Showing 60001 words to 63000 words out of 83144 words

Chapter 21 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11069

y ace cikin nuna tausayawa. “Wallahi ba wani akasi da aka samu, hasalima duk yau ita
kadai aka yiwa awon ciki a asibitin nan, shi ma dalilin da yasa aka yi mata, lokacin da aka kawo
ta yanayi na mai shigar ciki duk sun bayyanar da kansu a tare da ita, hakan ce ta san a bada
umurnin a yi mata awon cikin, sai kuma shi hakan ya tabbata”. Nuruddeen wanda tun fadr cikin
ya sandare, sai yanzu y ace. “Abba idan dai har cikin ne da mamaki, saboda kowa yasan
tarbiyya ta gidanmu”.
Alh. Ahmad ya dafe kansa, ya nutsa tunanin yadda abin ya faru, iya tunaninsa bai hango wata
baraka da zata sa Shuhuda fadawa wannan rayuwar banzar ba. Lokaci daya ya ayyana a
ransa, duk yadda aka yi Isah ne yayi mata cikin, musamman idan ya yi la’akari daga kasar waje
ya dawo, wata kila dama abinda yake aikatawa ke nana tun zuwansa kasar. Likitan ya girgiza
kai, y ace, “Alhaji wannan duk baa bin damuwa ban e, kawai ku kawo ta sai a zubar da cikin
asiri a rufe”. Nuradden ya yi saurin cewa. “Haka kawai ma ya dace”.
Alh. Ahmad y ace da Nuraddeen, “muje”.
Suka yi sallama da likitan suka nufo gida kowanne zuciyarsa cike da kunci, wai Shuhuda da ciki
na wata daya da kwanaki biyar?
Kafin su isa gidan Alh. Ahmad ya kira yayansa Alh. Sada ya ce su hadu can gida. Suna isa
harabar gidan shi ma Alh Sadan ya karaso gidan. Gaba daya suka karaso falo. A cike falon
yake, don haka aka wuce dakin mahaifinsu Alh. Rabiu. Dattijon yana zaune akan sallaya yana
lazimi, suka zube a gabansa suka kwashi gaisuwa. Alh. Rabi'u ya dubi dansa Alh. Ahmad ya ce.
"Ahmadu ya aka yi na ga duk kun shigo gaba daya?" Yayi shiru yana tunanin ta inda zai yanko
maganar abin kunyar da Shuhuda ta tafka muusu. Alh. Sada ya magantu ganin shirun ya yi
yawa, ya ce. "Ahmadu kai muke saurare, ka kirani a waya ka ce mu hadu nan, kuma ka yi
shiru". Ya dago kai cikin dauriya da shanye damuwarsa, ya ce, "Sakamako ne bai yi kyau ba,
domin Shuhuda ciki ne da ita na wata daya da kwanaki biyar!" Gaba daya dakin suka dauki
sallalami har shi kansa Alh. Amad din. Bayan sun dure sallalamin, Alh. Rabiu ya dora da cewa
"Lallai yarinyar nan ba ta kyauta mana ba". Alh. Sada mutum ne mai zafi, idan aka bata masa
rai bai iya daukar hukun ba. Yanzu ma cikin matsanancin bacin rai ya nufi falo, kira yake, "Ina
Shuhuda???"
