Showing 30001 words to 33000 words out of 83144 words

Chapter 11 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11087

ta kuma sanya masa kuka,
sannan ya samu karfin gwiwar cewa: Na ji dai na kukan ki nutsu ki min bayanin wadannan
sakonnin naki, don kwata-kwata ban fahimci inda kika dosa ba.
Ta tsagaita da kukan tana cewa:: Kawai na turo maka ne ganin cewa ba ka damu da ni ba, ka
manta da babina a rayuwarka, ko dan kiran da kake yi min a da muna gaisawa yanzu sam ka
daina. Yace: To layin waye wannan? Tace: Wai da gaske da ba kada lambata din ke nan?
Shi kansa sai yaji ba dadi kuma ta ya aka yi ya rasa lambarta a wayarsa bayan yasan yana da
ita? Bai sani ba! Don haka sai yace mata : Wayar ce ta samu matsala shi ne cire layin na saka a
wata wayar. Lambar ki tana a cikin waccan wayar, don a waya (phone) nake ajiye lambobi.
Sai ta dan washe kadan tace:

Sai ta dan washe kadan tace: Shi ke nan, amma don Allah Yah hamza ka daina yi min abin da
kake min, ka tuna irin dumbin son da nake maka......
Ya katse ta, kada ki damu.....
Ita ma ta katse shi, Ya zaka ce kada na damu bayan kai baka damu da ni ba? Yace: Duk da
haka, ai nace kada ki damu ko? Ki bari karshen watan nan zan zo, tunda 'yan jarrabawa sun
kusa kammalawa.
Tace: Shike nan Yah hamza sai ka zo. Ya kashe wayar yana kallon fuskar wayar(screen).
Zabura ya yi ya mike tsaye sakamakon sunan ZUWAIRY da ke yawo akan madubin wayar,
lambar da ya kira ce ta koma haka. Ko kuwa dai bai sani ba hannunsa ya lulubo lambar
zuwairiyya har ya kirata.
Sai ya shiga neman lambar har kundin ajiyar rubutaccen sako(inbox) sai da ya shiga, amma dai
sunan ZUWAIRY ya gani dauke da wannan sako. To ya haka?
A da yana zargin shuhuda ce aljana to yanzu ma ya dora alamar tambaya ga Zuwairiyya, domin
yadda al'amuran suka faru ba su da maraba da aikin jinnu, ko kuwa shine ma aljanin bai sani
ba? Ya shiga tuhumar kansa.
Cikin kwana biyu uncle hamza ya rame, ya susuce saboda tsananin damuwa da tunani da ya
sakawa kansa. Sam ba ya cikin nutsuwarsa, ko abinci ba sosai yake ci ba. Illa kayan
gwangwani ko na kwali. Hatta abokinsa zaharaddeen Lawan ya fahimci halin da yake ciki. Sai
dai ko da ya tambaye shi amsar da ya ba shi ita ce. " Ba ni cikin nutsuwa, ban san kuma yadda zan kwatanta damuwata ba". Don haka
zaharaddeen ya tsura masa idanu, dama yasan hamza mutum ne mai zurfin ciki, sai ka ce
bafulatani.
An fito daga jarrabawar Biology, daliban ilimin kimiyya(science) sun taru a lab. Saboda malamin
Biology yace za su yi hotuna, tunda wannan shine karo na karshe na shigarsu lab din Biology.
Uncle hamza yana daga cikin malaman da suka tsaya kai da fata gurin gudanar da jarrabawar,
don haka shi ma yana cikin jerin malaman da suka nufo lab din daukar hotunan.
An shirya kowa aka soma dauka, kowane dalibi cike yake da farin ciki, suna ganin darajarsu ga
malamai, tunda har suka bukaci yin hotuna da su.
A 6angaren uncle hamza zan iya cewa ya fi kowa farin cikin daukar wadannan hotuna ko ba
komai akwai HASKEN ZUCIYARSA a ciki. Tunda dama yana son mallakar hotonta, amma ya
rasa ta ina zai fara, sai ga dama ta zo masa, don haka cikin doki ya kosa a dauki hotunan,
wanda ya tsaya a bayan Shuhuda yana murmushi. Bayan an gama daukan hotunan bai samu yin magana da shuhuda ba, sakamakon aikin hada
takardun da ya tsare shi.
