Showing 36001 words to 39000 words out of 83144 words

Chapter 13 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11080

yiwa kaina, to
amma saboda wannan dalilin yasa na kan ajiye tambayoyina har zuwa ranar da zan samu
MATA'UL HAYAT.
To wannan fa nasan zan iya soyayya har na samu damar amsa tambayoyi, nawa da na wasu
ma gaba daya.
Ta daure masa kai matuka. Ya girgiza kansa, ya ce:
Shike nan, ni kuma zan jiraci wannan rana domin nasan ni ma zan samu MATA'UL HAYAT idan
har na samu rasarar auren ki.......
Ta sake daga masa hannu.
Yah Isah kada ka jefa rayuwarka a hatsari, kada ka yi gaggawar sanya SOYAYYA a tsakaninmu,
domin tana da mayukar hatsari.
Gargadi ne nake yi maka, ba shawara ko izina ba, idan ka ce zaka sanya soyayya a tsakaninmu
hakan zai iya haifar da TASHIN HANKALI, RUDANI, TAKAICI da kuma NADAMA marar amfani.
Tana kammala zancenta ta yi gaba yana kwala mata kira amma sam ta ki tsayawa.
Ya dade zaune a gurin yana murmushi, yasan ba komai ne ke ta6a mata zuciya ba illa zafi da
radadi ko na ganowa da ta yi, can baya ta yi soyayya da wani a tubalin sha'awa, ko kuma
mutuwa ta gitta ta raba su. Wadannan kuwa ababe ne masu radadi.
Ya mike tsaye ya nufi cikin gidan. Don tarar da shuhuda ya sanyayar mata da zuciya, sai dai
yana shiga falon ya tarar da Inna yaduwa zaune akan kujera ya nufi dakin shuhuda.
Ta sanya baki ta kira shi, ya dawo ya zauna a dayar kujerar tace:
Kada ka shiga gurin shuhuda, domin kana shiga zaka sanya ta tayar da hankalin mutane. Haka
ta tsiri wannan dabi'ar tun bayan kammala sakandiri dinta, da zarar an 6ata mata rai sai ta shige
daki ta yi ta kuka. Ai ka gani abin da ya faru kwanaki ko?
Don haka kyale ta, me ya faru ne a tsakaninku?
Yace: Daga na ce ina sonta shine ta shiga wannan yanayin.
Inna yaduwa tace: Kyale ja'ira kawai ci gaba da son nata, inshaa Allah idan rabonka ce zaka
aure ta.
Bayan an gama sallar magriba Isah bai samu komawa gida ba, saboda tun kafin su shiga sallah
Alh Rabi'u ya ba shi sakon da zai kaiwa Alh sada(Mahaifinsa) ya saka a mota, saboda haka ana
gama sallar kai tsaye can gidan mahaifin nasa ya nufa.
'''''''''''' ''''''''''''' ''''''''''' ''''''
Duk yadda ya so ya koma gida da wuri hakan ya ci tura, saboda kannesa da suka saka masa
shagwa6a lallai sai ya zauna sun sha hira tunda tun bayan dawowarsa bai zauna da su ba.
Dole ba don ya so ba ya zauna. Tun yana duba agogo yana tunanin i wannan lokacin yana tare
da su shuhuda a dakinsu yana yi musu hira, har tara da rabi ta yi ya tuna dai-dai lokacin yake
tofe musu dakinsu da addu'a ya koma dakinsa.

Goma dai-dai ya kissima yanzu su shuhuda sun dade da yin bacci, saboda dama a daddafe ake
yin hirar da ita zuwa karfe tara da rabi.
Saboda haka sai ya sare, gwiyoyinsa suka yi sanyi, ya tabbatar ya yi rashin wannan daddadan
hira da suke yi musamman ma da yake dokin ta yau zata fi kowacce hira armashi, tunda har ya
samu damar furzar da abin da yake cikin ransa.
Sam ba shi da niyyar tafiya, har sai da Hajiya Safiyya tace: Wai kai ba zaka yi harama ka koma
gida ba? Ta dubi su Asma'u tace: Ku tashi ku je ku kwanta.
