Showing 63001 words to 66000 words out of 83144 words
yasan an bawa Uncle Hamza auren
Shuhuda tunda yaga fuskarsa cike da annuri an kira shi ne domin a ba shi hakuri, a kuma
kunsa masa bakin cikin dab a zai gushe gare shi bs abadan abidina. Wato shi kadai ne yake
cikin kuncin zuciya, tunda ga Shuhudar ma sai washe baki ta ke tana jin dadin za a aura masa
wanda take so. Take ya ji kamar ya tashi ya fice kada a hauda jininsa.
Yayinda shi kuma Uncle Hamza ya sake jin wani nishadi ya mamaye masa zuciya, musamman
ma ganin yadda aka tara mutane da yawa, ciki kuwa hard a Alh .Sada mutuminda ya san alakr
Shuhuda shi wato mahaifi gareta, ganin Isah yana hada rai ma yasa shi jin nishadi ko babu
komai yasan yayi masa kub daya, ma’ana ya kasa shi. Bayan Uncle Hamza ya gaisheda su Alh.Sada y dube shi tare da cewa. “Na je makarantarku
nemanka an ce min kun fita Misra kai Mahaifinka asibiti, ya jikin nasa?” kansa na sunkuye a
kasa y ace ”da sauki, sun ma wuce Saudi-Arabia shi da yayana”. Alh. Sada yace. “Allah Ya kara
masa lafiya, amma ta ya ka samu labarin neman da ake maka?” a wannan karon said a ya
dago kai cike da mamaki, y ace. Yakub ne ya je har asibitin da muke ya duba mahaifina, sannan
ya sanar min sakonku”.
Sai aka shiga kallon-kallo tsakanin iyayen, Alh Rabi u ya ce "wane Yakub ke nan?" Mamakin
Uncle Hamza ya sake bayyana, ya ce. "Yayan Shuhuda!" Alh Sada ya maimaiita maganar,
tukunna yace. "Ai mu nan gidan ba mu da mai irin wannan sunan ma Yakub". Jin wanna batu,
sai Uncle Hamza ya yi tsuru tsuru, ya tuna can baya da ya fadawa Shuhuda ya je gidansu har
ya hadu da Yayanta ta nuna mamaki, to ya lamarin yake? Alh Ahmada ya ce. "Yaya kawai
agabatar da abinda ya assasa taron". Alh Sada ya dubi Shuhuda ya ce, "Ga Isah, ga Hamza
dukkan su suna ikirarin samarinke ne, don haka sai ki fada mana wanda yayi miki ciki a cikinsu
idan kumma babu daya sai ki fada mana wanda ya aikata wannan aika-aikar" da ga Isah har
Hamza ko wanne ya zabura ya mike tsaye cikin kaduwa, suna girgiza kai Alh Sada ya daka
musu tsawa yace. "Kun ga ku zauna". Suka zauna jiki a sabule, Isah ya ce "Wallahi ba ni ba
ne".
Shi ma Uncle Hamza ya ce. "Na rantse da girman zatin Ubangiji ba ni ba ne". Kafin wani ya yi
magana a cikinsu, Shuhuda ta mike tana murmushi ta ce "Baba ku yi min afuwa, zan je na
shigo da baki gasu can harabar gida".
Ran kowa ya baci, wato su zata mayar abokan wasanta, yaushe aka aiko ga bakin bare ta ce
haka? Sai dai kafin wani ya tanka tuni ta kai bakin kofa. Alh Sada ya biyota da hanzari yana
kira, har sai da suka fito harabar gidan. Lalle kuwa ya ga baki su uku, mace daya maza biyu,
turus! Ya ja tunga ya tsaya cike da tsorota ya Shuhuda tasan da zuwan bakin? Bai ga lokacinda aka kira a waya bare kuma turo mata sako ta duba ba. Yayin da ita kuma
Shuhudar ta rungume macen suna fara'a. Daya daga cikin mazan ya mika wa Alh Sada hannu
ya ce, "Baki ne daga Misra akan zaman da kuke yanzuu muka iso, kada ku damu, ku aminta da
mu". Alh Sada ya tsayar da zuciyarsa ganin yadda suka zo musu cikin salama, ya ce. "Ba
damuwa". Ya yi musu jagoranci zuwa cikin dakin. Uncle Hamza ya mike tsaye da sauri yana
nuna daya daga cikin bakin, ya ce. "Yauwa ga Yakub din". Shima Isah ya mikke yana nuna
sauran bakin biyu, ya ce. "Abubakar, Shuhuda me ya kawo ku nan?"
