Showing 15001 words to 18000 words out of 80273 words
ya fice daga gidan, Direct perking space ya nufa ya fad'a cikin motarsa, lokaci guda yayi
mata key, tun kafin ya k'araso lawan ya bud'e masa get d'in ya fice,
Cikin mintunan da bazasu gaza 15 ba ya isa gurin, a nitse yay perking sannan ya fito cikin
takunsa me cikeda izzah, a hankali yake takawa harya isa gurin, babu wasu mutane sosai se
wasu matasan "yan mata daketa faman tsalle tsalle, wayarsa ya d'auko tareda k'ok'arin kiran
Mujaheed d'in sabida yaji inda yake, hakanne yay daidai da fad'owar Ice Cream d'in dake
hannunta a jikin bak'in wandon dake jikinsa, a fisace ya juyo ya fara bin jikinsa da kallo, wani
irin tafasa yaji zuciyarsa tanayi, lokaci guda ya aiyana cewar tabbas babu abinda ze hanashi
shukawa yarinyar nan mari, a fisace ya juyo dan yaga wace shafaffiya da man ce ta zuba mishi
Ice Cream a jikinsa haka....!!!!
Comment
Nd
Share
*_Zm CHuBaDo_*
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:10_
___________í ½í³– dunk'ulewa tayi da sauri sabida yanda ta tsorata dashi, hannunta tasa ta kare
fuskarta idanun a cike tab da k'walla, bakinta banda rawa babu abinda yakeyi, da k'yar ta iya
bud'e baki tace "d...an gir..man Allah ka k..ayi hak'uri wllh ban saniba na zuba maka, ta k'are
maganar tareda fashewa da wani irin kuka,
Sosai abin ya k'ara bashi haushi, cikeda b'acin rai ya sunkuya dab da fuskarta yace " dilla
malama rufewa mutane baki idiot!!
Wani malolon takaici ne ya tsaya mata a wuya, harya mik'e ze tafi cikin kuka tace" karka sake
kirana da idiot, sabida niba ita bace, ta fad'a tareda turo d'an k'aramin lips dinta gaba, tsayawa
yayi cak, lokaci guda kuma ya juyo gareta tareda zuba mata manyan idanunsa masu matik'ar
haske gamida jan hankalin duk wani me kallonsa, shiru yayi yana kallon yanda taketa motsa
baki tanayi masa k'unk'uni, lokaci guda murmushi yay Escaping lips d'insa, wanda iya kacinsa
labbansa,
A fusace a k'aso gareta tamkar mayunwacin zakin dayay arba da abinci, da sauri Nusaiba dake
tsaye ta ranta a nakare sabida gaba daya ita mutumin ma tsoro yake bata, sunkuyawa yay dab
da fiskarta, cikeda zafin nama yasa hannu ya dank'e lips d'in data turo mai, zuciyarsa fal
mugunta ya matse mata shi da k'arfi ta yanda har seda ta saki wani sabon kukan na azaba,
wani miskililin murmushi ya saki tareda datse lips d'insa da hak'oransa sannan yace" dan kin
samu na barki shine kike tunani har kinada zarafin dazaki zageni na k'yaleki haka? K'ara matsa
bakin yayi cikeda mugunta sannan ya fisge mayafin datayi Rolling dashi, hakanne yay
sanadiyar baiyanar doguwar kalban dake kanta, sautin kukanta ta k'ara sabida azabar da lips
d'in nata sukeyi mata, gashi kuma ya hanata damar dazata bashi hak'uri,
Ice cream d'in data zuba masa ya shiga gogewa da mayafin abayar nata, seda ya gama
gogewa tsaf sannan ya jefa mata mayafin a fiskarta ya mik'e tareda nunata da yatsansa na
dama yace " idan kika sake bari wannan mummunar fiskar taki nayi ido biyu da ita koda kuwa a
inane wllh senayi miki rashin mutuncin dayafi wannan Idiot ya k'are maganar tareda watsa mata
