Showing 3001 words to 6000 words out of 83144 words
suka yi sallama ita da ISAH (dan Alh Sada mai kimanin
shekaru bakwai). Bayan sun zauna an gaisa Haj karima ta kawo musu abinci suka dan ci kadan
saboda a koshe suke.
Inna yaduwa ta dubi Haj karima tace; Karimatu musamman zuwan nan ba yi shi dominki.
Gaban Haj karima ya fadi tsoroi ya kamata ta tuna ranar da Alh Rabi'u yazo mata da bakin
labari tana gudu kada ace ita ma Inna yaduwan ta zo mata da bakin labarin mutuwar
mahaifanta ne(Ance idan maciji ya sare ka tsumma ka gani sai ka ruga. Inna Yaduwa ta lura da halin da Haj karima ta shiga sai tayi murmushi tace; Kwantar da
hankalin ki shawara ce zamuyi dake. Ta sauke gwauron nunfashi yayin da Inna yaduwa ta ci
gaba da cewa.
Shuhuda yanzu ta samu shekara daya sai dai duk wanda zai ganta zai dauka ta wuce haka
saboda girman jikinta ga wayo tana da shi. To sai nake ganin me zai hana wata uku masu zuwa
a cire ta daga nono tunda dama ba damuwa tayi da shi sosai ba??
Shiru Haj karima ta yi bata tanka ba saboda alkunya da yakana irin ta mutan da. Sai gwaggo
Zuwai ce tayi magana; ............................................................
................. Nima nayi wannan tunanin tunda a yini bai fi tasha nono sau biyu ko sau uku ba
musamman ma yadda zawarawa suka fito suna son aurenta sai na ga cire Shuhudan a nono
tayi aure zai fi da cewa. Inna Yaduwa tace Sannan kuma mai zai hana Ahmad ya maye gurbin
marigayi , tun da shima ya nuna yana bukata? Da sauri Haj karima ta mike tsaye tare da zaro
ido waje sai dai bata iya cewa komai ba sai girgiza kai da take yi tana ja da baya. Inna Yaduwa
tace Kinga zauna idan bai kwanta miki ba babu dole dama shawara ce saboda shi dan uwan
sagir ne zai iya zaunawa dake da yarki amma a wannan zamanin da wuya ne samun mijin da
zai rike agola. Koda ya riketa ma sai kinga bambanci,don haka na yi miki sha'awar auren
Ahmad to amma tunda bai kwanta miki ba , kada ki damu Allah Ubangiji ya za6a miki miji
nagari. Idan lokacin yayen yayi zan zo na kar6e ta na yaye miki ita. Tana karashe fadar haka ta
dubi Isah tace; Kai tashi Muje. Yace Kai Inna mun fa yi dake a nan zaki bar ni gurin 'yar uwata.
Ta yi dariya Idan na barka makaranta fa? Yace; Ba sai direban ya zo nan ya dauke ni ba? Tace;
kai ni taso mu ta fi, ka ta6a ganin maigida na gudun matarsa? Ba don yaso ba dole ya mike,
Inna Yaduwa ta dubi Haj karima tace; Mu mun tafi. Jiki a sa6ule Haj karima tace; Shikenan Inna
na gode Allah ya sauke ku lafiya. Inna Yaduwa ta amsa da 'Amin' sannan suka fice daga cikin
gidan. Bayan tafiyarsu Goggo Zuwai ta dubi Haj Karima tace: Ke kuwa 'yar nan meye aibun Alh
Ahmad da kika razana don an yi miki sha'awar aurensa? Idon Haj karima ya kawo kwalla a
idonta tace; Kin gane Goggo ba zan iya rayuwar Aure da Alh Ahmad ba, ba wai don baya da
kyawawan halaye ba sai dai don idan na dube shi zan dinga tunawa da kaninsa kuma ma dai
gaskiya ina jin kunya da tsoron matanshi. Goggo zuwai tace; Hakane to amma ai wanda ya
