Showing 48001 words to 51000 words out of 83144 words
Chapter 17 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf
gidan.
A cikin mota Isah n eke ta yarfa uwar masifa, yana kyamar tsatson Uncle Hamza tunda har suke
jifar Shuhuda da miyagun kalamai irin wannan.
Musbahu ne kawai yake tausarsa, a haka har suka isa gida.
BABI NA GOMA SHA DAYA
ANYA KUWA?
Misalin karfe goma da rabi na safiya su Isah sun gama shirinsu, Haj. Asmo da iyalenta su ka
rakosu har bakin mota, Musbahu na tsokanar Shuhuda.
“Ke bakauya sai ki shirya ina nan zuwa Kano neman aurenki, tunda nag a kowane tsuntsu ma
hawa bishiyar yake”.
Isah ya auna masa sakon harara, y ace.
“Sai ka maida niyya, albishir daya zanyi maka, kafarda ta kaika Kano neman auren Shuhuda,
ba ita zata maido ka ba”.
Nusaiba tana dariya, t ace.
“Kai ma yaya Musbahu da taya dora bari kake, ina kai ina wannan yariyar mai shanyayyar kafa?
Ai ka wuce ajinta, kana ganin ko iya daura zani bata iya ba”.
“Musbahu ya fashe da dariya, y ace,
“Ai dama ba neman mai saye ake ba”.
Haj. Asmo t ace, “Kai idan zaku tafi ku tafi, kada ku tsaya yi min shirme”.
Ta mayar da dubanta ga Shuhuda t ace.
“Idan kun isa kya gaishe min da Haj. Karimar Allah Ya sauke ku lafiya”.
Su ka amsa mata da ”amen”.
Yayinda suka shige cikin motar suka tafi.
Suna tafiya a motar da farko babu wanda yake Magana, sai daga baya da tunanin ya yiwa Isah
yawa, yasan kuma Shuhudan ce kadai zata iya amsa masa tambayoyin da yake da su, don
haka ya dago kai ya dube ta.
Kanta a rusune yake a kasa, tana kallon yatsun kafarta. Yace.
“Shuhuda!”
Ta dago kai kadan tana dubansa. Ya ci gaba da cewa.
“Waye Yakub?”
Ya daga mata kai.
“Eh, domin a maganganun malaminki ya ambaci wani yayanki Yakub, ni kuma a sani na duk
tsatsonmu bamu da Yakub, sai nake tunanin ko daga dangin mahaifiyarki ne?”
Ta girgiza kai, tukunna t ace,
“A’a, ni sam ban san waqni Yakub ba, ni ma nayi mamaki da na ji y ace waqi wani yayana
Yakub”.
Yadda ta yi maganar akwai alamun gamsarwa a ciki, don haka ya yarda haka din ne,
soki-burutsu ne da zafin rabuwa da masoyi ya sa Uncle Hamza ambatar sunan Yakubu a cikin
maganganunsa.
To amma fa akwai alamar tambaya, kuma akwai aiki ja agabansa, saboda ya lura kamar
Shuhudan tana son Uncle Hamza.
“Shuhuda wai da gasket kin san Hamza yana sonki?
Ya jefa mata wannan tambayar a ba zata.
Ta girgiza kai, t ace .
“Eh, ya taba fada min wai ya je gidanmu bayan ya je gurin Babanku ya zo namu gidan ya hadu
da wani yayana Yakub ya sanar da shi yana son aure na. Sai dai ni ban dauki maganar da
muhimmanci ba, saboda nasan duk gidanmu bam u da Yakub, watakila gidan su wata
Shuhudar ce ya je ba niba”. Ya dan samu nutsuwa kadan a zuciyarsa, ya ci gaba da cewa da ita.
“To ya ni kuma fa?”
Ta ce “ban gane ba?”
Ya dan juyo kadan yana kallonta, yace, “Ma’ana soyayyata a gareki”. Ya karashe maganar yana
mai langwabar da kai. Tayi murmushi, t ace, “Ai kai ne masoyina, me kake tantama?” y ace. “Na
sani ko za a so wani bare akan na gida?” Sai ta kama dariya, t ace. “Yaya Isah kenan, wani
lokaci RANAR NAKA………. Sai naka, wani lokacin kuma BARE ke zama NAKA”. Ya dubeta cikin rashin fahimtar inda ta dosa da maganarta, y ace. “Ban gamsu ba”
.
