Showing 15001 words to 18000 words out of 83144 words

Chapter 6 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11104

Sa'adatu ita kuma tayi
nauyin bakin cewa Shuhuda ba ta amshi nata ba. Yayin da Shuhudar bata ma san abinda ke
faruwa ba. Uncle Hamza ya ci gaba da yi musu bayani game da amsoshin da suka bayar ya
dora da basu shawarwari don ganin sun zama Zakaru a kowanne darasi ba lallai sai na sa ba. A
haka ya cinye lokacinsa sai da yaga wani malami a waje yana jiransa sannan ya dauki littafin da
ya a jiye a gefe yace; Wace ce Shuhuda Sagir Rabi'u a cikin ajin nan? Kowa ya mayar da
dubanshi can layin karshe inda Shuhuda ta ke zaune kanta rusune a kasa Sa'adatu ce ta yi
saurin cewa. Ga ta nan. Yayin da ta zunguri Shuhuda. Zumbur Shuhuda ta mike tsaye ta nufo
gaban allo ta durkusa(kneel down). Uncle Hamza ya cika da mamakin wannan yarinya daga
tambayar wace ce ita sai kawai ta fito gaban allo ta durkusa sai ka ce yace ta yi hakan? Ganin
rashin isashen lokaci tunda ga wani malamin a waje yana jiransa sai ya mika mata littafin ya
girgiza kai ya ficce ba tare da ya iya cewa wani abu ba. Uncle Hamza yana zaune akan
teburinsa cikin dakin malamai ta tagar dake ku sa dashi ya hango dalibai na shawagi a farfajiyar
makarantar alamar an fito tara (break fast)ke nan dama ya kosa lokacin ya cika saboda yana
son ganawa da Shuhuda akwai tambayoyin da yake son ta amsa masa su. Da sauri ya mike
tsaye ya nufi ajin su Shuhuda kamar yasan tana can. Ya tarar da ita tana duba littafanta sai ya
ja ya yi tsaye daga bakin kofa ba tare da ya karasa ciki ba. Ya tsura mata ido wato dama shi
yasa ta kasance mai hazaka tunda idan an yi break ma ba ta fita daga aji karatu ta ke yi?
Kamar ance dago kanki ana kallonki sai kuwa ta yi tozali da Uncle Hamza a tsaye yana
kallonta. Da yake bai sako bakin tabarau dinsa ba don haka tana kallon kwayar idanunsa. Shi
kuwa ganin ta dago ta dube shi sai ya tako sannu a hankali zuwa inda take ya zauna a kujerar
da ke gabanta. Yace Shuhuda Sagir Rabi'u. Kanta na sunkuye ta amsa Na'am. Ya yi gajeran
murmushi yace Mai yasa baki fita break ba bayan kowa ya fita? Muryarta a nutse cikin zakin
nan nata yaji tace: Bana fita break idan na ciyo abinci daga gida bana karaci cin wani sai na
koma. Yace amma ko ruwa kin bukata. Sai ta janyo lokar kujerarta ta fito da robar ruwa Swan
water ta nuna masa ba tare da ta yi magana ba. Ya jinjina kai yace: Ki ce tafe kike da gidanki?
Ba ta ba shi amsa ba haka kuma ba ta dago ta dube shi ba. Ya ci gaba da cewa yana kallonta.
Dama wasu tambayoyi nake son yi miki. A wannan karon ba ta iya jurewa ba sai ta dago kai ta
dube shi tace: Tambayoyi? Ya tabbatar mata da hakan ta hanyar daga mata gira sama ya ci

gaba da cewa. Ke musulmace kuma bahaushiya? Fuskarta ta nuna yanayi na mamakin jin
tambayarsa. Ta ce Eh. Yace Na ji ai cewa kika yi Eh ita kuwa kalmar Eh tana nufin DUKA ban
san wane matsayi zan ajiye amsar eh dinki ba. Ta yi shiru ba ta tanka ba. Yace: To misali ma
ace na ajiye ki a matsayin musulma shin mai ya hada sunanki Shuhuda da Izra'el? Ta dago kai
da suri tace; Izara'el? Yace Eh. Ta girgiza kai tace: Ni ban san Izra'el ba ban hada komai da shi
ba. Ya cika kwarai da tsananin mamakin jin maganarta amma sai ya daure yace: Idan baki san
Izra'el ba sannan ba ki da wata alaka da shi mai yasa idan an tambayi sunanki kike cewa
Izra'el? Ta kara fito da ido alamun dai nuna ba tasan zancen ba idan aka dubi kwayar idonta za
a tabbatar da haka. Ta ce Ni din kuwa? Ya kara cika da mamaki wai wannan wacce irin yarinya
ce mai wadannan halaye? Ya aminta idan ma kwalwa ce ta yi mata yawa to har da raini
tsagwaronsa. Yace to na ji bake bace amma mai yasa idan malami na cikin aji ba ki mayar da
hankali gare shi? Maimakon ta amsa masa tambayarsa sai cewa tayi.........