Haka ya mike ya yi musu sallama ya hawo motarsa ya nufo gida. Lokacin da ya iso gida sha
daya saura kwata. Kai tsaye 6angarensa ya shiga don yana da tabbacin sun dade da yin bacci.
Bayan ya gama duk abubuwan da suka zamo al'adarsa misalin karfe sha biyu da mintina
takwas bacci ya yi awon gaba da shi.
******* ******* *****
Shuhuda ina son!
Nasan haka''
Shuhuda ina kaunarki.
Na fi kowa sanin haka.
Shuhuda tunanina ya zan yi da raina.
Shine abin da ke nukurkusar min da zuciya, yake saka ni damuwa, amma kada ka damu mafita
ta zo gare ka.
Ta ya ya?
Mikewa ta yi daga inda suka yi tsugunnon su duka biyun, ta soma taku yana kallonta hat ta isa
inda garken kananun dabbobi suke, irin su kaji, Agwagwa, Talo-talo da tantabaru.
Yana kallo ta zama ZAKANYA ta soma taune kananun dabbobi, yana so ya daga baki ya yi
magana ya kasa, yana so ya yi amfani da kafafuwansa ya zura da gudu ya kasa.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤18¤¤
Yana nan tsayen ta gama taune kananun dabbobin nan tas! Sannan ta koma halittar mutum, ta
yi murmushi, tace:
Yadda ka ga na taune dabbobin nan haka zan yiwa 'YA'YAN CIKINKA, HANTA, KODA da ma
ZUCIYARKA. Wannan ita ce kadai mafita, idan ba haka ba babu wata mafita da zamu yi amfani
da ita, mun riga mun yi SAKACI wanda 'yan magana ke cewa: TUN RAN GINI RAN ZANE!
Firgigit Isah ya yi ya farka daga baccinsa mai kunshe da wannan hargitsattsen mafarki. Ya duba
agogon da ke dakin, amma bai iya ganin komai ba, saboda duhun da ke da akwai.
Sai da ya yi amfani da malatsin kunna fitila, sannan haske ya gauraye dakin. Karfe daya da
mintina shidda, tabbas tun ran gini ran zane na fadar shuhuda a mafarkinsa. Ai tunda ya dawo
ya saba kullum sai ya yi musu hira kafin daga bisani ya yi musu addu'a ya ja musu kofa ya
koma nasa dakin. Idan haka ne an tunatar da shi yau bai yi musu addu'ar ba kamar yadda ya sabar musu.
Saboda haka cikin mutuwar jiki da kuma sauran baccin da ke tare da shi ya mike don nufar
dakin nasu ya yi musu addu'a tukunna ya dawo ya dora nasa baccin.
Mamaki ya kamashi na hango haske da ya yi ta tagar(window) dakin bayan ya shigo falo, shin
me yasa ba su kashe kwai ba kafin su kwanta? Tagar ya fara nufa, ya kai hannu ya yaye

labulen tagar a hankali.
Das! Zuciyarsa ta buga sakamakon abin al'ajabin da ya gani, Inna yaduwa na kwance tana ta
sharar bacci cikin nutsuwa, ya yin da shuhuda ke gefenta ita ma baccin take.
Amma cikinta na juyawa kamar ana wana wani abu, kwatankwacin yadda idan an harba kwallo
ta ke juyawa kafin ta isa ga inda ake so.
Tambayar da ta fara darsuwa a zuciyarshi ita ce, shin dama haka shuhuda ta ke bacci, ko kuwa
ba ta da lafiya ne?
Amsar ta gaza samuwa a gare shi ya kuma dauki tsawon lokaci a wannan hali kafin daga bisani
ya bar jikin tagar ya nufi kofar shiga dakin.
A nan ma ya dauki lokaci yana ma ya dauki lokaci yana kallon abin al'ajabi, ga shi dai dare ne,
kuma a yanayin da shuhuda take kwance zai tabbatarwa dik wanda ya ganta lallai bacci ta ke,
hakan ke nan yana nufin haka ta ke baccinta, cikinta na juyawa kamar kwallo? Tunda da ace ba
ta da lafiya ne, hakika da ba a haka za a ganta tana baccin ba hankali kwamce. Ya karasa kusa
da ita cikin tafiyar sanda don kada karar takunsa ya tayar da su daga baccinsu, ya sani za su
tuhume shi me ya kawo shi dakinsu a irin wannan lokacin wanda ya ke da yakinin idan zai
kwana dubu yana fada musu addu'a ya zo ya yi musu ba zasu aminta da hujjarsa ba.
