Showing 3001 words to 6000 words out of 80273 words

Chapter 2 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

12 Jul 2025

2709

ta samu Mamie se aikace aikacen ta
take, a nitse tace Mamie ina kwana ?
Ko kallonta Mamie batayi ba har Seda ta sake maimaita gaisuwar sannan mamie takalleta a
A dak'ile tace, "lafy lau,

Jikin ta ne yayi bala'in sanyi sbda ko ba'a fad'a mata ba tasan mamien ta fishi takeyi da ita, nan
da nan k'walla ta cika mata idanu, cikin muryar kuka ta bude baki tace, " pls Mamie i'm so
sorry don All...!!,

Da sauri Mamie ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu, tareda nuna mata k'ofar fita daga
kitchine d'in alamar ta fita,

Bakinta na rawa tace, "Dan Allah Mamie kiyi haqur....

Bata bari ta k'arasa ba cikin d'aga murya tace, "I said get out right now!!!! ta fad'a cikin b'acin
rai,

Da sauri ta fice sbda ta San halin Mamie bata da wasa yanzu setayi mata shegen dukan da
setaji a jikinta, sabida ko kad'an bata tolerating shirman ta,

Daki ta koma tana ta faman sharar hawaye sekace wadda aka zane da bulala, sannan ta fara
shirin tafiya School, Seda ta had'a komai na tafiya school din sannan ta fito falon sanye da
uniform d'inta wanda sukayi mata bala'in kyau a jikinta,

Ya Usman ta samu da Rumana suna breakfast se kuma ya Farouq, kujerar daining ta fara
k'ok'arin ja, se faman cika take tana batsewa ita a dole anb'ata mata rai, babu wanda ya
tankata se Ya Usman dinta,

Dan haka ta k'ara turo baki gaba tana yarfe hannu cikeda tsantsar shagwab'a, Seda ta zauna
sannan tabisu d'aya bayan d'aya ta gaishesu,

Ba yabo babu fallasa suka amsa mata , a gaggauce Farouq ya gama break din sannan ya dau
brief case d'insa ya tafi office ya barsu,

Chips kawai ta zuba kad'an a flet, sannan tasa pride egg a gefe, A hankali ta shiga ci kamar
anyi mata dole, har Seda Rumana ta kammala amma ita ko rabi ma bataci ba, Kallonta Rumana
tayi sannan ta kalli agogo tace, "pls Umaisa u should be fast mana Dan Allah time fa yana
tafiya,
Hararar ta Umaisa tayi sannan ta dauke kai tace," to so kike na tafi School d'in banyi breakfast
ba?

Hararta ya Usman yayi sannan yace, dalla malama tashi ku tafi,

Mik'ewa tayi da sauri ta nufi k'ofa, hakan ne yasa Rumana ta k'yalk'yale da dariya, har suka
shiga mota, Rumana bata dena dariyar da take ba
Hakanne ya k'ara tinzira Umaisa, se kawai ta fashe musu da kuka a motar tamkar Allah ya
aikota,

Malam Musa drivern su dake kaisu makaran ta ya juyo yana 'yar dariya yace, "haba Rumana.
Ya zakisa 'yar gaban goshin Abba kuka irin haka ?

Dariya sosai Rumana tayi sannan tace, " ai Malam Musa kabar ta tayitayin kukan taga zata iya
ne, kokuma ince hawayen ne sukayi mata yawa shiyasa, wllh kaima ka iya taya bera bari
Malam Musa. Ta k'are maganar tana murmushi,

Dariya Malam musa yayi sannan ya kalli Umaisa da ta kifa kai da gwiwa tana ta aikin kuka yace,
"yahaquri 'yar Abba rabu da ita kinji?