¤
¤
ko me ta ce, oho!!! Sai ku biyo ni dan jin saura..........
da Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤09¤¤
uncle mu dawo kan maganarmu domin gaba daya ka daure min kai ina son gamsasshen bayani
daga gare ka. Ya kara cika da tsananin mamaki wannan wace irin yarinya ce da take neman
juyar masa da tunani? Bai gaza amsa mata alfarmar da ta nema ba ko ba komai a cikin bayanin
da za su tattauna zai iya fuskantar kowace ce ita. Don haka cikin natsuwa yace: Abu ne mai
matukar mamaki ga irin yadda kike wasu abubuwa. Ta katse shi da cewa: Uncle am sorry kamar
wadanne abubuwa? Kasan komai yana da dalili zai iya yiyuwa idan ka fada min misalin
abubuwan da nake yi na gamsu da zargin da nakewa kaina. Ya dube ta cikin ido yace: Kinga
kina kiran kanki da sunan namiji alhalin kina mace. Kuma namijin ba wanda ya haife ki ko
dan'uwanki ba. Ta yi murmushi tace: Auho! Ai uncle a tunanina ko wane suna mutum zai iya
amfani da shi wata kila akwai wata Hoyayyar ALAKA da ta sanya haka. Cike da rudani yace
6oyayyar alaka? Ban gane ba. Tace Ka tuhume ni akan abun da ko a mafarki ba zaka samu
amsarsa ba bisa wani 6oyayyen SIRRI mai wata irin YANAH mai duhuwa wadda idan za z
kunna dukkan hasken kwan lantarki dake fadin duniya ba zasu haske DUHUN da ke tattare da
ni ba. Illa wani muhimmin ABU wanda ko a mafarki bana tunanin kai zaka iya canko shi. Ya rasa
yadda zai yi ya fahimci wace ce wannan yarinyar da ke zaune a gabanshi. Ko a kalamanta na
yanzu kamar zai iya ajiye ta a sahun marasa cikakken hankali domin da farko kamar akwai
hankali a tare da ita amma koda ta kai tsakiyar maganar tata sai sokana da shirme suka ida
mamaye hankalin nata. To yanzu me ma zai furta mata? Kafin ya karasa lalubo abin yi ta cike
gurbin shirun da maganarta. Uncle wai waye MUTUM? Ni fa har yanzu ban san waye mutum ba
ban san mai ya alakanta shi da wasu jinsina ba. Maganarta wani tsani ne har wa yau da ya kara
hauhawar da rudaninsa cikin rudanin da rikitarwa ya lalubo abin cewa. Halittar MUTUM halitta
ce wadda Allah(S.W.T) Ya yi ta a doron kasa mai girma da daraja domin duk halittun da ke
duniya kama daga shi kansa mutum, jinnu dabbobi tsuntsaye da tsirrai to babu ya mutum . Ana
kiran mutum 'Yan Adam a jam'insu ma'ana idan za a tara mutane da suka zarce mutum daya,
idan mutum dayan ne ana kiranshi dan Adam saboda asalin halittar mutum daga shugaban

halitta ne Annabi Adamu (A.S) don haka duk mutum ake kiransa DAN ADAM mutane kuma ake
kiransu Bil'adama ko 'Yan Adam. Idan muka koma ga sauran halittun idan kika tsaya kika lura
zaki ga dukkan sauran halittu samuwarsu cikar farin cikin dan Adam ne. Ina fatan wannan
bayanin nawa ya gamsar dake sanin ko waye mutum? Ta jinjina kai tace: Haka ne, bana son
shiga hakki idan na yi tambaya aka amsa min ko na gamsu ko ban gamsu ba to na gamsu din
ne, ba kuma don na gamsu ba. Shin uncle, Ni da kai din nan mene ne a cikin halittu? Ko kuma
nace ni ko ka fahimci ni eace halitta ve a cikin halittu? Wadanne dabi'o'i ne mutane suke yi????