ragowar Ice Cream d'in dake cikin robar, kuka ta fashe dashi zuciyarta nayi mata zafi, tanaji
tana gani yabar gurin batareda ya sake waigenta ba, khalil ne ya k'araso gurin shida Nusaiba,
a haka suka sameta ita kad'ai a gurin tana kukan bak'in ciki da takaici, abinka da farar mace tuni
bakinta yay wani irin ja gamida kumburi, sabida tsabar matsar dayasha a hannun Maheer,
Cikeda takaici Khalik ya juya ga Nusaiba yace "uban waye yayi mata haka amma bakije kin
sanar dani akan lokaci ba harya bar gurin? Muzurai Nusaiba ta fara sabida ganin yanayin yayan
nata, kamar zatayi kuka tace " wllh ya khalil nima bansanshi ba, muna wasa ne fa shine ta
zuba masa Ice cream bata sani ba shine fa yayi mata haka..! Ta k'are maganar tana matsa ido
cikeda tsoro,
Ita dai Umaisa banda kuka babu abinda takeyi, gefe na zuciyarta kuma a cike yake taf da tsoron
Maheer, koya ta rintse idanunta maheer take gani tareda jiyo sautin kashedin daya suburbud'a
mata a kunnenta,
Kasa magana tayi dan haka da suri ta mike tareda barin gurin tana aikin kuka, sosai Khalil
yakejin sautin kuka a saman zuciyarsa, tareda d'inbun takaici rashin ganin wanda ya aikata
mata hakan, a haka suka mara mata baya shida Nusaiba, a mota suka sameta ta had'e kai da
gwiwa tana gurzar kuka.
Kasa ce mata komai Khalil yayi illa key dayayiwa motar sukabar parck d'in zuciyarsu a dagule,
tunda suka fara tafiya bata d'agoba har seda suka iso Zone E sannan ta bud'e idon ta, cikeda
k'warewa Khalil ya danna hancin motar zuwa cikin get d'in legislative Quaters d'in, tafiya kad'an
sukayi sannan suka iso bakin makeken gidandu Umaisan, bud'e k'ofar tayi zata fita ba tareda
tace da kowa komaiba sema share hawayen dake bin fiskarta datakeyi, da sauri Nusaiba itama
ta bud'e murfin motar ta fito, kusan a tare suka tura k'ofar Get d'in, babu kowa a farfajiyar gidan
se ya Khabeer da wani Friend d'in sa Hashim, cikeda gimamawa suka gaishesu sannan suka
kunna kai zuwa maine perlourn gidan, a nan suka samu mamie da kuma Ummie wadda keta
faman magana a waya, da alama da mamansu Beebah takeyi, katse wayar tayi tayeda cewa
"zan turo su Ruman da driver su kawo miki insha Allah.
Zuba musu ido mamie tayi, hakama ummie aka rasa wanda zeyi magana sabida ganin yanda
bakin Umaisan ya kunbuwa kamar wacce aka gabzawa naushi,
Nusaiba ce tayi k'arfin halin katse shirun ta hanyar gaishesu, ummie ce ta amsa tareda
tambayarta abinda ya faruda Umaisan, ko kad'an bata b'oye musu komaiba duk abinda ya faru
a tsakanin Maheer da Umaisa seda ta gaya musu, sosai ran Ummie ya b'aci da abinda Maheer
yayiwa Umaisan, dan haka ta dinga sirfa fad'a kamar ta ari baki, ita dai mamie tab'e baki tayi
tana binsu da kallo, sabida ita harga Allah bataga laifin yaron ba sema na Umaisan, dan haka ta
mik'e tayi sama tabarsu a perlourn Ummie tana ta sirfa fad'a kamar wadda taga Maheer d'in a
gabanta, ita dai Nusaiba sallama tayiwa Ummie ta kama gabanta kamar wata munafuka haka ta
fice abinta.
Hannunta Ummie ta kama suka nufi room d'in ta sannan ta dakko wani balm ta shafa mata a
bakin sannan tace tahau gado ta kwanta, tana kwanciya kuwa baccin wahala yay awon gaba
da ita.
