Showing 27001 words to 30000 words out of 83144 words

Chapter 10 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11097

kirashi da ita. Kuma babu suna ma'ana bakuwar lamba (New number) ce.
Sannan yana da rubutaccen sako guda biyu baki wanda bai karanta ba. Ya buda daya daga ciki
ya soma karantawa kamar haka:-
" Wata rana mai dumbin tarihi wadda ta kasance LITININ an yi kullaliya mai kulle kwalwa da
tunani. Ranar litinin an rasa an kuma samu . Ranar litinin anyi katari da wani shamaki, bayan
wasu al'amura masu murdiya da murde kwalwa. Shin mai yasa wannan rana ta kafu da
murdaddun abubuwa? Tambayar ke nan!" kuma a zahiri karshen sakon ke nan. Yanayin uncle hamza ya bayyanar da matsananciyar
damuwa, rudani gami da razana. Bai san ina sakon ya sa a gaba ba, bai san wanda ya turo

sakon ba, bai san me yasa aka turo sakon gare shi ba......
Da sauri ya buda dayan sakon don karasa tantance abin rudanin , shin shi aka aikowa ko kuwa
dai halin network ne kamar yadda ya dauki lambar Najeriya ya kaita Misra?
" Rayuka cikin kunci ba karamin tashin hankali ba ne, ace dan Adam ya rayu a gurbin da ba
wanda ya sani anbin a tausaya masa ne. Shi yasa ta ke ba ni tausayi, nakan ji alhini game da
lamarinta. Amma babu komai akwai Allah, shi ne maganin komai. Amma zaluncin ya yi
yawa....." Iya rudewa uncle hamza ya shiga, ya rasa ma yadda zai fassara wannan cukurkudadden
al'amari, hakika ko tantama babu halin network ne. Amma saboda ya fita daga wasu-wasin da
yake ciki, sai ya kira lambar.
a Hausa Book stories
MATAUl HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤13¤¤
Abubuwa da dama sun faru wanda sai yanzu ya samu kakkarfar hujja da zai saka Shuhuda a
jinsin jinnu. Alh sada, shi ma ya kasance daga jinsin jinnu, an rike shi ne don kawar da
tunaninsa ya aminta shuhuda mutum ce don ya aure ta a kaddamar da shirin da aka shirya.
Tana karatu a makarantar ne don an samu tabbacin zai shigo makarantar koyarwa. Ta ko'ina dai
babu hanyar da za a layance masa yace Shuhuda mutum ce ba aljana ba! Idan an bar zuciya
da tabo ba a yi mata magani ba. Lallai za a samu rudani. Komawa ubangiji a dukkan tsanani da
rudani, ko ma jin dadi shi yake haifar da nagartacciyar rayuwa. A duba. ****** ****** *****
BABI NA SHIDA
ANA ZATON WUTA A MAKERA......
Tun daga wannan rana uncle hamza bai kara shiga shirgin shuhuda ba, sam ya nuna kamar bai
san da wanzuwarta a cikin makarantar ba. Ko aiki ya ba su ya ga ta yi kokari ba ya nuna ya
damu bare ya yaba mata kamar yadda yake yi a da.
Sai ma ya koma duk lokacin da zai shiga ajin nasu idanunsa rufe da bakin tabarau, wai duk don
kada ta ga wallensa bare ta raina shi. Tunda ya gane aljana ce yta ke rayuwa acikin mutane.
Shi ba zai iya tona mata asiri ba, haka kuma ba zai kulata ba. Idan ma tana tunanin zata cimma
wani buri ne a gare shi, to ta sha karya, ba zata ta6a samun wannan damar ba.
Idan ya tuna yadda ta dinga yi masa yawo da hankali, sai ya ji haushin kansa. Ai tuni ya kamata
ace ya gane shuhudan aljana ce idan ba haka ba ta ya mutum zai ce bai san waye bil'adama
ba, bai san shi wane irin jinsin halitta ba ne?
Ai daga ji ma kasan wata kullalliya ce kawai ake kullawa.
An murda an tufka murdaddun al'amura don jefa shi a cikin tarkon da ba zai iya fitar da kansa
ba. To amma da yake shi Allah mai taimakon bawansa ne, duk da ratar dake tsakanin jinsin
bil'adama da jinnu hakan bai hana yayewar yanar da aka dankara a idanuwansa ba. Ya gane ko
wace ce ita. Wannan ma abin godiya ne ga Allah da ya ni'imta shi da wannan ni'ima, tunda har ya kare shi
daga kaidin jinnu. Ya sani ba hikimarsa ko kwarewarsa da dabarunsa ba ne ya ku6utar da shi
ba. Illa wata BAIWA da HIKIMA ta Ubangiji.
Wannan hukunci da ya dauka ya dan rage masa zafin da yake hada wa kansa, yanzu sam ba
ya irin wannan zaman na dogon tunanin ya ya lamarin shuhuda ya ke? Saboda yasan yadda

