Showing 66001 words to 69000 words out of 80273 words

Chapter 23 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

12 Jul 2025

2721

saki ƙara tana kiran Abba, dariya Usman yayi sannan yace "wayace kiƙi faɗa min
zuwan nashi eh??

to idan baki saniba ma to dani aka bada Aurenki nine nan waliyi a matsayina na yayan Amarya.

dariya Mama tayi sannan tace "kunfi kusa kaida ita indai Umaisa ce bame shiga tsakaninku yaji
kunya.

Dariya Ruman tayi sannan tace "yauwa mamah Ashe kin kuwa gane, indai yaya Usman ne
sunfi kusa shida ita.

Dariya yayi sannan yace "to azugwai kar dai kisa in saki layi a gaban surikin ƙanina.

Zaro ido Ruman tayi sannan tace "kai yaya Usman manyance.

Dariya kawai Abdul da mujaheed keyi shiko maheer sedai Murmushi kawai yakeyi a ransa yana
misalta barkwanci irinna Usmsn,

se'a lokacin Usman ya maida kallonsa ga Abdul, lokaci guda kuwa ya shaidashi don haka yace
"wa nake gani kamar cry-cry ɗin abokina na Sushmer Hospital?

Dariya sosai Abdul yayi sabida shina ya ganeshi sarai sannan yace "oh gaka kaikuma baka
mantuwa kamar wannan surikin naku, ya faɗa yana nuna maheer da hannunsa,

dariya sukayi gaba ɗayansu nan suka shiga hira dukda cewar maheer ɗin be wani saba da
Usman ɗin ba amma haka kawai seyaji ya kwanta masa a ransa,

maheer ya kalli Usman yace Amma senake ganin kamar da gajiya a tareda kai ko?

murmushi yayi tareda sassauta necktie ɗin dake wuyansa yace "Hmm kaidai bari, wllh yau har
abinda yafi gajiya ma nayi, wani aikine yasha kaina a office wanda yasa gaba ɗaya naji na sare
da al'amarin, seda nasha wahala sosai.sannan kuma daga baya nasamu nasarar kammalawa.
mujaheed yace "ai dama indai mutum baya koɗuwa a office baya sanin mahimmancin aikinsa
inji momyna,

murmushi Usman yayi sannan yace "hajiya momy ai kodan ta tsokaneka zata gaya maka haka
mujaheed.

A haka sukaita tattaunawa akan abinda ya shafi harkan aikin Usman ɗin.

Ɓangaren Ummie kuwa babu yanda batayi da Mamie ba ta fito su gaisa amma fir mamie taƙi
yarda har seda Ummie tayi fishi ta fita tabarta a kitchine ɗin ta koma perlourn, duk abinda
mutanen perlourn ke faɗa Mamie tanaji kamar a kitchine ɗin suke hirar, idan suka faɗi wani
abin sedai ta taɓe baki wani kuma tace "hm a haka su Ummie suka dinga hirarsu gwanin
shi'awa,

Usman kallon Ummie yayi sannan ya karya kai yace "Ummie na baki min oyoyo ba fa,

Daƙuwa tayi masa tana harararsa, kallonaheer yayi yace "kaga Ummie nan ko kullum haka
muke fama da ita sam bata bani seaport.

dariya ummie tayi tana kallonsa, sabida inda sabo yaci ace ta saba da shakiyancin Usman,

Charaf Abdul yayi yace "Eyyah aboki nima haka nake fama da wannan ya nuna maheer sannan
yaci gaba da cewa "sam nima baya bani seapo..... "Amma ai kanema ka samu yafi ka rasa
mahimmanci boy. Maheer ya faɗa yana murmushi.

kofin glass ɗin dake hannun Mamie ne ya faɗi ƙasa a lokacin dataji sauƙar wannan kalmar a
kunnenta, nanda nan idanunta suka fara wata irin yana wanda hakan ya haifar mata da
ɗaukewar ganinta na wucin gaɗi, cikin wani irin fitar haiyaci ta taka glas ɗin fasashshen kofin
dake gabanta ta nufi perlourn har tana karo da ƙofar kitchine ɗin,
Tana fitowa perlourn tayi ido huɗu da maheer. Cikin sassark'ewar murya da rud'ani take nuna
maheer da ya tsaya, bakin ta har rawa yake wajen furta...