_Afwan yau ban samu tim bane shiyasa banyi dayawa ba,í ½í¹_
Comment
Nd
Share
*Zm (CHuBaDo)*
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Fatima Aliyu badamasi, ni zm chubado naga saqonki haka kuma nayi farin ciki sosai da irin
soyayyar da kikeyi min, sedai ina roqonki wata alfarma pls kada ki sakeyin irin abubda kikayi
akaina, indai har son da kikemin na gaskiya ne, ni zm chubado nima sonki fisabilillahâ¤_
_Page: 11_
___________í ½í³– A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah, haka rayuwar gidan Alhaji Nasir
lamid'o ta sauya, komai idan za'a gabatar seda sanin Hajiya Murja kokuma amincewarta, komai
na gidan ya dagule hakama al'amuran Companynsa, a yanzu kwata-kwata bashida katab'us
akan komai se'abinda Murja ta zartar, wannan dalilin ne yasa wasu daga cikin ma'aikatansa
suka ajiye aikinsu, sabida bazasu iya jurar wulak'anci ba,
Shidai Abdul baya iya cewa komai, dukkan abinda suka ga dama shi sukeyi a gidan, wasu
lokutan ma haka zata tara mata da maza a gidan suyita rashin mutunci, amma bashida damar
dazeyi magana saidai kallo, idan abin ya isheshi ne ma seya saka takalmansa ya d'auki keys
din motarsa yabar musu gidan har zuwa lokacin da zasu gama,
Binta 'yar kwabo kuwa idan ka ganta a yanzu seka rantse itama matar gidan ce, sabida yanda
take cin karanta babu babbaka, abinda taga dama shi takeyi sabida yanda Hajiya Murja ta
lamunce mata yin hakan, shikuwa uban gaiyar bashida tacewa sunan dai yana gidan ne amma
bashida maraba da hoto,
Hatta 'yan uwansa dake yola bama ya zancen su, tun suna kiransa a waya baya d'auja har ya
gaji yayi blocking d'insu, sannan ya sanar da masu gadinsa cewar duk wanda yazo nemansa
muddin daga yola yake karsu kuskura su barshi ya shigar masa gida,
Wannan shine dalilin dayasa su Baffa Ibrahim suka janye jikinsu daga lamarin Alhaji Nasir
lamid'o, sedai su kansu sunaji a jikinsu cewar a kwai abinda yake damun d'an uwan nasu dan
haka suka yanke shawarar zasu tayashi da addu'a akan dukkan abinda yake damun sa,
Kusan kullum se Abdul ya gwada kiran wayar Maheer amma kuma kullum kalma d'aya ake
maimata masa itace *swich off*, sosai hakan yake k'ara d'aga masa hankali sabida rashin
sanin ainihin halinda yayan nasa yake ciki, wasu lokutan sedai yayta kuka yana rok'on Allah ya
kawo musu d'auki a cikin wannan babban Al'amarin da suke ciki,
Binta 'yar kwabo ce zaune a kan makeken daining d'in dake perlourn, sanye take cikin wani
d'anyen leshi wanda aka k'awatashi da d'inki na alfarma, gefanta kuma wasu manyan mata ne
kokuma ma ince hajiyoyin bariki, kowacce se faman taunar cigam sukeyi, kallo d'aya zakayi
musu ka fahimci cikakkun 'yan Bariki ne na ajin farko, duba da yanayin fuskokinsu yanda sukaci
uban bleeching kamar sun k'one, hirar su kawai sukeyi suna shewa sekace a gidan karuwai.
Hajiya bintace tayi murmushi tace "hajiya sa'a wai yaushe zaki tafi Dubai d'inne? Wadda aka
kirada Hajiya sa'a tace " wllh k'awata ni yanzu duk tafiye tafiyan nan isheni, ina ganin wani
Alhajin zan samu na aura ko nima na samu hankalina ya kwanta waje d'aya.
