Showing 48001 words to 51000 words out of 80273 words

Chapter 17 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

12 Jul 2025

2717


Da mamaki Abba yake kallonsu sannan yace "amma kaidai Farouq anyi sakarai wllh, ace ka
kira d'an uwanka har so biyu baka sameshi ba amma bakayi tunanin kace part dinsa ka duba
lfyarsa ba? Sosai kai Farouq yayi cikeda jin kunyar abinda yayi.

Ajiye cokalin hannunsa Abba yayi sannan ya mik'e ya nufi part d'in Khabeer, da sallama ya
murd'a handile d'in k'ofar, yana kwance akan doguwar kujerar dake perlourn hannunsa a nad'e
bisa k'irjinsa, sanye yake da milk colour d'in jallabiya ta *COMPANYN EMRATY* sosai ta karb'i
jikinsa dukda cewar bashida hasken Fata sosai kamar ta 'yan Uwansa, amma kallo d'aya zakayi
masa ka fahimci fatar jikinsa a goge take irinta maza 'yan k'walisa kuma masujida kansu, har
Abba ya zauna daga gefansa Amma sam Khabeer bema lura dashi ba ballantana ma ya yaji
motsinsa.

A nitse Abba ya maida kallonsa ga fuskar Khabeer d'in yana nazarinsa, sosai yaga fuskarsa tayi
masa fayau duk yabi ya fad'a, nan da nan hankalin Abba ya tashi lokaci guda kuma yakai
hannunsa kan goshin Khabeer d'in, sosai yaji jikin nasa da zafi sosai, don haka Abba ya shiga
tashin sa, a hankali ya bud'e lumsassun idanunsa wa'yanda sukayi masa nauyi sabida tashin
hankalin dayake ciki, hatta Abba seda ya tsorata da irin sauyin da idanun Khabeer d'in sukayi,
cikeda damuwa Abba ya kalli Khabeer yace " ya salam! Son meyake damunka haka?

Shiru Khabeer yayi yana kallon Abba wanda shima kallonsa yakeyi, ido cikin ido suke kallon
juna lokaci guda kuma Khabeer ya maida idanunsa ya lumshesu, jikin Abba ne ya k'ara sanyi
don haka ya jawo Khabeer din zuwa jikinsa, lokaci guda kuma ya Rungumeshi yana
tambayarsa damuwarsa.
Shiru Khabeer yayi sabida harga Allah yana jin tsoron sanar daahaifin nasu damuwarsa, sabida
harga Allah bemasan ta ina ze farayin hakan ba, sedai bashida wani zab'i wanda ya wuce ya
sanar dashi gaskiyar abinda ke damun nasa!

Zare jikinsa yayi daga na Abba, sannan ya kama hannunsa ya rik'e cikin nasa wata nannauyar
ajiyar zuciya ya sauke muryarsa na rawa ya kalli Abba yace " Abbana!! Bansan ta ina zan fara
sanar dakai damuwata ba, amma zanyi k'ok'arin gaya maka matsalata ta hanyar da zatafi min
sauk'i wajen fahimtar dakai Abbah!
Sabida a duniyar nan gaba d'ayanta mutane biyu ne kad'ai suke iya samun kusanci da zuciyar
mutum, sune iyayensa, Duk duniyar nan Kaikad'aine wanda ya kamata ya fahimci damuwata

Abbah Sabida banida wanda yafika a duniyarnan, Abba ina sonta haka kuma banajin zan iya
rayuwa da wata mace bayan ita, Abba! Ya fad'a yana me dafe saitin zuciyarsa da hannunsa
guda.

Murmushi Abba yayi sannan ya kalli Khabeer yace " Son gaba d'aya maganar daka fad'a duka
naji kuma na fahimta, kuma insha Allahu ni mahaifinka nayi maka alk'awarin cewar zanje har
gidansu iyayen yarinyar innema maka Aurenta ko 'yar wacece ita, don haka ka sanar dani
wacece yariyace wannan kuma 'yar waye a cikin garin nan?
Ido Khabeer ya bud'e yana kallon Abba sannan ya mayarda kallonsa ga k'asa yace " Abba Ba
kowace yarinya bace illah *_UMAISA_* wllh Abba ina son..... "Ka rufemin baki Khabeer!!!!!
Abba ya katseshi cikin karaji da kuma tsantsar fishi gamida b'acin Rai yace " Ada inayi maka
kallon mara hankali Ashema ka wuce hakan!
Ban tab'a zaton haka a tareda kai na khabeer, da alama notinan dake cikin kanka sun kwance,
shiyasa harka iya kallon idanuna kake gayamin duk maganar datazo bakinka!!! Wannan wace
irin masiface haka? k'anwar taka kake gayamin kanaso Khabeer? To wllh ka godewa Allah
dayasa bana d'aya daga cikin iyayen da suke saurin yiwa yaransu baki, in badan hakan ba wllh
dasena na'ance ka khabeer!!!!! A fisace Abba ya fice daga perlourn yana huci.

