Showing 12001 words to 15000 words out of 80273 words

Chapter 5 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2754

janyo tareda bud'e hadadd'iyan drower d'insa
dake manne a bango, wasu takardu ya shiga d'akkowa daga ciki drower d'in tamkar bazasu
k'are ba,

da'alama takardun masu mahimmancin gaske ne, yana gama xubawa yaja zip d'in ya rufe,

wata trolly d'in ya sake janyowa, sannan ya d'ebi kad'an daga cikin kayan sakawanshi ya
zuba a ciki, babban abinda ze bawa me karatu mamaki shine wasu k'ananan kaya Maheer ya
iba, wayanda sukafi kamada na jarirai ya zuba a cikin trolly d'in sannan ya jasu ya fita Dasu,

Yana fitowa masu aikin gidan suka nufoshi da sauri dan su karb'i kayan , tundaga nesa suka
fahimci irin halinda uban gidan nasu yake ciki, dan haka suka ja burki batareda sun k'arasa inda
yake ba, booth d'in motar ya bud'e tin kafin ya k'araso, dan haka yana zuwa ya jefa manyan
jakunkunan a ciki ya kulle, sannan ya figi motar da wani irin gudu, mamaki ne ya kama malam
mai gadi, dan haka ya wangale masa k'ofar get d'in tun kafin ya k'araso,

Da wani irin mugun gudu ya kwashi motar tamkar ze tashi sama ya fice daga gidan, tareda
k'udurtawa zuciyarsa cewar,,,,, komai daran dadewa baze sake waiwayar gidan ba, kamar

yanda Dady yace "ya sallamawa duniya shi, haka kuwa ze k'are Rayuwarsa a duniyar batareda
ya sake waiwayar sa ba...!!!


*_Wannan shine mafarin labarin_*


_More comment_
_More typing_


_Share pls_


*_ Zaynab muhmd CHuBaD'o�_*
_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


*_A gaskiya jiya naji matiqar dadi duba da irin comment d'in da kuka dinga zubamin, ngde sosai
Allah kuma yabar qaunar ta har'abada, yanda kuka farantamin jiya, haka nima zan faranta muku
da yardan Allah, ammafa idan banga comment yanda ya kamata ba, tofa bazaku kuma jina ba
senan da sati hudu🤣_*
*_Sanarwa ta musamman, kokuma ma ince albishirinku, Haziqan marubutan nan kokuma in
kirasu da tagwaye, JAMEELAH UMAR JANAF tareda sahibarta HAFSAT MUSTAPHA
(HAFNANCY) sun kawo muku wani irin salo wanda duniyar marubuta batatab'a zuwa da irinsa
ba, akan farashin Naira 200 kacal kowani littafi, ga wanda yake son duka biyun kuma akwai
garab'asar da marubutan sukazo da ita, inda zaku biya 300 kacal duka biyun. Wa'yannan
litattafai sune kamar haka, MALIKA MALIK da kuma KISHIN MATA, kada ku bari Abaku
lbri�_*


_Page: 8_

____________📖 tunda ya jefa motar kan baban titin daze kaishi garin Abuja yake ta faman
zuba uban gudu kamar me shirin tashi sama, a wannan yanayin abubuwa dayawa ne suka
dinga dawo masa tamkar a lokacin suke faruwa, lips d'insa ya had'e ya danne da fararen
hak'oransa sabida irin k'unar da zuciyarsa takeyi masa, lokaci guda kuma wani b'angare na
zuciyarsa ya aiyano masa cewar lallai yakamata yayi nisa da k'asar Nigeria gaba d'aya, badan
komai ba sedan muddin idan yana cikin Nigeria wata rana zasu iya had'uwa da Dady wanda shi
kansa bazeso hakan ba, a haka ya isa garin na Abuja zuciyarsa na k'una, Direct gidansa ya
nufa dake Garki, A wani madaidaicin gida yay perking wanda aka k'awata shi da kayan gini na
alatu, dukda cewar gidan ba wani babba bane sosai hakan baze hanaka ganin kyawunsa ba,
horne yayi a bakin Get d'in dan haka da sauri me gadin gidan mai suna Lawan ya wangale
masa Get d'in, da wani irin gudu ya danna kan motar ciki,