rasu ya riga ya rasu, su kuma matanshi ai sun san akwai aure a tsakanin ku. Tsoron me zaki ji
nasu? A kansu zaki zauna ko kuwa? Kowa zaman kansa zai yi don haka ina ganin shi ya dace
ki aura. Girgiza kanta tayi tace: Bazan iya aurenshi ba gwaggo. Tace To idan baki aure shi ba
wa zaki aura? Kin dai san dole ne ki yi aure ko? Sai tayi shiri ta rasa abinda zata ce Tana da
zawarawa da yawa wadanda sun fito ne domin su aure ta, kuma duk wanda ta za6a tana da
yakinin zai kyautata mata sai dai ba zai kai ya mijinta ba. Don haka babu wanda ya kwanta
mata. To amma tunda an 6illo da wannan maganar dole ne ta yo wani abu akai ko don tsallake
wannan suradin. Maganar Gwaggo zuwai ta katse mata tunani tace; '' Aure a musulunci sunna
ne daga cikin sunnonin Manzon Allah Muhammad(S.A.W) dama sauran manzanni da suka
gabace shi Allah (S.W.T) Yace; Hakika mun aiki manzanni gabanka kuma mun sanya matan
aure garesu da zuriyya(Ra'ad:38). Manzon Allah (S.A.W) yace ' Aure sunnata ce duk wanda
yayi kyama ga sunnata to baya tare dani. Allah (S.W.T) yace '' ku auri abinda yayi muku dadi
daga mata(Nisa'i:3). Akwai samun nutsuwa da kwanciyar hankali a 6angaren mata da miji. Allah
(SWT) Yace 'Daga cikin ayoyinsa ya halitta muku mataye daga kawunan ku don ku natsu zuwa
garesu? Ya kuma sanya soyayya da jin kai tsakaninku tabbas a cikin wannan akwai abubuwan
lura ga mutane masu tunani kawai.(Rum:21). Manzon Allah yace (S.A.W) yace; '' Muna cewa
duk namijin da bai yi aure ba to miskini ne komai yake da dukiya. Haka matar da bata yi aure ba
miskiniya ce komai take da wadata''. A 6angare daya kuma duk wanda ya yi aure toya sami
rabin addininsa,haka kuma al'umma suna mutunta da kuma fifita mai aure bisa ga wanda ba ya
da aure. Idan kika tattara duk wannan bayanan da nayi miki ya isa ki san girma da darajar aure
ga al'umma don haka kada ki bari zuciyarki tayi rauni ga gujewa abinda ya wajaba a gareki. Ita
ZUCIYA MUGUN NAMA ce ko da yaushe anaso bawa ya dinga neman tsari da sharrinta domin
idan ta gyaru gangar jiki ya gyaru,idan ta 6aci gangar jii ma ta 6aci''. ( ALLAHUMMA YA MU
SARRIFAL QULUB SABBIT QULUBANA ALA DA'A TIKA) { YA UBANGIJI MAI SARRAFA
ZUKATA KA SANYA ZUCIYARMU AKAN DA'ARKA)
.
Tayi shiru daga bayanin data ke yi yayin da Haj Karima ta kai hannu ta share kwallan dake
zubowa daga idonta muryarta a raunane tace;
Gwaggo zan yi aure ba zan ta6a gufunsa ba Inshaa Allah zan fitar da miji amma bazan iya
auren Alh. Ahmad ba.
Gwaggo zuwai tace Eh hakan ma yayi domin ba zamu tursasa ki auren da bai kwanta miki a rai
ba kece zaki zauna da shi don haka idan zuciyarki bata aminta da shi ba ba zaki samu
kwanciyar hankali ba Allah Ubangiji ya za6a na gari.
Can kasan makoshi Haj karima ta amsa ''Amin''
***** ***** *****
An shirya ranar juma'a da safe Inna Yaduwa zata zi ta kar6i Shuhuda don yaye ta kamar yadda
aka tsara tun farko cewa idan tayi shekara daya da wata uku za a yaye ta.