Ganin yadda ransa yake a bace yasa Inna Yaduwa tasan da walakin, akwai gagarumin laifin da
Shuhuda ta yi wanda yake nemanta, a yadda kuwa ta gani a kwayar idanunsa idan ya damku
Shuhuda watakila shi ne sanadin ajalinta. Ta ce. "Tana daki, lafiya?" Bai tsaya bata amsa ba,
yana huhhutai ya nufi dakin. Da sauri Inna Yaduwa ta bi bayansam. Yana shiga Shuhuda na
kwance akan gado ya wani damko wuyanta, ya daga hannu ke nan zai kifa mata mari Inna
Yaduwa ta buda muraya da karfi ta ca, "Idan har ka sake ka daki yarinyar nan ban yafe maka
ba!al Cak! Jininsa ya tsaya, Inna yaduwa. Ta ci gaba da cewa. "Abin da nutsuwa bata yi shi ba,
daga jijiyar wuya ma ba zai yi shi ba. Komai ta yi maka yadda bata da lafiyan nan karbar

hukunci ba nata ba ne". Dalilin Inna Yaduwa kuwa na dakatar da shi daga dukan Shuhudan bai
rasa nasaba da tuna halin da ta riski kanta a ciki lokacin da ta jaraba dukan Shuhudan din ba,
hannunta ya sankare, abin da har yanzu kuwa babu wanda yasan da faruwarsa. Sai ya saki
wuyan Shuhudan ya fice, ita ma Inna yaduwa ta bi bayansa. Ya shiga dakin mahaifinsa ya kifa
kai a bango kwallan da ke makale a gurbin idanunsa suka samu damar zubowa. Inna Yaduwa
da ta shigo dakin ta gansu sun yi jugum-jugum ta shiga tambayar abin da ya faru, Alh Ahmad
ne ya yi karfin halin fada mata komai.m Itama kukan ta fashe da shi, Alh. Rabi'u ya ce. "Kinga
daina kukan haka,ku nutstu mu tunkari kalubalen da ke gabanmu". Duk suka yi shiru zuwa wani
loka ci, sai can daga bisani Alh, Sada ya dago kai ya ce. "Cikin mutane biyun nan dole a samu
daya wanda ya yi mana wannan muguwar ta'asar, don haka a kira yaron nan a tambaye shi ko
shi yayi mata ciki". Alh Rabi'u ya dube shi, ya ce, "Wane yaro ke nan?" Ya ce, "Malaminta,
wanda ya same ni da maganar yana son aurenta. Hamza sunanasa, shi ma Isah zan kira shi a
waya duk abinda yake ya bar shi ya zo domin sanin gaskiyar lamari". Alh. Rabi'u ya girgiza kai,
ya ce, "Ba haka za a yi ba, kuu bar min komai. Zan tuhumi yarinyar idan yiwuwar kiransu ya
kama sai dai a bari sai lahadi don kada abin ya shafi aikinsu". Inna Yaduwa ta sharce kwalla,
sannan ta ce, "Malam ni a ganina kawai a zubar da cikinnan asiri a rufe ba sai wasu sun ji ba".
Alh. Rabi'u ya girgiza kai ya ce. "Ko day ban yarda da wannan gurguwar dabarar ba, mutane
suna daukar zubar da ciki wani abin rufin asiri, bayan kuma babban tonon asiri ne, kuma
budewa yaro kofar shiga bariki ne. Ciki dai an sameshi, kuma ko mun so ko mun ki dale ne mu
yarda da kaddarar da ta fada manam Saboda haka maganar ma zubar da ciki ba ta taso ba, ku
dai saurareni".
Da wannan shawarar suka tashi, Alh. Ahmad da Alh. Sada kowa ya kwashi zugar iyalinsa da
suka zo dubiyar suka koma gida bayan gargadin da suka yiwa Nura ddeen akan kar ya sake ya
fasa zancen ko da ga mahaifiyarsa ce. Alh.Rabi'u bai samu ganawa da Shuhusa a ranan ba, sai
washegari da safe ya sa Inna Yaduwa ta yi masa kiranta. Shuhuda ta shigo dakin ta durkushe. A agabansa, kanta asunkuye ta gaishe da shi, ya amsa.
Shiru na wani lokaci ya biyoo bayan gaisuwar, can ya daga harshe ya ce, "Shuhuda wani
mummunan labari ne ya zo min game da rashin lafiyar ki, wanda ya daga min hankali, shin me
ye gaskiyar lamarin? Da gaske wai kin siyar da mutmcinki har kin samu ciki ba tare da aure
ba?" Ba ta dago kai ba bare yaga wani yanayi na tsorata ko razani game da jin furucinsa ba. Ta
dai yi bakam kamar an dasa dutse. Ransa ya baci ya dan daga murya cikin barazanarwa ya ce.
"Magana nake miki, ki ba ni amsa". Har yanzu dai ba ta tanka ba, sai shi ma ya yi shirun yana ci
gaba da tsare ta da idanunsa. Ganin ba ta da niyyar tanka masa ya sa ya ci gaba da cewa.
"Shuhuda ba ki kyauta ba, kin kuma zubar mana da mutumci duk da cewa kkanki kika yiwa illa.
