Showing 63001 words to 66000 words out of 80273 words

Chapter 22 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2755


RABI'ATOU* ya zagaya duniya a cikin littafin *(BAFULATANA)*

Shiru tayi tana sauraronsa a hankali ta buɗe baki tace " JAAN!! ashe ka iya bada labari irin
haka?

murmushi yayi mata sannan yace "na iya bayarwa amma wa kekaɗai kawai Queen.

Murmushi sukayi gaba ɗayansu sannan sukayi sallama da juna inda Maheer ya alƙawaranta
mata cewar gobe zezo ya ganta da yardan Allah sannan kuma zatayi masa jagora zuwa cikin
gidansu danya gaisa dasu Ummie da kuma Mamienta.

sosai tayi farin ciki da maganarsa ta ƙarshe dayace zezo ya gaidasu Ummie, sabida a
Rayuwarta tana masifar martaba Ahalinta, a haka sukai sallama da juna cikeda tsantsar ƙauna
gamida Aminci.

_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:41_

___________ Bayan Maheer ya kammala wayar miƙewa yayi ya shiga cikin gida zuciyarsa
fess, yareda ƙudutawa kansa cewar gobe dole ne ya gaiyaci Abokinsa Mujaheed maƙocinsu
Umaisa yayi masa rakiya zuwa cikin gidan surukan nasa dan baze iya zuwa shikaɗai ba, a
perlour ya sami Abdul sanye cikin wasu Ash colour ɗin kayan spot irin masu dogon wandon nan
kunnensa a manne da wayarsa ƙirar iphone, taɓe baki Maheer yayi tareda sakin masa duka a
saman kafaɗarsa na dama, kwaɓe fuska Abdul yayi kamar zeyi kuka yace "waiyyo Dadaji kinga
wannan angon me saurin hannu ko?

Dariya yayar mahaifin nasu tayi daga cikin wayar sannan tace banishi mu gaisa da maheer ɗin,
ba musu Abdul ya miƙa masa wayar se faman cuna baki yake tareda susa inda Maheer ɗin ya
dakeshi.

Cikeda girmamawa maheer ya shiga gaida Dadaji, da sakin fuskarta ta amsa gaisuwan tareda
yi masa jajen abinda ya faru a kwanakin baya, shafa kansa yayi yana murmushi a lokacin data
tambayeshi ina Umaisa Amarya? Shiru yayi ya kasa bata amsa sabida wata irin kunyarta
dayakeji, a haka sukai sallama ya jefawa Abdul wayanshi,
Kallonsa Abdul yayi sannan yace "ya Maheer when zaka kaini naga Auntyna ne don Allah?

Batareda Maher ɗin ya kalleshi ba yace "se sanda ta tare a gidana tukunna zaka ganta. Zaro
ido Abdul yayi sannan ya dawo kusa da maheer ɗin yace "oh nagane muninta ne yayi yawa
shiyasa bakaso na ganta dan karna ma dariya ko? Whatever koma yayane tayi sa'a tunda har
ta samu nasarar Auren sadaukin yayana, ƴa faɗa yana yatsina fuska kamar wani ɗan yaro.
Hararar shi maher yayi sannan yace "ai wllh Queen tafika kyau nesa ba kusaba yaro, idanma
kana ganin wasa nake ai wata rana zakanta kaida kanka zaka fahimci she's so cute wllh. "Oho
dai inba tsoroba a kaini in ganta gobe mana, inyaso se'a gwada a tsakanin nida ita, Abdul ya
katseshi ta hanyar faɗar hakan,
Murmushi yayi wanda ya ƙarama fuskanshi kyau yace "nika dameni wllh da yawan surutunka
boy dama nasan nace Dady ya tisaka ku tafi yolan tare kaidasu Baffa Giɗaɗo.

Tabe baki Abdul yayi sannan yace "oho ɗai nasan dannace nafi waccan matan naka kyaune
yasa kace na dameka, ai kaima kasan gaskiya kafin a samu handsome kamana se'an shirya,
inba tsoroba kabari inyi wanka nashafa powder muje a gwada ma...... Nifoshi maher yayi a
sikwane yana faɗin tunda kai ɗan daudu ne ai senaji, da wani mugun gudu Abdul yabar
perlourn yana dariya.

