Showing 60001 words to 63000 words out of 80273 words
labarin dayaji mafi daɗi a rayuwansa,
don haka misalta farin cikin maheer ɗin abune mawuyaci a garni dashi gaba ɗaya, nan dady ya
shiga kiraye-kirayen wayan abokan arziƙi da manya-manyan abokansa,
Baffa umaru ne ya kira su Dadji ya sanar dasu dukkan abinda ya faru, sosai itama ta nuna farin
cikinta da auren maheer ɗin, a haka zuriyar suka kasance cikin walwala da farin ciki mara
misaltuwa,
Umaisa ce zaune bisa cafet ɗin dake ɗakinta duk ta zama wani iri kamar ba ita ba, a haka
Ruman ta shigo ɗakin jiki babu ƙwari ta zauna daga gefanta, tajima a zaune babu wanda yace
da ɗan uwansa ƙala, Rumance tayi ƙarfin halin miƙa mata goro da alawan dake hannunta tace "
wannan naki ne umaisa, haka kuma shine ze baki tabbaci wajen shaida cewar kin zama
mallakin *ZAƁIN RANKI* kamar yanda kike fata, haka kuma a matsayina na ƴar uwarki inayi
miki fatan alkairi a zaman dazakiyi da mijinki abin sonki, har kullum kallo ɗaya nake miki
umaisa, ban taɓayi miki kallon keba jinina bace, haka kuma ina matiƙar sonki ƴar uwata!"
ƙanƙame juna sukayi itada Ruman lokaci guda kuma suka saki wani irin kuka a tare, ko kaɗan
umaisa bata girgiza dajin batun Aurenta a bakin Ruman ba, sabida tashin hankalin datake ciki
ya shallake na maganar Aurenta da maheer ɗinta abin sonta!!!!
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:40_
*_Eid mubarak to all Muslim's Ummah, may Allah Subahanahuwati'Alah accept our Ibadah and
forgive our sins, Ya Allah kayi mana Rahamah sannan ka wadatamu a duniyarmu da kuma
lahiran mu gaba ɗaya, Ya Allah ka rufamana Asirin Duniya da kuma na lahiranmu inayiwa
ɗaukakin Al'umar Musulmai barka da Sallah_*
___________ lokaci guda taji gaɓɓan jikinta duk sunyi sanyi gefe guda kuma na zuciyarta ya
shiga bigawa A hankali, Hakanne ya saukar mata da wani irin yanayi me wahalar misaltawa,
sakin Rumana tayi lokaci guda kuma ta dafe kanta dayayi mata wani irin mugun nauyi,
murmushin ƙarfin hali Rumana ta saki tareda share tarin ƙwallar dake zubo mata tace "haƙiƙa
komai na duniya yana da mujarrabinsa, haka kuma kowani Ɗan Adam na duniya yanada kalar
tasa Ƙaddarar muddin a kwai Rai a cikin gangar jikinsa,
Rumana ta ƙara da cewa "muddin kai musulmi ne kuma me imani dole ne kayi imani da duk
wata jarrabawa da zakaci karo da ita a rayuwarka, mekyau ko mara kyau, amma Tabbas da ace
inada ikon canza wannan ƙaddarar data kunno kai kuma take barazanar Tarwatsa mana farin
cikin Ahalinmu wllh dasena canzata da gaggawa Umaisa!
Share hawayen dake zubo mata Umaisa tayi da bayan hannunta sannan ta sake kallon
Rumana a karona biyu tace "jarrabawar kenan Rumana! inda ace munada wannan damar wllh
tunkafin wani yayi yunƙurin canza Wannan ƙaddarar nida hannuna zan Riga kowa canzata ƴar
uwata, a kaina ni kaɗai Mutanen da Basu cancanta in sanyasu kuka ba yau gashi nida kaina
nasasu kuka Ruman, Tun tasowata suke ƙaunata basu taɓa banbantani da ƴaƴan cikinsu ba,
haka kuma sunyimin karamcin da a rayuwa Bazan taɓa iya biyasu da kamarsa ba koda Raina
zan bayar ya zama fansa a garesu!! se'a yanzu nake ganin tarin wautar dana Aikata Gamida
butulci me girma akan Gudan Jinin Abba da har na kasa Fahimtar damuwar Yaya Khabeer a
kaina!!
Umaisa tacigaba Da cewa "A halin yanzu ji nake gabaɗaya komai ya tsayamin cak, banida wani
buri wanda ya wuce insan Halinda Yaya khabeer yake ciki Ruman!!! Ta faɗa tareda fashewa da
wani irin kuka me taɓa rai.
