Showing 24001 words to 27000 words out of 80273 words
Chapter 9 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf
flastic chair dake
d'akin yaja ya zauna, sannan ya gaida su Ummie,
Kansa yad'an shafa sannan ya mik'e zuwa kusa da gadon Mamie, hanunta ya kama ya rik'e
gam a cikin nasa, sannan yace "Mamie ya jikin naki? Murmushi Mamie tayi sannan tace "da
sauk'i sosai Babana, ya gajiyar d'awainiya kuma? B'ata fuskan khabeer yayi yace "haba Mamie
don Allah, kemafa kamar Uwa kike a gurina, ban tab'a banbanta matsayinku keda Ummie ba a
cikin zuciyata, badan komai ba sedan irin d'inbin soyayyar da kika nunamin a rayuwata Mamie,
i beg you Mamie karki sake fadar haka na rok'eki plss!
Wata kwantacciyar kwallace ta tasowa Mamie, da sauri khabeer ya girgiza mata kai alamar
kartayi kuka sabida condition d'in ta, damk'e hannunsa Mamie tayi batareda ta sake ce masa
komai ba, inda a ranta take girmama irin k'aunar da khabeer d'in yake nuna mata a matsayinta
na kishiyar mahaifiyarsa, amma dukda hakan yaran basa wani nuna banbanci a tsakanin ta da
iyayensu. Shirun da khabeer yaji yayi yawane yasa ya kalli Ummie yace " Ummie mamie kuwa
taci abinci? Murmushi ta sakar masa sannan tace 'Ae taci sosai ma, a haka Dr. Abbas ya shigo
d'akin ya samesu,
Da sakin fuska ya mik'awa khaber hannu suka gaisa, sannan ya kalli su Ummie dake zaune ya
gaishesu, Ruman ce ta fara gaisheshi sannan Umaisa ma ta gaida Dr. Abbas d'in, murmushi
yayi sannan ya kali khabeer yace Dr. Khabeer ka tattara iyalanka kuje zuwa waje sabida zan
gana da mara lfy ta.
Murmushi kawai khabeer yayi tareda kallon su Ummie yace "iyalan Alaji Abba zakace bawai
iyalan khabeer mahmoud muhammad ba. Ya fad'a yana dariya,
sosai abin yabawa Dr. Abbas dariya, a ransa yace lallai khabeer baka da dama wllh, amma
kuma a zahiri yanayin rayuwarsu da iyayensa tana bala'in burgeshi, musamman yanda suke
wasa dakuma dariya a tsakaninsu, sekace wasu kakanni da jikokinsu,
Suna fita wata nurse ta shigo d'akin hannunta d'auke da wani babban faranti me d'auke da
magunguna da kuma injection da drip a ciki, da sakin fiska victoria ke tambayar mamie ya jikin
ta? Sosai mamie taji dad'in hakan harta kasa b'oyewa, a haka Dr. Yayi mata Alurar sannan ya
mak'ala mata ragowar Drip d'in daya rage, tun kafin ya gama saka mata drip d'in bacci yay
awon gaba da mamien, sabida a cikin Alluran da akwai me saka bacci, koda su Mama suka
dawo d'akin a haka suka sameta tanata kwasar bacci, don haka suka tattara suka bi Farouq ya
maida su gida, inda sukabar Umaisa da kuma Ruman.
*KADUNA STATE*
Wani babban Asbitin kudi Dady yasa drivern sa ya kaisu, kasancewar ansan da zuwansu cikin
mintunan da bazasu gaza biyarba suka karb'i Abdul cikin gaggawa, wani d'aki na musamman
suka nufa dashi don bashi taimakon gaggawa, lak'amewa Abdul yayi sekace wani mara lafiyan
gaske, ko motsin kirki bayayi illa hannunsa kawai daya d'ora bisa kan cikinsa yana juyi kamar
ze mutu, Latsa cikinsa likitan yake ta famanyi cikeda k'warewa gamida son gano abunda ke
damunsa, k'yallara ido Abdul yayi kad'an don ganin adadin mutanen dake d'akin gudun karya
b'ata wasansa, ganin babu idon sani a ciki ne yasa Abdul yay zumbur ya mik'e yace "haba Dr.