Yace Ni mutum ne dan Adam ke ma a yanzu kallon halittar dan Adam nake yi miki saboda kina
da suffa da tsari irin na halittar dan Adam. Sannan Bil'adama suna dabi'u na tafiya da kafafu
biyu yin ayyuka da hannaye biyu gani da idanu biyu shakar kamshi ko wari da hancina biyu.
Bil'adama suna dabi'o'i na tunani da fahimta suna da dabi'ar yin karatu ina tunanin haka ma ya
gamsar dake? Tace na fada maka kona gamsu ko ban gamsu ba na gamsu din ne. Yace Ai so
nake na sani. Tace Watakila na gamsu wata kila ban gamsu ba ko kuma zan gamsu.... Amma
dai na gamsu din tabbas. Dole unle Hamza ya shiga rudani domin gabaki daya maganganun
Shuhuda ababen rudani ne. Idan banda rudani ta ya mutum zai ce koya gamsu ko bai gamsu
ba amma ya gamsu din? Me ye MANUFAR hakan? Ba a gamsu ba ko an gamsu ya zama lallai
an gamsu? Wannan tatsuniya ce ko soki burutsu? Yace: Idan kin gamsu ko ba ki gamsu ba zai
zama hujjar gamsuwarki. To maimata min abin da na fada domin hakan shi zai ba ni kwarin
gwiwar baki amsoshinki. Tayo dariya. Uncle sai ka ce ni yarinya ce 'yar shekaru hudu a duniya?
Shekaruna fa sha bakwai ajina hudu a matakin sakandire ke nan zan iya rike duk abin da aka
fada min har ma na yi masa fashin baki? Shi ma dariyar ya yi amma tashi gajeruwa ce mau
kunshe da takaicin maganganun yace; Na ji maimaita idan da gaske kin riken. Ta kuwa
maimaita har ma da karin bayani. Da ta karashe yace; A maganarki kin ce ba kisan ke mece ce
a cikin halittu ba to amma na yi mamakin karin bayanin da kika yi min akan halittar dan Adam,
me ne gaskiyar lamari? Kai tsaye tace dashi. Idan har ka yi mamaki akan faruwar hakan to
kuwa zaka yi mamaki akan yadda dalibi ke fin malaminsa ililmi. Saboda shi dalibi makoyi ne
kwalwa kuwa takan taimaka wa wanda aka fadawa ya kara sanin abun da aka sanarda shi. Ya
baki zai kara magana ke nan dodon kunnensa suka jiyo masa karar kada kararrawar komawa
aji don haka maganar tashi ta katse ya mike tsaye gudun kada dalibai su tarar da shi. Shuhuda
akawai sauran tambayoyin da zan miki amma lokaci ya kure don haka sai idan mun sake
samun dama. Tac ce; To uncle ammaka shirya min tambayoyi da suka shafu wasu halittu ba
bil'adama ba domin shi ne dama ta karshe da zaka yi magana da ni. Ya daina mamakin
maganganunta ya ce; Ke ma ki shirya amsa min korafin da kika sjigar na yi miki tambayoyi akan
wasu halittu ba bil'adama ba. Ya karashe maganar yana kokarin ficewa daga ajin amma kafin ya
kai ga ficewar sai kunnuwansa suka jiyo masa furinta tana cewa. Wannan hirar da muka yi yasa
nasan kai MATA'UL HAYAT ne gare ni dama zan budi ido na ganni cikin yalwataccen guri
kwatankwacin dokar daji da na samu MATA'UL HAYAT wanda ba ya ta6a yankewa a gare ni.
