Showing 45001 words to 48000 words out of 80273 words
Chapter 16 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf
na yarda da
dukkan sharad'inka My Jan! Wani irin sanyi ne gamida nutsuwar xuciya sukayi masa dirar
mikiya a ilahirin jijiyoyin jikinsa, sabida jin irin sunan da Queen d'insa ta kirashi dashi, komai
nata burgeshi yakeyi musamman ma yanda take nuna masa kulawa da tattalinsa, "baka
fad'amin sharad'in naka ba My jaan, Umaisa ta katseshi cikin sanyin muryarta wadda ke d'auke
da wani sirri a cikin ta.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace " zan fad'a miki idan nazo anjima, shagwab'e masa tayi
sannan tace " to what time zakazo? A tak'aice yace " nan da 4 insha Allah.
Ajiyar zuciya ta sauke a ranta tace "yauwa nasan haryazo ya tafi su ya Usman basu dawo ba,
balle hakan ya zame mata matsala, tabbas tasan duk ranar da tayi sake suka ganta tana hira
da Maheer Ranar ta gama kad'ewa har ganyenta! Amma kuma a fili setayi murmushi tace " to
Allah ya kawoka lf..... "I cnt explaine how much i love you Queen, i really love you with all my
heart Umy. Don Allah karki zama silar kassara zuciyar da take a cikeda mayen k'aunarki
Queen, Maheer ya katseta cikin wata irin murya me d'aukeda tsantsar soyayyar gaskiya da
kuma mayen ta.
Shiru tayi ta kasa cewa komai, sabida har ga Allah batajin zata iya yaudarar wani ma ballanta
wanda takejin an halicceta ne domin shi, ita kanta batajin zata iya Rayuwa batareda shiba
ballantana harta samu zarafin yaudararsa, wasu siraran hawayene suka fara yi mata zarya
akan kuncinta, don haka ta kasa cewa komai ila wani irin bugawa da zuciyarta takeyi da k'arfi!!
Da wata irin murya Maheer ya kirata sunanta yace " Queen!! *KIYARDA DANI* bazan tab'a
cutarda zuciyarki ba, nayi alk'awarin cewar zan kula da dukkan damuwarki sannan zan soki a
ko wani irin hali kika samu kanki, *KIYARDA DANI* ni Maheer zan zame miki bango da zaki
jingina dashi har k'arshen Rayuwata!
Kasa jure sauraron irin kalaman dayake gaya mata tayi don haka ta ajiye kan wayar da sauri,
lokaci guda kuma wani irin tausayin sa ya wanzu a birnin zuciyarta, fashewa tayi da wani irin
kuka wanda babu komai a cikinsa face tsananin tsagwaron soyayyarta gareshi!
Shiru yayi yanabin wayar da kallo, ya jima a zaune sannan ya mik'e ya fad'a toilet, shower ya
sakarwa kansa, ya jima ruwan yana zuba a tsakiyar kansa sannan yayi wankan ya fito d'aure
da babban towel a k'ugunsa hannunsa kuma bisa kansa yana goge lallausar sumarsa da wani
k'aramin towel fari tass. Direct wajen dressing miror dinsa ya nufa, tsadadden man shafawarsa
na *Companyn OLAY* na maza, ya d'auka ya fara bin tattausar fatarsa da shi, seda ya shafe
duk jikinsa sannan ya d'auki cumb ya fara gyara sumar dake kansa.
A hankali ya fara takawa cikin takunsa na isa da k'asaita harya kai bakin makekiyar Drowar
dake manne a bangon d'akin, wata dakakkiyar giznah skey blue ya jawo se faman yarari take
tana maiko, kaillo d'aya zakayi mata ka fahimci me tsada ce, ma'ajiyar agogunan Rolex d'insa
ya nufa ya bud'e ya zaro wanda yafi ko wanne tsada da kyau ya ajiyeshi gefen kayan daya fito
dashi,
A gaggauce ya sanya kayan a jikinsa, sannan ya bud'e drower da yake sanya hulunansa a ciki
ya d'akko wata Royal blue din zanna bukar wadda aka tsaya sakarta se faman baza k'yali da
walwali takeyi, a lokacin daya sanya hular a kansa seda na sake kallonsa tareda yaba tsarin
halittar Maheer Nasir Lamid'o, wani dakakken takalmi me d'anyatsa ya sanyawa a k'afarsa
shima Royal blue, sosai yayiasifar kyau sekace wani ango, nanfa ya shiga fesa tsadaddun
turarukansa masu masifar k'amshi sannan ya ajiye ya kwashi car keys d'insa da kuma
wayoyinsa ya fice daga d'akin.