Dak'ar ya dinga lallaminta harya samu tayi shiru , suna zuwa school kamar jira take ta bude
murfin motar ta fice ta bar Rumana a motar,

Rumana na shirin fita daga motar Malam Musa ya kalleta yace, " af Rumana dan Allah kuyi
hak'uri na manta ban sanar da Alhaji cewar med'akina bata da lfy ba, shine nace bari in
gayamiki cewar bazan samu damar zuwa d'aukarku ba sabida zan biya na kaita Asibiti,

Murmushi kawai Rumana tayi sannan tace, "lah babu komai Malam Musa kaje kawai, idan an
tashi zamushiga texi kawai,

Murmushin jin dad'i yayi a ransa yana girmama halin kirki irin na yarinyar, kokad'an basuda
d'agawa irin ta yaran musu kudi.

Har aka tashi daga school Umaisa bata kula Rumana ba, sbda a cewarta wai Rumana itace
silar shouting din da yaya Usman yayi mata, har bakin class din su Umaisa Rumana tazo tace
mata tazo su tafi gida amma fir Umaisa taki koda kallonta, hakan ne yasa Rumana tayi fishi tayi
tafiyar ta tabar Umaisan a School d'in, dama kudin break dinta ta ajiye sabida su samu su tafi
gida dashi tunda Mlm Musa yace baze samu damar dawowa d'aukarsu ba, sbda uzirin daya
bata dazu,

Tana fita bakin Gate din School din ta samu me taxi tace masa "Apo zaka kaini don Allah,

Kallonta me taxi d'in yayi sannan yace, wani guri zakije a Apo?

A tak'aice tace, " Zone E zaka kaini cikin legislative Quaters,

Kallonta ya sakeyi a karo na biyu sannan yace, "shiga muje.

Shiga tayi ta zauna amma zuciyarta Sam babu dadi a kan abinda Umaisa tayi mata,
Tsaki tayi tareda zubawa titi idanu a ranta tace, "dik abida Umaisa takeyi wllh duk lefin Abba ne
daya shagwaba haka, shiyasa take abinda taga dama
A haka suka qaraso cikin unguwar, a nitse ta dinga nuna masa hanya har suka k'arasa bakin
k'ofar gidan,

Kallonta me taxi din yayi sanna ya kalli gidan a ransa yace ikon Allah amma gidan nan ya hadu,
haka kuma ya tsaru matiqa,

Kamar daga sama yaji tace, " Mlm nawa ne kudin ka?
Washe baki yayi sanna yace nera dubu zaki bayar,
Dubu 2 ta dakko sabbi dal a jakar ta ta mik'a masa sannan ta juya,

Da sauri yace k'anwa dubud'ya fa nace miki ba 2 ba?
Juyowa tayi sannan ta sakar mai murmushi tace kaje na baka kyau ta ,
Godiya yayi mata sannan yaja motar ita kuma ta shige gida,
A parlor ta samu su Ummie sunata hira, se kuma Ameerah dake ta faman wasa da Teddy's din
dake gaban ta, Da sallama ta k'arasa parlon sannan ta zube akan d'aya daga cikin kujerun
perlourn tareda fadin, "wash wllh nagaji sosai,

Murmushi mamah tayi sannan tace, " ai dole kicewa mutane kin gaji mana tinda garin Abuja
gaba d'aya kika zagaye,
Dariya sukayi gaba daya , sannan ta gaishesu ta mik'e donta wuce dakinta,

Ummie ce tace, "Rumana ina kika bar Umaisa ne?

Tsaya tayi sannan ta labarta musu yanda sukayi da ita a makaranta sannan ta wuce daki
abinta,

Sosai abin yayiwa Mamie ciwo a ranta ta dan haka ta dinga k'isma irin dukan da zata yiwa
Umaisa idan ta dawo,

A makaranta kuwa Umaisa na Zaune a kan sit dinta ta kifa kanta a kan jakarta se sharbar kuka
take ,
K'awarta Nusaiba Hashim ce ta hangota Dan haka da sauri ta nufeta, d'agota tayi lokaci guda
ta shiga tambayarta abinda ya sameta take kuka,

Cikin kuka umaisa ta fara labarta mata komai tin daga fad'an da ya Usman yayi mata har zuwa
dariyar da Rumana ta dingayi mata,

