Showing 9001 words to 12000 words out of 83144 words
Chapter 4 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf
lura wannan tsohuwar kwararon so tayi ta shake masa wuya ya mutu? Yace
Shikenan a saurare ni zan bincika lamarin. Tace Ni fa gaskiya duk laifinka ne domin kai ka nuna
iyalanka ba su da gata a gurinka.... Ya daga mata hannu ransa a dan 6ace yace: Kinga ya isa
haka, kin fada min nace zan bincika ba shikenan ba? Ta mike tsaye. Ai don ka sani ne bazan
lamunta da dik wani iya shege ba. Duk wanda ya ta6a min 'yaya sai na ji dalili. Ta karashe
maganar tana kokarin fita. Ya bita da kallo kawai batare da ya tanka ba su dai korafi shine abin
yin su inda yake jin dadin karima kenan. Sam bata kawo mishi korafin wani, duk abin da zata yi
wanda zai sanya shi farin ciki shi take yi. Yana kokarin saka jallabiya ne karima ta shigo
hannunta dauke da kofin ruwa a hannunta. Fuskarta dauke da fara'a amma idonta kadai zaka
kalla kasan ta sha kuka. Tayi sallama ya dago kai ya dube ta shima fuskar tashi dauke da fara'a
ya amsa mata. Don Allah ka yi hakuri na tsaya yin sallah ne. Yace Kada ki damu nima sallar zan
yi. Ya gama zura rigar ya hau sallaya ya gabatar da sallah. Sai da ya gama tsaf ya zauna yana
murmushi. Me aka tanadar min ne? Ta tsiyaya mishi ruwa a kofi tace: Ga ruwa dai ka fara jika
makoshi, ai sai kayi Isha'i zaka ci abinci ko? Ya daga mata gira yayin da ya kai kofin ruwa a
bakinsa. Ya sauke kofin yace; Yauwa yau su waye suka zo gidan?
Sai taji gabanta fadi ya fadi tana da tabbacin an sanar dashi abinda ya faru. Tace: Su Inna ne
suka zo kawo wagga mu gaisa. Ya gane wadda take nufi saboda ba zaka ta6a jin bakinta ya
ambaci sunan Shuhuda ba. Yace Okay har sun koma ne? Tace Eh. Yace Mai yasa ba a bar
mana Shuhudan ta yi mana ko dan kwana biyu ba? Sai tayi shiru, a ganinta idan ta fada masa
kamar ta rura wuta ne do haka ta za6i yin shirun. Yace; Binta ta ce min an dan samu rashin
fahimta don Allah karima ku zauna lafiya da junanku ku daina daga min habkali. Rashin zaman
lafiyarku yana dagula min lissafi da hana min sukuni, ko fita na yi kullum da fargaba nake dawo
wa. Cikin kwantacciyar murya tace; Inshaa Allahu komai ya wuce. Yace: Na gode na sanki
mace ce mai biyayya idan don take za a yi tashin hankali to an dade ba a yi ba. To amma halin
su Binta yana iya sauya miki hali don haka don Allah kada ki yi koyi da halayensu, ki dinga
kawar da kanki garesu. Tace: To amma ni ma ina rokon alfarma. Don Allah kada ka kara yiwa
wani iyalinka wani abu daga gare ni. Idan sun gaishe ni kan su ba kara min lafiya gaisuwar tasu
zata yi ba haka rashinta ma ba zai rage ni da komai ba. Yace; Shikenan Allah yayi miki albarka.
