Showing 12001 words to 15000 words out of 83144 words

Chapter 5 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11070

su dalibai masu
fahimta suna da rike abu a kansu. Yana cikin bayanin nasa ne ya jefo musu tambaya mai stauri
yace; Cikinku wa zai min bayani akan Radioactivity? A cikin harshen Turanci ne ya yi musu
tambayar don ka'idar makarantar ne haka ba a baiwa malami damar yiwa dalibai tambaya da
wani harshe ba idan ba Turanci ba, sai dai idan Islamic studie ne wanda shi harshen larabci
tsagwaronsa ake gabatar da shi ga musulman dalibai kenan. Gaba daya ajin aka yi tsit, wuta ta
dauke musu saboda ba a ba su darasin a cikin ayyukan da zasu yi a aji hudu ba su kuma
hankalinsu bai kai ga bincikar 6angaren ayyukan da ke gaba ba. ( Dalibai anan tsanyi tsokaci
idan kuka shiga makaranta ba dole sai syllabos din da aka ba ku zaku duba ba a'a ana son
dalibi ya kasance mai kutse-kutse yana binciko abubuwa da dama a harkar karatunsa yadda
idan kun zo gurin komai zaizo da saukiza kuga kamar maimaici ne ma kuke yi). Uncle Hamza
ya yi murmushi ganin cewa an rasa wandazai iya yi a gare su bai ce komai ba sai ya koma kan
kujera ya zauna yana baza idanu ya ga ta inda zai samu amsarsa. Aka dauki tsayin mintina
huudu a haka babu wanda ya ko motsa sai ya girgiza kai yace: Yanzu duk taron yawanku babu
wanda zai iya ba ni amsar Radioactivity? Karaf sai ji aka yi daga kujerar baya an soma bayanin
cikin zazzakar murya mai natsuwa. Kyam! Ya tsaya tare da tsura mata idanu yarinya karama
'yar fara mai kyawun sura tana ta bayani cikin hadadden turancin ta(Latent English) na kasar
Amurka babu tuntu6en harshe ko gwamutsawa da gur6ataccen turanci(Broken English) kuma
bayani take akan Radioactivity da tsurar saninta wanda kowanne malami zai saurara sai ya
jinjina mata. Haka ma idan a jarrabawa ne babu tantama zata sami maki(scores)mai yawa. Su
kuwa dalibai 'yan uwanta ba su yi mamaki ba domin duk wanda ya kwana ya hantse a
makarantar nan yasan shuhuda da kaifin kwalwa zai yi wuya a tuntu6eta sanin wani abu a rasa
amsa daga gare ta. Shuhuda ke nan mai abin AL'AJAB! Haka dalibai suke mata lakabi. Tana
kammala jawabinta ta koma mazauninta ta zauna ta mayar da tagumin alamar ta nutsa tunani.
Uncle Hamza ya rasa abin da zai ce wace jinjina zai yiwa yarinyar nan. Wace irin kyauta zai
bata wadda zata nuna jin dadin da ya samu kansa a ciki. Lallai ya yarda ya kuma aminta
wannan yarinyar 'yar baiwa ce kuma ga dukkan alamu gidansu ana dagewa akan karatun yaro.
