Showing 54001 words to 57000 words out of 83144 words
ambatr sunanasa
kai tsaye haka. Amma abin tambayar shi ne, dama tana ta aure? Ba mamaki hakan ne tafuya ta
kamata ita da mijin nata zuwa birnin Misra, asalinta 'yar Katsina ce, zaman aure ya kawo ta
Ibadan. A haduwarsu ta Katsina ta nuna sam ba tasan shi ba, yanzu kuma ta zo ta ambaci
sunansa har tana neman taimako, wannan rainin hankali da yawa ya.......
"Ka taimaka min, wallahi zai iya mutuwa!"
.
.
Wata sabuwa........!idan kai/ke ,ne/ce, zaka/ki taimaka?
Hanya, Isah zai taimaka???
da Hausa Book stories
MATA UL HAYAT
¤¤26¤¤
Ta katse masa tunani da fadar haka, hankalinta yayi kololuwar tashi. A matsayinsa na Musulmu,
wanda yake son ya kasance mai karfin imani da tausayawa halin da dan uwansa muslmi ya
shiga, sai ya ji zuciyarsa ta kare har ma yana kwadayin samun wannan gugguben ladar. Kawai
sai ya zagaya ya bi bayanta yana jefa kafafu tamkar wadda zata tashi sama. Ta bude gidan ta
zura kai, shi ma ya bi ta bayanta. Yana kwance a falo, magashiyan yake. Usah ya karsa gurinsa
da sauri yana taba jikinsa. "Subhan Allah". Ya dago kai ya dube tan ya ce, "Tun yanshe ne
bashi da lafiyar?" Cikin yanayi na rashin sukuni ta ce, "Yanzu ne na dawo na tarar da shi a
haka, amma lafiya lau ya baro ni gurin aiki". Ya ce, "bari na dauko mota". Ta katse shi, tana
mika masa makulli. "Ga tawa, mu je kawai". Ya kama shi suka fito harabar gidan, Ta yi sauri ta
bude masa gidan baya ya shiga da mara lafiyan, sannan ya zagaya mazaunin direba ya shiga,
itta kuma ta shiga gidan baya, Ya ja suka tafi.
Ba a bata lokaci ba aka karbe su, wani daki na musamman aka saka marar lafiyan, su kuma
aka bar su a bakin kofa. Isah yana zaune saman kujera, yayin da ita kuma ta ke zarya daga
bakin kofar dakin da mara lahiyan yake ciki zuwa tsakar falon da suke, tana takun tana buga
hannunta cikin daya hannun. Shi dai kallonta yake a nazarce don tantance shin da gaske ita din
dai ce ko kuwa kama ce? Amma iya duba da nazarinsa bai ga wata alama da ta banbanta da
Shuhudar da ya gani Misra da Katsina ba, har yanzu zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa a
lamarin, idan ya kamo wannan zare kafin ya tufke shi, sai ya gudu, ya sake kamo wani, shi din
ma babu nasara. Sun yi shiru su duka na tsayin lokaci babu wanda ya tankawa dan uwansa.
Can Isah ya dago kai yana sake dubanta, ya ce. "Ya kamata ki zauna, in shaa Allahu zai samu
sauki". Ta dan juyo a kaikaice ta ce masa. "Ina son mijina! Ina mararin zama da shi, kada ya
mutu idan na rasa shi ban san da wane namiji zan rayu ba. Wayyo yah Abubakar kada ka mutu
ka barni da maraici, kasan kai ne NURUL KALBI dina, kai kadai ne wanda zan kalla na ji sanyi a
kalbina". Idanunta suka soma zubar da hawaye. Sai ya ji zuciyarsa ta karaya ya soma
rarrashinta da sanyayen kalamai masu kwantar da zuciya da saka nutsuwa. A hankali ta nemi
guri a gafensa ta zauna tare da sanya hankici tana share hawayenta. Murya a raunane ta soma
cewa da shi. "A rayuwa idan mutum ya dace da masoyi na kwarai, wanda sai iya sadaukar da
rayuwarsa don sama maka farin ciki, ya yi tawaya akan komai don kai, ai ka gama samun komai
a rayuwa. Irin su Yah Abubakar Ibn Khaddab suna da karanci a duniya, duk macen da ta yi
sa'ar samunsa a matsayin miji to ta godewa Allah, domin ba karamin rabo ne ta samu ba". Isah
ya tuna sunayen 'yan gidan su Shuhudar Misra da ta lissafo masa a haduwarsu can Misran,
daga cikin lissafin nata tace su uku ne mahaifansu suka haifa. Ita kanta Shuhudan, Yayanta
Abubakar sai kaninsu Yusif, kuma dukkansu suna lakabi da sunan mahaifinsu IBN KHADDAB.
