Showing 6001 words to 9000 words out of 80273 words
kan wayar , amsawa yayi tareda yin sallama, murmushi Umaisa tayi sannan ta amsa
sallamar Abban nata tace "Abbaba ya office?
Da kulawa Abba yace " office Alhamdulillah my daughter ya gajiyar school?
Shiru tayi tareda yin narai narai da ido kamar zatayi kuka tace "pls Abbana ka dawo da wuri yau
don Allah..!! Ta fad'a tareda fashewa da wani irin kuka,! gigicewa Abba yayi lokaci guda
tareda da fad'in " Doughter meya sameki haka kike kuka? Waya tab'amin ke?
Sassauta kukan tayi sannan tace" ba kowa Abba kawai ina missing naka ne Abbana!
Rarrashinta Abbah ya dingayi sannan ya samu tayi shiru, seda ya tabbatar ta dena kukan
sannan ya kashe wayar murmushi kwance a kan fiskarsa yace, "huh doughter sarkin Rigima.
Tunda ya khabeer ya fita da sanyin safiya, be dawo gida ba har yamma ta kawo kai, abin
mamaki har ya Farouk ya dawo amma shiru Khabeer be dawo ba, shirun da Ummie taga yayi
yawane yasa ta fara k'ok'arin kiran wayarsa dan taji ko lfy, hakanne yayi daidai da da shigowar
Khabeer d'in, cikeda damuwa Ummie ta kalleshi tace "Babana lfy kuwa yau najika shiru?
Murmushi yayi sannan yace " Ummie wllh aiki ne yayi min yawa a Hospital shiyasa ban dawo
da wuri ba, ya fad'a yana kwance agogon fatar dake d'aure a tsintsiyar hannunsa,
murmushi Ummie tayi tareda shafa kan d'an nata cikeda soyayya tace " masha Allah son Allah
ubangiji yayi jagora maza ka k'arasa side d'inka kayi wanka ka huta zansa Ruman ta kawo
maka abinci, tab'e baki yayi sannan yace "no Ummie ba saita kawo ba ma naci abinci a office,
ya fad'a tareda mik'wa yabar perlourn. Murmushi kawai Ummie tayi tareda girgiza kai.
*GARIN KADUNA, ANGUWAN RIMI.*
*Hajiya Murja* ce a zaune bisa k'ayataccen perlournta, wanda aka k'awatashi da dukkan kayan
alatu na alfarma sanye take cikin wata dakakkiyar shadda gizna, anyi mata irin d'inki sinigalist
wanda yay matik'ar karbar jikinta, hannayensa sanye suke cikin wani murd'add'en warwarayen
zunare wayanda suketa d'aukar idanu,,
gefanta wata siririyar Matace wadda ake kiranta da suna, *Hajiya Binta 'yar kwabo* hajiya
Binta 'yar kwabo aminiyar Hajiya murja ce sosai tun suna 'yan mata suke tare, Auren da Hajiya
Murja tayine ya fara gina musu gatanga a tsakaninsu, lokacin da Hajiya Murja ta auri *Alhaji
Nasir Lamid'o* wannan shine dalilin dayasa Hajiya Murja tabar Unguwar kusfa dake Zaria, aka
kaita gidan mijinta dake Kaduna,
Duk da haka Amintar tasu bata Rabuba, musamman ma da Binta ta k'yalla ido taga irin tarin
dukiyar da mijin Aminiyar tata yake dashi, kullum Binta 'yar kwabo tana tafe a hanyar Kaduna,
ko tsoron titi ma ba tayi, yanzu da abin yay tsamari ma Hajiya Binta kwaso kayanta tayi gaba
d'aya daga Zaria ta koma Kaduna gidan Alhaji Nasir Lamid'o da zama,
Bayan ta dawo Kaduna da kwana sati biyu Alhaji Nasir Lamid'o ya dawo daga London, koda
yayi arba da Hajiya Binta sosai ransa ya b'aci da ganin ta a cikin gidansa , dan haka ya kira
Hajiya Murja yace "maza maza ki gaya mata ta tattara komatsanta ta barmin gidana, dan wllh
bazan amince da zaman wannnan matar a gidanan ba..!