Wani irin kallo nusaiba ke bin Umaisa dashi, wanda yafi kama Dana takaici sannan tace,

"yanzu ke Umaisa sbda Allah dan anyi miki fad'a shine zaki zauna ki b'are baki kiyita kuka ?
Haba Umaisa yaka mata fa ki fahimci cewr kefa yanzu ba yarinya bace kin girma, komai naki
kuka da abinda ya isa da Wanda ma be isa ba kuka?

haba Dan Allah, ai dole ne ki dinga bawa kowa haushi , wllh da a gidan mu kike inajin sekin
hadiyi zuciya kin mutu sbda tsawar da zaki dinga sha a gurin yaya Khalil d'in mu sbda komai
nasa fad'a ne, "amma kuma he is very social and nice, ta fad'a fiskarta dauke da murmushi
Shiru. Umaisa tayi tana kallonta se kuma ta sunkuyar da kanta k'asa tana tinanin yanda za'ayi
ta tafi gida,
Wayar Nusaiba ce ta fara ruri Dan haka da sauri ta d'aga tana dariya tace, "yaya wllh harna gaji
da jiranka,

murmushi yayi sannan yace, "i'm sorry Lil sis ai gani ma nazo,

Dafa Umaisa tayi sannan tace, "taso mutafi se mu ajiyeki a gida tinda hanya ne
Da sauri ta mik'e kamar jira take suka fita daga Class din zuwa inda Khalil yayi parking motarsa.

Suna zuwa nusy ta bud'ewa Umaisa bayan motar ta shiga ta zauna sannan ita kuma ta bude
front sit din ta shiga ta zauna,
Da murmushi akan fuskarta tace "yaya wllh harna kusa bushewa,

dariya yayi sannan yace Aida kin bushe din ma daya fi dariya sukayi gaba daya , sannan
Umaisa ta gaisheshi cikin girmamawa,

Da sakin fiska ya amsa mata sannan yace kece Asha ko?
Da mamaki ta d'ago ta kalleshi a karo na farko tinda ta shiga motar, cikn sa'a kuwa suka had'a
ido da ita , kasa d'auke idonta tayi daga barin kallonsa sbda ganin irin launin k'wayar idonsa ,
*(JANAF da qoqari� )*

mamaki ta dingayi a ranta tace "dama a kwai masu irin idon nan a qasar Nigeria?

Katseta yayi ta hanyar cewa "Lil sis ba wannan bace Aysha ?

Dariya Nusaiba tayi sannan tace "ba ita bace bafa yaya , wannan sunan ta daga U ya fara,

Hannunsa d'aya ya d'ora a kansa kamar me tinani wani abu sannan yace, "to nama San sunan
ta,

Da mamaki sukace to fadi muji idan ka sani,
Murmushi yayi sannan yace sunan ta Ummi ne,
Dariya suka dinga yi masa
sannan Umaisa tace " niba Ummi bane sunana, ni sunana *Umaisa Muhammad Mahmoud,*
kokuma kace *Fatimah.*

idonsa yad'an zaro kad'an sannan yace "wow nice name Umaisah,

Dariya tayi sannan tace "to kaifa ya sunan ka ?

Shiru ya danyi sannan ya saki wani k'aya taccen murmushi yace *"Khalil Nasir Abdullah*

Dariya tayi sannan tace nice to meet you ya Khalil
Amma ya naji sunan Abbanku ba d'ayaba da Nusaiba? kuma amma naji tace min kai yayanta
ne,

Dariya tambayar ta bashi har seda fararen haqoransa suka fito, sannan yace "ae ni yayanta ne
amma kuma baban mu ba daya ba,

Cikeda rashin fahimta tace "ban gane ba
Dariya Nusaiba tayi sannan tace ke cousin d'ina ne fa , se'a sannan Umaisa ta tsagaita masa
da yawan tambayoyin ta
,
Hira suka dingayi kamar sun dad'e da Sanin juna , a ranta tace "dama haka su yaya khabeer
suke Dana ji dadi,
Seda suka kaita har qofar gida, sannan suka kama hanyar nasu gidan dake Gaduwa Estate.

