malam Lokaci yayi daya kamata ka bude mata sirrin dake zuciyarka ko ka samu
kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, kaduba fa kaga irin condition din da kake ciki Khabeer!!!
A halin yanzufa Zuciyarka ta fara kumbura sabida damuwar da kake yawan addabar kanka
dashi, idan har bazaka iya sanar da itaba ninan zan sanar da ita sirrin Zuciyarka, *_KAYARDA
DANI Abokina.!!!_*
Lumshe tsumammun idanunsa yayi a hankali, lokaci guda kuma ya budesu tar akan Abdullah
yace "wai sonawa zan fad'a maka cewar na haqura da ita ne?
"Ka dakata da wannan maganar banzar da kakeyi malam! Abdullah ya dakatar dashi a fisace,
idan harka haqura da ita meyasa har yanzu ka kasa gogeta daga Zuciyarka?
"Sabida haka Allah ya ƙaddara min Abdullah! Khabeer ya katseshi ta hanyar fad'ar hakan.
Abdullah yanashirn yin magana Umaisa ta shigo d'akin. kai tsaye gun Khabeer ta nufa batareda
ta lura da drip din dake sak'ale a hannunsa ba ta wani fad'a jikinsa tareda sakin wanu irin kuka,
sabida tsabar kukan da takeyi bakinta har Rawa yakeyi, dakyar ya iya tattaro ragowar qarfin
daya yage masa ya dagata daga jikinsa, lokaci guda yaji zuciyarsa nayi masa wani irin zafi,
sabida yanda yakejin kukan nata yana wani irin narka masa zuciya, Allah shikaÉ—ai yasan irin
son da yakewa yarinyar! Daƙyar ya iya buɗe bakinsa ya fara tambayar ta dalilin kukan nata.
bata ɓoye masa komaiba ta warware masa dukkan abinda mamie ta gaya mata, a ƙarshe ta
ƙare maganar da cewa "wllh ya khabeer i love him so much, and i cnt live without him!!!
Ƙuri yayi mata tamkar wani sakarai, haka kuma ya kasa koda motsin kirki ballema ya iya cewa
komai, babu abinda yafi ɗaga masa hankali kamar kalmarta na ƙarshe!!!!
wata uwar harara Dr. Abdullah ya wurga musu dagashi har ita, sabida takaicin abokin nasa ji
yake kamar ya shaƙeshi koya samu sassauci a zuciyarsa.
Miƙewa khabeer yayi daƙyar Cikeds ƙarfinhali tareda kama hannunta, jajayen idanunta ta ɗago
tana kallonsa cikeda son jin inda zasuje, murmushin ƙarfin hali ya sakar mata sannan yace
"kiyarda dani gurin mamie zamuje muyi magana akan wanda kikeso É—in, i'm sure mamie zata
Barki ki Auri wanda kike so dear!
miƙewa tayi da sauri shikuma yana riƙeda hannunta, suna shirin fita daga ɗakin Abdullah ya
katsesu ta hanyar cewa "Stop deceiving your self khabeer!! Harzuwa yaushe zaka kai kana
azabtar da Rayuwarka akan wannan yarinyar, you should tell her how you fill about yanda kakeji
akan sonda kake mata, lokaci yayi dazaka sanar da ita cewar she's the only yarinyar da kajeji a
ranka sama da kowace budurwa a duniya. Amma sabida cutarkai kaƙi ka sanar da ita , wannan
abinda kakeyi ba sadaukarwa bace shirmene kawai Khabeerrr!
tunda ya fara magana Umaisa take kallon Dr. Abdullah, gaba É—aya jinsa kawai takeyi tamkar
wata zararriya, gaba É—aya jin sautin maganarsa takeyi tamkar saukar aradu, inda wani
ɓangaren na zuciyarta takeyi masa kallon taɓaɓɓe, a saluɓe ta mayar da kallonta ga khabeer
wanda gabaÉ—aya yabi ya wani daskare tamkar an dasashi, daga irin kallon dayake mata ta
fahimci cewar maganar Dr. Abdullah gaskiya ce, wani irin bugawa ƙirjinta yayi, don haka ta fara
jada baya tana zubarda hawaye, da sauri khabeer ya fara yun ƙurin binta, da wani irin mugun
sauri ta juya tabar É—akin su kuma duka mara mata baya.
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaÆŠo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:35_
___________í ½í³–binta yakeyi da dukkan sauran Æ™arfin daya rage masa, amma sam ya kasa
cimmata, bata tsaya a ko ina ba se'a babban perlourn gidan sakamakon ganin Ummie datayi a
daining aria ɗin, da wani mugun sauri ta faɗa jikin Ummie ta ƙanƙameta, gaba ɗaya duk tabi ta
birkice sekace wata zararriya, rikicewa Ummie tayi sabida yanda taga umaisan nayi kamar
wata taɓaɓɓiya, jijjigata kawai takeyi tareda jera mata tambayoyi, a haka khabeer da Abdullah
suka ƙaraso perlourn.
Fisge jikinta Umaisa tayi daga riƙon da Ummie tayi mata, lokaci guda kuma ta tawani koma
bayan ummie ta tsaya tareda fashewa da kuka tace "wllh Ummie ya khabeer ya haukace, wllh
ummie baya cikin hankalinsa, cewafa yakeyi wai yana sona kuma wai aurena yake sonyi! Wllh
ummie karki saurareshi kawai ki kira Abba akaishi Asibiti.