Sosai Hajiya Murja ta tada fitina a gidan kan cewar wllh Binta babu inda zataje, idan kuwa ya
sake cewa Binta tabar masa gidansa to wllh sedai su tattara su tafi tare, wannan Shine dalilin
dayasa Alhaji Nasir Lamid'o ya haqura ya zuba musu ido,
Alhaji Naseer Lamid'o shahararren d'an kasuwa ne, wanda yayi fice a fanin kasuwanci daban
daban, shiyasa ya mallaki kamfanoni da dama, tun daga kan kamfanin takalma har zuwa
kamfanin k'erek'eran ababan hawa daban daban. Duk wannan tarin dukiyar da Alhaji Naseer
Lamid'o yake da ita, yara biyu Allah ya bashi a cikin wannan duniyar, Babban Shine ake kira da
Maheer k'aramin kuma Abdussalam, suna kiransa da suna Abdul.
Maheer kyakkyawa ne ajin farko duk inda namiji me kyau da cikar halitta yake gamida cikar zati
yakai tofa Maheer ya wuce nan, fiskarsa a zagaye take wadda a turance ake mata lak'abi da
(Roud face) yana d'auke da manyan idanu ma'abota haske gamida d'aukar hankali,
Maheer ba ma'abocin magana bane, haka kuma bashida sakin fuska ko kad'an, idan har kaga
dariyarsa toda k'aninsa Abdul ne.
Maheer yanada wata irin d'abi'a wacce a yanzu ta zame masa jiki dukda kasancewarta bame
kyau ba, wannan dabi'a bata komai bace ta shaye shaye, kai duk wani nau'i na abin maye
maheer yana shansa, musamman idan ransa ya b'aci, sedai duk irin shaye shayen da maheer
yakeyi abin mamakin Shine baya neman mata ko kad'an,
Babban abinda ze bawa me karatu mamaki Shine, a Rayuwar Maheer ya tsani mata, sabida a
cewarsa wai gaba d'aya mata 'yan bin zak'i ne, haka kuma duk tinaninsu d'ya ne, suna da son
kansu sosai, mace guda d'ayace a Rayuwarsa wadda ze iya fada'ar alkhairin ta....
Maheer yana da zafin Rai sosai gamida Rashin son Raini, siyasa gaba d'ya basa shiri da
matar mahaifinsa wato Hajiya Murja, ya tsaneta matik'ar tsana shiyasa ma take bala'in
shakkarsa
Tofa wannan Shine Maheer Lamid'o yaro d'an gata me matik'ar jida kudi gamida Izzah.
*CIGABAN LABARI*
Hajiya Binta ta kalli Hajiya Murja tace " k'awata wllh wannan tak'adirin d'an naki ni tsoro ma
yake bani, shege d'azu saura kad'an ya bangajeni, ni wllh gani ma nake anya kuwa ze barki ki
ida nufinki a kan Mahaifinsa?
_Comment_
_Nd_
_Share_
*Zm muhmd*
*(CHuBaD'o)*
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page: 5_
__________Cikeda damuwa Hajiya Murja tace "wllh kedai bari kawai, nikaina shegeb yaronnan
ya gama tsayamin a Rai d'an iska! ni abinda yafi damuna ma wllh baya tsoron uban kowa,
idanfa yace zeyi abu wllh ko ubansa be isa ya hanashi ba, balle kuma ni karan kad'a miya, ta
fad'a tana kallon idon binta 'yar kwabo.
Wata uwar harara Binta ta watsawa k'awar tata sannan tace "Amma wllh kin ban kunya da har
kika bari al'amarin Maheer ya tsaya miki a Rai haka batareda kin d'auki wani babban mataki a
kansa ba, kinga malama kawai kud'i zaki fito dashi a tura Osun state gurin bokan mu yayi mana
aiki akan Shege, kamar yanda yayi mana a kan Ubansa, tayanda zamu dinga juyashi a tafin
hannun mu se yanda mukayi dashi, kinga ai shikenan kin huta da taurin kansa.
