Showing 30001 words to 33000 words out of 80273 words

Chapter 11 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

12 Jul 2025

2719


tunda shi ubansu ya saka musu ido sunk'i suyi Aure, dariya Mamie ta dingayi nan ummah ta
amshe maganar da cewar wllh Baba ni kaina nagaji da zamansu haka babu Aure, dariya
ummie tayi, a ranta tace "lallai idan su Farouq suka ga Baba a gida yau a kwai Drama, a haka
driver ya kwashesu suka nufi Birnin taraiya Abuja.

*B'ANGAREN MAHEER* kuwa ba laifi jikinsa da sauki sosai, sedai har yanzu be iya bud'e
idanunsa, sosai yake samun kulawa daga manyan likitocin Asbitin, Ranar da Umaisa ta fara
shiga d'akin da Maheer yake ta tsorata sosai dataganshi a kwance sanb'al, nan had'uwarta
dashi suka dinga dawo mata, dukda haka ba k'aramin tausayinsa taji a ranta ba, dan haka tun
tana saka ran farkawarsa harta dena, wasu lokutan har story books take zuwa dasu daga gida
taita karanta masa, har wasu lokutan idan tana karantawar har murmushi takeyi, idan kuma ta
gaji dayi sedai ta saka masa kuka wai yak'i tashi,

A haka harta cika sati d'aya tana abu d'aya, amma kuma dukda hakan babu wani canji, dan
haka ta ajiye Novel d'in dake hannunta ta zubawa fuskarsa manyan idanunta masu kamada
madara, ajiyar zuciya ta sauke sannan tace " kai wai yaushe zaka tashi ne? Nikam gaskiya na
fara jin tsoron kar wani abu mummuna ya faru dakai, yaufa satina d'aya kenan ina karanta maka
story books kala-kala amma ko sannu baka tab'a bud'e baki kace ba, ballan tana kuma
kacemin ka gode, oya bud'e idanunka ka kalleni, sannan kace min ka gode bisaga hirar
danakeyi maka kullum, ta k'are maganar tana lakuce masa hanci,

Kwab'e fuska tayi tareda turo bakinta gaba tace " oh dis guy, jibi yanda ya rufe idanu kamar
baya son ganin fuskata ma.

Duk abinda take fad'a Maheer yana jinta, sedai idanunsa ne bashida ikon iya bud'e su, amma
komai takeyi yana sauraronta, zuwa yanzu ma ya gama haddace muryarta a k'wak'walwarsa,
shi kansa a yanzu babu abinda yake fatan ya gani a rayuwarsa wanda ya wuce yarinyar dake
karanta masa story books a kowace Rana, don haka yake addu'ar Allah ya bashi ikon iya bud'e
idanunsa koya samu yaga wannan yarinyar ma'abociyar zazzak'ar muryar dake d'aukeda amo a
cikin ta......
_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*

*Aradu Banyi Editing ba�*

_Page:21_

___________ haka har yamma tayi sannan ya khabeer yazo ya d'auketa suka wuce gida,
nan wata nurse me suna fatima ta shigo ta gyara masa kwanciya tareda gyara masa zaman
robar dake hancinsa, a nitse ta yaye masa bargon dake jikinsa ta canza masa wani, a haka Dr.
Viru ya shigo ya sameta, cikeda girmamawa taja da baya tareda gaisheshi, d'aga mata hannu
yayi tareda yalwata murmushin kan fuskarsa, injections d'in dake zube cikin wani farantin silver
ya d'auka tareda had'awa sannan yayi masa, drip din dake manne a hannunsa ya zare masa
sannan ya juya ya fice,

harsu umaisa suka koma gida su Ummie basu dawoba, da Ruman suka fara cin karo a harabar
gidan, yamutsa fuska umaisa tayi sannan ta kaleta tace "Ruman don Allah me kika dafa wlh
yunwa nakeji, wani irin kallo Ruman ta watsa mata sannan tace " bansaniba 'yar renin hankali,
kuma wllh ki wuce ki cire wannan Uniform d'in kije khitchine ki k'arasa sauran aikin dana bari
don wllh bazanyi ba sekinyi shi, kwab'e fuska tayi tareda turo baki tace "uhm to malama naji
yanzu dai seki bari na fara cin abincin kafin surutun naki ya biyo bay...... "Kut nice ma nake miki
surutu Umaisa? Ruman ta katseta cikin d'aure fuska,

