Showing 18001 words to 21000 words out of 80273 words

Chapter 7 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2752

Tab'e baki
Umaisa tayi sannan ta bud'e murfin motar ta fito, tunda ta fito Beebah take kallonta sabida bata
tab'a zaton a kwai Umaisa a cikin motar ba, wani irin kalo ta dinga binta dashi, itako Umaisa yi
tayi kamar batama san tanayi ba, seda ta fara tafiya sannan ta juyo ta kalleta tace "Aunty
Beebah ina yini?

Sabida takaici kasa amsawa Beebah tayi a ranta tace" yanzu dama dan rashin mutunci ya
khabeer yasan da yarinyar nan a motar shine yake gaya mata magana a gabanta danta raina
ta!!! Katse ta yayi ta hanyar cewa " tunda bazaki gaidani ba matsa kiban hanya na fito. Cikeda
jin kunya tace "i'm so sorry kazo lfy?
Be bata amsa ba yay gaba ita kuma ta rufa masa baya, A ransa yace " a kwai aiki a gabana
muddin na bari su Ummie suka had'ani da wannan yarinyar, da sallama ya shiga parlourn
fuskarsa a sake, zaune ya samu su Hajiya Fatimah itada su Rumana tana ta faman tsokanarsu
musamman ma Umaisa, fad'ad'a murmushinta tayi sabida ganin Surukin nata, zama yayi a
d'aya daga cikin Royal chairs din da sukayiwa perlourn k'awanya, cikeda girmamawa ya
gaisheta tareda tambayarta mutanan gidan, da sakin fuska ta amsa masa sannan shiru ya
ratsa perlourn na d'an lokaci, kasancewarsa ba ma'abocin son magana ba, Umaisa ce ta katse
shirun da cewa "mamah ina Aunty maryam taje ne? Murmushi Hajiya Fatima tayi sannan tace "
mutuniyarki zakice min, bata nan tana gurin aiki se nan da jimawa zaki ganta, k'ilama kiji
shigowarta yanzu, murmushi Umaisa tayi sannan tace "Allah sarki Aunty maryam ba dad'e ban
ganta ba wllh, dariya ruman tayi sannan tace " wllh nima nayi missing d'in Aunty maryam.
Dariya sukayi gaba d'aya sannan mama tace " indai maryam ce nasan duk inda take yanzu tana
hanyar dawowa gida, kamar had'in baki kuwa se gata ta shigo perlourn da sallama, da gudu
Umaisa ta nufeta tana fd'in oyoyo Aunty maryam d'ina i miss you so much wllh ta fad'a tareda
yin hugging d'inta, hunging d'inta back maryam tayi tareda cewa i miss you too sweetheart, a
haka suka k'araso perlourn hannun maryam sark'e cikin na Umaisa murmushi kawai maryam
takeyi har ta zauna a kan kujerar dake perlourn, sannan kalli khabeer tace "ya khabeer sannu
da zuwa, ina yini? Da sakin fuska ya amsa mata sannan ya maida kallonsa ga Beebah wadda
ta gama cika fam kamar zata fashe, mik'ewa yayi ya fita daga perlourn dan haka Beebah ta
mara masa baya, guiding d'in gidan ya nufa sannan yaja flastic chair d'in dake gurin ya zauna,
bata da wani zabi dan taja kujerar itama ta zauna, tsareshi tayi da madaidaitan idanunta tana
kallonsa, tabbas ita kanta tasan tana matik'ar son khabeer, amma kuma har yanzu ta kasa gane
ainihin abinda ke cikin ransa a gameda ita, komai tayi dan ta burgeshi sam baya gani, wasu
lokutan ma har takanji cewar halaiyarsa ta ko in kula dayake nuna mata yana matiqar bata
haushi. duk wannan zancen zucin da Beebah takeyi khabeer bema san tanayi ba, danne
dannen wayarsa kawai yakeyi.

