Showing 72001 words to 75000 words out of 80273 words
Chapter 25 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf
aka fesa mata
wannan adon ya ƙara fito da ainihin izharin kyanta da be baiyana ba tun farko. ( niko nace ikon
Allah Ashe kyauma yanada izaharinsa shima )
duk wannan abin a cikin awa ɗaya akayishi ba wani ɓata lokaci, babu abinda ke tashi a shagon
se ƙamshi mayataccen turaren dake tashi a jikin Umaisa, A haka Aunty maryam ta fito da
bunch ɗin 1k ɗin da Ummie ta bata ta miƙawa Sushmah tana murmushi tace "mun gode sosai
haƙiƙa kin cancanci da abaki lambar yabo sabida kinsan aikinki.
murmushi Sushmah tayi mekyau sannan tace "nikeda godiya Amarya Allah ya sanya alkhairi
kinji.
Itadai Umaisa batace komai ba su Rumana ne suka Amsa sannan suka fita zuwa parking
space suka shiga mota Driver yajasu suka Nufi Gidansi dake Zone E Apo legislative Quarters.
Koda suka iso gida duk muta nan Ba wasu mutane sosai duk an gama kwashesu zuwa
babban Event Center ɗin dake central area inda za'a gabatar da walimar a can,
******
A ɓangaren su Maheer ma sosai suketa hada-hadar zuwa gurin walimar shida abokinsa
Mujaheed da kuma Abdul, sanye Maheer yake cikin wata ɗanyar shadda gizna maroon se
faman yararin tsada takeyi, kansa sanye yake cikin wata dakakkiyar hula me tafiya da zamani
irinta ƴan meduguri (Zanna bukar) itama maroon amma da ratsin milk sabida aikin dake gaban
babbar rigar shaddar dake jikin nasa, ƙafarsa sanye take cikin wani tsadadden takalmi ƙirar
Batozy wanda yayi daidai da kalar kayan dake jikinsa.
A gogon Rolex ɗin dake hannunsa yaketa faman fafutukar ɗaurawa sannan Mujaheed ya
kalleshi yace "hey dude duk wannan adon fa bakasa turare bafa.
Da sauri Abdul buɗe drower ɗin maheer ya zaro wani tsadadden turare *_ORIFLAME
PRODUCTS GIORDANI_* ya fara feshe Maheer wanda ke tsaye dashi, kafin kace me tuni
ƙamshi ya gama buɗe ɗakin, masha Allah sosai Ango maheer ya fito yayi masifar kyau kamar a
saceshi a gudu.
Abdul ma ya fito yayi kyau dashi sosai abinku da yaro ɗan ƙwalisa lol
Ƙarar wayar maheer ce ta kaure ɗakin da wani irin kiɗa me taushin gaske, miƙewa Abdul yayi
ya isa ga wayar yana murmushi, daga ɗan nesa dashi Maheer yace "who is calling boy?
Dariya Abdul yayi sannan ya kalli screen ɗin wayar yace " *ACP SALEEM KHABEER KUMO*
ne yake kira.
Dariya mujaheed yayi yana kallon Maherr yace " lallai mijin *MALIKHA MALIKH* wata ƙila ya iso
gari ne yasa yake kiranka yaji inda muke ne.
Sushmah✍️
Chubaɗo
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page: 47_
Not edited♀️
____Murmushi Maheer yayi sannan ya ƙaraso ya karɓi wayar yana me faɗaɗa murmushinsa ya
manna wayar bisa kunnan sa na dama, tun kafin yayi magana *_ACP SALEEM KHABEER
KUMO_* yace " pls dude you should be fast mana don Allah wllh kowa ya taru kukawai muke
jira kaida Amarya.
Jim kaɗan Maheer yayi sannan yace " You mean wai har ka iso Abuja?
Ae mana amma ni kaɗai nazo sabida ma'am batajin daɗi shiyasa na barta a gida tareda yara,
yanzu dai don Allah ku hanzarta ku fito jama'a duk sun taru kaida Amarya kawai ake jira. Da
to maheer ya amsa sannan ya katse wayar yana murmushi, a hanzarce suka gama shirin
sannan suka fito se faman baza ƙamshi sukeyi
Mujaheed ne ke tuƙa motar Abdul kuma na a gaba se maheer wanda ya hakimce a baya
shikaɗai, cikin mintunan da bazasu gaza goma ba suka iso ƙofar gidansu Umaisa, seda suka
tsaya sukai sallar magrib sannan Mujaheed ya kira Rumana yace Su fito da Amarya.