Tace Ameeen. Karfe Uku na dare wani irin mummunan ciwon ciki ya murde MAS'UD ihu kawai
ya ke zabgawa. Sunusi kaninsa da yake kwance yana bacci shine mutumin da ya fara jin ihun
yayansa. Cikin tashin hankali ya tashi ganin halin da dan'uwansa yake ciki ya daga masa
hankali. Da sauri ya nufi cikin gida yana kwankwasa kofar mahaifinsu. Alh jamilu da yake bacci
ya tashi a firgice yazo bakin kofa yana tambayar; Waye ne? Sunusi yace; Abba ni ne. Yace;
Sunusi lafiya? Kafin ya bude kofar Sunusi yace;; Abba ya Mas'ud ne bashi da lafiya. Da sauri
Alh Jamilu ya bude kofar suka nufi dakin. Kwance shame-shame suka tarar da sunusi jini yana
madodawa. Iya tashin hankali Alh Jamilu ya shige shi ya rasa abinda zai yi. Yanzu wane asibiti
za su nufa? Dare ne karfe uku na dare da wuya a samu asibitinb da za a tarar da likita. Ya tuna
yana da wani aboki likita don haka da sauri ya dubi sunusi yace; Maza je ka dakina ka dauko
min wayata. Sanusi ya nufi dakin, tare suka dawo da karima wadda a lokacin ta farka saboda
girkinta ne tana dakin Alh jamilun. Sunusi ya mikawa mahaifinsa wayar ya kar6a ya soma
lalubar lambar yayin da karima take sallallami ganin halin da mas'ud yake ciki. Bugun farko dr
Musbahu ya dauja saboda a lokacin yana kan na'ura mai kwalwa(computer) yana binciken
wasu cututtuka. Suka gaisa Alh jamlu ya sanar da shi halin da ake ciki. Dr musbahu yace; ga
shi nan zuwa. Amma kafin dr. Musbahu ya karaso gidan tuni Mas'ud yace Ga garinku nan. Anin
da ya daga hankalin Binta ke nan ta dinga kwarara ihu cikin daren shi kam Alh jamilu daukar
gawar Mas'ud yayu ya kai dakinsa zuwa safiya a suturce shi don sadar da shi makwancinsa.
****** ***** ********
BABI NA UKU ------------- ------------ ------------- AL'AJAB ---------------
-------------------------- Shuda ta soma zuwa makaranta inda ta ke a firamare(primary) Yarinyar
Allah ya zuba mata kwalwa da fahimtar gane abu zai yi wuya a fada mata abu ba ta hardace shi
ba. Matsalarta daya wani lokaci kamar gidi-gidi(marar hankali) take. Tana samun kulawa ga
dan'uwanta Isah wata irin shakuwa ce a tsakaninsu ta yadda idan daya ya yini ba tare da daya
ba to lallai zaka samu dayan cikin rashin sukuni. Tun lokacin da abin nan ya faru wato dukan da
mas'ud ya yi mata ba a sake kaita gidan mahaifiyarta karima ba, to ita ma yarinyar sai Allah ya
sa ba wani damuwa ta yi da akai ta gidan ba. Sai dai ita kariman ta kan zo duba ta shima ba
sosai ba, don ma dai hakkin uwa. A haka ta shiga aji shidda na firamare a lokacin ne kuma Isah
ya kammala karatun sakandire(secondry) dinsa don ma ya samu matsala ne a sanadiyyar wata
rshin lafiya da yayi kamar ba zai rai ba. Sai da ya share wata daya a kwance sannan ya warke
don haka aka maido shi baya tinda bai zana J.S.C.E ba. Mahaifinsa Alh sada ya sama masa
gurbin karatu a kasar senegal san Isah bai si hakan ba domin yaso ace a nan gida Nigeria ya yi
karatu saboda ya dinga ganin gudan jininsa Shuhuda, amma ina! Hakabsa ba zata cimma ruwa
ba lokacin da ake shurye-shiryen tafiyarsa, ba shi kadai ba ita kanta Shuhudan hankalinta a
tashe yake duk ta zabge ta ramr sau an yi da gaske take iya cin abinci. Suna zaune su uku a
falo Inna yaduwa ta dubi Isah tace: Ni fa wannan rama da kuke tana ba ni tsoro daga zuwa
karatu duk zaju bu ku tayar da hankalinku haka. Isah yae Wallahi Innada za a bi tawa ni dai a
fasa tafiyar ma sam bana sonra. Ta dube shi cike da mamaki tace; Ko akwai dalili? Yace Eh
Inna kinga na farko a ra'ayina na fi son ba yi karatu a kasarmu Nigeria, sannan abu na biyu......
