Showing 75001 words to 78000 words out of 80273 words
Chapter 26 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf
Allah komai zeyi daidai sakko
na tuƙa motar, ba musu Maheer ya fito daga motar ya koma baya tareda ɗora kan Mamie bisa
cinyarsa, a hankali yakejin matar tana ƙara samun kusanci da zuciyarsa se'a yanzu da ya ƙare
mata kallo sosai ya tabbatarwa da Kansa cewar Tabbas yanada wata alaƙa da ita.
A shekarun daya shafe ba tareda Mahaifiya ba abu ne mawuyaci Manta tsatson mahaifiyarsa
Kokuma kamanninta tun da yana da ƙaranci shekarun da ƙwaƙwalwarsa bazata iya riƙe hakan
ba.
Buɗe gaban motar Dr. Abdullah yayi ya shiga Cikin hanzari sannan Khaber ya figi motar suka
nufi Asbitinsu da ita. Cikin mintunan da bazasu gaza 10 ba suka iso Cikin Asbitin abinka da
masu abu da abunsu tuni nurses suka fito da gado suka ɗauketa zuwa ciki babu alamar Nfashi
a tareda ita.
A wannan lokacin baiyana irin tashin Hankalin da Maheer yake ciki abu ne mawuyaci a gareni
amma daga yanayinsa zaka fahimci baya cikin kwanciyar Hankali.
Zubewa yayi dirshan a ƙasan tiles ɗin dake Reception na Asbitin tareda dafe kansa da dukkan
hannayensa biyu, babu abinda yake firtawa se "Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!!!! Duk addu'ar
datazo bakinsa yinta kawai.yakeyi batareda ɗorata a muhalinta ba
*******
*_ƁANGAREN ƳAN BIKI_* kuwa tuni aka watse kowa yayi ta kansa Masu tsegumi nayi masu
kuka nayi ahaka duk aka watse ya zamana babu kowa se Makusantan Ango da kuma na
Amarya ne kawai suka Rage a gurin, kowa yayi jigum cikeda Rashin sanin madafa, Dadaji ce
ta kalli su abdul tareda sauran jama'ar dake gurin tace " ya kamata mubi bayansu dan musan
Halinda Badi'atoun take ciki.
Har lokacin Abdul ya kasa motsin kirki balle har ya iya motsa wata gaba dake jikin sa sabida
yanayin tashin hankalin dayake ciki, hawaye ne suka fara zubo masa Se'a lokacin ya samu
zarafin magana ya kalli Dadaji sannan yace "pls Dada tell me the truth who is she? "inaji a
jikina cewar tamkar inada wata alaƙa ta jini a tareda ita, a lokacin da hannunta ya taɓa jikina naji
zuciyata da gangar jikina duka sun Amsa a lokaci guda, wani irin baƙon yanayi na sabo da
kewa nkeji suna ƙara kusantoni, all i know is Zuciyata ta yarda da ita Kuma ina matiƙar sonta
fiyema da Rayuwata gabaɗaya..!!! Abdul ya faɗa yana Rushewa da kuka tareda faɗawa
jikin Dadaji.
Rarrashinsa ta shigayi tareda kama Hannunsa tace " tabbas dole ne a samu irin wannan
yanayin a yayin da kewar wani babban abu me mahimmanci ta ziyarci zuciyar mutum,
musamman ma idan akace Ƴar Uwar mahaifiya.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan taci gaba da cewa "Abdul wannan maganar bata nan
bace kayi haƙuri ka bari mu isa Asbitin muga Halin datake ciki tukunna inyaso mayi maganar
daga baya bayan komai ya daidaita.