ada Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)¤¤08¤¤
Kai ko da ma dagewar to akwai BAIWA ta musamman dake tare da ita, aiki ne wanda ake yi a
aji biyar ya tambaye su akai don kawai ya kafa harsashinsa ga dalibai su san cewa zai iya
daukarsu darasin da aka damka masa ba kamar yadda suka yi kuka da wancan malamin ba wai
ba su gane darasinsa sosai saboda sauri da yake a dukkan abin da zai koyar da su a takaice
yake yi musu. Don haka shugabar ajin ta kai korafi gurin shugabar makaranta aka yi katari da
sababbin malamai da suka samu sauyawa(transfer) daga wasu rassan makarantar. To shi ne
aka turo shi ajin ya taho da azamar ba su mamaki sa6anin haka sau ga shi daya daga cikin mafi
karantar daliban ta ba shi mamaki ba kuwa karami ba mamaki ne cike da AL'JAB da ace
dukkan daliban da ke ajin haka suke da budaddiyar kwalwa to tabbas da zai ji dadin

kasancewarsa malami a ajin. Uncle Hamza ya sauke ajiyar zuciya ya mike tsaye daga inda
yake zaune ya fito tsakiyar ajin yana duban inda Shuhuda take yace: Ke! Mike tsaye? Shuhuda
ta dago da kai ta dube shi duba na rashin fahimta wanda ke nuni tamkar ba ta ji abin da ya fada
ba. Ya sake maimata maganarsa, sai ta mike tsaye ta rusunar da idanunta kasa. Yace ya
sunanki? Ta maimaita maganarsa kamar wadda ke koyon magana amma ita cikin yanayin
tambaya da kuma jinjinawa ta yi maganar. Sai ya samu kansa cikin 6acin rai wannan wane irin
rainin hankali ne zai tambaye ta sunanta ta maimaita tambayar da ya yi mata, sai kace tana
magana da sa'anta? Duk fara'ar da ke fuskarsa ta kau a lokaci daya, yace; Tambayarki nake ya
sunanki? Kanta na duke a kas ta ce: Sunana IZRA'EL!!!!! Ya cika da al'ajabin jin amsar da ta ba
shi Izra'el? A yanayinta bai yi tsammanin zai ji sunan da ya dangantata da wata kabila wanda
ba bahaushe ba. Saboda akwai hijabi karami a jikinta kamar yadda yake duk musulmin da ke
ajin zaka samu bambancin kayansa da na sauran kabilu. To ba ma wannan ne al'ajabin ba shi
ai sunanta ya tambaye ta mai yasa zata fada masa sunan mahaifinta? Lallai wannan yarinya ta
raina shi, in baya da raini ta ya zata ba shi akasin tambayar da ya yi mata? Ya fito da ido waje
sosai cikin barazanarwa yace: Sunanki na tambaya ba na mahaifinki ba. Na ce ya sunanki? Ta
yi shiru bata ko motsa ba bare ta ba shi amsa. Abokiyar zamanta Sa'adatu ta mike tace: Uncle
ka yu hakuri haka take tana da matsala a kanta. Matsala? Ya maiaita kalmar ta ya za a ce
wannan yarinyar tana da matsala a kanta? Matsala ko rainin arziki? Idan ba haka ba ta ya
yarinyar da ta ba shi amsar da bai ta6a tsammanin samu a ajin ba za a ce tana da matsala?
Wato maganar da aka fada masa cewa 'yan ajin suna da rainin arziki abin ya zo kansa? Idan
kuwa haka ne shi zai yi maganin abun domin shi ba ya daukar raini ga kowane dalbi. Ya dubi
Shuhuda cike da 6acin ran rainin hankalin da ta zo masa da shi yace: Fita waje kika ma kunnan
ki. Tayi tsaye tamkar ba da ita yake magana ba.
Suka ce; Uncle ka yi mata hakuri haka ta ke tana da ta6in hankali. Ransa ya kuma 6aci ko
kadan ba ya son wannan kalmar rainin hankalin wai tana da ta6in hankali Sai kawai ya ja dogon
tsaki ya dauki dan littafinsa ya ficce daga ajin ba tare da lokacinsa ya karasa cika ba. Kowa yayi
tsit cike da al'jabi shi ke nan akan mace daya sun yu asarar ragowar lokacin da ya ragewa
Uncle Hamza? A take wadanda ke jin haushin Shuhuda a ajin suka kara jin tsanarta a ransu ta
zame musu GOBARAR TEKU. Washegari bayan an koma tara(break fast) Uncle Hamza yake
da period a ajin su Shuhuda don haka lokacin na cika ya nufo ajin, sai dai yau sam bai shigo da
fara'a ba wannan yana daga cikin matakan da ya tsara game da 'yan ajin saboda ya lura wani
lokaci sakarwa dalibin fuska yana kawo raini matuka. Abin da Shuhuda ta yi masa a jiya ya
zauna masa a rai koda ya koma gida kasa sukuni ya yi yana ta tunanin yadda lamarin yake