"wan .. wan.. wannan way?????

Maheer da hankalin shi ke kan wayar da aka kira shi minti biyu daya wuce, ya d'ago dan ganin
me Kiran nasa. Waigowar da zeyi suyi Ido hud'u da mamie.
Tsananin rud'u da firgici ne had'i da tsoro ya mamaye mamie, saboda abunda idanuwan ta ke
gane mata a yanzu. tsabar kaɗuwa lokaci guda mamie ta sulale ƙasa sumammiyah.

A lokacin da maheer ke kokarin tantance mamie, inaaah! Ai har takai k'asa.

gaba ɗaya ilahirin jama'ar dake parlour - n suka furta

Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!!!!! A tare sukayo kanta

Hankalin kowa yayi matuk'ar tashi over, baran ma umaisa, ummie da Ruman. Har rige-rigen
kai wa inda mamie ta fad'i k'asa suke yi.


Jijjiga ta suka shiga yi, suna furta

"mamie!!! Mamie!!! ". Cikin yanayi me nuna Tsananin tashin hankali.

Ummie ce tayi hanzari tashi ta shiga kitchen, ta d'auko ruwan roba, ba shiri ta shiga antaya wa
mamie su a fuska, Amma ba alamar zata farfad'o.


A b'angaren Maheer kuwa ya kasa Gano komai, gashi yana so yaga fuskar mamie Amma
hijabin ta ya rufe mata fuska, Wannan ne ya kasa bashi daman tantance ta. Gaba Ki d'aya kowa
ya shiga shock, kan kowa ya tushe.
Kallon tuhuma samarin suka fara bin maheer dashi alamun suna buk'atar Jin daga gare shi,
ganin Wannan baze fish-she suba yasa kabiru furta

"ummie ku d'auko ta, kusa ta a mota muje asibiti"

Toh! Shine kawai abunda ummie ta iya furtawa, cikin hanzari ta ta mik'e, da taimakon kabiru
suka tallabi mamie suka saka ta a mota, sauran jama'ar kuma suka bi Bayan su a motar
maheer.


Motar su Usman da faroug ce ta fara tsayawa, kafin tasu maheer su iso, har an fiddo mamie a
mota, a shiga da ita, kai tsaye emergency aka wuce da ita, saboda yadda jikin ya tsananta.


A tare maheer, Abdul da mujaheed suka fito daga mota, dikkan su cikin Tsananin damuwa,
cikin Asbitin Waige-waige suka tsaya yi Cikeda son su Gano inda aka bi da mamie,

Khabeer suka hanga ya rufa wa wasu nurses baya da suka gunguro injin oxygen, cikin
tsananin zafin nama gamida bajinta khabeer ya dasa mata oxygen ɗin cikeda fafutikar son
ganin ya samu daidaituwar numfashin ta.


Basu yi Wata Wata ba suka bi Bayan su suma, cikin kid'ime wa...




Cabdi! Ana wata ga wata masu karatu ku biyomu a cikin Shafi na gaba dan Jin yadda zamu
warware muku Wannan sark'ak'iyar...

_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:43_

___________ Koda suka shiga Reception ɗin guri suka samu suka zauna kamar yanda
sukaga su ummie sunyi, jigun-jugum sukayi aka rasa wanda zece ƙala ko wanne da abinda
yake saƙawa a cikin zuciyarsa a gameda ciwon na mamien,

Suna cikin haka Abba ya ƙaraso cikin Asbitin cikeda tashin hankali Shima, babu abinda yake
ƙara ɗaga masa hankali dayi masa yawo a kunnensa tamkar an kunna ansa kuwa kamar
maganar Dr. Abbas muhammad ta ƙarshe daya gaya masa, kan cewar muddin suka sakeyin
sake ciwon Mamie ya sake tashi tofa zasu iya rasata! Sabida yanda matin ciwon nata yakai,
Kasa magana yayi balle harya samu ƙarfin gwiwar tambayar menene maƙasudin faruwar
hakan, ƙarfin hali kawai Abba keyi dan haka a daddafe ya iya gaisawa dasu Maheer wanda
yakewa kallo a matsayin suriki.