Idanuwanta a lumshe suke tabbacin dai baccin ta ke yi. Zuciyarsa ta dinga ayyana masa
abubuwa da dama, ganin Inna yaduwa ta gyra kwanciya tsoro ya kama shi, kada ta bude ido ta
ganshi. Don haka ya yi sauri ya durkushe har sai da ya ji motsinta ya gushe sannan ya mike
cikin tafiyar sanda ya koma bakin kofa ya yi musu addu'o'in da ya saba tukunna ya fice ya ja
musu kofar a hankali bayan ya kashe musu wutar. Koda ya koma dakinsa kasa kwanciya ya yi,
zaune ya yi a gefen gado yana tunani, shin idan haka shuhuda ta ke bacci ya ya ke nan idan ya
aure ta? Amsar da ta gaza samuwa ke nan, amma lallai yana cikin zullumin tabbatuwar hakan,
domin yana da tabbacin ba zai samu sakewar da yake son samu ga matar aurensa ba
matsawar aka ce haka shuhuda ta ke bacci. Har gabatowar asubah Isah bai samu ya runtsa ba,
karshe ma sai da ya sallaci sallan asubah sannan ya koma kan gado ya nade. Bacci mai nauyi
ya yi awon gaba da shi. ***** ****** ***** Shuhuda! Isah ya kirayi sunanta lokacin da ta ajiye
masa abin karin kumallo. Ta juya zata fita ba tare da ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu ba. Turus
ta tsaya ba tare da ta juya ta kalle shi ba, fuskarta a daure sam babu alamat fara'a, sake cira
baki ya yi ya ambaci sunanta, sannan ya dora da cewa: Dawo ina son magana da ke. Ba ta juyo
ba, tace: Idan dai akan maganar jiya ce babu amfanin dawowata, tinda na fada maka ra'ayina.
Ya yi murmushi, yace da ita: No, ba wannan maganar ba ce, dawo ki zauna. Ta juyo idonta a
rusune ta samu kasan kafet ta zauna ta yi shiru. Yace: Dago idonki ki dube ni, sannan na isar
da korafin da nake son isarwa gare ki. Babu musu ta dago ido ta dube shi, duban da ya haifar
da abubuwan al'ajabi, daga ciki ya ji wani irin tsoronta ya shiga zuciyarshi, ta yi mishi wani irin
kwarjini, tambayar da yake son ya yi mata na abin da ya faru a daren jiya bayan mafarkin da ya
yi ta koma zakanya ta cinye dabbobi ya shiga dakibsu ya ga cikinta na juyawa kamar kwallo. Ya
ji tambayar ta yi masa nauyi a baki, ba zai iya furtawa ba, sam! Da sauri ya rusunar da kansa
kasa ba tare da ya iya isar da korafin rashin gaishe shi da ba ta yi ba. Ita kuma ta kasa cire
idonta a kansa, kallonsa ta ke, kuma sauraron abin da zai fada ta ke, amma har tsayin lokaci:-
Can tace: Ka tsayar da ni, kuma ka ki yin magana. Bayan ina da abubuwan yi.
Da kyar ya cafko abin da zai ce, bayan ya yi takaitaccen murmushi, yace: Dama cewa zan yi ya
kamata mu je katsina. Saboda me? Ta bukata a takaice.

Saboda mu gaishe da Goggo Asma'u da kuma mama karima.
Tace: Sai ka fidda lokaci. Ya ji dadin hadin kan da ta bashi, yace: Ina ganin kafin na tafi Ibadan
ya kamata mu je ko?
Tace: Duk yadda ka gani.
Yace: Sai muje karshen satin nan.
Tace: Ba matsala..... Shi ke nan?
Ya daga mata gira.
Tace: Allah ya kaimu lafiya.