.
Toh pa, ni dai nace na gamsu, don Shuhuda sai bare wato MAI JAR KOMA! Lol
.
Ta ce, abin da nake nufi a nan shine, wani lokaci zaka ga bare shi yake SADAUKAR da komai
na rayuwarsa akan abin da yake so, amma sai ka gad an uwa ya kwanta rashin lafiya wadda
yak e bukatar jinni amma duk cikin ‘yan uwa sai a rasa wanda zai iya sadaukarwa ya bayar da
jininsa. Ka gamsu?” Yayi murmushi, y ace,.....
da Hausa Book stories
MATA’UL-HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤24¤¤
Ya yi murmushi, y ace. “Na gamsu, sai dai ki sani bana daga cikin wadannan mutanen……….”
Ta katse shi da cewa. “Kash! Ba ba nufi na ken an ba, kuma ai ba a san mai cin tuwo
ba……….”
Yana dariya ya karshe mata Karin maganar cewa. “Sai miya ta kare , amman kin san hasashe
da tsinkaye na sa makeri yunkurin narka karfe ba tare da yana da tabbacin hakansa zata cinma
ruwa ba ko?”
Ta ce, “A’a, dutsen day a ke cikin ruwa ai bai san ana rana ba, don haka ka daina ma tunanin
akwai wani babban shamaki a cikin soyayyarmu”.
Ya girgiza kai cike da jin dadin yadda yadda ta karfafa masa gwiwa, y ace,. “To Allah Ya shige
mana gaba”. Ta amsa masa da . “Ameen”. Y ace, Yadace a samara min kyauta ta musamman
wadda zan gain na rinka jin dadi”. Ta yi dariya t ace masa”.
“Kyauta? Sha kuruminka, zan maka kyauta ta bajinta mai matukar muhimmanci”.
Yace, “Wace kyauta ce haka mai muhimmanci?”
Tace Dan mutum! Ko ba ka so na samara maka da?”
Ya juyo dube ta, wani sanyin dadi ta ratsa zuciyarsa tunda har tana yi musu fatan
samun sanyi idaniya.
Y ace, “Allah Ya kaimu lokacin”. Bata amsa ba, sai tayi hamma.
“Y ace ya dai? Bacci ne, ko yunwa?”
Ta ce, “Ina jin bacci ne, don jiya ban samu bacci ba”.
“Yace mai ya hana ki yin bacci?” Yayi tambayar zuciyarsa akuntace, don yayi has ashen tunanin
Uncle Hamza ne ya hanata bacci. Tce, “Naje wani taro ne”. Ya juyo ya dube ta, y ace. “Taro?
Wane irin taro, kuma a ina? Ta ce, “Ni ma ban san wane irin taro ba, kuma ban san gurin ba”. Ta
ce, “Eh kasan akwai abin da za ka yi kai kanka ba kasan me ka yi din ba”. Ya girgiza kai, y
ace.”A’a, na fi aminta cewar, kin yi mafarki ne, ko ba haka ba?” Ta ce, “Ina tunanin mafarki
amma ni da nasan ban kwanta bacci bay a zan aminta mafarki na yi?” ya ce, “Hakan yana iya
faruwa, wata kila saboda gajiyar hanya yasa kika fita hayyacinki har bacci ya sace ki baki sani
ba, a cikin baccin kuma kika yi mafarki ana gudanar da wani taro da ke. Sai muyi fatan Allah Ya
sa taron alkhairi ne”. Ya karashe maganar yana kallon hanya, yau ji shiru ba tanka ba, sai ya
dan waigo, ya yi katari da ita tana sharer bacci.
Murmushi kawai ya yi, yasan har yanzu akwai gajiya a tare da ita, ya ci gaba da tafiya akan titi
cikin nutsuwa da kwarewa.
Suna isa Karare ya juyo ya dubeta, har lokacin bacci take yi, ya ambaci sunanta, ba ta farka ba
sai ya kai hannu ya dan bugi cinyarta. Da sauri ta bude ido kamar ta tsorata. Ya yi murmushi y
ace,”Sha bacci ko?” Sai ta kuma dube-dube kamar ba ta yarda da kanta ba. Ta ce. “Ya na
ganmu a nan?” Y ace, “To a ina dama za ki ganmu? Ko so kika yi ki tashi daga baccin ki ganki
cikin gida?” Sai ta yi gum da bakinta. Ya ce, “Nuna min hanyar gidan”.