Seda suka shafe awa biyu cur sannan suka samu nasara wajen daidaituwar numfashinta ya

dawo dai-dai,

Allura suka kafa mata wadda zata sanyata dogon bacci sabida ta rage mata damuwa, sannan
zaratan likitocin guda uku suka fito fuskarsu a ɗauke da murmushi na musamman wanda ke
baiyana alamar nasarar da suka samu.

Gabaɗayansu office ɗin Dr. Viru suka wuce, wata matashiyar nass ce ta tsaya a gurinsu Abba ta
sanar dasu cewar an samu nasaran shawo kan matsalar mamien don haka Dr. Voru yana
buƙatar ganin Abba a office ɗinsa yanzu, tun kafin Abba ya iso ƙhabeer ya fito daga office ɗin
yana ƙoƙarin zare hanglove din dake hannunsa, kaciɓus sukai da Abba wanda ke ƙoƙarin
shiga, murmushi khabeer yayi sannan yace "Abba no need ma ka shiga, kawai ka faɗama su
ummie su wuce gida insha Allah komai zeyi daidai tunda yanzu mun gano bakin zaren komai.

Wata nannauyar ajiyan zuciya Abba ya sauke sannan yace "to Amma dai babu wata matsala
dai ko a tareda Badi'atoun?

Ɗaga masa kai khabeer yayi tareda bashi tabbacin hakan.

Nan suka ɗinguma da Abba da khabeer ɗin zuwa indasu Ummien ke zaune, basu wani sha
wahalaba khabeer yayi musu bayanin komai cewar jikin mamien da sauƙi tunda har gashi an
samu yanxu tana bacci.

Ajiyar zuciya duk suka sauke a tare tareda furta kalmar godiya ga Allah, sannan suka miƙe
sabida sanin cewar Asbitin ba'a buƙatar me jinya.

A harabar Asbitin mujaheed yayiwa maheer sallama yabi su Usman suka kama hanyar gida
tunda anguwansu ɗaya ne,

A motar ma jikin Abdul a matiƙar mace yake cikeda damuwa ya kalli maheer yace "ya maheer
wai me yake shirin fariwa ne haka?

"ni wllh jikina yayi sanyi sosai da ganin irin condition ɗin da matar nan take ciki! Ni babban
abinda ma yafi bani mamaki guda ɗaya ne da matar, yanda naga tana wani nunaka cikeda jin
haushi koma in kira hakan da tsana.

Murmushi kawai maheer ɗin yayi sannan yace nima kaina a duhun nake kamar kai Abdul!
Tayanda ma nakejin gaba ɗaya jikina yayi sanyi sabida a sanadina matar mutane ta samu kanta
a halin data tsinci kanta a ciki,

Shiru Abdul yayi kamar wanda keson gano wani abin sannan yace " ya maheer be kamata
mubar Umaisa a halin da muka barta a gidansu ba, kamata yayi ka zauna da ita kozata samu
sauƙin damuwar dake damunta, wllh ya maheer zuciyata ta kasa nutsu akan halin da mukabar
umaisa a ciki, musamman idan na tuna yanda take kuka a lokacin da aka fita da mahaifiyarta

zuwa Hospital!

Shiru maheer yayi tareda zare hular dake kansa yace "ni kaina inajin hakan Boy, sedai babu
yanda zamuyi don mu hanata kuka akan ciwon mahaifiyarta, insha Allahu nan zuwa gobe zan
koma Hospital ɗin kodan naga halin da mara lafiyan ke ciki.

da haka suka ƙarasa gida zuciyoyinsu duk a dagule.
_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:44_

___________Washe gari tun da safe Dady yayiwa Maheer waya ya Gaya masa cewar
yanada baƙi na musamman waƴanda ze gana dasu a ƙasar Turkey, Dan haka shi baze samu
damar zuwaba maheer ɗin ya shiya ya hacci taron bunƙasa kasuwancin na mahaifin nasa.