Kallonta Umaisa tayi sannan tace " toda dawa nake kuwa inba ke b..... Tunkafin ta k'arasa
maganar Ruman tabita da gudu sukayi cikin parlour, ya Usman ne kwance bisa doguwar
kujerar dake perlourn, da gudu Umaisa tayi kansa tana ihu, da sauri ya mik'e amma dukda
hakan seda ta fad'a masa a jiki, wata uwar harara ya watsawa Ruman dake tsaye tanata faman
hura hanci, tun kafin yayi magana Ruman tace "ya Usman wllh kayimin tsakani da wannan
yarinyar, bakaga irin Rashin kunyar datakeyimin ba dan taga bana lakad'a mata duka!!!

Had'e rai ya Usman yayi sannan ya kali Umaisa ya kalla mata harara yace " dalla malama fito
daga bayana tun kafin kisa na kwad'amiki mari marakunya kawai, kamar munafuka haka ta fito
daga bayansa tana sunne kai, a fusace yace " tell her sorry tun kafin nayi k'wallo dake a nan
gurin idiot.
Da sauri tace "uhmm im sorry, tana fad'a tabar perlourn tana tura baki, se'a lokacin ya Khabeer
ya shigo perlourn, yana ganin Usman yay saurin dora lab cord d'insa bisa kansa sabida karyaga
flaster din dake kansa, a tak'aice yace" Usman har ka dawo kenan?, tun kafin Usman ya bashi
Amsa yayi saurin barin perlourn, yana shiga side d'insa kayan jikinsa ya rage sannan ya fad'a
toilet.

5:30pm dai-dai su Ummie suka iso gida, sosai suka gaji sabida irin tafiyarda drivern yakeyi, tun
6:00am suka taso amma se yanzu suka iso Abuja sabida fad'an da Baba takeyi akan se driver
ya rage gudu indai bawai so yake ya kasheta ba�, shiyasa tafiyar tazo musu da haka.

Motarsu na tsayuwa Ruman ta fito da gudu ta rungume Ummah tana dariya, se bayan ta saki
Umma sannan ta nufi gurin mamie ma ta ringumeta tana dariyar farin cikin dawowar tasu, a
hankali tace "i miss you so much Mamie na.

Dariya mamie tayi sannan tace " i miss you to sweetheart, sosa kai Ruman ta fara sabida ganin
irin kallon da Ummie take binta dashi, da sauri ta nufota zatai hugging d'inta, dakatar da ita
Ummie tayi sannan tace " karkizo min nan bana buk'ar oyoyon ki, wato seda kika gama yiwa
iyayanki sannan zaki nufoni ko???
Tun daga k'ofar parlour Umaisa ta fara ihun murna, da gudu ta taho ta fad'a jikin Ummie tana
ihun murnar dawowar tasu, murmushi Ummie tayi tareda shafa fuskar Umaisan, kallon Ruman
Ummie tayi sannan tace "nima ga d'iyata nan ta fitar dani kunya, a haka Baba ta fito dak'ar
k'afafunta duk sun kumbura sabida zama, seda ta k'are musu kallo sannan ta tab'e baki tace
"ohni Binta yanzu yarannan duk sunyi girman haka amma Mamuda ya zuba musu ido suke
zaune haka babu Aure?

Da sauri Ruman da Umaisa suka nufeta suka Ringumeta suna dariya, Umaisa ce ta kalleta
tace " kai Granny kinga yanda kikai fresh kuwa? Wllh kamar wata 'yar budurwa haka kika zama,
dingure mata kai Granny tayi sannan tace "ja'irah.