Kasa magana Rumana tayi haka kuma ta kasa rarrashinta, a halin yanzu bazata iya misalta irin
abinda takeji a Zuciyarta ba gameda Umaisan, shin haushinta ya kamata taji kokuma Uzirin ya
kamata tayi mata? Miƙewa tayi tabar ɗakin zuciyarta gaba ɗaya babu daɗi, sam bataso ta tsani
Umaisa akan dalilin da Ko itace a matsayin umaisan iyakar abinda zatayi kenan, ɗan Adam
yana da ikon daze sarrafa rayuwarsa amma da zarar ƙaddara ta kunno kai dole ne kayi haƙuri
da canzawar wasu al'amuran, Dole ne kawai suyi haƙuri da abinda ƙaddarar tazo dashi na
Auren Umaisa da wanin yaya Golden. A haka ta faɗa ɗakinta Tana aikin zancen zuci tareda
murza keyy A ƙofar ɗakin ta faɗa gaɗo.
*_ƁANGAREN_* umaisa kuwa daƙyar ta iya miƙewa ta fito daga ɗakinta, zuciyarta na mata
wani irin nauyi wanda ta kasa gane ma'anarsa balle tasan dalilin wanzuwarsa, a hankali take
ɗaga ƙafafunta tana takawa harta samu nasarar isa ƙofar part ɗin Khabeer ɗin, da sallama ta
shiga perlourn, tsayawa tayi cak sabida yanda ƙwayar idanunsu ta sarke cikin na juna, sun jima
suna kallon junna kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarsa a gameda abokin gamin nasa,
itace ta fara yin ƙasa da idanunta sabida yanda taci karoda tsantsar tsagwaron zallar sonta da
kuma narkakkiyar ƙaunarta a cikin ƙwayar idon yaya Golden ɗin! Karo na farko kenan a
rayuwarta dataji cewar ta tsani kanta, haka kuma bata cika ƴar Halak ba tunda har ta kasa
sakawa ɗan mutumin daya Raineta tamkar ƴar cikinsa da soyayyarta a lokacin dayafi kowa
buƙatarta , tabbas ita Ɗan adamce kuma butulu haka kuma wada ta kasa mayarda alkairi da
kirki amma ta cike gurbinsa da Butulci, Zubewa tayi a ƙasa lokaci guda kuma ta saki wani
marayan kuka wanda yafi kamada na tsantsar dana sani Da nadama mara misaltuwa!!
Murmushi Khabeer ya sakin mata wanda yafi kamada na ƙarfin hali sannan ya Tako zuwa
gareta, a hankali ya durƙusa dab da ita tareda shanye duk wata damuwa dake kan fuskarsa
yace "haba ƴar Amaryan ƙanwata Kuma ƴar gaban goshin Abbah, meyasa kike kuka irin haka?
You have to know that we care for you so much dear, be kamata kiyi kuka ba a halin yanzu
your Dady is with you and Yaya Golden, ya faɗa yana nuna ƙirjinsa da babban yatsan hannunsa
na dama, fuskarsa kuma ɗauke da wani ƙayataccen murmushi me ɗaukeda son bata ƙarfin
gwiwa,
Ƙuri tayi masa tana kallonsa, ɗaga mata kai yayi ta tareda faɗin "Come on Amaryan mu taso
mana, ya faɗa cikeda rarrashi, amma a zahiri danne zuciyarsa kawai yakeyi sabida harga Allah
baya ƙaunar zubar hawayenta kokaɗan, a duk lokacin da take kuka ji yake tamkar ana zuba
masa narkakkiyar dalma a cikin zuciyarsa.
miƙewa tayi tsaye sannan ya nuna mata ɗaya daga cikin kujerun perlourn yace "zauna.
ba musu ta zauna system ɗinsa ya koma ɗaki ya ɗauko sannan ya fito ya zauna daga ɗan nesa
da ita kaɗan, amma ta yanda zata iya ganin Icon ɗin system ɗin, wani adireshin yanar gizo na
ƙasar Tourkey Ya shiga nan da nan wasu rantsatsun hotunan kayan ɗakin na Royal chair's ne
ƴan gaske Masu azabar kyau kala-kala suka baiyana a jikin Icon na computer ɗin, Murmushi ya
saki wanda har seda beauty point ɗin gefan fuskarsa na dama ya lotsa sosai sannan ya kalleta
yace "Oya zoki zaɓi wanda kikeso, a cikin nan.
