Showing 33001 words to 36000 words out of 80273 words

Chapter 12 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

12 Jul 2025

2724

d'akin,
ledar Fresh Milk d'in data ajiye a gefan gadon ta d'akko sannan ta koma kan wata lallausar
kujerar dake d'akin ta zauna, a hankali ta fara sha tana wani lumshe ido sabida yanda Fresh
Milk d'in yake mata dad'i.
A hankali ya fara bud'e idanunsa harya gama bud'e su Ras akan silin d'in d'akin, a nitse ya fara
bin d'akin da kallo tamkar wanda yake neman wani abun harya maida kallonsa kan kujerar
datake zaune a kai, tundaga kan cute zarazaran neils d'inta na k'arfa ya fara kallonta har zuwa
kan fuskarta wadda kofin hannunta ya hanashi ganin fuskarta, sedata shanye tass sannan ta
sauke cup d'in tana lasar baki, karaf idanunsa suka sark'e cikin na juna, nanda nan k'irjin
Maheer ya buga da k'arfi sabida tsabar kad'uwar dayayi, da k'yar ya iya tattaro kalaman bakinsa
yace " Qu..ee..n of tears??!!! wani irin kallo yake jifanta dashi wanda har seda taji k'irjinta ya
amsa itama...! Sabida irin kallon da yake binta dashi yana d'aukene da wasu manyan sirrika
masu wuyar fassarawa ga zuciyar data kasance bak'uwa a cikin al'amari na shak'uwa da kuma
mayen soyayya me matik'ar zafi da tasiri.....
_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


*_BANYI EDITING BA‍♀️_*

_Page:23_

___________ sosai k'irjinsa yake bugawa haka itama a b'angaren ta, a hankali ta mik'e
cikeda k'arfin gwiwa gamida farin cikin bud'ewar idanun nasa duk a lokaci guda, sedai yanayin
irin kallon dayake binta dashi ne yasa duk taji babu dad'i amma kuma seta dake harta samu
nasarar k'arasawa jikin gadon, murmushinta me kyau ta sakar masa, don haka ya kauda kansa
da sauri zuwa wani gefen daban, dafari ya zata gizo take masa kamar yanda ta saba tun daga
ranar daya fara d'ora idanunsa a kanta, dan haka zuciyarsa ta cika da Rud'ani me girman
gaske, wanda ya kasa warwarewa kansa balle ya fahimci tayanda ze siffanta shi, addu'a kawai
yakeyi Allah yasa ba wannan yarinyar bace yarinyar danake bege da marmarin kasancewa a
tareda ita ba!! Nanda nan wani b'angare na zuciyarsa yace dashi "to idan itace yarinyar da
zuciyarka da kunnuwanka sukai sabo da ita shin dawani idanun zaka kalleta Maheer? Duba da
irin hallaccin da tayi maka a Rayuwarka?

Dafe kansa yayi da sauri sabida wani irin sara masa da yayi, da sauri ta dafa kafad'arsa tace "
Eyyah sorry kabi a hankali kada ka fama ciwon dake jikinka dik da cewar saura kad'an ma a
sallameka zuwa gida.

D'aure fiska yayi tamau tareda bin hannunta wanda ta d'ora bisa kafad'unsa, da sauri ta janye
hannunta daga jikinsa, sabida mugun kallon dayake binta dashi, matsawa tayi daga jikin gadon
jikin ta a matik'ar sanyaye, a hankali ta koma kan kujerar data tashi ta zauna, juyarda kansa
yayi gefe guda ba tareda ya sake kallon inda take ba, itama bata kaleshi ba illa kawai abinda
take sak'awa a ranta gameda halaiyar sa, gaba d'ayansa idan yayi wani abin sekace me Aljanu,
muryarsa ta tsinkaya cikin Husky voice d'insa yace "keeee wai meyasa kiketa bibiyar Rayuwata
ne haka? Tunda na had'u dake kijeta kawo min tsoko a cikin Rayuwata, ko ina naje sekin bini
sekace wata aljanah, ok koda yake be kamata nayi mamaki ba sabida dama ku mata haka
kuke, gabad'ayanku 'yanbin zak'i ne, haka kuma muddin kuka k'yalla idon ku akan mutum to
kun dinga bibiyarsa kenan harse kunga bayansa sannan zaku barshi, har sonawa kike so na
fad'a miki cewar kifita a Rayuwata ne iyeee?