Sai dai abu ne mai wahala na samu MATA'UL HAYAT a wagga Sai dai abu ne mai wahala na
samu MATA'UL HAYAT a wagga........ Bai karasa jin furucin nata ba saboda samun nasarar
ficewa da ya yi amma kalmarta ta karshe ta zauna daram a kwanyarsa hakan ne ma ya sa
lokacin da ya koma dakin malamai ya shiga kogin tunani. Sam ya manta ma'anar kalmar daga ji
dai kalma ce ta Larabci musamman idan ya yi la'akari da HAYAT da ta sako cikin jam'in
kalmomin wadda ta sako cikin jam'in kalmomin wadda take nufin RAYUWA. To me MATA'UL ke

nu fi? Amsar ta gaza samuwa sai da ya dangano ga uncle Tukur Ahmad Sada wanda shi ne
H.O.D na Arabic ya isar da bukatarsa ta neman sanin ma'anar kalmar MATA'UL HAYAT ko ya
tantance me Shuhuda ke nu fi? Uncle Tukur ya yi murmushi yana duban uncle Hamza yace;
Kalmar MATA'UL HAYAT kalma ce da aka samo daga harshen larabci ma'anar gundarin kalmar
tana nufin JIN DADIN RAYUWA. To amma wani lokaci ana alakantata da kayan dadin rayuwa.
Uncle Hamza ya yi jinjina kai cikin gamsuwa. Uncle Tukur ya ci gaba da cewa. Wani bincike
kake yi ne da ya hado da kalmar? Uncle Hamza ya yi takaitaccen murmushi ya ce Eh. Yana
kokarin mikewa; Na gode . Ya koma teburinsa ya zauna. Wani tunanin ya bijiro masa idan
kalmar MATA'UL HAYAT na nufin JIN DADIN RAYUWA me Shuhuda ke nufi da ta ce shi
MATA'UL HAYAT ne gare ta? Wai kuma da zata samu kanta a cikin dokar daji to da ta samu
MATA'UL HAYAT wanda ba ya yankewa. Ke nan ta kasance mai son yin rayuwa a cikin dokar
daji? Me yasa ta ke da wannan burin? Wannan ma idan aka auna shi a mizani za a tarar da
soki-burutsu ne a cikin maganganun nata kamar yadda ta saba abubuwanta a cikin
soki-burutsu. To wai duk me ya yi sanadin hakan? Kwalwar ce ta yiwa Shuhuda yawa yasa ta
ke wasu rudaddun al'amura ko kuwa tana daga cikin jinsin mutane masu raunin hankali? A'a
gaba daya ma ba ta daga cikin jinsin halittun mutane? Aljana ce? Tabbas Aljana ce! Ya ji
zuciyarsa na son gasgata masa hakan bisa kwararan hujjoji. To amma ta ya zai aminta cewar
Shuhuda aljana ce? Idan ya alakantata da suffofin mutane ma'ana ba ta da kofato a kafarta idan
ba ta daga cikin jinsin mutane ko na jinnu a wane jinsi za a ajiye ta? Bai sani ba! Babu wanda
zai yi gajen yanke hukunci akan haka! Babu wanda zai iya cewa ga matsayin Shuhuda a
rayuwa illa dai Shuhuda wata halitta ce da ke yawo bisa doron kasa don haka yanzu abu mafi
rinjaye a tare da shi sanin nasabarta ma'ana asalinta iyayenta da ma sauran wasu al'amura da
suka shafe ta! Zuciyarsa ta kalubalance shi mai yasa zai damu kansa a cikin lamarin Shuhuda a
matsayinsa na malami wanda alakar karatu ta gada su? Da gaske ke nan abin da yake ji na
masa yawo a rai ya zama gaskiya? Ya kamu da son Shuhuda? Ta ya zai kamu da son abin da
bai da tartibin sanin ko mene ne shi? Lokaci daya ya kalubalanci wannan hasashen na shi
kawai abin da ya dace dashi ya share ta. Ya manta da wanzuwarta a makarantar bare ta dinga
caza masa kwalwa a karin banza. ANYA UNCLE HAMZA? DUBA DAI!!!
