Showing 39001 words to 42000 words out of 80273 words
Chapter 14 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:26_
___________Wani uban ashar ta zunduma tareda tuge d'ankwalin leshin dake kanta, nan da
nan wani irin gumi ya fara keto mata cikeda tashin hankali, kallon tsaf Binta 'yar kwabo keyi
mata sannan tace "ke wai lafiyarki kuwa, naga duk kinbi kin zare kamar wata me tab'in hankali?
Zufar dake goshinta ta goge sannan ta samu zarafin magana cikeda tashin hankali tace " Binta
shikenan Binta mun shiga uku mun fad'a komar 'yan damfar.... Zabura Binta tayi tareda shak'o
wuyan hajiya Murja cikin karaji tace "kutumar bura'uba wllh Murja baki isa kici Amanar Binta ki
zauna lfy ba, ni zaki Rainawa hankali? "Dalla malama sakarmun wuyan Rigata tun kafin in miki
Rashin mutunci. Murja ta katseta cikin karaji, harke kin isa ki Rik'emin wuyan rigata Binta?
Tafa hannun Binta tayi sannan tace " k'warai kuwa harma nayi yawa, ke na Rantse miki da
girman Allah idan baki dawomin da kud'ad'ena ba wllh sena tona miki Asiri a idon duniya,
A harzuk'e Hajiya Murja tayo kanta, hakanne yayi daidai da tashin k'arar wayar Hajiya Murjan, a
hanzarce ta nufi inda wayar take tareda zubawa Screen din wayar idanu, murza idanunta tayi
sabida ta tabbatar da abinda idanunta suka gane mata, Sunan *MANAGER* ta gani yana yawo
a Screen din wayar, a hanzarce ta answer wayar zuciyarta na dukan tara-tara, murmushi
manager yayi sannan yace "im sorry Hajiya, karkiga ban kiraki a waya d'azuba, wata 'yar
tafiyace ta kamani daga nan Abuja zuwa legos shiyasa, amma yanzu na dawo dan hka zamu
d'ora daga inda muka tsaya akan abinda muke gudanarwa, hka kuma gobe zanzo mugaisa
daku sabida muga juna dani dake sabida in tabbatar miki da wani babban al'amari wanda ze
jefaki a duniyar Rud'ani gameda kasuwancin da nake shirin k'ullawa.
Wata uwar ajiyar zuciya Hajiya Murja ta saki tamkar wadda aka k'wace daga bakin ingarman
zaki, murmushi tayi sannan tace " hak'ik'a Manager kana da abin mamaki wllh, ni gaba d'aya
da harna shiga Rud'ani dana kira wayarka ban sameka ba!
Dariya Manager yayi sannan yace "haba madam ai wasa farin girki tukunna, bayanzu ya
kamata kifara wannan tunanin ba senan gaba tukunna!
Shiri tayi tana nazarin kalaman Managern, katseta yayi ta hanyar cewa " keda zaki samu ribar
kudal'ad'e masu yawa meye naki na fargaba a akai?
Murmushin jin dadi ta saki sannan tace "oh hakane fa Manager na, yanzu dai inanan ina jiran
zuwanka goben insha Allah, a haka sukai sallama da Manager zuciyarta fess. se'a lokacin ta
juya ta kalli Binta " yar kwabo wadda ta zuba mata idanu tana sauraron duk tattaunawar da
sukeyi tace " hmmm Binta kenan na godewa Allah daya nuna min ainihin kalarki a fili na gani,
don haka zan dawo miki da Million 60 dinki, inyaso daga ranar dana baki kud'in ki babuni
babuke har Abada!! Tunda ke bakisan mutunci ba.
Jikin Binta ne yayi masifar sanyi, musamman ma dataji kalmar aminiyar tata na k'arshe, tabbas
idan har tabari suka Rabu da Hajiya Murja to wllh kashinta ya gama bushewa, nan da nan ta
shiga bata hak'uri kamar zata ari baki, dak'ar ta samu Murja ta hak'ura harta sakko suka d'an
tab'a hira, sannan suka mik'e suka fad'a d'aki mak'ale da juna.
