Showing 42001 words to 45000 words out of 83144 words

Chapter 15 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11088


alamun tabbatarwa. Sannan tacce: Karfe nawa zaku tafi katsinan? Yace: Sai sha daya. Tace:
Allah ya kaimu. Ya amsa da, Amin.
BABI NA TARA
RUDANI
Babu mai magana a cikin su biyun, tafiya kawai suke tamkar kurame, kowanne da abin da yake
sakawa a cikin ransa. Ga karar kira'ar Sheik Ahamad Sudeis na tashi cikin tausasshiyar
muryarsa, SURATUL MUHAMMAD ce ke tashi, wadda ta ke magana akan Manzon Rahama,
Manzon tsira, Manzon da babu kamarsa duk cikin Manzanni. Dan Amina baban fadima, Angon
nana khadija da nana A'isha, suruki ga sayyidina Aliyu(A.S) kaka ga Hassan da Hussain, wato

Annabin Annabawa, amintaccen Allah, Yardajjen Allah, Annabi Muhammad(S.A.W).
Surah ce wadda ta ke da muhimmanci akan kowanne musulmi yasanta, duk da cewa babu
surar da ba ta da muhimmanci ga kowanne musulmi ya sani a cikin littafi mai tsarki(Alkur'arni
mai girma).
Littafin da ya shafe kowanne littafi, tun daga kan Injila, Attaura, gami da zabura. Domin littafin
alkur'ani ya tattaro dukkan bayani kama daga kan asalin halittar dan Adam, abin da ke da akwai
a aljanna da wuta. Bayani na kissoshiin Annabawa, bayani akan ranar tashin alkiyama da
yadda aka halicci duniya da lahira, gami da abubuwan da Allah ya yi rantsuwa da su. Lallai Allah(S.W.A) gwanin HIKIMA ne, Arrahim ke nan mai saukar da rahma, Arrahim(mai
jinkan bayinsa). Arrazzaku(mai azurta bayinsa), Alfahatu(mai budawa bawa kofofin budi).
" An kar6o daga ubayyu dan ka'ab(R.A) cewar, manzon Allah(S.A.W) yace: Wanda ya karanta
suratul GASHIYA, to Allah zai yi masa hisabi mai sauki. Kuma wanda ya karantata akan rumbun
abincinsa to ya aminta daga cutarwarsa.
Haka kuma an kar6o daga ubayyu dan ka'ab(R.A) cewar; Manzon Allah(S.A.W) yace: Wanda
ya karanta suratul BALAD har zuwa karshen surar, to Allah zai amintar da shi daga fushinsa
ranar alakiyama.
Manzon Allah(S.AW) yace: Wanda ya karanta suratul LAIL, to Allah zai tseratar da shi daga
duhu guda biyu, duhun zunubi da kuma duhun kabari. Wanda ya lazimci karanta suratul Lail sau
dari har tsawon kwana arba'in tare da yin azumi da Riyadh(wato nisantar sa6o) to Allah zai yi
masa khasafi(wato zai samar da shi 6oyayyun ilmi). Wata rana Annabi(S.AW) ya cewa sahabbansa, shin ko kuna son Allah ya yi muku katanga
daga shaidan kamar yadda ya katange Yajuju da Majuju? Sai suka ce: Eh, Sai yace: To ku
karanta suratul QADR bayan sallar magriba, da bayan sallar asuba sau uku-uku kafin ku tashi
daga wajen da kuka yi sallar. Sannan sai kace: " Ya Allahu, Ya sahibul kadri farraji auni hammi
wakarbii"(ma'an
a:- Ya Allah, Ya mai iko, ka yaye min bakin ciki da 6acin rai).
Wannan duk daga cikin falalar alkur'ani ne, don haka alkur'ani rahma ne ga dukkan musulmi,
karanta shi na saka nishadi, sauraren kira'arsa na gusar da bakin ciki.
Har suka isa birnin katsina babu wanda ya yi magana daga cikinsu.
Sai da suka zo Welcome to katsina(sabon garin Dandagoro) a sannan ne Isah ya dago kai ya
dubi shuhuda tare da rage sautin karatun alkur'anin da ke tashi, yace:
Zamu biya NNPC mu sha mai, don na ga man ba zai ishe mu zuwa karare ba. Tace: To. Yaci
gaba da sulalawa da motarsa har ya shiga gidan man, ya jera layi a bayan motoci hudu da suke
gabanshi.
