Showing 21001 words to 24000 words out of 80273 words

Chapter 8 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2764

tattauna akan matsalar, ba musu Abba yabi bayansa inda shi kuma Khabeer ya nufi gurin
su Ummie.

Da sauri Ummie da Mamah suka kama hannnunsa sukace " ya jikin nata? Kasa magana yayi
sabida bema san ta inda zai fara gaya musu girman matsalar Mamien ba, da sauri Umaisa tazo
ta fad'a jikinsa tareda sakin wani irin kuka kamar ranta ze fita!!! Kasa ce mata komai yayi
sabida bema san ta inda ze fara rarrashinta ba yanda take kukan ne ya fara d'aga masa
hankali, dan haka ya zarota daga jikinsa tareda sunkuyowa dab da fuskarta yace, " kukan ya isa
haka don Allah, addu'ah zakiyi mata bawai kuka ba, insha Allah zataji sauk'i kinji ko? Ya fad'a
yana share mata hawayen dake zuba a kan fuskarta. Kallonsa kawai Ummie takeyi sabida
tasan baze tab'a gaya musu komai ba akan ciwon Badi'toun, kodan karya d'aga musu hankali
ma baze gaya musu ba.

Dr. Abas ya kalli Abba yace " magana ta gaskiya Alhaji gaskiya mara lafiyar nan she's in critical
condition domin kuwa ciwon nata yakai satage d'in da a yanzu tana tsakanin rayuwa da kuma
mutuwa, dan haka ina mai baka shawar cewa ka daure ka kuma dage wajen kiyaye dukkan
abinda ze d'aga mata hankali, sannan kuma seta dage wajen ragewa kanta damuwa kodan
cigaban lafiyata. Amma insha Allah Alhaji komai zeyi daidai da yardan Allah. Ya k'are maganar
yanyiwa Abba murmushi.

Tunda Dr. Abas ya fara magana zufa take ketowa Abba, dukda sanyin Ac n dake office d'in,
babu abinda yake nanatawa se innanillahiwainna'ilaihirraji'un! Shin ta ina ze fara fuskantar
wannan matsalar datake tinkaro su? Daurewa kawai yayi sannan ya mik'e yayiwa Dr. Abas d'in
sallamah, tabbas yasan cewar dukkan musulmi mai imani yana tareda jarrabawar ubangiji,
amma kuma idan yayi hak'uri seka ga Allah ya kawo masa d'auki! Wani irin tausayin Mamie ne
ya cika masa zuciya, lokaci guda kuma hawaye ya cika masa idanu, fitowar dayayi daga office

d'in ne yaja hankalin Umaisa zuwa gareshi, da gudu ta nufeshi tareda fadawa jikinsa ta saki
wani irin kuka, a hankali ya dinga bibbiga bayanta alamar rarrashi sannan ya zareta daga
jikinsa ya dinga bata haquri kafin ya samu tayi shiru.

Yana zuwa yacewa su Ummie su tattara su koma gidan kodan sabida yaran, a nan yake gaya
musu Dr. Yace abarta ta huta se zuwa gobe zasu samu damar ganinta, ba yadda suka iya haka
suka juya Farouq da Usman suka maida su gida, inda akabar Khabeer da kuma Dady.


B'angaren Maheer kuwa tunda yabar pharmacy d'in be dire ko ina ba se gidansa dake unguwar
Garki, a nitse yay perking motar sannan ya fito, da sauri Lawan mai gadi ya k'araso gurin,
cikeda girmamawa ya yayi masa sannuda zuwa sannan ya koma bakin aikinsa,

murmushi kawai Maheer yayi sannan yay cikin gida abinsa, sosai yake jin dadin zamada
Lawan, Direct bedroom d'in sa ya nufa takalmin fatar dake Manne a k'afarsa ya fara cirewa,
sannan ya mik'e ya fara b'alle botir d'in gaban rigarsa, yana kammalawa ya nufi kafceciyar
wodrobe d'insa dake Manne a jikin katafaren bangon dake d'akin ya bud'e, wani had'add'en
white towel ya d'akko babba sannan ya d'aurashi a k'ugunsa,

