Showing 9001 words to 12000 words out of 80273 words
gabansa,,,, wani siririn tsaki yaja hakanne yayi daidai da
isowarsu wani babban asibitin kud'i dake cikin Anguwan Rimin, perking yayi sannan suka fito
daga motar, hannunsa Abdul ya Rik'e kamar ze sakin masa kuka yace, "pls ya Maheer dan
Allah kada ka bari sumin Alura wllh bana so, ya fad'a tareda shagwab'e fuska kamar wani
k'aramin yaro. Wani irin murmushi ne yay escaping lips d'insa sannan yace" Abdul wai bakasan
ka girma bane yanzu? nasan da Momy tana nan da tuni kana da k'anwa, ya k'are maganar
idanunsa suna kawo k'walla, Rungumeshi Abdul yayi tareda fashewa da wani irin kuka sabida
tuno masa da Momyn da yayan nasa yayi,
Sosai Maheer d'in ya rikice sabida jin kukan Abdul, d'in sabida a duniya ya tsani abinda ze
sanya k'anin nasa kuka, to amma babu yanda ya iya akan abinda Allah ya k'addarowa
rayuwarsu, cikeda damuwa ya shiga rarrashin sa, harya samu yayi shiru, a haka suka shiga
cikin Asbitin, suna shiga wata farar ma'aikaciyar asibitin ta tarbesu da kulawa, cikin mintuna
kad'an tayi musu iso zuwa office d'in babban likita dake duty ranar, sosai ya shiga duna Abdul
d'in inda ya tabbatarwa da Maheer d'in ulcer ne take damun Abdul d'in, dan haka ya rubuta
masa maganin tareda bashi shawaran ya guji duk wasu abubuwan dazasu sanya ta kuma tashi,
Godiya sukayi masa sannan suka nufi babban phamarcyn dake cikin asibitin suka siya maganin
suka wuce gida, bayan sun dawo Direct side d'in Maheer d'in suka nufa sabida Abdul d'in ya
samu ya huta, suna shiga kwanciya Abdul d'in yayi akan doguwan Royal kujeran dake perlourn,
inda shi kuma Maheer d'in ya nufi bedroom d'insa danyin wanka, yana shiga Abdul ya mik'e
sabida wata irin k'ishirwa data matsa masa, madaidaicib prich d'in dake ajiye a perlourn ya nufa,
batareda tunanin komaiba ya bud'e, wata irin fad'uwar gaba ce ta ziyarci zuciyat Abdul d'in,
lokaci guda kuma idanunsa suka firfito alamar tsoro, sabida wasu manyan kwalaban giya dayay
arba dasu a cikin prich d'in, hakanne yayi daidai da fitowar Maheer daga bedroom d'in, juyowa
Abdul yayi tareda d'akko d'aya daga cikin kwalbar giyar wacce ta d'au sanyi se faman gumi
take,
Wani irin kallo Abdul yake bin Maheer dashi wanda yafi kama dana tuhuma, sannan yace " why
ya Maheer? Har zuwa wani loakaci zaka d'auka a haka? Kai kanka kasan da cewar wannan
d'abi'ar bata dace dakai ba sam, musamman idan mukai duba da illar datakeyiwa garkuwan jikin
d'an adam, shin kanaso kaima na rasaka ne kamar yanda muka rasa Momy? Ya fad'a tareda
sakin wani irin kuka......!
Yaune karo na farko a Rayuwar Maheer dayaji wata irin kunya ta kamashi dayaji irin kalaman
da tilon k'anin nasa ke fad'a , tabbas yasan shangiya ba abubane me kyau, amma to ya zeyi
tunda k'addaransa ne a haka? Da k'yar ya iya tattaro maganar data rage masa, sannan yace
i'm sorry brother, ni kaina bansan ya zanyi ba is just a destiny..... But. Kasa k'arasawa yayi
sabida wani irin kuka dayazo masa. Da wani irin mugun sauri Abdul ya taho ya rungume yayan
nasa cikeda soyayyah gamida tausayinsa.