Shuhuda ta yi wata irin zabura tare da cewa: Subhanallah!! Da sauri Isah ya dago kai ya dube
ta, kokarin fita take daga cikin motar, ya riko gefen hijabin da ke jikinta, yace: Me ya faru? Ina
zaki??
Fuskarta cike da fara'a da kuma doki, tace: Wata kawata ce na gani, ga ta can, fita zata yi daga
gidan man. Ta karashe maganar tana nuna masa budurwar da ke kokarin shiga motarta kirar
hummer jeep da aka gama zubawa mai.
Kafin ya yi magana tuni har ta fita, ta karasa inda ta ke tana cewa. Shuhuda dama kina raye?
Wadda aka kira da suna shuhuda ta juyo cike da farin ciki suka rungume juna suna masu
murnar haduwa.

Isah da yake cikin mota yana hango su, ya ga kamar ya ta6a ganin fuskar.
Da farko da zai share, amma zargin da ya ke na kamar wata FUSKA da ya ta6a haduwa da ita
watanni hudu da suka shude a birnin MISRA ya sa ya gaza hakuri, ya yi fit! Ya bude mota ya
tunkare su.
Yana isa ya soma nuna bakuwar fuskar da dan yatsansa yana cewa: SHUHUDA IBN
KHADDAB? Ta dube shi cikin yanayin tuhuma gami da mamaki. Ita kanta shuhuda mamakin ne
bayyane a fuskarta, tace: Yaya ina kasan Shuhuda?
Bai amsa mata tambayarta ba, yace da dayar shuhudan.
Yaushe kika zi Najeriya? Ko kuwa dama dai maganata ce ta zama gaskiya ke 'yar Najeriyar ce
tunda har kika san kanwata?
Mamaki ya sake bayyana a fuskar shuhuda Ibn Khaddab. Ta mayar da kallonta ga shuhuda
Sagir Rabi'u tace: wannan kuma waye a gare ki? Shuhuda ta dubi Isah, tukunna ta maido da
duban nata ga dayar shuhudar tace:
Yaya na ne Isah, wanda nake fada miki?
Shuhuda ibn khaddab tace: Auhi, Allah sarki yayanmu, barka da yini?
Kin amsawa ya yi, saboda ya ga ta raina masa hankali zahiran, in bacin rainin hankali su hadu
da ita sannan yanzu ta nuna masa ba ta ta6a saninsa ba? Shuhudan ma ya dauke ta a wadda
ta raina masa hankali, kuma MAKARYACIYA, ya tambaye ta shuhuda ibn khaddab ta nuna
masa ba ta ta6a sanin mai sunan ba, sannan shuhuda ibn khaddab ta nuna masa shuhuda
kanwarsa ba ta santa ba, hasalima ba su ta6a haduwa ba.
To ta ya kuma suka san juna bayan ya ji shuhuda kanwarsa ta yi ikirarin shuhuda ibn khaddab
kawarta ce? Wannan salon rainin hankali ne da yawo da tunaninsa, abin da kuwa ba su sani ba
shi ne, hankalinsa ya wuce nasu bare su sa shi a RUDANI, sa6anin haka ma sai dai shi ya saka
su. Shuhuda ibn khaddab tace gaba da cewa: Na yi ta neman yadda za a yi mu hadu na sanar da
ke auren Sa'adatu ban samu ba. Shuhuda tace: Ayyah, ashe anyi auren Sa'adatu? Makaranta?
Ta fasa ci gaba?
Isah ya ga za su dauke shi shawaragi sun share da shi sun ci gaba da hirarsu, saboda haka
ransa ya sake 6aci, yace:
Shuhuda ina yayanki Abdallah ibn khaddab? Ta juyo da sauri alamun mamaki, sai ba tace
komai ba, ta dubi shuhuda, tace:
Takwara wai don Allah ina yayanki ya sanni hat yasan Ya Abdallah?
Shuhuda tace: Ni ma mamakin da nake yi ke nan, saboda ba a nan ya yi rayuwarsa ba, kuma
lokacin da ya dawo muna jarabawa har muka gama bai je makarantarmu ba, bare na ce ko a
can ya sanki, yasan kuma yayanki da yake kawo ki makaranta.