A matsayinki na marainiya maimakon ki rungumi maraicinki da kyau, amma sai kika yi watsi da
kyakkayawar rayuwa. Shin wane rudin soyayya ne ya kai ki ga aikata wannan mummunan abu
wanda ko a fada ma akwai muni?" Har yanzu dai bat tanka ba, duk yadda ya so ta tanka amma
dai shiru. Ya kwantar da murya cikin tausayawa ya ce. "Isah ne?" Ta yi shiru, ya ce. "Ko Hamza
ne?" Nan ma tayi shiru, ya ci gaba. "Shi ke nan,Tashi ki je, amma na baki daga nan zuwa gobe
duk abin da ake ciki ki sanar min da wanda yayi miki wannan aika-aika”. Tayi shiru bat a mike
ba, kuma bata da alamar tashin, y ace, “Cewa nayi ki tashi ki tafi”. Kamar bad a ita yake
Magana ba, a’ah sai ya dan leka kansa ga fuskarta ya ga idanunta a rufe. Ya yi tsammanin kuka
ta ke, nan take tausayin maraicinta ya tsirga masa jiki.

Inna Yaduwa ta shigo dakin hannunta rike da kofin ruwa, ta ajiye a gabansa tana cewa, “Ta fada
maka?” Y ace “A’a amma abi a hankali, kamata ku tafi”.
Inna Yaduwa ta nufeta zata kamata da sauri Shuhuda tad ago kai tare da daga hannu. “Kada ki
taba ni, za ki kone idan kika taba jikina!” Inna Yaduwa ta dubi mijinta, shi ma ya dube ta cike da
mamaki, sai ta ja tsaki t ace.
“Wallahi ba hauka ba, kowace irin burkewa ce ba ki isa ki bata mana suna ba”.
Murmushi Shuhuda ta yi tun kafin ni tuni sunanku ya baci ko dan abu yana boye? Mhm, kuma
ku sani nib a tsatsonku b ace, ban hada komai da ku ba, taimako ne yasa na shigo cikinku,
kuma kun ki fuskanta. To amma masha Allahu tunda har wannan matakin ya sosa ranku har
kuka yi tunanin taron gangami, abin d azan muku matashiya da shi anan shi ne, tarkonku da
zaku yi don gano wanda ya yi min ciki said a taimakona don gudanar da taron a cikin sirri,
gudun idanuwan masu sirri kar su fuskanci sirri har su yi wani abu a cikin sirri kwatan-kwacin
yadda suka aiwatar da wani sirri a cikin sirri mai murdaddiya da tsuke tunanin duk wani mai
tunani.
A rayuwa ana so komai a yi shi cikin sirri, domin sirri abu ne mai matukar amfani” Gaba daya
daga cikin maganganunta babu daya na kamawa, illa tsabar rainin hankali da rashin kunya da
suke ganinta da su.
Alh. Rabi’u ransa y abaci, sai ya nuna musu hannu cikin daure fuska, y ace, “Na ce ku fice min
ko?” Idanuwan Shuhuda suka kawo kwalla rau-rau, ta durkushe a gabansa tana cewa, “Alhaji
don Allah, don Annabi ka yafe min idan maganganuna sun bata maka. Wallahi ni mai
taimakonku ce, ba kuma zaku yi nadamar taimakon da na ke muku ba”.Ta mike cikin azama ta
nufi kuskurawar dakinsa inda gadonsa yake, ta durkusa daga shi har Inna Yaduwan idanu suka
bita da su. Jim kadan tad ago tare da juyowa gaba dayanta dauke da wata roba wadda su duka
sun yi mamakin samuwar tata.
Ta durkusa a gaban Alh. Rabi’u t ace, “Ka ga wannan robar na tabbata ba kasan da ita ne a
cikin sirri, saboda kawar da idanun masu sirri. Wannan kadai zai iya zama shaida a gareku da
zaku aminta zamowata a cikinku RAHAMA ne, kuma taimakon rayuwarku ne”. Har yanzu ba
wanda ya fuskanci abin da ta ke nufi, illa zargin da suka dade suna yi akanta ya bijiro musu,
wato dai lokacin da aka haifeta jinnu sun yi musaya sun dauke asalin wadda aka Haifa sun ajiye
musu tasu ‘yar jinsun jinnu!