Nanda nan taswirar halitatarsa ta baiyana, haka kuma cikar zatinsa, toilet ya shiga tareda
sakarwa kansa ruwa, nanda nan tunani Abdul ya ya fara kwaranya a zuciyarsa, ya jima yana
wankan sannan ya fito d'aure da towel a k'ugunsa, inda ya ratayo k'aramin towel bisa lallausar
sumar dake kansa wacce keta faman d'igarda Ruwa, a bakin dresing miror d'in dake d'akin ya
tsaya, sannan ya fara goge sumar tasa da towel d'in, wasu tsadaddun mayuka ya fiddo na
companyn OLAY ya fara shafawa, cikin mintuna kad'an ya kammala sannan ya shiya cikin wata
black jallabiya qirar companyn Emraty wadda ta baiyana hasken fatarsa.

A hnkali ya nufi inda ya cire kayan dake jikin sa kafin ya shiga wanka, takalman ya fara
kwashewa ya kaisu mazaunin su, sannan ya sunkuya ya d'auki rigar da kuma wandon, wani
cute basket ya bud'e ze jefa kayan, ba zato yaji kamar abu ya sokeshi daga jikin rigar, a nitse ya
fara warware rigar dan ganin abinda ya soken shin, bisa ga mamakinsa seyaga d'an kunnen
mace, da mamaki ya d'aga d'an kunnen yana kallo tamkar wani me son tina wani abu, d'an
kunne ne k'irar indian fashtion me azabar kyau, se faman baza k'yalli yake, kalo d'aya zakayi
masa ka fahimci me tsada ne.

Ya jima yana kalon d'an kunnen tamkar baze daina ba, wani siririn tsaki ya saki tareda dukan
bangon d'akin yafirta "Queen of tears, tareda datse lips d'in sa da hak'oransa.

Comment
Nd
Share



*Zm chubado*�
_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:15_

___________📖 wani siririn tsaki yaja tareda jin wani irin haushinta, a ransa yace "yarinyar nan
bazata fita a rayuwata ba muddin ban nuna mata iyakarta ba, wani sirin tsaki ya k'ara saki
lokaci guda kuma ya saki tattausan murmushi, tareda maida hankalinsa kan d'an kunnen dake
hannunsa, k'ara fad'ad'a murmushinsa yayi, lokaci guda ya fara tuna had'uwarsu da Umaisa ta
farko a Silverbeard, har zuwa yanzu da suka sake had'uwa da ita a phamarcy, komai na
yarinyar idan tayi tana tuna masa da Abdul,

musamman yanda ya lura tanada saurin tsorata, abu kad'an ne yake firgita ta, babban abinda
yasa yarinyar take bashi haushi guda d'aya ne yanda take da arahan hawaye, sabida a
rayuwarsa ya tsani mutum me saurin kuka musamman ma mace, tab'e baki yayi tareda d'aga
kafad'arsa, sannan yace " meyasa ma nake b'ata lokacina ina tunanin wannan urgly yarinyar
bayan itama macece? Lokaci guda ya sakejin wani irin haushinta yana kwaranya a zuciyarsa,
tsaki yaja mai sauti sannan yace "i have to teach her a gud lession wanda ko mai kamada ni
bazata sake marmarin ta dinga bibiyar Rayuwarsa ba, a haka ya fice zuwa masallaci.


Abba ne ya kalli khabeer yace "A gaskiya lamarin ciwon nan na Badi'atou yana matik'ar
d'agamin hankali, musamman yanda Dr. Abbas muhammad yayi min bayani akai!!!.

Murmushin k'arfin hali khabeer ya saki irin nasu na k'asaitattun likitoci, sannan yace " Abbah
hak'ik'a jikin mamie wannan karon yayi tsanani sosai, sabida yanda take matsawa kanta gamida

sanyawa kanta damuwar datafi k'arfinta, wllh Abba muddin aka sake bari ta kuma shiga irin
wannan halin to a kwai yiwuwar ta rasa Rayuwarta ma gaba d'aya, shiru Abbah yayi yana
nazarin maganar khabeer d'in, murmushin k'arfin hali Abbh ya saki sannan yace "hak'ik'a
kowani halitta a duniya yana da irin k'addarar da Allah yake jarrabarsa a Rayuwa, mai imani
shine wanda yake karb'ar dukkan jarrabawar da Allah ya aiko masa, dan haka nayi imani da
Allah haka kuma na mik'a dukkan amarina a gareshi, idan har wa'adin Badi'atou yazo koda ciwo
ko babu ciwo wllh seta tafi, dan haka kadena fadin haka Son Allah dai ya bata lfy kwai. Cikeda
damuwa khabeer ya amsa da "Ameen Abbah, a haka suka suka fito farfajiyar Asbitin suna d'an
tab'a hira jefijefi.