Murmushi Rumana tayi sannan ta katse wayar ta kalli Aunty maryam tace "tofa Angwaye sun
iso ɗaukar Amaryarsu suna ma waje suna jiran fitowarta.
Dariya Aunty maryam tayi sannan ta miƙe ta ɗago Umaisa wadda ke zaune bisa Daddumar
data idar da sallah tace, Oya tashi kisa mu ƙarasa shiryaki tun kafin Maheer ya shigo da kansa,
hawaye ne suka cika ƙwayar idanunta da sauri Ruman ta dafata tace "haba kekuwa don Allah
karkiyi kuka mana ki ɓata kwalliyarki.
Banza tayi mata se faman tura baki takeyi a haka suka kammala shiryata Maryam ta rangaɗa
mata wani ubansun Roling dayake itama gwana ce a wannan fannin, kafin kace me Umaisa ta
fito tayi wani irin kyau tamkar bala'rabiyar ƙasar misirah.
Hannunta Suka kama zuwa falo a nan sukaci karoda Ya Usman da Farouq suma Sunci uban
ado cikin wata dakakkiyar Gizna Ash se faman yararin tsada da kyau takeyi, tsayawa sukai
suna kallonsu lokaci guda suka saki murmushi tareda ƙarasowa garesu, hotuna suka dinga
ɗauka sannan Aunty maryam ta tisata suka fice sabida idan tabi tasu Usman da Farouq to wllh
Zasuyita ɓatawa su Maheer lokaci ne.
A nitse suke takawa suna riƙe da hannunta, seda suka kusa dabda motar sannan Umaisa ta
tsaya cak taki tafiya, ɗaga haɗaɗɗen mayafin da Aunty Maryam ta Rufa mata tayi sannan ta
kalli Ruman tace "bazan iya tafiya ba indai banga Ya golden ba, tana kaiwa nan ta juya da gudu
tayi cikin gida direct part ɗin ya Khabeer ta nufa tareda buɗe ƙofar perlourn duk a lokaci guda,
A falon ta sameshi yana gyara zaman Hular dake kansa, dukda cewar baya cikin kwanciyar
hankali da nutsuwar zuciya sam hakan be Hanashi yin kyau ba, sanye yake cikin wada
dakakkiyar farar shadda ƴar ubansu wadda ta baiyana ainihin kalar fatarsa da kuma haibar
dayake tare da ita.
Tsayawa suka cak idanunsu ya sarƙe cikin na juna, kowa da abinda yake saƙawa a zuciyarsa a
gameda ɗan uwansa, da wani irin mugun gudu ta tafi ta faɗa jikinsa ta Rungumeshi, wata irin
nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a boye sannan ya zarota daga jikinsa sabida sam bayaso ta
fahimci Rauninsa, murmushi ƙarfin hali ya saki sannan ya tallafi fuskarta yace "Masha Allah sis
you look so pretty, don Allah karki bari kiyi kuka kodan karki ɓata kwalliyarki, Oya muje nasan
suna nan suna jiranki.
Ya faɗa yana Ruƙo hannunta suka fita waje, a harabar gidan ya samu su Ruman se faman
jiranta suke ya kalli maryam yace " kuyi haƙuri don Allah kinsan ƙanwar tamuce bata girma
kullum abin yara takeyi. Ya faɗa yana lakuce mata hanci
Har bakin motarsu maheer ya kaita yana riƙeda Hannunta sannan ya buɗe mata murfin motar
ta shiga ta Zauna se faman kallonsa takeyi idonta a cike taf da ƙwallar ƙaunarsa da kuma nuna
tausayawarta a gareshi. Da sakin fuska ya miƙawa maheer hannu sukai musabaha juna yana
me ƙara faɗaɗa murmushin dake kwance a kan kyakkyawar fuskarsa yace "kuyi haƙuri fa mun
ɓata muku lokaci.
Murmushi maheer yayi sannan yace "no my In-law karka damu wllh ba komai.