Ta dinga nuna masa yana shiga lungu har suka isa kofar gidan Alh. Jamilu, ya tsayar da motar
Shuhuda ta fito fuskarta ba yabo ba fallasa ta taryi yaranda suka fito da ga gidan suna yi mata
sannu da zuwa.
Ta kama hannun Amira zuwa cikin gidan, Isah ya dade a cikin motar bai fito ba yana kallonta
har ta shige cikin gidan. Sannan ya sauke ajiyar zuciya yana auna matsanancin son da yake
mata. Lokaci daya haduwarsa da Shuhuda Ibn khaddab a birnin Misra da kuma jiya da suka
hadu a gidan mai ta nuna bata sanshi ba sam. Abin duk ya dawo ya zauna masa a ransa
daram!
Yaran suna da salon barkwanci a cikin lamarinsu, abinda ya ayyan ke nan a ransa.
Sannan zuwansu gidan Uncle Hamza da abinda ya faru shi ma ya dawo masa. A bayyane ya
ce. "Zan sadaukar da komai na rayuwata don ganin na kwalaka a kasa, domin ni na sha
wahalar sonta tun tana cikin tsumma, tun bata mallaki hankalin kanta ba, har zamana cikin
jajayen kunne bai sauya zuciyata daga alkiblar sonta ba...." Shuhuda ta katse masa zancensa yayinda ta sunno kanta a tagar motar tana murmushi ta ce,
"Yaya, ka shigo mana ka tsaya a mota?"
Bai ce komai ba ya bude motar ya fito ya bi bayanta zuwa cikin gidan.
Haj. Karimatu ta karbe su hannu bibbiyu, kuma taji dadin yadda ta ga Shuhuda da Isah sun
hada kansu, sika shigo mata da tsarabar da suka zo da ita. Alh. Jamilu ya dawo cin abincin
rana ya tarar da bakin nasu. Ya dubi Shuhuda ya ce. "Ni kam bana marhabin da zuwanki tunda
kinki zama da mu". Shuhuda tayi murmushi kawai, shi kam yana son ace Shuhuda ta dawo
gurinsu da zama ko don yadda ya ke ga Haj. Karima na bukatar hakan, musamman tunda ya
aure ta bata taba haihuwa ba. Amma da ya ke ita mace ce ta gari, sai ta rungumi 'ya'yan da
Binta ta fita ta bari tamkar 'ya'yanta. Haj Karima ta ji dadin karar da ya nuna mata, ai a so naka
ma wata martabace. Isah ya karbe zance da cewam "Ai yanzuma sai da na tursasa mata ta zo".
Shuhuda ta juyo da sauri, ta ce. "Kai Yaya kar muyi haka da kai, ni fa na ce maka mu zo nan
din". Shima sai ya auna mata harara cikin sigar wasa ya ce. "Kun ji ta da son kai". Alh. Jamilu
ya ce. "To na ji ko ma ta ya akayi kuka zo munji dadi, kuma mun gode". Ya soma nufar dakinsa,
Haj Karima ta bishi a baya.
Sun sha yini a kauyen karare, sannan daga bisani suka yi haramar tafiya kano, Alh Jamilu ya
ce. "Ai na dauka zaku yi mana sati". Isah ya girgiza kai, ya ce. A'a, dama cewa muka yi bari mu
zo mu gaisheku". Ya ce, "To madaLlah". Ya dauko kudi zai ba su, sai Shuhuda tayi saurin cewa.
"A'a Baba ka barsu, ai ga kudi can mun ba Umma ta baka sako daga Alh". Isah ya cika da
mamaki, da yaushe Alh ya bawa Shuhuda kudi shi bai sani ba? Amma sai ya basar, shi kuwa
Alh Jamilun sai zuba godiya yake yana cewa. "Allah ya kara girma, ai kyautar dattijai ba a
mayarwa".
Haka suka yi musu sallama suka tashi. Sun soma tafiya a motar, Isah ya ce. "Wai ke na
tambayeki". Tayi shiru bata tanka mishi ba. Ya ci gaba da cew. "Yaushe Alhaji ya ba ki sakon
kudi da kika bayar?"