aka yi masa alayen irin na mutan 6oye (Jinnu).
To kuma ga shi an yi walkiya ya ga komai, saura da me? Tabbas dole ne ya samu nutsuwa, a
da kam ya susuce komai ya kunce masa, ba shi da wani tunani sai na yadda al'amuran
shuhuda suke har wani kira yake kwalwa ce ta yi mata yawa. Ashe ba kwalwa ba ce tsabar
rainin hankali ne da yaudara irin na shiryayyen lamarin da bai san dalilin shiryuwarsa ba. WAYE UNCLE HAMZA?
""""""""""""""""""""""""""""""
HAMZA A. Babba shine asalin sunan nasa dan asalin jihar katsina a karamar hukumar Batsari.
Mahaifina Alh Babba mai lakabin sunan Abdullahi sananne ne a fadin birnin katsina. Domin ma
aikacin gwamnatin tarayyar birnin katsina ne.
Ya rike mukamai da dama a ganiyar kuruciyarsa kafin daga bisani ya ajiye aiki saboda girma da
ya kamashi. Matansa hudu na aure, ko wacce kuma ta hayayyafa da shi. A takaice dai mutum
ne mai yawan iyali saboda yana koyi da sunnar ma'aiki.
Yawan 'ya'yansa bai sa aka samu nakasu ga tarbiyyarsu ba, tsaye yake tsayin daka gurin
kulawa da tarbiyyar yaran nasa.
Hamza yayi karatunsa na firamare a nan cikin kauyensu karare da ke cikin karamar hukumar
Batsari. Da ya gama ya tafi Technical Mashi, inda ya fito da takardu masu kyau, bugun farko na
Jamb dinsa ya samu 258point. Don haka bai samu matsala ba lokacin da ya nemi gurbin karatu
a A.B.U ZARIA. Tunda hamza ya fara karatunsa ba shi da wata matsala har ya kammala lokacin da ya dawo
gida yana hutun jiran aiki.
Akawai wata yarinya zuwairiyyah diyar kanin mahaifinsa da ta so shi tun can baya, to amma sai
aka samu akasi, zuwairiyya irin shagwa6a66un yaran nan ne, ba ta iya komai ba ga ta katuwar
bagidajiya irin dai yaran nan da ake cewa: GIRMA YA RIGA WAYO.
Hakan ne ma ya sa koda ya nunawa mahaifinsa rashin amincewarsa ga lamarin ba su zafafafa
ba, amma daya daga cikin kannen mahaifinsa mai suna Binta ta zafafa abin, wai ita don me
zuwairiyya zata ce tana son hamza zai ce ba ya sonta. Kuma a biye masa? Wannan salon
gur6ata zumunci ne. Rigima aka yi sosai, dama can hamza ba ya shiri da Gwaggo binta, wata irin masifaffiyar mace
ce, haka nan ta bushi iska ta zo gidan ma ta yi ta ruwan masifa.
Da yake Alh Babba mutum ne mai tsananin hakuri da son zumunci ba ya damuwa da halayyar
'yar uwarsa. Ba ma ita kadai ba duk cikin sauran 'yan uwansa shi daban yake bai dauki rayuwa
da zafi ba.
Duk hutun da hamza yake dawowa yana zuwa gaishe da dangin mahaifinsa amma ba ya zuwa
gidan Gwaggo binta saboda muguwar tsanar da ta yi masa tun yana yaro, har cewa take wai
hamza kamar musaya aka yi aka ba wa Alh Babba shi, amma sam bai yi shige da tsatson
gidansu ba. Idan 'ya'yanta sun zo gidan, misali ace an yi katari lokacin hamza ya zo hutu ba ya kula su.
Saboda yaran sam ba su da kunya wannan ya sake hura wutar kiyayyar Gwaggo binta da
hamza.
A lokacin da yake aji uku a sakandire dinsa wani zuwa ziyarar dalibai da mahaifinsa ya je yake
sanar masa dan Goggo Binta ya rasu, ko a kwalar rigarsa bai damu ba. Don haka da ya dawo
hutun ma bai je yi mata gaisuwa ba.