Ya jima a cikin motar bai fitoba, illa ma kifa kansa da yayi akan sityarin motar, gaba d'aya ji yayi
duniyar tayi masa zafi, haka kuma lokaci guda yaji mata sun fice masa A rai, a yanzu babu wata
mace wadda ze iya fad'ar alkhairinta a Rayuwarsa, hasalima gani yake duk mata halinsu d'ya,
a hankali ya bud'e murfin motar, lokaci guda ya ziro kyakkyawar k'afarsa ma'@bociya dogayen
yatsu waje, hakanne yay daidai da k'arasowan Get man d'insa bakin motar, cikeda girmamawa
Lawan yace "barka da zuwa Ranka ya dad'e.

Dak'ar Maheer ya k'ak'alo murmushin dole yayiwa Lawan, sabida a tsarin Rayuwarsa be yadda
da wulak'anta duk wanda Allah ya had'ashi dashi ba, koda kuwa waye, nuni yayi masa da booth
d'in motar dan haka da sauri Lawan ya k'arasa gurin ya fara sauke madaidaitan trolly d'in dake
bayan motar, a hankali ya fara takawa cikin takunsa me cikeda izzah gamida tak'ama har zuwa
babban perlorn gidan wanda aka k'awatashi da had'add'un Royal Chiar's 'yan Asalin k'asar
Turkiya.

Ajiye kayan Lawan yayi sannan ya juya dan ya koma bakin aikinsa, zubewa maheer yayi akan
d'aya daga cikin kujerun dake perlourn, lokaci guda ya saki wani irin kuka mai ban tausayi ga
mai sauraronsa, sosai yake kukan cikeda tausayawa rayuwar kansa da kuma ta k'aninsa wanda
ya kasance mafi soyuwa a gareshi, kiraye kirayen sallar da aka fara ne yasa Maheer ya tsagaita
da kukan ya mik'e, wani wani madaidaicin corridor naga ya nufa sannan ya bud'e wata babbar
k'ofa ya kunna kai ciki, wani katafaren dak'i, komai na bedroom d'in ya dace da inda aka
sanyashi tamkar d'akin turawa babu wata hayaniya a ciki, toilet ya nufa Direct nan ma ban
tsayaba seda na lek'a sabida in ganowa mai karatu wace duniyar ce a ciki, toilet ne mai girman
gaske wanda aka k'awatashi da kayan kamfanin Mayeesh salam dake k'asar Turkiyar, da gudu
na fito sabida ganin Maheer na k'ok'arin yin tsirara a gabana🤣

Kansa ya sakarwa shower cikin mintuna kad'an ya fito d'aure da towel sabida kar sallar ta
wuceshi, a gaggauce ya kammala shirin nasa sabida jin an tada ik'ama, da hanzari ya fito ya
nufi masallaci, seda aka idar da salla sannan ya dawo gida, yana shiga perlourn Direct prich d'in
dake perlourn ya nufa, dukda cewar bashida tambacin samun mutuniyar tasa a ciki,

Yana bud'ewa kuwa babu komai a ciki se ragowar guda d'aya d'akkowa yayi tareda zama bisa
kan kujera, se'a lokaci naga kwalbar giyar sosai an rubuta Brandy a jiki, ko kad'an be jira wani
cup ba ya tsige murfin ya kafata a bakinsa sannan ya wuce bedroom da kwalbar a hannunsa.



Afwan pls yau ba yawa sosai🙊

Comment
And
Share


*Zm muhd*
*(CHuBaDo)*�
_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page: 9_

__________📖 tin kafin yakai bedroom d'in ya fara tangad'i, da k'yar ya iya k'arasawa tsakiyar
d'akin sannan ya fad'i, lokaci guda wani irin nannauyan bacci ya samu nasarar d'aukesh a
wannan hali,


Tun bayan tafiyar Maheer Abdul yaketa faman kiran wayansa amma kuma bata shiga balle ma
yasan halinda yayan nasa yake ciki, tunda sauran haske yake jarraba kiran Maheer d'in amma
haryanzu da Dare ya farayi kalma d'aya ake sanar dashi itace *_Swich off_*, jefar da wayar yayi
a jikin bango sabida takaici, lokaci guda ta daki bango ta tarwatse, wani irin ihu Abdul ya saki
batareda yayi la'akari da Dare ba!! A haka baccin wahala yay awon gaba dashi a kan makeken
Royal Bed d'in Maheer d'in,