Ya dubi Shuhuda tare da nunata da dan yatsansa. Ina so na zauna jusa da 'yar uwata. Inna
yaduwa tayi dariya tace; Ka kai su dai in kaya ne. Idan ma don wannan kwailar yarinyar ne zaka
damu kanka ka bari domin ko kana nan ba zan bari ka aure ta ba, gwara ma ka tafi kayi
karatunka. Shima ya dan yi takaitacciyar dariya yace. Haba dai aike ma ba kya fara ba. Kuma
bari ganin zan bar kasar nan ni na tabbatar har naje na dawo ina nan cikin zuciyar Shuhuda ko
ya kika ce tawan? Shuhuda da ba tasan inda maganarsu ta dosa ba ta gyada kai. Isah yayi
dariya yace: Aha ni dama nasan ba mai shiga tsakanina da tawan. Inna yaduwa tace To na ji
amma don Allah ku sabya hakuri da nutsuwa a zukatanku ka dai ga inda zaka je kuma ba don
komai zaka je ba sai don karatun nab don haka ka mayar da hankali ga abin da ya kai ka. Isah
yace: Inshaa Allahu Inna zan yi karatu har sai na ga karshen biro da mai jan kunne. Ya karashe
maganar yana dariya ita ma dariyar ta yi tukunna tace: Sannan kuma don Allah ban da kula
masu jajayen kunne don ba ma zamu bari ka dauko mana jikanyar paparoma ba. Dariya ya
sake yi ya mike tsaye: Mhm kaji Inna tana tsoron mai jan kunne ta kwace mata miji, ke shuhuda
tashi muje gida Baba na kirana. Suka fice suka bar Inna Yaduwa tana tunanin yaran sun hada
kansu Allah yasa su dore a haka har zuwa girmansu. Tayi musu kwadayin zama ma'aurata. A
ranar da Isah zai tafi Senegak da kyar aka 6am6ari Shuhuda daga jikinsa yana kuka ya hau
jirgu dole aka sakata a mota aka juya zuwa gida ba tare da sun ga dai-daituwar jirgin a sararin
samaniya kamar yadda suka sa tsara ba, Tun bayan tafiyar Isah kasar Senegal Shuhuda ba ta
da sukun sai anyi da gaske ta ke cin abinci. Sai da aka samu ta saka dangana a ranta, ta dinga
cin abinci da walwalarta, sai dai wannan matsalar ta rashin wadatuwar hankali na nan har
yanzu a tare da ita. Yadda abin nata yake idan ka dube ta ba zaka ce tana da wata matsala ba
saboda a hutse ta ke, amma wani lokaci da ta yi magana zaka fahimci akwai shirmr a cikinta.
Jarrabawarsu ta fito ta ci makarantar kwana ta shekara. Amma sam Alh Sada yaki don haka ya
samo mata gurbin karatu a makarantar kudi mai suna AJURI MEMORIAL SCHOOL. Ta fara
karatun ka'in da na'in dama can dai Shuhuda yarinya ce mai kwanya, to har yanzu din ma dai
tana ta6ukawa. Mace ce mai nacin tambaya shi yasa malamai suke sonta saboda nagartar yaro
makaranta ya kasance mai yawan tambaya da naci akan komai. Hutunsu na farko Shuhuda ita
ta yi na goma cikin su talatin da biyar dake ajin. Kasancewarta bahaushiya kuma wadda bata da
cikakken hankali kamar yadda 'yan ajin nasu suke gani, sun sha mamaki matuka ganin cewa
wannan karamar yarinyar ce tayi na goma. Ba su sake samun wani mamakin ba, sai da aka
sake yin jarabawa, a wannan karon na uku Shuhuda ta dauka. Kwalwar Shuhuda tana da ban
mamaki joda yake babu mamaki ga lamarin Allah. ********** ******** ********** Haj. Karima tana ci
gaba da zaman hakuri a gidan mijinta amma dai abinn da sauki don ma sai da Alh Jamilu ya
tsawatar sosai. Binta cewa tayi Karima mayya ce ita da 'yarta sun lashe mata kurwar da. Da
farko habaice-habaice ne take yi har dai daga baya ta fito fili ta bayyana manufarta. Ai kuwa duk