Lokacin da ya samu sarari sai nemanta ruwa a jallo bai gan ta ba. Yana da tabbacin tuni ta dade
da komawa gida. Don wannan al'adarta ce, tun ma kafin soma jarrabawar da zarar an tashi ba
ta tsayawa jinkirin komai ta ke tafiya, to dama ita ba kawaye ba bare ace sun tsare ta.
Yayi takaitaccen murmushi, tare da lasar busassun la66ansa tukunna ya wuce izuwa mota.
Ko a cikin motar ma kafin ya tafi ya dauki wani lokaci yana jin dadin daukar hoton. Wannan
dama ce da zai yi amfani da ita gurin kwantarwa da Alh Babba hankali, zai nuna masa hoton
shuhuda a matsayin matar da zai aura. Inyaso an shafa masa lafiya akan zuwairiyyah, tun da
shi dai Allah bai saka masa sonta ko kadan a cikin ruhinsa ba. Shi kuwa ingancin zaman aure yana ta'allaka ne da ingantacciyar kauna. Da zarar aka ce anyi

aure daya ba ya so, dayan ma musamman namiji to kuwa za a yi katari da abubuwa marasa
dadi, to bare kuma shi da zuwairiyya wanda akwai karfaffen zumunci a tsakaninsu.
Da wannan tunani ya tayar da motar ya nufi gida.
Washegari aka wanko hotunan, a ranar kuma bau jarabawa, Mr philips ya kira shi a waya ya
sanar masa an wanko hotunan. Don dama tunda aka gama dauka yace a wanko masa duk
wanda shuhuda ta ke ciki. Har Mr. Philips yana dariya yana cewa: " ko dai ita ce Lobi din ne?"
¤¤¤
.
A lokacin da wayar ta same shi yana kauwar kwari inda zaharaddeen yake gudanar da
kasuwancinsu, kaya ne aka kawo daga MALAYSIA, don sun jefa hannun jarinsu da wani
kamfanin Material da ke Malaysia shi yasa suke kawo musu kaya akai-akai.
Babu laifi kuma wannan ya kara janyo musu daukaka, don ba karamin abin mamaki ba ne daga
fara kasuwancinsu a kasuwar kwari duka-duka shekaru biyu da watanni, amma suin shahara
irin haka. Wanda ga wadanda suka share shekaru aru-aru amma ba su yi irin wannan shaharar
ba. To shi da ma kasuwanci ribarsa saukaka abu, da zarar mutum ya yi hakuri da riba kadan, sai ya
tarar da tarin alkhairai. Amma muddin za a tsauwala to kuwa akwai ragee kwarjini da kuma
dakusar da kasuwancin.
( Don Allah 'yan kasuwa mu duba wannan lamari, barin ma idan Sallah ta zo ko Maulidi sai ka
ga an dauki dogon buri an dora a lokacin. Wanda babu wanda ake cuta sai talaka. Shi kuwa
talaka abin tausayi ne akan komai na rayuwarsa).
Zaharaddeen ya dago kai ya dube shi da yaga ya mike tsaye yace: Ina kuma zaka je? Uncle
hamza ya juyo da kansa yana dubansa, yace: Zan je na dawo ne, ba dadewa zan yi ba.
Yana karashe fadar haka bai jira amsar zaharaddeen ba ya sa kai. Sauri-sauri, gudu-gudu har
ya isa inda ya ajiye motarsa ya shiga ya tayar da ita. Nan da nan ya isa gidan hoton Mr. Philips,
suka gaisa, mr philips yana dariya ya dauko hotunan yana cewa:
Gaskiya yarinyar nan tana da kyau duba ka ga yadda tayi kyau a dukkan hotunan nan, duk fa ta
fi kowa yin kyau. Cikin harshen turanci yake maganar uncle hamza ya kai hannu ya kar6a.
Idanunsa suka kai ga abin al'ajab! Tashin hankali aka ce wanda ba a saka masa rana.