Babu yadda maheer ya iya dole a Ranar ya shika kimtsawa tafiyar dama besan da itaba gaba
ɗaya, bayan ya kammala wayar zuciyarsa babu daɗi ya miki ya fara shirin tafiyar sabida ta nan
Abuja se tashi, ɗakin dake kusada nasa ya shiga Wanda a Abdul yake zaune yanzu a ciki,
fuskarsa babu walwala Ya nufi gadon da Abdul ɗin ke kwance a kai yanata kwasar baccinsa.
Murmushin mugunta maheer yayi sannan Yasa hannunsa ya matse masa hanci ta yanda baze
iya shaƙar numfashi ba, ba shiri Abdul ya buɗe ido da sauri yana turo baki Yace "haba yyaa
maheer don Allah! mutum yana baccinsa kazo ka tasheshi.

Hararanshi maheer yayi sannan yace "oya malam tashi ka haɗa komatsanka ka wuce Kaduna,
nima kaina gaba zanyi Dady ya turani Qasar ISTANBUL zan wakilceshi akan buƙasa hannun
jarinsa a ƙasar, tareda halattar wani babban taro na ƙarawa juna sani.

Firgigit Abdul yayi ya mike zaune tareda dafa kafaɗar Maheer ɗin yace "why ya maheer don
Allah?

"sam yanzu be kamata kaje ko ina ba kabar Aunty Umaisa, becouse kai kaɗaine ƙarfin

gwiwanta, nasan yanzu she's so sad Akan halin da mahaifiyanta ke ciki, ni kaina i can't explain
how I feel when I seen her mother condition, wllh har muka dawo inajin tausayin maman nata a
raina, to ka misalta idan kaine a halin data tsinci kanta taya zaka fara Expressing ma wani ?

Shiru maheer yayi batareda ya iya ce dashi ƙala ba, wata uwar ajiyan zuciya ya sauke sannan
ya iya buɗar baki yace " hakane boy, but dukansu suna da mahimmanci a cikin rayuwata, now
Umaisa she's my wife but how can't I tell Dady bazan Iya zuwa inda ya turani ba?

"toba gani ba ya maherr ai zan iyayin dukkan abinda ya dace a taron, I will do all my best naga
mun cimma dukkan wata nasara da Dady yake fata, nidai babban fatana shine Stay with her
and you give her all the happiness she deserves for you, that's all Yaya heer!

Shafa kansa maheer tayi sannan yace "baran iya turaka ba boy, because this meeting is the
only oppotunity Da muke dashi, don haka karka damu insha Allah komai zeyi daidai, da
wannan maganar hirar tasu ta ƙare sannan Maher ya fita ya koma ɗakinsa tareda kunnan
system ɗinsa yayi booking jirgin daze kaishi ƙasar ISTANBUL ɗin,
Tiket ɗin Qarfe goman safe ya damu don haka ko zarafin samun Yin sallama Da umaisan ma
be samu ba, sedai yayi ƙoƙarin kiranta amma bata answer kiransa dan dole ya rabuda ita,
Abdul ne ya tuƙashi har zuwa air pod, a mota ya kira Abban Umaisa ya sanar dashi uzirinsa
tareda tambayarsa jikin mamie.
Da sakin fuska Abba ya amsa masa tareda yi masa Addu'ar alkhairi ta sauka lfy.

Koda suka isa air pod seda maher ya sake jaddadawa Abdul cewar ya tattara ya wuce kaduna
Amma fir yace wallh baze tafi ba har se sanda maheer ɗin ya dawo sa koma tare, tareda bashi
tabbacin cewar kullum ze dunga zuwa yana duba lafiyar Auntynshi da mahaifiyarta dake Asbiti.

Kallonsa kawai maheer keyi batareda yace dashi ƙala ba ya wuce yabarshi a nan, seda Abdul
yaga tashin jirgin nasu sannan ya bar air pod ɗin.

