Showing 42001 words to 45000 words out of 80273 words

Chapter 15 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2753

nufi hanya tana murgud'a mata mazaunai harta fice daga d'akin, Abbah ta
gani kawai a daining se kuma Ruman da ya Khabeer suna Breakfast, kusa da Abba taje ta
zauna tareda fad'ad'a fara'arta tace "My Abie ina kwana?

Shafa gefan fuskarta Abba yayi sannan yace " lafiya lau sweetheart, fatan Babyn Abba ta tashi
lfy? Washe baki tayi sannan tace "na tashi lfy mah Abie.

Se'a lokacin ta kalli ya khabeer tace "morning ya Golden .

D'ago manyan tsimammun Golden Eyes d'insa yayi ya zuba matasu har tsahon 3minute yana
nazarinta, sannan ya maida hankalinsa kan chips din dayake ci, haka kawai idan ya kalleta
yanzu seya kasa gane ma'anar canjin dayake tareda ita, musamman idan tana gudanar da
wasu abubuwan seyaga ita kad'ai tana murmushi, gashi sam batason zama a perlour kamar
yanda ta saba kullum tana d'aki sekace wata Amarya. Tsaki yayi tareda mik'ewa ya kalli Abba
yace " Abba ni zan wuce Office. Da sakin fuska Abba yace "to Allah ya bada sa'a son.

Kwab'e fuska Ruman tayi sannan tace " ya Golden yune fa Birthdayn Aunty Beebah, don Allah
ya khabeer kaje damu idan zaka, d'azu naji Tana gayawa Ummie. Wata uwar harara ya wuga
mata sannan yace" ba inda zakije magulmaciya, wato lab'e ma kikeyiwa mutane shiyasa ma har
kikaji maganar birthday d'in ko?

Turo baki tayi sannan tace "a'a wllh ya khabeer ba lab'e nakeyi ba, ummien ce da kanta ta fad'a
min d'azu danaje d'akinta gaida ita. Ta k'are maganar tana kallonsa,

Kallonta Umaisa tayi sannan tace " kema maganin ki, ni wllh Abba bana ma son shiga sabgar
Wannan Aunty Beebahn, sabida gabad'ayanta bata da mutunci sosai kamar Aunty Maryam,
wllh Abba dama ka hana Auren yaya Golden da i........ "Keep quete mara kunya kawai! khabeer
ya katseta ta hanyar daka mata wata shegiyar tsawa me firgita zuciya, ni sa'anki ne da zaki
dinga magana a kaina kamar wani tsaranki?
_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*

*_Jama'a Assalamu'alaikumí ½í¹. Ina makaranta litattafan hausa da kuma nazarinsa?_*
*_ina me sanar daku cewar, Shahararriyar marubuciyar nan wadda tayi fice a cikin duniyar
marubuta wato Sis NAJA'ART, tazo muku da sabon salon da ba'a tab'a zuwar muku da
kamarsa ba a duniyar marubuta ba, a cikin littafinta me taken FANSAR RAI.!!! littafin daya tara
tsagwaron sark'ak'iya a cikinsa mai wahalar warwarewa, maza ku garzaya ku nemu naku akan
farashi naira 200 kacal�_*



_Page:28_

___________📖 Tun kafin a rufa sati su Hajiya Murja suka fita haiyacinsu, duk sunbi sun kod'e
sun jeme tamkar basu ba, sabida yanda rayuwa ta juya musu, tun ba'aci litinin da talata ba tuni
suka sare da Al'amarin maheer d'in, sabida duk yanda suke zaton sa ya zarce tunaninsu, Binta
'yar kwabo kuwa ta tsinewa Hajiya Murja yafi cikin kwando dubu, sabida a cewarta wai duk itace
ta jefasu a cikin halinda suke ciki,

Wata Ranar Asabar d'in k'arshen mako ne Hajiya Murja tana goge kujerun k'arfen dake
farfajiyar Garding din gidan, wanda aka tanada domin hutawa ta musamman, akan hanyarta na
komawa ne ta cake da wani dogon k'arfe wanda Babu komai a jikinsa face tsatsa, nan ta
durk'ushe a gurin tana kurukuwar neman d'auki, Victoria ce ta nufota da sauri fuskarnan Babu
annuri balle a samu tausayawa a cikinta tace "ubanka ka tsayayi a nen? Tun kafin tayi magana

taji saukar bulala a gadon bayanta, seda tayi mata lilis sannan ta kwasheta ta jefa a d'aki ta
Rufeta da mukulli.