***********

*KADUNA STATE*

Abdul ne zaune cikin k'asaitaccen perlourn Maheer wanda a yanzu ya koma tamkar nasa,
gefansa kuma tarin takardune da kuma system, sosai ya mayar da hankalinsa akan system
d'in, kalo d'aya zakayi masa kasan abinda yakeyi is importan, turo k'ofar perlourn akayi babu ko
sallama, hakanne yasa ya mayar da dukkan hankalinsa ga k'ofar dan ganin wanda ya shigo
d'in,

Hajiya Murja ce tareda wani saurayi a bayanta wanda baze wuce sa'an abdul d'in ba a tsaye,
kallo d'aya yayi musu ya d'auke kansa tareda cigaba da abinda yakeyi,

Tabe baki tayi sannan ta kalli matashin saurayin tace "Mustapha kadaiga yanda perlourn yake
ko? Fatana dai Allah yasa yayi maka, idan kuma bemaka ba se mukoma wncan part d'in ka
zab'i wanda yayi maka tunda ba laifi gidan a kwai girma, ta k'are maganar tana kallon fuskar
mustaphan,
Washe baki Mustapha yayi sannan yace "a'a Mama wllh nan d'in ma yayi min sosai, sabida
komai ya dace da irin Zab'ina tamkar wanda ya shirya perlourn yasan Zabin Raina, wani
k'asaitaccen murmushi tayi irin na nuna isar nan sannan tace "nayi farin ciki daka zab'i nan d'in,
dama kai ya dace ka zauna a ciki, ga bedroom d'in can seka shiga da kayanka ciki, inayaso
shikuma Abdul din seya tattaro kayansa da kuma sauran kayan D'angiyan yayan nasa ya koma
d'akin waj....... "Enoug malama, Abdul ya katse ta cikin d'aga murya gamida zafin rai, nunata
yayi da yatsa, sabida b'acin Rai jikinsa banda rawa babu abinda yakeyi, nan da nan zuciyarsa
ta fara tafasa sabida magana data jefi yayansa kuma mafi soyuwa a zuciyarsa da ita, wani
banzan kallo yake binta dashi sannan yace "heeey you wiked women, stop saying wa'yannan
banzayen maganganun naki akan Yayana, idan ba hakaba wllh i will teach you a good lession
wanda harki mutu you will never foget it in your life....! Ya k'are maganar yana dukan k'aramin
table d'in glass d'in dake gabansa cikeda tsantsar b'acin Rai.

Kasa magana Hajiya murja tayi sabida tsabar yanda ta firgita da lamarin Abdul d'in, a Ranta
tace " au ashe dama yaron nan shima dan iskan kansa ne ban sani ba! To kodai shima ya fara

shan wani abunne?? tabbas na rabu da bukar kuma ga habu an haifa..... "Mama ya zaki tsaya
yaro k'arami yana gaya miki magana tamkar wata sa'arsa, wllh mama bazan k'yaleshiba sena
koya masa yanda ake girmama manya, Mustapha ya fad'a cikeda b'acin Rai, tareda nufar inda
Abdul ke tsaye!
Murmushin mugunta Abdul ya saki tareda fara k'ok'arin kwancen belt d'in Wandonsa, da sauri
Hajiya murja ta fara k'ok'arin tsaida mustapha, sabida harga Allah ta gama tsorata da lamarin
Abdul d'in, musamman yanda takaga jikinsa har wani rawa yakeyi kamar ana kad'a masa gangi,

A fusace Abdul yayi kansa, nan suka kaure da fad'a, abinka da maji k'arfi nan da nan Abdul ya
had'awa mustapha jini da majina, seda yayi masa lilis sannan ya k'yaleshi, banda ihu babu
abinda Hajiya Murja takeyi wai Abdul ze kashe mata d'a, har farfajiyar gidan ta fita tana ihub
neman d'auki, amma kaf ma'aikatan gidan babu wanda ya kalli inda take ballema tasa ran zasu
taimakawa mustaphan, haka ta gama kururuwarta babu wanda ya saurareta dan haka ta kwasa
da gudu ta koma perlourn,

A fisace Abdul ya kinkimo jakar mustapha ya jefata waje tareda jifansa da wani irin kallo wanda
yafi kamada na muzanci sannan yace " dalla malam tattara sauran k'azantar ka ka fice daga
prlourn nan tun kafin nayi maka lahanin da Uwarka zata kasa ganeka!!