Don Allah, irin wannan matsamin cikin da kakeyi ai seka fasamin hanjin ciki, ya fad'a yana gyara
zaman rigar dake jikinsa, hannun Dr. Ya kama sannan yace pls don Allah ina so nayi ganawar
sirri dakai pls Dr. ! Ya fad'a yana wani shanye idanuwa kamar gaske.
Ba musu Dr. ya amince da batun Abdul d'in inda ya buk'aci da nurses d'in su fita su barsu, haka
kuwa akayi, suna fita Abdul ya sanar da Dr. Uzirinsa tareda tarin hujjojinsa nayin hakan, sosai
jikin Dr. Yayi sani dajin irin labarin k'aryar da Abdul ya zuga masa, nan da nan ya amince akan
zai taimaka masa tareda bashi tarin goyon bayansa, wani mugun murmushi Abdul ya saki, a
zuciyarsa yace i'm comming 4 you whitch, a zahiri kuma ya wani marairaice yace "pls Dr. Don
Allah kasan yanda zakayi da babana sabida karya gane komai pls! Murmushi Dr. Yayi sannan
yace " karka damu nasan ta yanda zan b'illowa al'amarim, insha Allah kuma zamu sami abinda
mukeso, Rungumeshi Abdul yayi tareda share munafukar k'wallar dake idonsa.
Dr. yana fitowa daga d'akin ya kalli Dady yace "Alhaji muje office, ba musu Dady ya mara masa
baya suka nufi office d'in likitan, wanda naga an Rubuta Dr. Hashim a jikin k'ofar, suna shiga Dr.
Ya kalli Dady yace" ka zauna mana Alhaji, ba musu Dady ya zauna dukda cewar zuciyarsa
babu nutsuwa a cikinta hakan bai hanashi zaman ba, sometimes yakanji wani irin abu a saman
k'irjinsa tamkar an d'ora masa dutse a kai, sedai har zuwa yanzu ya kasa gane actueal abinda
ke damunsa, musamman idan ya kalli Abdul wanda yake ganin tamkar wani babban jigone a
Rayuwarsa, so tari idan ya kalli Abdul d'in yakanji wani bak'on al'amri a tareda yaron, sab'anin
wasu lokutan kuma da yakanji cewar baya k'aunar ganinsa ma gaba d'aya. Katse masa tunani
Dr.Hashim Yayi ta hanyar cewa" Gaskiya Alhaji Yaronka yana cikin wani hali, duba da irin ciwon
dake shirin kamashi, wanda yake tamkar wata babbar barazana ce a cikin Rayuwarsa, don
haka sekun kula sosai dashi, duba da irin matsalar dayake fama da ita, dole ne ku kiyaye b'acin
Ransa, sabida idan har kuka bari Ransa ya b'aci a kwai wata jijiya dake tsakanin mahad'ar
kansa da kuma k'wak'walwarsa, wadda idan jinin dake gudana ta jikinta ya tsaya tofa ze
dingayin abu tamkar wani mahaukacin zaki, wanda idan baku mik'e tsaye bama ze iya zame
masa tamkar hauka.
Zaro ido Dady yayi yace "Hauka kuma Doctor? Batareda Dr. Hashim ya kalleshi ba yace "
tabbas kuwa Alhaji, don haka you have to very carefull. cikeda kad'uwa Dady yace "insha Allah
zamu kiyaye, fatana dai Allah ya bashi lfy, murmushi Dr. Yayi sannan yace " karka damu insha
Allah komai zeyi daidai, da zarar Drip d'in da muka saka masa ya k'are zamu sallameku zuwa
gida.
mik'ewa Dady yayi tareda yiwa Dr. Godiya ya fita, chages d'in kudin yaje ya biya sannan ya
koma reception d'in Asbitin ya zauna tareda yin shiru, duniyar tunani ya tsunduma ciki,
zuciyarsa cikeda son tuna wani abu wanda har yanzu ya kasa tuna menene shi, so tari idan ya
zauna haka yakeyi, amma dukda haka har yau ya kasa tuna komai, wasu lokutan sedai kawai
jikinsa ya dinga bashi cewar tabbas a kwai abinda ya rasa a cikin Rayuwarsa mai matik'ar
mahimmanci wanda ya kasa tuna ko menene shi, *(niko nace babu abinda ke damunka se
kewar gudan jininka Maheer!!!)*
Se wanjen magrib aka sallamesu zuwa gida, tun a hanya Dady yake tattalin Abdul d'in, inda a
zuciyar Abdul hakan yayi masa dadi sosai, dukda cewar yana mugun jin tausayin mahaifin
nasa, sabida tunda ya dawo gida be samu ya huta ba ballantana ya samu damar cin abinci,
amma kuma ta wani bangaren na zuciyarsa dad'in haka yajii, sabida ko babu komai ze samu
damar cin Uwar su Binta 'yar kwabo da kuma uwar gaiyar tasu wato Hajiya murja da tawagar da
suke tara musu a cikin gida.