Yanzu wannan Shuhuda da ke gabansa ta ce sunan mijinta ABUBAKAR IBN KHADDAB ke nan
ba iata ce Shuhudan da ya tab sani a Misra da Katsina ba, tunda a bayyane yake babu aya ko
hadisin da suka halatta auren JINI DAYA.... Ta katse masa tunaninsa da cew. "Akwai wadda
nake zargi da ciwon mijina!" Ta mike zunbur kamar wadda aka tsirawa allura, ta ce, "Tabbas na
gano sanadin rashin lafiyar mijina!" Ta daga yatsanta sama kamar zata yi masa nini da wadda
ta ke nufi, shi dai ya tsura mata idanu kawai yana kallonta da sauraren maganganun da suke
fitowa daga bakinta.
"SHUHUDA SAGIR RABI'U ce! Ita ce ta bakunce mu a ofis ta ba wa mijina wani lemo. Da farko
bai karba ba, sai da na matsa masa a matsayinta na bakuwarsa bai kamata ta yi masa kyauta
ya ki karba ba. Ina tunanin lokacinda ya dawo gidan ne ya sha lemon, shi ne ya haddasa masa
rashin lahiya, wata kila wani mugun abu ne ta sanya masa..." Tun lokacin da ta ambaci cikakken
sunan kanwarsa ya mike tsaye cikin rudani, musamman da ya ji karashen maganarta. Yaushe
Shuhuda kanwarsa ta zo ibadan? Me ye alakarta da garin? Ba ta zo ba, kuma ba ta da alaka da
birnin Ibadan, to amman me maganganun wannan Shuhudar ke nufi? Sharri za ta jawa kanwar
ta, aminiyarta? Ko kuwa rainin hankalin da suka saba yi masa ne za ta yi masa don dilmiyar da
shi cikin rudani? Idan haka ne ba ta yi masa adalci ba, ta zoleye shi da yiwa kanwarsa sharri irin
wannan, rai ai ba abin wasa ba ne. Ba tare da ta damu da shi ba, ta ci gaba da maganarta.
"Dama tunda na ga kwayar idanunta na zargi wani abu, na dauka ko irin kishin nan ne namu na
mata yasa na zargi wani abu, ashe dai akwai wata kullalliyar da ta kullo mana?" Isah ya ske
tsintar kansa cikin wani rudanin jin tana tabbatar da zarginta akan Shuhudarsa. Amma sai ya
maze ya boye damuwarsa ya ce, "ki yi hakuri, kada zuciya ta sanya ki yi hasashe mara kyau
gudun saka rayuwarki cikin rudu"..
Wani murmushin takaici ta yi masa tukunna ta ce, "Mhm! Kai dai ayi sha'ani, maye ya ci dansa.