A farfajiyar gidan ya hangi binta 'yar kwabo tana goge masa mota, inda Hajiya murja keta fama
fa bawa filawa ruwa dukda irin kumburar da k'arfata tayi hakan beda su Victoria sun tausaya
mata ba. Tsaki yayi sannan ya shige cikin bak'ar Range Rover d'insa ya murza mata key ya nufi
*Sushmer Hospital*, koda yaje Asbitin seda ya fara yin sallar la'asar sannan ya shiga ciki, daga
d'an nesa da d'akin Maheer ya tsaya yana kallon Dady wanda ke sanye cikin pink d'in uniform
d'in Asbitin yana kallon, kallo d'aya zakayi masa ka fahimci baya cikin kwanciyar hankali da
nutsuwar zuciya.
Ya jima a tsaye yana kallon mahaifin nasa zuciyarsa na harbawa sabida kewarsa, cikeda
karayar zuciya ya juya yabar Asibitin sabida baze juri kallon Dadynsa a cikin Rashin kwanciyar
Hankali ba!
Be dire a ko ina ba se *zone E Legislative Quaters,* a bakin katafaren get din gidansu ya tsaya
tareda yin horne, cikin mintuna kad'an aka wangale masa get ya kunna kai zuwa cikin gidan,
wajen da aka tanada don perking d'in motoci ya nufa ya parker sannan ya zaro wayarsa ya
shiga kiranta don ya sanar da Uwar gaiyar zuwansa, seda ya kirata kusan sau biyu sannan ta
answer ya sanar da ita zuwansa, katse wayar tayi sannan tace"ganinan zuwa.
Bata wani jimaba ta fito, sanye take cikin wata bak'ar jallabiya k'irar *Companyn shahriyal
Abaya* tayi Rolin da mayafi Royal bue wanda aka k'awatashi da stones masu haske daga
k'asansa, sosai kayan suka karb'i jikinta sekace balarabiyar k'asar Misrah, a nitse take takowa
cikin takunta me jan hankali wanda hakan yasa gabad'aya Maheer ya shagala da kallonta harta
k'araso gabansa besani ba.
Zarazaran hannayenta tasaka ta rufe kyakkyawar fuskarta dasu, sannan Maheer ya samu
nasarar dawowa daga duniyar begenta, nuni tayi masa da wasu kujerun Roba wanda aka
sanya a ta bayan parking space d'in kad'an, zama yayi sannan ya kalleta yace "masha Allah,
komai Queen d'ina ta saka kyau yake mata, da ace inada tukuicin dazan bayar gareki wllh dana
baki a matsayin kyauta ta ta farko a gareki!
Kallonsa kawai takeyi sannan tace " ai tun a had'uwata dakai ta farko ka baki babbar kyautar da
har duniya ta tashi bazan tab'a mantawa ba, don haka *KA YARDA DANI,* kai kanka kyautace
ga Umaisa Mahmoud muham........ Kasa k'arasawa tayi sabida ganin irin kallonda Ya khabeer
yake binta dashi, nanda nan k'irjinta ya buga da k'arfi sabida tsabar tashin hankalin datake ciki!
Da k'yar ta iya had'a kallmomin da suka Rage mata tace " ya kha..kha..kah...khabeer!!!
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:30_
___________í ½í³–Wata irin mummunar fad'uwar gabace ta ziyarci zuciyar Umaisa, lokaci guda
kuma ta mik'e tsaye tana k'ok'arin komawa bayan Maheer sabida yanda duk tabi ta Rud'e da
ganin sa!
