Showing 1 words to 3000 words out of 83144 words
(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤02¤¤
.
¤Wannan Sadaukar wa ce zuwa ga..... Boss dina, Yaya na, Dan uwa na, Bappa na, wanda
adomin sa na ke nan, Allah ya ba shi sa'a da nasara a komai nasa da sauran en uwa musulmai
gabaki daya...
(MARABAS DAN ANTY) jinjina gare ka.¤
.
Ci gaban labari...
.
Yace; Me zan taho miki dashi? Tana murmushi tace; ''Goba'' Yayi dariya yace; Kedai kam ina ga
sai kin haifi da mai kalar goba...Shikenan sai na iso.
Ya kashe wayar ya dauki makullin motarsa. Yana shirin fita ke nan Basiru masinja ya shigo
ofishin rike da zungureren fayil(file) a hannunsa suka yi kici6us ya rusuna yace:
Yalla6ai ga takardun injinan nan da akayi bonanza daga ofishin peter yace akawo maka kasa
hannu.
Ya kar6i fayil din ya dora akan tebur ya dauki biro yasa hannu(signing) sannan ya mikawa
Basiru. Yana fita yaci karo da Alh. Sammani Sabo. Don haka dole suka koma cikin ofishin, suka
gaisa Alh. Sagir yana dan fara'a yace;
Alh. Sammani jiya nake tunanin na kira ka ban samu sarari ba. Alh. Sammani yayi murmushi
yace; kada ka damu ni gani nazo da kaina. Alh. Sagir ya dan yi shiru na wani lokaci sannan
yace;
Gaskiya nayi tunani mai zurfi naga hakan bazata samu ba, musamman idan nace zan 6ullo da
hakan a kungiya baza a aminta ba, don haka kawai nake ganin mu hakura......
Alh. Sammani ya bugi teburin da hannunsa yana dan murmushi yace; Kada ka damu
Abokina,Aminina ni na san kai masoyi nane ko bayan ba raina zaka iya taimakon iyalina.
Nagode da bayaninka yanzu yaushe ne za a dauka?
Alh. Sagir yace; Eh, to kamar yadda aka soma fada tun can baya. Alh. Sammani ya yunkura
yace; shikenan aminina ba matsala, amma ni zan yi tafiya zuwa Dubai har sai bayan komai ya
kammala zan dawo. Don haka ina neman afuwa ga kowa-da kowa, a kuma kula da ci gaba da
abubuwan da ake yi yadda ya kamata. Alh. Sagir yace; Yauwa aminina nagode kwarai da yadda ka hakura ka sadaukar. Babu komai.
Ya rako shi har bakin kofa, sannan shi kuma ya koma cikin ofis din ya dauko makullunshi daya
ajiye cike da farin ciki ya fito ya tunkari inda suke ajiye motoci.
Ya kusa karasawa kenan yayi tuntu6e da wani 'Kashi ya kife kasa, bisa tsautsayi ya kama aman
jini.
Mutanen dake shawagi a gurin suka ankara da abinda ya faru don haka da sauri suka tunkaro
shi, don kawo masa dauki.
Aman jinin yake kashir6an saboda haka sai ba a tsaya 6ata lokaci ba aka kwashe shi aka nufi
Asibiti dashi. Ko kafin a isa Asibitin ya gala baita sosai, da gaggawa aka shiga dashi Emergency
room.
Alh. Saminu wanda ya jagoranci zuwa Asubitin yayi amfani da wayar Alh. Sagir ya lalubo
lambar Alh. Ahmad ya kira shi. Bugu daya wayar ta shiga. Yana dauka yace; Yane Baban
gobe? Ko an sauka ne? Alh. Saminu yace; Bashi bane Daya daga cikin ma aikatan gidan
gonarsa ne, don Allah ka same mu a NAJNOOR HOSPITAL, Saboda oga yazo hawa mota yayi
tuntu6e ya kama aman jini. Shine muka kawo shi Asibiti. Cikin tashin hankali Alh. Ahmad yace; To gani nan zuwa. Mintin sha biyar a tsakani Alh. Ahmad
ya iso Asibitin. A lokacin suna da damar shiga inda yake saboda an samu aman jinin ya
tsagaita.
Suna shiga suka tarar dashi dik ya yamutse kamanninsa dik sun sauya,tamkar wanda yayi
ciwon shekara. Alh. Ahmad ya matsa kusa dashi yaga idanunsa sunyi jajur kamar jan gauta.