Washe gari kamar yanda Maher ya sanar da Umaisa zuwansa, don haka ƙarfe huɗu da rabi ya
faɗa toilet yayi wanka, haka kawai yakejin zuciyarsa cikin wani irin yanayi wanda ya kasance
baƙone a gareshi, a gaggauce ya kammala shirinsa ya fito perlour yana gyara zaman hular
dake kansa, a perlourn sukayi kaciɓus da Abdul yana gyara zaman Agogon Rolex ɗin dake
hannunsa, idan ka kalleshi seka rantse ba wannan Abdussalam ɗin bane Rainon Maheer
Lamiɗo, sosai kamalarsa da haibarsa suka baiyana tamkar ba yaro ɗan shekara 21 ba, sanye
yake cikin wata brown ɗin shadda anyi mata ɗinkin jampa, sosai kayan ya karɓeshi tareda
fito.da ainihin skin colour dinsa (launin fatarsa).

wani irin kallon Mamaki Maheer kebin Abdul ɗin dashi wanda yafi kamada na mamaki yace "kai
where are you going too naga kanata wani gyare-gyaran wristwatch eh?

Taɓe baki Abdul yayi da irin salonda maheer ɗin yayi tambayar sannan yace" i don't know but
I'm going to somewhere to see my brother wife Umaisa.

Wata uwar dariya maheer yayi sannan yace " your not serious boy, amma ina tabbatar maka da
cewan ba inda zani dakai sedai ka nima wanda zakabi bani ba, murmushin Rashin damuwa
Abdul yayi sannan yace "oh nagane tsoro kakeji kada kaje dani ta gane nafika kyau ?? Kaga
yaya Maheer karka damu ai ban shafa powder ba bazataga kyauna sosai b..... Kasan Allah
barani dakaiba seka zauna a gida kaita kallon kyan naka mumuna kawai.

Kwaɓe fuska Abdul yayi kamar zeyi kuka yace "im so sorry yaya heer amma nidai kam sena
bika naga my Aunty, dariya yaso yabama maherr ɗin dan haka ya kama hannunsa suka fice
zuwa parking lot, wannan black Range Rover ɗin na maheer suka shiga, nan da nan lawan me
gadi ya wangale musu get suka fice daga gidan suka ɗauki hanyar Zone E Apo Legislative
Quarters. a bakin ƙofar gidansu Mujaheed sukai perking kallon maheer Abdul yayi sannan
yace " amma dai ya Maheer ba shiga zamuyi ba ko? Wllh nasan muka shiga se mamansu ya
mujaheed tace na ƙara girma tasa wannan yarinyar me kan kwakwa ta raina ni.

dariya maheer yayi me sauti sannan yace"ai ba ƙarya tayi ba har yanzu kai yaro ne kuma
shagwaɓaɓɓe ma kuwa, haɗe rai Abdul yayi batareda ya qara cewa komai ba sabida haushi, a
haka mujaheed ɗin ya ƙaraso ya wajen motar shaheeda na biye a bayansa, da sauri Abdul yayi
ƙasan sit ɗin motar dan karta ganshi, shi'a dole karta rainashi, har bakin motar ta ƙaraso kanta
a lulluɓe da wani siririn mayafi wanda ya baiyana tsintsiyar wuyanta waje, dukda kasancewarta
ƴar 17years tanada gogewa da kuma shegen wayon tsiya, da gaiya maheer ya sauke glass ɗin
ɓangaren ɗa Abdul yake, zaro ido mujaheed yayi sannan yace "kai wa nake gani kamar Maheer

boy?

Da sauri shaheed ta matso jikin motar sosai ta leƙa wata irin dariya ta saki tareda tafa hannu
tace " lah yaya maaheer wannan ɗan lukutin ƙanin naka mara ƙarfin nan ne ya zama babban
saurayi haka ?