B'angaren Maheer kuwa sosai yaci gaba da bibiyar Rayuwar Umaisa da lamuranta, amma
dukda hakan bata canza zaniba, sosai take garashi son ranta, idan taso iskanci ma ko kallon
arzik'i batayi masa idan suka had'u, amma sam hakan besa Maheer ya rabu da ita ba sema
k'ara nane mata dayakeyi, kullum yana hanyar mkarantar islamiyarsu duk dan ya ganta yaji
dad'i a zuciyarsa.
Yau ta kama laraba ne don haka Maheer ya k'udurtawa kansa da zuciyarsa cewar yau za'ayita
ta k'are a tsakaninsa da Umaisa, dolenta yau ta tsaya ta saurareshi koda ace baxata karb'i
soyayyarsa ba.
A nitse take takowa cikin takunta me jan hankali, tun daga nesa ta hangi motarsa wadda ko'a
mafarki ta ganta zata shaida mamallakinta,
A hanzarce ya fito daga motar cikin takunsa na isa da k'asaita, jingina yayi da motar tareda
sark'e hannayensa a k'irjinsa tareda zuba mata tsimammun idanunsa, d'auke idanunta tayi da
sauri daga kansa, sannan ta maida hankalinta zuwa ga hanyar tafiyarta, harta iso dab dashi ta
fara k'ok'arin wuce shi, da sauri yasha gabanta yace "pls Queen don Allah ki tsaya ki saurareni
mana wllh dukkan abinda bakina ya furta akanki gaskiya ne, ni kaina bantab'a zaton zan fad'a a
tarkon son wata 'ya mace ba Queen, a lokaci gani kawai nake duk mata halinsu d'aya ne, ashe
sam abin ba haka yake ba, tabbas malaman kimiyar soyayyah sinyi gaskiya da sukace so a
zuciya yake ba'a idanu ba, haka kuma yayin da guguwar soyayyah zata d'ebi mutum bata
shawara dashi balle ta nemi izininsa, Nasoki a lokacin da idanuna basusan kamanninki ba
Queen, I love you Queen I really love you with all my heart, pls Queen say the samething to me
honestly kamar yanda na fad'a miki don Allah! Idan har kika amshi soyayya ta da dukkan
zuciyarki I promise to be yours forever and Ever Queen!!!!
*KIYARDA DANI* dukkan abinda zan fad'a miki babu komai a cikinsa face tsantsar gaskiya da
da zallar Aminci a cikinsa.
shiru tayi ta kasa magana, tabbas idan tace batajinsa a ranta tayi k'arya, sabida duk inda
masoyin gaskiya yake Maheer yakai ayi kwatance dashi, inda ace soyayyarsa bata gaskiya
bace wllh baze tab'a jure irin abubuwan datake yi masa ba, a lokacin dayake expresing mata
irin sonda yake mata ta tsinci wani babban abu a kalamansa da kuma idanunsa, babu komai a
cikinsu face tsantsar tsagwaron gaskiya.
Kasa magana tayi lokaci guda kuma ta maida kallonta ga kyakkyawar fuskarsa ma'abociya
kwarjini da kuma haiba, kasa jure kallon k'wayar idanunsa tayi dan haka da sauri ta juya ta fara
tafiya, binta yayi da sauri sannan ya sake tsayarda ita yace " Queen ki gayamin dukkan abibda
yake Ranki a gameda ni, duk abinda zuciyarki ta fad'a miki Akan Maheer Lamid'o kawai ki
fad'eshi, koda ace zezama barazana ga Rayuwata nayi miki alqawarin cewar zan fahimceki,
kuma zanyi miki uziri akansa Queen! Idan ma bakya sona ne wllh ki sanar dani nikuma nayi miki
alk'awarin cewar bazan k'ara bibiyarki ba har abada!!
Juyowa tayi a firgice tana kallonsa sabida yanda kalamansa na k'arshe suka firgita duk wata
nutsuwa dake tareda ita. Girgiza masa kai tayi hawaye na bin kumatunta wanda yake baiyana
tsantsar tsagwaron soyayyar datakeyi masa, a raunane tace " taya Queen of tears zata iya
Rayuwa batareda Maheer Lamid'o ba? Idan har soyayyar dakakemin gaskiyace meyasa
zuciyar Umaisa zata kasayin Uziri gareka Maheer? Wllh banajin a kwai Ranar dazatazo zuciyar
Umaisa ta buga batareda d'ingon amon soyayyarka a ciki ba Maheer!!!! *KA YARDA DANI* ina
sonka with all my heart! Se'a lokacin kukan datake dannewa ya samu nasarar k'wace mata.