Wayarsa ce ta d'au Ringing dan haka ya maida kallonsa ga me kiran, Mamien Umaisa ce take
kiransa, dan haka da sauri yayi picking cikeda girmamawa yace " Mamie, daga b'angaren
Mamie tace " khabeer dan Allah idan zaku dawo gida ka tahomin da maganin ciwon kan da ka
tab'a kawo min daga Asibitin ku, wllh ciwon kan ne ya matsa min dayawa, cikeda girmamawa ya

amsa mata da to mamie Allah ya sawak'e, yana kaiwa nan ya katse wayar tareda mik'ewa,
kallon Beebah yayi sannan yace " toni zan wuce, idan kin shiga ciki kice musu su fito mu tafi,
yana kaiwa nan yay hanyar perking space batareda yaji tacewarta ba. Da ido tabishi da kallo
harta dena hangensa, komai nasa masifar burgeta yake, Jikinta ne yay masifar sanyi dan haka
ta mik'e ta nufi cikin gidan kamar kazar da k'wai ya fashe mata a ciki, bata jima da shiga ba su
Ruman suka fito tareda maryam wadda ke rik'e da hannun Ameerah, har bakin motar ta rakosu
sannan ta kalli ya khabeer tace " har zaku wuce da wuri haka ya khabeer? Murmushi yayi
sannan yace" ae wllh maryam wani uziri ne ya taso min, dariya tayi sannan tace "ta likita bokan
turai, murmushi kawai yayi batareda yace komai ba,

Ledar hannun ta ta mik'a musu wadda ke shak'e da coclet da kuma sweet kala kala, godiya
sukai mata sannan yaja motar suka kama hanyar gida, a bakin wani babban phamarcy yay
parking, wayarsa ce ta fara Ringing, dan haka ya maida hankalinsa sosai a kan wayar, picking
yayi tareda kara wayar a kunnensa, wata k'aramar takarda ya zara a cikin aljihun gaban motar
sannan yayi d'an rubutu kad'an a jiki, mik'awa Umaisa dake gefansa yayi sannan ya zari 2k ya
mik'a mata, karb'a tayi sannan ta bud'e murfin motar ta nufin cikin pharmacy d'in, tana zuwa ta
mik'awa wata mata wadda ta gani sanye da farar riga, karb'a tayi sannan ta saka mata maganin
a ledar ta mik'a mata.

Karb'a tayi sannan tayi mata godiya ta juya, wata mata ta gani hannunta rik'e da wani cute popy
wanda yay masifar d'aukar hankalinta, sabida yanda ta shagala da kallon k'aramin karen harta
iso k'ofar glass d'in bata sani ba, kawai seji tayi tayi karo da mutum, jikinta ne ya d'au ki wani
irin rawa sabida tsoro
Hakanne yasa tatafi da baya zata fad'i Runtse idanunta tayi da k'arfi tana jira tajita a k'asa, da
wani irin mugun sauri ya tareta ta fad'o jikinsa.





*_Muje zuwa sisters yanzu aka fara wasan�_*



_Comment_
Nd
_Share_


*Daga alqalamin Zm chubado✍*
_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:13_

___________ Rintse idanunta ta sakeyi da k'arfi sabida yanda ta tsorata, k'urawa fiskarta
idanu yayi yana kallon yanda lips d'inta ya tattare sabida yanda jikinta ke rawa, kallonsa ya
mayar kan dogayen lashes d'inta, wa'yanda sukayiwa idanunta ado, hannunsa yasaka a daidai
kumatunta sannan yay taping kad'an, cikin huskey voice d'insa yace "ke zaki bud'e idanunki ko
kuma sena watsa miki mari?

A hankali ta fara bud'e manyan idanun harta gama bud'e su tsaf a kan Maheer, zaro ido tayi
sosai tana k'are masa kallo, nan da nan kashedin daya rangad'a mata last 2weeks da suka
wuce ya fara dawo mata tsaf a tunanin ta, tamkar a lokacin ya kora mata shi, nan da nan
idanunta suka cika taf da k'walla, banda motsi babu abinda lips d'inta sukeyi, a zahiri so take
tayi magana amma kuma ta kasa sabida yanda tsoronsa ya samu gurbi a cikin zucyarta yay
kanekane, mik'ar da ita yayi har ya samu ta daidaita tsayuwarta sannan ya sake kallon ta a karo
na biyu yace " hy Queen of tears, ko ki goge wannan hawayen naki marasa dalili, kokuma
yanzu in saki kukan idan shi kike buk'ata.