A bakin k'ofar perlourn sukai kacibus da Mamie wadda ke tsaye tana sauraron duk maganar da
suka tattaunawa, ko kallonta Abba beyi ba ya wuce yabarta tsaye a gurin.

Da k'yar ta iya d'aga k'afarta ta shiga d'akin, kallo d'aya tayi masa ta fahimci irin gagarumin
tashin hankalin dayake ciki, zama tayi akan kujerar dake kallon tasa, sannan tace " Babana
kayi kuskure guda d'aya a raywarka, wanda zan iya fassarashi a matsayin wauta kokuma
shirme, ita soyayya a kowani lokaci baiyanata akeyi ba b'oyeta ba, sabida zurfin ciki baya haifar
da komai face cutuwa da kuma danasani kokuma ma ince zalintar kai. Wanda na tabbata da
ace idonka be gane maka Umaisa da wani ba da bazaka tab'a fitoda abinda ke Ranka ba! Don
haka a matsayina na Uwa a gareka khabeer ina me baka tabbacin cewar insha Allah zanyi iya
bakin k'ok'arin don ganin ka samu cikar burin ka.

A'a Mamie banaso ki tilasta mata ta soni, sabida kona aureta bazatayi min kallon masoyi ba
sedai ta kalleni a matsayin mak'iyinta! wanda nikuma bazan tab'a iya jurar hakan ba! Har gara
ajalina ya riskeni akan Qanwata tayi min kallon wanda ya rushe mata farin cikin Rayuwarta!!!
Mamie idan har masoyi ya cika masoyin Qawarai to ze iya sadaukar da farin cikinsa domin farin
cikin abin Qaunarsa, haka kuma Sadaukarwa tana d'aya daga ciki jigon soyayyar gaskiyah!!!!

Amma khabeer idan har zamuyi maka adalci ya kamata mu samamaka farin cikin Rayuwarka a
matsayinmu na iyayenka "haka itama ya kamata kuyi mata adalci Mamie!. Khabeer ya katseta
ta hanyar fad'ar hakan.

Murmushin k'arfin hali khabeer yayi sannan yace " Zan iya fassara son da nake mata a

matsayin jarrabawane ta ubangiji a gareni Mamie, Amma kuma banajin zan iya jurar gani zubar
hawayenta komai QanQantarsu, ballantana kuma ace nine silar zubar su, nafiso Abarta ta Auri
wanda takeso kuma ta rayu dashi cikin aminci, ta hakane kawai zan cika adalin masoyi a gareta
idan har na sadaukar danawa farin cikin don tabbatuwar nata farin cikin.!!!!

Shiru Mamie tayi tana kallonsa a ranta tace "lallai khabeer yacika adalin Namiji, lallai masu iya
magana sunyi gaskiya da sukace kyan d'a ya gaji Ubansa, tabbas a wannan rayuwar abune
mawuyaci kasamu adalin masoyi kuma nagartacce a yanda son zuciyar mutane ya yawaita a
wannan zamanin, kowa kansa kawai ya sani, baya tunanin kowa.
Hak'ik'a a Matsayin ta na mahaifiyar Umaisa tajiyewa d'iyarta takaicin Rasa nagartaccen mijin
dayake mata sona gaskiya, mik'ewa tayi jikinta babu k'wari tabar d'akin, koda ta dawo perlourn
kasa magana tayi sabida tsabar damuwar dake cinta a Ranta, kujerar data bari d'azu ta koma ta
zauna, ko abincin ma kasaci tayi.
Usman ne ya kalleta yace " Mamie ya naganki haka?

Murmushin yak'e Mamie tayi tareda b'oye damuwata tace "wllh jikin Baban nawa ne danaje na
gani duk senaji babu dad'i.