Kasak'e yayi yana kallonta zuciyarsa na k'ara ruruwa da wutar k'aunar ta, tareda jinjinawa
jarumtar yarinyar, tunda harta iya b'oye abinda ke ranta harta kasa fitar dashi se'a yanzu, wani
irin farin ciki ne ta ziyarci zuciyarsa lokaci guda ya juya wajen motarsa se faman murmushi yake
mata, motar ya fad'a tareda barin unguwar zuciyarsa fesss sabida ya samu cikar burin
Rayuwarsa.
Motar tabi da idanunta harta dena ganinta sannan ta juya ta nufi islamiya zuciyar ta a cikeda
farin ciki.
Washe gari da safe kamar yanda Manager yayiwa hajiya Murja alk'awarin zezo don suga juna
Akan maganar plan dinsu na gaba da zasu gudanar kuwa haka akayi, wajen misalin k'arfe
biyar na yammacin alhamis Manager ya dira a cikin gidan, sanye yake cikin K'ananan kaya
wa'yanda suka baiyana cikar zatinsa da kuma haibarsa, inda kansa ke sanye cikin bak'ar hular
p cap, idanunsa sanye suke cikin wani bak'in glass k'irar Companyn prada, k'afafunsa kuma a
sulke suke cikin wani bakin takalmi k'irar Companyn Batozy, a nitse yake takawa harya tura
k'ofar perlorn ya kunna kai ciki, Babu kowa a perlourn se binta 'yar kwabo dake kallon wani
Hausa film, a k'asaice ya shigo perlourn ya zauna tareda hard'e k'afafunsa, a dake ya kalli Binta
'yar kwabo yace " kiramin Hajiya kice mata Manager ne yazo, washe baki tayi da sauri ta mik'e
tace "0h to bari na sanar da ita, jikinta har rawa yakeyi sabida tasan maganar kudi ce ta kawo
shi, tana shiga ta sanar da Hajiya Murja, kusan a tare suka fito perlourn,
da sakin fuska Hajiya Murja tace " maraba da Manager gidan kud'i yau dai gani gaka Allah ya
yarda, ta fad'a tana dariya harta zauna.
Kallon tsaf Manager yayi musu cikin bak'in gilashin dake manne a idanunsa, murmushi yayi me
sauti sannan yace "kamar yanda na fad'a miki a baya Hajiya yanzuma zan sake maimaita miki
cewar duk d'an daya haifu cikin Uwarsa da kuma ubansa tofa dole ne ya kasa manta
kamannin mahaifiyarsa, musamman ma idan wani ko wata ya zama silar zubar hawayen
wannan mahaifiyar tasa kokuma silar rushewar Ahalinsa, azoton ki kokuma tunaninki ya zafin
wutar fansar dakeci a zuciyarsa zata kasance yayin da yayi arba da abin harinsa agabansa???
Zaro idanu tayi cikeda tsantsar tsagwaron tashin Hankali take nunashi, lokaci guda miyan
bakinta ya k'afe k'af sabida tsabar tashin hankalin datake ciki, dak'yar ta iya tattaro kalaman
dake bakinta tace " mmmm... ..Mah...eer!!!
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:27_
___________ wani killer murmushi ya saki sannan ya sake maida kallonsa garesu a karo na
biyu, tab'e baki yayi sannan ya zare p cap din dak e kansa, a wannan lokacin babu abinda ke ci
a zuciyarsa face wutar fansa, glass d'in idonsa ya zare tareda d'ago dara-daran idanunsa
wa'yanda suka fara canza launi sabida fishi, nan da nan jijiyoyin kansa da wuyansa suka
mimmik'e, a nitse ya fara takawa har zuwa gabanta, wuyan ta ya dank'a da dika hannayensa
sannan ya wani shak'eta yace "shin zaki iya tuna ranar *28/12/1997 k'arfe 9:30pm* na dare? To
idan kin manta bari tafin hannuna ya tuna muki! Ya fad'a tareda d'auketa da wani mahaukacin
mari, wanda yasa taga wasu jajayen taurari sunayi mata shawagi a tsakiyar kanta.