*_B'ABGARAN GIDAN ALHAJI MAHMOUD MUHAMMAD KUWA_* khabeer ne zaune bisa
d'aya daga cikin kujerun dake perlourn, gefansa kuma system ce K'irar Companyn Apple
wadda ya mayar da dukkan nutsuwarsa a kanta, Umaisa ce ta fito daga Room d'in ta, sanye
take cikin wata bak'ar jallabiya wadda aka yalwata gaban rigar da chiristel stone masu launin
ja, hakanne yasa bak'in Rigar ya baiyana ainihin kalar hasken fatarta, a hankali take takowa
tamkar wadda k'wai ya fashe ma a ciki,

A haka harta k'araso inda yake, kanta ta d'an sosa kad'an tamkar wata mara gaskiya sannan ta
kalleshi tace, " ya khaberr, dan Allah dama so nake na fad'ama idan zaka tafi office da safe zan
bika ka saukeni a gidansu Nusaibah tunda hanya ne.... Pls yaya don Allah...!

Tunda ta fara magana be d'agoba ya kalleta ba har seda takai k'arshen maganar sannan ya
d'ago manyan Golden Eyes d'insa ya zuba mata, sosai yake nazarinta sannan yace " me
zakijeyi gidansu? Kinsan dai bana son yawo ko? Shagwab'e fuska tayi kamar zatayi kuka tace
" yaya ba yawofa zanje ba fa but she's not fleeng fine thts why nake so naje gidansu pls yaya
don Allah karkace A'a...! Ta fad'a kamar zatayi kuka!

Tabe baki yayi sannan yace "its ok naji Allah ya kaimu goben, da sauri ta zauna a kusa dashi
tareda k'ank'ameshi sabida murna, murmushi kawai yayi sannan ya maida hankalinsa kan
abinda yakeyi, a ransa yana k'ara jinjinawa shirme irin na k'anwar tasa.

tashi tayi tana 'yar dariyar farin ciki sannan ta nufi Room d'in Ruman dan ta sanar da ita batun
zuwanta gidansu Nusy, A Kwance ta Samu Ruman tana bacci, murmushi tayi sannan ta fita
daga d'akin, d'akin ummie ta nufa, da sallama ta shiga madaidaicin perlourn, a zaune ta samu
ummie tanacin dambun shinkafa, da sauri ta k'arasa inda ummien ke zaune tareda washe
fararan hak'oranta, sabida a rayuwar Umaisa tana bala'in son Dambun shinkafa,

Dungure mata kai Ummie tayi sannan yace " meye kika wani zauna min a gaba kina kallon na?
Dariya Umaisa tayi sannan tace "Eyyah ummie kinfa san meya kawoni nan dan girman Allah
kisammin ko kad'an ne kinji Ummie na.... Ta fad'a kamar zatayi mata kuka, dariya ta bawa
Ummie sosai sannan ta kalleta tace " ta uwar kwad'ayi, nima k'anwata ce ta aiko aka kawo min
shi, dan haka kema sekije taki k'anwar ta baki. Zaro ido Umaisa yayi sannan tace Ummie ni
inada k'anwar da akayiwa aure ne, dama yayata kikace se'ince na taso Aunty Rumana ta dafa
min tunda munada komai,

Wani irin kallo Ummie watsa mata sannan tace "lallaima yarinyar nan, dayake cutarta zakiyi ai
gashinan kina kiranta da Aunty wanda dacan ba hakan kike kiranta ba.... Da sauri tace "Ummie
forget about this chapter nidai ki samun dambu kawai, ta fad'a tana dariya, zama tayi dirshan a
kan tattausan capet d'in dake perlourn, sannan ta fara gabzar Dambun tana xubawa Ummie
santi, seda suka cinye tass sannan ta kalli Ummie tace " wllh daga jin Dambun nan Aunty
Maryamce tayi ba Aunty Beebah ba, nifa wllh Ummie nafi son Aunty maryam sabida tafi Aunty
Beebah kirki, idanfa mukaje gidan nida Rumana sekiga tanayi mana kallon wulak'anci, nifa

wllh da yaya Golden zeji shawarana cewa zanyi karya Auri Aunty Beebah. Ta k'are maganar
tana yatsina fuska, itadai Ummie kawai kallonta takeyi harta kai aya sannan tace