Zaro ido Usman yayi yace " Mamie wai kin manta Golden ne? Nanda safiya zakiga ya ware
kamar kowa, ni barima naje na dubashi, tashi Farouq ma yayi sannan yace "Muje nima na
dubosa tun kafin na sakeyin laifi a gurin Alhaji Abba. Dariya sukayi gaba d'aya sannan suka
mik'e harda Rumana da Umaisa suka tafi d'akin khabeer d'in.
Duk hirar da sukeyi, Itadai Ummie kasa cewa komai tayi, haka kuma abincin ma ba wani cinsa
takeyi ba sabida harga Allah ta gama tsorata da ganin yanayin Khabeer d'in.

Mamah ma tashi tayi ta marawa su Usman baya zuwa d'akin khabeer d'in, ya kasance daga
Ummie se Mamie, kallon Mamie Ummie tayi sannan tace " wllh Badi'atou inajin tsoron ciwon
nan na khabeer, kiduba fa ki ga yanda ya rame ciwon wuni da'aya sekace wanda ya shekara
yana jinya, nasan khabeer sosai yanada masifar zurfin ciki, wllh da ace ya sanar dani yarinyar
dayake so dani da kaina zan durk'usa har k'asa na Rok'eta ta soshi koda kad'anne!!!

K'irjin Mamie ne ya buga da k'arfi lokaci guda kuma wani irin gumi ya fara keto mata, hak'ik'a
dolene tayi wani abu akan wannan babban al'amarin dayake shirin ruguza farin cikin Ahalin.
Amma kuma a zahiri setace "Addu'a kawai ya kamata mu tayashi da ita, Allah ubangiji yayi
musu zab'in alkhairi gaba d'aya, a haka suka tashi zuciyar kowa a dagule.

*SUSHMER INTERNATIONAL HOSPITAL ABUJA,* su Baffa Gidad'o sun iso Abuja lfy, basu
dire ko inaba se Asbitin, tun kafin su perker motar Abdul ya bud'e murfin motar, seda Baffa

umaru yayi masa jan ido sannan ya dakata, a nitse suka sakko daga motar tareda kunna kai
zuwa cikin Asibitin, wata farar Nas Abdul ya tambaya yace " don Allah inane femele sogical
words din ku?

Nuna masa tayi sannan suka tafi, nan ma basu wani sha wahala ba suka samu d'akin da Dadyn
yake kwance, a nitse suka tura k'ofar glass d'in tareda sallama d'auke a bakunan su, kamar
daga sama Dady yaji muryoyin su lokaci guda kuma ya maida kallonsa garesu,

Da gudu Abdul ya k'arasa gareshi ya Ringumeshi k'am a jikinsa yana hawayen farin cikin ganin
mahaifin nasa......

_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:32_

*_Dis page is 4 you My darling UMMU DILSHAD mallakinki ne kiyi yadda kikaso dashi wllh na
baki shi kyauta�, haqiqa Qimarki ta musammance a idon Chubad'o, haka kuma karamcinki
gareni mai girma ne, sonso fisabilillahâ¤_*
___________📖 Sosai Dady yaji wani irin bak'on yanayi yana ratsa zuciyarsa wanda yafi
kamada tsantsar tsagwaron farin ciki, hak'ik'a ada ya riga ya gama yanke k'auna da sake
ganin danginsa ballantana kuma gudan jininsa, a yanzu babu abinda yake murk'usa zuciyar
Dady kamar abinda ya aikatawa gwarzon d'ansa Maheer!! Idan a kwai abinda yake d'aga masa
a yanzu be wuce Rashin Maheer d'in a tareda shi ba, Tunda suka shigo d'akin Dady yake kukan
farin cikin ganinsu gamida nadamar abinda ya dinga aikata musu a sanadin sakacin da yayi da
addu'a, musamman ma Baffa Gidad'o wanda gabad'aya kunyar had'a ido Dady yakeyi dashi,
don haka cikin kuka Dady ya had'a gaba d'aya hannayensa guri guda yace "don girman Allah
ku gafarceni ahalina! Akan abubuwan dana dinga aikata muku bisa Rashin sani, hak'ik'a na
tabka kuskure mai girma na sakacin danayi wajen wasa da addu'o'in neman tsari, shiyasa ma
har Murja da muk'arrabanta suka samu galaba a kaina irin haka!! Don haka ina Rok'on yafiya a
gareku 'yan uwana, musamman ma kai Gidad'o...! Ya k'are maganar yana sharar hawaye

Murmushi sukayi gaba d'ayansu sannan Baffa Umaru ya kab'i maganar yace " hak'ik'a ka tafka

babban kuskure Lamid'o, wannan kuskuren daka aikata kuwa shine yin sakaci da ambaton
Allah tareda wasa da addu'o'in neman tsari, da ace kayi Rik'o dasu wallahil'azeem da baka
tsinci kanka a irin halinda kasamu kanka a ciki ba! Amma babu komai dama komai
muk'addarine daga Allah, haka kuma tun Ran gini Ran zane Allah ya rubuta faruwar hakan,
sedai kawai a kiyayi gaba tareda Fatan Allah ya yafe mana gabad'yanmu.