Ana haka kuma auren Goggo binta ya mutu, tace: zata dawo gidan Alh BABBA kin amincewa
ya yi. Don yasan zama da Binta tashin hankali ne ba karami ba. Sai dai gidan wani dan'uwan ta
koma.
Ta yi zaman zawarci na shekaru hudu sannan ta yi aure. A lokacin hamza ya tafi ZARIA. Shi ma
auren ba wani dadewa ta yi ba ta fito saboda rashin hakuri da munanan halayenta ba kowane
namiji ne zai iya zama da irinsu Binta ba.
Ta koma zaman zawarci har hamza ya gamo karatunsa ya dawo ya fara aiki a nan cikin jahar
katsina. A wata makaranta MARIAMA AJURI MEMORIAL SCHOOOL Goggon tasa ba ta yi aure
ba.
Albashinsa na farko da na biyu zuwa na uku ya sayi tamfatsetsen filoti a nan cikin katsina
unguwar kanada. Tafiya ta tafi ya gina gidansa ya sayi mota sai kuma maganar zuwairiyya ta
kuma danno kai don har lokacin ba tayi aure ba.
A wannan karon an so fin karfinsa, to amma sai ya roki alfarma a makarantar da yake koyarwa
a mayar da shi wani reshen, tunda makarantar ta kafu tana da rassa da dama a garuruwa
daban-daban.
Yayi wannan hikimar ne don ya yiwa su zuwairiyya nisan zango. Idan aka ga ba ya kusa an gaji
a bata wani mijin ta yi aure.
Da farko za6i aka ba shi cikin Kaduna, Jos da kuma Bauchi. Ya duba duk cikin wadannan
garuruwan babu wanda ya kwanta masa a rai, ya dauki lokaci yana tunanin garin da zai za6a.
Kwatsam aka ce an turo shi Kano dama suna bukatar karin malamai. Ya yi farin ciki da hakan
ko ba komai kano gari ne na cibiyar kasuwanci idan yaje kanon zai iya samun wani kasuwancin
da zai yi ko ya saka hannun jari a wani kamfanin.
Hakan ko akayi, yana zuwa birnin kano ya fara aiki, a hankali kuma ya fada harkar kasuwanci
ya ba wa wani abokinsa kudi masu yawa yana yi musu kasuwanci a nan kasuwar kwari.
A kuma makarantar ne ya hadu da ALJANA! Kamar yadda ya kira SHUHUDA.
WANNAN KE NAN!!!
****** ****** *****
Rashin kulawar da uncle hamza ba ya yiwa Shuhuda ya sama masa nutsuwa na gajeran lokaci
ne kawai. Domin lokacin da su shuhuda suka shiga aji shida suna gab da soma jarabawa
tsumin abin nan ya taso masa haikan. Ya dinga jin a duniya babu macen da yake son ya aura
sama da Shuhuda. Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin
ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda
har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya.
Wato ranar da hamza zai aure ta. Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za
su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu).
To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya
saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin
jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar
da yake da hujjojin kiranta Aljana. Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa.
Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta

shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin
wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa.
Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai
ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa
kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba.
Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa
gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar
zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba.
Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a
falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda.
Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da
ya jike shi sharkaf Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a
lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta
ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta
zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta.
Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za
su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu).
To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya
saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin
jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar
da yake da hujjojin kiranta Aljana. Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa.
Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta
shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin
wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa. Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai
ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa
kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba.
Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa
gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar
zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba.
Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a
falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda.
Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da
ya jike shi sharkaf Zuciyarsa ta jagule, yana son furtawa yana tsoron abin da zai biyo baya. Shin
zai amince ya sake saka rayuwarsa a tarkon aljana? So wani irin makahon abu ne, duhu ne da
shi wanda yake makantar da zuciya gami da idanu tsinkaye da tarin kalubale. Idan haka ne so ya taka muhimmin rawa ga uncle hamza tunda ya hana ganin duhun son da zai
fada.
Cikin rashin walwala ya mike tsaye ya shiga bandaki ya yi wanka, sannan ya dawo falon, ya
dauki wayarsa yaga yana da kiran da aka rasa(missed call) guda sha uku, ya duba duk lamba
daya ne aka kirashi da ita. Kuma babu suna ma'ana bakuwar lamba (New number) ce.
Sannan yana da rubutaccen sako guda biyu baki wanda bai karanta ba. Ya buda daya daga ciki

ya soma karantawa kamar haka:-
" Wata rana mai dumbin tarihi wadda ta kasance LITININ an yi kullaliya mai kulle kwalwa da
tunani. Ranar litinin an rasa an kuma samu . Ranar litinin anyi katari da wani shamaki, bayan
wasu al'amura masu murdiya da murde kwalwa. Shin mai yasa wannan rana ta kafu da
murdaddun abubuwa? Tambayar ke nan!" kuma a zahiri karshen sakon ke nan. Yanayin uncle hamza ya bayyanar da matsananciyar
damuwa, rudani gami da razana. Bai san ina sakon ya sa a gaba ba, bai san wanda ya turo
sakon ba, bai san me yasa aka turo sakon gare shi ba......
Da sauri ya buda dayan sakon don karasa tantance abin rudanin , shin shi aka aikowa ko kuwa
dai halin network ne kamar yadda ya dauki lambar Najeriya ya kaita Misra?
" Rayuka cikin kunci ba karamin tashin hankali ba ne, ace dan Adam ya rayu a gurbin da ba
wanda ya sani anbin a tausaya masa ne. Shi yasa ta ke ba ni tausayi, nakan ji alhini game da
lamarinta. Amma babu komai akwai Allah, shi ne maganin komai. Amma zaluncin ya yi
yawa....." Iya rudewa uncle hamza ya shiga, ya rasa ma yadda zai fassara wannan cukurkudadden
al'amari, hakika ko tantama babu halin network ne. Amma saboda ya fita daga wasu-wasin da
yake ciki, sai ya kira lambar.
da Hausa Book stories
MATA UL hAYAT
¤¤14¤¤
Bugu daya kuwa ta shiga amma har sai da ta gama ringin ba a daga ba, ya sake kira a karo na
biyu shi ma ba a dauka ba.
Kamar ya share, sai da aka dauki tsawon lokaci sannan ya sake kira. A wannan karon an
dauka, muryar mace ce ya ji: kuma kamar ya ta6a jin muryar. Bayan ta gaishe shi yace: Yauwa
don Allah wa ke magana? Cike da tsananin mamaki aka amsa masa.
Wake magana fa ka ce? Amma wallahi Yah hamza ban san me ka dauke ni ba. Wai don Allah
me ye aibuna da ba ka damu da ni ba? Ya ji tsau! A dukkan sassan jikinsa, idan dai idanunsa
biyu ne yana a farke to zai iya cankar sunan wadda ke magana, amman ta yaya hakan ta faru?
Ko dai mafarki ne? Da ta ji ya yi shiru bai tanka ba, sai ta ci gaba da cewa: Ace wai ko arzikin ajiye lambata a wayarka ba ni da shi a gurinka? Haba don Allah, aiko ba ka
so ni don kyauna ba, ka so ni don arzikin alakar da ke tsakanin mu ta 'YAN UWANTAKA.
Idan ba ka so ni don haka ba, ka so ni ko don saboda shekarun da na share ina jiranka. Ka dai
san ba rasa samari na yi ba, amma na jure ina zaman jiranka, karshe sai ka saka min da haka?
Har yanzu bai tanka ba, har sai da ta dure da maganganun nata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login