*SUSHMER INTERNATIONAL HOSPITAL ABUJA* sosai Dady yake samun kulawa a
k'ark'ashin jagorancin Dr.khabeer mahmoud Muhammad, sosai khabeer yakejin Dady a Ransa
tareda nuna duk wata tausayawarsa gareshi, don haka wata irin shaguwa gamida sabo na
musamman ya shiga tsakanin Dady da khabeer, wasu lokutan idan Dady yana tareda Khabeer
yakanji wani irin bak'on yanayi a tareda khabeer d'in wanda shi kansa yakan gaza gane ma'anar
hakan,

b'angaren Maheer shima ba'a barshi a bayaba yanayin iya bakin k'ok'arinsa wajen kulawa da
mahaifin nasa, dukda cewar baya iya zuwa Asbitin da Rana har se sanda Dadyn yake bacci
sannan yake zuwa, sosai yakejin kewar mahaifin nasa, amma kuma babu yadda ya iya dole ne
yaci gaba da hak'uri har zuwa ranar da komai ze daidai ta.
Yau ta kama monday ne, don haka tun safe Umaisa ta shirya cikin uniform dinta don zuwa
makaranta, d'akin Baba ta shiga da sallamarta, a bakin gado ta samu Baba ta rafka uban
tagumi, dariya Umaisa tayi sannan tace "ke fitinanniyar tsohuwa meye matsalarki ne haka?
Cire tagumin Baba tayi sannan ta fashe da kuka harda sharar hawaye, zuru Umaisa tayi tana
kallonta sannan tace" ikon Allah yau naga abinda ya isheni ni Fatimah! Me nayi miki zaki sani a
gaba kinamin kuka?

Bakin zaninta ta kama tana aikin sharar hawayen dake fuskarta tareda fad'in "Ya naga abinda
yafi Qarfina ni Binta!! Wllh gabad'aya lamarin Mamuda ya gama tsayamin a rai, yo hakane
mana 'yar nan, ace gaba d'aya lamarin gidan mutum an gama cikashi da yahudanci kala-kala?
yanzu fisabilillahi ki kalli yarannan su Khabeeru da Faruku gaba d'ayansu sun zama magidanta
amma babu Aure kuma duk yabi ya zuba musu ido sekace wani sakare? nikam wllh inajiyewa
kaina tsoron abinda zeje yazo, nan kuma gaki ga Rumana dukkan ku Nono ya gama yi muku
sammako a k'irjin ku, Babu mijin Aure kuma dukda hakan ya zuba muku ido yana kallonku wai
ku karatu. ta k'are maganar tana sharar k'wallah.

Tinda ta fara magana Umaisa ta had'e rai tanayi mata wani kallo, tab'e baki tayi sannan ta mik'e
tace" lallai ma tsohuwar nan kin zak'e dayawa, to ai seki samomana mazajen da zamu aura d'in
tunda akanki muke zaune, ni wllh nazata ma wani abin arzik'in ne yake damun ki shiyasa ma na
tsaya ina b'atawa kaina lokacin sauraronki. Ta fad'a tana k'unk'uni, wata uwar harara Baba ta
zabga mata, sannan tace "yau naji tsigalalliyar yarinya, waiyyo Allah na binta! To kinga Uwar ki
Badi'atou kikayiwa da ubanki Mamuda, shegiya kod'ad'd'iya me zubin sadakar yallah.

Murgud'a mata baki Umaisa tayi sannan tace " oho dai naji d'in, ai wllh garama ni inada kyan
fasali, kekuwa daza'a kasaki a faranti ma wllh Babu me d'aukarki sadaka ma ballantana da
kud'insa, ta fad'a tana juyi a gaban Baba.

Tab'e baki Baba tayi sannan tace "ai duk tsiyarku dole ne kuyi aure yau da kaina ba aikeba zan

samu Mamudan inyaso se'inga ta tsiya, washe baki Umaisa tayi sannan tace " oho dai nidai ba
yanzu zanyi Aure ba har sekin mutu sannan zanyi Aure don haka duk bala'inki sekin mutu
zamuyi shagalin Bikin gidannan, ta fad'a tana dariyar tsokana tareda murgud'a mata mazaunai
harta fice daga d'akin, Abbah ta gani kawai a daining se kuma Ruman da ya Khabeer suna
Breakfast, kusa da Abba taje ta zauna tareda fad'ad'a fara'arta tace "My Abie ina kwana?