Wani malolon takaici ne ya tsayawa Abdul a wuya, a ransa yace "wannan shegiyan yarinyan
batada mantuwa, amma a fili kuma seya dake yaƙi cewa komai shi'a dole ze tsare gida�,

Bece mata ƙala ba harta gam asurutunta tabar gurin, shidai mujaheed da maheer babu abinda
suke se dariya, nan da nan Maheer ya cinna kan motar zuwa ƙofar gidansu Umaisan,
wangalemusu get ɗin Me gadin yayi Sannan suka kunna kai zuwa ciki, a nitse yayi perking
motar zuciyarsa fess gamida ɗaukin son ganin Habibiyar tasa, yau komai nasa na musamman
ne hatta adon daya ɗauka abin kallo ne ga kowa, abinka da kyakkyawan mutum kuma farin
fata, sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda gizna Ash colour (Ruwan toka)anyi mata ɗinkin
Muhammed,

Sosai kayan ya karɓi dirarren jikinsa yayi masa ɗas tamkar tare aka halicci jikin da kayan, hular
dake kansa se faman ƙyalli take tana yararin tsada, a takaice dai da ka ganshi kaga ango,
wayarsa ya zaro ya fara ƙoƙarin kiran Umaisan danya sanar da ita zuwansu, cikin sa'a kuwa
bugu ɗaya ta amsa da sallamah, wata Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya sanar da ita
zuwan nasu,

Murmushi tayi sannan Tace "ina zuwa gani nan fitowa 2mints pls,

A nitse suka sauko daga motar kowa tsab dashi suna jiran fitowar tasa, cikin mintunan da
bazasu haza 3 ba khabeer ya fito daga Cikin gidan cikin shigar manya kaya waƴanda suka
fitarda kwarjininsa Da kuma haibarsa, kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci yayi Rama sosai
tamkar wanda ya shekara yana ciwo, sosai fuskarsa tayi wani irin fayau da ita sabida saisayen
sajen dake fuskarsa da akayi wanda ya ƙarawa fuskar nashi kyau,

Kallo ɗaya yayiwa maheer ya ganeshi sabida har duniya ta tashi baze taɓa manta mamallakin
fuskar nan ba, cikin wani irin salo na yarda da kai khabeer ya danne zuciyarsa ya nufo inda su
maheer ɗin ke tsaye da wani irin murmushi a kwance akan fuskarsa yace " barka da zuwa
surikina, tareda miƙa masa hannu, murmushi maherr yayi sannan yace " Dr.!!
Nan khabeer suka shiga gaisawa dasu abdul da kuma Mujaheed shida kansa yayi musu jagora
zuwa wani ƙayataccen perlour wanda aka tanada dan baƙi na musamman.

Seda suka ɗan taɓa hira kaɗan sannan Khabeer yayi musu sallama ya fitah sabida a kwai
abinda zeje ya gabatar a Hospital ansu.

Cikin min tuna kaɗan Rumana ta shigo perlourn hannunta a ɗauke da wani babban faranti

wanda aka cikashi da kayan motsa baki, sanye take cikin wata Royal blue ɗin jallabiya wadda
tayi matiƙar karɓan jikinta, bakinta ɗauke da sallama Gaba ɗayansu kallon ƙofar suke tareda
answer sallama ɗin nata ko wanne da murmushi a fuskarsa saɓanin maherr wanda keta faman
latsa-latsen wayarsa, a haka harta ƙaraso inda suke ta ajiye farantin, da sakin fuƙa tace "lah ya
Mujaheed hardakai a rakiyar angon namu?

Dariya mujaheeda yayi sannan yace Rumana yayar Amaryar maheer se'a lokacin Maherr ya
ɗago ya kalleta a time ɗin da ita kuma Ruman ɗin ke kallon Abdul suna gaisawa, cikin sa'a
kuwa tana juyowa suka haɗa ido da maheer wanda shima ita ɗin yake kallo, da sauri tayi ƙasa
da idanunta sabida wani irin mugun kwarjini dayayi mata a ido, a daburce tace "in....ina yi..ni?
Da sakin fuska ya amsa mata sannan ya ɗauke idanunsa daga kanta, bata sake cewa komai
ba ta miƙe tabar perlourn da sauri, donta turo musu Umaisan. A ranta kuma tana jinjina
kwarjinin wannan miji na Umaisa, yanzu duk nazarin halaiyarsa datace zatayi sun tashi a banza
kenan? Ajiyar zuciya ta sauke me nauyi sannan zuciyarta tace mata" taya zaki iyayin hakan
bayan gashi tundaga kallon farko da kikayi masa kika kiɗime da kwarjininsa.

a hkaa ta isa perlour ta samu Ummie ta sanarda ita zuwan surukin nasu, murmushi Ummie tayi
sannan tace "masha Allah munayi masa maraba da zuwa tun kafin ya shigo ciki, kiyi sauri ki
shiga ki fito da ita nasanta da shen shirita karta ɓata masa lokaci.