Kwarfeta yayi tafad'i tim a k'asa har seda kanta ya bugu da K'aramin table din glass din dake
perlourn ya fashe, wata razananniyar k'ara ta saki lokaci guda tareda fashewa da wani irin kuka,
dariya Maheer ya saki wadda iyakacinta lips dinsa, lokaci guda kuma hawaye suka fara zubo
masa tamkar bazasu tsayaba, sunkuyawa yayi dab da ita sannan yace "meyasa kika saka
momyna kuka? Me tayi miki a rayuwa wanda yasa kikazama silar rusawar Rayuwarta?
"Shin meye laifin Mu da kika zama silar Rabamu da mahaifiyarmu? A sanadin abinda kika
aikatawa Momy yau gashi an wanyi gari mun rasata, tatafi tafiya ta har abada kuma duk *KECE
SANADI!!* dan haka na rantse da wanda raina yake hannunsa sena d'and'anawa Rayuwarki
irin kwatankwacin bak'in cikin da kika d'and'anawa tamu Rayuwar damu da mahaifiyar mu!
haka kuma sena sauyawa miki rayuwarki ta hanyar k'ask'antar dake mafi munin k'ask'anci,
tayanda sekin gwammaci mutuwarki akan komai, bazan tab'a barinki ki zauna lfy muddin ina
raye sena tabbatar da cewa na dasa miki bak'in cikin da zaki rayu dashi a cikin zuciyarki har
zuwa ranar da ajali ze riskeki riskeki!!
Mik'ewa yayi tareda k'arasawa gaban Binta 'yar kwabo wadda ta takure a guri d'aya sabida
tsoro da kuma tashin hankali, murmushin gefan baki yayi tareda wurga mata wani matsiyacin
kallo wanda yasa duk taji ta muzanta a gabansa sannan yace "saurin me kikeyi haka? Aike
banzo kankiba tukunna sabida ban fara nazari akan irin azabar dazan yi miki ba, don haka seki
zauna cikin shiri kafin na juyo kanki!
Ficewa yayi daga perlourn zuwa waje, a farfajiyar gidan ya tsaya tareda k'wallawa Lawan mai
gadi kira kamar ze fasa gidan sabida b'acin Rai, a hanzarce Lawan ya k'araso gurin tareda
sunkuyawa cikeda ladabi yace " ayi hak'uri Ranka ya dad'e Uziri ne ya kamani shine na
kewaya,
A tak'aice Maheer yace " ina ma'aikatan danace ka samomin?
Cikeda girmamawa Lawan yace yallab'ai suna d'akin dake baya a can na saukesu kamar yanda
kabada Umarni, murmushi Maheer yayi sannan yace " dakayu, maza kaje ka kira min su kuzo
tare, da Hanzari Lawan ya mik'e don cika umarnin da aka bashi, cikin minti kad'an se gashi ya
dawo tareda wasu manyan halittun 'ya'yan arna a bayansa,
Sanye suke cikin wasu riguna wayanda suka tsaya musu iya gwiwarsu sabida girmansu,
hakanne ya bani damar k'arewa damatsan k'afar su kalo, a murd'e suke sosai ga tsayi ga kuma
kauri, kaida ka gansu zaka fahimci sunji noma, sabida tsoron da suka bani har seda alk'alamina
ya fad'i k'asa, itakuwa *JANAF* suna had'a ido da ita ta zura da gudu ta cika wandonta da
iska
A haka suka k'araso gurin suka tsaya, cikeda girmamawa suka fara gaida maheer wanda ya
shagala da kallon irin girman halittarsu Victoria da kuma Yukeria,
Tab'e baki yayi sannan yace "kubiyoni, babu musu suka mara masa baya, se faman sauke
numfashi suke sabida tsabar k'ibar da suke dashi, a haka suka kunna kai cikin perlourn, cikeda
k'asaita ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun perlourn yana k'arewa su murja kalo cikeda
tsana, Binta 'yar kwabo kuwa tunda tayi ido hud'u dasu Victoria ta saki futsari a wandonta
sabida yanda ta tsorata dasu.