Shafa gefan fuskarta Abba yayi sannan yace " lafiya lau sweetheart, fatan Babyn Abba ta tashi
lfy? Washe baki tayi sannan tace "na tashi lfy mah Abie.

Se'a lokacin ta kalli ya khabeer tace "morning ya Golden .

D'ago manyan tsimammun Golden Eyes d'insa yayi ya zuba matasu har tsahon 3minute yana
nazarinta, sannan ya maida hankalinsa kan chips din dayake ci, haka kawai idan ya kalleta
yanzu seya kasa gane ma'anar canjin dayake tareda ita, musamman idan tana gudanar da
wasu abubuwan seyaga ita kad'ai tana murmushi, gashi sam batason zama a perlour kamar
yanda ta saba kullum tana d'aki sekace wata Amarya. Tsaki yayi tareda mik'ewa ya kalli Abba
yace " Abba ni zan wuce Office. Da sakin fuska Abba yace "to Allah ya bada sa'a son.

Kwab'e fuska Ruman tayi sannan tace " ya Golden yune fa Birthdayn Aunty Beebah, don Allah
ya khabeer kaje damu idan zaka, d'azu naji Tana gayawa Ummie. Wata uwar harara ya wuga
mata sannan yace" ba inda zakije magulmaciya, wato lab'e ma kikeyiwa mutane shiyasa ma har
kikaji maganar birthday d'in ko?
Turo baki tayi sannan tace "a'a wllh ya khabeer ba lab'e nakeyi ba, ummien ce da kanta ta fad'a
min d'azu danaje d'akinta gaida ita. Ta k'are maganar tana kallonsa,

Kallonta Umaisa tayi sannan tace " kema maganin ki, ni wllh Abba bana ma son shiga sabgar
Wannan Aunty Beebahn, sabida gabad'ayanta bata da mutunci sosai kamar Aunty Maryam,
wllh Abba dama ka hana Auren yaya Golden da i........ "Keep quete mara kunya kawai! khabeer
ya katseta ta hanyar daka mata wata shegiyar tsawa me firgita zuciyar wanda akayiwa. ni
sa'anki ne da zaki dinga magana a kaina kamar wani tsaranki?

Shiru tayi tareda k'ank'ame Abba kamar zata shige masa masa ciki, kasa d'agowa tayi sabida
yanda ta gama tsorata dashi, tsaki yayi sannan ya fice daga gidan zuciyarsa a dagule, koda
yaje office ma be wani zagaya wrds d'in kamar yanda ya saba ba, sabida gaba d'aya baya cikin
yanayi mai dad'i key ya murzawa office d'in sabida baya soma wani yazo ya takura masa.
Se wajen 4 daidai sannan ya bud'e k'ofar sabida zuwa masallaci, a hanyarsa ta komawa office
d'in sukai kacib'us da Dr. Abdullah, wanda ke sanye cikin riga da wandon farin boyal wanda
sabida haskensa har farar singlet d'in jikinsa ana gani, tab'e baki khabeer yayi sannan ya rab'a
ta gefansa ze wuce, tareshi Dr. Abdullah yayi sannan yace " ohhh khabeer wai har zuwa wani
lokaci zaka canza hali ne malam?

Tureshi khabeer yayi sannan yace "kaga malam i need to rest don Allah bana son wani dongon
surutun ka don Allah! Kasak'e Dr. Abdullah yayi yana kallonsa, dan haka ya matsa ya bashi
hanya ya wuce, Direct d'akin da aka kwantar da Dady ya nufa don ya sake duba yanayin jikin
nasa, da sallama ya tura k'ofar glass din dake d'akin tareda kunna kai zuwa ciki, a xaune ya
sameshi yana yana kallon News, da sakin fuska Khabeer ya k'arasa gareshi tareda zama a
gefansa, murmushi dady yayi irin na Dattijawa sannan yace " sannu da zuwa Dr.

B'ata fuska Khabeer yayi sannan yace "har sonawa zan cigaba da tuna maka cewar nima
tamkar d'a nake a gareka Alhaji? Murmushi Dady yayi sannan yace " ai sanin hakanne ma
yasa nake kiranka da Dr. Sab'anin kai dakake kirana da Alhaji.