Ya gigice ya kuma razane duk a sanadin abin da ya gani a jikin hoton. Maimakon ganin
shuhuda sai ya ga taswirar zuwairiyya.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤15¤¤
Mr. Philips ya dube shi cike da tsananin mamakin yanayin da ya gani a tare da hamza, yace:
Lafiya? Uncle hamza sam wuta ta dauke masa. Abin da yake damunsa shine: ta ya aka yi
zuwairiyya ta shigo a cikin hotunannan da suka dauka a makaranta? Ina inuwar shuhuda ta
shiga a cikin hotunan da bai ganta ba? Shuhuda ce ta yi wannan kullalliyar tunda ta kasance aljana. Su kuwa jinnu sukan yi fiye da
hakan! Abin da zuciyarsa ta ayyana masa ke nan. Bai san yadda zai yiwa Mr. Philips bayani ya
gamsu ba, don haka sai wayancewa ya yi da yin murmushi yace: Kyawun da ta yi ne ya firgita
ni. Mr. Philips ya dan daki kafadarsa yace: Kai mutumina zaka fa more idan ka mallaki wannan

zukekiyar yarinyar. Murmushi kawai uncle hamza ya yi ya dauko kudinsa ya bashi, tukunna ya
masa bankwana ya tafi.
Travelling bag dinsa ya saka hotunan bai kuma bin ta kansu ba. Haka bai kuma bi ta kan
shuhuda ba, don ko da suka dawo yin jarrabawa yana kallonta amma ba ya kulata. Wannan
yana daga cikin matakan da ya dauka na kauracewa abin da zai saka shi da-na-sani.
Ranar asabar yana zaune a falonsa yana lissafa wasu kudi da zaharaddeen ya kawo masa na
ribar da suka samu a wasu kaya da suka shigo dasu. Wayarsa ta yi kara, yana dubawa lambar
yayansa Alh Mukhtar ya gani akai.
Cikin girmamawa ya dauki wayar suka gaisa, Alh Mukhtar yace: Dama Abba ne ba shi da lafiya
yana asibiti, sun ba shi gado shine na ce bara na sanar maka. Hankalin uncle hamza ya tashi,
cikin rudani yace: Mai yake damunshi?
Alh Mukhtar yace: Ciwon hanta ne, mu ba mu san yana da shi ba, wai ashe dama ya dade yana
fama da shi yana zuwa ganin likita a 6oye. Uncle hamza yace: Allah ya ba shi lafiya, ina nan
tafe anjima. Suka yi sallama ya tashi ya soma shiri.
Karfe uku na yammaci ya isa birnin katsina, a gidansu ya fara sauka ya tarar da su Goggo binta
duk suna gidan har zywairiyyah. Suka gaisa ya ajiye jakarsa ya nufi asibiti.
Ya tarar jikin da sauki, don har ma ya samu bacci, saboda haka ya dawo gida. Ya tarar da
tashin hankalin da ya hautsina masa kwalwa a lokacin da ya shigo gidan.
Goggo binta ce rike da hotunansa da ya saka a jakarsa, tana kururuwa wai hamza zai janyo
musu MUGUN IRI a zuri'a, tunda yake yawo da hotunan MAYYA a jakarsa! Zuwairiyya kuwa sai
kuka take ana rarrashinta, tana kuma rusa ihu barin ma da ta ga uncle hamza ya shigo gidan.
Cikin sanyin jiki da takaicin binciken da aka yi masa ya karasa ya kar6i hotunan ya ga ba
ZUWAIRIYYA? to ya haka? Ko kuwa dama idanuwansa ne a wancan lokacin suka yi masa gizo,
suka nuna zuwairiyya a maimakon shuhuda?
Muryar Goggo binta ce ta katse masa tunani, inda ta ke cewa: Wallahi ita ce ta lashe MAS'UD,
diyar fa KARIMA kishiyata ce, wadda ta yi sanadin mutuwar aurena! Yarinyar nan muhun iri ce,
domin ta lashe ma wata mata daga ta tsarga yatsanta. Gadon mugun abu ta yi, kuma na
tabbata tunda na ga hotunanta a tare da hamza shi ma so take ta lashe kurwarsa....... Haj Mardiyya ta katse surutun da cewa: Ya isa haka binta, ya kamata mutuna halin da muke
ciki. Uncle hamza bai ce komai ba, ya saka hotunan a jakarsa ya fice zuwa dakin kaninsa
salisu.
Koda ya shiga dakin tunani ya sha masa kai, ya auna maganganun Goggo binta, sannan ya
daura al'amuran da suka faru gare shi, shin da gaske mayyar ce? Ko kuwa aljana dai? A'a wata
halitta ce daban! Ya rasa inda zai dorata a matsayi, mutum-mayya ko kuwa aljana-hatsabib
iya?