Alh Rabi u, Alh Ahmad, Alh Sada da Inna Yaduwa suka dinga kallon juna cikin mamaki.
a Hada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
29
Yakub y ace, “ku kwantar da hankulanku, sannu a hankali”
Yana fadar haka suka zauna, sannan su Isah ma suka zauna, sai dai gaba dayansu suna cikin
rudani. Bayan sun zauna Yakub din ne ya soma Magana.”Dan Allah ku yi hakuri da bakuncin da
muka kawo muku katsaham, akwai babban dalili na yin haka, dalilin kuwa ba zai rasa nasaba
da boyayyen sirri ba wanda muke bukatar nutsuwa daga gare ku. Da fatan fahimtarmu bias
kyakkyawar fahimta”. Ya mayar da dubansa ga Inna Yaduwa, y ace. “Inna ke mace ce, muna
bukatar idan ba zaki damu ba ki fita domin gudun razani a gareki. Idan kuma har zaki dake, ki yi
hakuri da kaddarar da ta faru, ba matsala”. Inna Yaduwa ta dubi Yakub cikin takaici, a ganinta
ya raina ta, yaushe a matsayinta na babbar mace yaron da a haife ta haife shi zai ce ba zata iya
dauke dafin da zai fada ba? Ta ce, “Shekaruna sittin da uku, a haife na haifeka, kuma dukkan
zafin kalma ba zata wuce ta rashin ba, ni kuwa na rasa mahaifana da dana Sagir, kuma na yi
hakuri, sai sanadin gurbata rayuwar jikata ne b azan dauke dafin ba?” Yakub ya yi malalacin
murmushibtukunna y ace. “ki yi hakuri Inna, ba nufi na ke nana ba, amma babu komai tunda
nag a alamar zaki nuna juriya ai shi kenan”.
Ba ta tanka ba shi kumja ya ci gaba da cewa. “wani labari ne za mu baku bias yarjejeniya, da
kuma alkawari”. Alh. Sada gwanin zuciya, y ace. “kun ga don Allah su waye ku? Kada ku zo
kukawao mana raini”.
Alh Rbi’u y ace, “ka ga Sada saurara”. Ya dubi Yakub ya ce “muna saurarena”. Yakub ya gyara
zama, sannan ya dora da cewa, “Ni sunana Yakub, wannan kuma Abubakar, macen it ace
Shuhuda. Mun kasance tare da ku tsayin lokaci….. koda yake ba wannan ke gabanmu ba,
muna a gabar sanin wani sirri da ke lillube a cikin sirri”. Ya dora idanunsa akan Alh Rabi’u y ace.
“Alhaji yarjejeniyar da zamu yi da ku it ace, ku amince zaku sauraremu har sai mun gama ba ku
labarin da zamu ba ku tukunna zaku tambaye mu abin day a shige muku duhu. Sannan
alkawarin, za ku yafewa wanda ya assasa komai laifinsa”. Alh Rabi’u y ace, “zamu amince da
yar jejeniya, amma maganar alkawari babu ita, tunda bam u san mai laifin ba…….. Hasalima
dai babu yafiya ga mutumin day a kunsa mana bakin ciki ba tare da yayi nadama ba”.
Abubakar ne wannankaron ya magantu, inda y ace. “Tunda harm u muka nemi hakan kun san
akwai babban dalili. Na farko dai shi mai laifin bay a cikin duniyar nan bare ya iya neman afuwa,
kuma a matsayinku na iyaye dole zai kasance kun e mutane na farko da zasu yi fatan ‘ya’yansu
su sadu da rahamar Ubangiji”. Babu wanda ya fahimci inda maganganun suka dosa, kuma
gaba daya yanayinsu ya nuna rashin fahimtar. Yakub ya ci gaba da Magana da cewa muna
rokarwa Marigayi Alh Sagir gafara a gurinku iyayensa bisa wani boyayyen sirri da ya assasa”.