Tofa lallai Abdul zaka kirawa kanka ruwa
*ABUJA*
A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah, haka kuma kullum kwanakin mu k'arewa sukeyi
Batareda mun ankare ba, a yau aka sallami mamie suka koma gida, sosai jikinta yayi sauk'i,
dan haka ta kwantar da hankalinta cikin iyalinta tareda ragewa kanta damuwa, a haka rayuwar
gidan ta dinga tafiya daidai kamar yanda suka saba, bayan sati biyu da sallamo Mamie Abba
yace su shirya zasuje Gano don su gaida mahaifiyarsar, sosai su Ruman suka dinga murnar
tafiyar sabida har ga Allah sunyi kewar kakar tasu,
Wani mugun kallo khabeer yake binsu dashi, sabida ganin yanda suketa uban Rawar kan
zasuje Gano, don haka ya kalli Abbah yace" Abbah banda su Ruman zasuje sabida a kwai
makaranta dan haka su hak'ura kawai idan sun samu hutu se Driver ya kaisu, k'ura masa ido
kawai su Ruman sukayi sabida jin irin manakisar da yayan nasu yake shirin k'ulla musu, Abba
ne ya katse musu tunani ta hanyar cewa " hakane kam khabeer, hak'ik'a kayi magana me kyau,
Ruman suka bari idan kun samu hutu seku tafi dasu Usman insha Allah, kukuma Badi'atou
seku shirya gobe Driver seya kaiku. A haka taron ya tashi Umaisa se faman cika take tana
batsewa sabida takaicin yayan nata,
Washe gari tunda sanyin safiya su Ummie suka gama shirin su, inda Ruman taketa hawayen
takaicin an hanasu binsu Ummie, Umaisa kuwa k'in fitowa ma tayi, sabida bazata jure ganin
tafiyar tasu ba, Ameearh kuwa banda d'agawa Ruman hannu babu abinda takeyi tana murna, a
haka Motar su Mamie tabar harabar gidan, kafin su dau hanya seda suka tsaya a wani babban
super maket suka jingi kayan abinci da kuma na tsarabar da zasu kaiwa mutanan Gano sannan
suka d'auki hanyar Garin Kano,
B'angaren Maheer kuwa zaune yake cikin motarsa k'irar Formatic, sanye yake cikin wani farin
yadi anyi masa d'inkin jamfa, dukda cewar kansa babu hula hakan be hanashi yin kyau ba,
lallausar sumar dake kensa ya shafa har zuwa gemunsa wanda yayiwa zagayayyiyar fuskarsa
ado da k'ara mata haiba, cikeda k'warewa yaje tukin harya iso Zone E d'in, wayarsa k'irar
sumsung ya zaro daga aljihun gaban motar tareda k'ok'arin kashe map d'in daya kunna dan yi
masa jagora, fitowa yayi cikin takusa me cikeda izzah gamida tak'ama, a kan boot din motarsa
ya zauna tareda k'arewa Unguwar kallo agogon Rolex d'in dake d'aure a hanunsa ya kalla
tareda jan wani siririn tsaki, tabbas yasan nanne legislative Quaters Unguwar su Mujaheed
amma sedai baze iya gane gidan ba sabida wasu sauye sauyen da aka samu,
hankalinsa ya mayar zuwaga wayar dake hannunsa, wata numver naga ya lalaubo wadda aka
rubuta Mujaheed a jiki, be jimaba ya kara a kunnen sa, tareda gyara zaman takalmin fatar dake
k'afarsa,
Bugu d'aya Mujaheed ya answer tareda fad'in Lamido badai harka iso ba? Tab'e baki Maheer
yayi tamkar Mujaheed d'in yana kallonsa sannan yace " Yeah nazo mana amma kuma wllh idan
baka fito da wuri ba yanzu zan san inda dare yayimin, dariya mujaheed yayi sannan yace "kaida
bazaka tab'a canzawa ba Maheer, katse kiran Maheer yayi tareda maida hankalinsa kan wani
babban Get dake mak'otaka da inda yayi parking, wanda ake k'ok'arin bud'e k'aramar k'ofar