Tunda ya fara magana take kallonsa tamkar wadda aka dasa sabida mamakin irin
maganganun da suke fitowa daga bakinsa, banda hawaye babu abinda ke zuba daga fararan
idanunta, babu abunda takeji a zuciyarta face wani irin tuk'uk'in bak'in ciki akan kalaman sa, da
k'yar ta iya bud'e bakinta wanda yayi mata nauyi sannan ta tace" hak'ik'a duniya a cike take da
mutane kala-kala, haka kuma komai na duniya yanada sakamakonsa, bazanyi mamaki ba
danka jefeni da kalaman da duk suka fito daga bakin ka ba, sabida kai d'in namiji ne, dama ba
duk maza bane suka san alkhairi ballentana harsu mayarda martaninsa, nagode da
sakamakon dana samu daga gareka, sedai inaso ka sani ko wacce mace tanada halaiyarta
hakama d'abi'unta. Tana kaiwa nan ta juya da gudu tabar d'akin tana wani irin kuka me cin Rai,

Tunda take a Rayuwata bata tab'a jin bakin ciki irin na yau ba don haka ta koma masallaci ta
had'a kai da gwiwa ta dinga rusar kuka kamar wadda aka aiko mata da mutuwar wani nata.

Tunda ta fita daga d'akin ya kasa d'auke idanunsa daga kan k'ofar, lokaci guda yaji wata irin
Nadama gamida haushin kansa sunyi masa dirar mikiya a zuciyarsa, shin meyasa ya fad'a mata

maganar datayi sanadiyar zubar hawayen ta? Kansa ya dafe sabida yanda k'irjinsa yayi masa
nauyi, idanunsa ya mayar ya lumshe yana me dana sanin abinda yayi mata,

Seda tayi kuka me isarta sannan ta nufi office din ya Khabeer, a hankali ta k'ofar tareda yin
sallama, kallo d'aya yayi mata ya fahimci tayi kuka, sabida yanda idanunta suka kumbura
fuskarta kuma tayi ja, abinka da farar mace, mik'ewa yayi da sauyi lokaci guda kuma ya rikice
yana tambayarta abinda ya sameta!
Wani sabon kukan ta sake fashemai dashi, tareda k'ok'arin fad'a masa a jiki, dakatar da ita yayi
ta hanyar zaunar da ita akan d'aya daga cikin kujerun dake perlourn, seda yayi mata da gaske
sannan ta nutsu ta dena kukan datakeyi, sannan ya fara tambayarta dalilin kukan, bata da wani
zab'i don haka ta shirga masa k'aryar cikinta ne yake mata ciwo, kallonta kawai yakeyi sannan
yace" tashi muje kisha magani sena maidake gida, ba musu ta mik'e kamar jira take ya ambata
mata kalmar tafiya gidan,

Da ido kawai ya bita a ransa yana mamakin hali irin na k'anwar tasa, sam bata raina abin kuka
sekace wta k'aramar yarinya, seda ya biya ta pharmacy din cikin asbitin ya siya mata magani
sannan suka nufi hanyar gida, har suka k'arasa gida fuskarta bata koma normal ba, a hankali
ta bud'e murfin motar ta fita, a babban perlourn gidn ta samu Baba tana kallon wani indian film
na fad'a, ita kad'ai se faman magana take ita kad'ai tana fadin "bazaka rama ba kana kallosa ze
kasheka?

Rumana dage tsaye a k'ofar khitchine ta rik'e k'ugu tana kallon Baba banda dariya babu abinda
takeyi, a haka umaisa ta wuceta ko sannu batace mata ba, tab'e baki Baba tayi sannan tace "
shegiya me kamada Bararo�

Ita dai Ruman batace komaiba ta koma khitchine taci gaba da taya mamie had'a abinci.