Kallon ta kawai khabeer yakeyi amma sabida tsabar tashin hankali yama kasa motsa koda
yatsan hannunsa ballantana na k'afarsa, wani irin nauyi k'irjinsa yayi masa tamkar an d'ora
masa k'aton katafaren dutse a saman zuciyarsa, gabad'aya kansa ya gama kullewa sabida
tsantsar tsagwaron tashin hankalin dayake ciki! Yanzu yarinyar dayake kalo a matsayin
duniyarsa gamida nutsuwar zuciyarsa itace yau take *_Exchanging Romantic love words_* da
wani d'a namiji bashi ba? Indai kuwa har Umaisa son Maheer takeyi Tabbas yana cikin
gagarumin tashin hankalin da harshensa baze taba iya tattaro kalaman dazasu iya baiyanawa
mekaratu shiba. Da k'yar ya iya d'aga k'afarsa ya nufi k'ofar shiga maine perlour d'in gidan,
Babu kowa a perlourn se Ummie wadda ke zaune tana kallon tashar Arewa24, ko sallama
kasawa yayi sabida yanda jinsa da kuma ganinsa suke barazanar d'aukewa, had'a hanya kawai
yakeyi inda ya d'ora hannunsa na dama a saitin zuciyarsa, zuba Masa idanu Ummie tayi tana
me karantar yanayinsa, sosai ta fahimci zallar tashin Hankalin dayake kan fuskarsa amma kuma
ta dake batareda tace dashi k'alaba haryabar perlourn.
mik'ewa tayi kawai tabi bayansa don kawai ta tabbatar da abinda idanunta suka gane mata a
tareda shi, yana shiga part d'insa ko k'ofar be rufeba ya fad'a kan makeken Royal bed d'insa
tareda zubawa saman d'akin idanu, k'ara danne saitin Zuciyarsa yayi, sabida wani irin harbawa
dayaji tanayi masa, Rintse manyan Golden Eye d'insa yayi wa'yanda suka canza launi sabida
Rad'ad'in da yakeji a zuciyar sa, a haka Ummie ta shigo ta sameshi, sosai tashiga damuwa
sabida tabbas tasan gudan jinin sa yana cikin tashin hankali dukda be gaya mata ba, haka
kuma ba k'aramin abubane ze d'agawa Khabeer hankali harya bari wanima ya fahimci hakan,
*_hak'ik'a duk duniyar nan babu halittar data san ma'anar kalmar d'a sama da mahaifiya! haka
kuma ita kad'aice take iya fahimtar damuwar d'anta koda ace be sanar da ita damuwar tasa
ba!!_* , hannu tasa ta shafa gefan fuskarsa tareda zama a bakin Gadon, kasa magana tayi illah
kallonsa kawai da takeyi, saukar hannunta dayaji akan fuskarsa ne yasa ya bud'e idanunsa ya
saukesu akanta, lokaci guda kuma ya mik'e ya Rungumeta k'am a k'irjinsa! Kasa motsin kirki
Ummie tayi sabida yanda take juyo irin bugun da zuciyarsa keyi, lokaci guda jikinta yay masifar
sanyi gamida fargabar abinda ke shirin faruwa dashi, tabbas tasan halin khabeer yanada
masifar zurfin ciki shiyasa abune mayuyaci kasan damuwarsa.
Bubbuga bayansa ta dingayi alamar Rarrashi, lokaci guda kuma taji dumin saukar hawayensa a
Gadon bayanta, cikeda tashin Hankali ta zaroshi daga jikinta tana kallon fuskarsa, tun kafin tayi
magana yace "wllh ina sonta Ummie na!! I love her with all my heart, Ummie tun bansan meye
so ba nake d'awainiya da dakon soyayyarta, tun tana k'arama Allah ya jarabceni da k'aunarta,
hakanne ma yasa bantab'a sakewa da ko wace mace ba ballantana ma har naji ina sonta,
Ummie hatta Beebah danak'i amincewa da Aurenta duk sabida itane nak'ita sabida banajin
cewar zan iya had'a son danake mata da wata mace daban!
Amma Se gashi lokacinda takai minzalin daya kamata ta fahimci irin yanda nakeji akanta seta
gaza yin hakan Ummie! Shikenan na Rasata a lokacin danafi kowa son kasancewa da ita!!!!!!
K'uri Ummie tayi masa tana kallonsa har ya rufe bakinsa, dafa kafad'unsa tayi sannan ta fara
magana kamar haka " Khabeer dukda cewar bansan wace yarinya kakeso ba Amma hakan
yasa naji a raina cewar bazaka Rasata ba, na tabbata Allah be d'ora maka sonta don ya
hanaka ita ba, sabida ni kaina na yarda dacewar ba k'aramin so kake mata ba!