dake jikin get d'in, beautiful legs d'inta ta fara sanyowa, wa'yanda ke sanye cikin wani bak'in
silipers k'irar companyn Vinci, fuskarta babu alamun dariya ko kad'an, sanye take cikin wani
brown yuniform wanda yay masifar yi mata kyau, dukda cewar doguwar rigace a jikinta da kuma
babban hijab wanda ya tsaya mata a daidai gwiwarta hakan bai hana fitowar shap d'inta fitowa
ba, inda hannunta na dama yake rataye da wana cute jaka mai d'aukeda Al-Qur'ani mai gima
gamida sauran litattafan addini, a hankalj take tafiya tana tura baki, da alama ba'a son Ranta
zata makarantar ba, a hankali take takawa tamkar wahainiya sabida k'asaita harta iso ta
gefansa zata wuce, kauda kansa yayi da sauri, a ransa yace "amma wannan a kwai maiyar
yarinya wllh, inba masifa ba wai meyasa bazata fita a cikin rayuwarsa bane? Katse tunani yayi
ta hanyar dirowa daga saman boot d'in dayake zaune, hakanne yay daidai da isowarta gurin
motar, shan gabanta yayi da sauri, hakanne yasa ta d'ago daradaran idanunta ma'abota haske
ta saukesu a kansa, wani irin dogon numfashi taja a matik'ar tsorace tareda tafiya luuuuu zata
fad'i.....
_Comment_
And
_Share_
*Zm chubad'o*
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
*_A yau sadaukarwar ta babban abokina ce, kokuma ince abokin fad'ana. Yau gagarumar
kyautar takace HUSSAIN 80k, wannan shafi kyuta ce a gareka don hka na mallaka makashi
halak malak_*
*_Gareku masu yad'a cewar soyayyace a tsakanina da Hussaini 80k wannan ba gaskiya bane,
magana ta gaskiya itace babu soyayya ko kuma wani abu me kamada haka a tsakanina dashi
banda mutuntawa, dan haka don Allah masu yad'a wannan maganar qaryar kuji tsoron Allah ku
dena plsí ½í¹_*
_Page:17_
___________í ½í³– tafiya tayi gabad'ayanta zata fad'i lokaci guda kuma idanunta suka fara rufewa
tamkar wacce ke shin suma, cikin zafin nama Maheer ya jawota da dukan k'arfinsa, bata dire a
ko ina ba se akan faffad'an k'irjinsa, wani irin abu ne ya tsirga masa tundaga kan babban
yatsansa har zuwa tsakiyar kansa nan da nan zuciyarsa ta sark'e da wani bak'on Al'amari
wanda k'wak'walwarsa da kuma tunaninsa suka kasa fassara masa shi, hak'ik'a malam kimiyar
soyayya sunyi gaskiya da suke cewa" abinda baki ya kasa isarwa, to babu shakka gabbai suna
isar dashi yayinda suka had'u da junansu a guri guda, fuskarta ya zubawa idanu tamkar a yau
ya fara ganinta, tunda yarinyar ta shigo cikin Rayuwarsa ya kasa gane dalilin dayasa take tsaya
masa a rai koda kuwa ace be ganta ba, isowar Mujaheed gurin ne yasa Maheer ya farka daga
duniyar tunanin daya afka, lokaci guda kuma ya saketa ta fad'i k'asa, fad'uwar datayi ne yasa ta
bud'e idanunta da sauri tana zaresu cikeda tsoro, kallonta Mujaheed yayi tareda kiran sunanta
yace "Umaisa are you allright? Kallonta ta mayar kan Mujaheed d'in tareda fashewa da wani irin
kuka tace "pls ya Mujaheed tsoro nakeji, wllh tsoronsa nakeji, don Allah ka fad'a masa ya fita a
rayuwata ya dena tsoratani haka plsssss ya Mujaheed!!! Ta fad'a tareda saurin mik'ewa tsaye,
duk yanda taso ta tsaida kukan tayiwa Mujaheed bayani kasawa tayi, don haka ta figi jakarta ta
nufi gida da gudu tana kuka.