Cikeda tsokana Abdul yace " ai wllh Dr. Karka yarda da zancen ya Maheer kawai faɗa yayi, tun
ɗazufa yake ce mana shi wllh idan ba'a fito masa da matarsa ba ciki ze biyota ya ɗakko abarsa,
amma shine yanzu daya ganka ze wani canza mag......... Duka maheer ya kai masa a bayansa
dole yasa Abdul yayi shiru yana danne dariyarsa.
Murmushi kawai Khabeer yayi sannan ya juya ze bar gurin, da sauri ta kama hannunsa na
dama tareda langaɓar da kanta , wani irin kuka ne ya taso mata amma sedai taƙi ta bawa kanta
damar yin kukan kodan karta ɓata kwalliyarta kamar yanda Ya golden yace da ita tayi kyau
sosai kuma don Allah kartayi kuka.
Dawowa yayi da baya yana sakin mata wani irin ƙayataccen murmushi yace "banace karkiyi
kuka ba?
Nima Dr. Abdullah nake jira da zaran ya iso muma zamuzo gurin. Ya faɗa yana zare hannunsa
daga nata sabida bayaso tana kusanta kanta da gangar jikinsa.
Dariya Abdul yayi sannan ya kalli Khabeer yace " lallai Amaryanmu yar gata ne dama nine ita
wllh, ya maheer ka gani kuma ka koyi yanda ake tattalin ƙanne ba irin yanda kake tafida naka
salonba.
Murmushi kawai Maheer yayi batareda yace dashi ƙala ba, rufe musu murfin motar khabeer
yayi sannan ya juya zuciyarsa a matiƙar raunane.
Cikeda ƙarfin hali yasa hannunsa na dama ya dafe saitin zuciyarsa sabida wani irin zafi da take
masa batareda ya bari kowa ya lura dashi ba, Farouq ya kalla yace "ku tafi tareda Ruman da
Maryam seku ajiyesu sabida be kamata kubar Maryam ta tuƙa mota a daran nan ba.
da mamaki Maryam ta kalleshi sannan tayi dariya tace " lallai Dr. Ka raina ƙwarewa ta, ai wllh
badan karkace na zaƙe dayawa ba to dase nace kokai bazaka nuna min ƙwarewa a gurin iya
tuƙi ba ballan tana waƴan nan. Ta faɗa tana nuna su Farouq
Dariya suka fashe mata dashi gaba ɗayansu sannan suka shiga motar Usman ɗin sukabar
harabar gidan suna masu marawa motar su Maheer baya Suka nufi inda ake gudanar da taron
liyafar.
*A CLASS PARK METAMA ABUJA*
A cikin ɗaya daga cikin manyan tantinan bikin dake gurin na hangi dandazon jama'a da dama a
wannan guri, kowa yana wane wannan Baban Gano ma dana ganta sam ban gane ta ba, sanye
take cikin wani ɗanyen leshi na nunawa sa'a hakama su Ummie da Umma Suma kowa ya
Cakare cikin dakakken leshinsa, can na hango Mamie Zaune bisa ɗaya daga cikin kujerun da
aka jera sabida baƙi ta hakimce a kai sekace ba Uwar Amarya ba, itama irin leshin jikin su
Ummie ne a jikinta sedai banbancin kala kawai, su Ummie da Umma ne kawai suketa faman
hada-hada amma banda Mamie itadai kawai se kallo takebin kowa dashi, gabaɗaya zuciyarya
babu nutsuwa a cikinta tanaga Khabeer wanda ta tabbatar da cewar dauriya kawai yakeyi akan
Rasa Umaisa dayayi, shiyasa gaba ɗaya komai na gurin bayayi mata daɗi.
Can na wallafa ɓangaren dangin ango maheer suma sun ci uban adonsu kamar baza'a mutu
ba, abinku da masu hannu da shuni, se faman hada-hada mutanan yola sukeyi musamman ma
Dadaji da gwaggwannin Maheer ɗin sautin dake tashi a cikin maque ɗin ya canza sabida zuwan
Amarya *_UMAISA MAHMOUD MUHAMMAD DA ANGONTA MAHEER NASEER LAMIƊO_*
Nanfa al'amari ya canza aka fara ruwan kuɗi bana tsiya ba kafin kace me guri ya kacame da
masu liƙa abin arziƙi.