"Kasota tun tana 'yar k'arama batareda ka tab'a sanarda ko wani mahaluki ba kamar yanda
kake sanar dani a yanzu, kaine ka fara sonta tun batasan kanta ba, haka kuma bazance maka
kaine zaka Aureta ba, sabida al'amari na Aure wannan hurimi ne na Ubanji (S.w.t) a matsayina
na mahaifiyarka ina me baka shawarar cewa ka mik'a dukkan lamarinka ga Allah Khabeer, na
tabbata bazaka tab'a yin danasani ba insha Allahu, sannan nima kaina zan tayaka da addu'a
idan yarinyar alkhairi ce a gareka Allah ya baka ita, idan kuma ba Alkhairi bace a gareka Allah
ya baka wadda tafita Alkhairi!
Rungume Ummie ya sakeyi yana me zubda hawaye, tabbas abinda ta gaya masa gaskiya ne,
haka kuma babu abinda ya gagari Ubangiji, sedai bayajin cewar ze iya cire soyayyar dayakeyi
mata a ransa koda ace be sameta ba sedai ya mutu da soyayyarta a zuciyasa! Sabida sonda
yake mata a jininsa yake, yariga ya gama ratsa duk wata gab'a da jijiyar jikinsa!
Dak'yar Ummie ta samu ya d'an Rage damuwarsa sannan ta fice daga d'akin, a ranta tana
mamakin wace yarinyace haka wadda ta samu nasarar samun tsagwaron soyayyar gaskiyar
Miskilin d'anta haka? koma wacece wannan yarinyar tabbas tayi babban dace data samu
gwarzon namiji irin khabeer, wanda ya had'a duk wasu Qualites daya kamata d'a namiji ya
kasance dasu. Tabbas bazata gusheba wajen rok'a masa Allah, har seya samu cikar burinsa da
ikon Allah.
Bangaren Umaisa kuwa kuka ta fashe masa dashi wanda gaba d'aya ta kasa sanin dalilinsa,
se'a yanzu take ganin wautarta da har ta bari zuciyarta ta rinjayeta ta gaiyato *_ZAB'IN
RANTA_* cikin gidansu, da ace ta bari sun had'u a inda suka saba had'uwa wllh da duk hakan
bata faru ba, shikenan yau ta shiga uku a hannun Ya Golden!
Shiru Maheer yayi yana kallonta batareda yace da ita k'ala ba, a tak'aice yace "Dr. Yayanki ne
dama? Yarfe hannu kawai takeyi tana kuka, don hka Maheer ya gimtse fuska lokaci guda ya
rikid'e mata ya koma mata ainihin Maheer Lamid'on data sani a baya, wanda murmushima aiki
yake zame masa ballantana kuma magana, sannan ya kalleta yace " meye dangantakar datake
tsakaninki da Dr. Khabeer mahmoud?
Da mamaki ta d'ago tana kallonsa tareda tsayarda zubar hawayen datake sannan tace "he's
my Brother, shine babban yayan mu ya Khabeer din danake yawan baka lbrinsa.
Shiru yayi zuciyarsa na wani irin harbawa tareda tariyo masa irin kallon dayaga Khabeer din
yana binta dashi d'azu, kallo d'aya ya samu nasarar yiwa Khabeer d'in ya fahimci zallar
soyayyar gaskiyar dake kwance a idanun Khabeer d'in gamida kishin ta, a nan ya fara kokonto
akan maganar data dinga gaya masa kwanaki akan Khabeer d'in, cewar Khabeer yayanta ne
amma kuma sam baya sake mata sosai, sedai dukda hakan baya iya jurar zubar hawayenta
ballantana kuma damuwarta, koda ace baze rarrasheta ba sedai kawai ya tashi yabar mata
gurin kokuma ya daka mata tsawa. Sedai dukda hakan tanason shi sosai haka kuma tana
jidashi, bama shi lad'aiba kaf ahalinta zata iya sadaukar da komai sabida farin cikinsu. Shin me
hakan yake nufi *?*
Mik'ewa Maheer yayi sannan yace " its ok dear kukan ya isa haka, maza tashi ki shiga gida se
munyi waya anjima ko?
D'aga masa kai kawai tayi sannan ta mik'e ta nufi hanyar dazata kaita kaita cikin gida, shikuma
maheer ya bita da kallo zuciyarsa na harbawa.