A haka suka d'inguma xuwa cikin gidan zuciyarsu fess, a perlour suka samu Usman kwance
bisa kujerar da umaisa ta barshi d'azu, yana ganinsu ya mik'e zaune yana murmushi, harararsa
Mamah tayi sannan tace " sannu malalacin mataimakin manaja, dubi yanda ka zube mana a
parlour sekace wanda ya shekara yana aikin noma, dariya kawai Usman yayi sannan ya kalli
iyayen nasa yace "uhmm nikam bantab'a jin inda akeyiwa d'a gori ba se'a gidan Alhaji
Mahmoud muhammad, ya Qare maganar yana " yar dariya cikeda shakiyanci, duka ummie
takai masa tana dariya, Baba kuwa banda tab'e baki babu abinda takeyi sabida d'inbin gajiyar
dake tareda ita,

Baki Usman ya saki yana kallon Baba sabida mamaki, a k'ufule ya kalli Ummie yace "haba
Ummie don Allah, meyasa zaku kwaso mana wannan gaiyar ciwon kan kutaho mana da ita? Ni
dana san da ita zaku taho wllh da senayi muku addu'a kunyi tayin faci a han......, "kaci gidanku
dan me garin ku, Ummie ta katseshi tareda kai masa dundu a baya, ihu ya saka tareda saurin
mik'ewa yana hararar Baba, nunashi Baba tayi sanan tace "Uwarka da ubanka Mamuda kake
harara bani ba, d'an banza me kamada sadakar yallah, dariya su rumana suka saki sannan
suka had'a baki sukace "amma dai dukda hakan yafiki kyau, carbin hannunta ta jefa musu
tanata faman fad'a kamar ta ari baki.

Dak'yar su Mamie suka lallab'ata ta dena fad'an sannan suka kai mata kayanta d'akinta, sannan
suma suka wuce nasu d'akunan dan suyi wanka, a haka har aka fara kiraye-kirayen sallah
magrib, seda suka gabatar da sallar kafin suka fito daining don suyi Dinner, wanda gabad'aya
girkin Ruman ce tayi shi, a nan ma seda aka sha fama da Baba, dan cewa tayi wllh bazata hau
Daining ba sedai a sakko mata da abincin k'asa taci abinta sabida bazata iya wannan rayuwar

ta yahudanci ba�

Se wajen 10pm sannan Abbah da Farouq suka dawo gida, kasancewar yau d'in tare suka fita
da Farouq ya kaishi wajen wani meeting da suka gabatar tareda Minister of Finance, se bayan
ya dawo ya huta kasancewar a d'akin Mamie yake nan take sanar dashi zuwan Baba, sosai yayi
farinciki da hakan, don haka yana fitowa daga wanka ya shirya cikin wata milk din jallabiya ya
nufi masaukin mahaifiyar tasa.


*KADUNA STATE*
AL'amarin Abdul kuwa tun bayan dawowarsu daga Asbiti da Dady nan ya koma d'aki ya dinga
tintsirar dariya harda rik'e ciki, seda yay me isarsa sannan ya fad'a toilet ya fesa wanka, be
jimaba ya fito a gaggauce ya shirya cikin wata brown jallabiya k'irar companyn Emraty, sosai
tayi masa kyau ba kad'an ba, sabida yanda ta baiyana cikar zatinsa sekace bad'an shekara 22
ba,

Maine perlourn gidan ya nufa, a nan ya samu Dady yana korawa Hajiya murja bayanan likitan,
yamutsa fuska kawai yakeyi tareda wani dafe ciki sekace majinya cin gaske, kamar zeyi kuka
ya kalli Dady yace "pls Dady ka sanar dani abinda Dr. Yace akan abinda yake damuna pls
Dady...! Hannu Dady ya mik'a masa alamar yazo gareshi, da sauri Abdul ya fad'a jikin Dady
yana matsar k'wallar k'arya, time to time yakan saci kallon fuskar Hajiya murja ba tareda Dady
ya lura da hakan ba ya galla mata wata uwar harara,

Dan dole ta mik'e tabar perlourn sabida bazata jure irin wannan muzancin da wannan d'an iskan
yaron yake mata ba.

