Showing 57001 words to 60000 words out of 80273 words
tattara dake da abokiyar cin mushen naki kuyi gaba, haka kuma na sakeki saki uku..!!!
wani irin kuka ta fashe dashi me matiƙar taɓa zuciyar duk wani me sauraronta, jiki a saluɓe su
dady sukabar gurin, nan akabar su maheer da abdul a gurin, kuɗi maheer ya zaro daga aljihun
wandonsa rafar ƴan dubu ɗaiɗaya guda biyu ya miƙawa Victoria yace "gashi wannan kuɗin
aikinku ne keda sister ɗinki, daga yau aikinku ya ƙare a gidannan. Cikeda farin ciki suka karɓi
kuɗin tareda surfa masa godiya, seda suka dingurewa su hajiya murja kai sannan suka bar
gurin suna masu ƙara godewa maheer ɗin, sabida tunda uwarsu ta haifesu basu taɓa riƙe kuɗi
masu yawan haka ba.
Daga ɗan nesa da ita Abdul ya tsaya yace "ke murja kike ko wane? Shin kinyarda da maganar
da muka faɗa miki cewar se munga ƙarshenki nida ya maheer?
"ada na tabbata baki taɓa zaton hakan zata kasance ba ko?" hhhhhhhhhh wannan kaɗai ya isa
ki gane cewar aikida hankali yafi aiki da agogo, ya ƙare maganar tareda zabga mata wani
azababben mari me lfiya.
da sauri ta dafe fuskarta tana hawaye, murmushi ya sakin mata sannan yace "kinsan meyasa
na mari wannan ƙazamar fuskar taki?
"na mareki ne sabida ki dinga tunawa dani a rayuwarki, ke kuma me kamada jinjirin biri ya nuna
Binta ƴar kwabo yace "kije basena dakeki ba ciwon dayake jikinki ma kaɗai ya isheki ishara.
Murmushi maheer yayi mai ƙayatarwa sannan yace "Muje yaron momy manta da waƴan nan
matan, har sun fara tafi maheer ya juyo yace dasu "yanzun kam zaku iya tafi duk inda kukeso,
sabida bana buƙatarku a cikin gidana, aiko kamar jira suke suka miƙe daƙyar harda ɗan
gudunsu suka fice daga gidan suna wani irin kuka gwanin ban tausayi,
a haka su maheer suka ƙarasa perlourn zuciyarsu feessss
cikin mintuna kaɗan order ɗin da maheer yayi musu na abinci ta iso, da kansa ya jera komai a
daining aria ɗin sannan ya koma bedroom ɗinsa ya fesa wanka ya fito sanye da jallabiya
maroon colour, suma su Dady ba'a barsu abaya ba seda suka Ashshaka wankansu sannan
suka hallara a daining sukaci suka sha, bayan sun kammala ne aka shiga hirar yaushe gamo,
nan baffa iya ya kira Dadaji a waya ya haɗata da dady sukaita hira tamkar bazasu dena ba, nan
Dady ya sanar da ita cewar insha Allah jibi zasu wuce kaduna, inyaso daga nan zezo gida ya
ganta tareda sauran ƴan uwa da abokan arziƙi.
Karɓar wayar maheer yayi shima suka gaisa da ita, sosai Dadaji ta jajanta masa abinda ya faru
tareda nuna alhininta akan hakan, dariya maheer yayi batareda yace komai ba sukai sallama.
Bayan sun gama hirar ne maheer yake sanar dasu dady batun soyayyarsa da Umaisa tareda
shaida masu yanda sukai da Abbanta a daran jiya.
Sosai suka nuna farin cikinsu akan hakan, nan Baffa Giɗaɗo yake tambayarsa cewar ya sunan
mahaifin yarinyar? A nan take maheer yace "sunansa Alhaji Mahmoud Muhammad kuma yana
aiki ne a Works of Housing fake nan abuja.
wani ƙaya taccen murmushi Baffa Giɗaɗo ya saki sannan yace "indai wannan ne ai baɗuwa
tazo daidai da zama Maheer, indai Mahmoud ne ai nasanshi tare mukai makaranta dashi a
KSUT dake wudil, asalinsa bakano ne a wani ƙauye dake maƙotaka da wudil ɗin, mutumin
kirkine sosai, don haka karkaji komai goɓe idan Allah ya kaimu zamuje mu nema maka Aurenta
da yardan Allah.