"Amma yarinyar nan kin iya iskanci wllh, dan gidanku surukar tawa kike kushewa,? Turo baki
Umaisa tayi sannan tace " Ummie ai gaskiya na fad'a, kema kanki ai kinsan halinta sedai kik'i
fad'a, wllh da yaya Usman ze Aureta sena zugashi yace ya fasa, inyaso senaga k'arshen jin
kan da take tak'ama dashi, duka Ummie takaiwa Umaisa, da sauri ta mik'e da gudu tana dariya,
Ummie ma dariyar tayi, a ranta kuma tana jinjina maganar Umaisan, tabbas tasan gaskiya ta
fad'a Beebah bata da halin kirki, amma kuma batajin hakan zesa tasa a jjanye maganar Aurenta
da Khabeer, sabida ko da babu maganar aure tsakaninta da Khabeer d'in ita me rik'eta ce,
tunda ita d'in diyar k'anwar ta ce. Ta jima tana tunani akan maganar Umaisa da Umaisan ta
fad'a, sosai abin yayi mata tasiri a zuciyarta har gari ya waye,

8:00am dai dai khabeer ya fito sanye cikin k'ananan kaya, wanda suka baiyana ainihin cikar
zatinsa, mukullin motarsa ne kawai a hannunsa inda d'ayan hannun nasa ke rik'e da wani abu
kamar file, a gaggauce ya fito daga side dinsa, da alama a cikin sauri yake, kacib'us sukayi da
Dady wanda ke k'ok'arin shiga side d'in nasa, cikeda ladabi ya rissina ya gaida mahaifin nasa,
cikeda kulawa Dady yace "ina zaka kuma da sanyin safiyar nan, bayan yau ranar hutu ne son?
Shafa kansa ya d'anyi sannan yace "Abba Asbiti zani inada mara lafiyan daya kamata in duba
ne, murmushi kawai Abba yayi sannan ya bashi hanya yay gaba, a hanzarce ya k'arasa
parking space, wata bak'ar toyota benza naga ya nufa sannan ya fad'a ciki tareda ficewa daga
gidan gaba d'aya,

Khabeefr bashi ya dawo gidan ba se wajen 2:00pm, a zaune ya samu Umaisa se faman
kunbure2 take, kobi takanta beyi ba ya nufi side d'insa don ya huta, sabida sosai yakejin gajiya
a jikinsa,

Kuka ta dingayi sabida ganin ko kallonta ma beyi ba, ya Usman ne ya fito da shirin fita, da
alama shima wani abinne ya taso masa, mik'ewa tayi da sauri ta nufeshi tareda kama hannunsa
tace " pls ya Usman dan Allah naxo ka saukeni a Gaduwa Estate? A tak'ace ya kalleta yace "
wa kika fad'awa zaki fita da ranan nan? Shagwab'e fusaka tayi sannan tace " mamie na ta
sani,sannan kuma na gayama ya khabeer, shiru yayi yana kallonta na d'an lokaci sannan yace"
muje, da sauri tabi bayansa tana washe mai baki kamar taci caca,

Tunda suka fara tafiya take zuba masa surutu har suka iso Gaduwa Estate d'in, da sauri ta bude
murfin motar zata fita, wani uban kallo ya watsa mata sannan yace " wllh ki kula dakanki, naga
se wani rawar kai kikeyi, sannan kuma nan dan 4:00pm zanzo na d'aukeki kinji ko? D'aga masa
kai tayi amar taji sannan ta fice daga motar shi kuma yay gaba abinsa,
A hankali ta dinga takawa harta shiga gidan, kasancewar irin manyan gineginen nan ne masu
kamada kinin gwamnati, a hankali ta tura k'ofar glas d'in dake perlourn, Mu'allim ne ya nifota
da gudu yana cewa "oyoyo Aunty Umaisa na, da fara'a ta d'agashi tana dariya, kasancewar
suna bala'in shiri da ita, hancinsa taja sannan ta kama hannunsa suka k'arasa babban prlourn