Duk wannan Jawabin da sukeyi kallonsu kawai Su Ummie da Mama keyi. Umaisa kuwa banda
kuka babu abinda takeyi gabaɗaya hankalinta ƙanin baya jikin ta ne, cikin kuka ta nuna Abdul
tace " kadena wasu yi mana wasu kalamanka na yaudara malam, tunda na haɗu da ɗan
Uwanka Rayuwata take shiga cikin matsala har zuwa Ranar da iyayena suka shaida Aurena
dashi, wllh sam Haɗuwata daku ba alkhairi bane tunda har kuke ƙoƙarin kashemin mahaifiyata
duk sanda ta ganku se ciwonta ya tashi waya sani ma nan gaba ko kune Ajalinta kaida
yay........!!!!! Kasa ƙarasawa tayi sabida wani irin kuka dayaci ƙarfinta
Farouq ne yayi ƙarfin halin Jawota jikinsa sannan ya kalli su Dadaji yace "kai wai duk waƴan
nan maganganun da kukeyi masu kamada jirwaye me kamar wanka duk ina suka dosa ne ? "Se
faman wata magana kukeyi wadda gaba ɗayanmu hankalin mu ya gaza fahimtar inda zancenku
ya dosa gabaɗaya, kun barmu a duhu ya kamata ku warware mana komai. Ya faɗa yana bin
Mutanan yolan da wani irin kallo wanda yafi kamada na tsana.
"aa farouq wannan maganar bata nan bace kamar yanda ta faɗa kayi haƙuri mu isa gida
tukunna, yanzudai abinda yafi mahimmanci shine lafiyar Mamie inyaso duk wata magana ta
biyo bayan samun lafiyar nata. Usman ya faɗi hakan ta hanyar dakatar da ƙudirin Farouq ɗin
"Amma Usman ai ya kamata musan komai ko, ka duba fa kaga tun daga ranar da wannan
mutumin ya fara zuwa gidan mu na fahimci zuwansa ba alkhairi bane a Rayuwarmu, shiyasa
tun farko ba wani soshi nake ba har Rain........... "Farouq!!!!!
Ummie ta dakatar dashi ta hanyar daka masa wata uwar tsawa sabida takaicin maganganunsa,
a hasale tace "karufewa mutane baki nace ka barmu muji da abinda yake damun mu..
Shiru yayi yanajin wani irin takaici a zuciyarsa, wannan wace irin masifa ce haka? Tunda
Maheer ya fara zuwa gidansu yaji sam be kwanta masa ba, to yauma ga abinda ganin nasa ya
sake haifarwa nan a kan mamien, nan gaba kuma wayasan meze faru
Damƙe hannun Umaisa Rumana tayi a lokacin da su Usman ke ƙoƙarin fita daga holl ɗin,
sannan ta janyeta daga jikin Farouq zuwa nata ta rungumeta.
Fitowa sukai gaba ɗayan su suka shiga motocinsu sannan Usman yayi musu jagowa zuwa
Asbitinsu yaya Golden ɗin.
Tun kafin su isa Asbitin Dadaji ta ɗaga waya ta shiga kiran wayar Baffa Giɗaɗo, zaune suke a
babban falon Dadaynsu Maheer shidasu Baffa Umaru gabaɗayansu Suna hirar, ƙarar wayarsa
ce ta kauraye ɗakin babban abinda yaja hankalinsa kenan musamman dayayi arba da sunan
Dadaji yana yawo bisa screen ɗin wayar, a nitse ya ɗauka gamida tattara duk wata nuysuwarsa
yace " Jaɓɓanduna Dada?
Dada tace "jam Giɗaɗo Noisare?
"Jam Alhamdulillah Dada ya taron kuma? Shiru ta ɗanyi sannan ta sauke ɓoyayyiyar Ajiyar
zuciya tace "taro Alhamdulillah dama fɗaa maka zanyi duk yanda za'ai gobe inason ganinku
gabaɗayanku A nan Abuja gidan Maheeru Sabida a kwai mahimmiyar maganar da zamu
tattauna A Kai daku me matiƙar mahimmanci a nan ɗin.
Cikeda girmamawa ya Amsa mata da "to Dada Isha Allahu goben zamuzo ɗin kamar yanda
kikace sannan sukai sallama da juna.
*****
Zaune yake dirshan a ƙasan tiles ɗin dake Asbitin idanunsa sunyi jajir sabida tashin hankali
lokaci- lokaci yakan ɗaga kai ya kalli ƙofar ɗakin da aka Shiga da Mamien zuciyarsa na
harbawa da wani irin Sauri, Babu abinda yake illa kiran sunan Allah Haka kuma duk Addu'ar
datazo bakisa yinta yake fatansa kawai Allah ya tashi kafaɗar wannan baiwar Allah.