Suma su Ummie da Umma basuyi ƙasa a gwiwa ba suka buɗe bakin jaka hakama su Farouq
da Usman inda kuka san bada guminsu suka nema ba.
Itadai Mamie tunda ta zauna bata tashi ba har Amarya da ango suka isa kan kujerar da aka
tanadar musu wadda ko wace budurwa take hari inda sukeyi mata laƙaɓi da ((Kujerar muna
fama))
Bayan lafawar komai ne aka fara gudanar da shirye-shiryan da aka tanada a gurin, Rumana
aka kira ta fito donta bada tarihin amarya Umaisa. A nitse Ruman ta fara bayaninta cikin
nutsuwa harta gama, tana ɗagowa suka haɗa ido da Abdul kawarda kanta tayi sannan ta nufi
mazauninta ta zauna, bayan ta koma ta zauna ne aka Kira Abdul shima ya fito donya bada
tarihin Rayuwar Yayansa Maheer inda ya fara magana kamar haka
"Assalamu'alaikum warahmatullah, kamar yanda aka buƙaci cewar na fito na bada tarihin waye
yayana Maheer cikin ikon Allah kuwa zan gaya muku wayeshi.
A taƙaice ɗai Maherr Naseer Lamiɗo mutum ne me matiƙar sauƙin kai gamida girmama duk
wanda Allah ya haɗashi zama ɗashi, din hak babu abinda zance a nan illah Amaryar Umaisa
kinyi dace da samun miji na gari.
Mamana kullum tana gayawa Yayana maheer cewar *_KANEMA KA SAMU YAFI KANEMA KA
RASA MAHIMMANCI_*
Wata irin zabura Mamie tayi daga kan kujerar da take zaune zuciyarta na wani irin harbawa
kamar zata fito waje, a matiƙar kiɗime ta miƙe ta isa har gaban Abdul ɗin ta tsaya tana binsa da
kallo bakinta na wani irin karkarwa tace " A...A'iii....na kasan wannan kalaman hikimar??
Da mamaki Abdul yake kallonta sannan yace "a bakin yayana nasansu, kullum seya gayamin
waƴan nan kalaman hikimar tun ina ɗan ƙarami a lokacin dayake Rainona har zuwa yau danake
tsaye a gabanki sabida yanda yake matiƙar son Mahaifiyarmu. Banajin a kwai Ranar da gari ze
waye Yaya maheer bemin zancen Momyn mu b......
Cakumeshi Mamie tayi lokaci guda kuma ta shiga girgizashi da dukkan ƙarfinta tana faɗin "waye
yayan naka tana faɗa tana wani irin kuka kamar zata shiɗe?
Shiru holl ɗin yayi tamkar babu wasu halittu masu Rai a cikinsa, tuni Maheer ya miƙe tsaye
yana binsu da wani irin kallo wanda yafi kamada na zallar kaɗuwa.
Hannu Abdul ya ɗaga ya nuna mata Maheer daga inda yake tsaye, sakin Abdul ɗin Mamie tayi
da sauri ta nufi inda Maheer ke tsaye, direct babbar rigar dake jikinsa ta fuzge da ƙarfin tsiya,
lokaci guda kuma ta yaye rigar dake jikinsa gaba ɗaya farar fatar dake bayansa ta baiyana,
ƙurawa bayan idanu tayi lokaci guda kuma tayi karoda tabon ƙunar dake bayansa ta kwiɓinsa
na dama lokaci guda kuma ta zube a ƙasa kan gwiwoyinta ta fashe da wani irin kuka tana me
riƙe ƙafafun Maheer ɗin.
Cikin mintunan da bazasu gaza 2 ba Numfashinta ya ɗauke ƙaff.
Hakanne yay daidai da shigowar yaya Golden, da wani irin mugun sauri ya nufi inda mamien ta
zube ya fara jijjigata yana kiran sunan ta amma ina babu inda yake motsi a jikinta.
Wani irin kuka Maheer keyi wanda ya jima beyi irinsa ba, daga tabawar da Mamie tayi masa a
wannan lokaci yaji irin abinda ya daɗe beji irin sa ba tun yana yaro ɗan shekara tara a duniya.
Tabbas yanaji a jikinsa cewar a kwai alaƙa me girma a tsakaninsa da wannan baiwar Allah
wadda yake kallo a matsayin Surukarsa.