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:38_
*KUKAN KURCIYA.....*
*_Ya ilahi! Haqiqa duniya a cike take da ababan mamaki kala-kala, haka kuma al'amarinta mai
girmane, tabbas bahaushe yayi gaskiya dayace inda ranka kasha kallo a duniya, duniya ta
zarce mahangin kowa shiyasa ma ta ishi kowa riga da wando, haka kuma duk shirinka da tarin
guzirinka wata rana seka barta, don haka yi maza ka tattala lokacinka wajen gudanar da abinda
ze fissheka a duniyarka da kuma lahirarka, yi qoqari ka iya furicinka komai qanqantarsa idan ba
haka ba seya jefaka cikin zargin jama'a, Yi qoqari kamaida komai ba komai ba a gaba seka
tadda rabo mafi girma da alfanu._*
___________washe gari kamar yanda baffa Giɗaɗo ya faɗa haka kuwa akayi, don haka
maheer ya kira Umaisa ya shaida mata zuwan magabatan nasa, duda cewar bata cikin yanayi
me daɗi hakan be hanata baiyana masa farin cikinta ba, seda suka ɗan taɓa hira kaɗan sannan
sukai sallama da juna cikeda zallar soyayya.
Tana kashe wayar wazu zafafan hawaye suka shiga sakki mata, yanzu inazata saka rayuwata
taji daɗi sabida Allah?
Shin ta ina zata fara neman mahaifinta da kuma danginta?
Ashe dama duk abubuwan datakeyiwa Abba yana haƙuri da ita ɗama bashine mahaifinta ba?
Rashin sanin amsoshin wannan tarin tambayoyin nata sunfi komai ɗaka mata hankali a
rayuwarta, musannan idan ta tuna wasu lokutan da suka gabata a shekarun baya, komai
ƙanƙantar ciwo idan ya sameta Abba baya taɓa samun kwanciyar hankali har seta warke
sannan hankalinsa yake kwanciya, a kwai lokacin datayi wani mugun zazzaɓi me zafu kamar
zata mutu a ranar Abba kasa bacci yayi, washe garin ranar ko karyawa beyiba ya tafi Asbitin ya
zauna da ita, tun daga ranar ya hana kowa zuwa yace a barshi shine zeyi jinyarta, amma wai
duk irin soyayyar daya nuna mata ace wai bashine ya haifeta ba?
"innanillahiwa'inna ilaihirraji'un waiyo ni Umaisa ina zansa rayuwata naji daɗi ne?
Ya Rabbi ka yaye min wannan ƙuncin rayuwar baƙin cikin danake cik.....!!! Wani irin kuka ne
yaci ƙarfinta dole ta kasa ƙarasa maganar dake kan harshenta.
Meyasa mamie zatamin haka a rayuwata ne?
Mamie dake tsaye a bakin ƙofar ɗakin duk jikinta ya gama sanyi sabida ganin Halinda Umaisan
ke ciki, a hankali take takowa har zuwa tsakiyar ɗakin, jiki babu ƙwari ta miƙa hannunta zuwaga
kafaɗun Umaisa, aiko hakan yayi daidai da juyowarta fuskar nan duk tayi ja sabida kuka tace
"A'a Mamie! Don girman Allah karki taɓani, a halin yanxu sam bana buƙatarki a taredani,
mutumin daya raineni batareda alaƙa ta jini ta shiga tsakanina dashi ba ya riga ya gama
cikemin gurbin duka dangina da maihaifana gaba ɗaya, don haka na roƙeki sabida girman Allah
mamie ki ficemin daga ɗaki ko zan samu hankalina ya kwant.......
Wani gigitaccen mari Mamie ta ɗauke umaisa dashi, wanda yasa jinta da kuma ganinta suka
ɗauke na wucin gadi, sannan mamie ta nunata da yatsa tace "haƙiƙa idan kika hukuntani akan
ƙaddarar da Allah ya aiko miki a cikin rayuwarki zaki tabka babban kuskure a Rayuwarki
Umaisa!! Nifa mahaifiyarki ce, wani adalci kike nema nayi miki wanda ya wuce na haifeki ta
hanyar Aure?"
"don kawai nayi miki laifi ban sanar dake waye mahaifinki ba se hakan ya baki damar dazaki
jefeni da maganganu masu zafi irin haka?"
"Kadafa ki mata cewar a kwai tarin ƴaƴa a duniyar nan waƴanda iyayensu suka haifesu
batareda aure ba, sukuma waƴannan yaran mezasuce da iyayen su kenan ?"