Isah ya shiga RUDANI matsananci da wannan bayani da ya ji suna yi, anya kuwa shuhudan da
ya hadu da ita ce a Misra yanzu a gabansa? Idan ba ita ba ce me ye alakar sunanta da sunan
yayanta da waccan shuhuda? Idan ita ce me yasa ta ke son yawo da hankalinsa?
Tun ranar da ya soma ganinta da salon yawo da hankalinsa ta fara, tunda ita ta soma yi masa
magana cewar ta ganshi kamar yayan Shuhuda Sagir Rabi'u, wannan kuwa idan ba kana da
alaka da sanin hakan ba babu yadda za ayi ace bincike na sanadin suna ya kasance idan sun
hadu ta shaida shi. .

Ci gaban labari.
.
Bayan basu ta6a haduwa ba.
Abin tambayar a nan shine me yasa suka yi amfani da wannan salon gare shi? Shin
kowaccensu sonsa ta ke yi ne shi yasa suke son juyar masa da kwalwa? A'a ba sonsa suke ba,
so suke su juya shi kai-kai ce, su rikita shi, su sanya shi cikin RUDANI, Su kuma tsotse ruwan
kansa bisa jagorancin shuhuda kanwarsa, don ita din ma ta nuna masa abubuwan RUDANI da
yawa, saboda ranar da ya ce yana sonta kin amincewa tayi, daga baya kuma ta zo masa da
amincewarta.
Tunda ya gane manufarsu kamata ya yi ya bi su da yadda suka zo masa. Murya a taushe kuma
yana murmurshin da yake kara masa kwarjini, murmushin da yake fito da cikar HAIBARsa(
Asalin sunan littafin)
Yace: Kada ki damu shuhuda ibn khaddab, haka nake na kasance mai binciken duk wata mace
mai sunan kanwata, don haka ne ma zan iya cewa na sanki, na san yayanki Abdallah Ibn
Khaddab.
Yanayinta ya nuna bata gamsu da bin da ya fada ba, amma jin karar hon din da ake ta doka
mata wanda ke nuni ta tsarewa na bayanta hanyar fita, sai ba ta samu damar tankawa ba. Ta
dubi shuhuda, tace: Don Allah minti daya na dai-daita tsayuwar motata.
Kafin ta amsa mata tuni har ta shige mota, Isah ya lura da zoben da ke yatsanta, wanda iri daya
ne sak da wanda ya sa yowa shuhuda kanwarsa da shi lokacin da ya tsaya a kasar Misra.
Da sauri ya dubi yatsan shuhuda kanwarsa inda ya saka mata zoben, yana nan daram, saboda
haka kama ce, ita ma ta sayi irinsa. Sai ya koma motarsa ya matso da ita, ya kasance motoci
biyu ne yanzu a gabansa.
Kafin ya baro jikin motar har an sanyawa daya daga cikin motoci biyun da ke gabansa mai,
saboda haka sai bai yi garajen barin gurin ba, ya tsaya. Cikin sa'a kuwa ita ma motar dake
gaban tasa ba wani mai yawa aka zuba mata ba, sai shi. Ya fadi adadin yawan da yake so, aka
zuba masa sannan ya iso gurinsu da motarsa. Yana isowa shuhuda ibn khaddab ta cewa shuhuda.
To takwara sai gani na biyu, da fatan zaki cika alkawari idan bikin ya tashi ki kawo mana katin
gayyata, da dai nace bazan kara zuwa bikin class mate dinmu ba, amma tunda ke ce da
yayanmu ba ji, zan zo.
Shuhuda ta rusunar da kanta kasa saboda kunya, tunda Isah na tsaye a kanta.
Shuhuda ibn khaddab ta dubi Isah tana murmushi tace:
Yayanmu Allah ya sa yadda ka binciko ni saboda ina da sunan kanwarka, idan lokacin aurenku
ya yi ka iya binciko ni ka kawo min katin gayyata. Kuma idan na koma gida zan sanarwa Yah
Abdallah na hadu da abokinsa ISAH SADA RABI'U.
Tana kammala fadar haka ta bude murfin mota ta shige.
Isah tsaye ya yi sararo yana kallonta, ya kasa koda motsin kirki ne, ambatar cikakken sunansa
da ta yi ya kara jefa shi cikin rudani.
Koda yake a wani 6angare bai kamata ya yi mamakin jin haka ba tunda ya ba su dama wata
kila a cikin lokacin shuhuda ta samu sararin fayyace mata cikakken sunansa, ko kuma dama ta
dade da saninsa,idan ya yi la'akari da maganganun da suka tattauna, wai makaranta daya suka
yi.