Sannan ya sake nuna Hajiya Murja da yatsa yace "kekuma daga yau zan nuna miki cewar nima
cikakken d'an bariki ne, ta yanda zan gagari duk wani motsinki a rayuwa, ke barima kijima na
fad'a miki wllh yanda kika saka zuciyata ta d'an d'ani bak'in cikin abinda kika dad'e kina aikata
mana wllh kema sena sakaki kuka da idonki, ya k'are maganar yana huci...!!
Da sauri mustapha ya fara yunk'urin tashi daga inda yake kwance, hancinsa banda jini babu
abinda yakeyi, Rungumeshi Hajiya Murja tayi tareda rushewa da wani sabon kuka, sannan ta
kalli Abdul tace " tabbas nayi sake d'an zaki ya girma, ammafa ka sani haryanzu sunana Murja
ban canza ba, kamar yanda ba'a canzawa tuwo suna, Narantse da Allah wllh sekayi nadamar
wannan abinda ka aikatawa wannan yaron, haka kuma sena sa shigowa gidannan ta
gagareka bama iya wannan perlourn ba, zan nuna maka cewar wanda ya rigaka kwana dolene
ya rigaka tashi, ta k'are maganar tareda jan hannun mustapha suka nufi k'ofar fita daga perlourn
tana huci kamar wata macijiya, harta d'ora hannunta akan handile d'in k'ofar zata murd'a Abdul
yace " heeeeyyy wiked women, lets start the game with killer smile. K'ura masa idanu tayi
zuciyarta na tafasa kamar zata mutu sabida bak'in ciki,

Tana fita motarta suka shiga itada Mustapha dan takaishi clinic, a fisace tayiwa motar key
sannan figeta zuwa get, nan da nan mai gadi ya wangale mata get ta danna hancin motar zuwa
waje, wani baban pravet Hospital suka nufa dake cikin Malali, cikin mintuna kad'an suka karb'i
Mustaphan tareda bashi taimakon gaggawa, seda suka tabbatar jinin dake zuba daga hancinsa
ya tsaya sannan suka rubuta masa magunguna harda pain Reliever a ciki suka sallamesu suka
nufo hanyar gida, tun a hanya Hajiya Murja take neman layin wayar Dady amma kuma ta kasa
samunsa, hakan ne yake matik'ar k'ara bata takaici.

B'angaren Abdul kuwa, tun bayan fitar Murja ya shiga zarya a d'akin yana tinanin ta yanda ze
b'illowa al'amarin tun kafin Dady ya dawo, yana tsaka da wannan tunanin ne yaji k'arar tsayuwar
motar Dadyn, k'irjinsa ne ya buga da k'arfi amma kuma ya dake, cikeda makirci Abdul ya fara
k'ok'arin k'ak'alo hawaye, kasancewar yanada arhan hawashi cikin mintuna kad'an kuwa ya fara
ambaliyar hawaye kamar an kunna fanfo, A haka ya fito fito daga part d'in hanayensa rik'e da
cikinsa yana wani irin kuka tareda kiran sunan Dady, tun kafin Dady ya ida fitowa daga motar
yakejin ihun Abdul, A rud'e Dady ya bud'e murfin motar tun kafin Driver ya gama parka motar,