Cikin harshen turanci Maheer ya kallisu Victoria yace " aikinku a gidannan shine, kullum idan
kuka tashi da safe ku tabbatar kun fitar da wa'yannan matan waje kun zanesu duka me lafiya,
sannan ku sakasu su goge duk wani lingu da sak'on dake cikin gidannan, haka kuma kafin su
kwanta ma ku tabbatar jikinsu ya gaya musu sannan ku maidasu d'akin da aka sauke ku a ciki
su dinga kwana, se kuma abu na k'arshe banyarda kubasu abincin daya wuce garin kwaki ba.
Cikeda ladabi suka amsa da "yesss sair, shin zamu iya fara aikinmu daga yanzu? Tab'e baki
yayi sannan yace " why not.
Tun kafin ya rufe baki Victoria ta sab'i hajiya murja a kafad'a tayi waje da ita, hakama Yukeria
itama ta cakumi Binta 'yar kwabo sukayi waje dasu, duk irin ihun da sukeyi hakan besa sun
k'yalesu ba seda sukayi musu lilis sannan suka k'yalesu.
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:28_
___________ tun kafin a rufa sati su Hajiya Murja suka fita haiyacinsu, duk sunbi sun kod'e
sun jeme tamkar basu ba, sabida yanda rayuwa ta juya musu, tun ba'aci litinin da talata ba tuni
suka sare da lamarin maheer, Binta 'yar kwabo kuwa ta tsinewa Maheer yafi cikin kwando dubu,
*SUSMER INTERNATIONAL HOSPITAL ABUJA* sosai Dady yake samun kulawa a k'ark'ashin
jagorancin Dr.khabeer mahmoud, sosai khabeer yakejin tausayin Dady tareda nuna duk wata
tausayawarsa gareshi, don haka sabo na musamman ya shiga tsakaninsu dashi, har wasu
lokutan Dady yakanji wani irin bak'on yanayi a tareda khabeer d'in, b'angaren Maheer shima
yanayin iya bakin k'ok'arinsa wajen kulawa da mahaifin nasa dukda baya zuwa Asbitin se sanda
Dadyn yake bacci sannan yake zuwa, sosai yakejin kewar mahaifin nasa, amma kuma babu
yadda ya iya dole ne yaci gaba da hak'uri har zuwa ranar da komai ze daidai ta.
Yau ta kama monday ne, don haka tun safe Umaisa ta shirya cikin uniform dinta don zuwa
makaranta, d'akin Baba ta shiga da sallamarta, a bakin gado ta samu Baba ta rafka uban
tagumi, dariya Umaisa tayi sannan tace "ke fitinanniyar tsohuwa meye matsalarki ne haka?
Cire tagumin Baba tayi sannan ta fashe da kuka harda sharar hawaye, zuru Umaisa tayi tana
kallonta sannan tace" ikon Allah yau naga abinda ya isheni ni Fatimah! Me nayi miki zaki sani a
gaba kinamin kuka?
Bakin zaninta ta kama tana goge hawayen fuskarta tareda fad'in "Na shiga Uku ni Binta da
lamarin Mamuda gabad'aya gidannan a cike yakeda yahudanci kala-kala, yanzu fisabilillahi ki
kalli yarannan su Khabeeru da Faruku gaba d'ayansu sun zama magidanta amma babu Aure
nikam wllh inajiyewa kaina tsoron abinda zeje yazo, nan kuma gaki ga Rumana dukkan ku
Nono ya gama cika muku k'irji amma kuma babu mijin Aure, ta k'are maganar tana sharar
k'wallah.
Tinda ta fara magana Umaisa ta had'e rai tanayi mata wani kallo, tab'e baki tayi sannan ta mik'e
tace" lallai ma tsohuwar nan kin zak'e dayawa, to ai seki samomana mazajen da zamu aura d'in
tunda akanki muke zaune, ni wllh nazata ma wani abin arzik'in ne yake damun ki shiyasa ma na
tsaya ina b'atawa kaina lokacin sauraronki. Ta fad'a tana k'unk'uni, wata uwar harara Baba ta
zabga mata, sannan tace "yau naji tsigalalliyar yarinya, waiyyo Allah na binta! To kinga Uwar ki
Badi'atou kikayiwa da ubanki Mamuda, shegiya kod'ad'd'iya me zubin sadakar yallah.
Banza tayi mata ta