"Seni dana haifeki ta hanyar Aure wanda Al'uma dadama suka shaida hakan ne zan fuskanci
irin wannan hukuncin daga gareki Umaisa?
"yau koda kece a matsayina umaisa abinda nayi shi zakiyi, bafa ninace mahaifinki ya sakeniba,
shine dakansa ya yanke wannan hukunci batareda yayi la'akari da cikinki danake ɗauke dashi
ba, shin a matsayinki na ƴa mace zaki sake waiwayar wannan mutumin a iya rayuwarki?"
Zubewa mamie tayi a gurin tareda sakin kukan data daɗe tana dannewa, da sauri Umaisa ta
matso jikinta ta rungumeta tana kuka tana bawa Mamie haƙuri akan bisa rashin kyautawar
datayi mata, bayanta mamie ta dinga shafawa sannan tace "ki gafarceni ƴata, haƙiƙi ban kyauta
miki ba sam, kawai dai babu yanda na iya ne umarnin mahaifina nakebi."
a haka wani wahalallen bacci ya ɗauketa, babu abinda take saukewa sama da ajiyar zuciyar
kukna data gurza, sosai fuskarta da bakinta sukai jajir sabida kuka abinka da farar mace,
kwantar da ita Mamie tayi a saman gadon tareda gyara mata kwanciya ta lulluɓeta da lallausan
bargon dake saman gadon, kallonta kawai Mamie takeyi a ranta tana mejin wani irin tsusayin
ɗiyar tata, yanzu ta ina zata fara neman Bawuro a Rayuwarta balle harta danƙa masa ɗiyarsa
ta huta?
Wasu siraran hawayene suka shiga zubo mata sabida rashin sanin cikakkiyar amsar tambayan
datayiwa kanta, share ruwan hawayen tayi da bayan hannunta sannan ta miƙe tabar ɗakin,
bayan fitarta babu jimawa Khaber ya shigo ɗakin, sanye yake cikin wata milk ɗin jallabiya
wadda tai matiƙar karɓar jikinsa, kallo ɗaya zakayi mai ka fahimci ramar dake fuskarsa, a
hankali ya dinga takawa cikin takunsa irinna ƙasaitattun maza masu jida kansu haryakai bakin
Gadon ya zauna, ƙurawa fuskarta manyan Golden Eyes ɗinsa yayi yana kalonta cikeda ƙauna,
wata sassanyar ajiyar zuciya ya saki wadda ke baiyana tsantsar kewarta dayayi, wani irin so
yakeyi mata wanda Yakejin baze iya musltawa ko wani mahaluki shiba a duniya, a hankali ya
miƙa hannunsa zuwa kan kyakkyawar fuskarta ya shafa, tsuke baki tayi kamar wadda ke shirin
magana amma kuna still idanunta a rufe suke tana ta kwasar baccinta, wani cute smile ne yayi
escaping lips nashi sannan ya zaro wayarsa dake aljihun gaban jallabiyarsa ya shiga snaping
ɗinta, ya jima a ɗakin yana aikin ɗaukanta hotunan sannan ya miƙe yabar ɗakin, kamar daga
sama taji anata kiraye-kirayen sallan Azuhur, da sauri ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka tareda
ɗauro Alwala, a gaggauce ta shirya sannan ta tada sallah, cikin mintuna da bazasu gaza 7 ba ta
idar, a nan ma seda taci kuka sosai tana ronƙon Allah kan yayaye mata damuwarta sannan
kuma yayiwa rayuwarta zaɓin dayafi zama alkhairi a gareta.
wayar gefan gadonta ta ɗauka ta shiga kiran Abba, nan ta sanar masa batun zuwan iyayen
maheer ɗin, murmushi Abba yayi me sauti sannan yace "mamana ai ya kirani ya sanar dani
zuwansu a yau ɗin, haka kuna nayi farin ciki da hakan, sannan ban Amince ki sanarda kowa
wannan batunba na zuwan nasu, daga nan zan shirya dukkan abinda ya dace, a ƙarshe kuma
ina me sanar dake cewar muddin ina raye wallahil'azeem wanda kikeso shi zan baki ki aura, ta
hakane kawai zan Sauke nauyin da Allah ya ɗoramin a kanki, karki taɓa yarda ki Auri khabeer
Da sunan zakiyi min kara, sabida bana cikin iyayen da suke matiƙar son kansu, ni ubane me
adalci ga Ahalinsa!
kasa magana tayi illah hawayen dake zubo mata kamar an kunna fanfo, muryarta na rawa tace
"i love you my bravo Dady!!
murmushi yayi sannan yace " love you too sweetheart."