Amma mutum? Mutum?" Ta sake maimaitawa cikin jinjinawa. "Mugun icce ke nan, mutum dan
masara kana goyonsa yana fidda kai. Kana kallonsa sumi-sumi amma mugun nifinsa ya wuce
misali. Shi ya sa na tsani mutumin da zan dinga kallonsa kamar salihi, na fi son kawai ka zo min
a tsayenka sai na fi aminta da nutsuwarka, amma sai su nuna su na gari ne, suna wani sunnar
da kai alhalin KATTIN MUGAYE ne!" Daga haka su duka suka yi shiru, Isah yana tunanin
hanyar da zai bi ya fitar da maganganun da ke cikinsa, amma yana tuna hakkin aure, bai
kamata ya tsawaita zance da matar da ba muharramarsa ba. Bai. San yadda aka yi ba, ya kasa
hakuri ya magantu. "Yauwa, don Allah a ina kika san sunana don na ki lokacin da kika zoneman
taimako a gurin kin ambaci sunana?" Ta dube shi fuskarta da dan yalwa, ta ce. "Ba mamaki, ai
duk mutumin da yake cikin unguwar nan musamman layin nan, mijina ya sanar da ni
wanzuwarsa gami da sunansa, don haka nake kiran kowa YAYA saboda na tabbata kowa ya
mirme ni". Bai gamsu da amsar da ta ba shi ba, ya buda baki zai kuma magana ke nan, likita ya
fito. Da sauri ta mtsa inda yake, ta ce. "Likita ya mutu? Wayyo ta kashe min miji!" Ta soma kuka,
liktan ya ce. "Saurara madam bai mutu ba, yana nan da ransa". Isah ya matsa shi ma kusa da
likitan ya ce da shi. "Ok, muna iya shiga gurinsa?" Likitan ya girgiza kai, ya ce. "Bacci yake, idan
har ba zaku yi masa kwarabniya ba za ku iya shiga, saboda yana bukatar hutu, ciwon ciki ne
yake damunsa". Isah ne kadai ya karasa sauraren maganganun likitan, ita kuwa tuni ta shige
dakin. Likitan ya wuce, yayin da Isah yayi tsaye yana mamakin wannan MURDADDIYA, ko ta
ina zai warware ta?
"Mhm! Hanya mai sauki!"
Wata zuciya ta ayyana masa.
"Idan ka danganta Shuhudan Misra, da ta Katsina da kuma wannan ka samu warwarar
labarinka". Zuciyar tasa ta kuma ayyana masa. Da sauri ya ciro wayarsa, ya lalubi lambar Inna
Yaduwa ya kira, ta yi kara sau daya, biyu, ana uku aka dauka. Shuhuda ce ta dauka, ko bari ba
ta yi ya yi magana ba ta soma magana cikin doki da murna. "Haba Yah Isah, yanzu haka
rayuwa ta ke? Zunmunci sai ya yi wuya?" Mamaki ya hana shi magana, yayinda ita kuma ta
dora da cewa. "Ai na yi tsammanin ko ba wani abu a tsakaninmu wanda ya danganci JINI, aka
nuna maka ni aka ce 'YAR UWARKA ce, ka dinga kirana muna gaisawa, amma saboda Allah
tunda ka tafi ka taba tunawa da ni? Yanzu ma ba don wayar Innar na hannuna ba, na tabbata
ba zaka ce a baka ni mu gaisa ba". Cikin kasalalliyar murya ya ce da ita "Kuna lafiya?" Ta ce,
"kalau waLlahi, ya birnin Ibadan? Don Allah Yah Isah me da me ke da akwai a ibadan wanda
babu a kano, wai akwai sanyi, ana barin wuta, matansu farare ne sol, wai ko ina cikin Ibadan
akwai cinkoso kamar nan K....." Ya katse ta da cewa. "Ya isa haka, ina Inna Yaduwa?" Muryarta
a raunane kamar wadda zata yi kuka, ta ce. "Kayi hakuri Yah Isah, ban san zan takura maka
har na bata maka rai ba, ka yi hakuri don Allah.... Inna Yaduwa ta fita unguwa, ni ma Shuhuda
Ibn Khaddab ce ta kawo min ziyara daga Katsina shi yasa ban bita ba, ita kuma ta manta
wayar".kamar zai tuhume ta abin da yake son tuhumarta, amma jin abin da ta fada sai ya kasa
magana ya katse wayar. Komawa ya yi akan kujerar da ya tashi ya zauna. Wani tunani ya darsu
a zuciyarsa, wai bakuwa ta yi... Shuhuda ibn Khddab ta kawo mata ziyara daga Katsina... Ke
nan wannan ta gabnsa ba ita ce wadda yake nufin ba, wata ce can daban? Lokacin da yana
Senegal suna yawan yin waya da kanwarsa Shuhuda a wayar Inna Yaduwa, da ya dawo ya
bukaci ya siya mata waya ta kawo masa kabli da ba'adi wai hannunta ba ya iya rike waya,
yanzu da wane hannun ta yi amfani ta rike wayar da suka yi magana? Da can da wane hannun
ma ta ke rike waya suna gaisawa? Gaba daya yaran nan sun gama raina masa hanka li, fita a
sha'aninsu shi ne mafitar MURDADDIYAR da suke saka shi! Sai dai zuciyarsa ta kasa wannan
yunkurin, Allah Ya jarabce shi da abu mafi tsauri, wato KINAYAR MATA, abin da ya fi ba shi
mamaki kasancewar yaran kanana, amma sai juya shi bai-bai suke kamar waina a tanda. Ya
dokantu ya ga an zo karshen wannan wasarere da hankalinsa da ake yi.