Shafa lallausar sumar dake kansa Khabeer yayi sannan yayi murmushi yace " ai hakan ma
tamkar manuniya ce dazata nuna maka tabbacin cewar Dr. Khabeer Mahmoud d'ane a gareka
Dady.

Hannunsa Dady ya mik'a tareda shafa kan khabeer d'in , nan da nan kewar gudan jininsa suka
cika zuciyar sa, se'a yanzu yakejin cewar tabbas ya tabka babban kuskuren da baze tab'a iya
gyarashi ba, yanzu ta ina ze fara neman gudan jininsa? Wasu zafafan hawaye ne masu zafi
suka shiga yi masa zarya a kan fuskarsa zuciyarsa nayi masa zafi bisa abinda ya aikatawa
gudan jininsa haka kuma jajirtaccen d'ansa maheer!

Dafa kafad'unsa khabeer yayi tareda fad'in "ya salam! Haba Alhaji don Allah, meyasa kake
zubarda hawaye irin haka bayan kuma kasan condition d'in da kake ciki? Murmushi Dady
yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace " hak'ik'a idan wani babban al'amari ya sark'e zuciyar
d'an Adam yakan zama mai wuyar warwarewa, musamman idan abubuwa biyu sukaci karo da
juna sekaga an gagara shawo kan matsalar balle akaiga warwareta Docter. A halin danake ciki
a yanzu babu wani magani wanda ze iya zama maganin damuwata face Yawan ambaton Allah
da kuma neman agajinsa! Ya fad'a tareda fashewa da wani irin kuka mai tab'a rai.

Shiru Khabeer yayi yana nazarin maganganun Dady, wanda ya kasa warwaresu balle ya
fahimci ma'anarsu, mik'ewa yayi zuciyarsa babu dad'i, a matsayinsa na likita dole ne yayi dik
me yuwuwa yaga ya datatar da zubar hawayen wannan adalin dattijon kobabu komai a k'alla ze
samu nutsuwar zuciya, hugging d'insa khabeer yayi a ransa yana mai tausayawa Masa.
Maheer ne zaune bisa dank'areriyar Royal chir d'in dake perlourn. Inda Hannunsa ke sanye
cikin system d'in sa yana typing, seda na matso dabdashi sannan na fahimci sak'o yake
k'ok'arin turawa, seda ya kammala rubuta sak'on sannan ya turawa Baffa Gid'ad'o ta Email d'in
sa.
*KADUNA STATE*

Sosai hankalin Abdul a gama tashi, lokaci guda kuma dik yabi ya rame sabida Rashin
kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, Dukda irin kulawar dayake samu agurin baffannin nasa,

sosai suke kwamtar masa da hankali inda wani b'angaren kuma suka sa aka tsananta addu'a
akan b'atan Dadyn.

Wayar Baffa gid'ad'o ce tayi k'ara alamar shigowar sak'o, sharewa yayi batareda ya dubaba,
sabida tashin hankalin dayake ciki ya wuce munzalin tsayawa duba massage, Baffa Umaru ne
yace "zuwa yanzu kam gaskiya ya kamata ace mun d'auki mataki akan b'atan Lamid'o, sabida
sam be kamata muzubawa al'amarin idanu ba. " tabbas kam maganarka gaskiya ce Baffa Iyah
ya fad'a cikin harshen fulatanci, sannan yaci gaba da cewa "taya zamu zuba ido muna kallon
mace tana juyamu sekace wasu sakarkaru? Gaskiya we have to take some action akan wannan
babban al'amarin dake shirin tinkaro mu.

Qarar wani sak'on ce ta sake shigowa wayar Baffa gidad'on, tsaki ya d'anyi sannan ya maida
hankalinsa zuwaga wayar don ganin sak'on menene haka aketa faman turo masa dashi ne
haka???
_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*

*_Yau page d'in naki ne me gaiya me aiki our Boss (REAL MOMYN AFRAH). Na mallaka miki
shi halak malak kiyi duk yanda kikaga dama dashi mallakinki ne, kome Intelligent writers suka
zama a Duniya kece sanadin faruwar hakan, don haka muna alfahari dake Aunty maryma Allah
kuma ya Qaramiki lfy our bossâ¤_*
_Page:29_