A haka suka gama maganar ya kashe wayar, duk wani abu daza'a buƙata Abba ya shirya komai
batareda su Mamie sun sani ba, ƙarfe 5:00pm su baffa Giɗaɗo suka hallara a unguwar Zone E
Apo legislative Quarters manyan motocine na alfarma, wanda kallo ɗaya zakayi musu kasan
masu matiƙar tsadane, a haka me gadi ya wangale musu ƙofar gidan duka danna hancin motar
zuwa cikin gidan, inda aka tanada don perker motoci sukaje sukayi parking sannan suka firfito,
ciki kuwa harda Dady wanda ke sanye cikin wata dakakkiyar shadda giznah wadda keta uban
sheƙi tana yararin tsada,
A nitse suka ƙaraso harabar gidan fuskokinsu duk a ɗaukeda murmushi, da usman suka fara
cin karo sabida Abba ya sanar dashi zuwansu kan cewar idan sun iso ya kaisu ɗakin baƙi na
musamman, haka kuwa akayi cikin mintuna kaɗan Usman yayi mudu jagora zuwa cikin
perlourn, nan da nan ya cika gabansu da kayan motsa baki iri-iri, sannan Abba ya fito shima
fuskarsa ɗauke da murmushin farin cikin ganinsu.
da sakin fuska ya ƙaraso perlourn tareda tarbar babban Abokinsa wato Giɗaɗo Abubakar
lamiɗo tareda ƴan uwansa, sosai Abba yaji daɗin ganin Aminin nasa, nan suka shiga hirar
yaushe gamo, bayan lafawar komai ne suka gabatar da bukatarsu ta nemawa Ɗansu Auren
ɗiyarsa, ba musu Abba ya Amince kuma ya basu, nan ya buƙaci da su fito da sadaki ayi komai
a wuce gurin inyaso daga Baya semu gudanar da sauran shagulgulan, sosai sukai na'am da
batun Abban, nan baffa Umaru ya zaro dubu hamsin Ya miƙawa Abba, a nan take mutanan
dake perlourn suka shaida Ɗaurin Auren Maheer Nasir Lamiɗo da Umaisa Mahmoud
muhammad, akan sadaki dubu hamsin,
Shiru Usman yayi zuciyarsa duk a dagule lokaci guda kuma wani irin tausayin yaya Golden ya
shiga kwaranya a zuciyarsa, yanzu shikenan ya Golden ya rasa Umaisa kenan?
Amma meyasa Abba zeyiwa khabeer haka? Indai kuwa har hakane Abba beyiwa khabeer
adalci ba, a haka taron ya tashi kowa yana san barka da karamci irin na Alhaji mahmoud, mota
baffa Giɗaɗo ya koma ya ɗakko daurin goro guda hudu mayanya da kuna katan na alawa ya
koma perlourn ya kai ya danƙarawa Abba kan cewar a rabawa mutane don su shaida.
se dabda marib sukayiwa Abba sallama suka wuce gida, a nan Abba ya kalli Usman yace "son
maza ka ɗauki goron nan da alawan ka shiga musu dashi gida, ba musu Usman ya kwasa yakai
maine perlour ɗin gidan, seda Abba yayi sallan magrib sannan ya shiga gidan, yakoyi sa'a duk
suna perlorn saɓanin Umaisa data ɗaura da zaman ɗaki tun lokacin dataji matsayinta a gidan,
da sallama ya shigo perlourn tareda zama a ɗaya daga cikin kujerun dake perlourn, seda suka
gaisa da Baba sannan ya miƙa mata goro da Alawar dake gabansa yace "Baba ga goro nan da
alawar ɗaurin Auren ƴata Umaisa da Maherr, seku rabawa sauran jama'a don suji kuma su
shaida, wata muguwar faɗuwar gaba Ummie yayi lokaci guda kuma ta zube a ƙasan
gwiwoyinta tana wani irin kuka.
Hakanne ayi dadai da shigowar yaya Golden perlourn!!!!!!