.
****** ******* *****
.
BABI NA BAKWAI
.
.
TSAUTSAYI KO KADDARA?
.

Daya ga watan satumba, wanda ya kasance ranar litinin jirgin Egypt air ya sauka a birnin Egypt
bayan da ya taso daga senegal don sauke wasu fasinjoji(pasingers)kafin daga bisani ya yi
hutun awa daya da rabi, sannan ya dage zuwa birnin kano.
Kamar yadda yake a bayyane masu Transit visa wucewa zasu yi, idan jirgin nasu ya huta ba
tare da ko airpot din sun fita ba.
bare ganin yanayin gari, ko yin wasu mu'amaloli nasu abinsu.
Da yawan mutanen da ke cikin jirgin dalibai ne, wadanda suka kammalo digiri dinsu a kasar
senegal, wasu kuwa 'yan kasuwa ne da ke zuwa siyayya, don haka mafiya yawan mutanen ciki
kabilu ne farare, dai-daiku ne bajkaken wadanda sauyin gari, cima, yanayi da kuma kwanciyar
hankali ya sanya suka saje da fararen fatan, amma dai kana kallonsu kasan asalinsu bakar fata
ne.
Bayan jirgin ya sauka, fasinjoji suka soma saukowa, ISAH SADA RABI'U yana daya daga cikin
masu saukowa daga jirgin. Amma shi zai shiga cikin gari ne saboda yana son ganawa da wani
malaminsa da yake mazauni a kasar Misra, aiki ne ya jai shi can kasar senegal daga baya
kuma ya dawo kasarsa ta haihuwa. To sun yi da Isah idan zai koma Nigeria zai biyo ta nan Misra, hikimar hakan gurin malamin mai
suna Dr. Outhman Ibn Abdulfatah shi ne, yana so ya samawa Isah aiki a ma'aikatar karafa da
ya bude ta kashin kansa mai suna KHAIR METAL, saboda tun yana koyarwa a makarantar ya
aminta da kaifin kwalwa irin na Isah, ba duka dan Nigeria ne ake samunsa da yin karatu idan ya
shallake kasarsa ba.
Mafi yawancinsu sun fi mayar da hankali ne ga shashanci wajen kula mata da shaye-shaye,
amma shi Isah ko kawance ba ya yi da mata, abin da ya kai shi kasar shi yake yi. Hakan kuwa
ya kara masa kwarjini da cikar HAIBA a idanun malaman makarantar.
Yana saukowar daga jirgi tafiya kadan ya yi ya isa inda ake bincike, aka gama yi masa duk wani
bincike da ya kamata a yi masa a matsayinsa na bakon kasar. A lokacin ne kuma ya samu layin
da ake amfani da shi a kasar ya kira layin Dr Outhman ya sanar da shi ya kammala komai shi
kawai yake jira.: Bayan gama wayar akwai wani guri inda ake zama musamman don irinsa. Wadanda za a zo
taryensu, ya zauna yana nazarin wani littafi SHOCK TREATMENT. Kamar an ce ya dago kansa,
sai ya yi sai ya yi TOZALI da wata kyakkyawar mace, fara tas. Ma-abociyar cikar zati,
idanuwanta narai-narai da kwalli radau a cikinsu. Tana cikin shiga ta bakar jallabia ta yafa gyalen rigar a kafadarta, sannan ta nade kanta da wani
yalolon dan kwali, wanda ya kara fitowa da kyawunta a sarari. Kana ganinta kasan balarabita
ce, amma bisa ga tsanin al'ajabi, kai tsaye gurin da yake zaune ta tukaro, kuma koda isowarta
cikin harshen Hausa ta yi masa sallama, tun kafin ma ya amsa ta soma jero masa gaisuwa. Mamaki ya cika shi don bai yi tsammanin jin harshen Hausa a bakin wannan Balarabiyar da ke
gabansa ba.
Baya da haka kuma yana mamakin saukin kai irin nata wanda har ya sa ta zo inda yake ta
gaishe shi ba tare da shi ya yi hakan ba a matsayinsa na namiji wanda ya ga mace yana so zai
tunkara.