Ahka Khabeer ya shigo perlourn da sallamah, kallon tsaf Baba tayi masa sannan ta kyauda kai,
da sakin fuska ya nufi kusada ita ya zauna a k'asan kafent din dake shimfed'e a perlourn,
hanunta ya kamo yace " ohhh my sweetheart yaushe kika zo ne babu ko labari? Aida na sani
wllh dana kawo muki cefane na musamman, ya K'are maganar yana fad'ad'a murmushinsa,
bige masa hannu tayi tareda fadin dalla sakarmin hannu, aini wllh babu abinda zakuce min
kaida Faruku, in banda bakuda mutunci ace harna kwan uku a garinan bakuzo kun gaidani ba
sabida baku d'aukeni a bakin komai ba, to wllh bari Mamudan ya dawo senaji idan shiyace
karku dinga mutunta ni.

Tab'e baki yayi yana kallonta, seda yaga tana shirin jik'a masa aiki sannan ya fara lallab'ata
yana bata baki, seda yaga ta ware sannan ya haura zuwa d'akin Ummie, nan ma kaca-kaca
Ummie tayi masa sannan ta k'yaleshi, har d'aki yaje ya gaida Mamah sannan ya kicin ya gaida
mamie itama, sannan ya samu zarafin tafiya side d'insa danya watsa ruwa ka kwanta kuma ya
huta.

B'angaren Umaisa kuwa wani sabon kukan ta sake fashewa dashi a saman madaidaicin
gadonta, nan zuciyarta ta fara aiyana mata maganganun Maheer, shin metayiwa bawan Allahn
nan ne a Rayuwarta haka dayasa ya tsaneta? Shin meye laifinta donta temakeshi a Rayuwa?
Dama wannan shine sakamakon alkhairin daya kamata ya saka mata dashi kenan?
Wani sabon kukan ta cigaba dayi har wani nannauyan bacci ya samu nasarar daukar ta.

*KADUNA, UNGUWAR BADIKKO.*
Binta 'yar kwabo ce zaune bisa wani k'ayataccen perlour wanda ya kasance mallakin Hajiya
sa'a, kallon Hajiya sa'ar tayi sannan tace "hmmm ni wllh yanzuma kin fara bani haushi, in banda
jaraba irin taki meyasa bazaki iya hak'ura da Abdul ba, wllh ni'a ganina indai ba aiki akai miki
akan yaronnan ba wllh ko kallon arzik'i baki isa yayi miki ba, idan ma tak'amarki kud'in da kike
dashine kema kinsan ubansa ba k'aramin mutum bane, dan haka kwai ki fito da kud'i malama
ayi miki aiki akansa seyanda kikaga dama zakiyi dashi a tafin hannunki,

Murmushin jin dad'i Hajiya sa'a ta saki, sannan tace " wllh Binta indai shawarar mugunta ake
nema to da anzo gurinki an gama, tafawa sukayi tareda shek'ewa da dariya irin ta cikakkun 'yan
bariki, har yamma suna yare suna hirar ta yanda zasu b'illowa lamarin Abdul d'in, daga k'arshe
suka mik'e Rungume da juna sukai nufi Bedroom d'in Hajiya sa'ar. Niko ina ganin sun shige
d'akin zan bisu, da sauri Momyn Fadyl ta dank'o bayan rigata, tareda fisge biron daga hannuna


B'angaren Dadyn su Abdul kuwa, sosai yke rashin lafya a tsatsaye, wasu lokutan ma idan abin
yayi tsanani har fad'uwa yakeyi sedai a d'agashi, wasu lokutan ma seyafi sati besan inda kansa
yake ba, wannan al'amarin shine babban tashin hankalin Abdul a yanzu, dan haka ya fara
fafutukar fitar da mahaifin nasa zuwa k'asar Cairo, don haka da sassafe Abdul ya shirya tafiya
zuwa Yola batareda sani kowa ba, sabida ya k'udurtawa zuciyarsa cewar seyayi duk me
yuwuwa ya daidai ta tsakanin mahaifinsa da kuma 'yan uwansa, wannan shine abinda yake so
ya cimmawa a halin yanzu, car keys dinsa ya dauka da kuma wayoyinsa, system dinsa ya
bude tareda shiga Email dinsa ya fara k'ok'arin turawa Maheer saqo akan Rashin lafiyar
Mahaifin nasu, yana gama rubutawa ya tura masa, sannan ya rufe system din ya fice tareda
kulle k'ofar part din gaba d'aya,