narai-narai tayi da ido zatamai kuka ya haɗe rai yace "wai ina wasa dake ne dazaki sani agaba
kinamin kuka? Ki sakko ki zaɓa nace bawai ki tsaya kinamin kuka ba, jikinta a mace ta sakko
ƙasa tareda matsawa inda yake tana kallon kyau da tsari irinna kayan, kallonsa tayi amma
setaga idanunsa Yafi karkata akan pic ɗin farko, drower ce me kyau bana wasa ba, hakama
gadon shima, sam fuskar gadon ba irin ƙatuwar nan bane amma an tsarata bisa tsari inda akayi
musu yarfen silver da Kuma ruwan zinare, haka kawai setaji zuciyarta tafi karkata ga wannan
hoton dataga yana kallo, tabbas tasan birgeshi sukayi shiyasa ma yake kallonsu, idonta a cike
tab da ƙwalla tasa hannunta akan hoton batareda tayi magana ba.
Shiru yaɗanyi kimanin 3mins sannan yace "da kyau amma kin iya zaɓe, nan da nan ya shiga
tura musu kuɗaɗen kayan zuwa Asusun Companyn, seda ya gama tsab sannan taga farashin
kuɗin kayan har kimanin Million 3 iya gado da kujeru kawai,
faɗawa tayi jikinsa a ranta tana mai girmama sanin ya kamata da kuma karamci irinna yaya
Golden, dukda cewar taƙishi ta zaɓi wani Akansabamma sam hakan besa ya canza komaiba a
tareda ita, koda ace yanzu zataga mahaifinta batajin ze iya nuna mata so samada wanda
Ahalin Alhaji Mahmoud Muhammad sukayi mata.
haɗe Rai yayi sannan ya kalleta yace "ɗagani malama, So nawa zan faɗa miki cewar ki ɗena
faɗomin a jiki?karfa ki manta cewar nifa ba muharraminki bane sabida bana cikin jerin waƴanda
Shari'a ta yarda kiyiwa hakan,
Cikin kuka da sarƙewar murya tace "amma ai kai yayana ne!
Murmushi yayi mata me kyau sannan ya kaleta yace "tabbas ko duniya zata tashi hakan baze
canza matsayinki na ƙanwa a gareni ba, sabida keɗin ƙanwata ce Umaisa.
sautin kukanta ta ƙara sabida bata da wani zaɓin daya wuce tayi kukan a halin yanzu,
murmushi ya sakeyi sannan yace "oya tashi kije ki kwanda dare yayi yanzu har kusan 12:00am
pa
Kasa miƙewa tayi don haka ta kalleshi tace "don girman Allah ya Khabeer kayi haƙuri , wllh ba
laifina bane ƙaddara ce tazo da hakan amma na tabb...... "Tashi ki tafi kije ki kwanta pls,
Khabeer ya katseta a hanzarce.
miƙewa tayi jiki ba ƙwari ta fice daga ɗakin ta koma nata zuciyarta sam babu daɗi, zama tayi a
bakin gadonta ta haɗa uban tagumi sekace wadda uwarta ta mutu, ta daɗe a zaune tana aikin
wahalar da ƙwaƙwalwarta (tunani) ganin datayi hakan baze wani amfaneta bane yasa ta miƙe ta
ɗauro Alwala ta fara gabatar da nafilfili tareda Miƙa dukkan lamarinta ga Allah, tareda rowaƙawa
yaya Golden mata ta gari wadda tafita komai a rayuwa, bayan ta gama kwarara masa addu'ar
ne ta fara roƙawa kanta da Ahalin Alhaji mahmoud muhammad alkhairin duniya da kuma lahira
sabida ɗimbin karamcinsu gareta, se wajen ƙarfe biyun dare wani wahalallen bacci ya
kwasheta,
washe gari da sanyi safiya Abba yayi tattaki da kansa har ɗakin Mamie, inda ya sameta a zaune
bisa dadduma tana tasbihi ga Ubangijin dukkan halittu (Allah) kallo ɗaya zakayi mata kasan
bata cikin kwanciyar hankali, gaba ɗaya idanunta sun koɗe sabida damuwar data sakawa
kanta.