Bakajin sautin komai sena kukan Umaisa da Maheer , da sauri Umaisa ta dafa kafaɗar Khabeer
tace "pls ya Golden help my mom I don't want lose her don girman Allah yayah!!!!!!
Hawaye ne suka cika idon khaberr sabida tausayin Umaisan, shin ta ina zd fara sanar da ita
cewar Mahaifiyarta ta Rasu?
Dr. Abdullah ne ya ƙaraso gurin sabida yanda yaga yanayin abokin nasa ya fara duba Mamie
wadda ke kwance, jikinsa ne yay masifar sanyi bashida wani zaɓi dole ya ɗago yana kallomsu
yace "there's nothing we can't do Umaisa I'm sorry!!!!!!!
Wata irin ƙara ta saki tana me faɗawa kan Mamie tana kuka.........
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
*_O'o qorafinku akan wannan littafi yasa naji qaimi a cikin jikina, sannan kuma yasa na fahimci
cewar Rubutunka kansa a qaunaceka qauna kuma irinta Fisabilillah❤ Alkhairin Allah har
bayanku mabiya wannan littafi_*
_Page:48_
_____Sandarewa Umaisa tayi lokaci guda kuma ta saki wani irin kuka me ban tausayi Lokaci
guda kuma ta zube a kan gwiwoyinta, Maheer ne yayi ƙarfin halin ɗagota ya Rungumeta yana
rarrashinta, Sabida har zuciyarsa yakejin kukanta gabaɗaya nutsuwarsa tayi ƙaura daga gangar
jikinsa zuwaga Mamie wadda ke kwance babu Numfashi, nan da nan Cikin hanzari Su Ummie
suka ƙaraso gurin suna kiran sunanta lokaci guda kuma idanunsu suka shiga zubar da ƙwallar
tausayin Mamien.
Cikin hanzari Dadaji yayar Mahaifin Maheer ta iso gurin Itama cikeda ƙarfin gwiwa Tana faɗin
"ku matsa mana ta dinga samun iska Karku rufeya in ba haka ba ai se zafi yayi mata yaw.......
Kasa ƙarasa maganar tayi Sabida arba datayi da Fuskar Mamie, da wani irin Karaji tace
*"BADI'ATOU!!!!!!!.*
dirƙusawa tayi bisa Kan gwiwoyinta sannan ta tallafo kan Mamien ta ɗora bisa kan cinyarta
Hawaye nabin Fuskarta.
Duk wannan abinda akeyi Gaba ɗaya Abdul ya kasa motsin kirki illa bin mutanan dake gurin da
kallo Kawai dayakeyi, Tun lokacin da Mamie ta dora hannunta bisa wuyan rigarsa yaji wani
baƙon al'amari yana ratsa duk wata gaba dake jikimsa.
cikeda Ƙarfin hali Khabeer ya Fara giji-gijin ɗaukar Mamien Amma kuma ya kasa yin Hakan
Sabida zazzaɓin dake tareda shi, koda Maheer yaga haka a hanzarce yayi gefe da Umaisa
wdda keta uban kuka Sannan ya naɗe hannayen rigar dake jikinsa ya sunkuya ya ɗauki
Mamien, direct ƙofar fita da Maque ɗin ya nufa Khabeer da Abdullah suna take masa baya, a
motarsa ya sanya ta sannan ya buɗe mazaunin Driver ya shiga ya zauna gaba ɗaya duk yabi
ya Ruɗe Yama rasa meya kamata yayi, a Irin halin dayake ciki bayajin ze iya banbance irin
Ruɗanin da zuciyarsa da tunaninsa suke ciki, wani irin kuka ya saki tareda ɗora kansa bisa
sitiyarin motar cike da rashin sanin makama, Bashida wani zaɓi wanda ya wuce yayi hakan
meyasa ƙaddararsa take zuwa a haka ne?
Dafa kafaɗunsa Khabeer yayi tareda bubbuga bayansa alamar rarrashi Yace "kayi ƙoƙari ka
ƙarfafi zuciyarka akan wannan baƙon al'amarin da ƙaddara tazo maka dashi Maheer, Karka bari
zuciyarka taja akalar rayiwarka a duk lokacin da ruɗani ya Sameka, na tabbata idam kayi hakan
watarana zakaci ribar haƙurin ka Lamiɗo, so pls be patient insha