Motar ya shiga tareda duba agogon Rolex din dake daure a tsintsiyar hannunsa, zaro manyan
idanunsa yayi tareda kunna motar da sauri sabida ganin time din tashin lokacin jirgin nasu ya
kusayi, kafin ya fita seda ya tsaya yayi magana da Baba mai gadi, sannan ya kira sulaiman
wnda yake kulada harkokin shige da fice na gidan gaba d'aya, kashedi sosai yayi masa kan
cewar karyabar kowa ya shiga b'angaren Dady koda kuwa Hajiya Murja ce dakanta, sabida a
halin yanzu sam beyarda da ita ba,

Keys din b'angaren Dadyn ya bashi sannan yace masa shima baze dad'e ba ze dawo yau insha
Allah, Addu'ar alkhairi suka dinga yi masa tareda fatan samun Abinda akaje nema. Godiya yayi
musu sannan ya gigi motar zuwa Air port, yana zuwa ko minti biyar beyi ba jirginsu ya d'aga

zuwa Birnin na yolah, se'ince Malam Abdul Allah ya bada nasara akan abinda akaje nema.

*ABUJA*
tun daga Ranar Umaisa bata sake zuwa Hospital d'in ba, sabida ta k'udurtawa kanta cewar
bazata sake shiga sabgar Maheer ba koda wasa sabida hankaka ne shi besan na gida ba, dan
haka ko ya khabeer yaje d'aukarta a schl sedai ta gudu idan aka gajida neman ta ba'a ganta ba
sedai ya tafi abinsa, wannan dalilin ne yasa gaba d'aya khabeer din shima be sake bita kanta
ba,

B'angaren Maheer kuwa tuni zuciyarsa ta dinga addabarsa ta hanashi sak'at, sabida yanda take
a cike taf da kewar yarinyar daya kasa tantance matsayinta a zuciyarsa, sosai yakejin haushin
kansa sabida koma meye ya faru dashi shine silar jefa kansa a cikin halin da yake ciki a yanzu,

Bayan sati d'aya aka sallami Maheer sabida yanda yaji sauk'i sosai ya koma normal yanda
yake, khabeer ne da kansa ya d'aukeshi ya kaishi har gidan Maheer din dake Unguwar Garki,
sosai Maheer din yaji dadin abinda khabeer din yayi masa, harta lawan mai gadi seda ya nuna
farin cikin dawowar shugaban nasa, dukda cewar yayi zaton Maheer din gida yaje shiyasa
tsawon lokaci be dawo ba se yau din, Khabeer be wani dade ba ya mik'e yayiwa Maheer
sallama, har bakin motarsa ya Rakoshi, a nan ne khabeer yake shaida masa batun motarsa,
murmushi Maheer yayi sannan yace "ba damuwa ze kira Asp din da kansa, wayoyinsa khabeer
ya bashi sannan yayi masa sallama ya tafi. Tunda Maheer ya dawo gida ya d'aura da tunanin
Queen of tears d'in sa, sosai zuciyarsa keyi masa zafi idan ya tuna sanda take kuka sabida
maganar daya fad'a mata, wasu lokutan har tambayar kansa yake shin meyasa ma ya fad'a
mata abinda ya zama silar zubar hawayenta?

Tsaki ya sauke tareda jawo wayarsa ya jona ta a chaji, sabida tun fitowarsa daga Hospital be
kunna ta ba, system dinsa ya jawo ya ya kunna, haka kawai yaji yana so ya duba Email d'insa,
kodan ya turawa Abdul dinsa sak'o.

Yana bud'ewa yayta cin karo da sak'annin mutane kala-kala, ciki kuwa harda na Mujaheed da
kuma na Abdul, na Mujaheed ya fara bud'ewa ya fara dubawa kamar haka: _" hyyyy Dude,
wai meye matsalarka ne inata faman kiran wayarka Amma kullum a kashe, hope kana lfy._

Murmushinsa me kyau yayi sannan ya bashi amsar yana nan lfy, kan sak'on Abdul ya koma
tareda bud'ewa ya fara karantawa kamar haka; *_Assalm my one and only ya Maheer, a duk
ida ka kasance k'aninka Yanayi maka fatan Alkhairi tareda farin ciki me dorewa na har abada,
sedai ina me bakin cikin sanar dakai cewar Dadyn mu yana fama da jarrabawa ta rashin lfy,
wanda a halin yanzu bema san wanda yake kansa, insha Allah nan da kwan Uku zamu fita
dashi zuwa Egypt!!!!_*