Washe gari tunda sanyi safiya Hajiya murja taketa faman zuruftu, kallo d'aya zakayi mata ka
fahimci tana cikin farinciki sabida dawowar maigidan nata, sabida ko babu komai yau zata
samu cikar burinta, akan Maheer, wanda take kallo a matsayin matsalarta a rayuwa. Wuraren
k'arfe 2 jirginsu Alhaji Nasir ya sauka, dan haka Maheer da Abdul suka tafi d'akkoshi daga air
pord d'in, tunda hajiya Murja taji dawowar mijin nata dan haka da hanzari ta nufi bakin babbar
k'ofa dake perlourn tareda d'aga d'an k'aramin kafent d'in daka shimfid'a a gurin, wani garin
magani ta zaro daga bakin zaninta sannan ta barbad'a, sannan ta mayar da kafet d'in yanda
yake, wani sahid'anin murmushi ta saki sannan ta koma kan daining nan ma ta gama tsubbace
tsubbacenta,
Su Maheer na zuwa suka samu dady A zaune yana jiransu, da sakin fuska suka nufi mahaifin
nasu suka Rungumeshi, sabida wani irin mugun missing d'insa da sukayi a kwana 2n da baya
nan, Dady ma hugging nasu yayi back cikeda tsantsar k'aunar yaran nasa, kallon fiskar Abdul
dady yayi cikeda kulawa yace " lafiyanka kuwa Abdul naga fuskanka ya fad'a min sosai, shafa
kai Abdul yayi tareda shafa dogon hancinsa yace, "dady ni lafiyana k'alau, dama ya Maheer ne
bashida lfy amma bani ba, ya k'are maganar yana kallon Maheer d'in cikeda tsokana, da gudu
Maheer ya bishi yana son kamashi amma ina tuni Abdul ya bud'e mota ya shige yana dariya,
murmushi kawai dady yayi a ransa yanajin wani irin dad'i sabida ganin hankalin yaran nasa ya
kwanta, a haka suka kama hanyar gida,
Cikin mintunan da bazasu gaza 30mn ba suka isa cikin anguwan Rimi, parking yayi a bakin
makeken get d'in gidansu, horn yayi sannan malam ya wangale musu get tareda d'aga musu
hannu cikeda fara'ah, kunna kan motar Maheer yayi zuwa cikin gidan,
Parking space ya nufa sannan yayi parking, Maheer da kansa ya fito ya bud'ewa dady kofan
motar sannan ya fito, cikeda ladabi ma'aikatan gidan suka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa,
tun daga kan masu bawa flower ruwa har zuwa kan masu share-share,
Murmushi kawai dady keyi tareda amsa musu gaisuwan cikeda fara'a, wannan dalilin ne yasa
ma'aikatan gidan suke jin dad'in zama a gidan, sabida kokad'an dady bashida raina mutane
balle kuma ya keta alfarman su, a haka suka k'arasa babbar k'ofar da zata sadasu da babban
perlourn gidan, a hankali dad ya murd'a handile d'in dake jikin k'ofar, batareda tunanin komai
ba ya d'aga k'afarsa da sallama ya shiga perlourn, yana taka kafent d'in ya tsaya cak....
_Sisters kuyimin haquri da wannan insha Allah zuwa jimawa zanyi qoqarin ganin na qara muku
wani idan lokaci ya bani damar yin hakan._
_Comment_
_Nd_
_Share_
*Zm muhmd*
*(CHuBaD'o)*
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:7_
___________í ½í³– da sauri Maheer ya jawo Abdul dake k'ok'arin bin bayan Dady, tsayawa Abdul
d'in yayi tareda turo baki kamar zeyi kuka yace ""ya Maheer kakusafa kasa na fad'i, ya k'are
maganar a shagwab'e kamar zeyi kuka, wani miskilin murmushi Maheer ya saki wanda ke
k'arawa fuskarsa kyau, sannan yace " wai yaushe zaka dena wannan shagwab'an ne? bakasan
ka girma bane? Yanzufa kana 23yrs nefa, " uhm ya Maheer niban girma ba har yanzu yaro ne
ni a gurin yayana,
Jan hancin Abdul d'in Maheer yayi, hakanne yasa Abdul ya saki k'ara, tareda saurin d'ora
hannunsa akan hancin, dariya sukayi gaba d'aya tareda kama hannun juna cikeda so gamida
k'auna,
a haka suka marayawa Dady baya zuwa cikin hamshak'in katafaren perlourn nasu,
A tsaye suka samu Dadyn tareda hajiya Murja wadda keta zuba masa kirsa da kisisina.