Banyi Editing ba🙅â€â™€ï¸

___________📖 Yana duba sak'on da aka turo masa yay zumbur ya mik'e tsaye, lokaci guda
kuma ya xube akan gwiwoyinsa tareda kai goshin sa k'asa don yin godiya ga Allah (S.W.T),
sarkin da jinsa da ganinsa basa shud'ewa. Nan Baffa Gidad'o ya shiga yiwa Allah kirari tareda
ambaton Ubangiji da sunayen dayafiso kuma yafi son a rok'eshi dasu *(Al-Haiyyu Al-Qaiyyum)*
sannan ya d'ago yana mai fad'ad'a murmushinsa a garesu,

Kallon mamaki dukansu su Ukun suke bin Baffa Gidad'on dashi, Baffa Umaru ne yayi k'arfin
halin cewa "Gidad'o wai meyake faruwa ne haka? Ya kamata ka sanar damu abinda ke faruwa

ko muma masamu hankalin mu ya kwanta, murmushi Baffa Gidad'o ya sakeyi a karo na biyu
sannan ya fara magana kamar haka "hak'ik'a masu iya magana sunyi gaskiya da sukace kyan
d'a ya gaji Ubansa, sannan kuma dukkan abinda bawa ya gaza yiwa kansa muddin ya mik'a
al'amarinsa ga Allah to Babu shakka Ubangiji ze isar masa.! Kallonsa kawai su Baffa Umaru
sukeyi ba tareda kowannensu yace dashi k'ala ba.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace " Lamid'o dai yanzu baya tareda Hajiya Murja, a yanzu
haka yana nan a k'ark'ashin kulawar Maheer. Zabura Abdul yayi ya mik'e tsaye tareda zubawa
Baffa Gidad'o manyan idanunsa wayanda ke cikeda k'walla yace "dnt say that Baffa Gidad'o pls,
how is that possible ace Dady yana tareda ya Maheer bayan dukan mu musan cewar ya
Maheer ya dad'e da barin cikin ahalinsa? Idan ma kunayin hakan ne don ku kwantarmin da
Hankali don Allah ku dena na rok'e ku, karku mantafa nima musulmi ne mai imani kamar kowa,
don haka na yarda da k'addara maikyau ko mara kyau kuma na shirya karb'arta a duk yanda
tazo min!

Takowa Baffa Gidad'o yayi har zuwa gaban Abdul d'in sannan ya dafa kafad'unsa yace "tabbas
dukann mutum mai imani dole ne ya yarda da dukkan k'addarar da Allah ya aiko masa da ita
Abdul, kamar yanda kaji na fad'a to haka maganar take *KAYARDA DANI* cewar mahaifinka
yana tareda d'an uwanka Maheer, don haka yanzu base anjima ba zamu kama hanyar Abuja
don muje mu duba lafiyar Lamid'o.

Haka kuwa akayi kamar yanda Baffa Gidad'o ya fad'a hakanne ya kasance, Inda Baffa Umaru
ya kwashesu a cikin d'aya daga cikin motocin gidan suka kama hanyar Abuja. tofa sedai muce
a sauka lfy mutanan yola zasu Abuja�

*LEGISLATIVE QUATER APO ZONE E ABUJA*, Umaisa ce kwance bisa madaidaicin gadon
dake d'akinta, sanye take cikin wata doguwar rigar atamfa wadda aka k'awata d'inki da fararan
stons da kuma adon ja a jiki, kasancewar launin atamfar a kwai launin ja a jikinta, sosai ta karb'i
jikinta tareda futo da ainihin hasken fatarta, kunnenta a manne yake da wayar tallphone din
dake ajiye bisa Bedside drower din dake manne a jikin gadon, kallo d'aya zakayi mata ka
fahimci tana cikin duniyar nishad'i gamida mayen soyayyah, murmushi naga tayi wanda yay
silar baiyanar fararan hak'oranta, lokaci guda kuma ta shagwab'e fuska cikin sigar shagwab'a
tace "uhmm nidai ban yarda ba, wllh yau nakeso na ganka kuma ba'a hanyar islamiya ba!

Ajiyar zuciya Maheer ya sauke sannan yace " Queen wai meyasa abin kuka baya miki wahala
be? To shikenan naji zanzo amma da sharad'i. Washe baki tayi sannan tace "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login