Shuhuda ta ci gaba da cewa, “Zan mayar da robar nan a inda ta ke don ci gaba da zama cikin
sirri gudun idanun masu sirri, sai dai ku sani duk iya duba idanunku ba zasu taba hango muku
inda take ba, tunda ita din an samara da ita ne a cikin sirri. Tunda ya kasance kun tsayar da
ranar taron gangami, ina ji it ace RANAR NADAMA! RANAR YAMMA! Wato ranar da kasuwa t agama ci, wadanda ke cikin kasuwar zasu waste!”
Su duka suna son yi mata Magana, amma sun kasa. Mamaki, tsoro, firgici, rudani gami da
damuwa duk sun mamaye sansanin zukatansu. Haka suna gain Shuhuda ta maida wannan
rufaffar roba inda ta daukota tukunna tga sa kai ta ficce daga dakin tana sharer kwalla a gurbin
idanunta. Bayan fitar Shuhuda sai aka shiga kallon-kallo tsakanin Alh. Rabi’u da Inna Yaduwa,
kowannensu da abin da yake son cewa dad an uwansa, amma sun kasa furtawa, sai dai kallon.
An kira Isah a waya cewar duk abinda yake ya tabbatar ya zo Kano karshen mako, hankalinsa
ya tashi ya shiga kiraye-kirayen lambobin kannansa don jin abin da yake faruwa, amma ba
labari. Nuraddeen ne dama yasan labarin shi kuma an gargade shi, don haka Isah ya kosa

matuka karshen makon ya zo ko ya je Kanon ya ji abin da kiran ya kunsa, yana addu’a kada
ace sanar masa za a yi an ba wa wani auren Shuhuda ba shi ba.
Shi kuma Uncle Hamza takanas Alh. Sada ya je har makarantar da nufin saduwa da shi, amma
bai tarar da shi ba, domin an ba shi labarin mahaifin Uncle Hamza wato Alh Babba ne ciwonsa
ya tashi a lokacin ma suna birnin Misra don nema masa magani. Haka ya baro makarantar jiki a
sanyaye ya dawo gida jiran zuwan karshen mako. The end
.
To bari mu gani me karshen makon zai haifar, da gasket din ne ranar taron zata zamo RANAR
NADAMA? RANAR YAMMA?
.
Ina shirye-shiryen makaranta, shi isa ban cika samun chance din typing ba, da patar zaku
cigaba da hakuri.
.
Sai ku biyo ni don jin karshen yadda zata kaya, taku har kullum Sadin Mama me kaunarku har
kullum
Ainihin marubuciyar wannan littapi Allah ya jink anta da rahama ya kara mata hasken kabari,
(ZAHRA’U BABA YAKASAI)
Hada Hausa Book stories
MATAU’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) BOOK 4
¤¤28¤¤
BABI NA SHA SHIDA
Tunda Isah ya shigo gidan ya ga wani sauyi, amma dai bai magantu ba, ya gaishe da Inna
Yaduwa ta amsa masa ba kamar yadda ta saba amsa gaisuwarsa ba. Sai yayi tsammanin ko
itace bata da lafiya aka yi masa wannan kiran gaggawan. Yayi murmushi yana dubanta y ace
“Yar tsohuwa mai ran karfe, hala hala lokaci ya yi ki ke neman yin gardama?” Ta yi masa shiru
illa wani irin kallo da take auna masa. Sam bai ji dadin hakan ba, y ace. “Wai don Allah Inna mai
yake faruwa ne/. ni fat un da Abba ya kirani hankalinaya gaza kwanciya, ga shi na iso na tarar
da sauyi atare da ke. Shin wani ne ba shi da lafiya? Ko kuwa na yi laifi ne b an sani ba? Idan
ma akan rashin zuwana net un bayan tafiyata Ibadan, wannan ai bai isa zama laifi ba, idan aka
yi duba ni sabon ma’aikaci ne”. Cikin kufula t ace da shi. “Idan don rashin zuwanka new a zai
damu? Je ka ma hakan dinne, asabar da lahadi suma ranakun aiki ne?..... Ture wannan, laifi
kam ai ka fi kowa sani tunda ka nemi tarwatsa farin cikin mu”.