dariya Ruman tayi sannan tace "ummie ai bashi kaɗai yazo ba ma shida abokinsa yaya
Mujaheed sukazo, da kuma wani me kama dashi ina zaton ma ƙaninsa ne.

zaro ido Ummie tayi sannan tace "ke Rumana na rabaki da irin wannan halin ta ina kikasan
ƙaninsa ne bayan bashi ya gaya miki hakan ba?

dariya tayi sannna tace "wllh Ummie bakiga yanda suke kamaba, dana kallesu ma ni na kasa
gane wanda yafi kyau a tsakanin....... "Dalla rufewa mutane baki mamie ta katse Ruman tana
binta da wata Uwar harara tace "tomu ina ruwan mu da kyansa?

Dariya Ummie tayi sannan tace "oh Allah Badi'atou har yanzu baki dena taya ɗan naki kishin
bane ?

shiru tayi bata tankaba ta koma kitchine abinta tana ta faɗa.

dafa Rumana Ummie tayi sannan tace "oya maza kije ki fito da ita nasan tsoron fitowa take
sabida bala'in faɗan Badi'atou.

da sauri Rumana ta nufi ɗakin Umaisan, a zaune ta sameta ta haɗa uban tagumi, kallo ɗaya
zaka mata ka fahimci a tsorace take, dariya Rumana tayi sannan tace "dalla meye haka kin bar
mutane sunata jiranki?

Narai-narai tayi da ido kamar zatayi kuka tace "Ruman tsoro nakeji sabida har yanzu Mamie na
fishi take dani, miƙar da ita Ruman tayi tsaye sannan ta zaunar da ita a gaban mirror ɗin dake
ɗakin, nan da nan ta gyara mata fuskarta ta fito tayi Rass da ita, wata haɗaɗɗiyar jallabiya ta
ɗakko mata wadda abba ya siyo mata a Dubai Maroon colour ta wadda aka ƙawata da fararen
stone's masu masifar haske da ɗaukar ido ta miƙa mata, ba musu ta karɓa ta sanya a jikinta,

sosai tayi kyau kamar a saceta a ɓoye, dayake mayafin rigar yanada ɗan girma sosai Rumana
ce tayi mata Rolling nasa, wow abindai se wanda ya gani abinka da farar mace, takalmi
Rumana ta jawo mata shima flat dashi ta saka sannan taja hannunta suka fita zuwa sit Room
ɗin.
_*KIYARDA DANI...!*_


*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*

*DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaƊo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


*_A yau ina miqa tarin godiyata gareki Sadiya sidi (sidiya the writer of BINAFA) Akhairinki gareni
me girma ne, haka kuna banida bakin dazanyi godiya a gareki SIDIDIN CHUBAƊO, wllh ina
alfahari dake ɗari bisa ɗari don haka na Mallaka miki wannan shafi halak malak har duniya ta
tashi mallakin ki ne sidiya ta�_*
_Page:42_


___________A nitse suke takawa har suka iso ƙofar perlourn hannunta a sarƙe cikin na
Rumana, A haka suka shiga perlourn da sallama ɗauke a bakunansu, tunda suka shigo idon
Maheer nakan Umaisa wata irin ƙaunar ta yakeji tana yawo a jinin jikinsa wadda bayajin ze iya
misaltata,
A haka suka shigo Ruman ta zaunar da ita akan kujerar dake facing angon nata, dariya
Mujaheed yayi sannan yace "lallai Rumana kin iya ɗaurewa ƙauna ƙafa harda wani zaunar da
ita tayanda zasu dinga facing juna?

Murmushi tayi a kunyace sannan tace "a'a yaya mujaheed nidai ba ruwana kawaidai na
sauƙaƙewa angon hanyar daze kalli amaryarshi cikin sauƙine.

Zaro ido Abdul yayi sannan yace "oh nagane kenan ke connecter ce ta masoya?

Dariya sukayi gaba ɗayansu har Maheer ɗin, kallon Umaisa Abdul yayi sannan yace "amma
wannan amaryar kin iya siddabaru, meyasa kika saka kaya kalar nawa? Nidai bari kiji na faɗa
miki duk abinki wadda ta fiki kyau zan Auro sabida nafi mijinki kyau da komai.