yarinyar mai kwalwa da hazaka wadda ta bayar da amsar da matsala a kwalwa? Dama ana
saun irin wadannan mutanen? Da tunanin ya yi masa yawa akwai wani abokinsa Dr Ishak da ke
Ibadan sai ya kira shi a waya ya yi masa tambaya akan kwalwa shin dama a cikin kashe-kashen
kwalwa akwai wadda mutu yake kasancewa haziki duk abin da aka tambaye shi ya bayar da
amsa sai kuma daga baya a same shi kamar wanda ba shi da hankali? Dr Ishak ya yi
kwan-kwance yana yi masa bayani cewa ' ana iya samun mutanen da idan suna da fasaha da
hikima wani lokaci ka gansu a hargitse. Uncle Hamza bai gamsu da bayanin Dr Ishak ba sai
yake ganin kamar bai gane tambayar bane saboda haka sai ya share ya yi kwance tare da
nutsawa tunanin don samun mafita shi dai kam yarinyar ta kwanta masa a rai, rayuwarsa yana
son mace 'yar fara mai matsakaicin jiki kamar dai yadda ya ga Shuhuda matsalar dai ita ce

fuskanta da ya yi 'yar rainin hankali ce. Wai tun tana karamarta ke nan ina kuma ga ta girma ta
zama babbar mace? Da wannan takaicin ya kwana. Washegarin ne ya yanke hukuncin 6illo da
sabbin matakai don tsirar da kansa daga rainin dalibai. Daga cikin matakan da ya tsara har da
daure fuska da kuma hukunta duk wanda ya kawo masa raini komai girman dalibi ko daliba.
Kamar jiya yau ma yana shigowa ajin dukkansu suka mike don girmamawa a gare shi. Yau har
da Shuhuda cikin masu isar da gaisuwarsu. Hannu kawai ya daga musu alamar su zauna ba
tare da yayi magana ba. Dukkansu suka zauna ya soma yi musu darasi akan Nitrogen it's
compound ba laifi suna fahimta domin Turancinsa mai kyau ne kuma a nutse yake musu
bayanin yana yi yana nuna musu a aikace. Inda Shuhuda take ma sam bai duba ba bayaninsa
kawai yake . Ita din ma ba ta damu da kulata ba ko akasin hakan tana dai saurare da duban
bakinsa. Yana kare yi musu bayanin yasa kai ya ficce daga ajin. Haka suka wanzu idan ya shiga
ajin ba ya duban inda Shuhuda take har zuwa ranar juma'a wato karshen mako(weekend).
Ranar second period yake da ita kuma double period ne don haka ya yi musu bayani sosai
game da aiki da ya yi musu bayani sosai game da aikin da ya yi musu. Daga karshe ya ba su
aikin aji(class work) ya umarce su yi maza su gama ya tafi da littafansu. Ba musu duk da
tambayoyin masu tsauri ne haka suka kukata suka gama. Shugabar daliban ajin (monitor) ta
daukar masa zuwa dakin malamai (staffroom). Uncle Hamza ya zauna akan teburinsa ya dauko
littafan daliban yana gyarawa yawancinsu duk gajerun bayanai ne(short note) suke yi game da
tambayoyin da ya yi musu sai dai ya yaba musu hakan na nuna suna fahimtar abin da yake
koyar dasu. Dama haka ne burinsa domin aikin(subject) dinsa babban aiki ne da ake son dalibai
da ke fannin ilimin kimiyya(science department) su sanshi sosai saboda Chemistry yana da
muhimmanci sosai gare su. Yana gyaran cikin nishadi, wani malami mai suna Uncle Joseph shi
ma yana zaune a teburinsa yana gyara takardun gwaji(test) da ya yi a ajin su Shuhuda a jiya,
Shine yake daukansu darasin lissafi(maths) kowannensu gyaran yake yana murmushi saboda
irin hazakar daliban. Uncle Hamza yana cikin gyaran ya zo kan wani littafin tun daga tsarin
rubutun ya isa mai littafin ya samu maki to bare kuma dogon sharhi(long note) da aka yi. Da
sauri ya juya bangon littafin ya tsurawa sunan da ya gani akai ido. SHUHUDA SAGIR RABI'U
ya gani an rubuta. Ya sanya kan biro a bakinsa yana jinjina kai wace yarinya ce wannan mai
kwalwa da hazaka irin haka? Bayananta sun fi na kowane dalibi tsaruwa ina ta samu wannan
BAIWA? Daga Allah! Abin da wani 6angare na zuciyarsa ya fada masa ke nan. Lallai kam Allah
mai baiwa ne ga wanda yaso lamarinsa ya wuce gaban mamaki domin idan bawa zai tsaya
yana mamaki ga lamarin Allah to ba shakka yana iya fita daga musulunci tauhidinsa ya yi rauni.