gidan gaba d'aya, da sallama suka shiga, babu mutane a perlourn se Hajiya Mariya mahaifiyar
Nusaiba, gefanta kuma Nusaibah ce se faman kunbure2 take sabida Rashin zuwan Umaisan,
tanaji muryanta ta mik'e da gudu tayi hugging d'in ta tana dariya, itama dariyar tayi a haka suka
k'araso cikin perlourn hannunsu a sark'e cikin na juna, har k'asa ta sunkuya ta gaida Maman su
Nusaiban, da sakin fuska ta amsa mata tareda tambayarta muta nan gidan, tashi tayi tabarsu a
perlourn ta koma d'aki sabida Umaisan ta sake da k'awar tata,

Sun dade suna hira suna dariya, a haka Khalil ya shigo perlourn ya samesu, sanye yake cikin
wata blue d'in gizna wacce ta baiyana cikar zatinsa, se'a lokacin na k'are masa kallo sosai,
dogo ne sosai ma'abocin kwarjini da kuma haiba, bugu da k'ari kuma gashi kyakkyawa, fad'a
murmushinsa yayi tareda cewa " kai Ashe dai babbar bak'uwa mukayi yau a gidan namu kenan,
ya fad'a tareda zama a kan d'aya daga cikin kujerun perlourn, dariya tayi harseda fararen
hak'oranta suka fito sannan tace "Ae yau nice a gidan su Blue Eyes. Dariya yayi sosai a ransa
kuma yana jin sunan data kirashi a dashi d'in,

Nusaibah ce ta kalleshi tace " ya Khalil dan Allah ka kaimu Millonian peck mana dan Allah, shiru
yayi sannan ya kalleta yace " ku shirya muje, da sauri Nusaiba tace " yaya a shirye muke
wallahi, mik'ewa tayi da sauri ta nufi Room d'in ta, cikin mintuna kad'an se gata ta fito da mayafi
a jikinta, seda taje dakin mama ta sanar da ita sannan suka fita daga gidan xuwa perking
space, wata bak'ar Anaconda suka shiga sannan Khalil yayiwa motar key sukabar harabar
gidan gaba d'aya, seda suka biya ta *Spar* ya siya musu ice cream da kuma tarkacen su coclet
sannan suka kama hanyar Silver bed, kasancewar yafi kusa da Da Spar d'in, sosai Umaisa ta
saki jikinta tamkar tayi shekara da sanin Khalil d'in, shikuwa Khalil hakan ba k'aramin dad'i
hakan yayi masa ba, musamman idan yaji ta kirashi da Blue Eyes. Duk inda tabi Khalil kallonta
kawai yakeyi, sabida komai yarinyar tayi birgeshi takeyi,

A haka sukaita shagalinsu da Nusaiba suna dariya,

___________________

Maheer kuwa tunda ya farka a daddafe ya mik'e ya fad'a toilet yay wanka, sannan ya d'aura
Alwala ya fara jero sallolin dake kansa, yana idarwa wayarsa ya jawo ya bud'e tareda zare Sim
card d'in dake ciki, sannan ya shirya cikin wasu k'ananan kaya, inda rigar ta kasance fara sol,
wandon kuma bak'i wuluk dashi, sosai kayan suka karb'i jikinsa, kallo d'aya zakayi masa ka
fahimci ainihin murd'ewar jikinsa, duba da yanda rigar ta wani lafe a jikinsa, dukda cewar baya
cikin walwala hakan baze hanaka ganin kyawunsa ba.

wata number yay dailing wadda naga an rubuta *MUJAHEED* a jiki da babban bak'i, Cikin
mintuna kad'an mujaheed ya d'auka cikeda mamaki yace " hy friend yau ka tina dani kenan?

Murmushi kawai Maheer yayi sannan yace" kana inane haka? A tak'aice yace" ina *Silver ved*
wllh nagaji da zaman gidan ne shiyasa nazo nan dan na huta.

A tak'aice myaheer yace " ganinan zuwa, sannan ya katse kiran, car keys d'in sa ya d'auka
sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login