A haka su Usamn Suka iso Asibitin suka sameshi, har kusan ƙarfe ɗayan dare babu wani
bayani da aka samu daga bakin likitocin akan mara lafiya, dole tasa Usman ya rarrashi matan
suka mayar dasu gida duk irin kukan da Umaisa keyi seda suka maida ita gida kan cewar
gobe zasu dawo da ita da safe, shiko Maheer da Farouq a nan sukaja tunga lokaci-lokaci yakan
zabgawa Maheer harara tamkar shiya ɗowa mamin ciwon a haka har gari ya waye suna zaune
tim tamkar an dasasu. Masallaci suka wuce sukayi sallah sannan suka dawo Reception ɗin
wanda hakan yay daidai da fitowar su khabeeer ko wanne fuskarsa ɗauke da murmushin
samun nasara, da hanzari suna isa gareshi suna tambayarsa yame jikin?
Dafa kafaɗar Maheer khabeer yayi Fuskarsa dauke da murmushi sannan yace " don't worry
about it Lamiɗo she will be fine insha Allah tunda har mun shawo kan matsalar numfashin. Ya
faɗa yana wucesu da sauri sabida lokacin sallah ya fara wucewa.
Sushmah
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
BANYI EDITING BA♀️
_Page:49_
_______Sosai hankalin Maheer ya kwanta dajin abinda Khabeer ɗin ya sanar dashi miƙewa
yayi cikeɗa ƙwarin gwiwa yabar Reception ɗin zuwa parking lot na Asbitin, motarsa ta buɗe ya
shiga ya zauna lokaci guda kuma yayi mata key yabar harabar Asbitin zuciyarsa a cike taf da
tarin al'hini, so yake kawai ya ganshi a gida Gaban dadaji sabida tsabar Ruɗanin daya Addabi
tunaninsa a haka harya iso gidan horne me lafiya ya zabga da hanzari me gadi ya wangale
masa ƙofar shikuma ya danna hancin motar zuwa cikin gidan, a nitse ya fito daga motar cikin
takunsa na isa da ƙasaita ya nufi ƙofar maine falon dake gidan, se'a lokacin ya lura da tarin
takalman dake bakin ƙofar wanda kobe tambaya ba yasan nasu Baffa Giɗaɗo ne da kuma na
Dadynsa.
Jiki a mace ya tura ƙofar haɗe dayin sallama gabaɗayan mutanan dake falon suka juyo suna
kallonsa musamman ma Dadynsa, sakin handile ɗin ƙofar yayi lokaci guda kuma ya sinkuyar da
kansa tareda ƙarasowa cikin falon ya nufi ƙofar bedroom ɗinsa ze shiga batareda yace da
kowa ƙala ba, Dadaji ce ta miƙe da Sauri tace "Ya jikin Nata Maheeru?
Tsayawa yayi cak batareda ya juyo ba yace "Da sauƙi. Ya shige ɗakin ya kulle da mukulli,
Drower bagon dake ɗakin ya nufa lokaci guda ya cire babbar rigar dake jikinsa ya jefarta gefe
guda sannan ya buɗe Drower ɗin da mukullin dake Hannunsa, ba komai a ciki se wata ƙatuwar
a kwati duk tayi ƙura da yana sabida Rashin buɗetan da ba'ayi, janyo a kwatin yayi ya fito da ita
lokaci guda kuma ya tsaya cak yana kallonta zuciyarsa na azalzalarsa akan ya buɗe kodan ya
tabbatar da zarginsa, mukullin dake jikin a kwatin ya ɓalle da ƙarfin tsiya har hannunsa na jini
sabida
Babu komai a cikin a kwatin se manyan Frams an juya bayansu ma'ana fuskar frams ɗin dana
kallon ƙasa ne, zarosu yayi da dauri lokaci guda kuma hawaye na wanke masa fuska a
sakamakon tuna lokacin da Dady yasa masu aikin gidansu su fitar masa da duk hotunan
Momyn su dake gidan su ƙonasu duk a ƙarƙashin jagorancin Makircin Hajiya Murja. Waƴan nan
hotunan uku ne kawai basu ƙona ba sabida suma ya ɓoye ne shiyasa suka tsira.