Ta karashe maganar tana yunkurin tashi, ya ambaci sunanta cikin jarumta, yanason ya yi mata
maganar abin al'ajabin, amma ko da ta juyo suka hada ido ya sake jin wani nauyinta ya kama
shi. Yana tunanin ta yadda zai furta maganar a gare ta, ai da kunya.
Jin ya yi shiru bai ce komai ba ya sa tace: Yah Isah ka cika matsala, ka ce ka gama magana na
mike zan ta fi kuma ka tsayar da ni, to me kake son na yi maka?
Yace: Dama cewa zan yi ki ba ni lambar wayarki? Tace: Waya? Ka manta ba ni da waya?
Fuskarshi ta nuna yanayin mamaki, don a zahiran bai san ba ta da waya ba. Yace: Kina nufin ki
ce sam ba ki da waya? Faduwa ta yi ko sacewa aka yi?:
Ta girgiza kai tace: Ko daya, ni ban ta6a rike waya ba. Yace: Saboda me? Tace: Haka nan!
Yace: To zan saya miki. Ta girgiza kai a karo na biyu. A'a ka barta.
Ko akwai dalili? Ya bukata. Eh-to, Ni ban iya rike waya. Yanayinsa ya sake bayyanar da
damuwa. Me ya samu hannun naki? Maimakon ta amsa, sai ta jefo masa tambaya. Kai me yasa
kake son dole na yi amfani da waya?
Ya yi murmushi, yace: Saboda a yanayinki na budurwa zaki bukaci rike waya ko don saurayinki
ya kiraki.
Ta hade rai, tace: Me ye kuma haka?
Jan aji irin na mata. Abin da ya ayyana a ransa ke nan, zahiran kuwa cewa ya yi.
Kamar yadda na bukaci yin mu'amala ta soyayya tsakanina da ke, har ta kaimu ga yin aure.
Tace: Bana soyayya. Kuma wannan yana daga cikin sharuddan haduwarmu da kai, muddin
wannan jigon ne zai dinga hada mu lallai zan kaurace maka don tsirar da rayuwar mu....." Tana
karashe fadar hakan ba ta jira cewarsa ba ta fice daga dakin, amma ya hango lokacin da kwalla
suka zubo daga cikin idanunta. Sai ya yi murmushi, ya ci alwashi ko ta ya sai ya ja hankalin
shuhuda zuwa gareshi, sai ya dandana mata zakin soyayya a ruhinta. Da daddare da ya shigo
dakin nasu domin yi musu hira, shuhuda nadewa ta yi a gado ta lumshe idanunta alamun ba ta
bukatar a yi hirar da ita ba wai don tana jin baccin ba. Ta yi bakam tana saurarensu, mafi
yawancin hirar duk akan zuwa katsina ne, Inna yaduwa tana cewa ita ma lallai sai an je da ita.
Yayin da isa ya jajurce babu inda za a da ita tunda tafiya ce ta matasa sabbin jini ba zasu
kwashi kayan tsufa su tafi ana musu wani gani-gani ba. A haka dai suka yi hirar ba tare da
shuhuda ba, karshe ya mike ya yi musu addu'a ya kashe musu wuta ya nufi dakinsa. Ya yi duk
abin da ya saba, ya kwanta bacci ya sure shi. Tarihi ya maimaita kansa, domin abin da ya faru a
daren jiya yau ma shi ne ya faru, mafarkin ya yi shuhuda ta koma zakanya ta shiga daji tana
cinye kananun dabbobi. Tana kammalawa da dabbobin ta dawo suffarta ta asali ta tsaya a
gabansa tana mai jifarsa da wani yalwataccen murmushi, tace: Kana son hawa keken shanu
don zuwa bigirena? Ya buda baki da nufin amsa mata ke nan, firgigi ya farka daga baccin nasa
yana raba idanu, yau dai bai baro dakin su shuhuda ba sai da ya tabbatar da ya tofe su da

addu'a, da ya dawo daki ya yi duk abin da ya saba yi. Illa abu daya wanda bai san ta yadda aka
yi ya manta bai yi ba, wato ADDU'A, shi dai yasan lokacin da ya yi wanka ya saka kayan
bacci(pyjames), sannan ya shiga duniyar gizo(internet) ta Lap-top dinsa. Da ya kammala da