_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*

*_Not Edited, kuyi haquri da typing Erorr don Allah_*



*_A yau shafin na D'iyar d'akin chubad'o ne wato MAMAN KHAUSAR (Hauly) har kullum

chubad'o tana alfahari da irin Qaunar da kike nuna mata, haka kuma ni zainab ina sonki
fisabilillah ❤_*



_Page:22_

___________ tun daga ranar Abdul ya shimfid'a tabarmar rashin mutunci a cikin gidan, duk
abinda yaga dama shi yakeyi, don haka ya hanasu Binta 'yar kwabo saqat da bala'insa, a haka
harya samu nasarar dasa tsoransa a xuciyar matan da suke tarawa a cikin gidan suka dena
zuwa ma gaba d'aya.

*ABUJA*
tunda Baba taxo basu had'u da khabeer ba, ko sannu da zuwa beje yayiwa su Ummie ba har
suka cika kwana uku da dawowa amma basuga k'eyar Khabeer ba, har break fast ma baya
fitowa ballantana kuma Deener, tun Abin baya damun Ummien sa harya ya fara damunta, dan
haka ta d'aga waya ta fara k'ok'arin kiran layinsa, bugu d'aya khabeer wanda ke zaune a office
d'insa ya d'auka, tun kafin yayi magana Ummie ta katseshi cikin b'acin rai tace " khabeer lallai
idan ka dawo gida ka sameni a d'aki ina son magana dakai kaji na gaya maka!

Tun kafin ya samu zarafin magana Ummie ta katse wayar, wata sassanyar ajiyar zuciya ya
sauke, tareda shafa gefan kansa inda ciwon yake, agogon fatar dake manne a hannunsa ya
kalla, dan haka da sauri ya mik'e tareda d'aukar car key d'in motar Usman daya fito da ita, a
gaggauce ya shiga office d'in Dr. Abdullah dan ya kwance masa bandejin dake goshin nasa,
nan Dr. Ya dinga takalarsa da surutu amma khabeer din ya shareshi, ko kafin ya kwance
masan ma seda yayta tsokanar sa sannan ya kwance masa, shidai khabeer bece masa
komaiba ya fice yabarshi yana 'yar dariya.

Yana fita Direct school d'insu Umaisa ya wuce, cikin mintunan da bazasu gaza 15 ba ya isa
Makarantar, a nitse yayi parking motar sannan ya fito, se'a lokacin na k'are masa kallo, sanye
yake da wata farar riga me ratsin sea'green a jiki, hakanne yasa ya dora sea'green d'in suite a
kan rigar, wadda ta dace da blue black d'in jeans d'in dake jikinsa, inda k'afarsa kuna take
sanye cikin wani dakakken takalmi k'irar companyn Batozy, a nitse yake takawa zuwa office d'in
principal d'in Makarantar cikin takunsa me d'auke da k'asaita da kuma tak'ama a cikin sa, yana
shiga suka gaisa da matar gaisuwar mutunci, bayan sun gaisa ne ya sanar da ita cewar shi
yayan Umaisa Mahmoud muhammad ne, kuma yazo d'aukarta ne bisa wani mahimmin uziri
daya taso, sosai ta nuna masa jin dad'inta, sabida tasan Umaisa sosai yarinyace me k'ok'ari
sosai, sedai a kwai shagwab'a,

nan da nan ta tura aka kira Umaisan batareda wani b'ata lokaci ba, godiya yayi mata sannan
suka tafi,

Tun'a mota Umaisa take tambayarsa jikin Maralafiyan, shiru yayi mata hakanne ya bata
tabbacin bazata samu amsar datake nema ba, tuk'insa kawai yakeyi cikeda k'warewa, cikin
mintuna kad'an suka isa Asbitin, bud'e motar yayi ya fita, da sauri itama ta bud'e motar tabi
bayansa, tsayawa yayi cak yana binta da kallo se faman kokawa take da Baread d'in dake
kanta, wata uwar hararar yajefa mata, tun kafin yayi magana ta juya da sauri ta koma mota ta
d'akko d'an k'aramin hijabin uniform d'in, wanda ko k'irjinta be gama rufewa ba, a haka tabi
bayansa zuwa office d'insa, a tsaye ta sameshi yana k'ok'arin saka lab cord d'insa da alama
duba marasa lafyansa zeje, wata farar ledah ya nuna mata wadda ke d'auke da manyan Robar
Fresh Milk guda 2 a ciki da kuma cups suma guda biyu a ciki yace " ki d'auka kije dashi, ki
tabbatar kin bashi yasha sosai sabida naga kwana 3 da suka wuce baya wan iya shan komai,
saura kuma kice sekin k'oshi sannan zaki bashi yasha. Ya qare maganar yana dingure mata kai.