Da Amin suka amsa gabad'aya, sannan Dady ya kallesu yace "Shin ya akai ma kukasan inda
nake har kukazo gareni?

Shiru sukayi gabad'ayansu aka rasa wanda zece k'ala a gameda tambayar da Lamid'on yayi,
Baffa Gidad'o ne ya dafa kafad'unsa sannan yace " mu kanmu mun samu labarin inda kake ba
tareda zato ko tsammanin hakan ba a safiyar yau, kuma mun samu labarin ne daga Bakin
Maheer.
"Maheer!!!! Dady ya fad'a cikin karaji gamida tsantsar kad'uwa!

Ae Maheer!!!!

Wasu zafafan hawayene masu zafi suka fara zubowa Dady, lokaci guda kuma ya damk'o
hannun Gidad'o yace " yanzu ina Maheer d'in yake? Don girman Allah ku kiraminshi innemi
gafararsa, hak'ik'a ban cancanci yazo inda nake ba, tunda nida bakina na gaya masa cewar
karya sake waiwayar inda nake a Rayuwa!! Haka kuma na fad'amsa cewar na sallamawa
duniya sh......... Numfashinsa ne yayi sama lokaci guda idanunsa sukayi sama.

K'arar na'urar dake nuna yanayin daidaituwar numfashin nasa ce ta tsaya chak, da wani irin
mugun sauri Baffa Umaru ya danna na'urar kiran gaggawa. In a second segasu Dr. Viru sun
hallara a d'akin.

Su kansu seda suka firgida da ganin irin halinda Dady yake ciki, nan suka shiga bashi taimakon
gaggawa, sunsha wahala matik'a amma still ba wani canji da aka samu. Dole yasa suka yake
shawarar kiran Dr. Khabeer.

Khabeer wanda ke kwance bisa makeken gadonsa a nan nad'e cikin bargo Mamie tana ta fama
dashi akan ya tashi yasha kunun tsamiyar data damamasa amma yak'i, a haka har Ummiensa
ta shigo d'akin ta Samesu, murmushi Ummie tayi sannan ta kalli Mamie tace" hmm ai kinsaba
tsayawa kina lallab'ashi akan abinci, shiyasa shikuma yake k'ara narkewa.
Dariya Mamie tayi sannan tace "ai Baban nawa d'an a lallab'a ne, don haka barni kawai dashi
wannan al'amarin na Uba da 'ya ne.

Dariya Mamie tayi sannan ta zauna daga bakin gadon tana binsu da kallo, seda Mamie tayi
masa da gaske sannan ya bud'e tsimammun idanunsa wa'yanda suka canza launi suka
k'ankance sabida damuwa, yamutsa fuska yayi sannan ya karb'a ya d'an sha, yana cikin shan

kunun wayarsa dake gefan Mamie ta d'auki k'ara, inda sunan Dr. Viru ya fito Rad'a-Rad'a a kan
screen din wayar, mik'a masa wayar Mamie tayi sannan ya amsa tareda kai wayar kunnensa.

Tun kafin yayi magana Dr. Viru ya sanar dashi abinda ke faruwa, da sauri khabeer ya mike ya
d'auki keyn motarsa ya fara k'ok'arin fita, dakatar dashi sukayi tareda cilla masa tambayar ina
zashi shida bayajin dadi?