Da sauri tasa hannu ta goge hawayen tareda turo d'an k'aramin bakinta gaba, matsowa yayi
dab da fuskarta sannan ya k'yasta hannunsa sau biyu sannan yace " ohhh da alama kina so
bakinki ya sake kumbura ne a karo na biyu. Da sauri ta dafe bakin da hannunta, sabida bazata
tab'a manta irin azabar daya gana mata ba, wani miskilin murmushi ya saki sannan ya ratsa ta
gefanta ya wuce, da sauri tasa hannu tura k'ofar glass d'an zata fice, muryarsa ya d'an d'aga
yace " heeey Queen of tears, karki sake bari mu had'u dake a karo na uku. Ko juyowa ba tayi
ba ta kwasa da gudu tayi waje, seda ta kusa isa parking space d'in sannan ta fara k'ok'arin saita
nutsuwarta, k'ofar motar ta bud'e sannan ta shiga ta zauna, bisaga mamakinta setaga har
lokacin yaya khabeer wayar yake be gama ba, wata sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke sabida
tasan da ace ba waya yake amsawa da tini ya farayi mata fad'an taje ta zauna Daga zuwa siyan
magani, tana rufe k'ofar khabeer ya figi motar suka nifi hanyar gida.

Minti 15minute ne ya d'aukesu zuwa gida, a nitse suka gita daga motar sannan suka nufi cikin
gida, babu kowa a perlourn se Usman da kuma Farouq, gefansa kuma Ummie ce ya d'ora
kansa bisa cinyarta, ya tsina fuska Usman yayi sannan ya kalli Ummie yace "pls Ummie don

Allah ku d'aga tafiyar nan naku mana, wllh Ummie banaso ku bar gidannan babu masu dafa
mana abin.... "Usman ka kiyayeni wllh kudai yaran nan wllh kunada samun guri, in banda
iskanci bakune kukace bakwason masu aikin ba da kanku? Turo baki Usman d'in a shagwab'e
tamkar wani k'aramin yaro yace "Eyyah Ummie nifa akan su Ruman nake magana pls kubar
mana su muzauna tare mana inyaso ku sekuyi tafiyar ku da Dadyn, mu mazo daga baya idan
sunyi hutu pls. Ya fad'a yana had'a hannunsa duka biyun yana kallon Ummie

Tab'e baki Farouq yayi sannan yace "Ummie wai yanzu don Allah har son zuwa gidan wannan
jarababbiyar tsohuwar kukeyi? Ni wllh bana son zuwa Gano sabida fitinar matar tsohuwar nan,
kana zuwa zata ishe ka yaushe zakayi aure, idan kace kai ba yanzu ba kuma tasawa Abba
kukan gulma.
Kunnensa Ummie ta murd'a sannan ta buge masa baki tareda ture kansa daga cinyarta tace " ai
wllh Hajiya Babba takeyi shine daidai, Allah yasa ma dukanku ta zab'o muku matan aure a can
garin naku inyaso muga ta tsiya, tashi yayi kamar zeyi kuka yace "haba Ummie don Allah....!!!

Dariya Usman yayi sannan yace "heey. dude ka rabu da Ummie kawai, taya za'ai Classy gay's
kamar mu muk'are da auren zab'in wannan tsohuwar. Dariya suka fashe da ita, suna shirin barin
perlourn su Rumana suka kunno kai da sallama,

Da sakin fuska Ummie ta tarbesu amma kuma kallo d'aya tayiwa khabeer ta fahimci babu
walwala a tareda shi, a dak'ile yace " Ummie ya gidan? Be jira cewarta ba ya nufi upstears,
Direct d'akin Mamie ya nufa, da sallama ya shiga perlourn tareda lumshe manyan Golden Eyes
d'insa sabida wani daddad'an k'amshin turaren wutar daya bak'unci hancinsa, babu kowa a
perlourn se k'arar Tv, a hankali ya nufi k'ofar bedroom d'inta, a hankali ya fara knowking d'in
k'ofar, be jima sosai ba ta bashi izinin shiga, a kwance ya sameta a kan Gado ta rufe duk jikinta
da babban blanket, da sauri ya k'arasa bakin gadon tareda bud'e bargon kad'an, cikeda
damuwa ya sanya hannunsa a kan goshin Mamie wadda jijiyoyin kanta sukan suka tashi sosai
sabida ciwon dayake mata,