Wani irin siririn haske ne acikin idonshi,sai kace yana saitin hasken kwan lantarki.
Cikin tausayawa Alh. Ahmad yace; sannu Alh. Sagir. Bai iya amsawa ba, sai dai idanu kawai da
ya zuba masa,kai kace wannan shine karo na farko da yayi tozali da shi.....
ada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤03¤¤
Dama baka lafiya ne ko kuwa sanadin tuntu6en ne? Har yanzu bai iya tankawa ba sai Alh.
Saminu ya amshi zancen da cewa; Gaskiya nima ina tunanin bashi da lafiya, domin yaui sukuku
yake a gidan gona,tunda ya shiga ofis dinsa bai fito ba sai da wannan sanadin ya faru.
Alh. Ahmad yace; To Allah ya bashi lafiya? Gaba daya suka amsa Ameen. Sun shafe mintuna
goma babu wanda ya sake magana daga cikinsu. Sai zuwa can Alh. Sagir ya lumshe ido Alh.
Saminu yace; Ina ga ma ya samu bacci.
Alh. Ahmad ya dago kai ya dubi Alh. Sagir, sai ya ga ya bude ido, amma kwayar idon ta sauya
launi ta koma KORE shar, sannan ta koma DORAWA, sai ta koma BAKI. Shikenan ya maida
idon ya rufe.
Gaban Alh. Ahmad ya fadi, bai fahimci abin da ya gani ba, ya dubi Alh. Saminu da sauri yace;
Ku duba ku gani yadda kwayar idonsa ke sauya launi.
Da sauri suka dubi Alh. Sagir amma sai suka ga kwayar idonsa a rufe Alh. Saminu yace ai bacci
yake. Alh. Ahmad ya dunga tunanin anya kuwa bai ga wani al'amari ya faru da dan'uwansa ba?
Amma jin amsar da suka bashi yasa ya share maganar.
Alh. Saminu yace ya kamata a sanar da maidakinsa. Alh. Ahmad yace; Eh ba ma ita kadai ba
harda mahaifanmu. Ya ciro waya yana niyyar doka kira kenan, Alh. Sagir ya mike a firgice ya
dafe kansa da hannunsa guda da ba a dora masa ruwa ba? Alh. Ahmad ya maida wayar a
aljihu ya matso da sauri kusa da dan'uwan shi yana tambayar; Ya jikin? Amma shiru bai tanka
ba daga karshe sai ya koma yaraf! Akan gado. Gaba dayansu suka saka sallallami, daya daga
cikinsu yayi saurin kirawo likita. Ya duba shi ya tabbatar musu da RAI YAYI HALINSA.
Kwalla suka sirnanowa Alh. Ahmad cikin karfin hali ya kirawo mahaifinsu ya shaida masa halin
da ake ciki. Sannan ya kira Alh. Sada shima ya bayyana masa abinda yake faruwa.
Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankalinsu a tashe.
Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankali a tashe, aka gama dik abinda ya dace
sannan aka basu mota (Ambulance) da zata kai musu gawar a gida.
Suka taho,kowannensu cike da wannan jimamin wannan BABBAN RASHIN da sukayi, Saboda
rashin irinsu Alh. Sagir yana da matukar ta6a zuciya.
Jan gwarzo jarumi wanda ya tsayu da kyautatawa na kasa dashi, zai yi wuya talaka ya kawo
kukansa ga Alh. Sagir ba tare da an share masa hawaye ba. Amma duk wannan yakana tasa
bata hana ya amsa kiran mahaliccinmu ba.
Laillai Allah baya barin wani don wani yaji dadi!!! Kuma dik jarumtar rai da nuna hazikanci, dole
ne ta dandani mutuwa.
(Dacin mutuwa mai ta6a zuciyar wadanda aka yi wa komai, ma'ana juriya da jarumta basu isa
su hana rai dandanar mutuwa ba, yayin da suka rasa wani nasu)
mu samman ma Alh. Sagir da ya zamto tamkar shugaba a wannan tsatso, saboda yapi kowa
kudi a cikinsu.
.
(ALLAH YA JIKAN MARUBUCIYAR WANNAN LITTAPIN YA GAFARTA MATA DA SAURAN
MUSULMAI BAKI DAYA AMEEN)
.
