Showing 24001 words to 27000 words out of 83144 words
tabbas
duk yadda aka yi akwai SANAYYA tsakaninsa da wanda ya kira kansa da Abubukar. Idan ya yi
la'akari da maganarsa ta karshe, wai ya gaishe masa da ALH. BABBA.
Mahaifinsa shi suke kira da Alh Babba, idan haka ne akwai alakar, ta ina? Waye Abubakar ibn
khaddab? Yaushe ya kira lambarsa?
Tambayoyin da suka damu kansa ke nan. Suka hautsina masa tunani ya rasa sukuni sat!
Washegarin ma bai samu kadaicewa da Shuhuda a makaranta ba, ana tashi ya neme ta ya
rasa, ko motar da ake daukarta bai ga lokacin da ta tsaya har Shuhuda ta shiga ba, bayan tun
kafin a tashi ya ke zubawa kofar ajin nasu idanu har ya soma hango dalibai na fitowa daga ajin
suna tafiya bai ganota ba.
Wannan dalili ne ya sa shi yanke shawarar zuwa gidan su Shuhudan. Kamar yadda ya shirya
zuwa gidan nasu haka ya dauki hanya yana tafe cike da tunanin abin da zuwan nashi zai haifar.
Yayin da ya isa gidan kafin ya tsaya a kofar gidan ya hango Yakub ya fito daga cikin gidan ga
dukkan alamu wani guri za shi. Sai uncle hamza ya bishi yana yi masa hon, sai da suka koma
can karshen lungun sannan Yakub ya tsaya, ya juyo yana duban uncle hamza da ke kokarin
fitowa daga cikin mota. Don Allah ka yi hakuri, wallahi ban san dani kake ba. Uncle hamza yace: Kada ka damu ab yini
lafiya? Yakub yace: Kalau, jiya ina ta magana bana jinka.
Dif! Wuta ta daukewa uncle hamza ya rasa mai zai ce dashi. Yakub yace: Shi yasa nbake
tunanin sauya layi saboda matsalar network da MTN suke fama da shi a kasar nan, kullum
daga wannan matsala sai wannan matsala.
Kwanakin ba ya ma don wukakanci da mutum ya saka kudi sai su wafce masa, suka 6illo da
wani tsari Magic number na yaudara.
Shi dai uncle hamza shiru kawai ya yi yana kallon Yakub da hakikance yana magana ba ya
jinsa. Bayab shi yasan da ya kira lambar Yakub din ba shi ya samu ba, kuma ma ai kiransa aka
yi bayan ya gama kira ba a dauka ba. Watakila gaskiyar Yakub din ne matsalar daga network
ne, lambarshi ta shiga wayar wani daga kasar waje. Yakub ya yi murmushi, tukunna yace: Hala mutumiyar taka ka biyo? Don tace min kwana biyu
ba ku gaisa ba. Murmushin karfin hali uncle hamza ya kirkiro yana shafa kasumbarshi yace:
Hakika an yi haka.
Yakub yace: Ai matsalar ba daga gare ta ba ne. Daga gida ne, an yi mata shamaki da kula
saurayi, har sai ta kammala sakandire dinta don haka idan ka ga ba ta kulaka ba kada kaga
laifinta.
Ina sauri zamuje taron matasan unguwa da muke yi duk karshen wata. Sai ga ni na biyu. Mun
gode da kaunar da ka nunawa tsatsonmu. Ya karashe maganar yana kokarin barin gurin. Uncle
Hamza ya yi saurin zura hannayensa cikin aljihu ya fiddo kudi yana cewa:
Ga wannan ka sha ruwa.
Yakub ya tsaya yana duban uncle hamza tare da kudin sannan yace:
Ayya na gode amma mu ba ma amfani da irin wadannan kudaden. Yana karashe fadar haka ya
yi gaba abinsa.
Mamakin uncle hamza ya sake hauhawa, sam bai gamsu da maganganun yakub ba, me yasa
su ba su amfani da irin wadannan kudaden bayan kuma a kasar Nijeria suke rayuwa? Lokaci
daya maganar Shuhuda ta dawo masa a rai, lokacin da ya bukaci sanin gidan su.