Qofar gate din ta tura zuciyarta fess babu fargabar komai ta shige gida ,
Takoyi sa'a babu kowa a falon Dan haka ta nufi dakinta,
Uniform din ta cire sannan ta shiga toilet tayi wanka,

seda ta d'au lokaci sannan ta fito, wasu Riga da wando ta d'kko Na Pakistan masu launin blue
black ta sanya a jikin ta,

masha Allah kayan sunyi matiqar yi mata kyau kasancewar ta doguwa kuma fara,

Dining aria ta nufa ta cika cikinta sannan ta mik'e ta nufi d'akin mamie,




Comment
Nd
Share


*Zm muhmd*
*(ChuBaDo)*�

_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page: 3_


____________ A hanali take hawa kan step d'in kamar wata mara gaskiya, cikeda tsoro ta
murd'a handile din dake jikin k'ofar ta shiga d'akin tareda yin sallama duk a lokaci guda, a
zaune ta samu mamie tana sanyawa Ameerah kayah,

Daga d'an nesa kad'an take kallon mamien kamar zatayi kuka tace, "mamie i'm sorry dan
plssss.. Ta wani ja pls d'in cikeda marairaicewa, kokallonta Mamie batayi ba balle ma tasa ran
zata kulata, har Mamie ta gama shirya Ameerah Umaisa na tsaye bata motasa ba, mik'ewa
Mamie tayi tareda jan hannun Ameerah dake rike Bobo tana k'ok'arin budewa, da sauri
Umaisa ta Rik'e hannunn Mamie tana kuka har da yarfe hannu, wani irin takaici ne ya cika
zuciyar Mamie , dan haka ta fusgota a fisace tayi cikin d'akin da ita, wayar dake jikin hand
drayer d'inta ta fizge cikeda b'acin rai tayi kanta da ita, sosai Mamie ta duka tsula mata wayar a
jikinta, bakajin komai a d'akin banda ihun Umaisa,

Ummie ce ta shigi d'akin da saurinta, sabida jin ihun nata, Salati Ummie ta saki cikeda tsoro
sabida ganin irin dukan da Mamien takeyiwa Umaisan, da sauri tasa hannu ta fisge wayar tana
bin Mamie da wani irin kalo wanda yafi kamada na mamki sannan tace, " Amma wllh kin bani
mamaki Badi'atou..!!, "yanzu fisabilillahi yarinya kamar wannan budurwa zaki saka a gaba
kina duka da wannan murtikekiyar wayar kamar zaki kasheta? Angaya miki fishi haukane?
Yanzu da kika sata a gaba kina duka me hakan ze canza iye?

A hankali Ummie ta dafa mamie sannan ta sassauta murya tace, " idan rai ya b'aci sam be
kamata hankalin mu ya gushe ba Badi'atou! Komai na Rayuwa yana da iyaka, kedai kawai kici
gaba dayi mata addu'ah insha Allahu komai zeyi daidai kinji? Ta fad'a tareda zaunar da mamien
a bakin gadon dake d'akin,
Cikeda takaici mamie ta kalli Ummie tace, "har zuwa wani lokaci za'a d'auka a haka sabida

Allah? Wllh Allah shikad'ai yasan halinda zuciyata take shiga a kan wannan yarinyar!! Babban
abinda yafi komai tsayamin a raina shine yanda Alhaji yabi ya sangartata, kokad'an baya
la'akari da cewar ita mace ne kuma gidan wani zata nan gaba.

Murmushi Ummie tayi sannan tace," lallai Badi'atou kina mantawa da Alhaji indai akan 'ya'yansa
ne, lokacin da ina goyom Khabeer wllh ya dingayi akansa, kokad'an baya son a tsawatar masa
balle kuma ace za'a dakeshi, sekace a kansa aka fara haihuwar yara, danaga abin ya isheni se
kawai na dage dayiwa yaron Addu'ah duk da cewa ma bashida wata k'iriniya,
Murmushi Mamie tayi har seda hak'oranta suka fito sanna ta girgiza kai, se'a sannan Mamah
ta shigo tana gyara d'aurin d'an kwalin dake kanta....