Ci gaban labari...
KADDARA TA RIGA FATA Haj. Karimatu tana zaune a falo Haj Asmo ta shigo dauke da faranti
a hannunta, fuskarta kunshe da fara'a tace; Yau dai ina sauke hakkin da ya rataya a wuyana.
Haj karima tayi murmushe tace; uhm kaji manyan masu gida, don anyi min sanwa shine ake
koda kai? To dama kin bari domin ba gwaninta kikayi ba tunda ba ci zanyi ba shi dai na karfen
ya dawo yaci. Haj Asmo ta zauna a gefenta tace ke kin isa? Ai bazan wahala a banza ba. Haj
Karima tace ; Ko yanzu ba kiyi wahalar banza ba,tunda dan'uwanki zai dawo,kinga kin
hutashshe dani. Tace wlh kuwa ke nifa yau tinda na tashi nake jin gabana na faduwa komai ba
yayi min dadi,hatta yawun bakina daci yake min. Ga shi dan da yake cikina yana ta yamutsamin
'ya'yan hanji. Haj Asmo ta danyi murmushi tace; To ko dai haihuwar ta zone? Don dama naga
cikin naki yayi kasa sosai. Haj Karima tayi murmushi ita ma tace; Wai ita mai tsohon ciki babu
wani ciwo ko damuwa da zata shiga sai dole nakuda? Ni fa wallahi tsoro ma nake kada na zo
haihuwar nan na wuce. Haj Asmo tace; Ai haihuwa ba mutuwa bace ke dai Allah ya sauke ki
lapiya, amma ki daure kici abincin nan zama da yunwa yana azabtar da mai ciki. Haj Karima
tace; Bazaki gane me nake nufi ba, sam ba na jin yunwa kuma bana iya kai komai a bakina. Ke
dai kici kawai ba ra na shiga daga ciki. Haj Asmo ta dan harare ta, ta wutsiyar ido tace; Ke dai
ko wayo kike so ki yi min ki shiga daki ki haihu sai dai na jiyo kukan jariri? Dariya Haj Karima
tayi tace; A'a wallahi kinga ma na fasa shiga dakin shike nan? Za tayi magana suka ji karar
tsayuwar mota Haj karima tace; Ina ga ma gashi nan ya iso. Haj Asmo tace mai yuwuwa bashi
kadai bane naji kamar karar tsayuwar motoci ne ba daya ba. Tace kila shi da Abokanensa ne
Kafin su gama tantancewa Alh. Sada ya danno kanshi cikin falon fuskarshi babu annuri suka
amsa sallamarsa. Haj Asmo ta dora da cewa: Ai naje gidanka baka nan shine na wuto nan kafin
anjima na koma. A takaice yace; Ai gwara ma da kika zo nan din. Ya dubi Haj Karima yace ina
makullin sitroom? Kafin ta bashi amsa sai da suka kalli juna ita da Haj Asmo sannan daga
bisani tace; Yana daki, yace kawo min. Zata tambayeshi ya daga mata hannu yace: Hanzarta
ana jirana a waje. Haj Asmo jikinta yayi sanyi ta dubi Haj. Karima tace; Ko ki fada min inda yake
sai na dauko, tace; yana kan dressing mirror. Haj Asmo ta nufi dakin a hanzarce ta dauko
makullin sitroom ta kawo masa. Ya kar6a ya fice ba tare da yayi musu bayanin komai ba. Sai da
aka shigo da gawar Alh Sagir tukunna Alh Rabi'u ya shigo falon. Ga ninshi da suka yi gabansu
ya tsananta faduwa, tabbas ya nuna musu akwai wani al'amari da yake faruwa sai dai basu san
ta ina abin yake ba. Suka durkushe su duka biyun suna gaishe da shi. Bayan ya daidaita zaman
shi akan kujera ya amsa musu ya dubi Haj Karima murya a taushe irin ta dattako yace.....
.
.
Gaskiya ban gane canzawar idanuwan sa ba!!!
Se ku cigaba da biyo mu, dan jin yanda za a kaya.......
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤04¤¤
.