* * * * *********
.
Kwana hudu tsakani tun bayan rabuwar Isah da wadda yake ganin Shuhuda Ibn Khaddab ce
bai sakata a idanunsa ba, sakamakon aiki da ya rufe masa kofa, sam ba shi da sukuni, idan ya
fita tun safe ba shi yake dawowa gida ba, sain gama sallar magruba. Lokacin da zai dawo a
gajiye yake, don haka a daddafe ya ke samu ya salaci jam'in isha'I ya shige gida ya yi wanka,
sai kuma maganar bacci. Yau ya kama ranar lahadi ce, baya zuwa aiki, tun asuba da ya yi
sallah ya koma bacci bai farka ba sai karfe sha daya. Kafin ya fito wanka Beka ya gama hada
masa abin karin kumallo. Yana gama karin ya fito barandar gidansa ya tsaya, sanye yake da
kananun kaya blue jeanz da red T shirt wadda daga bayan rigar aka rubuta Onlu for you.
Rashin sukunin da yake da shi ya sa ya dan rame, amma ramar sai ta kara masa kyau dama ga
shi kyakkyawan.. Yana tsaye a gurin tunanin abubuwan da suka faru suka dinga dawo masa a
rai. Wato tunani ma lokaci gareshi, hakika ba don aikin da ya sha masa kai ba da damuwar da
zai shiga Allah ne Ya yi yawa da ita, amma yanzu dan takaitaccen lokaci da ya samu na hutu
tunanin har ya bijiro masa. Sai dai bai yi nisa a tunanin ba ya hango Abubakar yana fitowa da
jakunkuna yana zubawa a mota. Mamaki ya kama Isah, lafiya? Ya tambayi kansa. Kafin ya
samu amsar tambayar tasa ya ga Shuhuda ita ma tana fitowa da wasu kayan, sannan tana
share kwalla da hannayenta. Hakan da ya gani ya tabbatar masa da lallai ba lafiya ba, akwai
wani muhimmin al'amari a tare da su. Da farko ya so ya shere da su, amman zuciyarsa ta ki
amincewa, makoci ba wasa ba, hakkin da yake kan makoci ba karamin ba ne, shi mutum ne da
yasan darajar makocinsa. Idan ya kyale su suka tafi bai san damuwarsu ba, abin zai dame shi,
wata kila ma rasuwa ce aka yi musu. Cikin karfin gwiwa ya soma takawa don isa inda suke.
Daga can nesa da su kadan ya tsay saboda Shuhuda na kusa da mijinta, yasan ko yaya ne
mijin nata ba zai ji dadi wani ya kusanta da ita ba. Ya dan daga murya, ya ce. "Malam Abubakar
lafiya dai na ga kuna loda kaya a mota kamar za ku yi doguwar tafiya?" Abubakar yana kallonsa
ya ce. "A'aha Haji isah karaso mana, ka toge daga nan?" Cikin karkarfan takunsa ya karasa
gurin yana kuma maimaita tambayarsa. Abubakar ya ce masa. "Eh, gida Kaduna zamu je, wata
yarinya ce ta yaudareni daga ta zo min bakunta ta zuba min magani a lemo shi ne na sanya aka
kamata tana yunkurin guduwa da dalolina, don haka zamu je. Sai munyi tsayin wata daya kafin
mu dao shi ne mai dakin nawa ke kuka.
A rayuwarta ba ta son zama Kaduna. Ta fi sha'awar nan ibadan ni kuma ina duba kadaicin da
zata shiga kafin na dawo. Isah ya ce da shi. "Akkah Sarki, ashe dai abin da gaske ne? An samu
nasarar kamata ke nan?" Shuhuda ta tsoma musu baki, ta ce. "Ai idona idon Shuhuda Sagir
Rabi'u sai ta raina kanta, muguwa, azzaluma kawai". Abubaakar ya dube ta, ya ce. "Ai sai ki yi
hakuri tunda dai. Ba ta kassara miki rayuwa ta raba ki da ni ba, ba ga shi ba da yake Alla ba Ya
barin hakkin wani akan wani ba, tun aduniya Ya toni asirinta ba?" Shuhuda ta ce, "Wallahi Yah
Abubakar ba komai nake ji da tafiyar nan ba. Illa dadewar da zamu yi ba ma nan, gida babu
kowa akwai matsala, musamman yadda bata-gari suka yi yawa a gari yanzu. Wannan shi ne
damuwata kawai ba wani abu ba".