Wani irin kallo suka dinga binta dashi, wanda yafi kamada na mamaki, tabe bak'i Binta tayi
sannan tace " Amma dai wllh Hajiya sa'a kin tabbata sakarai muddin kika Auri babban mutum a
wannan shekarun nakin, ina laifin ma ki samu k'aramin yaro sabon jini ki Aura, wanda ze mayar
dake cikakkiyar mace a gado, sannan kuma ku more Rayuwarku dashi,
Karaf Hajiya Asiya ta cafe tace " wllh 'yar kwabo kamar kin shiga raina, ni kaina burina kenan in
samu yaro shakaf in Aure, sannan in sangarta shi da kudi ta yanda zamuji dadin rayuwa dashi,
kinga daga nan semuci duniyar mu da tsinke. Tafawa sukayi sannan suka shek'e da dariya,
Hajiya sa'a tace "wllh mutanan nan bakuda dama, toni da kun barni ai tsoho zan kwasowa
kaina, dariyar suka kuma kwashewa da ita, suna tsaka da dariyar ne Abdul ya turo k'ofar
perlourn,
Da wani irin mayen kallo Hajiya sa'a da Hajiya Asiya suke binsa dashi sekace wasu tsofaffin
mayu, ko wacce da abinda take sak'awa a ranta a gameda Abdul d'in, batare da yace dasu
k'alaba yay wucewar sa, sabida kaf cikinsu bega wadda takai ya gaisheta ba. A ransa ya
k'udurtawa kansa cewar seya d'auki mataki akan wannan shaid'ancin dayake shirin kutso musu
cikin gidan su.
Muje zuwa
*Comment*
*Nd*
*Share*
*Zm chubado*
_*í ¼í¾€KIYARDA DANI...!í ¼í¾€*_
í ¼í¾€í ½í°¾í ¼í¾€
*♟ƖŊTÒ¼ÉÉÆ–ƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSÉ·í ½í³šâœ*
*í ½í²«DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:12_
__________í ½í³– a haka yabar perlourn yana tunanin ta yanda ze b'illowa lamarin, hajiya sa'a ce
ta kalli Binta 'yar kwabo tace "k'awata wannan yaron kuma fa daga ina? Murmushi Binta tayi
sannan tayi fari da idanunta tace " d'an me gidannan ne wllh sunansa Abdussalam, shine ma
k'arami, shegun yara haka suke da masifar kyau, wai dan ma bakiga yayansa Maheer ba wllh
yafi Abdul kyau nesa ma ba kusa ba, kama suke da ubansu, garama Abdul yafi kama da
uwarsa, idan kika ganta seki rantse ba *BAFULATANA* bace sabida tsabar kyanta.
murmushi suka saki sannan Hajiya Asiya tace " kai gaskiya Hajiya Binta ina kamun wannan
d'an beautyn yaron, kin ganshifa santalele dashi, wllh daga ganinsa zeyi abin kirki ta k'are
maganar tareda wani d'an iskan murmushi akan fuskarta, tab'e baki Hajiya Binta tayi sannan
tace "hmm kuma kunsan dai wannan yaron baku isheshi kallo ba, balle ma a kai ga maganar
Aure, indai har kinaso kuga komai ya tafi yanda ake so tofa sekun fito da kud'i ta k'are maganar
tana kallonsu with serious face.
*GARIN ABUJA*
Tundaga ranar da Umaisa sukaje silver ved, bata sake tunanin kuma fita ba, yau ta kama Friday
ne dan haka suka shirya cikin wasu riga da sket na atamfa itada Rumana, inada mamie ta
shirya Ameerah cikin wasu riga wando 'yan kanti k'irar *_Companyn Herjireenash_* hakama
takalmin k'afarta wanda ya kasance bak'i wuluk, kallo d'aya zakayiwa Umaisa ka Fahimci bata
son fita, kawai dan ba yanda zatayi ne, Ummie ce ta kalleta tace " saura kuma wllh kije kiyi
musu iskancin da kika sabayi a gida, kinsan dai halin Beebah sarai, dama maryam tana gidan
ne toda banja miki kunne ba, tunda ita tana iya jurewa rawar kanki. turo baki Umaisa tayi
sannan tace " uhmm to Ummie ai idan ma Aunty maryam bata nan ai Momynsu tana gidan,
base na zauna tareda ita ba kafin ya Golden d'in yazo d'aukar mu ba. Shiru Ummie tayi tana
kallonta, ita dai Mamah kallonsu kawai takeyi tana murmushi kamar bazata ce komai ba se
kuma can tace "to tunda basa shiri da Beebah meyasa bazaki tura Ruman da Ameerah kawai.