''Karima ina so ki sani Allah shiya halicce mu ba ya barin wani don wani kuma dikkan rai bata
wuce wa'adinta. Allah yayi wa mijinki rasuwa!!!! Yana sitroom ki taso ki masa wanka don a
sadar dashi da gidansa na gaskiya. Wasu taurari ta gani suna walainiya acikin idonta. Da sauri
ta runtse idonta tana tunanin mafarki ne take amma koda ta bude idon sai ta ga dattijon surukin
tsohon nata a zaune, wannan ke nuni da KADDARA TA RIGA FATA! Abinda kunnuwanta suka
jiye mata tabbas haka yake babu tababa. Yayin da Haj Asmo ta fashe da wani irin rikitaccen
kuka su duka biyun suka mike da sauri cikin faduwar gaba suka tinkari sitroom din. Suna isa
suka ga gawar shi a shimfede a kasa an lullu6e shi da sauri Haj karima ta kai hannunta ta yaye
mayafin da aka rufe mamacin idanuwanta suka yi tozali da jarumin mijinta ai bata san lokacin
da ta kurma kara ba. Ta zube kasa sumammiya. Gaba dayansu hankalinsu ya dugunzuma ya
tashi suka nufe ta suna sallallammi. Ba a jinkirta ba aka kwasheta zuwa asibiti ana tunanin ita
ma rai yayi halinsa. Lokacin da ta farfado daga sumanta ta farka ne tana ambaton sunan
mijinta. Haj Asmo dake gefenta ta shiga rarrashinta da tausasan kalamai. Ta rirrike zanin da
yake shimfide a saman gadon da ta ke kwance tana wani irin madodawa, Likita ya shigo yana
dubata yayi mata allura sannan ya dubi Haj Asmo yace; Haihuwace zata yi zamu kaita dakin
masu haihuwa. Haj Asmo tace shikenan Allah ya raba su lafiya. Aka mayar da Haj Karima dakin
'yan haihuwa sai dai ta jigata sosai kafin ta haihu. Ta haifo 'yarta mace santaleliya son kowa kin
wanda ya rasa. Haj Asmo tana zane da ita a dakin hutu rungume da jaririyar yayin da mai jegon
take sharar baccin gajiya. Su Alh. Ahnad suka shigo ta sanar dasu an sauka suka yi godiya ga
Allah da ya rabata da cikin lafiya. Haj Asmo tace har an rufo yayan? Alh. Sada yace Eh, Tace to
Allah ya jikansa ya kuma raya bayansa. Su duka suka amsa da Ameen. Misalin karfe tara na
dare Haj Karima ta farka da sauri Haj Asmo ta jawo kula ta zuba mata farfesu sannanb ta hada
mata ruwan shayi mai kauri ta matso kusa da ita. Tashi kisha wannan don ki samu karfin jikinki.
Tsananin yunwar data ke ji ne yasa ta kar6a tasha. Sai a lokacin ne ta lura babu cikin da ke
jikinta. Sam hankalinta bai kai ga jinjirar dake rungume a hannun Haj Asmo ba ta soma kuka.
Haj Asmo ta shiga rarrashinta Haj karima tace; Shima cikin nawa ya zube koh? Haj Asmo ta
mika mata jinjirar dake hannun ta tace; Bai zubeba ga abinda kika haifa 'ya mace ce. Ta dubi
jinjirar fara sol da ita kyakkyawa idanuwanta hancinta girarta dik na uwarta ne yankan bakinta
da tsawon ga6a ne kawai na mahaifinta. Tsotasar hannu kawai take tamkar me shan nono Haj
Asmo ta ga bata da niyyar kar6ar yar ta girgiza kai tace; Kar6eta ki bata nono muga zata kama
saboda tin da ta zo duniya ambata madara taki sha sai tsotsar hannu take gasi kuma ga dukkan
alamu yunwa take ji. Ai ta jigata da yawa Allah ma ya auna arziki da rabon zata rayu. A hankali
ta miko hannu zata kar6eta amma sai ta kasa Haj Asmo tace; Bari na daura miki ita a jiki ki bata
ta sha. Naga ba kya iya daukarta ma ko? Ta karashe maganar tana kokarin dora mata 'yar ajiki.