Dariya sukayi gaba d'ayansu tareda tafawa,
K'ofar perlourn aka bud'e dan haka suka maida hankalinsu gaba d'aya akan k'ofar perlourn,
Maheer ne ya shigo perlourn cikin takunsa na isa da izzah, sanye yake cikin wata rantsatsiyar
suite wacce ta baiyana ainihin cikar zatinsa gamida haibarsa, ko kallon inda suke beyiba ya
nufi hanyar dazata kaishi d'akin Abdul, gaba d'yansu da ido suka bishi cikeda rashin sanin abin
cewa,
A nitse ya tura k'ofar d'akin tareda kunna kai ciki, a kwance ya samu Abdul d'in dan haka ya
k'arasa kan gadon da sauri ya d'agoshi yana tattab'a jikinsa, yanda yaji jikinsa yayi zafi ne yasa
ya fahimci cewar Abdul d'in bashida lfy, d'agoshi yayi sosai tayanda har suna iya jin numfashin
juna, cikin husky voice d'insa yace" whats wrong with you Dear re you sick?
Ya jefa masa tambayar cikeda kid'imewa, sabida a Rayuwar maheer ya tsani abinda ze taba
masa brothern sa, tun suna yara ma balle yanzu da suka girma,
Abincin dake cikin flacks Abdul ya nuna masa dan haka da sauri Maheer ya sakeshi ya koma
gurin flacks din dan ganin meye a ciki, yana bud'ewa ya kafe abincin da ido yana nazarinsa,
spoon ya d'auka yad'an d'ebi abincin ya zuba a bakinsa, lokaci guda ya furzar da abincin
sabida wani masifaffen yaji daya gauraye bakinsa, nan da nan idanunsa suka canza launi,
cikeda bacin Rai ya dauki flacks din ya nufi kitchine dashi, cikeda bala'i ya fara kwad'awa masu
aikin gidan kira, kafin kace me harsun taru a gabansa, a matik'ar hasale yace "uban waye ya
dafa wannan abincin a cikin ku? Cikeda fargaba gamida tsoro Zaliha tace" nice ranka ya dad'e
dama hajiya ce tace a dafa mata sannan kuma asa yaji sosai,
A fisace ya koma perlourn yana binsu da wani irin d'an iskan kallo irin na Rik'ak'kun mazan nan
yace" malam daga yau karki kuskura kisake sawa a kaiwa Abdul Abinci, idan kuma kika sake
wllh zanyi abinda bana so. Yana kaiwa nan ya juya yabar perlourn zuciyarsa nayi masa zafi,
Wannan shine abinda yake faruwa a gidan Alhaji Nasir Lamid'o.
*********
A gidan Alhaji Mahmoud muhammad kuwa, tin wajen k'arfe 4:00pm na yamma Mamie ta shiga
kitchine dan gabatar da aiyukan dake gabanta, kasancewar duk Ranar litinin Abbah yakanyi
Azumi, shiyasa abin ya zame masa jiki,
Fride Rice Mamie take sonyi dan haka ta fito da duk kayan dazata buk'ata, inda Rumana take
temaka mata wajen wanke kayan lambun da mamien ta fito dasu,
gefe kuma Umaisa ce zaune bisa wata k'aramar kujerar Roba tana had'a coslow wanda yaji
k'wai da kuma Bama, cikin mintuna kad'an ta kammala had'awa sannan ta mik'e ta nufi babban
prizern dake kitchin d'in,
bud'ewa tayi sannan ta d'akko manya manyan kaji guda 3, ta nufi sink dasu, wani madaidaicin
kwanon silver ta d'akko ta zuba kajin a ciki, sannan ta sakar musu ruwa sabida k'ank'arar dake
jikin kajin ta saki. Seda ta tabbatar k'ank'arar ta saki sannan ta shiga wanke naman, seda ta
wanke shi tas sannan ta zuba a tukunya, seda ta hada komai tin daga kan kayan k'amshi har
zuwa kansu magi sannan ta d'ora a kan gas.
Cikin mintuna kad'an suka kammala aikin dake gabansu, Mamie ce ta kalli Rumana tace "
Ruman ki had'awa Abban ku pepe soup d'in kayan ciki sabida naga yana sonsa sosai.