Ta k'are maganar cikeda son jin ta bakin Umaisa,
Washe baki Umaisa tayi wanda tun fitowarta daga d'akinta ta had'e rai sabida a rayuwarta ta
tsani zuwa gidansu Beebah, komawa tayi kusa da mama sannan tace " yauwa Mamah na dama
kedai kike fahimtar uzirina indai akan maganar gidansu Aunty Beebah ne, dan Allah ki fahimtar
da matar nan kozata fahimce ni, ta fad'a kamar zatayi kuka. Sakin baki Ummie tayi sannan
ta kalleta tace " dan uwarki nice matar? Ta fad'a tana k'ok'arin dank'o ta, da sauri ta shige bayan
Mama tana dariya a haka mamie ta sakko ta samesu, murmushi kawai tayi sabida tasan
diramar Umaisa da Ummie, 'yar k'aramar jakar goyon dake hannunta ta mik'awa Ruman sannan
tace "gashi nan duk abinda 'yata zata buk'ata na saka mata a ciki, saura kuma ku saka min ita
kuka tunda kunga Uwarta bata tareda ku, ta k'are maganar tana kallon fiskar Ameerahn, dariya
dukansu suka saki a haka Khabeer ya shigo perlourn fuskarsa babu yabo babu fallasa, sanye
yake cikin wata skey blue d'in shadda anyi mata d'inkin jamfa, wadda ta baiyana cikar zatinsa
da kuma haibarsa, k'afarsa sanye take cikin wani bakin takalmin fata wanda ya baiyana
zarazaran dogayen yatsun k'afarsa, dukda cewar be sanya hula a kansa ba, hakan be hanashi
yin kyau ba,
Seda ya sake gaida iyayen nasa a karo na biyu sannan yay musu sallama ya fice daga
perlourn, kallonsu Mamah tayi sannan tace " jira kukeyi se ance muku ku bishi sannan zaku
bishi ko kuma yaya?
Tab'e baki mamie tayi sannan tace "ki k'yalesu indai khabeer ne ai yana daidai da iskancinsu,
tana kaiwa nan ta kama step tayi sama abinta, da sauri suka mara masa baya hannunsu sark'e
dana Ameerah wadda keta murna za'aje da ita gidansu Aunty Beebah. A haka suka cin masa
zaune cikin bak'ar motarsa k'irar *formatic*
Bud'e motar sukayi Umaisa ta shiga gaban motar Ruman da Ameerah kuma suka shiga baya,
motar yayiwa key sannan mai gadi ya bud'e musu Get suka fice daga gidan suka d'auki hanyar
Wuse 2, a bakin wani makeken gida tsaya tareda yin horne, cikin mintuna kad'an aka bud'e
musu get din,
Hancin motar khabeer ya danna zuwa cikin gidan, tun kafin suyi perking suka hango Beebah a
tsaye a harabar gidan ta cab'a uban ado sekace wadda zata zab'en sarauniyar kyau, a nitse ya
k'arasa yay parking wanda hakan yay daidai da k'arasowar ta gurin, se faman shan k'amshi
take tana zuba yauk'i, shikuwa uban gaiyar se faman basarwa yake shi'a dole beson raini,
Rumana ce ta fara bud'e murfin motar ta fito sannan khabeer ma ta bud'e side d'insa ba tareda
ya fito ba, itako Umaisa banda zunb'urar baki babu abinda takeyi, cikeda gimamawa Ruman ta
kalli Beebah tace Aunty Beebah ina yini? Cikeda sakin fiska tace "ina gajiya Ruman ya kike?
A tak'aice tace lfy lau. Daga haka bata sake ce mata komai ba ta kama hannun Ameerah suka
nufi maine perlourn gidan,
Se'a lokacin Beebah ta mayar da kallonta ga Khabeer tace "yadai na ganka haka kamar baka
farin ciki da ganina? Tab'e baki yayi sannan ya kalleta kimanin mintuna kad'an sannan yace " ke
a garin ku haka ake karb'an bak'o ba gaisuwa sedai a tareshi da surutun banza?