Tana shiga perlourn kasa tafiya d'akinta tayi sabida zarginta da zuciyarta takeyi, lokaci guda ta
nufi hanyar side d'in ya Khabeer k'irjinta na dukan tara-tara dak'yar ta iya murd'a handile d'in
k'ofar ta shiga da sallama, amma kuma babu kowa a perlourn don haka ta nufi k'ofar bedroom
dinsa tana karanta duk addu'ar datazo bakinta,
Tana tura k'ofar ta bud'e don haka ta kunna kai zuwa ciki dukda irin bugun da zuciyar ta keyi
mata, a zaune ta sameshi ya dafe kansa da dukkan hannayensa tareda zubawa kapet din dake
d'akin idanu, k'arar k'ofar ne yasa ya d'ago tsumammun Golden Eyes dinsa ya zuba mata yana
kallonta! Tun kafin yayi magana ta taho da gudu ta zube a gabansa, lokaci guda kuma ta fashe
masa da kuka tace "don girman Allah ya Khabeer kayi hak'uri karka dake ni don Allah, wllh
bazan sake ba, ni kaina bansan meyasa na gaiyatoshi ba!
K'uri Khabeer yayi mata yana kallonta, musamman ma yanda take magana cikeda k'uruciya a
ciki gamida k'arfin gwiwa, kallo d'aya zakayi mata ka fahimci zallar gaskiyar abinda ke Ranta
take fad'a. kamar daga sama taji ya cillo mata tambaya kamar haka " Kina sonshi kuma zaki iya
Aurensa?
Zuba masa manyan fararan idanunta tayi cikeda zallar mamakin tambayar daya jefo mata
gamida nazarinta, tabbas tanajin Maheer a zuciyarta, haka kuma batajin zata iya b'oyewa kowa
irin son da takeyi masa, don haka bakinta yana rawa tace "Ina sonshi yaya! Kuma zan iya
zama dashi a k'ark'ashin inuwa d'aya, badan komaiba se don irin sonda yakemin gamida
nagartarsa, Pls kada kak'i fahimta ta, wllh har raina nakejin inayi masa wani irin so wanda ni
kaina bansan adaddinsa ba balle na kwatantashi.
Wani irin bugawa k'irjin Khabeer yayi, lokaci guda kuma ya saki wani irin murmushi wanda yafi
kuka ciwo sannan ya kalleta cikin ido yace " karki damu k'anwa ta, insha Allahu yayanki ze
kasance a tare dake har zuwa ranar da zaki samu cikar burinki na auren wanda kike so kinji?
Wani irin tsalle ta daka ta fad'a jikinsa tareda k'ank'ameshi tana dariyar farin ciki, zareta yayi
daga jikinsa sannan yace "so nawa zan gargad'eki akan ki dena hugging dina kin girma?
Washe baki tayi sannan tace " im sorry yayana bazan k'ara ba, sannan ta fice daga d'akin
zuciyarta fessss,
Ido ya zuba mata harta fice daga d'akin lokaci guda kuma ya dafe saitin zuciyarsa tareda
lumshe tsimammun idanunsa tareda k'udurtawa kansa cewar " indai har sonda yake mata
gaskiya ne dolene ya haqura da farin cikinsa don tabbatuwar nata farin cikin, haka kuma so tari
a rayuwa abinda mukeso bashi yake zama alkhairi ga rayuwarmu ba, don Haka zeci gaba da
addu'a akan Allah ya zab'amasa abinda yafi alkhairi a rayuwarsa, sedai abune mawuyaci ya ira
raba zuciyarsa da soyayyar Umaisah!!!!
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:31_
*_Dis page is 4 you dear sis, Aisha musa Isah (Chubad'o), kome Zm chubad'o ta zama a
sanadin potolo ne, domin kuwa itace silar kasancewa ta marubuciyar yanar Gizo, i really proud
of you my darlingâ¤_*
___________í ½í³– 8:30pm zaune suke bisa makeken daining table dinsu kamar yanda Ahalin
gidan suka saba kasancewa kullum domin yin Diner, sedai wannan lokacin ya banbanta da
sauran lokutan sab'anin na kullum,
Usman ne ya kalli Farouq yace "heyy lafiya kuwa banga Golden ba? Tab'e baki Farouq yayi
sannan yace " nima tunda na dawo office nake nemansa na kira wayansa har kusan 2 times
amma beyi piking ba,