zama Abba yayi a kan ɗaya daga cikin kujerun perlourn wanda take facing ɗin fuskar Mamien
sannan ya fara magana cikeda dattako kamar haka "Badi'atou kada ki butulcewa Allah mana
akan ni'imar dayayi miki, ya baki miji tsahon lokaci batareda wayonki ko dabarar ki ba, amma
kuma a ƙarshe seya juya akalar Rayuwarki daga wata zuwa wata, ya kuma azurtaki da juna
biyu wanda a zahiri zamu iya cewa shine makullin ƙofar ƙaddararki har yazama silar haɗuwata
dake,
"Ashe wannan kaɗai be isa ya zame miki ishara a gameda Rayuwa ba?
tunda har kika iya karɓar ƙaddararki ta farko wadda tafi wannan zafi da ƙunci wannan ce bazaki
iya karɓaba Badi'atou?
a matsayina na mijinki ina me baki shawarar cewa karki yarda kiyiwa ɗiyarki mugun furici akan
aureta sabida ina jiye miki tsoron karki aikata kuskure irinna Mahaifinki Badi'ah!! A yanda na
ɗauki kaina ga Umaisa ni Mahaifine kuma me ƙaunar iyalinsa, Allah ya Azurtani da rainon
umaisa har hakan ya zama Rauni na sabida son da nake mata a Rayuwa, wllh ko ƴaƴan cikina
bana yi musu irin son da nakewa Mamana (Umaisa) ban sani ba ko hakan yanada nasaba da
tarin tausayin yarinyar danakeji ne.
"Badi'atou duk yanda kikeso Khabeer ya Auri Umaisa baki kaini son afkuwar hakan ba, amma
kuma se gashi abinda ƙaddara tazo dashi yasa na ɗauki hanun ƴata na miƙashi ga wani a
sanadiyar sonda take masa, ko kaɗan ban kasance uba me son kansa ga Ahalina ba shiyasa
na barta ta Auri Wanda takeso sabida nagartar iyayensa da kuma ta yaron (Maheer), amma
kuma ban sani ba kozaki nuna min iko ne akan Auren Umaisa dana daurane yasa kika kasa
yarda da hukuncin dana yanke akanta sabida bani na haifeta ba!!!
Da sauri Mamie ta ɗago jajayen idanunta wanda hawaye suketa faman yimata zarya tunda
Abba ya fara maganar girgiza kanta kawai take tana kallon fuskar Abba daƙyar ta iya buɗe
bakinta tace " wllh ko kaɗan ba haka bane Alhaji! Taya zan iya aiyana hakan balle har bakina ya
furta wannan mummunar kalmar a gareka? Wllh sam ba haka bane ko giyar wake nasha bazan
taɓa faɗar hakan ba, ai Umaisa ɗiyarka ce ba tawaba na daɗe da sanar dakai hakan, don haka
duk hukuncin daka zartar akanta wllh na amince dashi Allah kuma ya sanya mata dukkan
alkhairinsa a cikin Aurenta da mijinta!
Murmushi jin daɗi Abba ya saki sannan yayi mata ƴan nasihu a gameda haƙuri dukda cewar
yasan tanada haƙurin, a haka Rayuwar gidan tacigaba da tafiya babu walwala kamar shekarun
baya, Sedai ko wannanesu yayi imani da ƙaddaran da Allah ya aiko musu, sedai sam yanzu
Umaisa bata iya sakewa kamar da a cikin ƴan uwnta, wasu lokutan khabeer ne da kansa yake
sawa su usman da farouk suyita janta da hira har su dinga kaita yawo wai duk dan ta saki jikinta
dasu su koma kamar da.
Yau ta kama Asabar ne, wanda yayi daidai da ranar komawar Baba Gano, sosai ta jaɗasu a
babban perlourn Abba dukansu tayitayi musu nasiha akan Haƙuri da rayuwa, musamman ma
khabeer da Ummie inda ta nuna musu cewar Sam karsu taɓa bari wannan al'amarin Daya faru
ya taɓa zaman lfyansu da juna, suyi haƙuri su manta da komai, nan suka amsa mata cikeda
girmamawa, nan aka cigaba da wasa da dariya a tsakaninta da jikokinta maza, kafinta tafi haka
ta dinga jan Umaisa da tsokana har seda ta saki jikinta kamar da sannan tayi sallama dasu
driver ya ɗauketa zuwa kanon Dabo.