cikeda barikanci ta kama hanun Dady ta nufi daining aria dashi, duk yanda Dady yaso yace
mata zeje yayi sallah sam kasawa yayi, sabida wani bala'in shakkanta daya samu kansa da ita,
shidai Maheer kallonta kawai yakeyi a ransa yana mamakin sauyin mahaifin nasu, musamman
idan yayi duba da irin rawarkan da Dadyn yakeyi A kanta seyaji zuciyarsa nayi masa wani irin
zafi, shiko Abdul sunkuyar da kansa kawai yayi yana aikin zancen zuci, lokaci guda kuma wani
b'angaren na zuciyarsa na bugawa,
Wani had'add'en Flet tajawo zuwa gabanta, tareda bude babban food flacks d'in dake gabanta,
nan da nan k' ayataccen k'amshin abincin ya karad'e perlourn, wani irin lumshe idanu Dady
yayi lokaci guda kuma ya saki murmushi tareda yabawa matar tasa,
tana gama zuba masa kayan alatun data shirya masa a flet d'in ta mik'a masa, da kulawa Dady
ya karb'a seda ya gama kod'ata, sannan ya d'ebi abincin ya kai bakinsa batareda yin bisimillah
ba, tunda ya fara kai abincin bakinsa tunaninsa ya fara sauyawa, lokaci guda yaji a duniya babu
wanda yake so kuma yake k'auna fiyeda kowa Face Hajiya Murja, haka kuma babu wanda yake
k'aunar yaga farin cikinta kamar ita, a yanda yakeji a gameda ita ze iya rabuwa da kowa a
kanta, dan haka ya tsaya cak dacin abincin, tareda zuba mata manyan idanunsa,
Hakanne yasa ta saki wani d'an iskan murmushi tareda gyara zamanta ya koma irin na
hamshak'an matannan, wani far tayi da ido hakanne ya k'ara k'ular da Maheer, hakanne yasa
yaji ya k'ara tsanarta fiyeda ko yaushe a rayuwarsa, wani siririn tsaki yaja, hakanne ya mayar
da hankalinta gareshi, wata uwar harara ta watsa masa tareda d'aure fiskarta tama'au ta kalli
Dady tace " gaskiya Alhaji lamari yaron nan ya fara isata a gidannan, inda mutunci aini kamar
uwa nake a gurinsa, tunda ina Auren ka, amma ko kad'an yaron nan baya raga min balle ya
darajani, tamkar wata sa'ar sa haka yake kallona ta fad'a tareda fashewa da wani irin kuka
wanda yafi kama da na munafurci,,,,,!
Kallonsa Dady ya mayar ga Maheer wanda ya gama k'ulewa da kalamanta,
Cikeda wani irin zafin Rai wanda shi kansa besan yanada shi ba Dady ya kalli Maheer yace "
kai yaushe ka zama d'an iska ban sani ba? matar tawa zaka Raina min dan gidanku? Shin
bakasan Albarkacinta kukeci a gidannan ba? Mudin kuna son zama dani a gidannan wllh sekun
yi mata biyayya, fiyeda yanda ma kukeyi min, dan haka ka bata hak'uri yanzun nan batareda
b'ata lokaci ba""""".....! Ya fad'a cikin d'aga murya.
Cikeda kad'uwa Abdul yake kallon Dady!!! Shikuwa Maheer daskarewa yayi sabida mamakin
canzawar Mahaifin nasu a lokaci guda, sabida a iya Rayuwarsa dashi betab'a d'aga masa
murya irin na yauba, kuma dukda hakan ma a kan wannan shaid'aniyar matar?.
Wani irin zafi zuciyarsa ta shiga yi masa, dan haka ya k'udurtawa kansa cewar baze tab'a bata
hak'uri ba koda duniyar zata tashi gaba d'aya...
Cikeda tsoro Abdul yake kallon yayan nasa, sabida ganin sauyawar da yanayinsa yayi, tabbas
yasan ya Maheer bashida hankali idan ransa ya b'aci dan haka yayi hanzarin dafa kafad'arsa
yana yi masa nuni daya bawa hajiya Murjan hak'uri amma fir Maheer yak'i yin hakan,
Cikeda munafirci hajiya Murja ta dafa kafad'ar Dady tana kuka tace " dama na fad'a maka wllh
baze bani hak'uri ba, kana kallon yanda yake kallona kamkar ze dake ni...!