Inna Yaduwa tayi tsagal t ace, 2wani ne y ace muku muna fushi da shi? Ko salon ku bata masa
gawa ne? kai ni fa ban yarda da ku ba”. Alh .Rabi’u ya girgiza kai y ace, “Yaduwa idan ba zaki
iya saurara ba kina iya fita”. Ya kareshe maganar yana nuna mata hanyar fita daga dakin. Sai ta
yi mucus! Alh. Rabi’u y ace, “mun yafe masa, Allah Ya yafe mana baki daya. Suka ce
“Amin”
Yakub y ace,
“ina so hakan ya zamo alkawari ne, kada daga baya dokin zuciya ya sa ku sauya shawara”.
Alh. Rabi’u y ace. Mun yi alkawarin”. Yakub ya dubi Abubakar y ace, “wannan shi zai fara ba ku
labarin, saboda labarin ya kasu kashi uku, kowanne mud a bangaren da yake jagoranta,
Abubakar bismiLlah”.
Abubakar ya gyara zama ya soma da cewa.
BABI NA SHA BAKWAI
MAFARI
MATA’UL HAYAT
(JIN DADIN RAYUWA KO KYALE-KYALEN RAYUWA)
“Kamar yadda kuka sani Sagir ya taso da hazaka, uwa uba nutsuwa da yake da ita, wanda
hakan ne ya ja masa farin jin a gurin al’umma.
Da yake labarin a takaice ne zan baku shi, kun san lokacin da yake aji hudu a sakandire kun
sauya masa makaranta zuwa ta kudi, to a can ne Allah Ya hada Sagir da wani aboki IZRA’EL,
wanda tasu ta zo daya sosai don gurin zamansu daya ma, haka idan ana maganar kokarin daya
to za a sanya dayan. Wannan shakuwa tasu da hazakarsu ya sa malamansu ke kiransu 2
Effect, duk da wannan tarayya tasu Izra’rl bai taba taka kafarsa gidansu Sagir ba, hakan kuwa
daga Sagirun ne don yana tsoron mahaifansa, sanin Musulmai ne shi kuma Izra’el Krista, yana
ganin kamarbza a kalubalanci tarayyarsu. Sai dai shi Sagir ya je gidan su Izra’el wanda zuwan
nasa ya tayar da hankalin mahaifansa har said a suka hukuntashi akan don me zai yi mu’amala
da musulmi, dalilin haka yasa abotarsu ta soma ja baya, amma dai bas u rabu ba. Lokacin da
suka gama sakandire, sai ya kasance, suna haduwa a cikin gari. Tsutsayi mahaifan Izra’el suka
gano har wannan lokacin bas u rabu ba, don haka suka tura dansu karatu, can kudancin
Najeria. Wannan ya sa suka daina ganin juna, kuskure na farko da aka soma samu a rayuwar
Sagir shi ne, gidannan ba a tsaya sosai ga ilimin addinin musulunci ba, ita kuwa duki rayuwar
da aka bar ilimin addini akwai nakasu a tattare da ita. Shigar Sagir poly ta sauya masa rayuwa,
ta hanyar yin mu’amala da mutane daban-daban, na banbanta addinai, daga cikin mutanen day
a yi mu’amala da su akwai wata yarinya mai suna Akkina, wadda ta kasance daga addinin
Yahudawa. Akkina ta so Sagir, shi ma ya so ta it ace ma mace ta farko da aka soma
SADAUKARWA da ita, a wani bangare na sirri………..”
Inna Yaduwa ta katse Abubakar cikin daukar zafi. “ka ga malam dukkan mu nan ba yara ban e,
idan kun z one domin ku ci zarafinmu ku bata mana gawar da, to ku fice ku bam u guri”.
Alh.Rabi’u y ace, “kafin a soma bada labarin said a aka nemi shawarar idan ba zaki iya saurare
ba ki fita, don haka yanzu ma kofa a bude ta ke”. Jin abin da ya fada yasa ta yi shiru amma
tacika fam!