Mik'ewa yayi da sauri yabar d'akin, da sauri ya sakko, be tsaya yiwa su Ummie bayani ba ya
nufi side d'insa,

abin Auna jini (Sphygmomanometer) da wasu abubuwan da duk ze buk'ata, da sauri ya fito ya
sake wuce su Ummie wadda Rumana ke bata labarin Aunty maryam, da ido Ummie ta bishi
amma kuma se bata kawo komai ba, da sauri ya k'arasa cikin d'akin ya sameta a yanda ya
barta, yaye bargon yayi tareda kiran sunan ta, shiru yaji bata amsa ba, da sauri ya kara
hannunsa a bakin hancinta, k'irjinsa ne ya buga da k'arfi, da wani mugun sauri ya kara
kunnensa a saitin k'irjin Mamie n, a hankali yaji zuciyarta na harbawa, sedai na normal yanda
na masu lafiya yake beeting ba, hannunsa yasa a satin k'irjinta yana dannawa ko numfashin ze
dawo amma kuma shiru, mik'ewa yayi da wani mugun sauri ya fita yay downster, side d'insa ya
koma ya d'akko wayarsa da ya bari a gefan gadonsa,

Tun kafin ya fito ya kira waya Asbiti a turo musu Amblance, kashewa yayi sannan ya fito
perlourn, har ze wuce Ummie tace " wai kai lafiyanka kake ta faman zarya kamar kayiwa sarki
k'arya? Ba tareda ya juyoba yace "Ummie this is Emergency case, ciwon Mamie ne ya tashi..!
Da sauri Ummie ta mik'e tabi bayansa, inda Ruman da Umaisa suka fara kuka, Farouq da
Usman ne suka marawa su Ummie baya, cikin mintunan da basu gaza 15ba motar Asbitin ta
iso, nan da nan me gadi ya wangale musu Get suka shigo.

Wani dogon gado suka fito dashi daga motar sannan suka kunna kai zuwa cikin gidan, Rumana
ce ta kaisu har d'akin sannan su Farouq da khabeer suka kamata suka d'ora a gadon, k'arar
jiniyar motar Asibitin ce ta tayar da Ummah dake bacci, da sauri ta diro daga gadon ta fito, da
wasu noses ta fara cin karo dan haka ta fahimci tabbas jikin Badi'atou ne ya tashi, babu abida
take firtawa se innanillahi'wa'ina'ilaihirraji'un!!!!!!

A haka suka fito da ita sanbal a kan gadon, a gaggauce suka fito da ita sannan suka sakata a
motar, khabeer ne ya shiga tareda noses din sannan Drivern ya figi motar suka nufi Genarel
Hospital da ita..





_Commet_
_Nd_
_Share_



*Zm chubado, sushmer�*

_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


*_haqiqa qauna halittace ta ubangijin al'arshil'azeem, shikadai ne wanda yake sanya soyayyah

a zukatan al'ummah har su samu damar nunawa wanda suke so qaunah, SUMAYYAH
UTHMAN ADAM, and NUSAIBA ALI MUHAMMAD, ni Zm Chubado naga sakonku da kuma irin
tarin addu'o'in alkhairin da kukayi min, Allah ubangiji yabar zumuncin alkhairi, nima ina sonku
fisabilillah❤_*

_Page:14_

___________ suna isa Asbitin suka fito da ita a gaggauce sabida yanda condition d'in nata
is very worst, turata sukayi zuwa wani d'aki na musamman domin bata taimakon gaggawa, da
sauri Khabeer ya kunna kai zuwa d'akin da aka shiga da Mamien, tun kafin Dr. Abas
muhammad ya k'araso d'akin tuni Khabeer ya fara gudanar da abinda ya dace,
Har Dr. Abas ya shiga room d'in amma dukda haka babu wani cigaba da aka samu gameda
daidaituwar numfashin nata,

da sauri Khabeer ya kalli noses d'in yace " ku bani 325 miligram (preferably uncoated) na
Aspirin injection da sauri pls!!