Ana kuwa saka mata kan nonon a baki ta kama zuko shi? Haj Karima ta kama cije le6e saboda
yadda jinjirar take jawo ruwan nonon da karfi. Ji take tamkar zata tsinke mata shi. Haj Asmo ta
lura da hakan tace; Daure saboda yana sabo ne data saba ruwan nonon yazo sosai zaki daina
jin zafin. Da kyar ta daure 'yar ta sha ya ishe ta ta 6ingire da bacci Haj Asmo ta dauke ta ta
kwantar cikin gadonta sannan ta juyo kan Haj karima tana kuma lallaminta. Washe gari 'yan
uwa da abokan arziki suka yi ta zuwa ganin jaririya da yiwa Haj karima gaisuwar mijinta. Ita dai
kallonsu kawai take zuciyarta cike da radadin rashin data yi. Hakika tayi babban rashi a tsawon
shekaru shiddan da suka yi da maigidan nata dai-dai da rana daya basu ta6a samun sa6ani ba.
Kullum cikin tattali da nuna mata kauna yake. Ya koyar da ita matsanancin sonsa ta yadda ko
wata unguwa yaje wadda zai kwana take samun kanta cikin kadaici. To yau gashi mai rabawa ta
raba(Mutuwa) dole ne tayi kuka kuka kuwa mai ciwo, wanda baya da magani illa HAKURI da
DANGANA. Kwananta biyu a asibiti aka sallame ta an so a sallame ta a washe garin data haihu
to amma kasancewar tana fama da rashin afuwar jiki dole tasa aka jinkirta sai data kwana biyu.
Ana sallamar ta kai tsaye gidanta aka zarce da ita 'yan uwa sai rarrashinta ake yi ana dannar
zuciyarta don haka ta dan samu saukin zafin rashin da tayi.
Ranar daren suna Alh Sada yazo gidan da daddare ya same ta yana tambayarta tana da za6in
sunan da za a sakawa yarinyar? Kuka ta kamayi sai da ya rarrashe ta tayi shiru sannan tace;
Marigayi ya ta6a cewa idan mace na haifa SHUHUDA za a Saka mata . Idan kuma namiji ne
JAMILU. Alh Sada yace Shikenan za a saka mata Shuhudan sannan munyanke shawarar zaki zauna
anan gidan ki shayar da yarki har zuwa lokacin da Allah zai fito miki da miji ki yi Aure.
Ba ta iya ce mishi komai ba amma ita a zuciyarta bata tunanin zata iya auren wani namiji anan
gaba saboda da kyar ne ta samu wanda yake sonta kamar yadda mijinta yake sonta ba.
An yi taron suna da sadakar bakwai sai dai taron sunan babu armashi kamar yadda suka ci buri
idan an haihu za a yi. Sai dai wani abu daya daurewa kowa kai shine; TSOTSAR HANNU da
Shuhuda ke yi. Idan tana kwance aikin kenan haka idan wani ya dauke ta abin dake raba ta da
tsotsar hannu to kuwa sai idan mahgaifiyar ta tana bata nono ne. Ga shi yadda take tsotsar hannu abin ya wuce misali tsotsa take yi da karfi kamar me tsotsar
nono. Goggo Zuwai kanwar mahaifiyar Haj Karima ita ta zauna a gidan kasancewar mijinta ya
rasu kuma yayanta dik mata ne suna ma'auri.
Tana matukar kokarinta wajen ganin ta korewa Haj Karima damuwa ba laifi ana samun yadda
ake so Haj karima ta rungumi kaddararta hannu biyu tana yawaita aikawa mijinta addu'o'in
samun haske da rahamar Ubangiji a kabarinsa.
.
Tafiya sannu-sannu kwana nesa har aka samu tsayin shekar guda shuhuda tayi wayo sosai har
tafiya ma tana dan ta6awa saboda ta tashi da kazarniya.
Zuwa wannan lokacin zawarawa sun yiwa Haj Karima caa yawancinsu duk abokanan mijinta ne
sai dai babu wanda ta ke kulawa har yanzu tana kewar mijinta. Dangin mijinta sun yi maya
halacci domin suna matukar kula da ita babu mai son ya ganta cikin damuwa sun rungume ta
tamkar ita ce tasu ba mai rasuwar ba. Tana matukar jindadin haka ko dama can farko aurensu da mai rasuwar sun nuna mata kauna
kaunar ce ma har yanzu take bibiyarta. Ranar laraba da daddare misalin karfe takwas Haj
karima da Goggo zuwai suna zaune a falo bayan sun gama sallar isha'i suna kallon labaran
duniya.:
Inna Yaduwa( mahaifiyar mijinta)