Ya ji shiru ba ta tanka ba. Sai ya dago kai ya kalleta, ya ce. "Kina ji ina yi miki magana amman
za kiyi shiru ki kyaleni?"
Har yanzu ba ta tanka ba, ranshi ya sake baci, sai ya faka motar a gefen hanya ya juyo gaba
daya yana kallontta. Fuskarta a daure ta ke tamau kamar ma bata damu da shi ba.
Ransa idan ya yi dubu ya baci, cikin kakkausar murya ya ce mata. "Shuhuda ba magana nake
yi miki ba ki ka yi banza da ni?" Ta dago kai ta ce. "Me ka ce?" Ya hasala da maganarta, ya ce.
"Wannan wane salon rashin kunya ne haka?" Ta ce "kai ka ji ni dai Isah, me nayi na rashin
kunya?" Baki ya hangame yana kallonta cike da mamakin abin da ya fito daga bakinta, sam ba ta damu
da abin da ta fada ba ko ya bata masa rai ko bai bata masa ba, ita dai ba ta damu ba. Ya ce.
"Tambayarki nake, yaushe Alhaji ya baki sako ban sani ba?" Ta murguda baki ta ce. "Kuma lallai
idan zai aikeni sai ka sani tunda kai kadai ne jikansa mai 'yanci?" Ya kara hawa sama ya ce. "Ko
ba ni kadai ne jikansa ba, ai naga tare muka fito da ke ko? Ya akayi ban ga lokacinda ya baki
kudin ba?"
Ta ce, "Idan zai bani wani abu ne? Me kake nufi? Ni fa ban son shiga sharo ba shanu, ina
ruwanka?" Ya jinjina kai yana kallonta, ya ma kasa tofawa, sai kawai ya ja motar suka tafi ko
wanne na hura hanci.
.
BABI NA GOMA SHA BIYU
GA KOSHI GA KWANAN YUNWA
Alhaji Rabi u yana zaune a dakinsa rike da carbi yana lazimi, Isah yayi Sallama ya shigo
fuskarsa a daure. Zaunawa yayi akan kujera, yayinda Alhaji Rabi u ya dago kai yana murmushi,
ya ce. "Ya akayi ne mazajen? Na jiyo muryarku kuna shigo wa". Isah ya dan saki fuska kadan,
ya ce. "Barka da yini". Alhaji Rabi u ya amsa masa. "Yauwa, an dawo lafiya?" Ya ce "lafiya,
suna gaishe ku". Alhaji Rabi u ya ce, "Muma muna amsawa". Isah ya gyara zama sannan ya ce.
"Alhaji Jamilu ya ce ayi maka godiyar kudin da ka aika masa dasu ta hannun Shuhuda". Alhaji
Rabi u yayi murmushi ya ce. "Babu komai ai shi magidanci komai kudinsa yana bukatar
taimako, bare kuma irin Alhaji Jamilu, Ni kam bani da bakinda zan yi masa godiya akan rikon da
yayiwa Karimatu, tunda ya aure ta dai-dai da kwana daya bai tab kawo min korafinta ba, haka
itama, ba kuma taba jin ance anje gidansu da yaji ba". Ya karashe maganar yana alhinin
rabuwa da Karima a cikin ahlin gidansa. Isah ya gaza yin hakuri, ya ce.
"Wai Alhaji yaushe ka bawa Shuhuda sakon kudin? Kuma mai yasa baka bani ba a matsayina
na miji?" Alhaji Rabi u ya dube shi da yanayin rashin fahimta, ya ce.
A a, don zan bada sako dole sai a gabanka, ko kuwa kai kadai ne dan sakona?
Jin yadda Alh. Rabi u yayi maganar kamar acikin hasala ne, sai bai ji dadi ba, kuma dai
gaskiyar Shuhuda ne, ai ba shi kadai ba ne jika ga Alh. Rabi u, to don me zai damu kansa akan
an bawa Shuhuda sako ba shi ba? Ko da yake ai wani bangare dole ne ransa ya sosu, ai shi na
miji ne, dama gaba ya ke da Shuhuda, zai di kyautuwa ace shi aka damkawa duk wani sako, ko
don ta girmama shi, a'a duk ba ta wannan ba, me yasa lokacinda za a bada sakon ba a bayar a
gabansa ba, kuma ba a sanar da shi an bata ba, sai dai kawai yaji ta bada sakon, me hakan ke
nufi? Muryar Alh. Rabi u ta katse masa tunanin da yake.