To tun ranar talata da aka yi maganar yarinyar tayaye kanta anyi-anyi ta kama nono amma taki
sai dai tsotson hannun kawai take . Hankalin Haj Karima yayi matukar tashi ganin har yammaci
yayi amma shuhuda taki tasha nono abincin ma dan kadan taci kuma babu kuka babu fitina sai
ma bacci da take yawan yi. To a ranar anyu katari Gwaggo zuwai bata nan taje gidan yarta data haihu don haka gidan Haj
karima ce kadai. Ta rasa yadda zata yu ita bata ta6a yaye ba hasalima bata ta6a ganin yadda
ake yinsa ba saboda mace ce mai matukar tausayi bata son ganin yaro yana kuka yanzu ita ma
ta kama kuka. Ganoin yadda shuhuda taki kama nono sai ta dinga tunani ko dama haka ake yayen kafin ranar
tazo yaro ya daina shan nono? An gama sallar magrib Gwaggo zuwai ta dawo gidan Haj karima
ta kora mata bayanin duk abin da ya faru. Dariya tayi tace; Ai sai ki gode Allah dama haka wasu
suke idan suka ji za a yaye su to sai su yi fushi da shan nono wasu kuwa lokacin ma zaki ga
sun tsananta shan nonon.
Saukinmu daya daurin nan ya huda mata jiki don haka idan Allah ya kaimu safiya lafiya sai a
kaiwa surukar taki ita..
da Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤05¤¤
Haka kuwa aka yi gari na wayewa Gwaggo zuwai ta goye shuihuda a bayanta ta nufi gidan Inna
Yaduwa da ita. Tun bayan tafiyarsu Haj karima shigewa daki tayi ta kama rusar kuka ta tabbata
sai wani ikon Allah Shuhuda ta rayu a hannunta saboda ta lura da take-taken surukar tata so
kawai take taga ta kar6e shuhudan tunda ai tana gidan mai rasuwar inna yaduwa ta kar6o Isah
dan Alh Sada ya dawo hannunta tun daga yaye. Kwana biyu yarinya sai harkokinta take bata
kuka sam! Sai dai tana da yawan bacci idan ta farka kuma shiru zaka ji tayi tamkar kurma,haka
Isah zai zauna a kusa da ita yayi ta mata wasa. Idan yaje makaranta makaranta yayi mata
siye-siyen kayan kwalam da ragowar kudin da ake bashi na tara(break). Shuhuda ta samu wata
shida da yaye Allah ya fitowa Haj karimatu miji duk da ba wani kwanta mata arai yayi sosai
ba,ta daure ta amince dashi saboda yadda mahaifanta da danginta suka dame ta da maganar
aure dadin-dadawa kuma gashi Alh Ahmad na yawan zuwa gidan. Ita kuma ta gama karantarshi
tsaf fuskace dai bata ba bashi ba shi yasa bai yi mata maganar ba. Alh Jamilu Ahmad Karare,
dan asalin karamar hukuimar Batsari ne a wani kauye mai suna karare cikin jihar katsina Dan
kasuwa ne sosai yana da mata biyu da yaya shidda maza da mata. Haj karima ta aminta da
aurenn Alh Jamilu ne kawai don ba yadda zata yi ya fito ne 6angaren mahaifinta amma ba
tursasata yayi ba, ya dai nuna mata idan ta auri Alh Jamilun zai ji dadi zai yi farin ciki yana da
yakinin zata samu zaman lafiya a gidan aurenta. Duka-duka haduwarsu da komai bai fi wata
daya ba aka daura aure sati daya zata tare. Ta shiga tunanin yadda za ayi ta kar6o shuhuda
daga hannun Inna Yaduwa. Ranar Alh Jamilu yazo gurinta suna zaune a falo ta ke cewa dashi.
Alh. Wata alfarma nake roko gurinka. Yana murmushi yace mata. Fada ai kin wuce haka a
gurina. Tace Dama so nake na kar6o Shuhuda na riketa a gurina. Yayi jim na wani lokaci
sannan yace; Babu komai ai da na kowa ne musamman ma rikon maraya lada ne da shi. Sai
dai inda gizo yake sakar da ta nemi a bata shuhuda sam kin amincewa suka yi suka ce ba su
yarda Shuhuda tayi zaman agolanci ba dole a hannun Inna Yaduwa zata zauna. Haj karima
bata iya musu iya musu ba don haka ta sanyawa zuciyarta dangana ta bar musu Shuhuda.