Da sauri Umaisa tace " Mamie aina riga nayi masa tun d'azu kinga ma harna kaimasa shi kan
daining.
Batareda da Mamien ta kalleta ba tace " Da kyau tunda an gama komai se ku tashi kuje ku kai
abincin kan daining d'in sabida magrib ta kawo kai, ana idar da sallah zakuga yayyenku sun
dawo masallaci,
Ameerah ce ta shigo kitchine d'in hannunta Rik'e da Nutri milk duk tabi ta b'ata jikinta dashi,
dariya Rumana tayi sannan ta kama hannun Ameeran tace "hy sweetheart waya baki Nutri milk
kika b'ata jikin ki dashi haka?
Se'a sannan mamie takai kallonta ga Ameerah, salati Mamie ta saki sannan tace " oh Allah na
ni badi'atou wllh Ameerah lamarinki se ke wllh, dubi fa yanda kikayi da jikinki, ta fad'a tana nuna
jikin amiran,
Washe baki Ameerah tayi cikin kwab'abb'iyar hausanta tace " ya Faluk ne a bani kuma cinga
hadda sweet abani, ta fad'a tareda nuna musu jakar Big Bom d'in dake hannunta.
Da sauri Umaisa tace " Rabin Rai zoki bani guda d'aya kinji? Mak'e kafad'a Ameerah tayi
sannan tace "uhmm an baci ba, ni Aunty Ruman jan bawa.
Dariya sukayi gaba d'ayansu sabida yanda Ameeran take magana. Fita Mamie tayi daga
kitchine d'in ta nufi Room d'in ta danyi wanka sannan tayi Sallah. Mamie na fita Ameerah ma ta
nufi hanyar fita, tana ganin Umaisa ta mik'e aiko ta k'arasa ficewa da gudun ta, a zatonta alawar
Umaisan zata karb'ar mata.
Dariya sosai tabawa Umaisa dan haka sukai Murmushi kawai sunabin hanyar data fita da kallo,
mayan womers d'in da mamie ta zuba abincin suka dinga diba suna kaiwa daining, seda suka
jera komai sannan ko wacce ta wuce Room d'in ta danyi wanka da kuma sallah,
Farouq da Usman ne suka fito cikin sauri don tafiya masallaci, sanye suke cikin jallabiyar su
k'irar Emrati, sedai banbancin colour kawai, inda Farouq tasa ta kasance maroon shi kuma
Usman tasa milk colour ce, tafiya suke suna d'an tab'a hira a tsakaninsu, Usman ne ya kalli
Farouq yace" kai nifa yau kwatakwata ban sanya Goldeen a idona ba sam, dayake sunan da
suke kiran khabeer dashi,
Batareda Farouq d'in ya kalli Usman d'in baa yace "wllh bana ce ba ni kaina Rabona dashi tin
safe, kasan yanayin aikin nasa ne se'a hankali.