Wannan kenan.

A ɓangaren mamie kuwa sosai jikinta ke ƙara samun sauƙi, a ƙarƙashin kuƙawar Dr. Khabeer
da kuna Abdullah, kusan kullum Ruman da Umaisa suna hanyar Asibitin, Don haka Abba ya
takawa umaisan birki kan cewar sintirin zuwanta Asbitin yayi yawa, Gidan mijinta zata tattara su
kaita Bazema jira maheer ɗin ya dawo daga tafiyar dayayin ba, Garasu tattara ta su miƙata
gidanta shi baze iya da wannan zaryan ba, kuka umaisa ta dingayi duk a dalilin maganar da
Abba yayi na ze mayar da ita gidan wani.

Koda suka koma gida Abba ya sanar da ummie itama tayi farin ciki sosai, ko babu komai idan
umaisa ta tafi gidan mijinta zata samu Hankalin gwarzon ɗanta Khabeer ya kwanta har shima
ya fitarda matar Aure tunda yaƙi Beebah.

Da wannan hukuncin Abba ya koma side ɗinsa ya shiga kira wayar Baba donya danar da ita
cewar Jibi ze turo Driver ya ɗaukko ta sabida ranar juma'a da yardan Allah za'a kai umaisa
gidan Aurenta.

Sosai baba taji daɗin hakan don haka ta dinga sanyawa lamarin albarka tareda yiwa sauran
zaratan jikokinta fatan samun mata nagari.

Kamar yanda Abba ya faɗa hakane Kuwa ya kasance, tunda sanyi safiya ya tura Bala Driver
ɗinsa donya ɗakko baba daga Gano, Nan ma ba ƙaramin artabu sukai da baban Gano ba wai
ita ala dole bazeyi gudu da ita ba, babu yanda Balan ya iya dole yabi abinda baban tace, aiko
basu sukakai Abuja ba se ana sallar magrib.
Sosai Umaisa tayi murna da ganin Baba hakama Rumana, su Usman da Farouq kuwa ji sukai
tamkar anyi musu mutuwa sabuda zuwan Baban, tsaki Usman yayi wanda ke zaune biya kan
Daining yayi tareda ajiye spoon ɗin dake hannuɓsa yace "Oh ya Rabbi!! Shikenan ciwon kai
tazo.
Harararsu Rumana Farouq Yayi sabida ganin yanda suketa faman rawar kai akan Baban Gano,
taɓe baki yayi sannan yace "wannan ai ta wuce ciwon kai tunda idan tazo gidan mutane seta
addabesu ta hanasu sakat.

Daƙuwa Baba tayi masa sannan tace "Ubanku Mamuda ne addababbe bani ba, tareda wa
Ƴannan, ta faɗa Tana nuna su Mama da Ummie dake zaune suma sunacin Abinci,

Ɗakinta ta nufa su Ummie na biye da ita sannan su Ruman, tana zama ta fara tambayarsu ya
jikin Badi'atou n?

Murmushi mama tayi sannan tace "ai jikin da sauƙi sosai, wata ƙila ma kiga an sallamota daga
Asibitin yau ko gobe, washe baki Baba tayi sannan tace "to masha Allah bari na shiga wanka
konaji daɗin jikina tunda har jikin nata da sauƙi, dama Naso senaje Asibitin na dawo sannan
nayi wanka naci Abinci.
"Baba waye ze kaiki Asibitin to? Rumana ta tambayi Baban

Mujaddadi Usmanu mana, ta faɗa tana murmushi


Tabb Allah ya sauwaƙe in ɗaukeki a motana, Usman ya faɗa yana Ƙasa shigo ɗakin Yana ƴar
dariya.

Dariya Ummie tayi sannan ta miƙe tace "Baba barina kawo miki abincin nan kafin ki fito daga
wankan, da to Baba ta amsa mata tareda sanya masu albarka gabaɗayansu.

_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*

*Haqiqa naji daɗi sosai akan irin Tarin qaunar da kuka nunamin akan wannan littafi me taken
KIYARDA DANI, Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login