Shi kuwa tauhidi shine babban jigon musulunci. Mikewa tsaye ya yi hannunsa dauke da littafan
ya nufi inda Uncle Joseph yale ya dube shi cikin harshen turanci ya yi masa magana. Joseph ko
kasan wannan sunan a cikin daliban aji hudu 'yan ilimin kimiyya? Uncle Joseph ya kar6i littafin
ya duba sunan sai ya yi murmushi ya zaro wata takarda daga cikin takardun da ya gyara ya
mikawa Uncle Hamza. Eh ina jin wannan ma takardarta ce na gama gyarawa ko? Uncle Hamza
ya kar6i takardar ya duba da kyau tabbas ita ce tun daga tsarin rubutun zuwa sunannata duk
babu tababa a ciki. Kuma a nan din ma babu inda ta fadi har kyautar maki daya da rabi Uncle
joseph ya yi mata. Wannan na nuni ke nan shi ma Uncle joseph ya yaba da kwalwar yarinyar?
Ya jinjina kansa cikin gamsuwa yace: Lallai yarinyar nan tana da kokari? Uncle joseph ya
fadada murmushinsa. Shuhuda? Ai a tarihin makarantar nan ba a ta6a samun mai kwalwa irin
ta ba zai fi kyau ace wannan yarinyar jami'a ta ke ba wai sakandire aji hudu. Uncle Hamza yace;

Ni ma abinda nake gani ke nan saboda banyi tsammanin samun bayanan da na gani a cikin
littafinta da takardar dake hannuka ba.
Ya juya ya koma akan teburinsa cike da AL'AJAB ya kasa ci gaba da yin gyaran ya fada duniyar
tunani. Tabbas duk yadda aka juya wannan 'yar rainin hankalin yarinyar ce mai wannan littafin
saboda babbar hujjar da yake da ita a ajin ya yi musu tambaya mai tsauri aka rasa wanda zai
amsa masa sai ita ta yi bayani gamasasshe. Idan kuwa haka ne zai yi wuya ya kasance yanzu
ma a samu wani da zai yi bayanin gamsasshe kamar nata. Lokaci daya ya soma jin zuciyarsa
na sanyi akan tsanarta da ya fara yi a kuma lokacin ne ya soma aminta da bayanin abokinsa Dr
Ishak cewar akwai irin yaran da idan baiwa ta yi musu yawa sukan koma kamar marasa hankali.
Wani sashi na zuciyarshi yana karyata yiyuwar hakan domin masu irin wannan yanayin akan
same su cikin rashin shiga mai ta kamala kana ganinsu ba sai an fada maka ba zaka san cewa
suna da karancin hankali a tare da su. Ita kuwa Shuhuda kana ganinta ka ga cikakkiyar mai
hankali ta yanayin shigarta gami da nutsuwarta . Duk macen da ta samu kanta a irin yanayin da
Shuhuda ta ke ciki to tabbas za a iya kiranta cikakkiyar mai hankali amma abin tambayar a nan
mai yasa 'yan ajin nasu suke ikirarin tana da matsala a kanta bayan duk ta fi su kwalwa? Ko
kuwa hassada ce? Ai idan hassada ce da ya samu akasin haka daga gare su to amma wannan
a bayyane yake akawai SHIRME? Cikin kalamanta in banda shirme ta ya mace ke juyewa zuwa
jinsin namiji? Ma'ana ta kira kanta da sunan namiji bayan ta kasance mace? Idan ita ce yarinyar
da ake magana mamallakiyar littafin dake hannunsa ai ya ga cikakken sunanta Shuhuda Sagir
Rabi'u. To me ye hadin sunanta da Izara'el? Waye Izra'el din? Amsar da yake bukata ke nan a
yanzu amma bai san ta ya zai same ta ba. Lamarin shuhuda ya daure masa kai matuka tunda
yake rayuwarsa bai ta6a samun kansa a cikin dogon tunani akan lamarin wata diya mace ba,
sai akan Shuhuda. Me yasa ne ya soma a kanta? Wani 6oyayyen al'amari!! A ranar bai samu