wannan ya rufe lap-top din ya mayar da ita ma'ajiyarta, sai ya kishingida ya shiga tunanin yadda
shuhuda ta yi masa. Daga nan bai san lokacin da bacci ya dauke shi ba. Hakika rashin addu'a
ga rayuwar dan Adam wani babban gi6i ne, idan ya yi la'akari da jiya bai yiwa su shuhuda
addu'ar da ya saba yi musu ba, ya yi mafarki mai firgitarwa, wanda yake nufin tunasarwa a gare
shi na rashin yi musu addu'ar. Yau kuma ya sake mummunan mafarkinsa duk a sanadin rashin
addu'a don haka wannan IZNA ce gare shi da ma duk wani wanda ba ya addu'a ga lamuran
rayuwarshi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa a sarari. Alhamdulillah! Sannan ya mike tsaye
bayan zuciyarsa ta ayyana masa ya je dakinsu shuhuda ya kara tofe su da addu'a don nema
musu tsari daga shaidanun dare. Daram! Gabanshi ya yanke ya fadi lokacin da ya karasa a
cikin falon, ta taga ya hango hasken kwan lantarki. Ya dai san bayan ya yi musu addu'a sai da
ya kashe musu wuta sannan ya nufi dakinsa. Abu na farko da ya fara zuwa ranshi shi ne, Inna
yaduwa ko shuhuda daya daga cikinsu ya farka daga bacci ya kunna kwan lantarki watakila don
yin ibada ko kuma wani uzurin na daban.
Cikin dakiya ya karasa bakin kofa, yana tura kofar sai ya ji ta a bude ba a rufe ba. Yaye labulen
da zai yi idonsa ya yi masa tozali da al'amarin da ya faru a daren jiya a irin wannan lokacin,
wato cikin shuhuda yana juyawa kamar kwallo. Mamaki, tsoro, fargaba dukka suka durar masa
a lokaci daya, wai wannan wane irin rudadden al'amari ne ace mutum yana bacci cikinsa yana
juyawa kamar kwallo irin haka? Lallai ko tababa babu shuhuda ba ta sa lafiya, akwai cutar da ke
damunta, tunda haka nan ba zai yiwu cikinta ya dinga irin wannan juyawar ba, ko dai tana da
cutar kyambon ciki? Cikin sanda kamar yadda ya yi a daren jiya don gudun tayar da Inna
yaduwa, gaba daya jikinsa kyarma yake, ji yake kamar wani abu na fizgarshi karasawa inda
shuhuda ta ke, duk da cewar ya sani muddin daya daga cikinsu ta farka ba shi da hujja ko
kalaman da za su kare shi. Idan jiya yana da hujjar ya zo yi musu addu'ar da bai samu damar yi
musu ba, yau kuma mece ce hujjarsa? Zai ce ya yi mafarki shuhuda ta koma zakanya tana
cinye dabbobi shi ya sa ya shigo musu daki a dai-dai wannan lokaci? Hujjar ba mai kar6uwa ba
ce, illa ya sani tsautsayi ne ke fizgarsa. Idanu ya tsurawa cikin shuhuda har yanzu juyawa yake
yi kamar ana juya kwallo. Cikin shakku da rashin sanin fa'idar yin abin da yake yunkurin yi ya
daga hannu zai ta6a cikin, har ya kusa kai hannun ya yi saurin daukewa, sakamakon buhum
kirjinsa da ya tsananta. A karo na biyu ya sake kai hannunsa da nufin ta6a cikin, saboda
zuciyarsa da ta ke azalzalarsa ya ta6a cikin ya ji me ye yake juyawa haka? Wannan karon duk
kokarin da ya yi na hana hannun nasa isa ga cikin shuhuda sai da ya isa. Bisa ga tsananin
mamaki, hannun na isa cikin ya tsaya cak! Ma'ana ya daina juyawa kamar ace talabijin ce take
aiki aka sa hannu aka kashe ta. Da sauri ya dauke hannunsa yana ci gaba da tsura mata idanu,
har tsayin wani lokaci babu abin da ya kuma faruwa, cikin bai sake juyawa ba, haka kuma
shuhuda ba ta farka daga baccin nata ba. An shafe ya fi mintina takwas babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login