Cikeda k'unar Rai Dady yace "" wllh ko zaka mutu yau Maheer seka bawa Murja hak'uri, idan
kuwa ba hakaba wllh sedai kabar min gidana kaji na gaya maka..!
Cikeda tashi hankali suke kallon mahaifin nasu sabida basu tab'a zaton wannan maganar daga
bakin Dady ba,
Kuka Abdul ya saki sannan yace"" Dady mune fa yaranka Abdul da Maheer, shin ka manta
maganar da kake gaya mana kullum cewar mu kaida'aine mahad'in rayuwarka Dady? Amma
yau kaine da kanka kake cewa yaya Maheer d'in dakafi so yabar maka gidanka akan wannan
matar Dady?
Wata uwar harara Dady ya jefi Abdul da ita, sannan yace """ wllh bazan janye k'udirina ba, koya
bata hak'uri, kokuma yabar min gidana,,,
Da sauri Maheer ya kalli Dady yace" Dady zan bata hak'urin kamar yanda ka nema, cikin wata
irin murya ya Kalleta kamar wani d'an daba yace " kiyi hak'uri!
Yanda yayi maganar kawai ya isa ka fahimci daurewa kawai yakeyi,
Murmushin mugunta Hajiya Murja ta saki sannan sannan ta kalli Dady ta k'ara fashewa da wani
sabon kukan tace""" Alhaji kana ganin a yanda yake bani hak'urin kamkar wata sa'arsa....
Wani irin murmushi Maheer yayi tareda k'udirawa zuciyarsa cewar wllh baze sake bawa
wannan shaid'aniyar matar hak'uri kuma ba sedai duk wacce za'ayi ayi,
Hakanne yayi daidai da fitowar Binta 'yar kwabo daga d'aki, cikeda munafurci ta k'araso
perlourn tareda matswa kusada hajiya Murja dake kukan munafirci tace " haba kekuwa Murja
dan Allah kiyi hak'uri ki manta da komai, na tabbata da Maheer yasan koke wacece da bazeyi
miki haka ba,
Wani irin haushi ne ya ida cika zuciyar Maheer sabida jin abida Bintan tace, wani irin ja
idanunsa suka k'arayi sabida b'acin Rai, a fisace ya fara tafiya cikin takunsa me cikeda izza
taamar wani zaki ya tsaya a gaban Binta 'yar kwabon dake tsaye a kusada Hajiya Murja, cikin
wata irin murya mai kama data 'yan daba yace """ wace ita kuwa? Ba haihuwarta akayi kamar
kowa ba, aiba daga sama ta fad'o ba balle kice daban take da kowa, ya k'are maganar yana
Binta da wani d'an iskan kallo, wanda yafi kamada saura k'iris na mareki,
Sosai Binta ta tsorata da yanayinsa Maheer, musamman yanda jikinsa yake tsima kamar wanda
ake kad'awa gangi,
Koda wasa bata tab'a zaton tantirancinsa yakai haka ba,
Saukar Mari Maheer yaji akan fiskarsa, Dady ne ya d'aukeshi da wani lafiyayyen mari wanda
yasa fiskarsa ta d'aure sabida Azaba, tun kafin ya dawo daidai ya sake k'ara masa wani marin
wanda yafi na farko shiga, sannan ya nunashi da yatsa cikeda b'acin Rai yace ""Maheer Ashe
Rashin tarbiyarka yakai haka dazaka dinga cin mutuncin matata a gaban idanu na? Wllh
Maheer ka gama fice min a rai, tayanda naji cewar na tsaneka, haka kuma nayi nadamar
haihuwarka a Rayuwata, wllh dana san haka zaka zamemin da tin kafin kazo duniya nayi
addu'ar Allah yasa ayi B'arinka!, Dan haka ka tattara yinaka yinaka ka barmin gidana wllh daga
yau na sallamawa duniya kai..!!!!