Ta gabansa ta zo ta wuce yana kallonta tana kallonsa, tamkar tana son fada masa wani abu
amma ba ta tanka ba, illa murmushin da ya ki 6acewa daga fuskarta.Shuhuda tace: Yaya mu
tafi ko?
Ajiyar zuciya ya soma yi, kafin daga bisani ya girgiza kai ya nufi mota.Ta bi bayansa, duk suka
shiga cikin motar ya soma jansu zuciyarsa ta gaza nutsuwa, haka kuma ya kasa daurewa, yana
son cikakken bayani game da alakar da ke tsakanin shuhuda kanwarsa da shuhuda Ibn
Khaddab, don haka yace Amma kun sakani a RUDANI sosai. Ta dube shi tace: Wane irin rudani kuma yaya?
Yace: Wannan shuhudar ita ce muka hadu fa da ita a birnin Misra na tambaye ki kika ce baki
santa ba, ita ma ta ce ba ki santa ba, amma ita ta sanki ta hanyar bincike a dalilin sunanku ya
zamto daya, sai ga shi na ganta a Najeriya wanda a can ta tabbatar in ba ta ta6a zuwa Najeriya
ba, a yadda na lura na kuma fahimta a cikin kalamanku kun dade da sanin juna, kamar ma a
makaranta daya kuka yi, to mutumin da yace bai ta6a zuwa Najeriya ba ta ya kuma ya yi karatu
a Najeriya har yasan wasu mutane da ke rayuwa a cikinta? Thats my question (wannan ita ce
tambayata)
Shuhuda tace: Kai yaya anya kuwa ita ce wadda kuka hadu kuwa? Ita fa wannan a nan katsina
ta ke, karatu ya kaita kano ta zauna gidan yayan mahafinta. Da farko ba ma shiri, saboda
lokacin da na yi karatu ina rayuwa da hankali ne na awa biyu, sai gab da zamu soma jarabawa
muka soma shiri har ma muke zama mu yi hira. A nan ne ma ta sanar da ni ita 'yar katsina ce,
su uku mahaifanta suka haifa, daga ita sai yayanta Abdallah wanda yake karatu a Misra, sai
kaninta Yusufa su ke nan mahaifinsu suka haifa. Mafarin ke nan suke samun ingantacciyar
kulawa daga mahaifan nasu...
Har muka gama makaranta ba tasan gidanmu ba, ni ma haka dama kuma ba zuwa bikin
kawaye nake ba, shi yasa tun da muka gama makaranta ba mu sake haduwa ba sai yau.
Ya gama sauraronta ne kawai, amma bai gama fahimtar inda kalaman nata suka sa gaba ba,
shi dai ya yarda ya kuma amintar ma kansa, wannan shuhudar da suka hadu a Misra ce, wadda
ke bin kasashe yawon majalisin malamai, shuhudan da ta sanar da shi iyaye da kakanninta
dukkansu 'yan asalin Misra ne. Ya fi amincewa lokacin da suka hadu a Misra wani sanadi ne ya
kaita, amma ta 6oye masa saboda sun shirya hakan da kanwarsa shuhuda, wannan shi ne
hakikanin abin yarda.
Tammat bihamdillah
Gare ku fa makaranta? Kun yarda? Anya kuwa? Kai ko ni ban yarda ba, akwai dai yadda akayi.
Shin ina Uncle Hamza da zuwairiyyarsa?
Kada fa a yi danyen kasko mana? Ai kun fahimci labarin MATA'UL HAYAT ko? Idan ma ba ku
fahimta ba, zaku fahimta ne idan kuka ji muhimmin sakon da ya kunsa.
Kada dai ku manta da tarin abubuwan da suka faru tun daga littafi na farko zuwa na biyu.
Musamman rayuka uku da aka rasa saboda shuhuda, da sauran abubuwan da suka biyo baya?
Izra'el,Libhas,Tanzif me ye alakarsu da shuhuda? Ina aka samo keken doki da ta ke zuwa Misra
kamar yadda ta fawa uncle Hamza?
Yakub, Abdallah ibn khaddab, da shuhuda ibn khaddab duk me ye alakarsu da shuhuda.
Kai-kai-kai!!! Akwai fa yawa abubuwan, amma dai mu yi hakuri,juriya zuwa MATA'UL HAYAT-3
don jin yadda zata kaya.