Duk da ba ya mu'amala da mata, ya sha jin yadda aka tsayar da suke da girman kai
musamman idan aka tsayar da su. To amma ita wannan mai sanyin hali ce, ko kuwa ita ma
daga senegal din ta baro, sun yi tarayya a makaranta daya?

Murmushi ya sakar mata cikin harshen Hausa yace:
Kai duk ni kadai wannan gaisuwan? Ita ma murmushin ta yi masa, tukunna tace: Ai ka isa ne,
gani na yi kamar na sanka, don Allah kai dan Najeriya ne, a birnin Kano ko?
Bai yi mamaki ba, don ya sha jin ana cewa duk inda DAN KANO ya shiga ba ya 6uya, wata kila
hakan ne ya sa ta canki wannan tambayar. (Ta6! Ai ba ma hakan bane. Ni dai ban yadda ba. In
dai ba mayintan san kudi ba, kanawa ba su san komai ba, sai shirme. Da ma dai 'yan zaria ne
sune suka fita zakka a fagen gogewa da komai. Lolx) Gira ya daga mata ba tare da ya yi magana ba. Tace; Haba, kofa naji, unguwar SALLARI ko?
Yanzu kam ya sha mamaki, don jin ta ambaci sunan unguwar su kakansa, yana dubanta yace:
Hala ke ma 'yar can unguwar ce a kano, kuma Najeriya? Ta girgiza kai tace: .......
.
1- Abubakar Ibn Khaddab
2- Shuhuda Ibn Khaddab
3- Yusuf Ibn Khaddab
Uncle hamza ya hadu da Abubakar ibn khaddab.
Isah kuma ya hadu da Shuhuda ibn khaddab
To ni kuma bari na arce watakil nine zan hadu da Yusuf ibn khaddab.
ada Hausa Book stories
MATAUL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤16¤¤
Ta girgiza kai tace: A'a, Ai ni 'yar wannan kasar ta Misra ce, na dai sanka, ko ba kai ne YAYAN
SHUHUDA SAGIR RABI'U ba?
To yanzu fa mamakinsa ya kuma hau-hawa akan na dazun. Ya dube ta da kyau, yace: Kin ce ba
a Najeriya kike ba, ya aka yi kika san garinmu, unguwarmu, dama kanwata?
Tayi murmushi, sannan ta ce dashi. " Ai sunanmu daya da kanwarka, ni kuwa duk inda mai
sunana ta ke sai nasan wace ce ita.
Murmushi ya yi mata, saboda ya fahimci wasa ta ke, ita ma din 'yar Najeriya ce. Yace: Kina
nufin ki ce min saboda sunanku daya dakanwata shi yasa kika santa, har kuma kika san ina da
alaka da ita. Yadda duk inda kika ganni za ki iya shaida hakan?
Ta daga masa kai cikin tabbatarwa, ita ma fuskarta dauke da murmushi.
Yace: Ban yarda wannan zai zama karfaffiyar hujja ba, don haka kada ki wahalar da kanki gurin
zolayata ta wannan hanyar, don ba ni kadai ba, duk wanda ya ji ma ba zai gasgata ba.
Tace: Wallahi rantsuwar dan musulmi ke nan ko? Na sanka, na san kai kuma yayan Shuhuda
ne, da Babanta mai rasuwa da Babanka mai rai uwa daya uba daya suke.
Shi kam dariya ta ba shi matuka, yana daritar yace: Eh, ai ba cewa nayi ba ki sanni ba, na
aminta kin san duk wadannan alakar da ke tsakanina da shuhuda, amma hujjar da kika bayar
cewar saboda sunanku daya da shuhuda kanwata kika san haka ba mai kar6uwa ba ce. Idan
ma har zata kar6un to cikin dayan biyu. Ko dai kin hadu da shuhuda ko wani da yake da alaka da tsatsonmu, ko kuma kacokam a
kasarmu, jaharmu kuma unguwarmu kike. Idan ba ta wadannan hanyoyin ba bazan ta6a yarda
da abin da zaki ce ba.
Tace: Ni asalina 'yar wannan kasar ce, ban ta6a zuwa Najeriya ba, amma nasan kanwarka
shuhuda sagir Rabi'u ta hanyar tsananin bincike da KAIFIYYA irin tawa...... Ba ma kanwarka

kadai ba, a kasarku kuma jiharku, na san masu sunana SHUHUDA sama da trilliom,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login