" Gidan mu?.... Gidanmu da nisa.... Misra fa.... Akan wani keken doki nake zuwa.... Kullum fa na
koma gida sai na suma, mamata ta yi ta kwara min ruwan sanyi, sannan nake farfadowa...."
Idan ya tattara maganganun Shuhuda da kuma maganganun da suka gudana tsakaninsa da
yakub sun isa su zame masa hujja na cewar yana mu'amala da ALJANU a matsayin MUTANE.
Wani kunci da takaici suka lullu6e masa zuciya kawai ya rufawa kansa asiri ya rabu da lamarin
Shuhuda ya sa wa kansa salama ya cire sonta daga ransa shine kawai abin da zai sama masa
nutsuwa. Idan ba haka ba kuwa zai yiwa rayuwarsa BARA DA BANA, ma'ana ya hana
zuciyarsa samun matar da zai rayu da ita akan son da yake wa Shuhuda, wanda a bayyane
yake babu aure tsakanin jinsin mutane da aljannu.
Ko da ma ace zai iya auren aljana, ma'ana an halasta aure a tsakanin jinsin bil'adama da jinsin
jinnu, to ba zai auri Shuhuda ba. Tunda bai san manufar da ta ke so da shi ba. Bai san me ye
shirinta na kulle zuciyarsa da sonta ba.
a Hausa Book stories
MATAUl HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤13¤¤
Abubuwa da dama sun faru wanda sai yanzu ya samu kakkarfar hujja da zai saka Shuhuda a
jinsin jinnu. Alh sada, shi ma ya kasance daga jinsin jinnu, an rike shi ne don kawar da
tunaninsa ya aminta shuhuda mutum ce don ya aure ta a kaddamar da shirin da aka shirya.
Tana karatu a makarantar ne don an samu tabbacin zai shigo makarantar koyarwa. Ta ko'ina dai
babu hanyar da za a layance masa yace Shuhuda mutum ce ba aljana ba! Idan an bar zuciya
da tabo ba a yi mata magani ba. Lallai za a samu rudani. Komawa ubangiji a dukkan tsanani da
rudani, ko ma jin dadi shi yake haifar da nagartacciyar rayuwa. A duba. ****** ****** *****
BABI NA SHIDA
ANA ZATON WUTA A MAKERA......
Tun daga wannan rana uncle hamza bai kara shiga shirgin shuhuda ba, sam ya nuna kamar bai
san da wanzuwarta a cikin makarantar ba. Ko aiki ya ba su ya ga ta yi kokari ba ya nuna ya
damu bare ya yaba mata kamar yadda yake yi a da.
Sai ma ya koma duk lokacin da zai shiga ajin nasu idanunsa rufe da bakin tabarau, wai duk don
kada ta ga wallensa bare ta raina shi. Tunda ya gane aljana ce yta ke rayuwa acikin mutane.
Shi ba zai iya tona mata asiri ba, haka kuma ba zai kulata ba. Idan ma tana tunanin zata cimma
wani buri ne a gare shi, to ta sha karya, ba zata ta6a samun wannan damar ba.
Idan ya tuna yadda ta dinga yi masa yawo da hankali, sai ya ji haushin kansa. Ai tuni ya kamata
ace ya gane shuhudan aljana ce idan ba haka ba ta ya mutum zai ce bai san waye bil'adama
ba, bai san shi wane irin jinsin halitta ba ne?
Ai daga ji ma kasan wata kullalliya ce kawai ake kullawa.
An murda an tufka murdaddun al'amura don jefa shi a cikin tarkon da ba zai iya fitar da kansa
ba. To amma da yake shi Allah mai taimakon bawansa ne, duk da ratar dake tsakanin jinsin
bil'adama da jinnu hakan bai hana yayewar yanar da aka dankara a idanuwansa ba. Ya gane ko
wace ce ita. Wannan ma abin godiya ne ga Allah da ya ni'imta shi da wannan ni'ima, tunda har ya kare shi
daga kaidin jinnu. Ya sani ba hikimarsa ko kwarewarsa da dabarunsa ba ne ya ku6utar da shi
ba. Illa wata BAIWA da HIKIMA ta Ubangiji.