Fito dasu maheer yayi dika waje yana kallon hotunan yana kuka Momynsu ce zaune se kuma
Dady daga gefanta shikuma Maheer yana jikinta lokacin tana da cikin Abdul akayi hoton
dukansu suna dariya, ɗayan kuma yana ɗan shekara 12 a duniya sukai Hoton shida ita se
kuma Abdul wanda ke ƙaramin yaro ɗan shekara 4 shima duk suna dariya, ɗayan kuma ita
kaɗaice A jiki da tsohon ciki a jikinta tana Murmushi, to Anan ne fa Maheer ya ƙura mata idanu
ya tabbatarwa da kansa cewar tabbas Matar dayakewa kallon Suruka Fa Mahaifiyarsa ce. Wani
irin ihu ya kurma wanda yasa gabaɗaya gidan ya Amsa
Da gudu Su Dady suka nufo ɗakin bayan Dadaji ta gama zaiyane musu duk abinda ya faru a
gurin Walimar tareda shaidawa Dady cewar Tsohuwar matarsa BADI'ATOU fa tana Raye bata
mutu ba, be gama dawowa daka mamakin daya sha kansa ba sukaji ihun Maheer, kuka kawai
Maheer keyi zuciyarsa nayi masa zafi tamkar zata fashe
Wato dama Mahaifiyarsu tana Raye amma shine sharesu ta manta da cewar tana da ƴaƴa har
guda biyu a wataduniyar bata taɓa zuwa ta gansu ba koda so ɗaya ne ? "What kind of mother
she is? Maheer ya faɗa cikin ɗaga murya lokaci guda kuma ya shiga jifa da hotunan tamkar
sabon mahaukaci
Buga ƙofar sukaita yi amma fir yaƙi buɗewa se faman kurma ihu yake sekace me hawa iska,
juyawa Abdul yayi da sauri ya ɗaukki wuƙa a khitchine ya fara ƙoƙarin kwance Handle ɗin ƙofar,
cikin ikon Allah kuwa ya samu nasarar buɗe ƙofar suka kunna kai zuwa ciki, gadan2 Dady ya
nufi inda Maheer ke tsaye ya dafe kai da dukkan hannayensa ya ɗago da sauri yace " don't
come near me Dad you are the responsible for everything, don haka kar ka ƙaraso ida nke a
halin yanzu dukankubana buƙatarku a Rayuwata sabida baku ɗaukemu ƴaƴa ba, bazan taɓa
cewa na tsaneku ba sabida kuɗin iyayena ne but lemme tell you something Daddy I will leave
this House write know kuma wllh both of you daga kai har ita you will never see me again nida
ɗan Uwana!!! Ya faɗa yana miƙewa yaja hannun Abdul da ƙarfi zasu bar ɗaki
Baffa Umaru dake jikin ƙofar ɗakin yana tsaye yana kallon dukk haukan da maheer keyi lokaci
guda ya ɗaga hannu ya zabga masa wani Uban mari me lafiya, tun kafin ya dawo daidai ya ƙara
kwasa masa wani marin Sannan ya nunashi da yatsa yace " don Ubanga Nasiru dake tsaye
idan ka fasa tafiya kaiba ɗan halak bane, karka manta gabaɗayan mu nan babu wanda be
haifeka ba kai harma da wanda yayi jika dakai, lemme tell you something Maheeru iyaye ba
abin wasa bane duk ɗanyan kanka wajibi ne ka saukesu kayi musu biyayya, sannan ya
sassauta murya yace "kaifa ba yaro bane yanzu kaika minzalin da har ka ajiye mata Maheer ya
kamata ka dinga danne zuciyarka kodan karta kaika ga halaka, mu kanmu babu yadda muka
iya da abinda ƙaddara tazo dashi Maheer dole ne mu karɓa
Zubewa Maheer yayi a gurin ya dinga gurzar kuka har seda yayi me isarsa sannan ya miƙe ya
ɗauki mukullin Motarsa batareda yace da kowa ƙala ba ya fara ƙoƙarin fita, Riƙeshi Dadaji tayi
tareda fizge mukullin motar. Rarrashinsa suka dingayi mutanan dake ɗakin shiko Dady babu
abinda yakeyi se kuka
Abdul ma kukan yakeyi tamkar baze dena ba. A haka dai gidan ya kasance babu walwala a