Abubakar ya jinjina kai yana kallonta tukunna ya dora da cewa, har Sagir ya kamala diplomarsa
suna tare da Akkina, yana ta neman aiki bai samu ba, rannan da yammaci ya je gidan zoo shi
da Akkina, wadda ta kasa komawa mahaifnta tun kamala karatunta, saboda tunaninta idan ta
koma Sagir ba zai bi bayanta ba, ita kuwa a rayuwarta babu wanda ta ke so irin Sagir, don haka
ta ki komawa ta zauna a gidan abokin mahaifinta inda ta soma zama ganiyar karatunta. Suna ta
yawon kallon dabbobi, kowanne a cikinsu yana nuna abin da ke burge shi na daga dangin
dabbobi. Sun zo layin da ked a akwai zakuna, sun tsaya a dai-dai kejin wani zaki suna kallo,
kawai sai sager ya ji an ambaci sunansa. Dago kan da yake suka yi tozali da Izra’el, nan take
suka rungume juna cike da jin dadi. Sun dau lokaci a wannan hali kafin daga bisani sun saki
juna suna kallo-kallo a tsakaninsu.Sagir ya ga sauyi sosai a tare da Izra’el mamakinsa bai boyu
ba, saboda shigar day a yi ba karamar shiga ba ce, shiga ce irin ta wadanda ke jin dadi, duk da
dama mahaifan Izra’el masu kudi ne, to amma ga dukkan alamu yanzu sun fi kudi. Izra’el y ace,
“mutumina yanzu wane aiki ka ke?” Sagir ya girgiza kai, y ace”bana aiki, na dai gama karatu ina
ta neman aiki ban samu ba”. Murmushi Izra’el ya yi y ace “aiki a kasar nan ai wahala ne, idan
bad an wane kake ba baza a taba baka aiki ba”. Ya ciro wani kati(comlementory card) daga
aljihunsa, yace. “yanzu dai babu isasshen lokaci, amma ka same ni a gida sai mu tattauna”. Ya
karashe maganar yana mika masa katin Sagir ya sa hannu ya karba, a haka suka rabu. Kwana
biyu a tsakani day a shirya ya yi amfani da adireshin da ke jikin katin ya je gidan Izra’el, gida na
alfarma wanda ya kunshi duk wani nau’in abu na shagalta, ko kafin Izra’el ya fito daga daki, said
a Sagir ya yi kauyanci. Yana fitowa, tsoron ma hada hannu da shi ya yi don gaisawa, sai
zubewa ya yi a kasa yana gaishe shi.
Dariya Izra’el ya dinga yi, sannan ya tayarda Sagir ya zaunar da shi saman kujera, su kadai ne
a falon, sai mai aiki da t agama zube nau’o’in ababen cid a na sha, ta fice. Sagir ya gaza hakuri
y ace. “kai mutumina, yaushe Bos dinka ya zama hamshakin mai kudi ne haka?” Izra’el y ace.
“a’a duk abin da ka gain a gidan nan mallakina ne, ni na hada komai da kudina da kuma
gumuna, domin bayan tafiyata karatu mahaifina ya rasu, yanzu haka ni ke rike da duk
dawainiyar gidanmu ba kuma da gadon mahaifina ba”. Mamaki ya sake mamaye zuciyar Sagir,
ya dinga dube-dube, fuskarsa na nuna matukar kauyancinsa.
Izra’el ya yi murmushi, y ace “to yanzu dai fara cin abinda da aka ajiye maka kafin mu shiga
tattaunawa”. Hka ya ci abubuwan da aka jera masa shi kuma Izra’el ya koma cikin wani daki, jim
kadan ya dawo hannunsa dauke da wata ‘yar karamar jaka, ya ajiye ta a gafe, ya zauna akan
kujera yana kallon Sagir har ya kamala. Sannan suka gaisa tare da tambayar juna bayan
rabuwa. Izra’el y ace, 2Sagir na tausaya maka matuka, acebsaurayi kamarka babu ‘yan cnji ko
aikin yi akwai fargaba, amma kada ka damu, ni zan taimakeka saboda shakuwar da muka yi da
kai, zan sama maka aikin yi ko don abotar da ke tsakaninmu tun kuruciya, sai dai akwai
sharadin d azan gindaya maka muddin ka amince shi ken an”.
Cikin zakuwa Sagir y ace da shi “wani sharadi ne?”