Wannan hukunci da ya dauka ya dan rage masa zafin da yake hada wa kansa, yanzu sam ba
ya irin wannan zaman na dogon tunanin ya ya lamarin shuhuda ya ke? Saboda yasan yadda
aka yi masa alayen irin na mutan 6oye (Jinnu).
To kuma ga shi an yi walkiya ya ga komai, saura da me? Tabbas dole ne ya samu nutsuwa, a
da kam ya susuce komai ya kunce masa, ba shi da wani tunani sai na yadda al'amuran
shuhuda suke har wani kira yake kwalwa ce ta yi mata yawa. Ashe ba kwalwa ba ce tsabar
rainin hankali ne da yaudara irin na shiryayyen lamarin da bai san dalilin shiryuwarsa ba. WAYE UNCLE HAMZA?
""""""""""""""""""""""""""""""
HAMZA A. Babba shine asalin sunan nasa dan asalin jihar katsina a karamar hukumar Batsari.
Mahaifina Alh Babba mai lakabin sunan Abdullahi sananne ne a fadin birnin katsina. Domin ma
aikacin gwamnatin tarayyar birnin katsina ne.
Ya rike mukamai da dama a ganiyar kuruciyarsa kafin daga bisani ya ajiye aiki saboda girma da
ya kamashi. Matansa hudu na aure, ko wacce kuma ta hayayyafa da shi. A takaice dai mutum
ne mai yawan iyali saboda yana koyi da sunnar ma'aiki.
Yawan 'ya'yansa bai sa aka samu nakasu ga tarbiyyarsu ba, tsaye yake tsayin daka gurin
kulawa da tarbiyyar yaran nasa.
Hamza yayi karatunsa na firamare a nan cikin kauyensu karare da ke cikin karamar hukumar
Batsari. Da ya gama ya tafi Technical Mashi, inda ya fito da takardu masu kyau, bugun farko na
Jamb dinsa ya samu 258point. Don haka bai samu matsala ba lokacin da ya nemi gurbin karatu
a A.B.U ZARIA. Tunda hamza ya fara karatunsa ba shi da wata matsala har ya kammala lokacin da ya dawo
gida yana hutun jiran aiki.
Akawai wata yarinya zuwairiyyah diyar kanin mahaifinsa da ta so shi tun can baya, to amma sai
aka samu akasi, zuwairiyya irin shagwa6a66un yaran nan ne, ba ta iya komai ba ga ta katuwar
bagidajiya irin dai yaran nan da ake cewa: GIRMA YA RIGA WAYO.
Hakan ne ma ya sa koda ya nunawa mahaifinsa rashin amincewarsa ga lamarin ba su zafafafa
ba, amma daya daga cikin kannen mahaifinsa mai suna Binta ta zafafa abin, wai ita don me
zuwairiyya zata ce tana son hamza zai ce ba ya sonta. Kuma a biye masa? Wannan salon
gur6ata zumunci ne. Rigima aka yi sosai, dama can hamza ba ya shiri da Gwaggo binta, wata irin masifaffiyar mace
ce, haka nan ta bushi iska ta zo gidan ma ta yi ta ruwan masifa.
Da yake Alh Babba mutum ne mai tsananin hakuri da son zumunci ba ya damuwa da halayyar
'yar uwarsa. Ba ma ita kadai ba duk cikin sauran 'yan uwansa shi daban yake bai dauki rayuwa
da zafi ba.
Duk hutun da hamza yake dawowa yana zuwa gaishe da dangin mahaifinsa amma ba ya zuwa
gidan Gwaggo binta saboda muguwar tsanar da ta yi masa tun yana yaro, har cewa take wai
hamza kamar musaya aka yi aka ba wa Alh Babba shi, amma sam bai yi shige da tsatson
gidansu ba. Idan 'ya'yanta sun zo gidan, misali ace an yi katari lokacin hamza ya zo hutu ba ya kula su.
Saboda yaran sam ba su da kunya wannan ya sake hura wutar kiyayyar Gwaggo binta da
hamza.
A lokacin da yake aji uku a sakandire dinsa wani zuwa ziyarar dalibai da mahaifinsa ya je yake
sanar masa dan Goggo Binta ya rasu, ko a kwalar rigarsa bai damu ba. Don haka da ya dawo
hutun ma bai je yi mata gaisuwa ba.