Abubakar ya yi dan takaitaccen murmushi, ya ce. "Ka ji hasashen matan ko? Sai ka ce wadda
ta tsauna dukiyar Nigeria gaba dayanta". Isah ya ce, "A'a kada ka ga laifinta, ai ko naira biyar
aka sace wa mutum dole ya ji zafi, ba satar ke da ciwo ba, abu mai muhimmancin da aka sace
shi ne ciwon". Abubabakar ya ce. "Haka ne, amma an fi so mutum ya saka karsashi a
zuciyarsa, babu abin da zai same shi face rubutaccen al'amari ne daga Allah". Isah ya ce. "Idan
haka ne, kada ku damu in sha Allah zan saka a dinga kular muku, ni ma idan ina gida zan dinga
kula". Abubakar ya ce. "Ai kuwa mun gode da wannan taimako da ka yi mana". Ya dubi
Shuhuda ya ce. "Ina makulli? Kawo mu ba shi daya ko da wani abu zai taso na bukatar shiga
ciki". Isah ya yi saurin cewa. "A'a ba ma sai na karbi makullin ba, zan dinga kula, inshaa Allahu
babu abin da zai faru har ku dawo". Abubakar ya girgiza kai, ya ce. "Idan dai har ka amince
zaka yi mana wannan taimakon, to karbar makullin yana da amfani". Bai tsawaita jayayya da su
ba, ya karbi makullin tunda ya ga sun aminta da shi, bai kamata shi ya ki aminta da kansa ba.
Yana kallo suka ja mota suka tafi suna daga masa hannu, shi ma yana daga musu nasa
hannun. Har yanzu dai kwakwalwarsa ba ta gama wartsakewa da yadda lamarin ya gudana a
tsakaninsu ba. A yadda dai suka nuna masa su din wadansu mutane ne na daban wadanda ba
su da alaka da wadancan da yake hasashen su ne. Abu daya ne ya fi aminta da shi, wannan
Shuhudar ko tantama babu Shuhuda Ibn Khaddab ce, amma ta ya ta ke auren dan uwanta na
jini? Ko kuwa zakin soyayya ce ta sanya ta alakanta sunanata da sunan mahaifin mijinta
(surukinta), ko shi mijin nata ya alakanta nasa sunan da sunan mahaifin matarsa (surukinsa)?
Lamarin dai akwai matukar rikitarwa da juyar da hankali har ma mutum ya soma lalubar hanyar
WARWARA!
An samu tsayin makonni biyu da tafiyar su Abubakar Kaduna kamar yadda suka sanar da Isah,
a tsugin babu wata damuwa da ke tare da Isah, ya kawar da kai da kokarin cusa harkokin ofis a
cikin ransa a kowanne lokaci don samawa kansa zaman lafiya da nutsuwar zuciya. Yau ya taso
aiki da wuri, ya kuma iso gidan nasaa da wuri. Ya fito harabar gadan yana shan iska, haka
kawai zuciyarsa ta ayyana masa ya je gidan su Abubakar don kewaya. Bai yi kasa a gwiwa ba
kuwa ya tunkari gidan, ya kewaye shi tsaf ya ga komai lahiya, tukunna ya koma gidansa ya
dauko makulli ya zo ya bude gidan.yan zura kafarsa cikin falon gidan yayi katari da wata farar
takarda, mai dauke da rubutu. Ya durkusa tare da kai hannu ya dauka. Abu na farko da ya fara
gani an rubuta shi ne:-
"BUDADDIYAR WASIKA
Daga Shuhuda Ibn Khaddab
Zuwa ga Isah Sada Rabi'u.".
.
Gabansa ya yi wani irin yankewa ya fadi, ya shiga matsanancin rudani, anya kuwa sunansa ne
a jikin wasikar? Idan dominsa aka