A hankali khabeer ya far takowa zuwa inda Ummie ke tsaye, wata uwar ƙara Umaisa ta ƙwala
wadda seda gidan ya amsa gaba ɗaya, tareda ƙanƙame ummi tana faɗin "tell him karya mato
inda muke wllh Ummie ya khabeer baya cikin haiyacinsa, ta faÉ—a tana wani irin kuka kamar
Ranta ze fita daga jikin ta,
Ihun data kurma ne yasa mutanan gidan gaba É—aya suka hallara a perlourn, ciki kuwa harda
Baban Gano, kallonta kawai mutanan dake perlourn sukeyi, haka kuma sunyi tsit bakajin
komai se sautin kukan umaisa, hakanne yayi daidai da shigowar Abba perlourn tareda Usman.
Da wani irin gudu ta ƙara inda Abba ke tsaye tareda faɗawa jikinsa ta saki wani irin kuka tana
nuna masa khabeer wanda ke dafe da kansa sabida tsabar tashin hankali take faÉ—in "Don Allah
Abba ka taimakeni mukai ya khabeer Asbiti wllh abba ya haukace, bakaji irin maganganun
dayake faÉ—amin ba Abbah, cewafa yakeyi wai ni yakeso ya aura!
Wata irin uwar zuface ta shiga ketowa Abba, lokaci guda kuma yanayinsa yay masifar sauyawa
sabida ɓacin rai, a nitse ya zarota daga jikinsa yayi gefe da ita, loƙaci guda kuma ya maida
kallonsa ga khabeer, wani irin tuƙuƙin baƙinciki ne yake taso masa daga zuciyarsa, cikin wani
irin karaji da rawar jiki ya ƙarasa inda khabeer yake tsaye, wani irin gigitaccen mari Abba ya
É—auke khabeer É—ashi, ji kake tasss!...tass!!...tasss!!!.
A kausashe ya nunashi da yatsansa yace "khabeer ada inayi maka kallon shasha-sha, Ashema
kafi wuce haka, sonawa zan sanar dakai cewar wannan hanyar daka biyo bame ɓillewa bace?
Taya kake tsammanin zan iya baka Auren É—iyata ta cikina?
Shin bakasan cewa ƙanwarka bace babu Aure a tsakaninku kai da ita ba?
"harzuwa yaushe zakaci gaba da ɓoye wannan sirrin Alhaji mahmoud.! Mamie ta katseshi cikin
wani irin karaji me É—aukeda Amo a cikinsa, lokaci guda kuma wasu irin hawaye masu masifar
zafi suka shiga bin kumatunta, wanda hakan ya sanya kowani halitta dake cikin perlourn kansu
yay masifar É—aurewa, musamman ma Baba da Ummie da kuma Ummah. Farouq da Usman da
Rumana kuwa kasa motsin kirki sukayi sabida tsabar mamakin irin almarar dake shirin faruwa a
zuriyar tasu gabaÉ—aya.
"Ki rufe min baki Badi'atou, Abba ya katseta fisace cikin É—aga murya..!
Girgiza kai Mamie tayi tana kuka Lokaci guda kuma ta zube a ƙasan capet ɗin dake perlourn
tace "kayi haƙuri Alhaji amma a irin karamcin da zuriyarka dakai kanka kayimin banajin zan iya
cigaba da ɓoye musu wannan sirrin, koda kuwa hakan ze zama silar mutuwar aurena dakai!!
yana shirin yin magana Baba ta katseshi ta hanyar É—aga masa hannu tace "mamuda, idan har
ka É—aukeni a matsayin uwar data haifeka to ina me baka umarnin cewar karka kuskura ka
hanata baiyana wannan sirrin da kuka ɓoye kaida ita!
wannan maganar ce tasa dole Abba ya nemi guri ya zauna a É—aya daga cikin kujererun
perlourn, wata irin zuface take keto ma Abba duk irin sanyin Ac dake tashi a perlourn, dole gaba
ɗaya ahalin suma suka nemi guri suka zauna, sannan Mamie ta maida idanunta ƙasa tana
sharar hawaye ta fara magana ksmar haka.
*_LABARIN AINIHIN ABIDA KE FARUWA SHINE_*
Asalina ni haifaffiyar garin Adamawa tantagaryar cikin mabilwa, mahaifina malamin makarantar
Alo ne, nikaÉ—ai Allah ya bashi a tsayin Æ´a, haka kuma ya bani kulawa sosai a cikin Rayuwata,
ina Æ´ar shekara goma kacal a duniya Allah yayiwa mahaifiyata Rasuwa, wannan mutuwar ta
girgiza mahaifina sosai haka nima, tundaga loƙacin Babana ya ninka kulawar dayake bani
fiyeda wadda yake bani kafin mahaifiyata ta rasu.
bayan wani lokaci me tsaho babana ya sakeyin Aure badon radin kansa ba sabida matsin
dayake samu daga mahaifiyarsa wato kakata, tunda babana yayi Aure kwanciyar hankalina ya
ragu, duk wata kulawa danake samu daga babana nazo na dena samunta, hasalima kafin mu
haÉ—u dashi aiki ne,
tundaga lokacin rayuwata ta koma tamkar ta baiwa mara Æ´anci ko tausayina mahaifina bayayi,
wasu lokutan ma a gabansa Adda Dije take dukana tana azabtarwa, amma kuma baya iya
hanata. Kwatsam wata ranar juma'a Babana ya shigoda