Abdul na k'yalla ido yaga yanda Dadyn ya gama rud'ewa ne yasa ya wani fad'i k'asa yana juyi
kamar wanda za'a zare masa Rai, da wani irin mugun gudu Dady ya isa gurin da Abdul yake
kwance, in les than 2minute ma'aikatan gidan sun zagayesu, hakanne yay daidai da k'arasowar
Hajiya Murja, wani mahaukacin horn ta saki, ba shiri Bala mai gadi yaje ya bud'e mata get d'in,
cikeda k'warewa ta danno hancin motar zuwa farfajiyar makeken gidan, tun kafin ta k'arasa
parking space ta kashe motar, wani irin ihu Abdul ya sake saki tareda narkewa a jikin Dady
tareda k'ank'ameshi yana kuka kamar gaske, hakanne yajawo hankalin Hajiya zuwa gurin, tsaki
ta saki tareda k'arasawa dan ganin abinda ke faruwa,

Tana zuwa gurin tayi truss tareda bin Abdul d'in da kallon mamaki, cikeda gadara tace "tace
haba Alhaji don Allah wai meyasa kaketa biyewa wannan yaron har haka ne? Wllh ba wani ciwo
dayake damunsa kawai tsabar k'warewa ce a iya Drama, ka dubafa kaga irin dukan da yaron
nan yayiwa mustapha kamar ze kashemin shi, sannan kuma dan renin hankali ya wani zo yana
juyi kamar wanda za'a zarewa rai? ta fad'a tanata faman hura hanci kamar wata zakanya,

Shiru Dady yayi yana kallonta sabida mamakin halinta yama kasa magana gabad'aya, " Alhaji
ka gafarce ni don Allah, amma dole ne mu fadi gaskiya akan ainihin abinda ya faru, Musa ya
fad'a, sannan ya cigaba da cewa "magana ta gaskiya wancen yaron shiya fara takalar me
gidanmun Abdul da fad'a, amma kuma duk da haka Abdul d'in be kulashi ba, daga k'arshema
shi mustaphan muka gani ya dunk'ule hannu ya gabzawa Abdul d'in a ciki kamar ze kasheshi,
tun daga nan Abdul ya yanke jiki ya fad'i a bakin k'ofar part d'in mai gida Maheer, cikin ikon
Allah kuma se gaka nan ka dawo.

kallonsa kawai Hajiya Murja takeyi tareda sakin baki,

kauda kai Musa yayi da sauri sabida kallon datake binsa dashi sannan ya kalli abokan aikinsa
yace "koba haka akayi ba?

Da sauri suka amsa da tabbas kuwa Musa haka akayi akan idonmu akayi komai, kallonta ta
mayar kan Abdul a ranta tace " lallai tsugune bata k'aremin ba, hakanne yay daidai da saukar
idonta cikin na Abdul, wani d'an iskan kallo ya jefa mata taredayi sakar mata wata uwar harara,
a fisace taja hannun Mustapha sukayi cikin gida, inda shi kuma Dady suka kama Abdul suka
sakashi a mota dan su kaishi Asbiti.

*GENERAL HOSPITAL ABUJA*

Mamie ce kwance kance bisa d'aki na musamman, gefanta kuma Ummie da kuma Mama, se
kuma Ameerah daketa faman zuba surutu, A haka su Ruman da Umaisa suka shiga d'akin
hannunsu d'auke da manyan ledoji wa'yanda ke shage da kayan marmari, da sallamah suka
shiga d'akin, mamah ce ta amsa musu sallamar sannan tace "tun d'azu se yanzu kukai R'ayin
isowa aida kun sani ma kunyi zamanku tunda muma yanzu zamu tafi gidan, Ummie ce ta
karb'a maganar tace " hmm kina manta sha'anin Drivern nasu, ekace bakisan halin Farouq da
shirita ba, hakanne yayi daidai da Shigowar Farouq d'in dan haka ya kwabe fuska yace "Eyyah
Ummie nine ma shiriricin😕 ?

Dariya su Ruman suka saki ciki kuwa harda Mamie wadda ke kwance tana jinsu, masha Allah
jikin Mamie yayi sauk'i sosai, sedai yanayin jikin baikai a basu sallama ba shiyasa aka bari ta
sake warwarewa sannan a sallamesu.






*Comment*
*Nd*
*Share*


_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:16_

___________📖 Hira suka dingayi suna dariya duk dan su d'ebewa Mamie kewa, ko babu
komai zata rage yawan damuwar datake damunta, a haka khaber ya shigo d'akin ya samesu,

kallo d'aya zakayi masa ka fahimci a kwai gajiya a taredashi, d'aya daga cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login