A takaice yace " Mamie hospital zani, mara lafiyan dayake k'ark'ashin kulawata ne ciwonsa ya
tashi, kuma wllh He is in cretical Conditon, shiyasa nakeso naje na taimaka masa da abinda
Allah yayi min baiwa dashi, kasa magana sukayi gaba d'ayansu, a ransu suna mamakin Qarfin
hali irin na khabeer din.
Yana fita yaji kansa ya fara juya masa, don haka dole ya kira Usman ya tuk'ashi zuwa Asbitin,
A nan ma seda Usman d'in ya kamashi sannan ya iya takawa har zuwa cikin Asbitin,

Shi kansa Usman mamakin yayan nasa yakeyi, lallai wannan mutumin na musamman ne a
gurin khabeer, tunda har ya iya tasoshi yana cikin halin jinya, a haka suka k'arasa bakin k'ofar
d'akin da aka shiga da Dadyn, tsayawa Usman yayi, don haka khabeer ya kalleshi yace "ka
kaini ciki mana inyaso seka fito, haka kuwa akayi har ciki Usman ya kaishi, inda ya tarar dasu
Dr. Viru sun kacame wajen ceto Rayuwar mutumin da bayama iya ma hango fuskarsa daga
inda yake tsaye, haka kawai se Usman yaji cewar yana shi'awar ganin fuskar mutumin, a
hankali ya dinga takawa harya samu nasarar yin arba da fuskar Dadyn, sosai yaji mutumin ya
bashi tausayi haka kuma ya tsaya masa a Rai, da sauri ya juya ya fice daga d'akin a ransa
kuma yana jinjinawa aikin su khabeer din. Lallai likitoci suna QoQari sosai, haka kuma babu me
iya biyansu sai Allah (S.w.t).

Cikin ikon Allah kuwa khabeer ya samu nasarar shawo kan matsalar, dama ba wata babbar
matsala bace bututun iskar Dadyn ne ya toshe sabida yanda ya matsawa kansa da yawan
tunani da kuma damuwa, a haka suka turo gadon suka fito dashi zuwa d'aki na musamman,

Shiko Usman tunda ya fito daga d'akin yake kallonsu Baffa Gidad'o wa'yanda ke cikin tashin
hankali sabida Rashin lfyar Dadyn, babban abinda yafi jan hankalin Usman zuwa garesu shine
Abdul, sosai yaji tausayinsa haka kuma seya samu kansa dajin zafin hawayen da Abdul d'in
yake Zubarwa, haka kawai seyaji bayason ganin kukansa ko kad'an.
A hankali ya Qarasa gareshi tareda dafa kafad'un Abdul d'in, nan Abdul ya dago idanunsu ya
sark'e cikin na juna!!

Tofa babbar maganar!
_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:33_

___________📖Kallon juna sukayi kusan kimanin 5scond sannan, Abdul yace "kamar nasan
fuskar nan? d'auke hannunsa Usman yayu daga kafad'ar Abdul d'in sannan yace "a kwai
yuwuwar hakan amma abune mawuyaci nafi tunanin kamace kawai, any way i'm Usman
mahmoud muhammad, ni Qanin Dr. Khabeer mahmoud ne wanda ke kula da Rashin lafiyar
mahaifin ka, hannu Abdul ya mik'a masa yace" nikuma Abdussalam Nasir Lamid'o, murmushi
Usman yayi wanda ya baiyana fararan haqoransa yace "Nice to meet you Abdussalam, "mee
too Abdul ya fad'a shima yana murmushi, se'a lokacin Usman ya gaidasu Baffa Gidad'o tareda
tambayarsu ya mai jiki, da kulawa suka amsa masa a haka har wata nurse tazo ta samesu inda
take sanar dasu cewar zasu iya shiga su duba mara lafiyan, na musu suka nufi d'akin inda
shikuma Usman ya nufi office d'in ya khabeer donya d'aukeshi su koma gida,

A nan ya samu Dr. Abdullah se faman masifa yakewa khabeer d'in sabida yanda yake Qoqarin
kashe kansa akan abinda shiyafi cancanta daya sameshi, ganin Usman ne yasa Dr. Abdullah ya
rage fad'an dayake masa tareda tsira masa al'urar dake hannunsa, had'e rai khabeer yayi sosai
sabida bayaso Usman ya samu damar yi masa wata tambaya, sabida be shirya amsa masa ko
wace tambaya ba a halin yanzu, magunguna Dr. Ya mik'awa Usman yace " ka tabbatar kullum
yasha su akan lokacinsu, sannan ya maida kallonsa ga khabeer d'in yace "duk wasu magani
dazan baka da wasu dokoki dazan fad'a maka duk kasansu Golden, tunda you are a Doctor,
idan har baka kwantar da hankalinka ka Rage yawan tunani ba babu abinda maganin nan ze
maka, gobe da safe zanzo har gida naga jikin naka. Yana kaiwa nan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login