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:39_
*KUKAN KURCIYA*
*_Haqiqa ilimi baiwane, Rayuwa kuma hikayace, Jahilci ba uziri bane balle yazama katangar
jingina ga kowa, Yi qoqari ka hangi abinda yake kusa dakai ba wanda yake nesa dakai ba,
yawan walwala yafi yawan Qunci, yi qoqari kaso kowa idan kayi hakan dame zaka ragu.♀️_*
___________ kasa motsin kirki khabeer yayi, daƙyar yake iya ɗaga ƙafafunsa har zuwa inda
Abba ke zaune, murmushin ƙarfin hali ya saki tareda kama hannun Abba yace" Na tayaka
murna sosai Abba, da har kasamu nasaran sauke nauyin da Allah ya ɗora maka a matsayinka
na Uba me adalci ga Ahalinka." yana kaiwa nan a maganarsa ya miƙe yabar perlourn
zuciyarsa na masa wani irin zafi,
Wani irin kallo Baba ta dinga bin Abba dashi, amma sedai babu yanda ta iya tunda ya riga yayi
gamon kansa wajen bada Auren Umaisa ga wani can daban, ƙaddara kenan tariga fata.
Mamie kuwa kasa magana tayi sabida yanda taji maganar kamar saukar aradu a tsakiyar kanta,
amma meyasa Abba zeyi haka bayareda neman shawaranta ba? Yanzu meye ma'anar abinda
ya aikata kenan?
Zubewa tayi a gurin tana mai firta "hasbunallahuwani'imal wakeel, yanzu dawani ido duniya
zata kalleni ni Badi'atou?
Kukan Ummie ne kawai yake tashi a tsakiyar perlourn, Usman ne yayi ƙarfin halin ƙarasawa
inda Ummien ke zaune ya riƙeta tareda faɗin "don girman Allah ummie kiyi haƙuri kidena kukan
nan, idan kema kina kuka taya zamu samu ƙarfin gwiwan Rarrashin ya Golden?"
"Ummie kefa Uwace kuma me bamu ƙarfin gwiwa akan komai, don haka don Allah ki dena
damuwa ki manta da komai mubarshi a matsayin ƙaddaran da Allah ya aiko mana gaba ɗaya,
Miƙewa Abba yayi yabar perlourn sabida baze iya juran ganin zubar hawayen Ahalin nasa ba,
shi kansa babu yanda zeyi ne shiyasa, haka kuma bayaso ya tauye umaisa ko kaɗan, tunda har
yayi alƙawarin ze cike mata gurbin mahaifinta dole ne ya bata abinda takeso muddin beci
karoda koyarwan addini ba, musamman ma yanzu dayake a kwai ciwo a rayuwarta wanda yasa
take keɓance kanta ita kaɗai, wannan kawai ya isa yasa ya bata abinda takeso badan komai ba
kodan sabida farin cikinta.
Dafa kafaɗun Mamie baba tayi, sabida yanda ta lura da irin tashin hankalin data ke ciki, sabida
kalaman na Abba, a hankali Baba ta buɗe baki tace "Kiyi haƙuri Badi'atou ki karɓi Abinda
ƙaddara tazo dashi, tun ran gini ran zane Allah ya rubuta cewar ba Khabeeru bane mijin
Fatsima, shiyasa kukaga har hakan tafaru, a halin yanzu babu yanda muka iya wanda ya wuce
mu sanyawa ƙamarin albarka tareda yi mata fatan zama lfiya a gidan Aurenta.
Wata doguwar ajiyar zuciya Mama ta sauke, lokaci guda kuma ta shiga share zufar dake yanko
mata tace "tabbas abinda Baba ta faɗa gaskiyane, haka kuma babu wanda ya isa yaja da yin
Allah, dama kama nakane Allah yana nashi, duk musulmin ƙwarai dolene yayi imani da dukkan
Abinda Allah ya ƙaddaro masa a rayuwa, don haka munayiwa Umaisa Fatan Alkhairi a gidan
Aurenta, shikuma khaberr Allah yayi musu zaɓin alkhairi.
Da amin suka amsa gabaɗayansu Amma banda Mamie wadda gaba ɗaya ta koma kamar wata
sakarya sabida yanda abin ya girgizata ainun.
A haka ahalin suka kasance cikin ƙunci a wannan rana.
A ɓangaren su maheer kuwa ba ƙaramin farin ciki suke ciki ba musamman ma da sukaji
abindasu Dadyn sukazo dashi, a rayuwar maheer shine