Izra’el ya yi murmushi tukunna y ace masa yana kallon kwayar iadanunsa. ‘”a’a ba yanzu zan
fada maka ba, ka dai bi ni sannu a hankali”. Haka suka ajiye Magana, da zai tafi Izra’el ya
damka masa wannan jaka day a fito da ita, wadda ke dauke da manyan agoguna guda hudu
kowacce daya zata kai dubu goma, sai tsabar kudihar na dubu talatin. Sagir ya rude, ya rasa inda zai saka kansa don dadi, ya shiga zabga masa godiya tamkar an ba
shi kyautar aljanna. A takaice sun ci gaba da haduwa a lokuta mabanbanta, da haka har yawon
dare suke zuwa, tukunna Izra'el ya bullowa Sagir maganar aiki. Iya kaduwa ya kadu da ya ji irin
aikin da Izra'el din yake ikirarin ya samar masa, wannan shi ne dalilin dauke kafarsa ga gidan
Izra'el, amma ko da aka dauki lokaci ba su hadu ba, sai ya ji zuciyarsa ta karaya, har ya
amincewa kansa zama daya daga cikin 'ya'yan kungiyar safara da shan jinin mutane...." Ko da
Abubakar ya zo nan a labarinsa, gaba daya sai gurin aka dauki salati. Inna Yaduwa kam
fashewa ta yi da kuka. Abubakar ya ci gaba da cewa, "Tun Sagir yana dari-dari har ya bada kai
bori ya hau, ya je ya samu Izra'el ya sanar masa ya amince. Gudun kada a gano shi tunda ba
aiku yake ba, kada a ganshi da manyan kudade a zarge shi da wani abu, sai daya daga cikin
'y'yan kungiyar ya sama masa aiki a ma'aikatar kula da tsirrai na jihar Kano. Tashin farko abin
da dodon tsafi ya fara bukata ga sagir shi ne jinin Akkina a matsayinsa na wadda ya fi so fiye da
kowace mace. A ranar sam bai samu yin bacci ba saboda yana tunanin yadda zai iya sadaukar
da Akkina ga dodon tsafi bayan dumbin son da yake yi mata. Sai da ya dauki tsayin kwanaki
hudu a halin damuwa da rashin sukuni, sannan ya amince. Ya tsarata akan zasu je Abuja
holewa kamar yadda sukan yi, amma ba ya son kowa yasan da tafiyar, don haka ta yi karya a
gidan da ta ke zaune cewar zata je can gidan su mahifarta. Wannan shi ne dalilin da ya sa har
yau iyayenta ba su san yadda aka yi da gawarta ba. Bayar da Akkina ga dodn tsafi ya kara
samarwa Sagir daukaka a kungiyarsu, sannan hakan ne ya sa ba wanda yayi zargin ta ya ya
samu wadannan dukiyoyin nasa. A kungiyar tasu akwai Hausawa da yawa a ciki, irinsu Alh.
Badaru mataimakin shugaba, Alh. Nuraini da dai sauransu. Alh. Sammani shi ne mutumin da
kusan suka shiga kungiyar a tare, shi mutumin jihar Jigawa ne, a shekaru ma za su kusan
sa'annin juna. Bisa ga yadda shugabancin kungiyar yake shugaba wanda yake akan karagar
mulki shi ne mai alhakin zabar wanda zai maye gurbinsa a lokacin da wani sanadi ya taso, ko
mutuwa ko kuma rashin cika ka'idojin shugabancin kungiyar. To tun kafin daya daga cikin
wadannan abubuwa biyu su taso yake zabar magaji wanda zai gaje shi. Wanda yake
shugabancin kungiyar a lokacin wani inyamuri ne mai suna John, tun lakacin da Sagir ya shiga
kungiyar ya kasance yanna kaunarsa, don haka shi ne ya kasance yana kaunarsa, don haka shi
ne ya zaba a matsayin MAGAJINSA, wanda hakan bai yiwa da yawa 'ya'yan kungiyar dadi ba,
ganin cewa akwai waganda suka shafe Sagir a shekaru, kuma akwai wadanda suka fi shi
dadewa a kungiyar, bugu da kari ma akwai wadanda sunfi shi gogewa a harkar tsafin nasu,
amma ace Sagir shi ne zai shugabance su? Wannan dalilin ne ya sa aka yi ta cece ku ce a tsakaninsu,sun manta da cewar muddin shugaba
ya fidda Magaji shi ke nan maganar ta zauna, ko da shi shugaban ne ba zai iya kankare abin
ba. Wannan tsari ne na abin tsafinsu, don haka ya koma gefe yana kallonsu sai da daya daga
cikinsu ya samu nutsuwa