Amma a yadda ta so, ta so ace ta rayu da Shuhuda a inuwa daya domin ta dinga debe mata
kewar mijinta data rasa sai dai ba yadda zata yi ita mace ce mai kawaici da hakuri don haka a
nan din ma dole hakurin ta sakawa ranta. A haka har ranar tarewa tazo aka shiryata aka mikata
gidan mijinta can cikin jihar katsina cikin karamar hukumar Batsari a karare inda gidan Alh
Jamilu yake. Tun durar yan rakiyar amarya da ita kanta amaryar suka soma cin karo da cin
mutunci saboda matan Alh Jamilu irin matan nan ne na kauye wadanda suka dauki kishi da zafi
,amma kowaccensu baka raina haduwarta ba.don kana ganin uwargidan kaga barumayar asali
ita ma ta tsakiyar barumayar ce farare tas dasu illa rashin iya zama da miji da kyautata masa
kadai dake dawainiya dasu. Sai uwa-uba kazanta ga rashin iya girki mai dandano ba.
Tun daga yan rakiyar har ita Hajiya kariman ba wanda ya kula da cin kashin da kishiyoyin suke
yi haka suka gama komai suka ba wa Haj karima hakuri akan ta jure duk abin da zata gani ga
matan nan idan ta yi haka sai ta ga komai ba komai ba. Suka yi mata sallama aka kwashe su
cikin motocin da aka kawo su aka koma da su. ***** ****** ****** BABI NA DAYA IDAN AJALI
YAYI KIRA........ Shuhuda ta tashi da wata irin bahaguwar rayuwa. Idan tana tsotsar hannun ko
abincin bata cika ci ba . Inna yaduwa tayi fadan har ta gaji amma ba abinda ya ragu. Wata irin
shakuwa ce tsakanin Shuhuda da dan' uwanta Isah ya kasance komai zai yi yana tare da
Shuhuda makaranta ce kadai idan zai tafi yake rabuwa da ita. Har Inna Yaduwa na tsokanarshi
tana cewa: Ka gama wayon naka amma baka isa kayi min kishiya da wannan bagidajiyar mai
tsotsan hannu ba. Sai dai yayi murmushi kawai wani lokaci kuma yace; Kece bagidajiya amma
shuhuda ba bagidajiya bace. Shuhuda tana da shekaru shidda aka sakata a makarantar
islamiyya yarinyar tana da kwalwa sosai sai dai matsalar dake damunta tsorsar hannun nan
nata. Yan ajinsu su yi ta tsokanarta wai ta girma tana tsotsar hannu bata damuwa don bata yi
wayon da zata fahimci me suke nufi da hakan ba. Jarabawarsu ta farko sai ga shi Shuhudan ce
tayi na daya har kyautuka aka yi mata a makarantar. Inna Yaduwa ta sanyata a gaba tana cewa:
' Kinga Shuhuda da zaki daina tsotsar hannu da sai kin fi haka kokari saboda mata masu tsotsar
hannu ba sa da kokai. Don haka ki daina tsotsar hannu kin ji?? Tayi Shiru kawai ba tare da ta ce
komai ba kuma ba ta daina tsotsar hannun ba. Shuhuda tana da kwalwa da kaifin basira ba ta
yadda za a yi a koya mata abu ba ta dauke shi a kanta ba. Alh Sada suna matukar kulawa da
ita tare da dukiyarta da mahaifinta ya rasu ya bari duk wata kadara tasa tun daga nan gida
Nigeria zuwa kasashen waje babu abin da ba a kiblatasu ba kuma an ci gaba da tafiyar da
harkokin kasuwancin yadda aka saba tun can baya.
Yau ya kama ranar lahadi Shuhuda tana zaune ita da yayanta yana koya mata karatun
Islamiyya a lokacin ba ta fi mintina sha biyar daga tashi a bacci ba. Inna Yaduwa na zaune
gefensu tana kallonsu Ta gaza hakuri saboda yadda taga ana koyawa Shuhuda karatu amma ta
zurmuka ya tsanta a baki sai tsotsa take yi. Ta mike tsaye da sauri cike da 6acin rai ta karasa inda Shuhuda take ta sa hannu ta gwa6e
yatsan da take tsotsa. Ke kam kin ji haushin kanki kullum a yi ta abu daya dake sai kace mai
kwalwar tumaki to na ga kin kara tsotsar hannun a gidan nan.