Dariya sosai maheer ya keyi kamar ba wannan miskilin matashin ba, ita kanta Umaisa seda ta
ɗago ta saci kallonsa kaɗan sannan ta maida kanta ƙasa, maherr "yace Mujaheed kanajin yaron
nan ko?

Murmushi mujaheed yayi sannan yace "aida gaskiyarsa ko ƙanina ? Abdul ya ɗaga kai yace
sosai kuwa ya Mj,

Miƙewa Abdul yayi ya canza gurin zamansa sannan ya kalli Umaisa yace " ni bantaɓa ganin
amarya irinki ba wllh se faman sunkuyar da kai kikeyi sekace kazar datake tsoron yanka, kodai
kinajin tsoron ganin fukata ne dan karkiga nafi mijinki kyau ne?

Ɗagowa Umaisa tayi ta saci kallon inda su Maherr suke cikin sa'a kuwa ta fahimci ba ita suke
kallo ba sannan ta ɗago ta kalli Abdul ɗin sosai tace "ina koda wasa mijina yafika kyauda komai,
don haka ka ɗena haɗa kanka da mijana ɗan samari.

Dariyace ta kama kowa dake perlourn ciki kuwa harda Rumana wadda ke gefan Umaisa, shima
kansa Abdul ɗin dariya yakeyi sannan yace " yanzu kam na yarda zaki iya kularmin da yayana
tunda har kika iya mayar min da wannan martanin, a haka hirar ta tashi Abdul na cikasu da
surutu.
A nan Rumana da Umaisa sukayi musu jagora zuwa maine perlourn gidan suna biyeda su a
bayansu, da sallama suka shiga perlourn dikansu hakanne yayi daidai da fitowar Farouq
perlourn shima, kallonsu kawai yakeyi a zuciyarsa yana mamakin ƙannen nasa da kuma yanda
akai har Umaisa ta iya kallame zuciyar wannan koɗaɗɗen mutumin a cewarsa lol, amma kuma
a zahiri seya ɗan saki fuskarsa sabida ganin Mujaheed dayayi a taredasu, hannu ya miƙa musu
suka gaisa sannan ya haye sama zuwa ɗakin Mamah,

A nan ma Abdul beyi shiru ba se faman kwasar Umaisa da Rumana yake kamar wasu
kakanninsa yana dariya, Mamie dake Kitchine tana haɗa Abincin dare duk tana jinsu a Ranta
tace "kai wannan Yaro a kwai shegen surutu sekace kenari.

Cikin mintuna da bazasu kaza 3 ba Ummie ta sakko perlourn sanye cikin wani dogon hijjabi milk
colour, da fara'a kwance a fuskarta wadda take nuna ainihin murnar ganin surukin nasu, a haka
Mama ma ta sakko itama cikin shigar mutunci kamarta Ummie, nan da nan su Maheer suka
zube suna kwasar gaisuwa a wajen surikan nasa wanda yaji har A ransa cewar sun kwanta
masa, Ummie tayi.murmushi tace "Mujaheed yau kaine a gidan namu albarkacin babban

surikinmu ko?

Wata irin kunya Mujaheed yaji sannan yace "wllh Ummie ba haka bane aiyukane kawai sukamin
yawa shiyasa ban samun lokacin ziyara, murmushi Mama tayi sannan tace " yakamata dai a
dinga daurewa ana yin ziyarar yafi.

"insha Allah zan ƙoƙarta Mamah, wai ina Mamie ne ban ganta ba?

miƙewa Ummie tayi tace "tana kitchine barin mata magana.

Ummie na fita Usman yana shigowa hannunsa ɗauke da briefcase ɗinshi inda ɗaya hannun
nasa kuma ya riƙo Rigar saman suite ɗin dashi, kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci a gajiye
yake, a haka ya ƙaraso perlourn da murmushi dukda cewar besan su waye a perlourn ba,
zubewa yayi akan ɗaya daga cikin kujerun perlourn sannan suka shiga gaisawa dasu maheer
ɗin, kallon Mamah Usman yayi sannan yace " Mama sannu da gida baƙi mukayi ne haka?

murmushi Mama tayi sannan tace "ai waƴannan ba baƙi bane ƴaƴa ne, mijin cry-cry ɗin Abbane
yazo gaisuwar surukai.

kallon Umaisa Usman yayi sannan ya miƙe ya nufi inda take zaune ya wani watse mata kunne,
lokaci guda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login