Wani irin bugawa k'irjin su yayi lokaci guda musamman ma Maheer wanda jinsa da kuma
ganinsa suka fara barazanar d'aukewa!
zubewa kawai yayi a k'asan tiles d'in dake perlourn cikeda tsantsar tashin hankali, lokaci guda
kuma ya saki wani irin kuka kamar ransa ze fita,
Da gudu Abdul ya k'asa kuda Dady lokaci guda kuma ya zube a gaban k'afafunsa ya rik'e
sannan ya fara magana cikin kuka yace, " dan girman Allah Dady kada kayi haka, wllh ya
Maheer baya cikin hankalinsa shiyasa yayi abinda ya aikata, wllh Dady nayi maka alk'awarin ni
zan sanyashi ya durk'usa a kan gwiwowinsa ya bata hak'uri, indai har zaka janye kalamanka a
kansa pls Dady ya fad'a yana k'ara k'ara damk'e k'afar Dady n,
Fisge k'afarsa Dady yayi daga ruk'on da Abdul d'in yayi masa, sannan yace " na rantse da Allah
mai girma bazan janye ba, kuma muddin ka k'ara Rok'ona akan wannan maganar senayi maka
baki kaima Abdussalama" ya fad'a a zafafe!
Maheer dake zaune bisa tiles mik'ewa yayi idanunsa suna zubar da hawaye, wanda suka
k'arawa idanunsa ja sabida tashin hankali yace " Abdul karkace komai kamar yanda Dady yace,
dan haka zan tafi kamar yanda ya buk'ata, sedai ina neman Alfarma a gareka k'anina, dan Allah
ko nan gaba kada ka aikata abinda Dady zeyi fishi dakai kamar yanda yayi dani a yanzu, inaso
kayi min alk'awarin cewar ko babu Maheer a rayuwarka zakayi Rayuwa me Aminci fiyeda wacce
mukayi tareda kai a baya k'anina, abu na biyu kuma shine don Allah Abdul ka kulada Dady
sosai, sannan karka bari tafiyata ta zama silar sauyawar Rayuwarka daga farin ciki zuwa k'unci,
yana kaiwa nan ya mik'e tareda sakin wani irin murmushi wanda yafi kamada na takaici ya nufi
k'ofar fita daga perlourn,
Da wani irin mugun gudu Abdul yaje yafad'a jikin Maheer sannan ya rungumeshi ta baya, tareda
fashewa da wani irin kuka yace " pls ya Maheer dan girman Allah karka tafi, i cn live without you
ya Maheer plsssss, ya wani ja pls d'in tamkar ze shid'e,
Juyowa Maheer yayi ya tareda rungume k'anin nasa sabida jin yanda yake kuka kamar ze
mutu,!!
bayansa ya dinga bibbigawa, lokaci guda kuma ya zare jikinsa daga na Abdul d'in ya fice daga
perlourn.
Zubewa Abdul yayi a k'asa tareda sakin wani irin kuka me ban tausayi, lokaci guda kuma ya
maida kallonsa ga hajiya Murja, idanunsa a cike tab da k'wallah, daga irin kallon da Abdul d'in
keyi mata zaka fahimci na tsantsar tsana ne,
mik'ewa yayi da da sauri zebi bayan Maheer d'in, sabida bayajin ze iya barin yayan nasa ya tafi,
dole ne ya tsayar dashi.
cikin d'aga murya Dady yace "wllh Abdul idan ka fita daga perlourn nan kabi bayan Maheer
sena tsine maka....!
Wani irin kuka Abdul ya saki, cikeda tausayin rayuwar da yayan nasa, tabbas yasan halin
Maheer yanada wata irin zuciya me wahalar tank'waruwa, babbar damuwar sa yanzu itace,
yasan ya Maheer ze sake dawo da d'abi'ar daya bari a kwanakin baya ta shan Giya.
Sabida yayi imani da Allah kan cewar yanzu itace zata zame masa abokiyar rayuwa a inda
zashi, dama ya lafiyar kura balle tayi zawo?
Sautin kukansa ya sake k'arawa cikeda tausawa kansa ta yanda ze rayu batareda ya Maheer
d'insa ba,
hannunsa ya d'aga yana kallon sama cikeda k'ask'antar dakai yace _""" ya Rabbi ka tsaremin
yayana daga dukkan sharrin mutanan dake cikin wannan duniyar, sannan ka cika rayuwarsa da
dukkan farin ciki na har abada, ya Allah ka shiga lamarin mahaifin mu, kasa kuma ya fahimci
illar abinda ya aikata a nan kusa ya Rabbí ¾í´².._, ya k'are addu'ar yanabin Hajiya murja da wani
irin kallo wanda yake nuna tsantsar tsanar dayake mata a fili, a fisace Dady yabar perlourn
yana huci tamkar wani bak'in kumurcin maciji.
B'angaren Maheer kuwa wata black d'in trolly ya