"Isah kada dai ka ce min kana daga cikin mutane masu kyashi ga 'yan uwansu? Ai ko kana
daga cikin irinsu bao dace ka nuna kyashinka ga Shuhuda ba. Musamman idan kayi la akari
nan gaba kadan zata zamto mata a gareka, ka ga kuwa,wannan hali bai dace da kai ba sam".
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤25¤¤
Da sauri Isah ya girgiza ka, ya ce. "Ba haka nake ba Alh, sam ban kyashi akan ka nunawa
Shuhuda soyayya, ai ita ma jika ce gare ka, kuma marainiya. Shi kam maraya ana son a na son
a nuna masa kauna a sarari ko don kada maraici ya dameshi".
Alh. Rabi u ya saukar da ajiyar zuciya ya ce, "Ko da naji, kasan zamanin ne ya lalace, sai ka ga
dan uwa yana kyashin dan uwansa ya samu ci gaba, Musamman ga mata da miji, idan ya
kasance matar ta fi mijin samun hanyoyi alkhairi, sai ka ga mijin na nuna mata tsana duk
saboda haka, baya tunanin ko wane Dan Adam da hanyar arzikinsa". Alh. Rabi u ya kawar da
wannan hirar, ya dora da cewa. "Ya maganar tafiyarka Ibadan?" Isah ya ce, "Tana nan, mako
mai zuwa zan tafi". Alh. Rabi u ya ce, "To sai a kula, a san mutumcin kai da kiyaye addini.
Nasan san ka mutum ne mai yawan ibada, saboda haka sai ka dage kada kayi watsi da addu a
domin addu a takobin mumini ce, duk wanda ya juri yin addu a a rayuwarsa ba zai tabe ba".
Nasiha mai ratsa bargon jiki Alh. Rabi u ya yi wa Isah, sannan daga bisani sukayi sallama, isah
ya fice daga dakin.
Kwana hudu sam Isah Isah ya rasa kan Shuhuda, ba ta kulashi, idan tana zaune a falo da zarar
ya shigo sai ta tashi ta shige kuryar daki. Shi bai ga abin fushi da bata rai ba akan wannan dan
sabanin da suka samu ba. A ganinsa tunda har rashin fahimta ne ya kamata ta tsaya ta saurare
shi, amma ta kiya, ta ki yi masa uzuri a matsayinsa na dan Adam wanda yake da yawan
ajizanci. To sai bai nuna mata ya damu da wannan hali da ta kirkiro musu ba, amma ya damun
fushin nata na nukurkusar mai zuciya.
.
KUNGA MAZAN KIRKI, BA IRIN SU 'O'O BA! lol.... (Sadin mama)
.
Ana yau gobe zai tafi Ibadan yana zaune a falo shi da Inna Yaduwa suna hira wani yaro ya
shigo.
"Wai ance ana sallama da Shuhuda"
Isah da Inna Yaduwa suka dubi juna duba na mamaki isah ya dago kai ya dubi yaron ya ce.
"Waye ke nimanta?" Yaron yace. "Wai inji Hamza ne". Isah ya bata rai ya ce da inna yaduwa.
"Wani malamin makarantarsu ne yake neman ya shigar min hanci a kudundune, haka fa da
muka je Katsina ya nemi tarwatsa mana farin ciki". Inna Yaduwa tayi shiru bata ce komai ba,
yayinda Isah ya dubi yaron ya ce. "Ka je ka ce bata nan". Har yaron ya juya zai fita, tsallam!
Shuhuda ta fito daga daki tana tsayar da yaron. "Ka ce masa ga ni nan zuwa". Inna Yaduwa da
Isah suka sake kallon juna, yaron ya fice yayinda Shuhuda ta koma daki ta dauko gyale ta fito
falo, ta nufi hanyar fita. Inna Yaduwa ta ce. "Ke Shuhuda ina zaki je? Ca na ke ance baki nan?
Shuhuda ta juyo tana kallon Inna