yadda Karima ta ke da hakuri sai da maganar ta kai ta bango ta shiga daki ta soma hada
kayanta, a dai-dai lokacin ne Alh Jamilu ya dawo gidan. Tambayarta yake abinda ya faru ya ga
tana kuka ga kaya kuma tana hadawa amma ta kasa magana kukan kuma ya ki tsayuwa yi
kawai take zuciyarta na kuna. Da yaga bata da niyyar tanka masa sai ya samu gefen gadonta
ya zauna ya zuba mata ido har ta kammala shirya kayan ta saka hijabinta ta janyo jakar zata
fice daga dakin. To a lokacin ne ya yi zumbur ya mike ya sha gabanta yana kallonta ido cikin ido
yayi karfin hali yace: karimatu tun da na aure ki ban ta6a samun ki mai yin wani abu ba tare da
izinina ba. Shin ina zaki da kika hada kaya wani ne ya rasu? Ta girgiza masa kai Yace; To mai
yasa kika za6i datse zamanki a gidana? Wani laifi na yi miki? Ta sake girgiza kai yace: Ki fada
min damuwar ki ta dai yi shiru ta kasa cewa komai ya ja hannunta ya zaunar da ita akan gado
yace;
Jirani ina zuwa. Ya fice zuwa dakin Hassu matarsa ta biyu. Tana zaune a dakinta tana zaune a
dakinta tana karatun wani littafin Hausa yayi sallama ya shigo yace:
Hassu me ya faru a cikin gidan nan bayan ba ni nan? Ta tashi zaune daga kwancen da take
akan doguwar kujera ta yatsina duska tace: Eh rigima ce ake yi wai Binta ce tace: Karima
mayya ce, su suka lashe mata kurwar Mas'ud.
Yace Subhanallahi. Sai ya mike tsaye ya nufi dakin Binta. Kwance take akan gado yace. Binta
kin kyauta shi dai jaki duk yadda aka yi da shi sai yaci kara. Ta yunkura ta tashi zaune fuskarta
a daure tace: Kana nufin ni ce jaka?
Yace Eh ai abin da kika yi ko jakar ma ba zata yi ba. Banda jahilci da duhun kai ta ya Allah ya
amshi ran Mas'ud zaki ce Karima mayya ce sun lashe miki da? To bari ki ji wallahi na gaji da
munanan halayenki baki isa ki ja min surutu da bakin jini ga al'ummar gari ba.
Ta watsa mishi wani mugun kallo tace:
Dole ka zoi ka yi ta yi min hargowa tunda an ta6a 'yar gwal mowar mata. Karya ake mata ba
mayyar ba ce? Idan kai ba ka sani ba ni na samo cikakken tarihinta karima mayya ce ita ta
lashe mijinta haka wata mata daga ta tsarga hannun 'yarta ta lashe ta saboda muguwar maita,
don bakin cikin zata yi mata lahani a jininta, sannan ta lashe Mas'ud. Sai a hana ni fada? To na
fada karima mayya ce a yi yadda za ayi da ni....'
Ba tasan ya aka yi ba sai dai ganin wasu taurari ta yi suna walainiya a cikin idanunta
sakamakon kyakkyawan marin da Alh jamilu ya dauke ta da shi. Yana huci ya cigaa da cewa;
Maza ki fice min daga gida, zama da ke annoba ne har kullum ba za a ta6a jin alkhairi a bakin ki
ba dai sharri. Ba tayi mamaki ba domin ta lura mijin nata ya zauce akan wannan afiruwar matar
tasa. Ita kam ba inda zata kuma ba zata ta6a barin jinin danta ya tafi a banza ba.
Alh jamilu ya cigaba da cewa; Kuma wallahi kika sake furta maganar nan ga wani sai na sa an
kulle ki, mutumiyar banza marar hankali. Cikin dakewa tace da shi:
Idan kasa an daure ni ka jefa mukullin cikin kogin maliya zama daram kuma a cikin gidan nan
ban ga 'yar isakar macen da ta isa ta fitar dani ba.
Yaja wani dogon tsaki ya fice daga dakin ya barta tana kananan maganganu.