Shuhuda na kwance a saman gado, inna yadywa ta shigo dakin tana cewa. Ke burkakkiya tashi
ga wannan fitinannen yaron ya hanani sukuni wai sai ya yi waya dake. Shuhuda ta dago kai ta
dubi inna yaduwa da wani irin kallo mai rikitarwa ta ja dogon tsaki ta mayar da kanta ta kife a
filo. Ran inna yaduwa ya 6aci ta janyo Shuhuda tana cewa: Ke ni kike yiwa tsaki don gidanku?
Shuhuda ta daga mata hannu tace: Kada ki kara ta6a ni idan ina wanka ki fita ki bar kallona....
Nace ki fita idan ba so kike na yi miki wanka ba? Inna yaduwa ta ture Shuhuda tace: Ja can
burkakkiya kawai. Tana karashe maganar ta fita daga dakin. Isah da yake jiyo hayaniyarsu ta
cikin wayar yace: Haba Inna bai kamata kina yiwa Shuhuda irin wannan tsawar ba ya kamata
ace kina rarrashinta domin wannan matsalar da ta ke fama da ita ba karamar matsala ba ce: Ta
katse shi da cewa: Bayan matsalar ma har da shakiyanci don kawai tana ganin ni kakarta ce sai
ta dinga raina min hankali. Wai na shiga dakinta amma sai tace wai tana wanka na fita... Oh ni
Yaduwa yau na gamu da gamona!! Isah yace: Wane irin wanka? Inna yaduwa ta ce; Shi ne abin
da ke ba ni takaici, kwance fa ta ke akan gado sanye da doguwar riga baka amma don tsabar ta
dauke ni wata karabiti shine zata ce tana wanka? Isah ya jinjina maganar yace: To don Allah
Inna ki dinga hakuri da Shuhuda kuma ya kamata fa ace ya zuwa yanzu an san wane irin ciwo

ne da ita. Saboda barinta cikin wannan matsalar ba karamin cutarwa ba ne a gare ta? Inna
yaduwa tace To ai magana ba hannuna take ba wannan sai ka tuntu6i mahaifinku. Yace Shi ke
nan zan yi masa maganar idan ma ba a samu kwararriyar asibitin da za a magance mata
matsalara nan gida Nigeria ba ko nan Senegal sai a kawo ta tunda ba laifi suna da kwararrun
likitoci. Inna yaduwa tace: Dada dai ai ni kuma na gama magana kai ni kyale ni haka yara kun
zame min karfen kafa. Daga wannan ya yi watandaririya da ni sai wannan ya juyo ni sai ka ce
masa a tanda? Tana karashe fadar haka ba ta bari ya tanka ba ta datse kiran. Washegari Alh
Ahmad ya zo gidan ya tarar da inna yaduwa a falo tana matse lemon tsami a kofi ya zauna
yana gaishe ta. Ta amsa masa cikin sakin fuska. Yace: Me zaku yi da lemon tsami? Ta ce: Sha
zan yi kasan yana wanke dattin ciki. Shi yasa yake son zama da tsaffi ko banza zaka samu
magungunan gargajiya. Yayi murmushi yace; To ina Shuhuda da ba ku ba ta ta matse muku ba?
Ta kya6e baki tace: Wannan burkakkiyar yarinyar wani abu ta iya? Ya ce Kai inna rannan fa na ji
kina yabonta akan dambun da ta yi muku? Ta sake kya6e baki ta ce: Ai ranar ma sa'a aka ci.
Amma Shuhuda ba tasan komai ba daga kwanciya sai karatu, haka kawai yarinya ta tsiri wata
tsurfa ana magana da ita sai ta yi shiru idan an matsa mata ta shige daki ta kudundune cikin
bargo sai ka ce mai fama da lalurin basir saboda yawan kasala. Alh. Ahmad ya girgiza kai yace:
Yau ma ke nan baccin ta ke? Tace: Ba fa bacci take ba. Kwance kawai take koda yake dazun
tace min wai kanta na yi mata ciwo sannan cikinta na yamutsawa na ce ta dauko lemun tsami ta
sha ta ce min. Wai ita rabonta da shan lemun tsami tun tana ciki kafin a haife ta don haka yanzu
ba za ta sha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login