Suna cikin hirar ne suka hangi Khabeer d'in da Abba sun shiga masallaci, Murmushi sukayi a
tare sannan suka mara masu baya zuwa cikin masallacin suma,
bayan an idar da sallar da jimawa sannan Zaratan mazan suka fito ko wanne da Murmushi akan
kyakkyawar fuskarsa, kafad'unsu Abba ya dafa inda suka sanyashi a tsakiya cikeda tsantsar
k'aunar mahaifin nasu sannan suka nufi hanyar gida,
Tun kafin su shigo gidan k'amshin turaren wuta ya bugi hancinan su, Murmushi Usman yayi
sannan yace " wannan dagaji aikin Aunty Amarya ne, a haka suka shigo gidan fuskokinsu
cikeda annuri,
Da sallama suka shg perlourn, da sakin fuska iyayen nasu suka amsa musu sallamar, daining
d'in suka nufa sannan kowa yaja kujerar ya zauna, Rumana ce ta fara fitowa sannan Umaisa ta
fito, sanye take cikin wata farar riga me fogon hannu, se kuma street siket baki, wanda yay
bal'in karban jikinta,
A haka ta k'araso perlourn fuskarta d'aukeda Murmushi sabida ganin Abban ta, da sauri ta
k'arasa kusa dashi tace Abba sannu da shan Ruwa, cikeda kulawa Abba yace "yauwa my
precious daughter, washe baki tayi sannan tace Abbana nayi maka special pepe soup d'inan
kayan cikin nan da kake so,
Murmushin jin dad'i Abba yayi sannan yace " ngde sosai diyar albarka Allah dai ya baku miji na
gari nayi muku Aure, rufe fuskarta tayi da zarazaran hannanyenta cikeda jin kunya,
Dariya gaba d'aya sukayi amma banda golden daya k'ara had'e girar sama da k'asa, sabida shi
ya tsani yawan surutu a rayuwarsa,
Kallonta Usman yayi sannan yace " to malama pepe soup, dan Allah ki rabu da Abba haka
yasha ruwa, ya k'are maganar yana dariya, chuno masa baki tayi sannan tace "uhm aidai
Abbana ne dai ko,
Dariya Abba da Rumana sukayi sannan ta shiga serving d'in kowa dake daining d'in, sannan ta
zuba nata ta faraci, bata wani ci sosai ba ta mik'e tareda yiwa kowa sallama ta wuce Room nata
sabida tana so ta sakeyin nazari akan littattafanta na makaranta....
_Comment_
_Nd_
_Share_
*Zm Muhmd* *(CHuBaD'o)*
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:6_
___________ duk wannan budurin da Umaisa takeyi ko kad'an hakan besa khabeer ya kalli
inda take ba, hasalima harkan gabansa kawai yakeyi, ita kanta Umaisan kusan hakan ya zame
mata jiki, tun abin yana tsaya mata a rai har ya dena tsaya mata, a haka iyalan suka kammala
Deenar d'in tasu zuciyar kowa a cike da tarin farin ciki,
B'angaran Gidan Alhaji Nasir Lamid'o kuwa, sosai Ran hajiya Murja ya b'aci bisaga abinda
maheer yayi mata akan Abdul, hakanne yasa ta mik'e a fisace ta nufi Room d'inta, cikin
mintunan da bazasu gaza 30 ba ta dawo perlourn hannunta d'auke da bunch d'in dubu dari ta
wurgawa Binta 'yar kwabo tace "gashinan inaso ki turawa Adebayo kud'innan yanzu, sannan ki
shaida masa abinda ya dace yayi akan wannan d'an iskan dayake shiga rayuwata, koma me
zeyi yayi Alhaji ya kori Maheer da kansa yabar gidannan, kuma tafiya ta har abada,,,!! "
murmushin mugunta Binta 'yar kwabo tayi sannan tace" angama K'awata dan haka kawai
kijirani kawai kiga me zanyi a kai, daga yanzu zuwa gobe, ta k'are maganar tana murmushi irin
na marasa imanin nan,
Koda Maheer yabar d'akin Direct Room d'in Abdul ya koma, taimakawa Abdul d'in yayi ya canza
kayan dake jikinsa, sannan suka fito dan zuwa Hospital, a perlour suka wuce su Hajiya Murja
wacce keta faman cika tana batsewa, ko kallonta beyi ba ya kama hannun k'anin nasa suka
fice daga parlourn,
Parking lot suka nufa inda Maheer d'in ya nufi wata had'ad'd'iyar bak'ar venz me shegen kyau,
a nitse ya bud'ewa Abdul d'in front sit, sannan ya koma mazaunin driver, a hankali yayiwa
motar key cike da nutsuwa lokaci guda kuma ya nufi get cikeda k'warewa, horn ya saki me
lafiya, da sauri malam Haruna ya taso ya wangale masa get d'in shikuna ya danna hancin
motar zuwa kan titi, a nitse yake tukun sabida Abdul, jefi jefi yakan yakan kalli k'anin nasa
cikeda tausayin yaron, a hankali wata irin tsanar matar uban nasa ta dinga ratsa masa zuciya,
tabbas dole ne ya d'auki tsatstsauran mataki akan wannan matar, jira yake kawai Dady ya dawo
daga Yola, inyaso se'ai wacce za'ayi a