Shin Hamza ko Isah? Akwai dai sadaukarwa, waye mai sadaukarwar? Kuma ta ya ya?

ada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)Book 3
¤¤21¤¤
.
KUSKURE.
.
Idan aka duba littafi na biyu page na 150 sakin layi na karshe an yi amfani da sunan Abdallah
Ibn Khaddab a maimakon Abubakar Ibn Khaddab har zuwa karshen littafin a haka ya kare.
Matsalar ta faru ne daga gare ni ne, da parko Abdallah shi ne asalin sunan, bisa wani dalili na
maida Abubakar, na ci gaba da bi ina replace da Abubakar, tuun daga page din da aka samu
matsalar gaskiya ban duba ba, lokacin ba ni da lafiya, kuma har aka gama aikin ban ga
kuskuren ba, sai da na yi nisa a 3 sannan ma na fuskanta. .
A gafarceni bisa wannan kuskure.
Zahra u Baba Yakasai.
.
Allah ya jin kanta da rahama ya saka mata da Aljannah.....ameen.
.
Ci gaban labari..
.
Shuhuda ta dan dube shi a kai kaice, tukunna ta ci gaba da cewa. 'Shuhuda tana da mutumci,
ta na da kaifiyya da bincike akan abin da ya shafi harkar taimako. Ka ganta dai yarinya ko,
amma wallahi idan ka ji irin mutanen da ta binciko ta taimaka musu abin sai ya ba ka mamaki
matuka. Shi yasa a rayuwa duk wanda ya kasance yana da kaifiyya ya ji dadi'. Wannan kalma ce da Shuhuda Misra ta yi amfani da ita a lokacin da ta ke sanar da shi yadda
aka yi tasan kanwarsa Shuhuda, ta ce tana amfani da bincike ne gami da kaifiyya. Wannan ma
kadai ya isa ya zamo hujja agare shi, Shuhudan Misra ce ya yi tazali da ita a Nigeria.
Ya so ta ba shi lambarta, gami da adireshin gidansu a can Misra ta goce masa, kuma babu
amfanin da ba shi lambarta don gudun kada idan sun hadu a Nigeria ta nuna ba ta sanshi ba ya
kira wayarta ta yi kara a gabansu asirinsu ya tonu, shirin da suka yi ya ruguje.
Lallai idan haka ne ya ci a jinjinawa wannan kaifin hankali nasu, tunda har suka iya wannan
tufkar ba tare da an samu rauninsu ba kasancewarsu MATA masu tarin rauni, da kuma
kuruciya. Domin mace mai shekaru sittin a duniya ba ta kai namiji mai shekaru ashirin kaifin
hankali ba, su dama mata haka suke, rauni ne da su. Abin da suke tunanin idan sun yi dai-dai
ne, amma idan maza suka tace sai aga abin ba dai-dai ba.
.
(Sadin Mama yar Anty, ni dai na ce what a man can do, woman can do far much better )
.
Ku yi hakuri yan uwa na mata, kada kuce na yanke mu, gaskiya ce idan kuwa gaskiya ta zo ana
son fadarta komai dacinta.
.
Shiru ya yi bai kuma tanka mata ba domin ta gama yawo da hankalinsa, ta gama kunce masa
duk wata jijiya ta tufka da warwarashi.

.
BABI NA GOMA
TABDIJAN!
Shagari low-cost nan ne unguwar da Haj Asmo ta ke, a kofar gidan suka tsaya suna jiran
maigadi ya bude musu get. Koda ya bude Isah ya sulala da motar cikin harabar gidan, Shuhuda
ta bude kofa ta fita ta nufi hanyar shiga cikin gidan.
Isah ya sanya baki ya kirayi sunanata. Ta juyo tana dubanshi ba tare da ta tako ba.
Ya ce, "ki tsaya mu shiga da tsarabarsu mana".
Cikin shagwaba ta ce masa, "mu tara shiga mana, ba sai a samu wadanda zasu shiga da
tsarabar ba?"
Yana kyabe baki ya ce da ita.
"Shi ke nan".
Yara kusan su shida suka tarar a falon suna kallo, da ya ke sun san Shuhuda don haka suna
ganinta suka mike da sauri suna mata oyoyo-oyoyo.
Ta dauki Sajida 'yar shakara hudu ta saba a kafadarta.
Hayaniyar yaran ce ta fito da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login