safiyar Ranar gabaɗayanta
*****
Can Asibiti kuwa Mamie bata farka Se wajen ƙarfe 11:00am na safe tana farkawa da Sunan
Maheer ta fara tana kuka, sosai hankalinsu Dr. Khabeer ya tashi suka Rasa yanda zasuyi da ita
Wayarsa ya zaro ya shiga kiran Abba donya Sanar dashi Halin da ake ciki, bugu ɗaya Abba ya
amsa tareda yin Sallama, gaidashi khabeer yayi sannan ya shiga zaiyana masa abinda ke
faruwa, hankalin Abba dake Adamawa ba ƙaramin tashi yayi ba akan batun Badi'atoun don
Haka yace "ka kwantar da hankalinka Khaber insha Allah nima ina hanya yau zan biyo jirgin
shabiyun Rana zuwa Abuja insha Allah sannan ya katse kiran
Kamar yanda Abba ya faɗa kuwa hakanne ya kasance ƙarfe ɗayan Rana a garin Abuja tayi
masa kasancewar bashi kaɗai bane yasa ya fara zuwa gida ya sauke bakin nasa sannan ya
ɗauri niyar Zuwa Asibitin, ko ɗakin da Mamie take Abba beje ba Direct office ɗin khabeer ya
nufa da sallama ya tura ƙofar. Zaune ya sameshi da file a gabansa
Ajiya file ɗin yayi sannan ya kalli Abba yace "Sannu da zuwa Abba ka dawo lfy? Lafiya lau
khabeer Abba yace hakan sannan ya sake kallon khabeer a karo na biyu yace "Son ina fatan
matsalar Badi'atoun ba ciwonta bane ya tashi? Khabeer yace "Ae abba ba ciwon bane kawai
firgita tayi wanda har hakan yasa ya suma bayan hakan ba wata matsala nanda Anjima zamu
Sallameta zuwa gida. Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan yace "to babu matsala to whynot ku
bamu sallamar yanzu mu tafi kawai.
Shiru khabeer yayi sannan yace "to Abba bara na duba naga ko drip ɗin da aka saka mata ya
ƙare. Ya faɗi hakan ya miƙewa yabar office ɗin, seda sukai Sallar Azahar sannan suka kama
hanyar gida har khabeer ɗin, tun kafin Su isa gida kiran Baffa Giɗaɗo ya shigo wayar Abba da
kulawa ya ɗaga babu wanda yaji abinda yace masa illa kawai amsar da Abban ya bashi
yakamar haka "to se kunzo Giɗaɗo Allah ya kawoku lfy. Ya faɗa tareda katse wayar.......
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:50_
______Tunda Motarsu Abba ta sako kai cikin gidan Gaban Mamie keta faɗuwa dama ga
tashin hankalin data samu kanta a ciki na daran jiya , Gabaɗaya komai ya denayi mata daɗi ta
rasa inda zatasa zuciyarta taji ɗaɗi shiyasa gabaɗaya ta ɗinke bakinta ba magana sedai kallo
kawai,
A halin datake ciki a lokacin babu abinda takeso tayi kamar kuka amma kuma ta kasayin hakan,
a yau kam Mamie ta yarda da cewar yin Kuka ma idan damuwa tayi maka yawa shima solution
ne. a haka Abba ya faka motar suka fito zuwa cikin gidan jefa ƙafa kawai Mamie keyi tamkar
idanunta zasu rufe ta zube a ƙasa a haka suka shiga cikin gidan kowa se farin ciki yake da
samun sauƙin nata musamman Umaisa wadda ta miƙe da sauri ta nufi Mamien ta rungume ta
ƙam, ita ko Ameerah tana jikin Ummie tana bacci ta gama rigimar ita Mamien ta zataje har tayi
bacci.
Sama Mamie ta hau ta buɗe ɗakinta ta shiga ta zauna lokaci guda ta fashe da wani irin kuka
wanda ta daɗe batayi irinsa ba, kukan kawai takeyi sabida rashin kwanciyar hankalin datake ciki
a haka Abba ya shigo ɗakin ya sameta, ko kaɗan beyi yunƙurin hanata kukan ba har tayi me
isarta sannan