Hankalinsa ya kuma tashi, idanunsa a waje y ace, “Ni din Inna? Me ya yi zafi haka shi ba wuta
ba?” sai tag a kamar ma ya raina mata hankali, ta ja baki ta tsuke bat a ko kara kallon inda yake
ba. Shi kuma abin day a sa shi shakku ken an, can ya nisa y ace, “Ina Shuhuda?”
Ta ce “ban sani ba, mugu kawai wanda ba shi da tausayi bare tsinkaye da maraici”.
Wannan gugar zana ce ta yi masa, atunanintsa ken an, duk yadda aka yi akan Shuhuda ne aka
yi masa wannan kiran gaggawan, yanzu haka akan ya katse mata waya ne duk ta bi ta tayar da
hankalin mutane, ashe dai tana sonsa, yawo da hankali ne yasa ta wulakanta shi a gaban wani
bare? Ganin yadda Inna Yaduwa ta ke amsa masa maganganunsa sai bai kara cewa da ita
kanzil ba, ya nufi sashensa, don lokacin Alh Rabi’u baya gidan. Amma zuciyarsa fal ta ked a
damuwa na rashin sanin tartibin kiransa. Da daddare bayan sallar Isha’I Alh. Rabi’u ya kira Isah

adakinsa, sai dai ya rasa ta inda zai kamo zancen. Isah ya shiga laluben laifinsa da har yasa
dattijon ma ya kasa cew da shi komai, anya kuwa laifin na katse waya ne? suka yi shiru tamkar
kurame, can da Isah ya ga shirun bai zai haifar dad a mai ido ba, sai ya magantu.
“Baba ko shakka bana yi, wani gagarumin laifi ne na aikata mafi muni tunda har kai ma ka gaza
ce min komai, amma don Allah ina rokon ku afuwa akan aikata laifi bias kuskure”. Alh. Rabi’u ya
jinjina kai y ace, “Lifi kam ka aikata, sai dai na kasa furta abin da na ke son furtawa duk da
cewar ga abin a raina, bakin ne yaki furtawa. Amma gobe idan Allah Ya kaimu lafiya za a yi
wani taro akan laifin da ka aikata da misalign karfe tara na safe”. Isah ya dube shi a kai-kaice y
ace “Allah Ya kaimu lafiya”.
Alh. Rabi’u ya kawar da hirar da cewa, “ya gurin aikin naka, da fatan dai babu wata matsala?”
DANKARI!
Ya ayyana a ransa, matsala kam akwai ta, sai dai ba zai so fadar wannan labari na al’ajab din
day a faru a zuwansa birnin Ibadan, don bai ga fa’idar fadar ba. Suka dan zanta tukunna ya
koma sashinsa.
Tun day a dawo bas u hadu da Shuhuda ba, hakan kuma bai dame shi ba.
.
Karfe takwas da mintina sha uku na safiya, Alh. Ahmad da Alh. Sada sun hahllara a gidan,
yayin da su Inna Yaduwama duk sun gama shirin day a dace na Karin kumallo. Shuhuda sai
wani irin farin ciki ta ke, sai ka ce ranar sallah, abin day a bai wa kowa mamaki kenan. Au
shidda suna a dakin Alh Rabi’u an ci an sha, ana shirin soma maganganun da suka assasa
tarin, maigadi ya doka sallama daga bakin kofar dakin. Alh .Ahmad ya leka yana lekawa yana
amsa sallamar, maigadi y ace, “Wani ne ya zo ya ce a fada muku Hamza A. Babba ne ya iso”.
Ya bi maigadin zuwa harabar gidan, Uncle Hamza yana jingine a jikin motarsa, sanye da farin
boyel day a sha dakakken aiki, fuskarsa na fitar da annuri. Alh. Ahmad ya ba shi hannu suka yi
musabiha, tukunna y ace. “Mu shiga daga ciki”.
Ya yi gaba, Uncle Hamza na binsa a baya, zuciyarsa na cike da farin ciki. Tunda ya samu sakon
nemansa da ake gidan su Shuhuda ya samu kansa cikin farin ciki, saboda tunaninsa magar
aurensu ce ta taso, don haka ya zabi zuwa gidan cikin farar shiga.
Koda suka shiga dakin, kowa ya bishi da kallo, gaban Isah ya soma dukan tara-tara ba ma
uku-uku ba, shi ken an zargin da yake ya zamo gaskiya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login