A yau karo na farko a rayuwar Maheer yaji cewar be kyauta ba daya zamo silar zubar hawayen
yarinyar, haka kawai seyaji zuciyarsa dukta dagule masa, dafashi Mujaheed yayi tareda fad'in
"friend a ina kasan Umaisa pls? Tab'e baki Maheer yayi tareda d'aga kafad'unsa yace " a ina
kuwa na santa banda a nan gurin? Nifa ban tab'a ganinta ba se yanzu, kallon tuhuma
Mujaheed kebin Maheer dashi sannan yace " baka santa ba kace friend? Amma kuma in har
baka santa ba ya akai take cewa ka fita a rayuwar ta, sannan kuma meyasa ka tareta a lokacin
datake k'ok'arin fad'uwa?
Kallon tsaf Maheer keyiwa Mujaheed sannan yace " don zata fad'i na tareta wannan bashi yake
nuna alamar nasanta ba Mujaheed, kowama zan iyayi masa hakan a matsayin taimako,
sannan kuma maganar in fita a rayuwarta kuma wannan shirme ne kawai irin na mata, wata k'ila
ko tatab'a ganin mai kamada nine a mafarkin ta shiyasa take fad'ar hakan, ya k'are maganar
tareda d'aure fuska tamau, shi'a dole beson renin wayo. Shiru Mujaheed yayi yana bin
Maheer d'in da kalon mamaki a ransa yace "amma Maheer a kwai cikakken d'an duniya, dubi
yanda ya had'e rai tamkar besan wani abu waishi dariya ba. Tab'e baki kawai yayi sannan yace
masa "muje.
Suna shiga gidan direct maine parlourn gidan suka nufa dan Maheer d'in su gaisa da Ammi
mahaifiyar su Mujaheed, da sallama suka shiga perlourn, babu kowa a parlourn se Shahida
k'anwar Mujaheed tana kallon wani indian series a tashar Zeeworld, sosai ta mayarda dukkan
hankalinta ga Tv, shiyasa duk sallamar da suke zabgawa ma bataji su ba, har Mujaheed ya
shigo tsakiyar perlourn bata lura dashi ba, don Haka a fusace ya d'au remote d'in dake ajiye
bisa rantsatstsiyar Royal chair d'in da sukayiwa perlourn Qawanya ya kashe Tvn, se'a lokacin ta
lura dashi, kamar zatayi kuka tace " pls ya mujaheed kaban rimote d'in na k'arasa kalla kar'ayi
min nisa plssssss, ta wani ja pls d'in. Had'e rai yayi tareda galla mata harara yace "dilla can
rufewa mutane baki, ai dama na lura dake na abinda kika iya se kallon film, wllh idan kikai
wasa sena hanaki kallon gaba d'aya, ya k'are maganar yana binta da harara, mik'ewa tayi tana
wani tura baki kamar zatayi kuka ta nufi hanyar khitchine, a kausashe yace "inkinso ma ki mutu
don Allah sabida haushi, shiru kawai maheer yayi yana kallon dramar da sukeyi tsakanin
Mujaheed da kuma Shahidah, haka kawai seyaji sun tuna masa da Abdul d'insa, juyowa
shahida tayi se'a lokacin taga Maheer, washe baki tayi tareda k'arasawa inda yake tace " lah ya
Maheer kaine yau a gidan mu, lallai shiyasa ashe naketa jin ana iska ashe mahadin kaduna ne
ya shigo Abuja. Ta fad'a tana dariya sosai, shima Maheer dariyar yayi sannan ya kalleta yace"
au nine ma Mahadin ko??
Dariya tayi sannan tace "ae mana sabida wahalar gani dakai, shiyasa na kiraka da Mahadi me
dogon zamani, harararta Mujaheed yayi sannan yace " to suda uwar zance zoki kira mana
Ammi a d'aki, tab'e baki tayi sannan ta fara tafiya, seda ta tabbatar kai hanyar da zata kaita
d'akin Ammi sannan tace " indai ni sudace to wllh gado nayi a gurin yayana Mujaheed. Tana
kaiwa nan ta arce sabida karya biyo ta, dariya Maheer ya kwashe da ita sannan ya Qaraso
parlourn ya zauna suna jiran fitowar Ammi.
*Afwan bana samun tim sosai, don Allah kuyi haquri da wannan.*
_Comment_
Nd
_Share_
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_