D'aga masa kai kawai tayi tana tura baki sannan taja ledar ta fice, wayarsa ya d'auka ya jefa a
aljihun wandonsa sannan shima ya fice dga office d'in a ransa yana mamakinta.

A hankali ta tura k'ofar d'akin tareda sallama, wata sassanyar ajiyar zuciya Maheer ya sauke
sabida jin sautin muryar wadda zuciyarsa ta cikada cewar besan ya kamanninta suke ba a
idanunsa ba, amma hakan be hanashi yin farin ciki da zuwan ta ba, tabbaswani b'angare na
zuciyarsa na shiga damuwa idan kunnuwansa d kuma jijiyoyin jikinsa basuji sautin muryarta ba,
so tari wasu lokutan yakan samu kansa da tsananin kewarta musamman ma a kwanaki ukun
dabeji d'uriyarta ba!!

a hankali take takowa har zuwa gaban gad'on da Maheer din ke kwance, murmushi ta saki
sabida ganin bakinsa na motsawa, a hankali ta kalleshi tace "lallai sauk'i ya fara samuwa tunda
gashi har maralafiyana ya fara k'ok'arin motsa bakinsa kamar kowa, yanzu dai bari na fara baka
abincin ka kaci sabida D.r yace kwana biyu baka son cin abinci, yau dai sena tabbatar da ka
k'oshi sannan zan k'yaleka, nan da 1:30pm senaje masallaci nayi salla, idan na dawo sena
karanta maka New Novel d'in danazo maka dashi me dad'i.

Wani cute Murmushi ya sakar mata wanda ya k'ara fito da tsantsar kyawunsa da kuma ramar
dake fuskarsa, dukda cewar har yanzu baya iya Magana sabida yanayin aikin da akayi masa
hakan be hanashi motsa bakinsa ba,

Dariya tayi me sauti tareda tafa hannunta tace " kai Ashe dama wannan fuskar taka tanayin
kyau da murmushi? Kasan mene? "Wllh kafi kyau idan kana murmushi, seka zama kamar ba
kai ba. Ta k'are maganar tana dariya, idan ka ganta a yanayin datake maganar seka rantse kan
cewar ta samu matsalar k'wak'walwa ne yasa take hakan.
Gadon ta d'ago ta yanda zataji dad'in bashi Fresh Milk din, wani farin towel ta shimfida masa a
qasan wuyan sa, sabida karta b'ata masa jiki, a nitse ta fara zubawa a cikin cup d'in sannan ta
fara bashi, a hankali yake seeping Fresh Milk d'in kamar anyi masa dole haryata samu ya
shanye dika, goge masa baki tayi da tishu, sannan tace " to bari na tafi masallaci sabida kar
time ya wuce, fita tayi ta barshi a zaune sabida abinda yasha yayi dagesting a cikinsa kmar

yanda ya kamata,

Bayan fitarta babu jimawa Dr. Viru ya shigo shida team d'insa suka tura gadon Maheer zuwa
Tiater Room, nan da nan suka shiga duba lfyar idanun nasa, basu sha wahalaba cikin ikon Allah
kuwa suka gano bakin zaran matsalar, harma da abinda yake hanashi maganar seda suka
ganoshi, wani daskararren jini ne ya tare masa a mahad'ar bututun fitar sautinsa, dan hka suka
tura masa wata na'ura ta bakinsa cikin mintuna kad'an suka samu nasarar kwarfe jinin batareda
sunyi masa wata allura ba, sosai yake fargabar bude idanun nasa sabida yawan hasken dake
d'akin, don haka Dr. Viru ya bada umarnin a maidashi d'akin da aka d'akko shi kasancewar
babu haske sosai a d'akin ze bashi damar bud'e idanunsa batareda wata matsala ba,

Seda ta idar da sallar sannan ta koma d'akin, da sallama ta tura k'ofar ta kunna kai cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login