Sankin baki tayi tana bin Mamie da kallon mamaki sannan tace, "yanzu Badi'atou seda kika
daki yarinyar nan sabida Allah? Ta fad'a tareda maida kallonta ga Umaisa daketa faman
sharb'ar kuka kamar zata hadiye ranta.

A nitse ta k'arasa inda Umaisan ke dunk'ule tana aikin kuka tace, " maganinki kenan ai ba kin
iya Rashin jin magana ba, maza tashi ki wuce d'akinki kiyi wanka, sannan kisha pracetamol ki
kwanta ki huta 'yar k'wal uba.

Da sauri ta mik'e tareda ficewa daga d'akin tana sharar hawaye, a hankali take sakkowa daga
kan step d'in harta gaba sakkowa. A perlourn k'asa sukaci karo da Ya Usman d'inta ya dawo
daga office,

Tsayawa tayi tana kallonsa lokaci guda kuma ta saki wani irin kuka tana yarfe hannu, Da sauri
ya ajiye brief case d'in dake hannunsa a kan d'aya daga cikin Royal chiars d'in dake perlourn ya
nufeta da wani irin mugun sauri, hannun ya kama da sauri yana dubawa, shatin bulala ya gani
kwance a jikin farar fatar jikinta, nanda nan ransa yay masifar b'aci, cikeda fishi yace," who did
this to you? Ya fad'a yana wani irin huci kamar macici.

Cikin kuka tace "Mamie ne wai da ban dawo gida tareda Rumana ba, kuma wllh yaya laifi
Ruman d'in tayi min shiyasa nak'i yarda na biyota na taho ni kad'ai, ya fad'a tareda k'ara sautin
kukanta,

Hannunta yaja suka koma saman, murd'a handile d'in kofar yayi, bisa ga mamakinsa seyaga
duk iyayen nasu suna d'akin Mamie, kallonsa Mamie tayi sannan ta d'aure fuska tace " lfy kuka
shigomin d'aki babu sallama, kodai zuwa kayi ka Rama mata ne?

Da sauri yace "A'a Mamie ba haka bane kawai dai naga kamar dukan yayima jikinta yawa ne,
kumafa idan Abba ya dawo ya gani wllh Mamie zeyi fad'a. Wani d'an isakan kallo suka watsa
masa a tare d'yansu, tun kafin suyi magana yaja hannunta suka bar d'akin da sauri, basu tsaya
a ko ina ba se'a perlourn k'asa, zaunar da ita yayi a gefansa, sannan ya hawo jakar daya dawo
da ita ya bud'e, kwalin sneeker's ya d'akko ya mik'a mata, sannan yace " oya jeki d'aki ki b'oye

nakine ke kad'ai na siyo miki.

Karb'a tayi lokaci guda ta washe baki tace " thank ya Usman, sannan mik'e ta nufi hanyar room
d'inta harda tsallen murna, sekace ba ita bace wadda ta gama gurzar kuka ba.



_Comment_
_Nd_
_Share_


*Zm muhmd*
*(CHuBaDo)*�

_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*

_Dan girman Allah masu bina prvt suna cewa in canza akalar labarina pls kuyi haquri, sabida
bazan iya canza tsarin labarina ba, idan kinga hakan be miki na dan Allah ki barmin littafina
babu dole🤷â€â™€_


_Afwan yau page din bashida tsaho, banida caji ne😊_

_Page:4_


____________Tana shiga d'akin kan gadonta ta fad'a tareda d'aukar tellphone d'in dake gefan
gadonta ta shiga kiran wayar Abbanta,

Abbah dake zaune bisa kujerarsa ta office, yayi nisa cikin nazarin takardun dake zube a
gabansa, yaji wayarsa dake gefansa ta fara k'ara, murmushi yayi tareda mayarda hankalinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login