Wani irin bugawa k'irjin Maheer yayi da k'arfin gaske, mik'ewa yayi da sauri tareda nufar drower
dinsa, wani mukullin mota ya d'auko ya fito da sauri, parking space ya nufa inda na hangi wata
zabgegiyar Reng Roba baka wuluk, se faman d'aukar idanu takeyi, a hanzarce ya shiga ciki ya

zauna tareda d'aura sit belt a jikinsa, yana kunna motar maganar Dady ta fara yi masa yawo a
cikin kwanyar kansa, musamman ma sanda yake gaya masa cewar "ka fice ka barmin gidana
Maheer, wllh na sallamawa duniya kai, haka kuma muddin ka sake waiwayar inda nake wllh
senayi maka baki Rayuwarka tafi hka lalacewa!!!!!
Wasu siraran hawaye ne masu zafi suka dinga bin kyakkyawar fuskarsa, a hankali ya shiga firta
" innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un, wannan wace irin Rayuwace haka?

_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:24_

___________ jikinsa ne yay masifar sanyi daya tuna da kalaman mahaifin nasa akansa,
wasu zafafan hawayene suka shiga zubo masa, cikeda sarewa ya mik'a hannunsa ya zare
mukullin motar tareda kasheta, sit belt din ya cire daga jikinsa tareda bude murfin motar ya fice
gaba d'aya zuwa cikin gida, direct Re-fregerator din dake perlourn ya nufa, tareda b'alle
murfinsa da k'arfin tsiya, lokaci guda ya janyo kwalbar Brandyn dake ciki, murfin ya b'alle
tareda k'ok'arin kafawa a bakinsa, tsayawa yayi cak, lokacin daya tuna da maganar da
masoyinsa Abdul yake gaya masa a lokacin dayakeyi masa tuni akan haramcin shan giya, nan
da nan wani b'an gare na zuciyarsa ya fara aiyana masa cewar, "a'a maheer kada ka sake
aikata wani babban kuskuren a Rayuwarka, sabida babu wata mafita dazaka samu a tareda
abinda Allah yayi haramci akansa, a yanzu babu abinda kake buk'ata face ka gyara alak'arka da
ubangijin ka, sabida babu wani mutum wanda ze d'auki sab'on Allah ya zama abin aikatawarsa
kuma ya zauna lfy! Dole ne Rayuwa ta juya masa baya,

Shin baka zaton cewar dalilin shan giyar da kakeyi ne Allah yake jarrabaka ta wannan
b'angaren? A halin yanzu babu abinda kake buk'ata kamar yafiyar ubangi Maheer, tabbas idan
ka lazimci istig fari Allah ze duba dukkan lamarinku daga kai har mahaifin naku, dan gwarar da
kwalbar yayi, still idanunsa suna zubar da hawaye, mik'ewa yayi da sauri ya koma khitchine ya
d'akko wani madaidaicin kwando ya fara zuba kwalaban giyar a ciki, seda ya kwashesu tass
sannan ya fita ta k'ofar baya ya watsasu a kwandon shara, tundaga wannan Ranar Maheer ya
lazimci istig fari don ya gyara alak'arsa da Ubangijin sa tareda addu'ar yiwa Mahaifin sa addu'ar

samun lfy, sosai Maheer ya fita daga haiyacinsa sabida yawan tunanin da yake matsawa kansa
dashi gefe da'aya ga damuwar ciwon Dadyn sa, inda d'aya b'angaren kuma tunanin Umaisa ya
hanashi sakat, wasu lokutan har har unguwarsu yake zuwa amma baya samun ganinta,
yauma kamar kullum sanye yake cikin k'ananan kaya wanda sukai matik'ar karb'ar jikinsa, daga
d'an nesa da gidansu ya parker motar, jifa-jifa yake ganin masu irin Uniform d'in daya tab'a
ganinta dashi suna nufar wani babban masallacin dake unguwar, hakanne ya bashi tabbacin
cewar a cikin masallacin islamiyar take, a hankali ya koma cikin motar tareda k'udurtawa kansa
cewar yau baze tab'a barin unguwar ba har seya sanyata a idanunsa,

Daga nesa kad'an da masallacin ya tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login