komawa ajin na su ba, saboda kwalwarsa da ta dau caji, eh mana ai ko inji ne wannan aiki ya
kamata ya huta, bare kuma kwalwa da ke jikin dan Adam wadda a kowane lokaci ake so bawa
ya kasance yana saukaka mata wajen yawaita sanya mata abubuwa masu nauyi.=========-
===============
===========- =======BABI NA HUDU========- ---------------
--------------------------- ======MAFARKI KO GASKE======- RANAR litinin kamar yadda a tsarin
shigar malamai ya ke a ajujuwa yau ma Uncle Hamza ya shiga nashi ajin a dai-dai
lokacinsa(period). Sanye da kananun kaya bakake wuluk da yake fari ne sai kayan suka amshi
fatarsa. Idonsa sanye da karamin bakin tabarau shi din ma ya kara masa kyau ainun saboda
matashi ne mai jini a jika. Ya aje kasumba a fuskarsa wadda ta sha gyara ta yi luf ba ya da haka
ma kana dubansa kasan ya fito daga tsatson RUMAWA don akwai ma tsagen biyu-biyu a gefen
fuskarsa. Bayan ya gama kar6ar gaisuwa daga dalibansa sai ya nemi guri ya zauna akan
mazauninsa.
Can karshen bango inda kujerar su Shuhuda ta ke ya tsurawa ido yana nazarinta. Amma farat
daya baza ka ce ita yake kallo ba. Kanta na sunkuye kasa ta tallabe ha6arta da hannayenta.
Akwai abinda ya lura da shi sai ya ga kamar lokacin da dalibai suka mike suna gaishe da shi ita
ba ta tashi ba, kuma ba ta dago kai ba har kowa ya zauna. Amma abin ya tsaya masa a rai mai
yasa ita ba ta mike don gaishe shi ba? Shin ita wani ne ta fi a ajin da ba za ta iya girmama
malamanta ba. Eh to zai iya cewa tafi sauran 'yan ajin kokari to amma kokari babu ladabi ai
shirme ne duk nagartar kokarin mutum idan ya kasance bashi da ladabi to ya kan zama

FANKO. Ya kyale ta ne bai nemi ba'asin rashin da'ar da ta nuna masa ba saboda mikin farin
cikin da ya shigo da shi ajin na samun gamsassun bayanai na amsoshim da ta bayar. 'Yan ajin
suka shiga damuwa ganin Uncle Hamza ya shigo ajin har tsayin mintina sun fi goma amma bai
fara yi musu darasi ba sai suka dinga tunanin ko don ba su ta6uka wani abin kirki ba ne a cikin
aikin da ya ba su ranar juma'a. Suka tattara komai suka tsura masa idanu don jin hukunci ko
wani abu da zai iya yi. Uncle Hamza ya yi huci tare da mikewa tsaye ya isa gaban allo (Black
board) hannunsa rike da alli(chalk) ya rubuta sunan darasi Chemistry sannan ya rubta kwanan
wata da aikin da zasu yi yau akan MAGNETIC FIELD sai da ya rubuta sannan ya juyo zai fara
bayani sai ya tuna littafansu na hannunsa. Yace Ku yi hakuri na manta littafanku na hannuna.
Ya dubi shugabar ajin yace Je ki kwaso. Ta fita shi kuma ya cigaba da cewa. A yau zamu yi
darasinmu ne akan maganet to amma tunda lokaci ya kure zamu tattauna game da aikin
ajin(class work)da ya gabata in yaso gobe sai mu dora wannan. Yana rufe baki shugabar ajin ta
dawo dauke da littafan ta dora akan teburinsa ya soma kiran sunaye yana damkawa kowacce
daliba nata har sai da ya zo kan na karshe sai ya ajiye shi a gefe. Yace An bawa kowa nasa?
Suka ce Eh. Saboda ba wanda ya lura Shuhuda ba ta kar6i nata ba sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login