Ya tarar da Haj karima har lokacim kuka ta ke. Ya zauna kusa da ita ya soma share mata
hawayenta yace:
Don Allah ki yi hakuri karima an fada mim duk abin da ya faru.
Ta yi shiru bata tanka ba. Zaman gidansa ya fice mata a rai saboda tunda ta shigo gidan ba ta
da kwanciyar hankali. Yau dai hakurinta ya kai gaci a ganinta gwara ta kauce masa ko matansa
sa samu sarar tunda dama tunda ta zo gidan ba ta nasa ko kwai ba bare dan adam. MAITA? Ai
kalmar ta yi mata nauyi ba ko a kai ba. A'a a dukkan sassan jiki da ma rayuwarta gaba daya. Ta
matse hawaye tace dashi; Alhaji ka yi hakuri amma na hakura da zama gidanka ka yi hakuri. Ya
tsura mata ido cikin tsananin tausayi yace: A'a karima kar mu yi haka dake. Ki fahimce ni, ni
nake aurenki , zamana kike..... Karo na farko yana magana ta katse masa hanzari tunda take
da shi. Zamanka nake amma kuma zaman matanka tunda suna juya ni kamar waina a tanda.
Yace: Hakane ban ce kin yi karya ba amma ki yi hakuri komai yazo karshe tunda na sauwakewa
Binta. Dama ita ce matsalar gidana don ta Hassu za a iya zama da ita. Da sauri karima ta mike
tsaye maganarshi ta dakar mata zuciya sosai ta soma girgiza kai. A'a Alhaji ka maido Binta, tare
na tarar da ku ni na fi dacewa da wannan hukuncin domin zuwana ne ke neman hargitsa
zamanku. Yace Ba zuwanki bane karima dama can Binta 'yar butsu ce hakuri kawai nake da ita.
Karima tace Yanzu din ma hakurin zaka ci gaba da ita. Yace Hakurina ya kare. Tace Ni ma
nawa ya kare don haka ina so ka maido matarka. Ya cika da mamakin yadda yau karima ta ke
sa'insa da shi. Matar da ta kasance magana daya zai yi ta zauna, babu jayayya ko rashin
amincewa amma yau sai ga akasin haka a tsakaninsu? Yace Wallahi kinji na rantse Binta ba
zata zauna min a gida ba ke kuma dole ki zauna. Ya karashe maganar cijin bayar da umarni.
Sai ta duke ta sunne kai a kasa tana rusar kuka shi kuma yayi am fani da kaifin basisararsa a
matsayinsa na jangwarzo ya rarrashe ta da tausar zuciyata. Mata har kullum rauni garemu don
haka zuciyarta ta yi rauni ta aminta da ci gaba da zaman gidan mijinta. Wannan ke nan!!!!
***************
************** A kwana a tashi Shuhuda ta shiga aji hudu na sakandire karatu ba kama hannun
yaro kowanne malami yana alfahari da ita saboda kwazonta da mayar da hankali akan karatu.
Ranar litinin bayan an gama assembly kowanne dalibi ya shiga aji don daukar darasi. Shuhuda
na zaune a mazauninta a kujerar karshe ita da abokiyar zamanta mai suna Sa'adatu. Kowanne
dalibi ka duba karatu yake kafin malami ya shigo dama haka al'adarsu ta ke ba ka ta6a ji dalibai
suna hayaniya irin na sauran makarantu. Amma banda Shuhuda da ta yi tagumi ga dukkan
alamu tana cikin yanayin nata. Wani malami ya shigo gaba daya daliban suka mike tsaye don
girmamawa a gare shi banda Shuhuda wadda ba tasan da shigowarsa ba. Ya amsa gaisuwarsu
ba tare da ya lura da rashin mikewar Shuhuda ba Ya ba su umarni da su zauna. Bayan kowa ya
zauna ya gabatar da kanshi a gare su a matsayinsa na sabon malamin da zai dinga daukarsu
darasin chemistry. Ya duba littafan wata daliba da ke kujerar gaba ya ga inda suka tsaya a
karatunsu sai ya dora da yi musu karin bayani. Ya ji dadin yadda ya same