Wani d'an isakan kallo Dr. Abas yake bin Khabeer dashi, sannan yace "taya za'ai kayi mata
Aspirin injection bayan kuma muna sa ran daidai tuwan numfashin ta a hakan? Wani kallo
Khabeer yayi masa sannan yace "a hakan kake zaton zamu samu daidaituwar numfashi a
hakan? Kaduba fa kaga a irin condition d'in da take ciki malam, karkayi min kallon mahaukaci
malam, i'm a madical Doctor kamar yanda kake, ya k'are maganar yana gyara zaman oxcigyn
d'in dake fuskar Mamie,

Ba tareda ya kalli Inda Dr. Abas d'in yake ba yace " abinda yasa kaji nace abata Aspirin injection
sabida, Aspirine can help break up the blood clot that is cousing the heart attack shiyasa, a
matsayinka na likita ya kamata ka fahimci hakan!

Alurar ya karba sannan yayiwa Mamie batareda ya sake bi ta kan Dr. Abas ba,

Jikin Dr. Abas sanyi yayi sosai sabida betab'a zaton Khabeer likita bane, shiyasa yayi masa
hakan, sauke duk wani girman kai dayake ji dashi yayi sannan suka had'u duka su biyun akan
Mamie, duk wani taimakon daya kamata su bata sun bata, amma sam babau wani cigaba da
aka samu, sabida har yanzu basu samu nasarar daidaituwar numfashin nata ba,
Ja sukai da baya duka su biyun sabida yanda sukaga numfahin mamien yana sakeyin k'asa,
daga 100 ya dawo 60, wani irin bugawa k'irjin Khabeer yayi, lokaci guda ya maida kallonsa ga
Dr. Abas, dafa kafad'arsa kawai Dr. Yayi sannan yace "im sorry Dr. amma munyi iya bakin
k'ok'arin mu, sedai kawai mubarwa Allah sau........... Tun kafin ya rufe baki Mamie taja wani
dogon numfashi, bisaga taimakon oxcigyn d'in dake manne a hancinta. Ajiyar zuciya suka
sauke gaba d'yansu sannan suka k'arasa bakin gadon da suri, Allurar bacci Dr. Abas yayi mata

sannan ya bada umarnin a turata zuwa d'aki na musamman, sannan kuma kar'abar kowa ya
shiga inda take har seta farka,

Cikeda gimamawa suka amsa masa, cikin mintunan da bazasu gaza 15ba suka kammala komai
cikin tsari, sannan Dr. Abas yabi bayansu ya sanya mata Drip ya fito daga d'akin,

kusan a tare suka fito da Khabeer, wanda keta faman kalon su Usman wanda suketa safa da
marya a reception d'in Asbitin, mamaki halin Usman da Farouq kawai yakeyi musamman daya
hangi uwar gaiyar da suka kwaso suka taho da ita, Dr. Abas ne ya katseshi ta hanyar mik'a
masa hannu alamar su gaisa,
Ba musu shima ya mik'a masa nasa hannun, da sakin fiska Dr. Abas yace i'm Dr. Abas
muhammad Adam. Murmushi kawai yayi sannan yace " i'm Dr. Khabeer mahmoud muhammad,
murmushin jin dad'i Dr. Abas yayi sannan yace " nice to meet you Dr. Khabeer. A haka suka
fito reception d'in Khabeer na biyeda Dr. Abas d'in a baya, da Abba suka fara cin karo, cikeda
damuwa ya nufi Dr. Abas d'in tareda tambayarsa jikin matar tasa, murmushi yayi sannan yace
"karka damu Alhaji insha Allah komai zaizo da sauk'i amma kafin nan mu k'arasa office inyaso
semu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login