*_ƁANGAREN MAHEER KUWA_,* sosai hankalinsa ya kwanta ya ƙara wani irin haske fiyeda
yanda yake a da, komai na rayuwa yana tafiyar masa yanda yakeso tamkar ba maheer ɗin da
Ya haɗu da jarrabawa ba, wani irin son umaisa yakeji a kowace daƙika na rayuwarsa Yana ratsa
gaboɓin jikinsa, sometimes har mamakin kansa yakeyi akan irin muguwr ƙaunar dayakewa
yarinyar, tunda yake a rayuwarsa betaɓa jin yanayiwa wani mahaluki irin sonda yake mata ba
idan aka cire momy da Dadynsa (iyayensa)
wani kyakkyawan murmushi ya saki wanda ya ƙarawa fuskarsa kyau gamida kwarjini tareda
zaro wayarsa ƙirar Samsung ya shiga kiran matar tasa (Umaisa) bugu biyu aka amsa kiran
cikin wata baƙuwar murya me tarin amo a cikinta wadda ya tabbatar da cewar bata Queen
ɗinsa bace. Shiru yayi kamar bazece komaiba, don haka Ruman tayi murmushi me sauti tace
"kayi haƙuri surukina amaryan tana sallah ne amma da zarar ta idar zata kiraka.
se'a lokacin Maheer ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya batareda yace mata ƙalaba ya
kashe wayar sabida tsabar miskilanci irin nasa,
Tana idarwa Rumana ta miƙa mata wayar tana murmushi tace "wannna angon naki wllh seke
Umaisa gabaɗaya bashida sakin jiki da mutane muskilancinsa yayi masa yawa ta yanda har a
wayama yi yake, niko zanso na ganshi a zahiri ta yanda zan samu damar nazartar halayensa
gaba ɗaya.
Dariya Umaisa tayi sannan tace "tabdi lallaikuwa a kwai tarin aiki a gabanki indai har halaiyar
Maheer zaki nazarta. Shiru sukayi sabida ƙarar wayar data gauraye ɗakin, tin kafin Umaisa ta
amsa wayar Ruman tayi ta kanta tabar ɗakin, sabida a cewarta wai masoya suna buƙatar sirri a
tsakaninsu (ba irinsu MOMYN FADYL ƴan sa Eyes ba)
A nitse ta amsa wayar da sallamah, wata uwar ajiyar zuciya ya sauke sekace irin yaron dayaci
kuka ya godewa Allah ɗinnan, nan sukaci gaba da hirarsu me cikeda wani Irin sirri a cikinta
wanda ni kaina na kasa nazarta shauƙin dake taredasu balle harna fassarashi, wata irin
shaƙuwace a tsakaninsu me wuyar misali balle har ayi kintacenta. Umheer kenan Maƙura a
gurin shaƙuwa da kuma nuna ƙaunarsu ga juna❤
Maheer yay shiru sannan yace " Queen kinsan wani irin so nake miki kuwa?
Queen kinsan yanda nakeji a gamedake kuwa?
Da sauri ta girgiza kanta tamkar yana kallonta tace "a'a!
Murmushi yayi me sauti sannan yace "wani irin sihirtaccen so nake miki wanda bazan iya
ta'allaƙashi da so ba sedai kawai in kirashi da ƙauna, wllh ƙaunar danake miki a cikin jinina take
yawo tayanda ma nakeji cewar I can't express it to anyone, nikaɗai nasan menakeji a zuciyata a
gamedake, abinda na sani kawai *KE ALHERICE* a rayuwa ta kamar yanda *MALIKHA MALIK*
ta zama a cikin Rayuwar *ACP SALEEM KHABEER KUMO,* jikin Umaisa ne yay masifar sanyi
don haka ta gyara zama tace " Jaan waye kuma *Acp Saleem Khabeer kumo?*
Murmushi ya sakeyi kamar tana kallonsa sannan yace "wani abokina ne wanda ya gina rayuwar
aurensa akan ƙudirin fansa akan wata matashiyar yarinya mejida kuɗi gamida izzah, sabida
kawai ta mareshi akan wani banzan ƙudiri nata, a ƙarshe kuma reshe ya juyeda mujiya
Dariya sosai Umaisa tayi sannan tace "amma naji daɗi daya faɗa tarkon malikha, amma
gaskiya nikam zanso jin ƙarshen labarin *MALIKHA MALIK da ACP SALEEM KUMO,*
murmushi maherr yayi sannan yace to Queen ki nemi *JAMEELAH UMAR JANAF* na tabbata
tanada cikakken labarin seta siyar miki ki karanta kiji meya faru a tsakanin rayuwar mutum biyu
*(Saleem da Malikha)* Saleem da kansa ya yarjewa janaf ɗin kan cewar ta rubuta labarinsu
daga farko har ƙarshe ta yanda ze yaɗu a duniya kamar yanda labarin *MUZAFFAR DA