Ana haka kuma auren Goggo binta ya mutu, tace: zata dawo gidan Alh BABBA kin amincewa
ya yi. Don yasan zama da Binta tashin hankali ne ba karami ba. Sai dai gidan wani dan'uwan ta
koma.
Ta yi zaman zawarci na shekaru hudu sannan ta yi aure. A lokacin hamza ya tafi ZARIA. Shi ma
auren ba wani dadewa ta yi ba ta fito saboda rashin hakuri da munanan halayenta ba kowane
namiji ne zai iya zama da irinsu Binta ba.
Ta koma zaman zawarci har hamza ya gamo karatunsa ya dawo ya fara aiki a nan cikin jahar
katsina. A wata makaranta MARIAMA AJURI MEMORIAL SCHOOOL Goggon tasa ba ta yi aure
ba.
Albashinsa na farko da na biyu zuwa na uku ya sayi tamfatsetsen filoti a nan cikin katsina
unguwar kanada. Tafiya ta tafi ya gina gidansa ya sayi mota sai kuma maganar zuwairiyya ta
kuma danno kai don har lokacin ba tayi aure ba.
A wannan karon an so fin karfinsa, to amma sai ya roki alfarma a makarantar da yake koyarwa
a mayar da shi wani reshen, tunda makarantar ta kafu tana da rassa da dama a garuruwa
daban-daban.
Yayi wannan hikimar ne don ya yiwa su zuwairiyya nisan zango. Idan aka ga ba ya kusa an gaji
a bata wani mijin ta yi aure.
Da farko za6i aka ba shi cikin Kaduna, Jos da kuma Bauchi. Ya duba duk cikin wadannan
garuruwan babu wanda ya kwanta masa a rai, ya dauki lokaci yana tunanin garin da zai za6a.
Kwatsam aka ce an turo shi Kano dama suna bukatar karin malamai. Ya yi farin ciki da hakan
ko ba komai kano gari ne na cibiyar kasuwanci idan yaje kanon zai iya samun wani kasuwancin
da zai yi ko ya saka hannun jari a wani kamfanin.
Hakan ko akayi, yana zuwa birnin kano ya fara aiki, a hankali kuma ya fada harkar kasuwanci
ya ba wa wani abokinsa kudi masu yawa yana yi musu kasuwanci a nan kasuwar kwari.
A kuma makarantar ne ya hadu da ALJANA! Kamar yadda ya kira SHUHUDA.
WANNAN KE NAN!!!
****** ****** *****
Rashin kulawar da uncle hamza ba ya yiwa Shuhuda ya sama masa nutsuwa na gajeran lokaci
ne kawai. Domin lokacin da su shuhuda suka shiga aji shida suna gab da soma jarabawa
tsumin abin nan ya taso masa haikan. Ya dinga jin a duniya babu macen da yake son ya aura
sama da Shuhuda. Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin
ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda
har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya.
Wato ranar da hamza zai aure ta. Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za
su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu).
To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya
saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin
jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar
da yake da hujjojin kiranta Aljana. Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa.
Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta
shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin
wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa. Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai
ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa
kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba.
Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa
gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar
zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba.
Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a
falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda.
Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da
ya jike shi sharkaf Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a
lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta
ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta
zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta.
Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za
su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu).
To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya
saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin
jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar
da yake da hujjojin kiranta Aljana. Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa.
Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta
shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin
wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa. Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai
ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa
kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba.
Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa
gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar
zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba.
Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a
falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda.
Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da
ya jike shi sharkaf Zuciyarsa ta jagule, yana son furtawa yana tsoron abin da zai biyo baya. Shin
zai amince ya sake saka rayuwarsa a tarkon aljana? So wani irin makahon abu ne, duhu ne da
shi wanda yake makantar da zuciya gami da idanu tsinkaye da tarin kalubale. Idan haka ne so ya taka muhimmin rawa ga uncle hamza tunda ya hana ganin duhun son da zai
fada.
Cikin rashin walwala ya mike tsaye ya shiga bandaki ya yi wanka, sannan ya dawo falon, ya
dauki wayarsa yaga yana da kiran da aka rasa(missed call) guda sha uku, ya duba duk lamba
daya ne aka