Isah yace; Ke Shuhuda ki daina tsotsar hannu kin ji ko? Ta yi shiru hannunta na ajiye a kasa
Inna Yaduwa ta koma ta zauna akan kujera tana bambamin fadanta. Ai kuwa tana zama
Shuhuda ta maida yatsan a cikin baki tana tsotsa Inna Yaduwa ta sake harzuka tace; Wai ni
uban me kike tsotsa a yatsan nan ne da ba zaki dai na ba? Dai-dai lokacin Salmai mai haja ta yi sallama a cikin falon Sam Inna yaduwa ba ta tsinkayo
muryarta ba saboda tana rigima da Shuhuda tana son cire mata yatsan daga baki ita kuma
Shuhuda ta kiya sai kakaniya suke.
Salmai tace Haba Yaduwa ni da me ye haka? Inna yaduwa tace Bar ni da yar nan Salmai ta
raina ni ne, kullum sai nayi fama da ita akan tsotsar hannu amma kamar mai kunnen kashi ta ki
ta daina ta maidani mahaukaciya.
Salmai tace Ayyah! Ai laifinki ne idan yaro yana tsotsar yatsa aka yi-akayi da shi ya ki dainawa
mai dungurugum ake yi masa sai a samu zaman lafiya.
Inna Yaduwa ta yamutsa fuska cikin rashin fahimta tace. Ban gane mai dungurugum ba? Salmai
ta yi dariya dai-dai lokacin da ta ajiye jakar hajarta kasa tace.
Tsarga hannun ake a saka masa borkono gobe ko cewa aka yi ya tsotsi hannun ba zai fara ba.
Inna Yaduwa ta ce Ai ni tausayi nake ji bana iya tsarga hannunta da tuni na yi maganin
abun.Salmai tace aikuwa idan ba ayi maganin abun da wuri ba haka zata mike har girmanta...
Ke har ma ta haihu tana tsotsar hannu ga 'ya'ya a gabanta suna kallo wannan kuwa kuwa ai ba
karamin faduwa bane.
Inna Yaduwa ta jinjina kanta tace ; Lallai kam to ni yanzu ban san ya zan yi da wannan 'ya ba
taurin kanta har mamaki yake bani ga ta 'yar karama yarinya amma idan ta kafe akan abu babu
wanda ya isa ya tankwarata.
Ai haka dama wasu yaran suke akan tsotsar hannu ka rasa me suke tsotsa. Haka kawai yaro ya
sanyawa kansa fitina ko abinci sai ki ga sai an yi da gaske yaro ke ci. To ni zan yi miki maganin
abun dauko min dakakken barkono da sabuwar reza kiga ikon Allah.
Isah ya yi sauri yace: Don Allah Inna kada ku tsaga mata hannu wannan zalunci ne!......
Inna Yaduwa ta kai mishi bugu. Kai ni rufe min baki sai a bar yarinya ta yi ta tsotsar hannu?
Ta mike a zafafe ta dauko barkono da sabuwar reza ta kawo wa Salmai, amma ta kasa rike
Shuhuda wai bata iya ganin tsarga hannun saboda tausayi.
Ita kuwa Salmai ta kama Shuhuda take ta kokarun kwacewa, amma ina aikin gama ya gama.
Tuni Salmai ta tsarge mata yatsa.!!!!
Tashin hankali wanda ba a saka masa rana ai ko da tsarge yatsan sai RUWAN NONO fari kal
ya dinga ambaliya maimakon JINI!!!!!
Yau mun shiga uku!
Yayin da Isah duk ya kidime ita kam wadda abin ya faru gare ta babu alamar tsoro ko razana a
tare da ita sai ma daga yatsan tayi sama tana gyarawa nonon gurin zuba.
Inna Yaduwa tana ganin abin da ya faru ga Shuhuda ita ma kidimewa tayi ta matso gurin tana
sallallami. Isah yace; Inna kin ga abin da ake gudu ya faru. Ta juyo da dubanta gare shi tare da
cewa :
Yi sauri ka kira min mahaifinka a waya. Jikinsa na mazari ya kira lambar Alh Sada kara daya ya
dauka yace: Ya dai Isamanu dan maryama? A figice Isah yace Abba kazi inji Inna za a kai
Shuhuda asibiti
Alh Sada yace Me ya